Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada ki karanta mini muddin ba ki biyani hakkina ba, mu kula sosai hakki komai kankantarsa sunan hakki.

"Na gode sosai, da wannan sadaukarwar taki, kin daraja mahaifiyata. Kin kar'bi ro'konta, wannan dalilin ya sanya na baki gurbi mai girma a zuciyata. Ba ni da ra'ayin aure a yanzu saboda tarin matsalolina. Amma ba ni da k'wanjin yin turjiya ga umarnin mahaifiyata. Kada ki damu yaranki ki zo tare dasu, ai d'a duka na kowa ne, Allah Ya raya su, ke kuma Allah Ya ba ki hakuri da juriyar zama da ni."

"Ba zan iya zama da mazina ci ba. Ba zaka same ni ba har abada. Aure an d'aura dai amma zai zama na kwangila. Zan zauna a gidanka zan cigaba da hurd'odina na yi hakan ne saboda mahaifiyarka, amma ni ba ni da burun auran irinka, abinda yake cikin zuciyata na fito na gaya maka. Kana da damar auro wata, amma ni kam ba zan iya had'a jiki dakai ba."
Ido cikin Ido na gaya masa haka domin tun yanzu gwara ya san manufata. Haka kawai nake masa kallon mai cutuka a jiki. Domin duk mutumin da yake zina ba zaka raba shi da matsaltsalu ba.

Ya jima yana kallona kafin ya nisa. Ya daga kafadarsa yana fad'in." Ai aure ba abin wasa ba ne, ni ba munafiki ba ne, kuma ba zan fara a kan wannan karamin dalilin ba. Ni ya kamata na kyamace ki saboda mazan da ki ka yi tarayya dasu a baya. Amma har kina da bakin fad'a mini magana. Ki zauna a shirye duk lokacin da na tashi kar'bar sadakina zan turo miki likita ta auna ki. Domin ni har yanzu saurayi ne babu wata mace da na sani."

Wani irin kallo na yi masa a watse na ce." Sai dai a auna mu a tare don wallahi ba zan yarda ka shafa mini 'kanjamau ba."
Sai ya fashe da dariya irin wadda ban ta'ba ganin ya yi ba. Ya nuna kirjinsa da hannu yana cewa." Ni ne mai kanjamau!"
Murgud'a bakina na yi na kawar da kaina gefe.

Ya nisa kafin ya ce." Okey to shikkenan yanzu dai ki tashi muje abokaina suna falo wai sai an yi mana hoton tarihi Ina ce Hajiya Saratu ta gaya miki ko?"

Shiru na yi ban bashi amsa ba, kuma ban tashi ba.
"Kin ji ni ko?" Ya fad'a can kasan makoshinsa. Ban motsa ba.
"Amina."
Ya furta sunana a hankali tare da dora hannunsa a kafada. Na goce tare da mikewa tsaye ina gyara karamin hijabin din wuyana. Kawai na tsince shi yana satar kallon kirjina. Da sauri na dan gicciya gabana na faduwa. Ya miko mini hannunsa.
"Sa hannunki a cikin nawa, ai ko ba ma son juna ba za mu nunawa duniya ba ko?" Yafad'a yana matsowa jikina. Na matsa da saurin gaske. Sai ya gyara fuskarsa babu fara'a. Ya furta." Ba na son sakarcin banza, ko kin shirya ba ni kunya ne a cikin mutane? Duk abinda za ki nuna a yanzu kamar kina gayawa duniya yadda akayi auran nan ne, kin san matsayina a ko'ina, kiris jama'a suke jira su samu abin magana. Yadda nake daure zuciyata kema ki daure zuciyarki a yi lamarin nan cikin girma da mutunci ko nawa kike so zan baki."
Hawaye suka zubo mini Ina kuka na ce." Ni bana buk'atar ko kwabo. kuma don Allah ka ce musu ba ni da lafiya su tafi yadda nake jin ciwo a raina ba zan iya nunawa duniya auran so muka yi ba."

"To na ji, yanzu dai ki yi mini wannan alfarmar kin ji ko, a cikin mutanan da suke falon nan akwai manyan 'kasar nan. Kuma kin san balaraben mutum da kara da karramawa, na amince duk yadda ki ka tsara zaman za a tafi a haka, ni ma ai na san tunda na yi rashin Samira a duniya ai babu wata mace da zata maye mini gurbinta. Amma dai ni dake muna cikin damuwa. Ki b'oye kamar yadda nake b'oyewa.

Nasa hannu ina goge fuskata. Sai ya shiga taya ni, Yana cewa."Mutane da fahimta suke Amina, kin ga kukan da kike ta yi ya janyo idanunki sun kumbura sun yi jawur, ummm, ki yi hakuri haka kin ji ko, ki barwa Allah kamar yadda ni ma na bar masa."
Cikin rararshi yake magana yana ta gyaggayara mini fuskata da tafin hannunsa da yake yake kamshi
Na d'auke hannun da sauri bai ce komai ba ya riko hannuna muka fara tafiya a jere daf da za mu fita ya tsaya yana kallona, ni kuwa sai kawar da kai nake yi. Kawai ba zata na ji saukar hannunsa a tudun kirjina da sunan Yana gyara mini zaman karamin hijabin wuyana.
Da sauri cikin zafin nama na buge hannun. Dan ban san ma na yi hakan ba saboda gigicewar da na yi. Na matsa gefe tare da buga kafata. Murya na rawa na ce." Wai menene hakane?"
Ya dube ni cikin nutsuwa ya furta." Menene kuwa, kawai don na gyara miki hijabi shine za ki bige mini hannu."
Zumbura baki na yi." Ba na so ni gaskiya."
"To, na ji ba zan sake ba, mu je, amma ki saki fuskarki."
Ban ce masa komai ba. Amma na saisaita fuskar tawa. Ya kama hannuna muka fita haka.

Har kasa na zube na gaishesu sun kai su shida kuma kamar yadda ya fad'a manya ne don yawancinsu da masu tsaronsu .
Hajja kam sai murmushi take yi ta yi ado sosai cikin wani leshi bulu da farin mayafi. Babanmu ma cikin sababbin kaya.
Hotona akayi sosai duk Ina kusa da shi, wani ya d'an rungomo ni jikinsa wani kuma ya rike hannuna. Shi ma yana ta walwala ni kuwa sai ya'ke na ke yi na rasa abinda yake yi mini dadi a cikin raina.

Gabad'aya da sadakina da kyautukkunan da na samu Hajiya Saratu ta had'a a kwati ta bawa Babanmu shi kuma ya shigo har d'akin da nake ya kawo mini yana kara yi mini bayani sadakina dubu dari biyu ne duk da kudin garin aka biya. Sannan kuma yana kara gaya mini daga zarar mun koma zan tare. Ni dai ban iya ce masa komai ba kawai na ce to shikkenan Baba. Ya kama hanya ya fita zuciyarsa fes. Hawaye na goge ya zame mani dole na zauna gidan mutumin nan ko don dorewar farincikin da Babanmu ya riski kansa a ciki. Duk yadda Allah ya yi da ni shikkenan

****
Shi ya riga mu yin gaba. Kwana biyu muma muka yi dawafin bankwana muka tattaro kayanmu muka nufo gida. Sai da muka fara sauka a gidan Hajja tukkuna da daddare ta sanya direba ya kaimu gida a bakinta ma ni nake jin ogan baya garin a she a legos ya sauka yana can kuma, wai sun yi waya ya gaya mata ranar juma'a na zauna a shirye zai zo mu tafi can din zan zauna.

Na daure na ce." Hajja dan Allah mu zauna tare nan ba na son yin nesa da gida wallahi. Idan Hakan ma ba zai yiwu ba idan yana da gidaje anan din sai ya ajiye a d'aya daga ciki.
Ta ce." Ni ma hakan na so amma ya ce ya fi so ki bishi can din saboda zamansa ya fi yawa a can amma sa'i da lokaci za ku dinga zuwa. Ko Kuma ni na kawo muku ziyara."
Tunda ta fadi haka sai na ja bakina na yi shiru ban sake magana ba. Ita da Babanmu dai sai tattaunawa suke yi.

Koda Sahura ta zo kawo mini Yusi tunda da zan tafi ita ta d'auke shi. Mu ka zauna muna ta nanata yadda al'amarin ya kasance fadi take ko a mafarki bata ta'ba tsammanin hakan zata faru ba. Ni kam ai tun a saudia na riga na gama mikawa Allah lamarin. Sai dai yadda zuciyata take tsalle da rawa shine abinda ya fi damuna. Sai nake ganin kamar ni ma idan na tare a gidansa mutuwa zan yi. Dalilin da ya sanya kenan na gaza jurewa a ranar da Sahura ta zo bayan ta tafi da daddare na kira wayarsa da yake Hajiya Saratu ta sanya mini a wayata. Yana d'agawa na rushe da kuka ina fad'in." Ni ba zan tare a garin da ba ni da kowa ba. Ka bar ni a gidana na kuntau duk sanda ka yi ra'ayi sai ka zo, idan ma ba za ka zo ba shikkenan."
Kuka nake yi sosai irin wanda na tara a cikina. Ya ce." Ni ba zan bijire maganar iyayena ba, ba kuma za ki gindaya mini son ranki na yi ba, na gaya miki ban shirya takarki yanzu ba, idan ma abinda kike tsoro kenan. Ki yi hakuri ki samarwa Hajjja nutsuwa da kwanciyar hankali, ki kuma dubi irin k'aunar da take miki wanda a tarihi babu wata mace wadda na aura ta nuna mata ko da Samira take 'yar kanwarta bata nuna mata so irin naki ba." Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Duk ina biye miki ne saboda ba na son damuwarta. Idan ba za ki yi don Allah ba ki yanke adadin kudi ko kadarar da kike buk'ata daga wurina ni zan mallaka miki."
Hanci na ja tare da cewa ." Ni bana buk'atar dukiyarka kawai Ina tsoron yarana su zama marayu gaba da baya. Na yi bincike sosai a kanka an ce aljanna ce ta aureka, kuma ba zata bari ka zauna da mace ba, shiyasa duk macen daka aura sai ta mutu. Bayan haka kuma ni babu tsarin auran namiji d'an duniya a rayuwata."

Cikin b'acin rai ya ce." To ni kuma muddin mahaifiyata tana raye a duniyar nan ba zan yi jayayya da ita ba. Ni kaina ba sonki nake yi ba, saboda ni mutum ne mai tsantsami. Kin yi tarayya da maza biyu har kin haihu kafin ni. Mai zai sanya na takale ki kai tsaye na gaya miki babu wata mu'amular aure da zata ratsa tsakaninmu. Mutuwa kuma ko kin aure ni ko ba ki aure ni ba za ki mutu. Wannan itace maganata dake ta karshe. Zan kuma kira mahaifinki na sanar da shi, duk da shi d'in ma na lura kin fi 'karfinsa. Amma dai shine ya haifeku wata'kila zai iya gaya miki ki ji. Idan na zo ba na son bata lokaci ki zauna cikin shiri."
bai jira na ce wani abuba ya kashe wayarsa....
'þ
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*TALLAH!*
<Ø2ß<Ø3ß<Ø?ß&þ
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim Opey bank
*8*
"Ta ce addu'a kam koyaushe cikin yin ta nake babu dare babu rana, duk wani abu na gaya maka akan yarinyar nan a daran jiya ba wayo da dubararka ba ne Allah ne ya baka ita, amana ce a wurinka. Ka kula da ita da kyau ko bayan raina ban yarda ka munana mata ba. Wannan shine adduata a gareka Allah Ya yi wa auranku albarka.
Ya amsa da "Amin Amin." Ni kam kasa daurewa na yi dalilin abubuwan da suka cunkushe mini a kirji. Ita wannan matar ban santa ba, wata mu'amula bata ta'ba hadani da ita ba amma tana jifana da mugawayen kalamai. Na rarrafa har kusa da ita na kama hannunta hawaye na kasa tsere a kumatuna na ce.
"Hajja ban san da irin kalamin da zan yi godiya a gare ki ba. Hakika kin nuna mini k'auna ba tare da kin san asali da nasabata ba. Kin so ni a lokacin da dama jama'a ke munana zato a kaina. Hakika Ina yaba kyautayi da kawaici da k'aunar da kike nuna mini. Wannan shine ya tilasta mini kar'bar muradinki ba tare dana shirya yin hakan ba. Yadda ki ka zame mini uwa haka za ki same ni mai biyayya ga umarnin ki Hajja ni 'yar halak ce, kuma ina girmama duk wanda ya kaunace ni tsakani da Allah. In sha Allah zan yi kokarin ganin na yi wa umarninki biyayya, na gode sosai da wannan karamcin naki."
Ta ri'ke hannuna katamau! tana kuka take ce wa." Ni ma ai kin taimake ni Amina, ina ga da ba dan ke ba wata'kila da tattake ni za a yi a wurin nan, ke kika fito da ni har na shaki iska. Sannan na ji ro'ko da magiyar da kike wa Allah akan bukatunki. A lokacin Ubangiji ya kimsa mini kasancewarki mata ga Tajo zai zama alheri. Na san an fi karfin ki ne, amma ki kyautata ha'kuri in sha Allah nan gaba kad'an za ki yi farinciki Ubangiji Allah Ya yi muku albarka. Kuma kamar yadda na fad'a miki zan dinga kawo miki ziyara sa'i da lokaci, Allah Ya ba ku zuria masu albarka."

Ban iya amsawa ba sakamakon kukan da ya ci karfina. Na yunkura na tashi da kyar Hajiya Saratu ta kama hannuna muka kama hanyar fita dama shi Yallabai tuntuni ya fice shi da Yusi.
Koda na shiga motar ban iya dubansa ba. yana zaune Yusi a kusa dashi ya bashi wayarsa yana dannawa. Sai ya zamana mun sa yaron a tsakiya. Hajiya ta Saratu ya zagaya gefan da yake zaune suna magana. Ban ji abinda suke cewa ba saboda ba na cikin nutsuwata. Sai bayan da motar ta tashi tukkuna ta zagayo tana fad'in Amina a sauka lafiya sai mun zo in sha Allahu. Na daure a hankali na ce." In sha Allahu na gode Mamana.
Sai da muka hau titi sosai na juya a hankali na dubi Yusi da yake ta fama yi masa jagwalgwalo a waya na mika hannu na kar'ba ba tare dana dube shi ba na mik'a masa..." Ka kar'bi wayarka kada ya shigar maka wani wurin."

"Ni na bashi ai." Ya fad'a a takaice! ban ce komai ba, na ajiye wayar saman cinyata. Na juyar da kaina gefe. Yaron ya zuro hannu zai d'auka na juyo da sauri tare da buge hannunsa. Da ido na gargade shi. Lokaci guda ya shiga hankalinsa.

Ya dube ni a tsanake yana cewa." Wayar nan tawa ce ai, kuma ni na bashi ina ruwanki idan ya lalata humm? Na lura kina da saurin hannu, da hantara yaro ba abinda ya yi miki kin buge shi, ba ni wayata."
Na mi'ka masa abarsa kamar yadda ya buk'ata. Sai ya kara mikawa yaron. Shi kuma ya'ki kar'ba yana satar kallona.
Ya dube ni ransa a 'bace." Kin nuna masa akwai wata manufa ko?"
Kallonsa na yi da sauri domin ban yi tsammanin fassarar da zai yi mini kenan ba. Ni na yi hakan ne a ko'karin cigaba da kula da tarbiyar yarona. Don ba zan yi sakaci ta samu tangarda ba dalilin na lura shi din kamar ba mai tsawatarwa ba ne.....
Jikina ya mutu sosai ganin yadda ransa ya 'baci, amma kuma girman kaina ya hana na bashi ha'kuri ko na nuna masa nufina ba haka ba ne.
Kafin mu isa filin jirgin yana ta amsa waya tunda na lura wayoyin nasa kusan uku ne manya biyu da karama daya kuma wadda ya bawa Yusin itace bata da wani amfanin sauran.

Har muka isa Legos babu wata muhimmiyar magana a tsakaninmu. Yusi tuni ya langabe a jikina bacci yake sosai. Muna sauka escort dinshi suka tare mu su uku ne, daya ya d'auki Yusi yasa a kafada sauran kuma suka d'ibi kayanmu zuwa mota.

Na 'dan jima ni kadai a mota kafin ya shigo. Domin muna sauka daga jirgi jama'a suka fara taruwa domin gaisawa dashi. Na dinga hangen yadda yake sakewa da mutane da wasa da dariya har da tafawa idan ta kama. Nan na sake fahimtar cewa shi din mutum ne mai sau'kin sha'ani. Kuma dukiyarsa ba ta sanya masa girman kai da d'agawa ba. Yana rayuwarsa ne daidai da kowa.

Ba zan iya fasalta muku haduwar gidanshi ba. Na san dai ni kaina Allah ya gama yi mini gamnakatar na jin dad'in duniya muddin na samu kwanciyar hankali a cikin wannan gidan Allah ya sallame ni anan duniya sai dai na nemi lahirata. Wallahi tallahi a mafarki ban ta'ba tunanin yin irin wannan auren ba balle na hasaso mini shiga irin wad'annan gidajen da muke ganinsu a kasashen waje. Sai dai Allah yana zartar da buwayarsa ne a duk lokacin da ya ga dama.

Gidan cike da ma'aikata kowa kuma da aikinsa. Tun a haraba suke ta zuwa gaisuwa sai da muka shiga ciki tukkuna sannan na dan samu nutsuwa. Na yi kokarin daidaita nutsuwata domin ina tsoron ya fahimci rud'un dana shiga. Na nemi kujera na zauna kafafuna na dan karkarwa. Yusi ya zo ya zauna kusa da ni Ina kallonsa ta gefan Ido yana bin katafaran falon da kallo irin na rashin sabo. Gabad'aya jikinsa ya yi sanyi shi kansa babu kuzarin da ya taho dashi.

A nutse ya nufo wurin da muke yana fad'in." Gidanki ne, za ki iya zabar duk d'akin da ya yi miki a cikin dakunan da suke falon nan. Idan kuma kina sha'awar zama a sama sai ki hau ki duba d'akin da ya yi miki. Ni ma a can nake Sannan da safe idan kin huta zan tara ma'aikatan gidan kaf sai na gabatar musu dake, ina fatan babu matsala."

Ajiyar zuciya na sauke tare da dan duban farcen yatsuna. Na ce." Babu komai, shikkenan Allah Ya kaimu." Sai Ya juya da sassarfa ya fara hawa matattakalar benan da take da wani irin kwalmade kwalmade gashi anyi wa karafunan dake jikin benan wani irin ado da zaiba mai kamar gold sai d'aukar Ido yake yi.
Yusi ya tabo ni yana cewa." Mama kin ga irin benan nan ko, a wani film din indiya na ta'ba ganin irinsa lokacin Umma Sahura ta kunna mana sa'in da kika tafi saudia."
Na dube shi sai kawai dariya ta kwace mini. Na ri'ke hannunsa a hankali na ce." Ni ma haka na taba ganin irinsa a wani film.
Ya ce." Mama gidan nan ya yi kyau wallahi."
Shiru na yi ban ce masa komai ba ina ta nazartar girman falon da yadda aka kawata shi da kujeru da labuleye launi launi.

Wani mutum siriri da shigar masu dafa abinci ya fito daga wata kofa hannunsa da wani 'katon tire na silba da abinci a jere akai. Ya dan risina yana gaisheni, na amsa a takaice. Sai ya wuce sama inda maigidan yake da tiren abincin a hannunsa.
Minti biyar ya sauko da abincin yana kallona yake fad'in." Oga ya ce a shirya muku abinci zai sauko yanzu."
"To.'' kawai na iya cewa na tashi a hankali, hannun Yusi na ri'ke na nufi wata kofa na murd'a ta bude muka shiga.

Hajiya 'kawata kuma 'kanwata ko kuma nace yayata wannan littafi mai suna GUDUN AURE na kudi ne kada ki karanta mini sai kin biya ni hakkina. Kada mu raina hakki komai 'kankantarsa.

Bedroom ne babba wanda yake d'auke da katon gado da kwaba bango guda. Gabad'aya kewaye yake da wasu narka narka labuleye masu beza kasan kafet ne mai laushin gaske. Kofar bandaki kawai na hanga a d'akin sai can gefe da aka shirya shi da kujeru biyu irin na hutawa da teble a tsakiya. Banda sanyi da kamshi mai dad'i babu abinda d'akin yake yi. Na ajiye handbag dita a nutse na cire mayafin jikina. Na dube Yusi da yake ta ko'karin ciro mini wayata daga cikin jaka. Na ce" Ban san a inda ka saba da wasa da waya ba Yusi tunda ni dai ba baka nake yi ba. Dama ina so na gargad'eka kada ka k'ara yi wa maigidan nan wasa da waya ko baka ya yi."

"Mama shine fa ya ba ni kafin ki fito daga gidan Hajja ya ce na yi game, Umma Sahura itama tana ba mu tata, kuma ba mu ta'ba lalata mata ba."
"Duk da haka dai Yusi wayar Umma Sahura daban da wayarsa, ka kula na gaya maka." A hankali ya ce." To, mama."
Bandakin na nufa kai tsaye komai a na buk'ata akwai, na warware babban towel sabo bayan na gama wanka na daura a jikina. Kana na lulluba wani.
Na fito na same shi ya yi tsuru ga wayar agefensa bai d'auka ba sai ya ba ni tausayi.
Na ce." Kana jin yunwa ko?"
Kai ya daga mini. Na ce to bari na watsa maka ruwa ka wartsake." Sai ya kama dariya yana cewa." Mama ai na iya wanka fa a gidan Umma Sahura da kaina nake yi. Na ce." To muje bandakin na gani, idan naga ka iya shikkenan ni ma na huta.
muka shiga bandakin tare na hada masa ruwa ya fara yana ta cudawa Yana cewa." Ai da zamu taho ma don dai kin hana ni, amma da ni zan yi." Na ce." Ai daga yau kai zaka dinga yin abinka tunda naga ka iya." Na juya na fita daga bandakin Ina cewa." Idan ka gama sai ka dauro wannan towel din dana ajiye maka."
Ina fitowa daga bandakin ya turo kofar d'akin ya shigo ko ya akayi ya san muna ciki oho. Wata'kila kuma mutumin da yake masa abinci ne ya gaya masa ko kuma motsi ya ji. Hannunsa na janye da akwatin kayanmu. Ni kuma gabad'aya jikina ne ya shika sakamakon rashin kamilalliyar suttura ajikina. Towel ne ya dan sauko kasan gwiwata amma duk sharab'ata a waje take sannan kuma kaina babu dankwali babu sabon kitso.
Na dube shi ta kasan Ido har yayi wanka ya canza kaya marasa nauyi. Ya dan tsaya nesa dani yana ce wa." Amina ga kayanku nan, idan kun kammala sai ku fito mu ci abinci, domin Ina so na fita kafin magriba."

A nutse na ce." To shikkenan. Har ya juya zai fita sai ya kara dawowa ya tsaya kusa da ni. " Kin ga text dina shekaran jiya ko?''
Na dube a hankali na ce." Wane irin text?"

Ya kalli cikin idona sosai ya

Please Login or Register in order to submit comment