Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai ko'karin ganin ta samar mini da nutsuwa cikin kowane yanayi na gode sosai Allah Ya yi miki albarka."
A tak'aice na amsa da amin ina ta kallonsa ganin ya wartsake idan ma da ciwon kan to a kashi dari hamsin ya sauka sai abinda ba za a rasa ba.
A haka likitansa ya zo ya dudduba shi yana fad'in jininsa ya hau kad'an shine kuma ya haddasa masa tsananin ciwon kai da jirin da yake ji ya zama dole ya daina tsanantawa kansa damuwa.
Ya tashi ya fita minti talatin a tsakani ya dawo da magungua a leda ya yi bayanin yadda ya kamata a ce an yi amfani da su daga yanzu. Ban sauka ba sai da na tabbatar da cewar ya ci abinci sosai sannan ya sha maganin a gabana tukkuna na yi masa sallama na sauka gwiwata kamar an rad'e da gora saboda mugun sanyin da jikina ya yi jin wannan batu......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*143*
Ni jin wannan batu gabad'aya ya kassara mini dukkanin karsashin jikina. Na yi shiru zuciyata na harbawa tare da tariyo maganganunsa akan auran da yake yi wa lak'abi dana cushe. Ba ni fargabar ya yi aure a gidan nan saboda na riga na san matsayina a zuciyarsa idan ma yana amfani da kalaman yaudare wajen nuna mini soyayya tabbas to akwaita a zuciyarsa ko da kuwa da akwai matsugunin wata. Matsalar dai anan 'kankanuwar yarinyar da zai auro ya kawota cikinmu shine tashin hankali tun lokacin da yake gaya mini zuciyata take hasaso mini Hajara ce domin kaf yaran da suke gidan Malam D'aha itace a samansu ba su kaita girma ba ita zamu kira da budurwa amma a rashinta domin yadda take a tsamure a tsuke sai uban tsayi bana tsammanin ta fara jinin al'ada.
Lallai wannan babban lamari ne da ya tunkaro mu gabad'aya domin idan har Allah Ya kaddara auran nan to sai da ya rainin yarinyar nan duk da matarsa ce ba zan yarda ya haye musu kan d'iya ta had'u da lalaruba. Malamai suna ta wa'azi kan cewa iyaye su daina irin wannan auran na cutarwa to da haka za mu kira shi ma a wannan zamanin domin dai muddin a fake da cewa sunnar manzon rahama ce yin haka to akan jefe yara cikin halin damuwa a gaba. Dalili zamanin Annabi Muhammadu S.a.w daban yake da wanda muke ciki a yanzu idan an fake da cewa za a yi koyi da shi akan abinda ya wanzar lokacin zamaninsa ana samun matsala dalili shi daban yake cikin duk wata hallita. Kai tsaye a yanzu ba zan zargi Malam D'aha da cewa shima kwad'ayin dukiya ne ya sanya shi daukar yarsa 'karama irin wannan ya bawa tsoho wanda idan da ya yi aure da wuri babu shakka ya kusa jika da ita domin dai Hajara ta wuce a ce 'yarsa idan auransa na fari ya d'ore duk da lokacin ma sai da ya zama tuzuru ya yi ya kuma fara da mace to ba ba shakka Hajara sai dai ta zo a jikanyarsa ta farko. Fisabillahi Malam D'aha bai dubawa yarinyar nan ba kuma ya tauye mata rayuwa ko da Alhaji Sulaiman ya yi aure eh tabbas budurwa ce amma wadda ta jima bata auru ba domin na ga calendar su shi da ita ta girmi Hajara sosai a k'alla ita za ta yi irin ashirin da biyar zuwa da bakwai. To idan ya zame masa dole auran budurwar sai ya nemi mai k'wari ba irin Hajara ba wadda yanzu ne take tasowa ba tasan ma menene auran ba. Na yi zaman sati daya a gidan na kuma fahimci cewa gidan na da tarbiya masu wadatar zucci da malunta ina ganin saboda kwad'ayin dukiya ba zai d'auki yarsa ya bayar ba sai don wani dalili nasa ko hango nagarta da tabbacin za a ri'ke masa 'yarsa a kula da ita. Wannan shine abinda na fi gazgatawa daga gare shi ba wai ya bashi ita ba ne domin ganin yana da kudi da rufin asiri.
Kwanan tunani da zullumi na yi kan wannan lamari gabad'aya kaina ya d'aure na rasa yadda zan yi na auna mas'alar a sikeli domin hango cancanta da dacewa.
Ina fitowa daga wanka kira ya shigo wayata dake aj 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~iye a gefan gado na krasa da sauri na d'auka. Baban Saude ne gabana ya yanke ya fadi domin ban kawo komai ba sai mutuwa. Shikkenan Dada ta rasu ban je na dubata ba Allah ya raba ganawarmu.
Hannuna na rawa na sanya wayar a kunnena cikin mutuwar jiki da saranda na yi sallama. Ya amsa da dakakkiyar muryarsa wadda hakan bai zame mini abin mamaki ba tunda sanin da na yi masa mutum ne tsayayye ba komai ne yake gigitashi ba ko da kuwa mutuwar ce.
Murya na rawa na gaishe shi ya amsa a dakile kafin ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita. Na yi kasa'ke da waya a kunnena ina sauraransa domin dai abinda ya tsana kenan yana magana a katse shi shiyasa na bari sai da ya tsahirta tukkuna gabana na dokawa na furta." Baban Saude Hauwa sharri ta yi mini wallahi tallahi ina ko'karin ganin na kiyaye shiga hakkinta wallahi Allah d'aya kenan ban san abinda yake tsakaninta da mijinta ba. Bana ta'ba yarda ranar girkinta na 'kebe dashi na tsayin lokaci ko jiya ma ita ta gaya mini bashi da lafiya na hau domin duba shi kuma babu abinda ta same mu muna yi a zaune kawai ta same mu."
Ya furta." Na dai gaya miki ki kula idan har don kina ganin kin fi ta fada a wajensa kuke had'e mata kai har ku dinga shiga hakkinta ki daina domin ba ni so a ce ranar lahira kun tsaya a gaban Ubangiji ana yi muku hisabi yadda ta kira ni tana kuka haikan shine abinda ya daga mini hankali Amina kada ki zalinci duk matan da zai kawo gidanki, ki yi iyakacin bakin kokarinki wajen ganin kin fita hakkin kowa ki kuma nuna masa kuskuran abinda yake aikatawa. Kada don kin samu dama a wajensa ki cutar da wata mu maza ba mu da tabbas watarana zai iya juyowa kan ki hakkin wad'anda ki ka zalinta ya fara bibiyarki. Ko kin ta'ba jin an ce gaskiyar mutum ta k'are. Idan kina da gaskiya da gudun hakkin wani sai ki ga kin zauna lafiya a duniya domin Allah ba ya shiri da mai zalinci.''
Ya kai k'arshen maganar da tausawa.
Na ce." In sha Allahu Baban Saude zan kula na gode sosai Allah Ya kara girma."
Ya amsa da "Amin Ya Allah."
Muka yi sallama. Na ajiye wayar ina dubawa. Lallai Hauwa bata da mutunci yau kuma abinda ta shiryo mini kenan.
Kayana kawai na zura zuciyata na tsalle na fita falon shiru ina d'an jiyo maganganun yara a d'akinsu suna shirin makaranta.
Na buga kofar dakinta da d'an karfi na ji tana fadin." Wanene?" Kai tsaye na ce." Ni ce"
Ta d'auki murya bata sake magana ba jim kad'an ta bude tana sanye da kayan bacci cotton riga da wando da hula.
Muka had'a ido ganin yadda fuskata take a murtuke ya sanya itama ta daidaita yanayinta. Na ce." Daga yau sai yau kada jahilar k'wakwalwarki ta yi miki tunanin kiran wayar wani daga cikin alhalina ki kai masa 'karata Hauwa wai shin me na yi miki ne? Ni ce matsalarki ko mijinki Hauwa? me yasa ki ka sanyo ni a gaba ki ke haka kan ki sukuni a kaina me na tsare miki na fad'a da babban sautin da kowa zai ji na ce.'' Yau sai kin gaya mini abinda na yi miki a gidan nan Hauwa ashe rashin mutuncin na ki har ya kai ki kira Baban Saude ki juya masa magana a kaina ni na yi mini ko mijinki da za ki nemi ki hada ni da iyayena."

Kada ki karanta wannan littafin ba tare da kin biya ba na kudi ne

Babu damuwa a tare da ita ta furta." Abinda ki ka yi mini a bayyane yake Amina tunda kin buk'aci ki sani ai zan gaya miki ko kin zata tsoronki nake ji ne? "
Ta fito falon sosai ta tsaya daf da ni ta cigaba da cewa." Na gaji da wannan kisan mummuk'en da ki ke yi mini a gidan nan, na gaji shiyasa na sanar da Baban Saude tunda na lura shi kad'ai ne yanzu zai gaya miki ki ji kuma ba mazalinci ba ne, kin had'a kai da miji kun ware ni kuna nuna mini cewa ni ba matar gida ba ce. Kin kanainaye shi da kissa kin hana shi yin mu'amula da ni, me yasa zan yi shiru a kan ki Amina ai ba ki isa ba wallahi dole ne na gayawa magabatanki."
Na ce." Banza shashasha sakarai kawai to kin fad'a kin ji dad'i duk yadda ki ke ganin Baban Saude ya ba ki goyon baya ba zai ta'ba ajiye ni ya d'auke ki ba, gaud'iya kawai wadda ba ta da lissafi."
Ba ta tsammaci wad'annan maganganun daga wajena ba ta tunzura ainun ta fara auno mini zagi manya-manya tana kusanto ni kamar yadda dai ta dinga yi wa Hajiya Maryam. Masu aiki kaf dinsu da yaran suka fito suka tsaya muryarta ce kawai take tashi.
'Yar iska kawai ni za ki kira jahila wanda asali da nasabata ta fi taki. Matsiyaciya na fa san tarihin rayuwar da ki ka gudanar a baya kafin ki yi tsalle ki shigo gidan nan ta karfi da ya ji kin dabaibaye mini miji ta ko'ina. Amina ba tsoronki nake ji ba fa ki ka kara zagin.......Ba ta kai ga krasa maganar ba ya d'auke fuskarta da wani lafiyayyan mari. Da yake ita kadai ce ba ta ga sakkowarsa tunda ta juya baya tana kallona tare da nuna ni da yatsa shiyasa ba ta ankara ba amma ni da masu aiki da yaran duka mun ga lokacin da ya sauko a ki'dime domin duk zurfin samansa sai da ya ji shouting dinta.
Ta dafe kuncinta a gigice tana nishi ta juya suka dubi juna ita da shi yanayin fuskarsa ya canza ainun da mugun takaici da b'akinciki.
Ya furta." Kin gani ko? Hauwa idan na ce miki kece matsalar gidan nan ki ji haushi yanzu tsakani da Allah menene haka wace irin sakarai ce ke mara hankali da wayo tsokane mata ido za ki yi ne ko kuwa dukanta za ki yi ba ki duba abinda take d'auke da shi a cikinta a gaban yara kina ta zaginta me ki ke so ki nuna musu?"
Hawaye suka dinga karakaina a kumatunta tana fad'in." Ita ba ka ji zagin da take yi mini ba yanzu ban girmi Amina ba idan lissafi shekaru za a yi me ya sanya don ta zo a Uwargida nake mutuntata daidai gwargwado ita sheda ce har dakinta nake bin ta na gaisheta me yasa za ta kira ni da sakarai shashasha. Kuma na zauna ina kallonta da kai da ita abinda kuke yi mini Ubangiji Allah yi muku fin sa."
Ya furta." Gaisuwar banza da wofi daga yau ki daina gaisheta tunda ba don Allah ki ke yi ba. Duk abinda kuke yi ina hankalce kuma nasan halin kowacce daga cikinku rashin mutunci za ki yi mini a gida abinda nake ji yana faruwa a waje shine ki ke ko'karin wanzar mini da shi a gaban yarana. Dame ki ke so su tashi ko su tasirantu, ke ba za a taba zaman lafiya dake ba ballantana na sanya a raina cewa ko bayan raina za ku had'e mini kan yarana su gaza banbance uwar da ta haife su. Wata matsalar ki ke so ki samar mini da ita a gida ta zage-zage Allah Ya jikan Maryam duka tarbiyar da ta yi musu tare da goyon bayan wad'annan bayin Allan mai inganci ce tunda nake da yaran nan ban ta'ba jin wani ya yi mini zagi a gida ba saboda baki da mutunci ki tsaya gaban uwarsu kina zaginta akan wane dalili?"
Ta yi shiru tana kuka mai tsuma zuciya domin dai zahiri marin nan da ya taska mata a kumatu ya dakushe duk wani karsashi da 'kumajinta.
Ya dube ni rai a b'ace yana fad'in." Wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe Amina ba zan d'auki wannan shashacin ba. Kada ku kuskura makamacin abinda ya sake faruwa da wannan safiya ya kara kasancewa. Duk abinda ya shiga tsakaninku a same ni a gaya mini na yi hukunci amma ban yarda da irin wannan rashin mutuncin ba a gidana a kuma gaban yara."
Na daure sosai zuciya na 'yar hantsile na ce." In sha Allahu."
Ya juya ya dubi yaran suna sanye da uniform sun yi tsuru-tsuru Khalil na ra'be a gefe yana kuka sauran kuma idonsu ya gwale kamar su rushe da kukan suma. Ya yi wani irin tsaki mai tsayi abinda ba da'biarsa ba ya ce da Mairo su koma ciki da yaran.
Ganin ya bar wajen ya sanya ni ma da gaggawa na shige d'akina na zaune gefen gado kawai sai hawaye suka kwaranyo mini Hauwa ta zame mini annoba. Wai dama haka ake kishi shiyasa ashe ake kashe-kashen juna. Ita Hajiya Maryam na ta kishin na sabauta rayuwa ne a yi mutuwar kasko ban mora ba ke ma ba za ki mora ba. kishin ramuwar gayya da kwantar da mutun har zuwa kushewa.
Lallai ne Hauwa duk ranar da ta samu dama a kaina za ta iya yi mini illah dalili na ji tsoro k'warai da gaske ganin yadda take tsalle da han'koro a kaina kamar za ta kawo mini naushi a hanci a son ranta ma kawai mu gwada 'yar kwanji tunda ta mayar da ni jaka mara lissafi da tsinkaye irinta. Har duniya ta nad'e ba na tsammanin zan yarda na had'a kwanjina dana kishiya.
To wai shin me ta sani a kaina ne da take ta nanata cewa ta san irin rayuwar da na yi a baya? Me na yi mai muni wanda zai janyo mini zind'e da gori a rayuwata.
Na sake goge hawayen da yake sauka a dakalin fuskata. Hauwa ba ta sona yau na sake gazgatawa asalin kishi mai muni take yi a kaina. Kuma ba kowane ya kara rura wutar tsanata a zuciyarta face shi da yake nuna mata 'kiyayya tare da kiran sunana a matsayin matar da ya ratayawa fulawar soyayya a kanta ita da take ganin ta taka tudu biyu matsayin matarsa kuma jininsa.........
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700....VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*144*
Ya shigo dakin yana tambayata mai ya had'a mu kai tsaye na ce." Ka je ka tambayata me ta sani a akaina kafin ka shigo ka tuhume ni. Yau ina so a yi ta 'kare a gidan nan lallai ya zama dole Hauwa ta sanar da ni da kai abinda ta ce ta sani a kaina domin yadda ta fad'i hakan to dole ne akwai abinda ta sani din a kaina wanda ta ji a duniya ko kuma a lokacin da kake neman auranta ta gaya mata wani abu kafin ka aure ni. Na ji da kunnena kana gaya mata mace mai irin jikina bata burgeka wa'ala a lokacin giyar soyayya ta sanya ka gaya sanar mata cewa Amina fasika."
Subahanallahi! Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ya dinga nanata wad'annan kalmomin kafin ya zauna a kusa da ni da wani irin sanyin jiki ya riko hannuna na cire ina dubansa idona tsaye na ce." Ba zan saurareka ba a yau har sai Hauwa ta gaya maka abinda ta sani a kaina kafin 'kaddara s
aure ta ratsa tsakaninmu magana ce mai harshen damo ta furta."
Ya yi shiru kansa a kasa tsayin wani lokaci ya dago yana dubana lokacin zuciyata ta gama bushewa 'karyar neman fitina Hauwa take yi yanzu ne asalin rigima ta da ita zai fara.
Ya furta." Ki saurare ni Amina ba ni son damuwa da tashin hankali idan kin duba halin da nake ciki na rashin wadatacciyar lafiya kada zantukan Hauwa su yi tasiri ku daga mini hankali."
Na ce." Kowa cikin lalura yake ni ba ka ganin abinda ka 'kunsa mini ne, ina so ko ba na so na ha'kura ina ta ibada dashi a tare da ni. Na fi ka jinjiki a wannan ga'bar mu cire maganar ciwo ta gaskiya za mu yi wallahil-azimin idan har yau Hauwa ba ta gaya mini abinda ta sani a kaina ba sai ka sake ni."
Ya zura mini idonsa ransa a b'ace ya ce." Me ya kawo maganar saki a cikin maganar da muke yi ke ba ki da hankali Amina?"
"Ba mu da hankali har kai gabad'aya taron mahaukata ne a gidan.
Ya furta." Zagi na za ki yi?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Ni ka zage ni."
Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya ce." Ba ki ga hukuncin da na yi mata ba kenan a kan ki ai na ji abinda take fad'a.
Na ce." Wannan damuwarka ce kai da ita ni ina gaya maka cewa ka tashi ka je ka tambayeta abinda ta sani a kaina na abin kunya."
Ya ce." Ba zan tashi ba tunda abinda na yi mata a kan ki bai yi miki ba ki d'auki matakin da ki ke ganin za ki d'auka ba fa tsoronki nake ji ba Amina."
Na ce." Ina ruwana da abinda da ka yi mata ai ka saba zalintarta. Yau ka fara?"
Shiru ya yi bai dube ni ba tashin hankali ya gama bayyana a tare da shi.
Ya tashi ya fita bai sake cewa komai ba. Ban yi a kasa a gwiwa na bi shi saman sai na same shi kwance ya hard'e hannunsa a k'irji abin duniya ya ishe shi
Na zauna gefansa ya kalleni na kalle shi na ce" Ka tashi mu yi magana don wallahil-azimin yau sai Hauwa ta gaya mini abinda ta sani a kaina."
Bai tashi ba illa iyaka ido da ya zuba mini yana kallona.
Jim kad'an ya tashi zaune idonsa har yanzu a kaina ya furta." Ni dai ban san komai a kan ki ba face alheri Amina kuma babu wani dalili da zai sanya na zauna ina 'bata ki a gaban Hauwa to na ce me kan ki wannan ba d'abia ta ba ce."
Na ce." Ba zan yarda ba a wannan ga'bar domin da kunnena na ji a shekarun baya kana gaya mata kalmar kaskanci a kaina ba ka son mace mai irin suffata.
Ya furta." Eh da farko ra'ayina kenan amma yanzu na canza ina so dalilin da ya sanya ma kenan ba ni yin wani doki da marmarin wannan yarinyar da aka ba ni bunkure."
Na ce." Da farko kuma ka ce kaima ba kasan yarinyar ba. Anan ma ka sake tabbatar mini da cewa baka jin kunyar 'karya
Ya furta." Kin d'auke ni munafiki kenan?"
Na gyad'a kaina ina kallonsa ido cikin Ido.
Ya ce." Na ji tashi ki je kada ranki ya 'baci.''
Na ce." A shirye nake ai ko kana tsammanin akwai wani b'acin ran da zai dame ni wanda ya danganceka."
Ya yi shiru tare da komawa ya kwanta.
Na cigaba da sakin maganganu masu zafi har sai da ya fusata ya sake tashi zaune jikinsa na kyarma ya nuna mini hanyar fita.
Na ce." Ba zan fita ba wallahi sai ka kira Hauwa yanzu ta fad'i abinda ta sani a kaina na sharri."
Ya ki'dime sosai yana d'an tari ya ce." Bala'in ki ya kashe ni Amina ko kuma kawai ki sanya fillo ki 'karasa ni ki huta wace irin masifa ce wannan."
Na ce." Ba zan kashe ka ba amma ba zan yi shiru ina kallo ana yi mini abinda bai dace ba.
Ya ja tsaki ya sake komawa ya kwanta na janyo kafarsa daya ya tashi zaune da azama yana kallona da mamaki abinda na yi fuskarsa gabad'aya ta canza da tsoro da fargaba dalili bai hangi nutsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni ba."
Ya tashi ya kama hanyar fita babu kuzari.
Mintina biyar suka shigo dakin tare da ita. Har yanzu a hargitse take idonta ya yi luhu-luhu saboda tsabar kuka.
Ya dube ni kafin ya ce." Gata an ki tambayeta amma ni ki daina tuhumatta akan abinda ki ke zargi."
Na dube ta sosai ina fad'in." Kin ce kin san komai a kaina har irin rayuwar dana gudanar kafin na auri d'an uwanki to ina so ki gaya mini mai ki ka sani a kaina mai muni ki gaya mini kuma ki ba ni sheda da hujja a sannan ne zan saurara miki don na rantse da buwayar Ubangiji wannan lafazin naki ka iya kai mu ga hukuma domin dai ba zan yarda ki yi mini sharri ba."
Ta fara kame-kame murya a dashe take cewa." Ai tsayawa yi miki bayani bata lokaci ne Amina kowa ya san abinda ki ka yi kina budurwa da kuma rayuwar zawarcin da ki ka yi a baya abinda duniya ma ta sani me yasa kike neman sheda da hujja a kaina ."
Wanzar na tashi daga inda nake na nufe ta jikina har kyarma yake yi ta d'an tsorata domin ko ga yanayin yadda ta mayar mini da martani a tsorace take kuma tashin da na yi da azama na nufe ta ya bata tsoro dalili d'azu ta sha mari a kaina ta zage ni yanzu kuma ba ta san abinda zai faru ba.


Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Yana zaune yana kallonmu bai ce mana komai ba.
Na ce." Ai dole sai kin gaya mini da wane namiji a kama ni a hotel ko kuma lokacin da nake sharafina a social media update dina ya fito wannan hujjar ita kadai nake so na ji daga gare ki"
Ta d'an ja baya tana ta'be bakinta ta furta." Ba ta mini lokaci ki ke yi a banza ke ce ba ki sani ba amma har yanzu akwai sauran hotonanki a wayoyin wasu mazan...... Ba ta krasa na fitar da hannu na tsinka mata wani mari wanda ban san ma na iya shi ba.
Ya taso da sauri ganin ta 'baci a lokacin da take han'koran rama marin da na yi mata ya shiga tsakiyarmu yana fadin." Me yasa za ki mare ta Amina zan 'bata miki rai fa."
Ya rike ni da kyau na fizge na bi ta gefensa na janyo rigar jikinta botiran suka zube. Ta yi saurin dafe kirjinta. Ya juya da sauri ya tura ni na zauna d'abas a saman gado zuciyata na harbawa. Ban yi tsammanin zan iya yin cacar baki da kishiya ba sai gashi yau tsananin bacin rai da takaici na nema ya sanya ni na hada jikina da Hauwa da zumar kokawa so nake yi kawai na dake ta sosai mu fitar da raini tunda na gama gane irin sharrin da take so ta la'kaba mini.
Ya rike ta da kyau ya hana ta zuwa wajen da nake zagi kuwa sai auno mini shi take tana fad'in sai ta rama marin da na yi mata wallahi."
Ya furta." Yana da kyau ni ma naga hujjar nan Hauwa sai na gazgata maganarki kada ki ga na goyi da bayanta ki sanar da ni abinda ki ka sani a kanta.
Ta yi shiru tana huci! wannan karon hawaye bai fita ba.
Ya riko hannunta suka zauna gefan gado yana tsakiyarmu yana fad'in." Ba ki fa da gaskiya Hajiya akan wannan maganar ni ma ba zan iya barinki ba domin kina ko'karin mini 'bata mini sunan matata, lallai ya zama dole na ga sheda Amina ta ga sheda ko kuma ki bata ha'kuri a ciki biyu za ki yi daya. Idan na ga shedar abinda ki ka fada a kanta ni ma za gazgata muddin kuwa ki ka gagara kawo sheda dole ki bata ha'kuri ki kuma nemi afuwarta amma ki sani ba zan iya hana ta ta bibiyi hakkinta ba."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ya ce." Ya kuke so a yi muku yanzu na kwanta na fad'i na mutu shine burinku ashe da raina zan ga wannan masifar."
Ta ce." Abinda ya fi haka ma za ka ga ni wallahi mutukar ba ka d'auki mataki akan dukan fuskata da ta yi

Please Login or Register in order to submit comment