Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jinya kada ka yi mamaki.
Na karaya sosai da sosai cikin kukan da nake ta dannewa na ce." Ba zaka mutu a gidana ba, wane hali kake so na shiga wasu cewa za su ni ce na kashe ka."
Ya yi shiru bai ce komai ba. Na cigaba da kuka a hankali don ba na so dalilin abinda yake faruwa Yusura ta tashi. Kansa da yake cinyata nake ta shafawa ina ta jijjigashi domin na rasa ma abinda zan yi, ba na ajiyar magani balle na bashi gashi an yi ruwa dare ya tsala ba na tsammanin za a samu masu chamis.
Agogon da yake d'akin na duba sha biyu da arba'in, ruwan ya d'auke tsaf. A hankali na sauke kansa na janyo zannuwan na rufe shi gabad'aya har fuskarsa na tashi zan fita. Na ji ya ce." Ina za ki je?"
Da sauri na ce." Zan duba shago ne idan ba su kwanta ba sai na ce Hamusu ya duba chamis mafi kusa a samo maka magani.
Ya ce." Dawo a bari sai gari ya waye abu daya za ki yi mini na samu bacci."
Na dawo na zauna ina fad'in." Menene?
Ya tashi zaune yana kallona muka zubawa juna ido da gaske ciwo yake domin alamun hakan ya bayyana a fuskarsa.
Ya furta." Ni ban iya mura fa ba, tana galabaitar da ni sosai, ki shimfidar da katifar."
Ban ce komai ba na tashi na yi abinda ya bukata domin ni a wannan ga'bar kokarina kawai na samu bacci ya d'auke shi da safe koma menene sai ya faru.
Ya dube ni a hankali ya ce." Cire hijabin ki kwanta."
Wallahi sai a sannan na tuna da karamin hijabi a wuyana."
Na cire na kwanta kamar dai yadda ya buk'ata, na zuba masa ido ina jiran ganin abinda zai yi a gaba. Ya hayo katifar da zannuwan dana rufe shi kawai naga ya kwanta a saman jikina ya fara gyara zannuwan domin lullube mu.
Jikina ya d'auki zafi sakamakon zafin da jikinsa yake yi, shiru kawai na yi ban ce masa uffan amma shi kansa ya san ba zan iya daukarsa a haka har garin Allah ya waye ba kamar akwai zalinci a ciki.
Cikin d'an karamin sauti a daidai fuskata na ji hucin numfashinsa Yana fad'in. " Zan d'an fi jin sau'kin sanyin da yake damuna, idan kin gaji sai ki maye gurbina."
Cikin d'an jan numfashi na ce." Ban gane na maye gurbinka ba, amma kai ma kasan hakan ba zai yiwu ba ko kana fa da nauyi.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky
*TALLAH!*
*Albishirinku mata an walisa matan da suka amsa sunansu mata, waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na awa da awa Waya tamkar da dubu, sha undum, mai suna?*
*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*
*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*
*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*
*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*
*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari asa_asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da buata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*=G<
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse melaabin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da a mace duk ramarta, da anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin daWi*
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456
*45*
"Duk nauyina ai ban kai ki ba, na ce idan kin gaji ki dawo samana shikkenan ko?"
Shiru na yi. Muka cigaba da sakin numfashi jikinsa ya fara shikawa alamun bacci ya fara d'aukarsa. Daga zarar na motsa zai motsa shima. Na furta." Gaskiya sai dai ni na maye gurbinka da kyar fa nake numfashi wallahi ka fi ni nauyi."
Bai ce komai ba ya Birkita ya kwanta kan katifar yana fad'in." Hau shikkenan ko?'
Na gyara zannuwan na hau yasa hannuwansa biyu ya tallefeni na lullube mana jiki da zannuwan amma basu ratsa mu duka ba.

Cikin hukuncin Allah kuwa bacci mai nauyi ya kwashe shi. A hankali na zame jikina na dan kwanta a gefansa Ina kallonsa yana sauke numfashi mai tafe da sarkewa daga kirjinsa ya yi. Har yanzu ina jin d'umin jikinsa a jikina da gaske zazzabi da mura ne suka kama shi da gaske.
Zannuwan na gyara sosai ya rufe har kafafunsa amma ban da fuskarsa saboda fitar numfashi.
Na yi amfani da wani karamin mafici na roba Ina dan kore masa sauron da yake ta zarya a d'akin.
idona biyu asuba ta yi. Masallatai ana ta kiraye kirayen sallah.
Na tashi zaune a hankali ina dubansa lokacin ya motsa da wani irin tari wanda yake nuna alamun k'irjinsa a cushe yake da majina.
Cike da zullumi cikin zuciyata na kama salati domin ni a ganina wannan dan dukan ruwan bai kai ace ya lafke irin haka ba.
Ya tashi zaune yana cigaba da tarin na zuba masa ido har ya lafa a hankali na furta."Sannu."
Ya amsa can kasa kafin ya ce." Ya zan yi na yi sallah ne, ni kaina na fara nadamar zuwa gidan nan naki Amina."
Na dubi rijar jikinsa duk ya yi wata kala ya firgice na dan ji tausayinsa kad'an domin da gaske baya jin dadin jikinsa.
Na ce." Ni ban san yadda za ka yi ba. Ga kayanka nan duk sun jike har gajeran wandon da singilitin."
Ya yi shiru yana dubana kafin ya furta "Zan yi sallah a haka ai akwai uzuri ki zuba mini ruwa." Ban ce komai ba na tashi na shiga bandakin da yake jikin d'akin na zuba masa ruwa a buta Na fito lokacin har ya sauko daga katifar na bashi hanya ya shige bandakin.
Dadduma na shimfida masa na jira shi ya fito tukkuna ni ma na shiga na dauro alwalar....
Koda ya idar da sallar katifar ya koma ya kwanta bai ce mini komai ba a wannan karon tarin shi yafi matsa masa.
Ni ma ban ce dashi komai ba na kwashi kayansa na fita dasu. Na samu Yusura tana motsi na dan bubbigi kafarta ta tashi da sauri na ce." Taso ki yi alwala."
Na fita tsakar gidan da kayan a hannuna wanke su na yi tas na shanya cikin ikon Allah rana ta fito mai haske sai na mayar da kayan idonta domin su yi saurin bushewa.
Yusura ta fito tana fad'in." Mommy ina kwana mun yi baki ne?"
A takaice na bata amsa da cewa." E jiya kina bacci ba."
Ba ta sake cewa komai ba ta nufi kicin tana cewa." Dame zan fara mama"
Na ce." Ki dora ruwan shayi ki sanya kayan kamshi sosai ki dan sanya barkono a ciki ko uku ne."
Ta amsa da sauri kafin ta bude kicin din ta shiga.
Na sake komawa d'akin na kwashe takalmansa na shige masa dasu ciki. Na dube shi har yanzu bacci yake yi lakadan.
Wayata na d'auka na fito falon na nemi Hamusu yana d'agawa na ce." Ka tafi asibitin ne baka shigo mun gaisa ba."
Da sauri ya ce." Haba dai anti na ce bari na dan jira gari ya kara yin haske sai na shigo mu gaisa kafin na wuce ko kina bukatar wani abu ne.
Na ce." Sosai kuwa wai d'an dukan da ruwa ya yi muku jiya fa Yallabai na kwance kashir'bar mura da zazzabi har da tari sun kwantar dashi."
Cike da damuwa ya furta." Subahanallahi! ai anti shiyasa nake ta ce miki ki bude kofar kin san akwai yanayi na girma da shekaru bayan haka kuma jikin bai saba ba, ni kin ga lami lafiya na kwana kuma na tashi garau da ni, ba na jin wani sauyi.
"Hakane yanzu nan babu wani chamis da suka bude tunda yanzu gari ya waye kana da abun hawa ka je can asibitin wurin masu sayar da magungua ka samo masa maganin mura da tari amma mai kyau."
Da sauri ya furta." Anti ba ma sai na je har can ba Ina fita babban titi zan samu."
Na ce." Shikkenan sai ka dawo.'' Shi ya riga ni kashe wayar kafin na ce me na ji tashin karar babur d'insa Hamusu kenan.
D'akin na koma ina jin Yusura na ta aikace aikace sosai yarinyar ta horu da aiki gashi nan babu abinda ba ta iya ba na rayuwa.
Ido a bud'e na same shi yana numfashi da baki. gabana ya bada wani irin sauti rass! yadda ya tsayar da idanuwansa a saman rufin dakin sai naga kamar wanda ba a jima da zare masa rai ba.
A sukwane na nufe shi kafafuna na kyarma. duban da ya yi mini shi ya dan sassauta fargabata. Na zauna kusa dashi ina fad'in ." Ka tashi ga tea na dafa maka mai kayan kamshi zai taimaka maka sosai muryarka ta bude yanzu Hamusu zai kawo magani sai kasha, amma ni ba na tsammanin wannan dukan ruwan ne ya haddasa maka wannan murar saboda ka fa yi tafiyar mota."
"A jirgi na zo ni malama." Ya fad'a yana lumshe idonsa. Na ce.'' Na sani amma ai ka ninka dambatta sau biyu wannan iskar daka sha'ka ta isa sanya maka lalurara.
"Ke a tunaninki a wace irin mota nake irin wannan tafiyar?"
Shiru na yi ina nazari. Gaskiya ne a irin motocinsa babu wata kafa da iska zata shiga har ta janyo masa toshewar hanci manyan motoci ne masu tsaro.
Ya furta." Ko kin so ko kin ki kece sila, ni ai ban zo da niyyar kwana ba ruwan da ya ritsa dani ne, kuma na gaya miki sulhu na zo wurinki ba wani abu ba."
"Ai sulhu ya k'are tsakaninmu na gaya maka ba zan koma can ba gaskiya abinda yake zuciyata kenan."
Na fad'a tare da kawar da kaina gefe.
Ya nisa kafin ya ce." Na ji amma kin san kema ba ki da hujjar da za ki ce sai a nan za ki zauna ko ba zai yiwu ba, muddin na amince miki akan bukatarki dole ni ma ki bi ra'ayina ki zabi daya daga cikin gidajen da nake da su anan ki zauna."
"Menene da nan din?"
Bai kai ga magana ba attishawa ta tare shi ya dinga yi har sai da na tashi na nemo masa tissue ya dinga fyace majinar data tsinke. Ya tara tissue din a wuri d'aya na kwashe na je na zuba ashara na dawo na same shi har yanzu yana ta attishawar dai.

Kada ki karanta littafin nan ba tare da kin biya ni hakkina ba. Littafin gudun aure na kudi ne.

Lallai a yau na sake tabbatar da cewa mura tana daya daga cikin manyan laluran da suke galabaitar da jikin dan adam, daga jiya zuwa yau gabad'aya kamminsa sun canza fuskarsa har ta dan kumbura ga dukkan alamu ma dai yana da matsalar sanyi a jikinsa shiyasa da aka motsa shi ya tashi gabad'aya.
Fita na sake yi daga d'akin na samu Yusura tana soya indomi da kwai na ce ta miko mini fulas din shayin da yake gefanta ta had'o mini da kofuna biyu masu dan girma na gilas.
Na sake komawa d'akin yana kashingide attishawar ta lafa.
Ya bi ni da kallo a lokacin da na krasa wurin da yake har na tsiyaya masa shayin da yake ta tiriri da k'amshin kayan shayi bai d'auke idonsa daga kaina ba. Ni ma ban ce masa komai ba na fara motsa masa shayin har sai da ya yi daidai yadda zai yi dadi sha. Na mika masa babu jayayya ya kar'ba har da godiya.
Gefe na zauna ina d'an sauke ajiyar zuciya. Na ji yana cewa." Har yanzu ban gayawa Hajja kina garin nan ba, haka zalika ma na gargadi Yusuf akan kada ya sanar mata Ina so ni dake mu gama magana yanzu da daddare na d'auke ki a mota domin ki duba gidan da za ki zauna."
Ba tare da na kalleshi ba na ce.'' Wai me yasa ba ka so Hajja ta san abinda ya shafe mu ne, kada fa ka manta mahaifiyarka ce, baka da hurumin boye mata abinda yake faruwa da rayuwarka."
"Wannan ai ba abin alheri ba ne shiyasa nake lullube mata."
Na ce.'' Yanzu ka amince kana kuskure ko?"
Ya d'aga mini kai alamar E.
Girgiza kaina kawai na yi ban kuma yi mamakinsa ba domin duk abinda yake yi mini a yanzu yana yi domin ya samu kaina, shiyasa duk abinda na ce ya yi kai tsaye yake amsawa babu ja'inja, a ganina kuma hakan ba zai hana shi watarana idan na ha'kura ya sake kuntuka mini ba."
"Na ji dadin shayin nan sosai na gode miki."
Maganarsa ta dawo ni da hayyacina. Na dube shi sai na ga yana kallona shima kafin a hankali ya ce." Kin kasa samun nutsuwa ballantana ni ma na samu nutsuwar da zamu cigaba da gudanar da rayuwarmu, akwai abinda nake so na gaya miki wanda ya shafe mu ne gabad'aya da duk wani makusancina amma ina fargabar ki juya mini magana ko ki ji kamar da gayya na gaya miki."
A tsanake na ce." Ni babu irin wannan gilin a zuciyata me zai sanya ka sanar da ni alheri kuma na ji b'akinciki idan ba ka sanya ni daya daga cikin masoyanka ba to na tabbatar zan zo a ta biyu don haka ina yi maka fatan alheri akan duk abinda ya sami rayuwarka."
"Na gode sosai, Allah Ya yi miki albarka."
D'akin ya yi shiru ni ina ta jiran na ji ya gaya mini abin alheri ya yi shiru yana ta kurbar shayin yana lumshe ido da gaske ya yi masa dadi. Na ce.'' Idan bai isheka ba akwai sai na tsiyaya maka."
"A a, ya isa wannan din an jima dai kafin na tafi zan kara shan wani."
Na kar'bi kofin daga hannunsa na ajiye sai na ji ya ce." Kin cire key din motata cikin aljihun rigata ko?"
Ban ce komai na janyo handbag d'ita na d'auko masa mukkulin .
"Ina Hamusu ba shi ya bude motar ya debo mini wayoyinsa.
Rufe bakinsa ke da wuya Hamusu ya shigo gidan na tashi da sauri na fita na same shi suna magana da Yusura hannunsa ri'ke da ledar magungunan na kar'ba tare da mika masa key din motar na ce." Yallabai ya ce ka debo masa wayoyinsa a mota."
Ya kar'ba ya fita da sauri
Allah Ya sa jiya da ya yi mini sayayya ya sayo rowan roba swan na d'auki daya na sake komawa d'akin.
Na ce." Ga magunguan wayoyin kuma yanzu zai kawo."
Ya kar'bi ruwan da maganin Ina daga tsaye duk Ina kallonsa ya 'balli maganin ya sha. Na ce." Ko na dan dafa maka wani abu mai dan nauyi kafin ka tashi nasan maganin mura da kashe jiki wata'kila ma bacci ya d'auke ka yanzu."
Ya ce." Da kuwa kin kyauta amma towo na garin dawa, miyar kuka kuma."
Na ji shigowar Hamusu a karo na biyu muryarsa a falo yana fad'in." Anti ga wayoyin." Fita na yi da sauri na amso masa shi kuma ya juya zai fita na ce." Akwai abin kari Yusura ta yi Hamusu ka zauna ka karya zata had'a maka komai sannan don Allah idan ka shiga cikin gari ka hado mini kayan towon dawa."
Ya ce." In sha Allahu anti."
K'aramar wayar a kashe take babbar ce a kunne na mik'a masa ya kar'ba cikin nutsuwa ya fara dubawa, ganin haka sai na juya zan fita hankalinsa na kan wayar ya ce." Ina za ki je kuma ke da ki ke jinya."
Dawowa na yi na zauna ban ce komai ba.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky

*TALLAH!*
*Albishirinku mata an walisa matan da suka amsa sunansu mata, 
waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na awa da awa Waya tamkar da dubu, sha undum, mai suna?*
*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*
*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*
*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*
*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*
*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari asa_asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da buata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*=G<
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse melaabin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da a mace duk ramarta, da anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin daWi*
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456


*46*
Ya d'an duba abinda zai duba kafin ya dube ni a nutse ba tare da nuna nishad'i ba ban dai sani ba ko b'oyewa ya yi ya furta." Kin san da cewa Hauwa tana da juna biyu?"
Gabana ne ya buga da karfi sakamakon jin maganar da ta yi tsalle ta fito daga bakinsa ban kuma tsammaceta anan kusa ba.
Sai da na yi namijin ko'karin daidaita kaina don gudun kada ya gane kid'imewata na kar'bi maganar da ya dumfare ni da ita da annashuwar da ban shirya yinta ba na ce." Kai ma sha Allah ko shine dama abinda ka ke cewa za ka gaya mini?"
Ya gyada kansa da kwarin gwiwa ya furta." Kwarai kuwa na so na gaya miki tun kwanakin da suka shige to ban san yadda za ki ji a ranki ba, sai kuma wannan rikicin ya b'alle a tsakanimu zan fi so ki samu nutsuwa mu daidaita a tsakaninmu ke ma ki samu na ki cikin zan ji dad'i na ga kuna yi mini jereran haihuwa."
Na danne abinda yake yun'kuro mini na tsantsar kishi da tausayin kaina na furta." Na taya ku murna sosai, Ubangiji Allah Ya raba lafiya ya kuma raya abinda za a samu. Maganar na samu ciki na haihu ina ga abu ne mai wahala domin ba abin wasa ba ne d'aukar ciki da rainonsa balle a zo kan k'adami na haihuwa. Tunda har jininmu bai hadu ba ina ganin mu ha'kura kawai da haihuwar nan Yallabai ai kai baka da matsala ni ce ma abin tausayi."
Na kare maganata idona a tsakiyar nasa idon.

"Ina ce wannan maganar mun rufe babinta tun wattanin da suka gabata dalilin da ya sanya fa kenan nake jin shakkun gaya miki saboda na fi kowa sanin halin rigimarki."
Na ce." Me ka mayar da ni mara son zaman lafiya ko me? ko duk wannan addu'ar da fatan alherin da na yi muku baka gamsu ba har sai ka jefe mini magana idan ka boye mini cikin matarka ai ba zaka 'boye mini haihuwar ba tunda ba zata ta'ba dawwama dashi a jikinta ba."
Shiru ya yi mini bai tanka mini ba.
Hakan ya kara dagula mini raina. Gabad'aya ma sai nake ganin yana so ne ya raina mini wayo ne ya muna tsaka da rikici ya wulakanta ni har da tukwicin saki ban yi masa komai ba kuma ya zo ya ce mini na taya shi murna akan wane dalili. Haushinsa da nake ji sai ya dawo sabo dal, na ji kamar na ce ya bar mini gidana amma babu halin hakan.
Ya kwanta tare da rufe idonsa yana jina ina ta sakin maganganu bai tanka mini ba. Na goge hawayen da ya d'an zubo mini a kumatu na tashi na fita.
Hauwa tana da ciki wannan ya nuna cewa daga zarar ta fara haihuwa zata kar'bi gidan. Ni kuma saboda son zuciyarsa na d'auki ciki na yi wahalar rainonsa da nakud'a na haihu daga baya abinda na haifa ya mutu. Ita Hauwa itace mai rayayyun 'ya'ya kenan.
Kishi ya rufe mini ido gabad'aya tunanina ya kulle har sai da muka yi waya da Anti Yagana ta sake mayar da ni hanya tukkuna na dan samu sasaauci tabbas Allah ne mai yi kuma shi ne mai kashewa da rayawa. Idan ya so duka yaran da Hauwa zata haifa su zama rayayyu idan ya so kuma ya d'auki ransu ba kuma tare da

Please Login or Register in order to submit comment