Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo shi ya kuma kwana biyu cikin iyalinsa kafin ya koma.
Akwai sanayya a tsakaninsu tun lokacin kuruciya amma dai ba kamar yadda suke da Malam Rabi'u ba domin dai shine sa'ansa. Malam Nuhun ya d'an girme shi tunda sakon Malam Rabi'u ne girman dai ba wani mai yawa bane sai dai da yake shi mutumin karkara ne duk ya manyata sosai ya tsofe ga d'auwaniya da lissafin rayuwa ga hidimar iyali duk mai mace uku a yanzu da yara sama da ashirin da biyar kuma yana ciyar dasu kowace rana babu tangard'a lallai shi ya kamaci da a kira namiji dalili anan shine da yawa maza mace daya ma suna gaza ri'ke ta balle mace biyu da yaranta. Suna nan birjik a gari wad'anda jima'in kawai suka sani duk dare babu fashi sai sun yi amma ba su san hanyar da za su kula da abinda jin dadinsu ya haifar musu ba domin kuwa jin dadin ai shi yake kawo albarkar 'ya'ya bayan an rabauta da shi.
Aka shiga gaishe-gaishe da tambayar bayan rabuwa. Daga lokacin ne ya dan samu nutsuwar bud'e bakinsa da ya yi masa masifar nauyi kasantuwarsu da malamin a d'aki ya kasa duban wajan da yake zaune saboda tsabar jin nauyi da kunya tare da zullumin abinda zai biyo bayan uzurinsa. Ya zurawa Malam Nuhu ido yana nuna Dr Iliyas cikin ko'karin jaddada jarumtarsa ya ce." Wannan sunanshi Dr Iliyas Musa k'wararran likita ne da ya karanci fannoni da dama yana aiki a babban asibitin nan kano wato Malam Aminu."
Malam D'aha ya sake mikawa Dr Iliyas hannu suka yi musabaha a karo na biyu bayan wadda suka yi da farko a lokacin da suka same shi shi kadai a zauren nasa. Malam Nuhu Shima ya mik'a masa hannu baya suka sake yin musabaha cikin dai karamaci da kulawa.
Wajan ya d'auki shiru na d'an wani lokaci. Kafin ya yi gyaran murya ya cigaba da cewa." Wato Malam Nuhu na ji dadin zuwanka a yanzu saboda wani babban uzuri wanda ya assasa mini rashin nutsuwa da kwanciyar hankali da tunanin yadda zan tunkari Malam da wannan uzurin da duka ya shafe mu gabad'aya."
Shiru ya sake ratsa wajan a karo na biyu babu wanda ya tanka Malam Nuhu dai kacokan ya mayar da hankalinsa gare shi yana sauraransa. Ya nisa kafin ya sake tattago jarumtar da neman rinjaye dangane da abinda yake faruwa ya cigaba da cewa." Wani abu ne da ya zama ruwan dare ko kuma na ce babban kalubale da rikicewar tunani ga ma'aurata wad'anda Allah Ya jarabta da hakan. Kasancewarku mutanan karkara nasan dai da wahala a ce wasu da suke rayuwa a wannan garin ba su gazgata cewa rigafi ya fi magani ba. Kuma hausawa suna cewa taya Allah kiwo ya fi Allah na nan."
Malam Nuhu ya ce." Yallabai ya kamata ka yi magana kai tsaye domin wallahi gabad'aya ka sanya ni cikin nazari da zullumi." Ya dubi malamin yana fad'in." Ko ba haka ba ne Malam?"
Malam D'aha ya gyad'a kansa cikin nutsuwa ya furta."Tun zamansu a wannan wurin na fahimci da akwai abinda yake tafe da su domin dai tunda aka fara hidimar nan Alhaji Tajo bai ta'ba bugo mini sammako irin yau ba sai kwanaki biyu da suka wuce da ya zo da kansa ya d'auki Hajara ya ce da ni za su je asibiti a zaman da nake yi a yanzu ina sauraran ji daga gare shi ne ko Hajara tana d'auke da wani ciwo wanda mu ba mu san da shi ba sai yanzu."
Malam Nuhu ya ce." Ya Malam Hajara kalau take domin tunda aka haifeta a gidan nan bata ta'ba kwanciya wani mummunan ciwon da zai gigita mu ba. Kusan a yanzu ma duk ta fi yaran gidan kuzari da hankali."
Ya gyada kansa amma bai ce komai ba. Suka dai zuba masa cikin yanayi na damuwa gabad'ayansu domin ga yanayin yadda ya fara yi musu magana sun san lallai akwai matsalar da take shirin faruwa.
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cire shakku da jin nauyin malamin ya dubu idonsa sosai ya ce ." Malam a gafarce ni idan har na yi lefi ina neman afuwa. Ban zo nan na d'auki Hajara na kaita asibiti domin a yi mata wani gwaji na mummunan ciwo ba face samun nutsuwa da ita domin ingantuwar auranmu da kuma samun yara masu albarka da wadatar lafiya."


Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya gyada kansa yana fad'in." Babu cutuwa ko cin zarafi tsakanina da zuri'ar Alhaji Ibrahimu kai din daidai kake da wannan da yake zaune a gefanka." Ya nuna Malam Nuhu. A daidai lokacin Malam Rabi'u ya shigo da daurikan goro kusan bakwai ya jibge a gefe d'aya.
Yazo ya zauna a ka gaisa da shi yanayin da ya gan su a cikin na alhini da zullumi ya sanya ya fara tambayar d'an uwansa lafiya.
Malam Nuhu ya furta." Lafiya ba lafiya amma dai mu saurare daga Alhaji Tajuden."
Duka suka zuba masa ido sai ya cigaba da cewa." Ina godiya Allah Ya gafarta Malam wannan da yake zaune da na gabatar muku da shi shine likitan da ya yi mana gwajin jini da yarinyar nan Hajara cikin kwarewa da irin hikimar da Allah ya huwace musu ya tabbatar mini da cewa akwai matsala domin kuwa jini na dana yarinyar nan bai yi daidai da yadda ake buk'ata ba. A irin hasashen da suke yi da kuma yadda muke gani a kan wasu da Allah Ya jarraba da samun yara masu d'auke da wannan cutar mai kisa farar d'aya ya sanya shi din ya ba mu shawara a matsayinsa na jami'in lafiya dakatar da abinda ake shirin yi a yanzu dalili anan kuwa shine za mu kasance ni da yarinyar nan cikin yanayi na damuwa da tashin hankali a duk lokacin da Ubangiji Allah Ya ba mu rabo na haihuwa yaranmu za su zo d'auke da wannan lalura ta sikila wadda take kisa a take ta kuma wahalar tare da jirkita hallita da matsancin ciwo mabambamta idan kwana bai k'are ba."
Shiru kamar an yi ruwa an d'auke babu wanda ya ce uffan amma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ban da malamin da wani murmushi ne ma na mussaman a saman le'bansa.
Dr Iliyas ya yi kundubala ya dubi malamin da wasu takardu guda biyu a hannunsa yana bud'a su ya ce." Ya Malam a matsayin mu na likitoci muna yin iyakacin bakin kokarinmu akan kowace irin ma'asala domin mu dora jama'a akan hanyar da za su samu mafita da kuma wadatar lafiya. Babu nufin yi wa Allah shishsigi domin shi Ubangiji shine ya d'an sammana sani daga cikin abinda mu ba mu sani ba sanin abinda yake kudira sai shi buwayi gagara misali."
Malam D'aha ya zuba masa idoo yana sauraransa. Ya cigaba da cewa."Yawaitar wannan ciwo da yadda masu d'auke dashi ke shiga gagari da k'unci na rayuwa da azaba mai tsanani a duk lokacin da ya motsa ya sanya kungiyar manyan likitoci daga 'kasashe daban-daban mahukunta da kuma gwamanti had'a karfi da k'arfe domin yin bincike akan dakile hanyar da wannan lalurar za ta cigaba da yaiwata a kowane sassa na fad'in duniyar nan gabad'aya.
Binciken da k'wararru suka yi tare da taimakon Allah Ya sanya suka gane cewa mataki na farko da za a d'auka domin dakushe yad'uwa da haihuwar yara masu d'auke da wannan lalura yin gwaji na jini domin sanin matsayin namiji da mace a duk lokacin da za a k'ulla auratayya wanda muke kiransa da (genotype) Ta wannan hanyar ne kawai za mu duba mu ga cancanta da dacewa wad'anda suke so kulla aure domin yin rayuwata ta din-din tare da samar da yara masu ingantaciyar lafiya.
Daga lokacin da muka fahimci cewa As da As na da mutukar had'ari a matakin jini ko Ss da Ss Muna yin iyakacin bakin kokarinmu wajan ganin mun hana su kulla aura ba don komai ba sai don gujewa 'kin juna da tsanar junansu da za su yi a nan gaba dalili kuwa anan shine suna fara haihuwa za su ci karo da jinyya mai tsanani daga albarkar da suka samu. Iyaye na kasance tamkar majinyyata marasa nutsuwa da fargaba a duk lokacin suka dubi abinda suka haifa a kwance cikin mawuyancin hali na ciwon ga'bobi da kumburi da 'konewar jini zafin jiki da koke-koke Mu likitoci muna yin misali da ciwon nakud'a irin na mata ga yaro ko yarinyar da suka tsinci kansu a cikin wannan yanayin. Nakud'a idan Allah Ya sau'kakawa mace cikin dan k'aramin lokaci zata haife abinda yake cikinta sa'banin mai d'auke da wannan ciwon a duk lokacin da ya motsa masa yana ficewa ne daga hayyaci tare da jefe zukatan iyaye rayuwar ce ko mutuwa.
Ya nisa cikin sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa." Ita wannan cutar ana gadonta daga iyaye biyu wato uwa da uba kamar yadda na yi muku misali da farko idan ya kasance an samu rashin daidaituwar jini uba ya kasance As uwa ma ta kasance As to akwai yiwuwar su samar da yara masu dauke da cutar kuma mafiakasari yaran da za su haifa duka za su rinjayi masu lafiyar yawa. Akwai misalin Ss da Ss shima kamar As din ne akwai buk'atar ha'kuri da juna tare da neman mafita daga kowane bangare domin gujewa samar da abinda zai zama damuwa da zubar hawaye a gaba.
Kamar yadda Yallabai ya yi bayani da farko kafin ba ni damar magana ni likita ne massanin fannika da dama da suke da ala'ka kowace lalura kuma ina yin iyakacin bakin kokarina wajan ganin na bayar da shawara akan abubuwan da su kawo rud'ani da cutar da wani bangare.
Shin yaya ake gane cewa an haifi yaro da wannan cutar dalili anan shine yaro yana karami ba shi da bakin da zai fad'i cewa ga wajan da yake masa ciwo sai dai kuka da kumburin jiki kafafu da cikinsa da kuma jirkitar launin idanu daga fari zuwa ruwan dorawa (yellow) alamu na farko kenan sai yanayin suffa da rashin kuzari ta wani gefan tafiyarsu ma tana bambamta da irin ta masu cikakkiyar lafiya.
Abu na farko da za a yi shine idan yaro ya nuna irin wad'annan abinda na lissafa da farko ayi maza a kai shi asibiti domin auna shi don tabbatar da lafiya mu kuma a matsayinmu na likitoci daga lokacin muke fara namu taimakon da shawarwari ga iyaye akan yadda za su kula da yaronsu don kiyaye tashin ciwon a kai kai."
Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya kafin ya nisa cikin nutsuwa." Ya cigaba da cewa." Allah Ya gafarta Malam ban zo nan wajan domin katse sunnar manzon rahama ba face bada shawara a matsayina likita amma ina ji Malamai da yawa na fad'in cewa akwai maganinta mu dai a likitance wannan matakin muka d'auka domin dakushe k'ara yawaitar haihuwar masu dauke da wannan lalura."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ya yi gyaran murya a nutse ya furta." Babu wata cuta da Allah bai yi maganinta ba Iliyasu ban katse maka hanzari ba kuma ban raina sanin da Allah ya yi muku ba a matsayinku na masu taimakawa. Kafin na bawa Alhaji Tajo auran yarinyar Hajara na nemi zabin Allah na kuma yi istahara akan lambarin a kuma duk sanda zan wayi gari nakan tsinci kaina cikin farinciki don ganin zuriata da ta abokina za ta had'u waje daya domin haifar da wata zuriar da ba za mu iya iyakance adadinta ba. Mu bar wa Allah da ni daku gabad'aya mu yi imani da tauhidi cewa babu mai kashewa da rayawa face shi wannan karamin dalilin da kuka zo gabana da shi ba zai zama silar da za a warware wannan alkawarin ba da ya zama saura k'ankanin lokaci a d'aura shi.
Ba mu isa mu hana Allah abinda ya shirya ba domin duka a can baya tun kafin mu kan mu mu zo duniya iyayenmu suke auran juna ba tare da wannan binciken na nunawa Allah iyakarsa ba. Iyaye suka haife mu lafiya lau babu ciwo ko kad'an mu ma muka rayu lafiya muka auri matayenmu babu ciwo kuma suka haifar mana da zuria masu tarin yawa da ba su d'auke da wata lalura makamaciyar wannan don haka wannan magana da kuka zo mini da ita ba za ta dakatar da ni daga abinda na niyyata ba a yau idan har Alhaji Tajo ba kai zaka nuna mini cewa ba ni da alfarma a wajenka ba."
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! abinda yake ta fad'i kenan a cikin ransa zuciyarsa na wani irin dokawa da tashin hankali da damuwa. Babu fa wani dalili da zai sanya shi yin rayuwar aure mai nisan zango da yarinyar nan dalili kuwa shine yana da burin kara samun haihuwa. Tabbas Allah ne mai yin yadda ya so idan ya so zai iya bashi lafiyayyun yara da yarinyar ba kamar yadda yake hasashe ba amma rashin nutsuwa da lamarin ya sanya masa fargaba yarinyar ba tsararsa ba ce gabad'aya koda an daura masa aure da ita ba ya tunanin zai iya had'a shimfida da ita balle har ta kai ga ta d'auki ciki suka shiga cikin zullumi akan abinda za a haifa mai lafiya ne ko mara lafiya. Amina ta riga ta zama k'addararsa shine dalilin da ya sanya yake ji a zuciyarsa wannan dalilin ba zai sanya ya rabu da ita ba kuma zai iya cigaba da zaman aure da ita. Amma dai a yanzu ba ya tunanin zai sake yarda ya auri wadda jininsa da nata bai daidaita ba.
Maganar Malam Nuhu ta katse tunanin da yake yi ya ji shi yana cewa..........
'þ
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*152*
Suka juya gabad'aya suna kallonsa a lokacin da ya fara magana kamar haka. " Ya kamata a k'ara duba wannan uzurin da suka zo da shi Allah Ya gafarta Malam nasan da wahala Alhaji Tajo ya d'auki aniyyar tozartaka a irin wannan ranar da gabad'aya ta zame mana abar alfahari da farinciki mussaman da muka tabbatar da cewa wanzuwar lamarin shine abinda ka fi buk'ata a yanzu domin sake kulla zumunci mai karfi tsakaninka da abokinka Alhaji Ibrahimu Allah Ya yi masa rahama da gafara."
Suka amsa da "Amin gabad'ayansu kafin ya sake nutsuwa sosai ya cigaba da cewa zahiri wannan lalura da suke magana akanta akwaita kuma har yanzu tana k'ara yaduwa a wasu wuraran da ba su d'auki abinda ya zo a zamanance da muhimmanci ba. Malam ko dai ka manta shekarun baya ashirin da biyu da suka wuce muka dinga dawaniya da mai sunan Inno har Allah Ya d'auki ranta a asibitin Murtala na cikin garin kano wanda sai a lokacin ne gabad'aya muka san ga cutar da ta zama ajalinta."

ABINDA YA FARU.
Shekaru ashirin da bakwai can baya Malam Nuhu ya auri matarsa ta fari Lantana wadda a yanzu ba ta raye ta rasu dalilin farfadiya tunda tana da mutanan b'oye sa'i da lokaci sukan tashi. Auran soyayya suka yi a cikin kauyen nasu kamar yadda al'ada take duk da wannan lalurar tata ta farfadiya hakan ya zauna da ita tunda yana sonta shi kansa mahaifinsa ya bashi gudumuwa kwarai wajan yi mata magani idan ciwon ya tashi. Da ta samu ciki sai wahalar da take sha ta sake ru'banya tunda kowa ya san yadda masu wannan ciwon suke shan ba'kar wahala a duk lokacin da iskar ta buge su a kan titi ne ko a kasuwa ko a gida sun dinga katantanwa kenan da jikinsu suna malkwadewa tare da taune lebensu da kumfa dafara mai hade da jini.
Suka dinga bige ta a kai akai don babu wanda ya tsammaci za ta haife wannan ciki da yake jikinta lafiya saboda yadda take jigata.
Cikin ikon Allah da lokacin ya zo ta haihu kalau aka samu 'ya mace wadda ta ci sunan Inno Ramatu suke kiranta da Rahma. Tun tana yarinya jinjira ta fara nuna alamun rashin lafiya ido ya jirkice daga fari zuwa yellow cikinta ya yi kurcici sai siraran kafafu da hannu. Da masifar kukan tsiya da zafin jiki domin koyaushe idan aka ta'ba jikinta radau ake jikinsa. Da yake kauyene a wancan lokacin da babu wayewa sosai kamar wadda suke ciki a yanzu sai duka daga can b'angaran iyayenta dana shi Malam Nuhu suka alak'anta lalurar da yarinyar take yi akan shafar aljanu dalili uwarta tana da su kuma sun tashi sosai a lokacin da take d'auke da cikinta a jikinta..
Suka dukufa wajen yi mata jike-jike na maganin gargajiya daga can b'angaran malamin kuwa yana yi mata rubutu da tofi ana bata tun tana jaririya ta saba da shan sassaken magani mai d'auke da ruwan rubutun da kakanta yake yi mata. Har hayaki sukeyi wa yarinyar saboda duhun kai har rukiya sai da Malam D'aha ya yi mata da abin ya ci tura duk a tunaninsu aljanu ne suke tsotse ta kuma suke hana ta bacci da daddare suke firgitata tana kwanan kuka. Duk wannan wuyar da yarinyar take ci Allah bai amshi abarsa ba sai da ta yi shekaru hud'u tukkuna cikin halin rai da rayuwa domin a duk lokacin da ciwon nata ya tashi hayaki ake yi mata aka dingi bata sassake da saiwa wadda aka dafa da jar kanwa.
Wajan cirani can Katsina uban suke hira da abokinsa yana gaya masa halin da yake ciki da yarinyarsa wannan mutumin a irin bayanin da ya yi masa ya gane cewa babu maganar iska sai dai idan wata lalurar ce shine ya ba shi shawara kan cewa ya kaita asibitin cikin gari na kano general ne na kowa da kowa domin yawanci ma mutanan kauyen sun fi morarsa har ya ta'ba bashi labari shima daga nan k'atsina garinsu ya ta'ba kai mahaifiyarsa asibitin na Murtala aka dubata har ta kwanta na tsayin sati hud'u kuma ta samu kulawa kwarai ya ce masa su jarraba yin na asibiti ko za a dace.
Koda ya dawo gida ya sanar da Malam D'aha da kyar ya amince da a d'auki yarinyar a tafi da ita a ganinsa abinda yake damunta bai had'a hanya da asibiti ba domin duka sun d'auka cewa lalurar uwarta ce ta shafe ta.
Ba a tafi da uwar ba tunda tana halin ciwo Inno kakarta ita ta goyata suka tafi dawowar da yarinyar ba ta yi ba kenan domin kwanansu daya a asibitin ciwon ya tashi da masifar k'arfi likitoci suka dinga kai kawo a kanta inaaa babu jini ya kone ta rasu.
A wannan lokacin ne likitan da yake tsaye a kan yarinyar ya zauna ya dinga yi musu bayanin musabbabin abinda ya yi ajalinta babu iska sai tsananin ciwon da Allah ne kadai yasan maganinsa.
Duka ba su gazgata hakan ba a lokacin suka dawo gida da gawar yarinyar daga lokacin ne Malamin ya ce kada a sake daukar wani daga cikin zuria'arsa a kai asibiti duk cuta akwai maganinta cikin al'kur'ani mai girma.
Shekara biyu bayan rasuwar yarinyar uwar ma Allah Ya d'auki rayuwarta sakamakon wata fad'uwa da ta yi iskokai da suke tare da ita suka bugeta a bakin kofar bandaki daga lokacin jikin nata ya'ki dad'i har dai rai ya yi halinsa.
Wannan shine abinda ya shud'e a shakarun baya kuma a iya gwagwarmayar da yake da sauraran redio hurd'a da mutane bambamta tunda a can katsina wajan da yake gudanar da sana'arsa birni ne ba kauye ba ya tabbatar da cewa duk bayanin da ake yi akan wannan lalura gaskiya ne ya gazgata itace silar yarinyarsa ta fari Rahma wanda ada can suke d'auka shafar aljanune.

Malaman D'aha ya yi shiru jikinsa ya d'an shika kadan a lokacin da yaron nasa ya tariyo masa abinda ya shud'e a cikin wasu shekaru da suka gabata. To amma shi a ganinsa wannan kadai ba zai hana k'ulla aure ba domin a zamanin baya wanene ya san da yin wani gwajin kafin a yi auran kuma cutar ba ta yawaita ba."
Malam Rabi'u da jikinsa ya gama mutuwa saboda wannan lamari ya furta." Ya Malam a duba wannan lamari a kawo sasanci a cikinsa domin kada a zo a yi abu anan gaba a koka tun yanzu ya kamata a ce an magance matsalar nan domin ana yin aure ne domin samun zuri'a wadatattu kuma masu lafiya muna neman alfarma a duba a kuma yi adalci ta kowane bangare."
A dan sanyaye ya furta." Rabi'u ba na 'ki ba ne zuwa yanzu ni ma jikina ya yi sanyi tunda zamani aka ce, Annabi Muhammadu S.a.w shi kansa ya yi magana akan zamani duk yadda muka kai ga ta'kawa da gudun sa'bawa Ubangiji idan abu na zamani babu yadda muka iya amma abin lura anan shine mu yi yaya da jama'ar da muka tara domin taya mu murna wannan shine abinda ya fi damuna a yanzu."
Malam Nuhu ya furta." Abu ne mai sau'ki Ya Malam kana da almajira da suka 'yantu da yawa wasu sun shiga cikin gari neman arziki kamar yadda ka saba duba nagarta da cancanta a cikinsu ka bashi auran Hajara a daura da duk wanda ka zab'a mata in sha Allahu ba za a samu wata matsala ba daga kowane bangare."


na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Daga can b'angaransa kuwa ya kira sunan Ubangiji babu adadi ya yi tahamidi tare da jaddada godiyarsa a gare shi ganin yadda aka samu kan malamin cikin k'ankanin lokaci ya magantu cikin kwarin gwiwa ya furta." Idan babu matsala an kuma ba ni wu'ka da nama ina nemawa wani aminttaccen yarona auran yarinyar zan kuma zame musu Uba gabad'aya."
Malam Nuhu ya washe bakinsa Yana fad'in." Ka ji wani iko Allah ko Malam ina ganin duk wanda zai fito daga wajen Alhaji Tajo za a samu nagarta da sasihancin abinda ake buk'ata an samu mafita cikin sau'ki sai a juya d'aurin auran zuwa gare shi.""
Malam D'aha ya dube shi cike da damuwa ya furta." Na so tabbatuwar auran nan da raina ya kwadaitu da shi Alhaji Tajuden amma ga yadda Allah Ya juya lamarin muna fatan hakan ya zama alheri da samun abinda ake buk'ata na kuma baka wu'ka da nama akan Hajara."
Ya dinga godiya kuwa kamar wanda ya yi masa gagarimar kyauta Malam Nuhu fadi yake yi mu ne za mu yi godiya fa Alhaji Tajo mune muke da godiya a wurinka.
Ya tashi ya fita tare da fad'in su jira shi lokacin rana ta yi sosai sha biyu da rabi ana ta haramar tafiya massalaci kai tsaye mota ya nufa Sukairaju ya hango shi ya fito da sauri ya bude masa ya shiga ya mayar da kofar ya rufe ya tsaya daga waje tare da harde hannunsa a k'irji.
Ya sauke ajiyar zuciyar da ba zata lissafu ba godiyar Allah kuwa a cikinta yake yi sai dai yana d'an zullumin saurin yanke hukuncin da ya yi bai kira ta ya ji ya ake ciki ba. Shin wane yaro ne take nemawa aure a yadda yanzu malamin ya karrama shi tare da bashi amana baya tsammanin zai yarda da kowane irin za'bi. Idan wanda take nemawa auran bai yi masa ba zai aurawa Sukairaju yarinyar duk tsiya ya fi shi kuruciya kuma ya tabbatar da cewa zai rike masa ita da amana amma hanzari ba gudu ba shine menene matakin jini tunda dai shi a kan haka ya bijire yana da kyau daga kowane bangare ya samu gamsashen bayani kafin a k'ulla auran.
Jikinsa ya sanyi sosai ya lalubi wayarsa dake cikin aljihu sai a lokacin ma ya lura da kiran da ta yi masa.
Ina zaune jikina duk ya yi la'asar ganin d'aya saura na rana zuciyata na tabbatar mini da cewa wannan auran fa sai an daura shi da mijinki Amina tunda ki ka ga har yanzu bai kira ki ya gaya miki wata matsala ba. Dama fa yana so yaudara ce kawai yake yi miki akwai wani namijin da zai ce baya sha'awar budurci mussaman na yar k'aramar yarinyar irin wannan wadda yanzu take tashi.
Na kwanta a hankali saman gado ina kallon Minal tana yi mini 'buruntu saman madubi yaran dake cikina sai wutsil-wutsil suke yi tabbacin suna buk'atar abinci ba ni kuma da niyyar

Please Login or Register in order to submit comment