Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce." Ina kwana."
Ya amsa amma bai dago ba."
Na d'an zuba masa ido Ina nazarinsa wato kamar ba shi ne mutumin nan na jiya da daddare ba, sai wani hade rai yake yi.
Na gyada ina dan jin zafi abinda yake yi mini a cikin raina. Gabad'aya yanzu ya gama sare mini, kuma dama tun farkon auranmu ban manta ba ya ta'ba gaya mini Allah ya ba ni ha'kurin zama da halinsa. Ashe ya san yana da wahalar sha'ani.
Wata'kila dama yana jira mahaifiyarsa ta tafi sai abin ya k'ara tsamari tunda tun tana nan yake d'an yi, yanzu kuwa babu wadda zata gaya masa ya ji. Itama Hauwan wanene ya san abinda ya guma mata.
Na daure zuciyata na ce." Dama zan gaya maka ne jiya anti Yagana take gaya mini ana biki a can garinsu mamanmu maiduguri shine aka ce a gaya mini, to ina so zan shirya gobe ko jini sai na wuce."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba, kamar ma bai ji abinda na gaya masa ba.
A da kufule na ce." Ka ji."
Bai dube ni ba ya furta." Ban bari ba."
Sai na ji wani 'kullutun abu ya tokare mini a wuya, duk irin suburbudar da ya yi mini jiya da abinda zai saka mini kenan, ai tsayin shekara da wani abu ban ta'ba tambayarsa zuwa wani wuri ba, ban yi tsammanin zai hana ni ba.
Zuciyata na yi mini zafi na ce." Dada ce fa ta ce a sanar mini, 'yan uwa duk za a had'u kowa zai je, to ni me yasa zaka hana ni, tun fa da na zo garin nan shekara har da doriya ban je wani wajan ba."
"Ni dai na ce ban bari ba." Ya fad'a hankalinsa a kwance.
Kawai sai na ji hawaye sun fara gudana a kumatuna. Ina jin dai d'an tahalikin nan ciwo yake so ya haddasa mini.
Ya dago kai yana kallona lokacin da kukana ya yi karfi.
Sai ya mayar da kansa ya rufe laptop ya rufe ya dan gyara zamansa yana dubana amma bai ce komai ba.
Naja hanci a shake na ce." Wannan zalincin ya yi yawa, kwata-kwata ka hana zuciyata nutsuwa kullum sai ka gumama mini b'akinciki, ban san me na yi maka a rayuwa ba a rayuwa."
Ya ce." Me na yi na zalinci, ba yunwa ba ishirwa haka zalika ba tauye hakki a shimfida, don kawai na hana zuwa unguwa shine zalinci."

Na ce." Zalinci ne mana, kana fita ka yi walwala ka hadu da 'yan uwanka ku gaisa, ni ma na gaya maka Ina so na ga dangina domin Ina kewarsu ina so kuma zuciyata ta samu sasaauci."

"Ko da ke, ko babu ke, za su yi bikinsu, ba ni so iyalina su yi nisa da dai kusa ne sai na barki amma gaskiya maiduguri ya yi nisa, kuma kin ga sai kin yi kwanaki kafin ki ce zaki dawo."
Jin ya fadi haka ya sanya na ce." Ai kai zaka fad'i kwanakin da zan yi."
Ya yi shiru yana lumshe ido kamar me shirin bacci.
Na dawo kusa dashi na zauna na ri'ke hannunsa a hankali na ce." Ka ji my love."
Ya bude idonsa da suka dan canza yana kallona ya ce ." Yaushe rabon da na ji wannan sunan abakinki, yanzu ai kina bukatar zuwa biki ko?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Ya girgiza kansa tare da sake rufe idonsa. Jikinsa na sake matsawa sosai a hankali na ce." Ka ji sweet love." Bai tare da ya bud'e idonsa ba ya ce." Matsa kada ki sanya na yi abinda ban yi niyya ba."
Ban matsa ba, sai ma hannuna dana sa Ina d'an jan gemunsa a hankali.
Ya bude Ido muka tsirawa juna ido.
Hauwa ta turo kofar d'akin ta shigo hannunta ri'ke da wani kwando cike da kayan abinci.
Janye idonta ta yi ta wuce can wajan da yake zama domin cin abinci ta fara shirya wurin.
A hankali na dan matsa daga kusa dashi ina fad'in." Ka amince ko?"'
"Zan yi shawara tukkun zuwa yamma zan gaya miki abinda na yanke."
Don kada ya tsinka ni a gabanta ya sa na tashi daga kusa dashi ba tare da na ce komai ba na kama hanya fita. Na ji ta ce." Amina tsaya kawai a yi ta ta kare, ba zan bari a ginu a haka ba domin dukkaninmu musulmai ne, ba maguzawa ba, idan shi mijinki yana jin tsoronki, ni gaskiya ba a haifi wata mace da zan ji tsoro ba, kuma ba zan yarda na yi zaman boranci ba, ba kuma zan yarda a tauye mini hakki ba."
Na ce." Akan me kike wannan zantukan."
Da mamaki da takaici ta ce.'' Au tambayata ki ke yi akan me nake yin magana."
Na ce." 'Kwarai kuwa."
Yana zaune yana jin mu bai ce komai ba.

Ta ce." Jiya girkin waye?"
Na ce." Oho!"
Ta zo iya wuya kawai sai ji na yi ta lallayo ashar ta jefo mini tana huci." Ni za ki mayar sakarai, kina abu kamar mai tabin kwakwalwa, na rantse miki da Allah ba za mu wanye lafiya dake ba, tunda ni ban shiga huriminki ba, ba zai yiwu ranar girkina ki dinga yi mini kutse ba."
Na dube shi shima yana cike da mamakin zagin da ta yi don sai hararta yake.
Na ce." Ka ji tana zagina ko?"
Ya ce." Je ki kawai, ki kyale ni da ita."
Ta kara fusata tana cewa." A dake ni a hana ni kuka, kuma a ce ba zan yi magana ba, sai ta fashe da kuka mai karfi
Ya ce." Idan zagi ne ni zaki ga domin ni na kwana da Amina a ranar girkinki, amma ita bata da lefi, Hauwa wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe kada ki kuskura na kara jin zagi a gidana, kin nuna mini rashin tarbiya da kuma rashin aiki da ilimi.
Ni ba namijin da mace take d'agawa hankali ba ne, ni na yi miki ba daidai ba, a wurina zaki nemi hakkinki, ita Amina ai bata da lefi.
Ta sake fusata tana cewa." Haka zaka ce ko? Ni me yasa ba ka nemana a ranar girkinta duk da bata zuwa dakinka ai baka taba zuwar mini da bukata ba."
Ya ce." Ai shiyasa na ce miki a wajena za ki nemi hakkinki, domin itama dole na yi mata."
Ina tsaye ina jinsu duk abinda ta fad'a a kaina sai ya tare maganar yaki bari sunana ya fito. Cikin raina na ce idan don na ji dad'i ne ban ji ba, domin kuwa wataran ni ma zai iya kware mini baya a gabanta, na bude d'akin ba fita na barsu suna ta turzawa, amma na yi mamakin sosai, domin ni a tunanina tunda ba na zuwa dakinsa ranar girkina ita da shi suna kwanciyar aure, ashe zargin hakan kawai nake, ashe shine dalilin da ya sanya jiya ya famshe kwanakinsa.

Yini na yi cikin zullumi da tunanin zai barni ko ba zai barni ba.
Har na yi shirin kwanciya sai gashi ya shigo shi ma da shirin kwanciyar na zuba masa ido har ya k'araso ya zauna a gefana, yadda nake kallonsa shima haka yake kallona.
Na daure na ce." Da ka sani ka ce na fito falo sai mu yi magana, kada ta zargi wani abu."
Ya ce." Ina jin tsoronta kenan?"
Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ba haka nake nufi ba, kai zaka nemi zaman lafiya a gidanka."
"Kada ku zauna lafiya don Allah kin ji ko."
Jan bakina na yi na shiru na rabu dashi abinda dai na kudire a raina shine idan za ta ce zata yi mini hayaniya ko ta zage ni kaniyarta zan ci, tunda ga wanda ya yi mata nan
Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Na kira Anti Yagana a waya kan maganarmu dake ta d'azu."
Yanayin yadda ya yi maganar ya sanya ni jin sanyi a cikin raina, har ga Allah ina jin dadin yadda yake mutunta anti Yagana har ya sakaya sunanta.
Na nutsu Ina kallonsa. Ya cigaba da cewa." Na amince za ki je amma da sharad'in kwana uku kacal za ku tafi a jirgi ke da Yusi da Sukairaju nasa a yi muku shirin hakan, kada ki sa'ba umarnina."
Da sauri na ce." In sha Allahu na gode sosai Allah Ya kara girma." Ya amsa da "Amin." Kafin ya cigaba da cewa." Ni ma yana da kyau na bada gudumawa ko."
Murmushi na yi ban ce komai ba.
Ya ce." Nawa ki ke ganin zan basu."
Na dube shi sai na dan ji tausayinsa, shi dai abin sa bai rufe masa ido ba.
Na ce." Ko nawa ka basu sun gode."
Ya ce." Ai shawara na tambayeki sai ki ce mini ka basu abu kaza."
Na ce." Wallahi ban san abinda zan ce maka ba.
Shiru ya yi yana lalube a wayarsa.
Shigowar sa'ko na ji a wayata dake gefana na d'auka ina dubawa miliyan goma ne.
Na dube shi cikin mamaki mai tsanani. A nutse ya ce." Ki cire miliyan biyar ki basu gudumawace ni dake. Miliyan biyar din kuma kudin yaranki ne wanda na yi muku alkawarin satikan da suka wuce ba ke kadai na bawa kuna da yawa.
Na ce." To ai ni ban ce ina neman hakki ba."
"Idan ba ki ce ba yaran fa?" Ya fad'a yana kallona.
Na ce." Ni dai gaskiya dawo maka dasu zan yi wallahi.
Ya mike yana fad'in." Ki dawo mini dasu sai ki ga 'bacin rai, ki ajiyewa yaran zasu amfana anan gaba in sha Allahu, kuma koda jita jita zata sake tashi a gari ba zasu zarge ni ba.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky

*TALLAH!*
*Albishirinku mata an walisa matan da suka amsa sunansu mata, waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na awa da awa Waya tamkar da dubu, sha undum, mai suna?*
*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*
*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*
*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*
*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*
*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari asa_asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da buata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*=G<
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse melaabin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da a mace duk ramarta, da anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin daWi*
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456

*33*
Kawai sai na bi shi da Ido bakina ya yi nauyin da na kasa ce masa komai ya bud'e kofar d'akin ya fita.
Gari yana wayewa na kira Anti Yagana a waya muka gaisa sosai na ce." Ashe kun yi waya da maigidan."
Ta ce." Jiya ba ya kira ne domin karin bayani akan maganarku ai ya ce zaku taho gobe ma."
Na ce." E in sha Allahu anti Yagana amma don Allah don Annabi duk abinda na zo muku dashi kuyi mini kyakykyawar fahimta."
A sanyaye ta ce." Me Kuma ya faru?"
Na ce." Sai na zo din kawai zan miki bayani." Ta ce." Ni wallahi kin kashe mini garkuwar jiki Amina, ba fa na san fitina yadda mijin nan naki yake sonki me zai miki."
"Humm! Anti Yagana kenan akwai matsaltsalu sosai, ke ba za ki gane ba ne wani irin mutum ne."
Ta bata rai tana cewa." Kamar yaya wani irin mutum duk mazan fa haka suke Amina daga manya har yara, kin san Allah akan mutumin nan zamu 'bata."
A sanyaye na ce." Anti Yagana me ya yi zafi haka ni ce fa taki,
Ina ganin yana da kyau ki dubi uzurina."
"Ki gaya mini kawai yanzu ina jinki ba na so ki barni da damuwa a raina.
Ajiyar zuciya na sauke na ce." Anti Yagana kin san babban abinda yake lalata aure shine zargi ko?"
Ta ce." Kwarai kuwa."
Na cigaba da cewa." To shi wannan mutumin halayarsa ce, domin kuwa bashi da ta'ada mai kyau, ba na so tafiyarmu a haka ta ginu har tayi kwari, kin ga ina da kishiya ita kuma budurwa ya aureta. Ni kuma daga zarar mun samu sa'ba ni ya dinga ya'ba mini magana kenan, na auri maza biyu na yi harkar social media, ba ni da kunya ba ni da tarbiya, ina tallata surata a duniya zan 'bata masa suna maganganu da makamantan wad'annan, shine nake so manya su shiga lamarin nan dan gaskiya akan wannan wallahi a shirye nake da na rabu dashi."
A dan sanyaye ta ce." To me yasa ba ki gayawa Babanmu ba."
"Anti Yagana mutumin nan baya ganin girman Babanmu kin san ba wani girmansa ya yi da yawa ba yana ganinsa haka, shi ma kuma Baban namu ba zai iya tararsa da maganar ba, balle kuma Baba Sule."
Ta ce." To nan din idan ki ka zo wa za ki gayawa?"
Na ce." Anti Yagana ko ke ba za ki iya yi masa magana ba."
Ta ce." Na ce masa me? Amina ni kwarjini yake yi mini wallahi."
Na girgiza kaina tare da cewa." Shikkenan anti Yagana sai na zo din sai mu sake tattauna maganar.
Jikinta a sanyaye ta ce." To shikkenan Allah Ya kawo ku lafiya.

Baban Saude shine na biyu a gidansu Mamanmu mutum ne mai zafi da rashin san wargi, a iya tunanina shi kad'ai zan iya gayawa matsalata ya yi mata duban tsanaki, kuma ya tsage gaskiya duk d'acinta. Yadda na fahimta kwata-kwata ba zan samu goyon bayan anti Yagana ba domin gabad'aya mutumin nan ya gama dabaibayeta da alherinsa. Ba ita kadai ba ma kusan da wahala na samu goyon bayan duk wanda zan gayawa korafina akansa shiyasa sam ban tunkari Babanmu ba saboda na san zai tankwarani ne kawai ya ce na yi hakuri ko da kuwa ya duba maganartawa da k'amshin gaskiya. Anti Yagana tafi sha'kuwa da dangin Mamanmu tunda ita a can ta girma har ta yi aure, ni kuwa ban shaku dasu sosai ba domin har yanzu wasu daga ciki ma ban gama saninsu ba tunda gaskiya suna da family mai girma, shi kansa Baban Saude sai a shekarun baya na waye dashi domin matafiyi ne duk zuwan da nake yi ba na ganinsa sai an yi katari ya zo gida tukkuna, bashi da wasa ko kad'an kuma mutum ne mai dattako da sanin ya kamata, sannan kuma yana gaskiya dan ko hukunci za a yanke a family din akan ce a bari ya dawo.
Kudirin dana yanke kenan a cikin raina idan na je na huta zan ke'be dashi na gaya masa sai na ji abinda zai ce akan hakan don gaskiya duk mutumin da yake da hankali ya kuma san menene aure da zamantakewa ba zai dinga zargin matarsa ba Koda kuwa a gidan karuwai ya aurota.

Wannan maganar ita na sake jadaddawa anti Yagana bayan saukata a garin a kuma gidanta. Sai ta fusata ainun tana fad'in muddin za ta fad'a mini na ji to na janye tashin maganar nan a family domin abin zai zama abin gotsiri tsoma kowane aure akwai jarabawa a ciki, a cewarta muddin na ce zan dinga bankada sirrina kowa ya sani to a shirye wasu suke da su lalata mini aure, kuma don Baban Saude ya kashe mini aure ba abinda zai dame shi ba ne, tunda saboda tsaurinsa yaransa uku suna nan a zaune a gida suna zawarci saboda irin tijarar da yake yi wa mazajensu yau da gobe sun gaji sun koro su.
Na so na fahimtar da anti Yagana bafa nufina a kashe auran ba, a dai yi masa magana ya gyara kawai, ba zai yiwu ace don yana da iko ya zamana kowa yana shakkarsa ba, duk abinda ya aikata daidai ne ko da kuwa kuskurene. Na san ta san gaskiya kawai tana takewa ne dalilin dabi'unsa na bayyane kafewarta akan hakan ta sake tsamari da na gaya mata adadin kudin da ya bada gudumuwa sai ta kara jajurcewa kan cewa ba da yawunta a tozartashi ba.
Ni kuma na san baban Saude ba zai yi masa magana domin ya bata mini aure ba sai dan gyara ko da take fad'in yaransa suna zawarci ban yarda saboda halinsa aka yi masa haka ba face kaddara domin kuwa yana kishin nasa ne bai yarda a wulakantasu ba. Mazan na yanzu sun riga sun zama abinda suka zama don ita Allah ya taimaketa tana zaune da nata lafiya lau ba zai yiwu a ce kowa haka yake ba.
Duk da na ha'kura na bi umarninta ba ta daina jin haushina ba motsi kad'an sai ta ja tsaki tana fad'in." Allah Ya rufa miki asiri kina so ki butulce masa ko Amina, ni ganau ce ba jiyau ba, mutumin kamar ya tsuguna miki saboda kulawa amma lallai sai kin kago masa lefi, to ya ni ma ba zan ce kin fi sha'awar rayuwar tallata surar jiki ba, idan wasu ne suke rudarki wallahi za su kai ki su baro."
Na gaji dai na rushe da kuka domin tuntuni shi yake damuna, ta hana ni na yi magana kuma na hanu amma tana gasa mini bakaken maganganu. Na tashi na shige d'aki na kwanta ina kukan yadda zan yi.
haka aka yi shagalin bikin da ni cikin kunci domin duk yadda na so da na danne abinda yake damuna na kasa. Ni kaina ba zan so lissafin aure ba, to amma idan kaddarata ce hakan ya zan yi. Akwai fa matsaltsalu masu yawa dangane da zamana da mutumin nan amma ba kowane zai fahimci hakan ba.
Sai Babandi ya takura mini da tambaya domin shi ya yi mini farin sani bayan anti Yagana babu wanda yake saurin fahimtar damuwata sai su dalili ina da yawan wasa da barkwanci kuma koyaushe fuskata a sake take.
Matsanta mini da ya yi da tambaya ya sanya na dan tsakura masa kad'an daga cikin abinda yake faruwa
Ban ta'ba tsammanin zai fusata ba. Kawai ya dinga bala'i yana kumfar baki fadi yake yi Idan baya sonki ya sake ki mana akwai masu so da yawa shi bai san dami ya tsinta a kala ba.
Wannan ai jahilci ne ka auri mace tana zaune a gidanka kuma kana zarginta dan kin auri maza biyu kafin shi shine me? Wallahi ko yau ya sake ki ni zan aureki, idan ma kin ce ba kya sona akwai wanda zan hada ki dashi saurayi kuma mai rufin asiri, dama sautari auran masu kudin nan ba tomo ba ne.
Da kyar na sassauto dashi ya yi shiru sai huci yake yi abin ya dinga ba ni mamaki. A wurin kafin mu rabu na nuna masa cewa lallai dole ya boye mini sirrina ba na so kowa ya ji, shi ma na gaya masa ne domin ya ba ni shawara, dan idan ya fasa maganar kowa ya ji mai raba ni da anti Yagana sai Allah.
Illai kuwa duk kaffa kaffan da nake yi sai da ta tsargu ganin mun fito daga storoom din gidan tare muna magana tana cikin jama'a amma kaf hankalinta yana kanmu..
Gabad'aya jikina ya yi sanyi na wuce na karbo abinci cikin fulas na nemi Yusi dake can cikin yara na bashi ya kaiwa Sukairaju can gidan anti Yagana tunda tare muke ya zame mini jela duk inda zan je yana bina a baya bisa bin umarnin ubangidansa. Gidan bikin ne na ce masa ba na so ya biyo ni kawai ya zauna zan aiko masa da abinci shi ma ba a son ransa ba sai da na hada da fad'a tukkuna.

Muna komawa anti Yagana ko ta bari mu huta ta fara surutai. " Idan Babandi ya zugaki kike kashe auranki Amina bai wuce shi din ya aureki ba tunda na gane dama tuntuni yana sonki bai fad'a ba ne sai yanzu, to me na sama ya ci balle ya bawa na k'asa. A yadda kike Amina ai sai irin su Alhajin Tajon din, shi din ma sai dai Allah ya k'wace shi, amma muddin Babandi ya aureki sai ya gane shayi ruwa ne shege yana yawo da bakar fuska.
Duk da kuncin da nake cikin sai da na yi dariya na ce." Anti Yagana ina da wani mugun hali ne da za ki ce haka, ni fa abinda kike zargi ba shi ba ne, kin san dai Babandi mutumina ne ko?"
Ta share ni ba ta ce mini komai ba, amma motsi kad'an za ta yi kwafa ta girgiza kanta tabbacin abin yana damunta. Sai ta ba ni tausayi domin na gama fahimtarta ita dai kokarinta ta danne ni na zauna saboda kada duniya ta zage ni, a kuma yi mini lissafin aure shine kawai abinda take gudu.
Da daddare misalin goma da wani abu ya kira ni a waya. Dama tunda na sauka a garin sau d'aya mukayi waya kuma shi ya kira ni. Ina sane na ki d'agawa har sai da ta katse ya sake kira ta katse a k'alla sai da ya kira sau hud'u na daga ina sallama.
Ya ce." Wanene Babandi?"
Gabana ya buga da karfin gaske! jin sunan Babandi a bakinsa. Da kyar na daure na ce." 'Dan uwana ne."
"Shine kuka 'keba a wajan da babu gilmawar mutane? idan dan'uwanki ne me zai sanya ba za ku tsaya a bainar jama'a ba."
Na daidaita nutsuwa sosai domin yin hakan shi kadai zai kwace ni daga mummunar zarginsa. Shin a ina ma ya san na yi hira da Babandi.

Don girman Allah ki tausaya mini ki biya ni hakkina idan har kina karanta wannan littafin kada ki bari hakkin wani ya kamaki.

"Anan din ma sai ka tuhume ni akan abinda baka da hujja wai dan girman Allah a gidan karuwai ka auro ni Baba, ko kuma dai ka fara tu'ammalli da muggan kwayoyi da suke fad'a maka karya da gaskiya."

"Kina mamaki ne don na tuhume ki, ki ba ni amsar tambayata kawai idan har Babandi dan'uwanki ne na jini me zai sanya ki 'kebe dashi shi kadai, daga barin ganin idanun jama'a, idan 'yan uwantakar ta gaskiya ce mai yasa ba za ku yi hirar a kan idanun jama'a ba."

"Saboda akwai muhimiyar maganar da muka tattauna, Babandi Kuma d'an'uwana ne na jini tunda iyayenmu cikinsu d'aya, kuma tun kafin na

Please Login or Register in order to submit comment