Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba yadda abubuwa suke ta faruwa da rayuwarka shine abinda ya fi daga mini hankali."
Ya yi murmushi yana cewa." Kin fadi hakane kawai Amina ko da wannan to ba shine musabbabin sanya ki kuka tuk'uru ba. Idan ba kya samun gamsuwa da ni ai akwai cutarwa ko?"
Yafad'a cikin rauni wanda ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Hawaye ya sake ciko mini ido na ce." A a fa na gaya maka ba haka ba ne."
Shiru kawai ya yi bai ce komai ba yana dai ta murza hannuna da ya rike.
Na dago na dube shi a tsanake ina fad'in." Wannan matar ba sonka take yi ba idan har haka aka so to Allah ya wadaransa ba zan yafe mata ba."
Ya ce." Idan ta karya karsashina na d'a miji za mu tsaya a gaban Allah da ita Amina wallahi tallahi ba zan yafe mata ba ni ma."
Ya fad'a da masifar damuwa. Cikin wannan yanayin kira ya shigo wayarsa ya cika ni ya tashi.
Ni ma na d'auki rigata na sanya na nufi toilet na ji yana fad'in.'' E, gobe nake so na tafi Abuja a alhamdulillahi fa jiki da sauki wallahi, amma tunda ka ce za ka zo za mu jira ka in sha Allahu."
Na shige na je na tsarkake kaina ina fitowa yake gaya mini da Baban Saude suka gama waya yana tafe.
Na ce." Ka gaya masa baka da lafiya ne?"
Ya ce." Ya kira wayoyina lokacin da nake kwance a bunkure Bai same ni ba sai shekaran jiya ya sake kira yake gaya mini yana ta neman wayata bata shiga har taki ma ya kira bata tafiya a lokacin na ce masa na kwanta jinyya ne wallahi, ya yi fad'a sosai wai da mutuwa na yi ashe sai dai ya ji labari ba za a gaya masa ba.''
Na ce." Gidan malamin fa akwai matsalar network sosai ni kaina sai na yi da gaske wataran nake samun damar kiran waya amma idan ya zo sai a ba shi ha'kuri ko?"
Ya ce." Haka za a yi domin wannan Baban namu rigimamme ne, koda yake ai ya fara tsufa ba za a rasa shi da rikici ba."
'Dan hararsa na yi na ce." Zan kuwa gaya masa idan ya zo to dame kwado ya fi gaya kaima ai ka fara tsufan Baba."
Yana dariya ya ce." Ke ma haka malama kin tsufa kawai gaya miki ne da ban yi ba."
Ta'be bakina na yi ina cewa." To menene a ciki tsufa dole ne fa kowa ya tsufa kuma darasi ne."
Ya gyad'a kansa tare da janyo hannuna na zauna a gefensa ya ce." Ina kallon ki a matsayin matata har a cikin aljanna. Abokiyata makusanciyata da babu wani shamaki a tsakaninmu Amina me ki ke ganin ya cancanta da Malam 'Daha umara dai na bashi shi da Rabi'u in sha Allahu da azimin nan da za mu shiga amma bayan wannan ina so na yi masa alheri wanda zai nuna masa cewar na yi alfahari da taimakon da ya yi mini a ganina kudi sun yi kad'an wajan biyansa wannan hidimar."
Shiru na yi Ina nazari lallai Malam D'aha ya cancanta da ayi masa komai dalilin namijin ko'karin da ya yi har yanzu ma yana kan yi. Na ce." Ka sanya a rushe gidansa tsaf tunda na ga na kasa ne ginin da a zamanantar dashi a gyara masa tsangarsa sannan ka samawa wasu daga cikin yaransa maza aikin yi ko da a karkashinka ne duk da zaman da muka yi a gidan na fahimci ba su da yunwa dalili duka yaransu suna fita gona amma yana da kyau a ce sun fito cikin gari sun waye sun dan yi karatun zamani da hurd'a da jama'a da kasuwanci."
Ya dinga gyada kansa yana saurarena har na gama maganata ya ce." Haka za a yi my love shawarar nan taki ta yi mini sosai za a yi duk yadda ki ka ce in sha.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


Masu buk'atar a tallata musu hajarsu kofa a bud'e take za a yi akan farashi mai sau'ki in sha Allahu rabbi


*Gudun aure paid book ne 2k complete on Telegram normal What'sapp group kuma 1k ko AREWAPEN via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*132*
Baban Saude dai lokacin da ya ji abinda matar da yake yabawa ko'kari da bajintarta ta fannin kula da miji har ma yana bada misali da ita tare da jaddada goyon bayansa akan abinda a gaya masa a kanta sai da ya ki'dime sosai. Mutum ne shi jarumi jajurtacce wanda ko rasuwa aka yi bata gigita shi ainun domin ko lokacin da Mamanmu ta rasu ya nuna jarumta da dakiya a cikin 'yan uwanta ko yanzu a ka tashi zancenta yana tsawatarwa da masu yi mata kuka cewa ba daidai ba ne sai ga shi jin irin mugayen ayyukan da maccen da yake misali da ita tare da ko'karin tabbatar mata da aljanna ta aikata ya yi shiru yana zare ido har abin ya so ya ba ni dariya na danne ban yi ba. Da farkon da abokin nasa ya fara bashi labarin ya dinga dakatar da shi yana nuna babu yadda za a yi ta aikata haka tunda shi kansa ya sheda soyayyar da take masa a ganinsa babu dalilin da zai sanya so ya sanya ka nakasta wanda kake so. Ganin yadda yake rantse masa da girman Allah da buwayarsa ya sanya jikinsa saduda ya yi tsuru kawai yana sauraran bayanin da yake yi masa da yadda ya ci tsananin wahala kafin ya samu kansa a yanzu da yake zaune suna magana.
Ya jima yana girgiza kai da tu'ajibi da mamaki kafin ya bud'e bakinsa yana fad'in an yi shed'aniya amma mai suffar munafukai tana sunkuyar da kai kamar mutuniyar arziki ashe macijiya ce mai mugun dafi Allah Ubangiji ya saka muku da mu kanmu da ta jefe cikin zullumi da tashin hankali da damuwa.
Da k'yar da jibin goshi ya yarda ya kwana a gidan Hajja a cewarsa zai je ya kama hotel idan ya duba Baba Sule a asibiti sai ya d'auki hanya da sassafe tunda jibi zai komai bakin sana'arsa.
Da 'kyar ya lalla'be shi ya amince.
Da daddare gabad'aya har da ni muka je asibitin domin duba jikin Baban Sule kamar dai yadda ya fad'a.
Alhamdulillahi jikinsa da sauki wai ashe basir ne yake damunsa irin mai daure cikin nan. Ya yi tsiro kuma yana fitar da jini sai da aka yi aiki duk ya rame kuwa ya zabge kamar ba Baba Sule ba Sunusi babban d'an sa shine yake jinyarsa.
Na tausaya masa sosai kuma ban san haka ciwo ya ci karfinsa ba duk da ba ni cikin hayyacina amma ina da hakki a sanar mini domin na bada taimakona asibitin gwamnati ne amma dole ai za a sayi magani shi kuma bashi da k'arfi asalin ubangidansa Alhaji Muntari ne kuma ya rasu don ma yaransa maza sun tashi sune suke ta dawainiya da shi da taimakon Babanmu tunda alhamdulillahi yanzu shine yake da rufin asirin da ba su dashi tun farkon samun d'aukakata dana bude masa shagon huluna yake cigaba da gudanar da kasuwancinsa.
Bacci yake yi har muka gama zamanmu a d'akin da yake bai farka ba da za mu tafi Baban Saude ya bawa Sunisu dubu goma ya ce a sayi magani shi kuma Yallabai din ya ce zuwa gobe zai ga sa'ko.
Jin haka ya sanya ni kar'bar lambar wayar Sunusin da ta asusun ajiyarsa nasan lallai tunda ya fadi haka zai buk'aci da na bashi details din da zai saka kudin.
Duk da dare ne ashe da yawa wasu sun ankara da shigowarsa asibitin muna fitowa kuwa jama'a suka rufe shi ni da Baban Saude muka ja gefe muna kallon ikon Allah uwar zuma kenan ki tashi a biki idan har za ka bayar to babu shakka za ka ga tarin masoya da yawa.
Sukairaju da yake bayansa ganin abin ya yi yawa ya sanya ya fara ko'karin korar mutane muka nufi mota suka biyo mu har da mata masu zaman jinyya.
Mota muka shiga gabad'aya har da shi ya bude ma'ajiyar kudinsa ya fito da kudi da d'an yawa ya mik'awa Sukairaju wani dattijo ya bawa daga ciki ya ce su kasftaa.
Ya zo ya shiga motar da saurin gaske domin ganin jama'a na sake k'aruwa a wajan.
Baban Saude tun a mota yake tsokanarsa wai zai yi kyau da siyasa ya nemi kujera gwaman Kano.
Ya dinga dariya yana fad'in abinda bai taba sha'awa ba kenan siyasa ya yarda dai ya yi gwagwarmayar ta neman kudi a ko'ina ya tara ta hanyar halak amma mafiakasari 'yan siyasar nan da suka ci suka tada kai suna bushasha da dukiyar jama'a suna mutuwa da nauyin al'umma a kan su.
B'angaran ba'ki na cikin gidan Hajja ya sanya Sukairaju ya gyarawa Baban Saude ya kwana anan da sassafe kuwa ya kira shi a waya yana fad'in shifa ya shirya.
Ba shiri muka fito harabar gidan ni da shi sai a lokacin ma muka gaisa aka yi aka yi dashi ya jira aka kawo masa abin kari ya ce a a. Sai da ya yi masa dubara kan cewa yana da kyau ya yi wa Hajja sallama kafin ya tafi sannan ya yarda muka shiga ciki a tare anan Hajja ta sanya aka kawo masa abinci funkaso da miya da kuma kayan shayi ya sha ruwan shayin babu madara sannan na zuba masa funkason manya guda biyar zan zuba miya ya ce na cire biyu na bar masa uku ya isa.
Na yi yadda ya ce din ya sake sosai da Hajja ana hira da shi har aka ta shi labarin abinda ya faru ya kara jadadda mata mamakin da ya yi da aka ce masa Hajiya Maryam mashirika ce duk nagartar da ta nuna masa a farkon ganinta da shi bai taba tsammanin haka daga gare ta ba.
To bayan tafiyar Baban Saude da kad'an ni ina tare da su Hajja a falo muna hira har da ita inna Uwanin shi kuma ya bi bayan Baban Saude amma bai dawo ba.


Littafin kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Na ji maganar Hajja cikin nutsuwa tana kiran sunana.
Na amsa tare da mayar da hankalina gare ta ta ce. "Amina."
Na ce." Naam Hajja."
Ta ce." Hauwa ta koma dakinta tun Tajo yana bunkure a kwance."
Na d'an saki fuskata ban nuna mata cewa na sani ba na ce." Ma sha Allah Hajja ai haka ya fi Allah ya kiyaye gaba."
Ta amsa da Amin Ya Allah. Ta cigaba da cewa ita da mahaifiyarta suka buk'aci hakan ga ta a zaune hakane Uwani?"
Ta amsa "Hakane Hajja."
Sa ta cigaba da cewa." Hauwa a cewarta tana jin kunyarku ke da Tajo bisa abinda ta yi na rashin kyautawa a baya ta yi nadama ta kuma gane ba daidai ba ne. Ta ji labarin ibtila'in da ya samu mijinku shine ta ce tunda ke kina tare dashi kina jinyarsa ita sai ta koma ta kula da yaran. Jin hakan ya sanya na bada goyon baya domin yaran za su samu kulawa sosai kuma za su ji dad'i akan ace suna tare da masu aiki."
Falon ya yi shiru ina sauraran ta cigaba da magana domin nasan ba ta gama ba. Can kasan zuciyata kuma ina mamakin ta hanyar da suka b'ullo wato dama mafaka suke so su samu tunda ta fara gane kuranta tana bibiyarsa yana shareta da ya kwanta ciwo kuma ta tabbatar ina tare da shi ta san yara sun dawo hannuna sai ta lallaba ta koma ta fake da cewa za ta kula da yara da haka suka tsara Hajja har ta amince take kuma ganin sun kyauta sun yi tunani mai kyau.
Babu wata sha'kuwa tsakanin Hauwa da yara har na cikinta domin ba da ita suka rayu ba abinda yake tsakaninsu tsawa ce da hantara wataran har da duka. Khalil dai yana shan rank'washi ko ta kwashe fuskarsa da mari na gani kusan sau biyu. To balle Minal ma da bata son zuwa wajenta. A ganina babu wata mafificiyar kulawar da za su samu a wajenta baya ga ta Mairo da Taburni tunda da su suka saba kuma duk wata nau'in kulawa suna samu a tare da su.
Ta cigaba da cewa." A wani zuwa da Tajo ya yi nan farkon rikicinsu ya ce mini ya mayar da ita kusan wata hud'u kenan har yanzu tana a matsayin matarsa a yadda na sani dai ban san kuma shi abinda yake zuciyarsa ba sai ya shigo sai na tambaye shi."
Ta Nisa kafin ta cigaba da cewa." Shekaran jiya mun jima da ita a waya sosai na ja mata kunne kada na ji kada na gani ba ni son wata matsala ta sake faruwa idan ta shure maganata zan cire hannuna a kanta kuma zan bawa Tajo za'bi zama da ita ko rabuwa."
Inna Uwani ta yi k'asa da kanta cikin damuwa Amma ba tofa ba.
Na ce." In sha Allahu ma babu abinda zai sake faruwa Hajja, ni da ma tsakanina da Hauwa ai girmamawa ce wallahi kuma na ji dadin wannan sulhu wanda da tun farko ta yi aiki da shawarata hakan ba za ta faru ba, ina yi musu fatan alheri."
Ta ce." Ba wai ina goyon bayan Tajo ba Uwani ki zauna ki yi nazari da tsinkaye anan Hauwa ta yi daidai na yi shiru ne kawai ba wai don abin bai yi mini ciwo ba. Ban isa na bata umarni ta bi ba na sha gaya masu daga ita har abokiyar zamanta a duk lokacin da suka samu sa'bani da magidansu su sanar da ni, amma saboda ta raina kowa ta haihu da d'anyen jego ta tafi ke kuma ki ka bata wajan kwana har kina aiko mini da sa'ko iyayen Hauwa sun ce a ba su takarda domin su ga sheda."
Inna Uwani tasa kuka tana fad'in." Hajja ni kaina Hauwa taurin kanta ya ishe ni wallahi nasan bata kyauta ba kuma b'acin rai ne ya sanya na fadi haka abinda ya kara dagula mini lissafi yadda ta ce mini yana dukanta kuma ya mayar da ita koma baya a gidansa har hakkinta na aure baya bata shine hankalina ya tashi."
Hajja ta harareta tana fad'in." Baya bata hakkinta na aure a ina ta samu wannan cikin da ta haife wad'ancan yaran biyu Khalil da Minal a ina ta same su?"
Inna Uwani ta yi shiru tana jan hanci tare da goge ragowar hawayen idonta.
Ta gyad'a kanta tana fad'in. "Ai ban 'ki komawar ba domin ban san abinda Allah ya lullube ba, shiyasa tun da farkon faruwar lamarin na tura shi can bauchin domin a samu sasanci ba ni da niyyar raba uwa da yaranta tunda ni ma babu wanda ya yi mini haka. Nasan soyayyar da take tsakanin iyaye da yaransu me yasa na yi masa fad'a sosai a lokacin da ya kwashe musu yara ya kaiwa Hajiya Maryam. Ba daidai ba ne amma dole a wannan ga'bar mu yi masa uzuri tunda ba a hayyacinsa yake ba har yaran gabad'aya nasan yanzu ko giyar wake ya sha ba zai k'ara yarda ya d'auki d'ansa da'ya ya kai wani wajen ba sai dai idan ya zama dole."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Hakane wannan hakane."
Ta ce." Ki ja mata kunne kwarai idan za ta ji tunda ta fi karfin ki ba tun yau ba na fahimci haka wannan ya zama na farko ya zama na k'arshe ta zauna ta kula da yaranta."
Ta ce." Ai tun a gida na yi mata fad'a sosai Hajja ai abinda ya fi alheri shine ta koma cikin yaranta domin duk wanda zai rike maka yara ba kamar uwa ba."
Hajja ba ta ce mata komai ba ta juyo gare ni tana fad'in." Ya gaya mini cewa gobe za ku tafi hakan ya yi ba zan dakatar da shi ba domin nasan yana da hurd'odi da yawa. Ki yi hakuri ki 'kara akan wanda ki ke yi Amina ni dai babu abinda zan yi domin na saka miki alherin da ki ka yi mini sai da na ce Allah Ya yi miki albarka ya albarkaci zuri'arki ya sa su zama abin koyi da kwatance a duniya."
Na ce." Wannan addu'ar ita kad'ai ta isa Hajja ai ban yi domin a gode mini ba ni ma kaina na yi wa kuma in sha Allahu ni dai daga bangarena zan yi iyakacin bakin kokarina wurin ganin mun samu zaman lafiya da juna."
Ta saki fuskarta sosai tana fad'in." Na gode sosai Amina Allah Ya yi miki albarka na gode."

To a daran ranar ta kira shi ya je ya same ta nasan dai ba zai wuce maganar da za ta yi masa ba kenan. Ko da ya dawo ya same ni tare da Yusi muna bankawana ban ga wani can ji a fuskarsa ba ya zauna cikinmu ana hirar da shi har yana tsokanar Yusi ya zama saurayi ko yana da budurwa ne shima. Abinda ya assasawa yaron tashi ya fita kenan yana sinne kai shi kuma sai dariya yake masa yana fad'in." Ta'b wa ya ga su wa'e da suruka humm tsufa ya zo garinsu wata mata."
Na gane da ni yake na share shi ban tanka masa ba ya cigaba da cewa ni kuwa kin ga ko yanzu zan iya auran budurwa ba ni da matsala.
Ban kula shi ba na tashi na shige band'aki ina murmushi wani sa'in idan yana barkwacin har mamaki yake ba ni.
A wannan daran kafin mu kwanta ya kar'bi details din Sunusi dubu dari da hamsin ya sanya masa ni kuma na sa hamsin a kai ya zama dubu dari biyu ta What'sapp na yi masa magana na ce ya duba sako an tura masa.
Ya kuwa kira ni a waya ya yi ta godiya kamar zai ari baki.
To duk yadda na kai ga nok'ewa a wannan daran kasawa na yi domin ha'din kai na bashi zuciyata na dokawa muka jima cikin wassanin soyayya ya yi kokari kwarai ta wannan hanyar ya samar mini da nutsuwa kafin ya nemi hanyar biyan tashi buk'atar cikin k'ankanin lokaci yana farawa ya kammala. Akwai sha'awar sosai da mazantakar amma karfin da za a jima ana yi ne babu wannan kuwa babbar matsala ce.
Da sassafe muka d'auki hanyar abuja bayan duka mun yi sallama da wad'anda suka dace....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: *GUDUN AURE PAID BOOK 2K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K KO KU GARZAYA AREWA PEN.*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*133*
Yadda yaran suka dinga tsalle da murnar ganin Babansu haka ni ma suka yi mini kamar dama can akwai tsananin sabo a tsakanina da su. Minal dama can 'yar gidana ce kai tsaye wajena ta taho da dan gudunta tana tsalle da dariya na kuwa sunkuya na sunkuceta duk nauyinta ni ma ina dariyar murnar ganinsu tsaf cikin annashuwa. twins kuwa dama wajan Babansu suka nufa ya rirri'ke hannayensu shima fuskarsa kamar gonar addu'a Allah ne kad'an yasan yadda yake ji a cikin ransa ganin ya dawo cikin ktoshin lafiya domin cigaba da rayuwa da su. uwa uba kuma samun iyayen rainon da suke tsananin kula da su tamkar suna rayuwa da iya 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~yensu. Yarinyar ta dabaibayeni sosai ta sa'kalo wuyana da hannayenta tana ta dariya duk acikin farincikin ganin mun dawo. Ina nishi sosai gajiyar tafiya da yanayin jikina ga kuma nauyinta na fara ko'karin sauketa k'asa ina kallonsu Mairo da suke tsaye suna ta driya na ce." Minal ta kara girma da nauyi a 'yan kwanakin nan Mairo me kike bata?''
Cike da kulawa ta sinne kai ta furta. " Abici take ci ta k'oshi Hajiya bayan haka babu komai tunda ita dama can ba gwanar ciye ciye ba ce."
Shiru na yi ban ce komai ba na sauke yarinyar a k'asa tana riko gefan hijabina ina jin Mairo da Taburni suna yi masa sannu da zuwa. Baba Tabawa ta fito daga cikin fuskarta a washe take fad'in." Sannunku da zuwa Alhaji sannuku da dawowa."
Ya tsaya suka gaisa sosai kafin ya kama hanyar samansa yaran suka bi shi a baya Khalil da twins ita Minal tana tare da ni ta ri'ke mini hannu tamau.
Muna magana da Mairo Hauwa ta fito daga d'aki muka kalli juna babu yabo babu fallasa ta furta." Kun dawo kenan?"
A tak'aice na ce." E, mun same ku lafiya?'' Ta amsa da 'Kalau.' Ta nemi kujera ta zauna na d'an dubeta ta gefan ido ta k'ara ramewa abinka da mara jiki dama ai zaman gida sai dole ta so ta yi wa kanta ganganci. Ta yi kwalliya sosai wata'kila ta tar'bar angon nata ne naga har da lalle ja da ba'ki irin wanda yake so ya yi kyau sosai a farar fatar 'kafafu da hannayenta.
Na kama hanyar d'akina jikina a galabace Minal tana take mini bayana.
Ban yi wanka ba tukkuna sai da na yi sallar magriba na fito na sami yarinyar ta bingire a gado bacci ya d'auketa. Ba ta yi wani murnar ganin uban ba kamar sauran sau daya ta je wajensa ya d'an ri'ke ta kamar yadda ya yi wa sauran ta dawo wurina. Kamar yadda twins din suka yi mini.
Sai da na shirya tukkuna na tashe ta muka fita a tare babu kowa a falon. Kai tsaye d'akin ya yaran na nufa Mairo tana ta fama da su Khali na can gefe yana rubutu a littafi.
Ta burni kuma tana gyara musu wardrobe.
Na ce." Mairo a bawa Minal abinci." Da sauri ta ce." To ta janyo hannunta zuwa ciki. Usai ta biyo bayana muka zaune kujera a tare jim kad'an itama Hassanar ta fito na daga kai na dube su a nutse tare da fad'in." Kun yi sallah ko?"
Suka daga mini kai a tare na ce." Abici fa?''
Girgiza kansu suka yi. Na d'an 'bata fuska ina fad'in.'' Bebaye ne ku?''
Usai ta ce." Menene Bebaye Mama?"
Sai na fara gwada mata maganar kurame da hannuna da bakina." Aikuwa sai dariya gabad'ayansu suna kallon bakina yadda nake yi. Ni ma na kama dariyar ina fad'in." Bebaye ne masu magana da hannu da kuma gyada

Please Login or Register in order to submit comment