Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faWa ba, da zan yi tun tana da rai ko dan na faranta mata rai. Haushin kaina nake ji da ban bar komai ya wuce tun tana raye ba, da ace nayi abinda take so da zan ga fuskar ta da farin tunda abinda take buri kenan. Amma yanzu ko na yi bazan ga hakan akan fuskarta ba, meyasa ban bari ya wuce tun tana da rai ba?.

Nayla ta ce, "Ko yanzu zata yi farin ciki, kai baza ka gani ba amma na tabbatar zata yi. Yin abinda take so shine cikar aunar da ka ke yi mata, kuma zata tanadi kyakykyawan murmushin da zata yi maka a aljanna, kuna haWa ido zata yi murmushi kyakyawan haoranta su bayyana." A irjinta ya kifa kansa ya sauke ajiyar zuciya hawaye na zuba a idanunsa. Kansa take shafawa a hankali da ya cika da gashi ta ce, "Ka cigaba da zubar da hawaye a duk lokacin da suka zo, kar ka dakatar dasu, zubarsu shine zai sassauta maka nauyin da ka ke ji."

Bai ce komai ba yana kwance a jikinta itama bata ce komai ba. Ya mie zaune ya goge idonsa ya ce, "na rasa iyayena Jidda, amma ban san haka zafi da Wacin mutuwa yake ba sai yanzu. Ban san haka ake ji ba sai a wannan lokacin. Ni na san bazan sake yin farin ciki ba har abada, zan zauna zaman jiran lokacin mutuwa yazo, dan rayuwa babu Didi baza ta yi min daWi ba.

"Na rasa mahaifiyata nima YaMar, amma ban san Wacin mutuwa ba sai yanzu" ta faWa tana kallonsa. Ta ce,  ka daina cewa baza ka sake farin ciki ba, Allah ne yake bada farin ciki da akasinsa, rashin Didi bazai hana ka farin ciki ba, tunda ba itace take bayarwa ba Allah ne. FaWar wannan kalmar bai dace ba, in kana faWar hakan kamar baka karSi addara ba kenan. Allah ne ya halicci Didi ya baka aronta, yanzu kuma ta koma gare shi, daman tashi ce ba taka ba.

Ya girgiza kai yana suke numfashi ya ce, "Didi ta yi min komai a duniya, ta hana kanta ta bani, ta i ci ta bani, ta i sha ta bani, ta yi wahala dani, itace nemana har police station, itace kawai mai damuwa da na ci ko ban ci ba, ita kaWai ce mai shiga damuwa da damuwata, itace kaWai mai yin jinya da rashin lafiyata Jidda. Ta sadaukar da komai nata saboda da ni, kullum tunaninta wacce hanya zata bi dan ingnata min rayuwata, ko yaushe cikin tausayina take, bata so ta ga na yi fushi balle na kasance cikin Sacin raiii!. Ashe iyakacin rayuwar da Allah ya tanadar mata kenan, ashe raunin da take cewa tana so ta gansa a fuskata raunin mutuwarta ce, ashe lokacin da take magana akan barin komai ya wuce na ahlina mutuwar ta ce sila! Ya ja numfashi ya sauke ya ce,  Allah ka jian wannan baiwa ta ka, Allah ka karSi shahadarta, halin ta na gari ya bita."

"Amin ya hayyu ya qayyu" Nayla ta faWa a sanyaye.

Ya ce, "Jidda na yanke hukunci ba tare da izininki ba, na je wajan mijin Didi na roe sa ya bani rion Marmerh ya kuma bani. Ban nemi shawararki ba kafin na aikata, bana so Marmerh ta bar hannuna ne shiyasa. Allah yasa ban takura miki ba."

Nayla ta Wan yi murmushi ta ce, "Didi tawa ce fa YaMar, ko bana auren ka wallahil azim ni mai rie mata Marmerh ce, balle kuma jininta nake aure. KarSar Marmerh da ka yi shine daidai, tunda mahaifinta ya amince ina maraba da zuwan ta. Allah ya bani ikon kula da ita, Allah ya bani ikon yi mata tarbiyyar da Didi zata yi alfahari da ita a ranar lahira."

Ya aname hannunta yana girgiza kai tare da cize baki ya ce, "Amin Jidda, na gode, na gode Jidda. Na gode da soyayyar da kike yiwa Didi da zuciyarki da gangar jikinki, Allah ya saka miki da alkhairi."

Murmushi ta yi ta ce, "Amin ya rabbi. Ka daina gode min don Allah, Marmerh ata ce, Didi kuma Yayata ce. Ina aunar Didi har zuciyata, ina ganin girmanta, ina jinta kamar jinina. Bani da mai bani shawara sai ita, ko Sata min rai ka yi ita nake kira ina kuka na faWawa, ta bani hauri ta kuma bani shawarar yadda zan yi, bata taSa kallona a matsayin matar aninta ba, ko yaushe kallon anwarta take yi min. YaMar nayi babban rashi a rayuwata, ba kai kaWai ka rasa Didi ba har dani."

Ya yi murmushi ya ce,  daman ta ce min sai ta riga ni mutuwa, daman ta ce min tana so ta bar duniya kafin na rigata, saboda tana so ta barwa Marmerh ni a duniya. Huhhh..ashe haka Allah ya tsara, zata bar duniya ta bar Marmerh a hannuna.

Nayla ta bishi da kallon tausayi, gabaWaya ya canja mata kamar ba shi ba, yayi sanyi da rauni kamar an canja masa halayya, ko a kamanni ya canja gabaWaya. Sanyi da raunin da Didi take fatan gani a tare dashi sai da ta bar duniya ya bayyana.

Nayla ta ce, "Daman ba ta ce maka ka daina faWa akan cikin jikina ba, har ta ce maka ka yi addu'ar Allah ya ingnata cikin ba?. Har ta ce baka da tabbacin zai zauna ko?. Huhhh YaMar cikin fa ya zube, amma wallahi..." dakatar da ita ya yi ya ce, "Kar ki rantse, koda zubar dashi ki ka yi da kanki na yafe miki balle kema baki san ya fita ba. Tashin hankalin da kika shiga har cikin jikinki ya fita ya tabbatar min ba aramin matsayi Didi take dashi a wajanki ba."

Ta ce, "bayan kun fita daga Wakin asibiti ku ka bar mu ka san me ta ce?." Ya girgiza kai a sanyaye, ta ce, "Ta ce in na haifi mace a saka sunan Hajja, in namiji a saka sunan Abiy. Sai nayi dariya ban Wauka wasiyya take bar min ba" ta faWa murya na rawa sosai ta kuma cewa, "na ce mata in an biyu ne fa, ta ce in duka mata ne a saka sunana dana Hajja, in kuma ne maza ne a saka sunan Abiy da sunanka" ta faWa tana kallon idanunsa.

Nayla ta ce, "ina ta dariya a lokacin ban Wauka wasiyya ba ce, ta kalle ni ta ce kana sona sosai, nima na ce ai nima ina sonka. Ta yi dariya bayan ta yi salati ta kalle ni ta ce itama tana sonka ba ni kaWai ke sonka....." Nayla ta faWa tana kwantar da kanta a irjinsa tana kuka. Ido ya lumshe yana shafa bayanta. Nayla ta ce, "ashe ruwan da na bata ruwan arshe ne, ta ce min kamar bata sha komai ba ashe na arshe ta sha a duniya."

Bayan ta yake shafawa a hankali ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Mun yi babban rashi, Allah ya gafarta mata, Allah ya lulluSeta da rahamarsa. Tabbas Allah baya barin wani dan wani ya ji daWi, da ace hakan na furuwa da Allah ya bar min Didi a duniya ko dan maraicina. Duk da wahalar da ta sha dani sai Allah ya karSi rayuwarta ya bar ni a duniya, sai da ta zama silar shiryuwar halayema sannan ta tafi ta bar ni. ar halak kenan!.

Nayla ta amsa da amin, tana jingine a jikinsa har lokacin kafin ta Wago ta kalle shi ta ga ita yake kallo. Kallon afarsa da hannunsa ta yi, sai ta mie ta arasa wajan drawer ta Wauko nail cutter ta dawo ta zauna kusa dashi, gyara masa farce take yi tana yi tana hawaye. Sai da ta gama ta fita zuwa falo wajan Umma.P118

Ranar Omar da Marmerh ya kwana a kusa dashi, hannunsa yana jikin ta cikin kewar mahaifiyarta. aunar Marmerh yake ji fiye da komai a duniya, ji yake a baya ba sonta yake yi ba, sai yanzu yake yi mata asalin so.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin alhinin rashin Didi, Omar bai dawo daidai ba, yana oarin karSar addara ne amma wani lokacin yana gazawa. Haka zai zauna a Waki yayi kuka son ransa sannan ya daure ya cigaba da harkokinsa. Ya rame, ko baccin kirki baya samu balle abinci, kullum cikin tunani da kallon hoton Didi yake. Sai da aka sake yi masa hoton irjinsa saboda nauyin da yake yi masa aka sake bashi magani.

Kamar yadda burin Didi na arshe ya kasance Omar ya cika mata shi, gidan danginsu na uwa da uba babu inda bai je ba. Baba Adamu da Kawu Sulaiman godiya ya dinga yi musu akan gida da kayan Wakin bikin Didi. Farin ciki suka dinga yi ganin Omar a gidajensu kamar ba shi ba. Ya sake yana girmama kowa, babu Waurarriyar fuska balle tsawa ko masifa.

Tun daga lokacin ya zama Wan dangi, wannan ya kira shi wannan ya kira shi. Girmamasu yake yi kamar yadda Didi take yi, kuma ya basu matsayin iyayena zuciyarsa. an uwansa wanda basu san shi ba yanzu duk sun san shi, cousins maza da mata duk sun karSi number Omar ana gaisawa.

Omar ya zama mai sanyi, duk wannan hargagin nasa da faWa babu, magana ma sai ta zama dole yake yi balle har ka ga Sacin ransa. Kamar yadda Didi take yawan tambayar abinda zai saka shi yayi rauni amsar ta bata bayyana ba sai bayan babu ranta, ashe rashinta shine raunin Omar. Ko yaushe Marmerh tana kusa dashi, hatta bacci a kusa dashi take yi. Yadda yake nuna aunar Marmerh arara baya nunawa Musliha, baya iya Soye aunarta da kewar mahaifiyarta da yake ji a zuciyarsa.

Tsohon gidansu na kusa da gidan Hajja ya saka aka rushe gabaWaya, aka siyi gidajen da suke kusa da gidan aka tayar da ginin babbar islamiyya wacce za a dinga karatu da komai kyauta. angaren haa ruwa, siyan abubuwa da za a iya yiwa mamaci gata dasu Omar ya yiwa Didi babu adadi, fatansa Allah ya kai ladan kabarinta. Duk wannan hidimar kafin Didi tayi kwana arba'in ya yi su, har lokacin bai ji a ransa ya yi mata abinda zai wadaceta a kabarinta ba.

Ranar da ta kwana hamsin da biyu a kabari, suna zaune da Nayla da Marmerh da Musliha kamar ko yaushe. Omar ya yi shiru ya jingina da kujera yana kallon sa, Musliha tana kwance a irjinsa, Nayla tana zaune a gefensa ita da Marmerh da take ta game a waya. Nayla ta bishi da kallo, sai su kwashe awa Waya a haka indai ba ita tayi magana ba bazai ce komai ba, ya takure rayuwarsa sosai, ya koma zaman kaWaici ba ko yaushe yake yin magana ba. Gani yake kamar farin ciki da walwalarsa ta tafi, gani yake tunda ya rasa Didi murmushi ya are a rayuwarsa.

Kowa ya san shi aka yiwa mutuwa, duk wanda zai yi kewar Didi a bayansa yake, shiyasa ya koma kamar ruwa ko yaushe ciki bin asa yake yana kwanciya. Shiyasa dangi da an uwa suka dage da yi masa addu'a, dan lamarin nasa sai an haWa da roon Allah. A ranar ne ya sakko daga sama ya zauna a falo, amma kullum yana sama, saman ma a cikin Wakinsa.

A sanyaye ta ce, "YaMar." Ya sauke kai asa ya kalle ta bai amsa ba, ta langwaSar da kai ta ce, "tun Wazu nake magana baka ji." Ya gyara zaman Musliha a jikinsa ya kalle ta ya ce, "Ban ji ki ba."
"Ta ya zaka ji ni kana tunani?." Ya sauke numfashi bai ce komai ba. Nayla ta ce, "Ka cigaba da hauri, kar tunani ya jawo maka ciwo. Kaga likita ya ce dole ka cire damuwa, jininka yai dawowa normal, sannan ga ciwon kan da ka ke fama dashi. Nauyin da ka ke ji a irjinka shima ance damuwa ce, in baka yi oarin kawar da ita ba zata jawo ciwo babba" ta arasa faWa a sanyaye tana kallon sa.

Ya kalle ta suka haWa ido ya ce, "Kin taSa rasa wanda ki ke so Jidda?." Nayla ta kalli idanunsa ta ce, "Na rasa mahaifiyata, na rasa Didi." Yayi murmushi ya ce, "Mahaifiyarki daman baki rayu da ita ba, kai tsaye zan iya cewa baki santa ba. Baza ki Worar da zafin rashin wanda ka ke so a kanta ba. Duk da mahaifiya ce, ko baka tashi ka santa ba rashinta yana taSa zuciya. Nima ban san tawa mahaifiyar ba, amma ina jin zafin rashinta a kusa dani." Nayla ta bishi da kallo ganin yana Wan murmushi ya ce, "Na san kina son Didi, kina aunarta sosai, zaki ji zafi da ciwon rashinta a zuciyarki. Amma baza ki Worar da Wacin mutuwa akan Didi ba, zaki Worar da zafinta ne a lokacin da kika rasa makusantanki Ya faWa tana lumshe ido tare da jan numfashi, ya sauke numfashi ya buWe ido ya kalle ta ya ce, "zaki WanWana zafin rashin wanda ka ke auna ne in aka wayi gari na mutu na barki, daga lokacin zaki tabbatar da ba aramar juriyar rasa Didi nake yi ba. Juriyar da nayi baza ki iya irinta ba, ko rabin jurewar da nake yi baza ki iya ba Jidda!. Yanzu duk abinda zan faWa miki baza ki fahimta ba, kina kallona a matsayin wanda ya kasa karSar addara kawai, ba ke kaWai ba, kusan kowa a haka yake kallona. Na yi miki uzuri, baki san Wacin mutuwa ba!.

Nayla ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai, ta mayar da hawayen da suke oarin sakko mata, dan yanzu ya zama mai raguwar zuciya, ko ya tayi hawaye a gabansa sai ya tayata, baya iya rie kansa ko kaWan, indai ya tuna da Didi sai ya zubar da hawaye. Saboda haka ko da taji kukan rashin Didi bata yi a kusa dashi, zata ta tashi ta kulle kanta a banWaki tayi kuka ta wanke fuska ta fito. Yana buatar kulawa saboda har lokacin jininsa bai sauka yadda ake so ba, ga nauyin da irjinsa yake masa, ga ciwon kai da yake fama dashi kullum.

Sai da ta mayar da hawayen ta Wago ta ce, "Haka jarabawar Allah take, akwai zafi da ciwo da raWaWi. Sai dai mu yi fatan Allah ya bamu ikon cinye ta ba tare da kuskure ba." Ya lumshe ido ya ce, "Amin Jidda. Akwai ciwo, akwai raWaWi kam sosai. Shiyasa bana fatan ki riga ni barin duniya, in sha Allah ni zan tafi na bar ki." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba dan muryar ta tayi rauni sosai, ta ja numfashi ta jingina da kujera tana shafa kan Marmerh da take ta game cikin nishaWi.

Omar ya sake sauke numfashi ya kalle ta ya ce, "Jidda." Ta kalle shi ba tare da ta amsa ba ya ce, "na manta ban faWa miki ba, gobe zamu tafi umrah in sha Allah, zan je na yiwa iyayena da Didi addu'a." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Allah ya nuna mana goben lafiya."

"Amin ya rabbi. Kin san meye?." Ta girgiza kai alamun a'a, ya gyara zama ya ce, "tun Wazu nake so na faWa miki sai na manta. Na yi mafarki da Didi cikin kyakykyawan yanayi, tana faWa min duk addu'ar da nake mata tana zuwa inda take" ya faWa yana kallonta da murmushi.

Nayla ta ce, "ikon Allah, nima nayi mafarki da ita YaMar. Wai a mafarkin kana ta tafiya baka yi mata magana, sai take cemin kalle shi sai fushi yake yi akan yana gaishe ni bana amsawa, kuma fa Nayla ina amsawa ji ne baya yi, amma yanzu na faWa miki ki faWa masa ina amsawa. Bana haddace mafarki in nayi, kafin na tashi daga bacci na manta. Amma wannan har hango shi nake yi a idona."

Lokaci Waya fuskarsa ta washe zuwa annuri da farin ciki, ya gyara zama cikin farin ciin da ta jima bata gani a kan fuskarsa ba ta ce, "Da gaske?." Ta yi murmushi ganin shima murmushin yake yi ta ce, "Wallahi da gaske nake." Ya rio hannunta ta matso kusa dashi ya ce, "na jima ban ji labarin da ya yi min daWi kamar wannan ba, kin ga hakan yana nufin addu'ar da nake yi mata tana zuwa gareta ko?." Ta Waga kai alamun eh, ya yi mata pecking Winta a goshi ya ce, "Naji daWi sosai Jidda."

Murmushi ta yi yana kallon sa, ya ce, "Kin san ne nake kuWuri a raina?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Su Umma nake so na kai umrah, da Umma da Mama da Anty Aisha. Ya ki ka gani? A haWasu dasu Kawu?."

Nayla da murmushin jin daWi ta ce, "YaMar indai akwai dama a haWa dasu kawai, ladan da za a samu wanda zai je har kabarin iyayenmu da Didi." Ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah zan yi hakan. Har su Bashir nake so su je, da nayi niyar mu tafi da Bashir to in bana nan shine akan komai, ya fisu ilimi da wayewa, yana kuma saurin Waukar abu in aka koya masa shiyasa nake iya bar masa komai. In muka dawo sai yaje, in ya dawo sai biyun su je su ma. an amanata ne, tun muna marasa jin magana muke tare har yanzu."


Nayla da take ta murmushin jin daWi ganin ya kawar da damuwar kamar ba shi ba ta ce, "Allah ya cigaba da buWa maka a rayuwarka, baza ka taSa yin baya ba saboda kyautatawa na asan ka da ka ke yi. Rashin Didi ya saka ka manta komai da ya wuce, gashi kana udirin alkhairin da ladansa zai je har inda take ya same ta."

Murmushi ya sake yi yana rie da hannunta har lokacin. Ya ce, "Haka ne Jidda. Tabbas da ace Didi tana da rai da babu dalilin da zai saka na kalle su..." sai ya girgiza bai arasa maganar ba ya canja wata ya ce, "sai mijin Didi, ina so na shigo dashi cikin harkar kasuwancina, duk da yana aikinsa amma ina so na shigo dashi mu cigaba da yin komai tare, ya ki ka gani?." Nayla ta ce, "shawara ce mai kyau, amma ka tuntuSe shi ka ji." Ya girgiza kai alamun zai yi hakan.

Sallama aka yi tare da shigowa falon, suka amsa a tare suna kallon wacce ta shigo. Narma ce ita da Safna, sanye da hijjabi har asa. Ta tako cikin nutsuwa zuwa cikin falon suka zauna tana kallon su tana murmushi. Narma ta ce, "Ina yini." Nayla ta amsa da fara'a tana kallon ta. Narma ta kalli Omar da tunda ya amsa sallamar ya Wauke kai ta ce, "Ina yini Omar, ya aka ji da haurin Didi?."

Omar ya ce, "Alhamdu lillah."
"Allah ya gafarta mata, Allah yasa ta huta."
"Amin ya rabbi. Na gode" ya furta a sanyaye ba tare da ya kalle ta ba .

Narma ta ce, "Na so nazo tun lokacin, bana Nigeria kuma ba lafiya ce dani ba, sai da na samu saui sannan nazo." Jin yayi shiru bai bata amsa ba sai Nayla ta ce, "Babu komai, Allah ya ara miki lafiya, Mun gode da zuwan ki." Narma ta yi murmushi ta ce, "Amin, na gode. Didi Yaya ce a gare mu gabaWaya, ta yi min nasihar da ta shiga zuciyata lokaci guda, kuma nayi amfani da ita naga riba mai yawa a rayuwata. Allah ya haskaka kabarinta."

A tare suka amsa da amin kafin Nayla ta ce, "bara a kawo muku ruwa." Narma ta ce, "A'a mun gode, akan hanya muke zamu koma Abuja yanzu" ta faWa tana miewa tsaye. Ta kalli Omar da ba ita yake kallo ba ta ce, "za a yi aurena cikin kwanakin nan, muna son design na product Win ku zamu bayar as souvenirs." Omar ya girgiza kai ya kalle ta ya ce, "Allah ya kaimu, ya sanya alkhairi." Ta amsa da amin ta yi musu sallama suka tafi.

Narma tana fita Nayla tayi ajiyar zuciya mai tsaho, Omar ya kalle ta suka haWa ido sai ya Waga gira sama, murmushi ta yi dan ta lura a hankali ya fara dawowa Omar Winsa, addu'ar da ake yi akansa ta fara ratsa shi.

Shima murmushin ya yi bai ce komai ba, ya kalli Marmerh da take gefe kamar babu ita a falon tana game a wayarsa. Yayi murmushi yana kallon ta ya ce, "Marmerh kamar bata nan, tana ta game kamar babba." Nayla ta kalli Marmerh, ta kalle shi ta ce, "ba kai ka koya mata ba?." Ya kalli Musliha da take jikinsa a kwance ya ce, "ita kam Didina babu ruwanta, ta kwanta a jikin aninta Omar shine kawai abinda take so" ya faWa yana yi mata pecking Winta a goshinta.

Nayla tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ya dawo da kallonsa gareta ganin tayi wani iri kamar ba ita ba. Ya san tunda aka yi rasuwar nan ya canja mata, ya watsar da lamarinta, ba ko yaushe yake damuwa da lamarinta ba. Baya nuna mata soyayya da kulawar da take buata daga gare shi, bashi da lokacin komai sai na tunanin Yayarsa da zubar da hawayen rashinta. Ya san tana buatar lokacinsa sosai, ta yi hauri da juriyar halin da yake nuna mata, sanann ta taya shi jimamin rashin da ya yi, bata taSa nuna masa gazawa a kan hakan ba. Ya ji rauni da tausayinta ya mamaye masa zuciya, sai yayi nufin kawar mata da damuwa, cikin murya mai daWi ya ce, "yaushe za a yi Yayata anne ne Madam?."

Nayla ta Wan wara ido tana Wan murmushi ta ce, "nima ban sani ba." Ya shafa beard Winsa yana girgiza kai tare da murmushi. Rabon da wani abu ya shiga tsakaninsa da ita an kwana biyu sosai, dan tun kafin mutuwar Didi ma ya bata hutu saboda laulayin da take fama dashi, a haka mutuwa ta riskesu. Maganar wata biyu da wani abun ake yi, ya san tayi hauri dashi sosai, yana jinjina mata matua a kan hakan. Bata taSa nuna masa wani abun a kan hakan ba, duk da hainta ne, amma ganin baya cikin nutsuwarsa sai itama ta bashi lokaci dan ya nutsu. Wannan Wabi un nata yana ara mata matsayi da girma a idanunsa, yana ara aunarta da aunar son kasancewa da ita a ko yaushe. Ya Wan Wage gira sama ya ce, "zaki sani ne an mata." Nayla tayi aramar dariya dan ta ji daWi da ya dawo nutsuwarsa, ko babu komai zai karSi addara ya cigaba da rayuwarsa cikin walwala da jin daWi.KRB3P119

Da safe suka shiga Madina, basu fito sallah ba sai da suka yi la asar a hotel sannan suka fito masallaci. Nayla baby pusher ta shiga mai wajan yara biyu ta Wora yaranta Omar yana tura su gwanin burgewa. A Madina Hilton suka sauka, Waya daga cikin five star hotels na garin madina, suna fitowa daga hotel sai harabar masallaci. Tunda suka rabu a harabar masallaci ya shiga ciki wajan maza ta shiga wajan mata basu sake haWuwa ba har aka yi i sha. Marmerh da take da son game tunda ta haWata da waya shikenan aka zauna lafiya, Musliha kuma tana hannunta. Bayan an idar da sallar i sha bata koma ba sai da ta shiga rauda ta fito sannan suka wuce gida zuwa lokacin duk sun yi bacci.

Tana buWe room Win yana fitowa, ya bita da kallo ya ce,  ina ta jiranki tun Wazu, nayi kira ki WhatsApp call baki Wauka ba. Nayla ta ce,  ai ban siyi sim card ba, kuma babu wifi a masallaci shiyasa baka same ni ba, Am sorry. KarSar pusher Win ya yi ya arasa ciki ya kwantar dasu akan gado ya ce,  na bar ki da aiki kina ta wahala da yara biyu, shiyasa nake ta kira ki nazo na taimaka miki. Nayla ta Wan yi murmushi ta ce,  Ai da yake babu nisa, ba gajiya sosai. Na shiga rauda ne shiyasa.

Ya zuba mata ido ya ce, Baki gaji ba dai ko?. Ta kalle shi ta yi murmushi ta ce, 

Please Login or Register in order to submit comment