Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda ka yi da safe. " Ya ce." Ai ba zan iya bacci ba idan ban yi shi ba Amina, kada ki damu bari na yi na fito ki kawo mini abinci."
Na ce." To a sanyaye na fito na bar shi a toilet din na sau'ka kasa cikin 'yar damuwa ya jima kuwa bai kwanta ciwo ba tun bayan zazzafar murar da ya yi a gidana sakamakon ruwan saman da ya dake shi a shekarun baya.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *Gudun aure paid book. 2k complete on telegram. What'sappa Gruop 1k Via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*121*
Lokacin da na koma d'akin bai fito ba na zauna ina jiransa ya fito a rikice da d'ari irin na zazzabin ya sake ninkuwa kaya masu d'an kauri na d'auko masa ya kar'ba yana ko'karin sanyawa ya ce na d'auko masa hular sanyi duk a cikin kayan nasa ina fad'in." Abinda nake ta gudu kenan. Ya gama sanya kayan jikinsa ya zauna gefan gado cikin yanayi na ciwo da kaina na shafa masa basiline a jikinsa gabad'aya. Ya sanya hular har ta rufe kunnuwansa. Kafin na fara zuba masa abincin ya d'auki wayarsa ina jin ya kira likitansa ya yi masa bayani ya bashi tabbacin cewa gashi nan zuwa yanzu.
Cokali biyu ya iya ci na abincin ya dakata. Gabad'aya ni ma sai na ji zazzabin yana nema ya rufe ni. Babu zato ba tare da tsammani ba na ji yana fad'in." Kira mini Hauwa a wayarki Amina."
Da mamaki mai yawa nake dubansa. Ya d'an lumshe idonsa kafin ya bud'e yana gyad'a mini kai.
Ban iya cewa komai ba na tashi a hankali na sauka kasa da nazari a k'wanyata. To ko dai an daidaitasu ne ban sani ba wata'kila kafin mu fito daga d'aki ni da Sahura mahaifiyarsa ta zauna dashi akan hakan zuciyata ta dinga yi mini sa'ke-sa'ke. Na koma d'akin na same shi a takure a gado ga blanket din bai rufa ba.
Na zauna tare da rufe masa k'afafunsa har zuwa saman kirjinsa sannan a tsanake na fara neman layin Hauwa. Bugun farko ta daga ta kama sunana. Na amsa kafin mu gaisa ban ji ta sake yin gaisuwa ba kawai ta yi shiru sai na daure na ce." Maigidan ne yake son magana dake?"
A yatsine tace." Kamar yaya menene a tsakanina da shi, kuma ai yana da lambata mai ya sanya sai kece za ki kira ni.''
Na danne b'acin ran da nake ji yana taso mini na furta." Haka dai ya ce ni na kira ki Hauwa."
Ta ja siririn tsaki wanda ya yi mini ciwo sosai a rai amma ban katse wayar ba na mik'a masa yana daga kwance don bai tashi ba ya kar'bi wayar yasa a kunnansa. Sunanta ya kira ta amsa a dakile.
Ya d'an yi jim ban sani ba ko yana jiran gaisuwarta ne ko kuma yana jiran ta yi masa ta'aziyya ko daya dai ba ta yi ba.
Ya furta." Kina lafiya ko?''
"Umm" Ta ce cikin basarwa. Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya furta." Idan kin ji wani canji ko yaya ne a jikinki kada ki yi shiru."
Na yi zugum ina kallonsa da mamaki wai yau Hauwa yake rarrashi har yana fad'in idan ta ji canji na ciwo a jikinta kada ta yi shiru ta sanar da shi. Duk ina k'iyayyar da yake fadin yana yi mata. Mamaki ya kasa bari na janye idona daga kansa har sai da suka yi sallama ya miko mini tare da lumshe idonsa. Na daure ina fad'in." Alhamdulillahi na ji dadin wannan abin da ya faru, Ina fatan Allah Ya sa ya zama na karshe."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Ni ma na yi shiru ina d'an duba wayata sai dai can kasan zuciyata wani takaici ne na dinga tunanin daga ina yake ai ni nake so Hauwa ta dawo mu cigaba da zama to mai zai sanya don ya yi waya daya da ita yau na ji haushi idan hakane kuwa gaskiya zuciyata bata kyauta mini ba.
Ban iya tashi na fita daga d'akin ba har sai da likitansa ya zo ya duba shi sosai ya yi masa BF domin yana kuka da ciwon kai sosai jininsa ya haura amma ba sosai ba, dama kuma yana da hawan jinin sai dai ba kasafai yake tashi ba sai da damuwa kamar shakarun baya da ya motsa masa lokacin ina amarya yana neman hanyar da zai samu kaina ni kuma na'ki bada fuskar hakan tun zamana na farko Legos kenan a iya sanina tun daga lokacin bai kara motsa masa ba sai yanzu.
Suka yi sallama yana fad'in " Za su tafi da Sukairaju yanzun domin ya bashi magungua. Ya ce mini lallai ya ci abinci sosai kafin ace ya sha maganin.
Da kyar da jibin goshi kamar wani yaro ko d'an yayen da yake rigima ya ci cokali biyar bayan biyun da ya ci da farko yana fad'in bakinsa babu dad'i, ba zai iya ci da yawa ba. Haka nan na ha'kura na kyale shi tunda iya naci da magiya na yi masa akan ya kara yace a a.
Sukairaju ya kawo magunguan ya tsaya ya yi masa sannu kafin ya fita. Na duba kowanne akwai yadda za a ba shi.
Na dube shi idonsa biyu rufe idon kawai Yayi kamar mai bacci.
Na ce." Ka tashi kasha maganin to."
Bai yi mini jayayya ba ya tashi na d'auki ruwa na tsiyaya a cup na mik'a masa ina ciro maganin ina bashi yana sha tsaf ya gama ya ajiye zai kwanta na ce." Ka dan bari ya fad'a maka." Bai ji ba ya yi kwanciyarsa minti biyu kuwa sai yun'kurin amai. Ya tashi da azama ya nufi toilet ya fara watso shi duk abincin da yaci da maganin da sha suka yo waje.
Na rasa yadda zan yi gabad'aya damuwa ta dabaibayi ni. Haka nan na tarairayo shi muka fito ya je ya kwanta ya nishi. Na lura baya son ciwo kuma bashi da wani dauriya idan bashi da lafiya haka ya yi mini lokacin da ya kwanta ciwon mura a gidana na kuntau na sha dawaniya.
Toilet na gyara na fito na same shi bacci ya d'auke shi sosai. Aikuwa ba zai yiwu ba, tashinsa na shiga yi ya bude idonsa na ce." Dole fa sai ka tashi ka sake cin wani abincin da maganin idan yaso sai ka yi baccin."
Bai ce komai ba ya gyara kwanciyarsa ya rufe Ido.
Na ce." Ka tashi don Allah ka ji.''
Ya yi mini shiru bai motsa ba. Kawai sai na zuba masa ido tsabar takaici da damuwa na ce." Shikkenan gaskiya zan sanar da Hajja an ta'ba yin ciwo ba cin abinci da magani."
Ya bude idon yana kallona yace." Wai ba na ci ba ne?".
Na ce." To nawa yake wanda ka ci, kuma duk ka amayar dashi da maganin."
Ya tashi zaune tare da tallafe ha'barsa. Sosai na zura masa ido ina nazarinsa sai nake ganin kamar bayan ciwon da yake damunsa akwai wata damuwar. Zuciyata ta fara raya mini ko ya fara kewar matarsa ne da ta rasu. Wani sashe na daban yake ce mini 'Anya kuwa' ai an yi masa mace-mace da yawa ya ha'kura kuma bai ta'ba yin wani ciwo ba, kawai dai ciwon ne ya zo masa akan ga'ba ne.
Nasa hannu na cire hannunsa da ya tallefe ha'barsa da shi a d'an sanyaye na ce." Wai menene don Allah, kada ka jefe ni cikin tashin hankali, yau kana tallafe ha'ba ko akwai wani abu da yake damunka?"
Ya dube ni. Muka tsirawa juna ido sosai mun jima a haka bai ce komai ba sai ni na janye idona na sake zubo masa abincin da kaina na dinga bashi cikin ikon Allah kuwa ya ci da yawa da kamar minti goma tukkuna na sake bashi maganin a karo na biyu, ban yarda ya kwanta ba sai da muka yi zaman kimanin minti ashirin har ya fara gyangyadi sannan ya kwanta ni kuma na sauka k'asa.
Na samu anti Yagana ta jima da yin bacci. wanka na yi a gurguje na sanya kayan bacci tare da a turare a jikina na koma saman. Lokacin baccinsa ya yi nisa sosai, na shiga cikin bargon kusa dashi sosai na kwanta kafin na fara yin addu'ar kwanciya bacci.
Da asuba da d'an kuzari ya tashi domin ya riga ni ma tashi motsinsa na ji a bandaki na yun'kura da sauri na dira daga gadon domin ina tsoron ya ce zai watsawa jikinsa ruwa. Na same shi yana alwala sai na sauke ajiyar zuciya na tsaya har ya kammala tukkuna ya fita zuwa massalaci sannan shiga toilet din sosai domin yin nawa uzurin.

Tun bayan da ya fita da asuban bai dawo ba sai wajejan goma da arba'in na safe. Na d'an shiga yar damuwa saboda yanayin jikinsa. Amma nasan abinda ya zaunar dashi bai wuce yin addu'a ba kamar yadda aka yi duk ranar da mamaci ya cika kwanaki uku da rasuwa.
Anti Yagana Hajja da inna Uwani Gwaggo sun shirya tsaf da Shirin tafiya muna falo da su gabad'aya domin jiran shigowarsa Kamalu ya riga shi shigowa da kusan minti goma kafin ya shigo.

idan kin karanta ba ki biya ni ba ina bin ki bashi.

Cikinmu ya zo ya zauna kujera kusa da ni. Suka gaisa sosai. Hajja ta gaya masa tafiya za su yi. Na d'auka zai ce su yi hakuri su bari ayi bakwai sai bai nuna damuwarsa akan hakan ba ya ce ." Ita anti Yagana ta bari zuwa an jima kadan Sukairaju ya dawo sai ya d'auketa a mota ya kaita har gida. Hajja kuwa dama a babbar mota suka zo da direbanta duk zai kwashe su har Hajiya Saratu Kamalu da Yusi da Shima shigowarsa kenan yanzu a lokacin da suke maganar cikin shiri tunda ya san da tafiyar tun jiya 'dan uwansa ya gaya masa
Cike da damuwa muka yi sallama na kasa daurewa sai da na yi kwalla na d'auko hijabi muka bi bayansu harbar gidan ni da anti Yagana har sai da suka shiga mota suka tafi tukkuna muka koma cikin gidan.
Anti Yagana ta koma d'aki ta kwanta jiran dawowar Sukairaju kamar yadda maigidan ya fad'a.
Na bi shi saman na same shi a kwance.
Na zauna a d'an sanyaye ina fad'in." Ina kwana?''
Ya tashi zaune yana amsa da kulawa tare da tsira mini ido. Tun jiya yawan kallon nan da yake yi mini ya fara damuna."
Na ce." Ji ki ya yi sau'ki ko?"
Ya gyad'a kansa yana fadin." Alhamdulillahi, na ji sau'ki ina godiya."
A tak'aice na furta." Me za ka ci yanzu?"
"Shayi kawai zan sha idan da hali a yi mini farfesun kifi bakina babu test ko daya."
Na ce." Da hali mana da kaina ma zan yi maka sai ka had'a da bread ko?"
A tak'aice ya ce." Amma fara had'a mini tea din."
Na tashi na sauka kasa kicin na nufa Baba Tabawa tana ta gyare-gyare tare da wanke kwanunan da aka yi karin kummalo na hada duk abinda zai buk'ata na kai masa.
Na sake komawa kicin din Baba tana fad'in na bari ta yi na ce mata a a kawai ta bari ta huta jiki da jini tun asuba take tashi tunda aka yi rasuwar nan ga hidima da Sultan dama wani lokacin yana hannun inna uwani ko Gwaggo.
Farfensun ya yi masa dad'i sosai kuma ya sha da yawa ya hada da bread har da gyasa Yana fad'in." Ya yi mini dad'i sosai na gode."
Na ce." Sai shan magani?"
Ya gyad'a kansa yana dan murmushi na dinga cirowa ina bashi daya bayan d'aya ya sha. Sannan ya kwanta yana. yi mini godiya.
Sai wajan sha biyu muka yi sallama da anti Yagana wai ita da ta zo gaisuwa har sai da ya bata kudi bayan sanyawa da ya yi a kaita. Tare muka fito har da shi muka yi mata rakiya Sukairaju ya d'auketa a mota tana d'ago mana hannu.

Gidan ya kasance shiru kowa ya watse gabad'aya ma area ta yi tsit kamar ba a yi wata hada-hada ta jama'a ba tunda zahirin gaskiya ta samu mutane wannan kuma yana da ala'ka da su waye mazajen da ta aura da kuma fannin kasuwancinta sai danginsu daga can jos din da suka dinga zuwa.

Tun da ya yi sallar azuhur ya kwanta sai daf da la'asar tukkuna na tashe shi. Ya tashi kuwa da kuzari sosai ya ce zai yi wanka na ce a a tunda la'asar ce babu kyau haka annabi ya ce. Kuma gashi ba shi da lafiya.
Yana d'an murmushi ya ce." Ban ta'ba jin wannan hadisin ba Amina, sannan a ina aka ce idan mutum ba shi da lafiya ya daina wanka, ba zan iya ba gaskiya."
Na b'ata rai ina fad'in." Wallahi haka aka ce babu kyu wankan daf da la'asar da bacci. Sannan kuma duk mai zazza'bi bayan son ruwa sai ka ga ciwon ya sake tsananta ka manta jiya kana zubawa jikinka ruwa ya rikice."
Ya ce." Kwarai kuwa hakane amma ai yau gabad'aya ban yi wankan ba fa tun safe kin ga kuwa babu lefi don na yi yanzu, tunda na ji sau'ki gaskiya."
Na ce." Kadai bari sai da daddare idan za ka kwanta."
Bai ce komai ba ya nufi toilet din ba bi shi a baya sai naga yana burush ina tsaye ina kallonsa ya gama ya daura alwala ya fito.

To a daran ranar can gidan Hajiya Maryam dai ba su rintsa ba duk da an cire rumfuna kuma maigidan ya sallami kowa amma su anti Yabi ba su tafi ba. Ita Nabila dama ta ci alwashin zama domin ta cigaba da kula da yaran. Anti Yabi Saliha da Rukky da shi Bashir din suka zauna wai sai an yi bakwai sai gidan ya kasance sai su kadai da masu aiki Taburni da Mairo sai yara Khalil Twins da Minal da suke hannun Mairo domin itace jigon kula da su shi Khalil yana tare da Adam tare suke kwana dakinsu daya itama Nusaiba tana nan ba ta tafi ba tukkuna.
Talatainin dare wajan biyu da yan mintina duk sun yi bacci Bashir ya kusa kansa d'akin da suke kwance wanda ya kasance nan ne bedroom din Maryam din matattarar sirrinta anan suke ta dabdalarsu. Anti Yabi da Saliha sun yi washar da su a makad'ed'an gadonta suna ta bacci yayin da Nabila ke kwance kasan kafet ita kuma Rukky na can kan wata shirgegiyar kujera dake can gefa bacci ya shammceta ta bar wayarta a kunne tana yi kallo take yi wata'kila baccin ya cimmata.
A kan Nabila ya tsaya yana fad'in." Ta shi, ke anti Nabila."
Ta tashi zumbur ta ganshi a tsaye dogare a kanta ta ce." Baka da hankali za ka shigo mana a wannan daran wai Bashir me yake damunka ne?"
Ya ce." Na gaya miki tun muna sheda juna ku sallame ni na ware, idan ba haka ba wallahi sai na yi muku illah."
Ta mutsika idonta sosai tana fad'in.'' Dame zan sallama ka Bashir na rantse da girman Allah zan yi magan..... Ba ta krasa ba ya fille 'yar k'aramar askar da take hannunsa mai bala'in kaifi ya yi mata bille a kumatu gefan idonta. Cikin tsananin kid'ima da tashin hankali ta kurma ihu! jini ya mamayeta fuska tunda askar ta shiga sosai kuma ta samu tsokar kumatu.
Gabad'aya suka tashi zaune.
Ya dinga bin su daya bayan d'aya yana fad'in." Illa zan yi muku na rantse da girman Allah idan ba ku fito da abinda yake rabo na ba kun ba ni, shegu yan iska taron tsintsiya babu shara, wallahi zan tsinke miki yatsun hannunki anti Yabi."
Ya dumfareta a zabure yana rangaji da askar a hannunsa mai la'kanin gayawa jini na wuce.... Suka yi tsuru-tsuru ganin yadda fuskar Nabila ta yi gaja-gaja da jini tana ta kuka.
Anti Yabi ta nuna masa kusa da ita tana fad'in." Zo ka zauna nan kusa da ni Bashir mu yi magana ka ji ko, kada ka sake illata kowa a cikinmu mu din 'yan uwanka ne.''
Ya yi rangaji yana wani abu da hannu kafin ya dumfareta a karo na biyu yana fad'in." Ku ba ni abinda yake hakkina kawai na tafi tunda dama kun sallamawa duniya ni.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


**Gudun aure paid book complete 2k akan telegram. Normal Gruop wsp 1k via 0542382124... Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*122*
Da farko har ya zauna kusa da ita kamar yadda ta buk'ata sai kuma ya tashi zumbur ya fara d'urawa Rukky ashariya yana fad'in ta daina kallonsa. Anti Yabi ta dinga jan hannunsa tana zaunar dashi yana fizgewa tare da ko'karin zuwa inda Rukky take domin dama can sakuwarsa ce kuma abokiyar fadansa.
Da azama ta d'auki wayarta ta fice daga d'akin cikin tashin hankali don ganin kamar itama yana so ya yi mata lahani.
Yabi ta fara fadin." Babu komai na kudi a d'akin nan Bashir tun daran jiya mun binceke komai sai sutturunta kai kuma namiji ne me za ka yi da kayan mata. 'Yar ta Nusaiba ce ta kwashe duk abinda muke hankoro ta boye sai waccan munafukar Nabila itama tana daya daga cikin wad'anda suka san sirrinta amma saboda ba'kar mugunta ta'ki ba mu goyon baya. Da tun farko ta amince mana da duk haka ba ta faru ba ni kaina a cikin wannan nazarin nake ace an watse ba mu tashi da komai ba."
Nabila na kuka take fad'in." Anti Yabi ba kya ganin abinda ya yi mini lefi ma ki ke ba ni, kina ganin yadda ya yanka min kumatu amma duka baku da damuwa."
Saliha tace." Ke ma kin so haka ta faru Nabila tuntuni muke miki magana kina nuna ke ba ki san komai ba bayan na tabbatar da cewar mukkulin dirowar can yana hannunki mugunta ce ta sanya ki boyewa tunda gashi kina fad'in za ki zauna a gidan. Ina yaran suke da za ki ce zaki kula dasu duk sun zama samari. Su wad'anan 'kananun dole ubansu ya mayarwa da iyayensu Nusaiba kuma ba zama za ta yi ba itama gidanta zata koma, kina so mu tafi sai ki yi wad'aka da dukiya ko to ai duk cikinmu babu yaro mun fahimci me ki ke nufi ."
Yabi ta ce." Tunda abin ya fara zama haka Nabila ki fito da key din dirowar nan nasan anti Maryam a cike take ajiye sirrikanta wata'kila zamu samu gwalagwalanta a ciki da takardun shagunanta da ta mallaka sai mu d'auki wani abu daga ciki mu kasafta a tsakaninmu.."
Cike da damuwa da jin rad'adi ta furta." Ban san inda key din nan yake ba anti Yabi ko ku yarda ko kada ku yarda wallahi ni ma ban d'auka ba. Wayoyinta da ATM dinta suna hannun Nusaiba to key din ma yana wurinta ku je ku binkiceta.
Ya tashi yana rangaji da d'ura ashariya ya fita falon ya ritsa Ruky a zaune domin d'akinsu Mairo ma a rufe yake zage-zagen da yake yi ne ya tashe kaf har da yaran abinda ba su saba ji ba sai kuka. Adam da Salim suka tashi a firgice yayin da Bashir ya dinga bugun kofar d'akin da Nusaiba take kwance da yaranta. Itama a gigice ta tashi tana bud'e kofar ya yi ciki da ita ya ritsata. Salim da Adam suka bi shi d'akin. Itama Rukky ta koma d'aki a guje tana gaya musu gabad'aya suka fito a gigice
Lokacin har ya sa mata wu'ka a wuya wai ta bashi kud'i da mukkulin dirowa an ce komai yana hannunta.
Salim ya yi tsalle ya buga masa duka a bayansa tunda yana tsakiyar Nusaiban ya raba kafufunsa a kanta ya saita ta da wuka.
Gidan ya cika da koke-koke a guje-guje. Mairo da gudu ta ja yaran suka koma d'akin suka rufe. Salim ya d'agata ta shi da gaske ya gilla mata wukar a wuya har ya yi sheda ta matsa gefe tare da ri'ke ma'kogwaronta da ya fara d'an fitar da jini kad'an. D gaske yankar rago ya yi shirin yi mata. Jama'a 'kwaya bala'i ce.
Yaranta ihu kawai suke yi. Nabila ce kad'ai ta iya zuwa wurin da take amma su anti Yabi suna can sun rirri'ke Salim da ya shemar da Bashir din a kasa yana dukan hancinsa.
Da yake ba sosai yake kashe wayoyinsa idan zai kwanta ba. Cikin bacci muka ji kiran waya gabad'aya kusan a tare muka tashi zaune ni dashi ya d'auka da sauri yana sanyawa a kunnansa muka ji muryar Adam cikin rud'u da tsananin tashin hankali yana fad'in." Baba ka zo babu lafiya ka zo yanzu Bashir ne zai kashe anti Nusaiba."
Da wani irin hanzari ya sauka daga gadon na taso na biyo shi ya ce na koma. Har ga Allah na tsorata duk da gidansa cike da tsaro ina jin tsoro ya fita jin ana maganar kisa.
Na koma na zauna cikin tsananin tashin hankali da damuwa wace irin masifa ce wannan kuma.
Lokacin da ya shige gidan Bashir din ya samu nasarar ta shi yana ta kai wa Salim suka da wu'kar da take hannunsa 'karama ce amma kisa da illa take yi nan take. Ihu da koke ya cika gidan ita Nabila ga yanka a kumatu ga iskokai.
Da hanzari ya nufe shi duk da ya hangi abinda yake hannunsa. Amma da ya gama fahimtar bashi da wani kuzarin kirki irin na maza dalilin shaye-shayen da yake ya dakusar da garkuwar jikinsa sai ya nemi ma'karfafansa ya kai masa duka a k'irji kafin ya falla masa mari ya murd'e hannunsa da kyau ya k'wace wu'kar ya mi'kawa Salim ita ya kar'ba duk ya yi wujiga-wujiga ai yayi namijin kokari ma wai aka ce ranar naka sai naka tabbas da da tsautsayi yau Nusaiba zata ba'kunci lahira itama.
Ya ce da Adam maza ya fita ya kira masa Sukairaju da 'Dahuru sune majiya k'arfi sosai fadi yake kisan kai za ka yi mana a gida Bashir dama dan ta'adda ne."
Ya yi shiru yana ciccije baki. Ya dubi Nusaiba dake zaune a gefe yaranta biyu a kusa da ita tana share hawaye sai ya girgiza kansa cike da tsananin damuwa ya kalli Anti Yabi yana jin kamar itama

Please Login or Register in order to submit comment