Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ha'barsa a dokin wuyana. Cikin tsananin tashin hankali na fara ko'karin raba kaina dashi amma ban samu nasara ba domin wani irin riko ya yi mini mai tsauri wanda ya sanya lokaci kan'kani ga'bobin jikina suka fara amsawa
Ban san abinda ya gigitashi ba kawai ya dinga bin jikina yana shanshanawa yayin da hannuwansa keta mammatsa mini naman jikina. Sai na rushe da kuka mai tafe da kururuwa domin har ga Allah gani nake yi kamar Yana ko'karin keta mini mutunci duba da irin yadda lokaci guda babu wata sha'kuwa da ala'ka ta soyayya mai k'arfi a tsakanina dashi amma cikin 'yan sakkoni ya samu jikina yana luguigiutawa har da zura hannunsa cikin rigar mamana.
Na dinga doke hannun ina tunkud'eshi da bugun bayanshi ya'ki sakina ya ma sanya k'afafunsu duk biyun ya kanainaiye ni...Shi kansa hularsa da gilashinsa na gado sun fad'i domin a ki'dime yake baya cikin hayyacinsa. Da kyar da na samu ya cika ni, na tashi da sauri na d'auko hijabina na zura domin na lura ganin tsaraicina a waje shine ya asassa faruwar hakan tunda ai muna had'uwa wuri d'aya tsayin wattanin da nayi a gidan bai taba kwatanta rike mini hannu ba balle har ya rungume ni.

Kuka nake yi sosai gabad'aya na tattare a jikin bango banda so ya fita daga d'akin ba abinda nake yi. Ashe k'arfi ne dashi a haka duk da ba wani jikine dashi sosai ba amma yadda ya rike ni kamar ina hannun katon gardi. Gabana ya cigaba da bugawa sabili da tuna irin mutsukar da ya dinga yi wa tsokokin jikina.
Kusan mintina goma da faruwar al'amarin ya daidaita nutsuwa domin tunda na 'kwace yake kwance lakadan a gado kamar matacce ido a rufe sa'ilin kuwa da naga ya tashi zaune sai na sake tsorota domin gabad'aya ya zama wata kala fatar goshinsa tabi ta tattara kuma babu wani kuzurin kirki a tare dashi.
Ina kallo ya d'auki hula da gilashinsa ya sanya a idonsa ya zo ya tsaya daf da ni, ta cikin gilashin ya tsira mini ido babu yabo babu fallasa ya furta." Yau ce rana ta farko dana fara rungumar wata 'ya mace har na ji wani yanayi mai wahalar fassaruwa a tattare da ni, ban shigo nan da niyyar yi miki wani abu ba domin a raina na ajiye cewa na aminta da duk irin zaman da kike so ayi zan baki goyon baya. Na shigo ne domin na tambayeki dalilin da ya sanya kika daina zaman break fast tare damu, kuma ina so na tabbatar da shin gaskiya ne maganar da Yusuf ya gaya mini cewa abinci sau daya kike ci a yini wai saboda kada ki yi 'kiba to kuma sai lamarin ya canza domin ganin zahirinki ya tayar mini da sha'awata ta d'a namiji, kuma nan ba da jimawa ba zan yi kokarin ganin na kawar da ita." Ya numfasa kafin ya cigaba da cewa." Ina ganin babu amfanin horar da kai da yunwa domin zama yadda ake so, ke ai daka ganin ki jikinki na ki'ba ne duk abinda za ki yi domin guje mata sai ta riske ki, a shawarce kada ki kara yi wa kanki horo da hakan. Akwai abubuwan motsa jiki a gidan nan. Ki ci abinci ki koshi sannan ki dinga motsa jikinki, Ina ganin ko kibar ta riske ki ba zata yi miki muni ba. Sai kuma abu na gaba shine in sha Allah cikin satin nan zan turo likita za a yi miki gwaje-gwaje domin tabbatar da lafiya. Ni ma zan nuna miki result dina don hankalinki ya kwanta na yi gwaje gwaje na tun lokacin aurena da Matata Samira Allah Ya gafarta mata. Ni ba yaro ba ne, haka zalika kema ba yarinya ba ce, kin yi aure a k'alla har sau biyu kin san maza, ba zai yiwu a ce kina zaune a haka babu buk'atar d'a namiji ba. Ko ba ma son juna sai mu zama abokanan d'ebewa juna kewa ko ba haka ba ne?"

'Kokari na yi na dubi tsabar idonsa kamar yadda yake duban nawa na furta." Ni ba wani namiji da yake gabana a halin yanzu, maganar kuma ba ka taba rungumar wata 'ya mace ba ko al'kur'ani zaka dafa ka rantse mini ba zan yarda ba. Shin wai ko ka manta ni ce dai matar nan da ta zo ofis dinka ka kawo mata maganar banza. Idan ka manta ni ban manta ba, ka neman matan banza wannan shine abinda ka nuna mini tun kafin k'addarar aure ta shiga tsakaninmu.
Ai na san ciwon kaina duk da aure-auren da na yi nasan mazan dana aura nutsatstsu ne, cikinsu babu wanda ya ta'ba kawo mini irin maganarka. Don haka ni ban shirya yin wata mu'amula da kai ba a yanzu."

Babu damuwa a tare dashi ya ce." Ba zan rantse miki don ki yarda da ni ba. Ban ta'ba sanin wata mace ba har yanzu idan kin yarda shikkenan idan kuma ba ki yarda ba mu tafi a haka." Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Lokacin dana bijiro miki da buk'atata a can baya na jarrabaki ne,domin ina neman matar aure na kasa samu dalili duk wata mace da zata tunkaro ni da manufarta. Shigowarki ofis dina kawai na ji a raina bari na gwadaki sai aka ci sa a kika cinye. Lokacin na ji kin kwanta mini a raina Ina jin zan iya auranki duk da ba kya daya daga cikin jerin matan da nake burin na aura. Ashe Allah ya kaddara hakan dalilin da ya sanya kenan da Hajja ta nuna mini ke ban musanta ba, sai dai Ina ta jinjina mazan da ki ka aura shine kad'ai damuwata yadda nake saurayi nan ni ma ina so na auri budurwa domin na ji yadda ake ji."

Cike da takaici na ce." To ai hanya a bud'e take Malam sai ka auro budurwar bai dami Amina ba, yadda babu tsarin auran mace Irina a tare dakai ni ma babu tsarin auran namiji irinka domin har yanzu ban ji zuciyata tana sonka ba."

Na gaya masa hakan domin shi ma ya ji zafin da nake ji a cikin zuciyata. Bai nuna komai ba ya kara kusanto ni yana fad'in." Shiyasa ai nace mu dinga d'ebewa juna kewa kina da sha'awa ni ma ina da ita, ko babu k'auna a zukatanmu ai akwai muradin wani lamari da Allah ya sallad'a a gangar jiki da ruhi. Don gaskiya babu ra'ayin yin wani auran a yanzu, kuma ni ba zan iya zuba miki Ido ba bayan na san ke halalina ce, sannan Hajja na can a zaune tana jiran shekara mai zuwa ta d'auki jika, kin ga dole na yi kokarin cika mata burinta."
A sakarce na ce." Ai ni maza biyun sun ta'ba ni har na haihu, to me zaka samu a wurina, ai gwara budurwar tunda kai saurayi ne sai kuje ku gwada budurci da samartaka."

Murmushi ya yi kawai ya dubi agogon da yake daure a tsintsiyar hannunsa na hagu yana cewa." Ni dai na gaya miki cikin ko wane lokaci zan iya takarki don gaskiya ba zan iya jurewa ba. Domin ina ji a jikina akwai wani abu da ki ke amfani dashi don fizgar hankalina zuwa gare ki, amma in banda haka ni sam mata basa gaba."

Yamutsa fuska na yi tare da kawar da kaina gefe. A raina sai nake ta jin haushin yawan ambaton Samira da yake yi. Ko nauyina baya ji. kuma na gano yana sonta sosai tunda ya fad'a itace first love d'insa. Ya juya ya kama hanyar fita daga d'akin yana furta." Ni na fita ki kula da kanki."

Na ja jiki a sabule na nemi gefan gado na zauna Ina nazarin maganganun da ya yi kafin ya fita. Ban ga alamun wasa a cikin maganarsa ba idan na yi la'akari da yadda lokaci kan'kani ya nuna kwadayinsa a kaina kamar yadda ya fad'a cikin kowane yanayi zai iya zuwar mini da bukatarsa.
Gabad'aya kaina ya kulle a yinin ranar na rasa abinda yake yi mini dadi sai sanda Yusi ya dawo daga makaranta tukkun na dan sake. Tare muka ci abinci muna dan ta'ba Hira hana cewa duk lokacin da aka shirya zuwa duba d'an'uwansa Kamalu zai nemi izini a makaranta koda zata kasance ranar da karatu. Shi dai koyaushe maganar Kamalu idan kana so kaga dariyarsa to yi masa zancen d'an'uwansa. Sai na ce ai ya sha kuruminsa weekend za mu je ranar da makaranta.
To har karfe tara da wani abu maigidan bai shigo ba, abinda bai taba kasancewa ba kenan. Duk rintsi idan ya fita magariba a gida take yi masa sai dai a wasu lukutan yakan sake fita idan ta kama.
Yusi ya damu da maganarsa karshe dai kawai sai gani na yi ya kira wayarsa da yake shi da kansa ya siya masa waya sabuwa a cewarsa zata dinga taimaka masa wurin karatunsa kuma zata d'ebe masa kewa.
Har suka gama wayar idona yana kan yaron shi ma ya dube ni Yana cewa." Gashin nan akan hanya wai ya sallami wasu baki ne da suka zo masa.
A ta'kaice na ce." To Allah Ya kawo shi lafiya.
Minti goma Sha biyar tsakani ya shigo escort d'insa a baya daya da wayoyinsa a hannu dayan kuma da 'yar jakarsa. Kusa da Yusi ya zauna shi kuma da sauri ya k'ar'bi wayoyin dake hannun escort din nasa suka fita. Falalu babban yaronsa da yake yi masa hidima a dakinsa ya shigo da sauri kai tsaye sama ya wuce ruwan wanka zai had'a masa. Sau daya na dube shi na fahimci sauyawarsa domin ba haka ya fita ba. Cikin nazarin da nake na ji Yusi yana cewa." Baba hannunka da d'umi sosai fa ko baka da lafiya ne?"
Na dubi yaron sai naga hannuwansu a sarke a wuri d'aya. Yayin da shi kuma yake bud'e idonsa a hankali ya dube shi yana cewa." Lafiya lau na fita da yamma nan na ji alamun zazzabi amma yanzu nan zan kira wayar likitana in sha Allahu."
Cike da kulawa ya ce." Allah Ya baka lafiya baba." Ya amsa yana ko'karin tashi. Na yi kokarin cewa." Sannu Allah Ya sawwa'ke." Ba tare da ya dube ni ba ya amsa ya kama hanyar samansa. Yusi ya tashi ya bi bayansa da wayoyinsa da jakarsa. Tausayinsa ne na ji ya dan tsarga mini a lokacin lallai bashi da lafiya ko ga yanayin tafiyarsa.
Ban yi yun'kurin bin bayansu ba tunda bai ta'ba gayyatata ba, na tashi a sanyaye na nufi d'akina domin yin shirin kwanciya, amma kuma motsi kad'an sai gabana ya fad'i haka kawai ciwon nasa ya tsaya mini a rai ban san menene dalili ba. Ina bandaki ina wanka Yusi ya shigo yana kwala mini kira. Gabana ya yanke ya fad'i sai na kasa daurewa har na fito na amsa da ce wa ." Menene wanka nake yi." Muryarsa na rawa yake cewa." Baba ne yanke jiki ya fadi yanzu nan bayan ya fito daga wanka gashi can ya kasa tashi ya ce jiri ne yake dibarsa. Cikin tsananin tashin hankali na ajiye soson hannuna na watsa ruwa a jikina na dauro towel na fito ban ga Yusi a d'akin ba. Ban tsaya sanya kaya ba na d'auki hijabi na zura a ki'dime na fita.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k vip akan telegram Normal What'sapp group kuma #700hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*11*
Kofar d'akin a bud'e take na shiga sai na ganshi magashiyan a cinyar Falalu shine wanda yake hidima dashi ta fanni abinci da kula masa da dakinsa. Yusi kuma yana tsugune a saitin kansa ya rike hannunsa. Kafin na krasa na dinga nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.
Na tsinci kaina da kiransa da "Baba" Kamar yadda Yusi ke kiransa. Idonsa a rufe. Na dubi Falalu tare da cewa." Ka kira likitansa mana." Ya ce." Na kira shi yana kan hanya in sha Allah."
Gabana na fad'uwa na dan tsuguna kusa dashi na kama hannunsa na ri'ke sai na ji yana ta karkarwar jiki.
Hawaye suka zubo mini lallai d'an Adam ba a bakin komai yake ba. Na dinga sanya gefan hijabina ina goge hawaye haka kawai tausayinsa nake ji har cikin zuciyata. Likitansa na zuwa shida Falalu suka cicibe shi suka dora a gado. Sai bayan ya gama duba shi ya sanya masa ruwa ya dube ni a tsanake yana tambayata mussababi. Na ce lafiya lau ya fita kawai ya dawo da zafin jiki sai kuma aka zo aka ce mini jiri ya mamaye shi."
Ya ce." Tension ne kawai da kai kawo da lissafi da kuma rashin samun ishashhen bacci da hutu. Dama wasu masu kudin suna fuskantar irin wannan matsalolin ga lafiyarsu. Kwanakin nan sai tunaninsa ya tsananta shine dalilin da ya sanya jinininsa ya haura in banda haka Yallabai yakan jima bai yi ciwo ba. Idan ya tashi sai a dinga kula sosai. Zama dai mu yi waya da safe in sha Allah, Ubangiji Allah Ya bashi lafiya."
Gabad'aya muka amsa da amin. Ya harhada kayansa ya fita. Falalu ma ya kama hanyar fita yana cewa." Hajiya idan da buk'atar wani abu sai a kira ni."
Ban iya ce masa komai ba saboda tunanin da ya yi mini yawa
Ido na zuba masa ya na kwance sambal a gado bacci yake yi numfashinsa na fita a hankali a hankali lokaci guda kwarmin idonsa ya rufta. Ya ba ni tausayi sosai dalilin da ya sanya ma kenan na kasa matsawa nan da can. Ina zaune a gefensa tunani ya yi mini yawa. Wato mu a wautarmu idan Ubangiji Ya baka kudi baka da wata matsalar rayuwa bayan kuma ba haka abin yake ba an ce ma wasu masu kudin koyaushe cikin fargaba suke ga tarin makiya da mahassada bayan lissafi na rayuwa da yadda za a juya dukiyar ta kara bunkusa. Shi wannan mutumin kaf d'insa abin a tausaya masa ne, a yanzu da nake gefansa a zaune nake yin nazari a kan rayuwarsa. Gashi nan sai kudi da kadarori sanayya da d'aukaka shahara a duniya duk Allah ya yi masa. Amma bashi da magaji ma'ana yaran da ko bayan ya rasu zasu gaje shi. A k'alla yanzu shekarunsa sun haura arba'in da biyar wanda a iya sanina idan talaka ne a matakin shekarunsa muddin ya yi auran wuri ya aurar da 'ya mace idan da ita ya fara. yanzu ne na gane dalilin da ya sanya ya d'auki son duniya ya dora akan Yusi ko bai fad'a ba akwai wani ciwo da yake d'ankare a zuciyarsa. Gani dai kusan wata uku a gidansa zazzabi kwana daya ban ta'ba yi ba sai ma kibar da nake shigarwa wannan kadai ya isa ya tabbatarwa da jama'a cewa babu mahalu'kin da yake mutuwa sai kwanansa ya kare. Ni kaina da farko na tsorata amma yadda iyaye da 'yan uwa suke kara mini kwarin guiwa akan tawakkali da yarda da kaddara shine dalilin da ya sanya na barwa Allah ikonsa tunda ko na zauna da Alhaji Tajo ko ban zauna dashi ba idan kwanana ya kare dole na mutu. Hakika ya bani tausayi sosai ta wannan gefen domin haihuwa rahama ce kuma baiwa ce, kowane dan Adan zai so ya bar magaji bayan babu shi a duniya

Na daga kaina can na hangi Yusi kan sofa ya bingire bacci yake yi sosai. Ni kam gabad'aya idona ya soye nazari da lissafin rayuwa ya dabaibaye ni.
Gefen asuba bacci ya shammace ni, na bingire a gefansa ba tare da na san haka ba. Sai ji na yi Yana dan ta'ba hannuna da kiran sunana.
A firgice na tashi zaune da sauri shi ma ya tashi yana ri'ke ni." Menene salati ake yi idan an tashi daga bacci." yafad'a cikin taushin murya.
Na sauke ajiyar zuciya ina dubansa a hankali na ce." Ya jikin naka?"
"Alhamdulillahi Ya furta cikin nutsuwa.
Na ce." Allah Ya kara afuwa.

Ya dubi gefan da Yusi yake kwance yana cewa." Anan kuka kwana ke da Yusuf?"
Sunkuyar da kaina na yi a nutse na ce." E, jiyan ne jikin naka ya rikice sosai baka ma san wanda yake kanka ba."

Ya furta." Shine ki ka ji tausayi na ki ka kwana kusa da ni?"
Shiru na yi ban iya bashi amsa ba. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Na gode my wife Allah Ya yi mini albarka." Daga hakan sai ya sauka daga gadon ya nufi bandaki. Na janye idona daga hanyar da ya bi, jikina duk a salube na tashi Yusi domin ya yi shirin massalaci. Ya ce zai je tare da Baba. Ban matsa masa ba, na kyale shi a d'akin ni na kama hanya na fita da tunaninka masu yawa a tare da ni.

Ni a jikina nake jin canzawar yanayi game da mutumin nan. Wani yanayi ne wanda na kasa tantance shin tausayinsa nake yi ko kuma sonsa nake yi ni dai ban sani ba amma ina jinsa a raina, ina kuma jin mugun tausayinsa yadda yake mu'amulantata cikin sau'kin kai hakan yana k'ara karya lago na. Uwa uba k'aunar yarona da yake yi tamkar shine ya haife shi.
Ko yanzu da nake wanka Allah-Allah nake na gama na shirya na koma d'akina domin sanin halin da yake ciki, ni kaina mamakin lamarin nake tsakanin jiya da yau mutumin ya tsaya mini a zuciya.

Cikin doguwar riga mai adon duwatsu na shirya a jikina hankalina na sake komawa d'akin nasa. Sai na tarar dashi a zaune har ya yi wanka yana cikin kananun kaya singiliti da boxar wasu wuraran na jikinsa duk a bayyane. Falalu yana fifita masa shayi shi kuma hankalinsa na kan wayarsa shigowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya. Ni Kam jikina ya yi sanyi ganinsa a haka, sai na dinga jin nauyin had'a Ido dashi, duk da ba yanzu na saba ganin namiji da irin shigar jikinsa ba, amma dai shi din kwarjini yake yi mini.
Na ji shi yana cewa da Falalun ya je kawai tunda na shigo. Ya zo ya gifta ni yana gaishe ni na amsa cikin nutsuwa. Ya bude d'akin ya fice, cikin sanyin jiki na krasa kusa dashi na dan zauna kan kujerar dake fuskantarsa ina gaishe shi da tambayar jikinsa, ya amsa hankalinsa gabad'aya a kaina. Kallona yake yi sosai wanda ya sanya jikina kara mutuwa. Saukar numfashinsa na ji a hankali ya furta." Yusuf ya tafi makaranta ko?"
Na dube shi ni ma cikin kulawa na ce." Ai kai zan tambaya Yallabai." Sai ya yi murmushi yana cewa." Ai sai da na rarrashe shi tukkun ya tafi ya shirya wai saboda Baba bashi da lafiya ba zai je ba zai zauna ya kula da ni."
Murmushi na yi tare da cewa." Yusi kenan, na jima ban ga mutumin da ya saki jiki dashi kamarka ba."
Murmushi ya yi bai ce komai ba, tsayin minti goma d'akin ya yi shiru sai saukar numfashinmu a hankali na ji maganarsa yana cewa." Ina son Yusuf sosai Ina ji kamar ni na haife shi, Amina ni ma za ki yi mini alfarmar haihuwa ko?"

Yadda ya yi maganar kowaye kai dole ya baka tausayi. Na ce." Ai Allah ne yake bayarwa ranka ya dad'e, kuma indai muna tare Yusuf naka ne, ai ban isa na raba wannan k'aunar ba."

"Na aminta da hakan my wife ni yaushe za ki ba ni nawa?" Ya furta cikin kyakykyawan lafazi. shiru na yi ban iya bashi amsa ba.
Ya nisa kafin ya sake cewa." Kin san ciwon nan nawa har da fargabar yadda zan tunkareki da buk'atata domin na lura da gaske bakya 'kaunata. To kin ga wannan lamarin yana buk'atar soyayya. Da gaske haihuwa nake so wallahi."
A hankali na dube shi tare da cewa." Ka daina cewa ba na k'aunarka don Allah."
Ya ce." To, na daina cewa, amma idan da gaske kina kaunata ki watsar da makamanki kamar yadda na watsar da nawa makaman mu yi rayuwar aure domin zama cikakkun ma'aurata. Sannan ki taso ki zo nan kusa da ni."
Cikin 'yar shagwaba wadda ma ban san ina yi ba na ce.'' Ba ka ce sai an auna ni ba, ni ba zan iya kusantar inda kake ba yanzu saboda kada na shafa maka ciwo."

Ya yi mini wani irin kllo wanda na kasa gane na menene cikin taushin harshe ya furta. Ni da kike cewa mai kanjamau fa! Ni fa babu wata mace dana sani Amina. Amma kefa maza biyu ni ne ai abin tausayi, kuma dole na ji wa kaina haushi.
Ban iya ce masa komai ba. Ya ce." To, tunda kin ki zuwa ni bari na zo." Ya ajiye wayar hannunsa ya nufo wurin da nake zaune.
Hannun kujarar ya zauna. K'amshin turaransa ya buge ni. Ni dai Ina masifar son kamshinsa ba tun yau ba. A rikice ya riko kafadata yana ko'karin rungume ni ya ce." Ina son wannan 'kamshin na jikinki Amina. Za ki mallaka mini kanki ko?"
A tsorace nake don ban yi tsammanin cewa daga ya zo zai rungume ni ba, bayan haka ma sai hari yake kaiwa k'irjina wanda na fahimci tunda na zauna a d'akin hankalinsa yana kai. Na cire hannunsa da yake ta mammatsa mini jiki a sarke na furta." Baka da lafiya fa Baba sannan ga tea dinka can zai yi sanyi."
Idonsa a lumshe ya kwanto gabad'aya a jikina ya sakar mini nauyinsa yana nishi wanda ya yi masifar daga mini hankali lokaci guda na ji yanayina ya fara canzawa. Wani masifaffan shau'ki na shiga wanda tunda uwata ta haifo ni ban ta'ba jin irin yanayin ba. Ban san yadda aka yi ba kawai na tsinci kaina da tallafar kansa na matse tsam! a kirjina. Yayin da yake yin nishin ni ma shi din nake yi. Lamarin da

Please Login or Register in order to submit comment