Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani saboda tijarar Omaar. Ya dinga faWa kenan yana cewa an faWa musu bashi da kuWin da zai yi min komai ne, kai lefe ma da nace an kai gidan kawu ya yi min shiru ne amma zai nuna min yaji haushi nan gaba."

Hajja tayi dariya ta ce, "Omar kenan, Omar mazan fama, Omar carbin ™wai, ya ci sunan nasa damisa kamar yadda ake faWa masa." Didi ta ce, "wallahi na rasa abinda zan yi, ga makullin ya aiko min dashi amma na masa faWawa Omar saboda sa™on Baba. Shiyasa nazo na same ki don Allah ki kira shi ki ce masa kece kika Wauki nauyin abinda Baba zai yi, yana ganin girmanki sosai, ke kaWai ce kaf duniya zan ce kin yi bazai musa ba, duk da zai yi magana amma ™arama ce shikenan ya wuce. In na ce Baba Adamu ne ranar sai kowa ji kan mu dashi."

Hajja ta ce, "shikenan kin kawo dabara. Ki bawa kawun na ki makullin ni ki turo min shi in anjima. Kar ki damu ai an wuce wannan matsalar." Didi tayi murmushi ta ce, "Na gode Hajja. Kin kasancewa uwa a gare ni kuma kakata, bani da mai share min hawaye a duniya sai ke Win kawai. Allah ya shirya miki zuri'arki gaba da baya." Hajja ta yi murmushi ta ce, "Amin. Aisha ai an zama Waya kar ki damu." Didi tana ta murmushi suka Wan cigaba da hira kafin ta tashi ta koma gida.

Washe gari da safe take sanar masa da Hajja na son ganinsa, ya Wan yi jimm yana kallon ta kafin ya ce, "lafiya take son ganina?." Didi ta ce, "Omar
ya za a yi na sani? Ta ce min kawai na ce kaje." Ya Wan Wauke ido daga kallon ta ya ce, "to in na fita yanzu zan shiga." Bata sake kula shi ba kar tayi magana ya gano sai tayi shiru ta cigaba da aikin ta.

Kamar yadda ya ce da ya fita kam gidan Hajjan ya shiga da sallama, mai aikin Hajja ta amsa ta ce ya shiga ciki Hajjan tana ciki. Hajja ita kaWai a zaune tana lazumi, ta amsa sallamar ya zauna sai ta ajjiye carbin suka gaisa ta ce, "Ummaru daman na ce kazo ne akan batun kayan Wakin Aisha na aure. Na karSi makullin gidan da Aisha zata zauna a hannunta, ni nake so nayi mata komai na Waki a matsayina na uwa a gare ku. Shiyasa na ce ta turo min kai na faWa maka da kaina kar ka ji hakan a bakin ta bai maka daWi ba."

"Ina kallon ku matsayin jikokina ne, Aisha ta Wauke ni kamar uwa tana faWa min duk damuwarta. Ana zaman mutunci da amana shiyasa zan sauke ha™™in da yake kaina matsayin uwa a gare ta. Ina fatan hakan bazai Sata maka rai ba." Shiru ya yi bai amsa ba Hajja ta ce, "Ummaru baka ce komai ba." Ya kalle ta ya ce, "babu abinda zan ce, tunda an yanke hukunci shikenan." Hajja tayi dariya kaWan ta ce, "an yanke kam, sanar da kai yanzu ma nayi ba neman shawara ba."

"Shikenan, an gode Allah ya saka da alkhari" ya furta a kasalance dan bai ji daWi ba. Hajja tana lura da yanayinsa tana girmama ™arfin hali irin na Omar, da gaskiyar Aisha da ta faWa masa asalin su waye suka yi da babu zaman lafiya.

Sallama ya yi mata ya fita ya koma wajan Didi ya shiga har cikin Wakinta ya samu tana mopping a lokacin. Kallon sama da ™asa ya yi ya ce, "Daman abinda aka tsara kenan shiyasa baki faWa min dalilin kiran ba?." Didi ta ce, "Shiyasa na ce ta faWa maka da kanta."
"Ai wallahi tunda naga kin kasa kallona kafin na fita na san akwai munafurcin da kika haWa, da farko nayi tunanin akan waWancan makiran ne ashe sabuwar gulma ki ka samo hanyar ™ullawa." Didi tana jinsa bata ce komai ba sai ma dariya da yake so ya bata.

Omar ya fusata ya ce, "Ni fa bana son shishshigi a cikin lamarin rayuwata, an ce mata bani da kuWi da zan iya yi miki ne da za a yi miki a waje?. Ba dangin iya babu na baba a ce itace tayi miki kayan Wakin auren ki haka daidai ne?. Salon nan gaba azo na yi min gori ace kayan Wakin Yayata ma ma™ota ne suka yi mata saboda na gaza?."

Didi ta kalle shi ta ce, "Omar kyautatawa ce fa ba wani abu ba." A fusace ya ce, "Allah ya tsinewa kyautatawar!." Didi ta yi shiru jin abinda ya ce. A kausashe ya ce, "in kyautatawar ce a yi ta wani Sangare mana lallai sai ta kayan Waki? Yanzu kaf unguwar nan sai a san itace tayi ko dan a faWa, ni kuma a cigaba da yi min kallon mara amfani tunda ni Allah ya Worawa yi miki ba wasu a waje ba."

Shiru tayi masa bata tanka ba kar ta tanka ta sake tsokano shi, ta san halin kayanta tsaf shiyasa take gujewa abinda zata sake tunzura shi. Shirun da tayi ma bai saka ya yi shiru ba ya ce, "wai komai na kayan Waki ita zata yi ko a matsayin ta na wa oho?. Nuna min ake yi ni bani da kuWin da zan yi kenan? ko ke kika ce mata bani da kuWin da zan yi miki ita tayi miki?."

Didi a sanyaye ta ce, "ni bamu yi haka da ita ba, abinda ta faWa maka shi ta faWa min." Omar ya yi ™aramin tsaki yana binta da harara ya ce, "To meyasa baki ce mata zan miki ba? Meyasa kika amince har ki ka ce ta faWa min da kanta?. Kenan kina tunanin bazan iya ba ko?." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Nidai ban ce ba."

"Mtsw! Na rantse da Allah ba dan Ina ganin girmanta baza'a karSi kayan nan ba, to babu yadda zan yi mata ne amma da sai ta bar kayanta ai ba ro™a muka yi ba." Shiru Didi ta sake yi masa ta cigaba da aikin ta bata ce komai ba ya sake yin tsaki ya ce, "Abin haushi." Ita dai bata ce masa komai ba tana mamaki hali irin na Omar a zuciyarta, tabbas da ace ya san Baba Adamu ne ya yi ba Hajja ba da sai an yi ya™in duniya na uku saboda bala'i da masifar da zai dinga zazzagawa kowa.

Juyawa ya yi ya fita ta bishi da kallo ta ce, "Na kuSuta. Alhaji Omar manya, Allah ya shirya ka ya taimake ka a rayuwarka" ta faWa tana cigaba da aikinta tana dariya da tunanin irin kalar tizajarar da zai yi mata in ya san asalin su waye zasu yi kayan Wakin.

Haka ya wuni rai a Sace, ko kula ta ma bai yi saboda baya son maganar, gani yake kamar an raina masa hankali ne da za a ce wata a waje ce zata yi kayan Wakin yayarsa ba shi ba. Ita kuma tana sane ta share shi, tana yin magana zai sake yin sama ™arshe ma ya ce zai je ya samu hajja ya ce gaskiya bai yarda ba shiyasa ta yi masa banza.

Washe gari ™arfe bawai na safe ta buga masa ™ofa, da yake bacci yake yi a lokacin sai ya taso yana cewa, "Didi kin san ™ofar a buWe take amma sai ki ta buga min ™ofa kin san na tsani a buga min ™ofa amma sai kin yi, lafiya?." Didi ta ce, "na san a buWe take ai, shigowa ne bazan yi ba. Ka tashi ka yi wanka ™arfe takwas zamu wuce." Ya kalle ta ya ce, "Zuwa Ina?." Harararsa ta yi ta ce, "ban sani ba, ka koma ka kwanta in ka manta" ta faWa tana wucewa ta ™yale shi. ˜aramin tsaki ya yi, dan kawai ya san mahimmacin alkhairi ne da bazai je ba wallahi.

Wanka ya yi ya shirya cikin ™ananun kaya a lokacin Didi ta fito daga falo shi kuma ya fito ta kalle shi ta ce, "Omar don girman Allah ka koma ka saka manyan kaya, ba dan ni ba, don Allah ka saka manyan kaya har hula ka saka." Bata barshi yayi magana ba ta dinga magiya dole ya koma tunda ba son magiya yake yi ba, ba jimawa ya dawo da shadda kalar blue mai haske har hula ya saka kamar yadda ta ce.

Murmushi tayi tana kallon sa ta ce, "Ko kai fa. Ka  ci abinci sai mu wuce." Shayi kawai ya sha aka kawowa Didi sa™on gurasar da ta bayar ayi, duk yana kallo ta juye a babban bokitin roba sabo dal da ta siya. Kallon sa ta yi ta ce, "ranka ya daWe in in ka gama sai mu tafi ko?."
"Ki jira na je na samo mai motar da zai kai mu ko?."

"Ai da driver Hajja zamu tafi." A kaikaice ya kalle ta ya ce, "Hajja dai?." Didi ta ce, "eh Omar, ita tace zata saka ya kaimu bazan ce mata a'a ba."
"Daman ai komai baza ki iya ce mata a'a ba tunda ga wacce ta haife ki, wallahi da na san haka ne bazan je ba."
"Shiyasa ban faWa maka ba, mu je" ta faWa tana fita ta bar shi kar tayi wani abun ya ce ya fasa.

Ransa a Sace ya fito zuwa ™ofar gidan ya kulle gidan ya tarar da driver Hajja ya fito da motar ga Salma a tsaye a jikin motar da alama tare zasu je. ˜aramin tsaki ya yi lokacin su Bashir suka zo wajan ya tsaya yana yi musu magana, Didi ta shiga motar shima bai jima ba ya ™araso ya shiga gaba su kuma daman baya suka shiga, motar ya yiwa key bayan sun gaisa da Omar da Didi suka Wauki hanyar Kaduna ransa duk a Sace.KRB2P0011
Arewabooks@nanahaleema11.

Sha Waya da mintina na safe suka shiga Kaduna, da yake gidan su Nayla ba ba™o bane a wajan driver Hajja ba Sata lokaci suka isa har ™kofar gidan ya tsaya yana danna horn. Didi kallon gidan ta ke yi tana girgiza kai, domin gidan yana da matu™ar girma da kyau. Duk da bashi da ™yale-™yale daga waje amma kana gani ka san gidan babban mutum ne ba gidan yaro matashi ba. Ko iya masu gadin da suke zaune a gate Win sun kai su biyar ko wanne da uniform kalar blue a jikinsa.

Ganin driver Hajja ya saka aka buWe musu gate na farko a nan suka ajjiye motar. Bayan ya faka Salma ta ce, "Mu je ciki" ta faWa tana fitowa tana Wan jijjiga hannunta dan ta gaji da zaman. Omar dai bai fito ba yana zaune Didi ta kalle shi ta ce, "ka fito mana." Ya kalle ta ya ce, "Sai na shiga gidan mutane babu izini? Ku je dai." Didi ta saki baki tana kallon sa ta ce, "ikon Allah! Sabon salo."

Salma tayi dariya ta ce, "Didi mu je zai shigo daga baya." Didi tabi bayan Salma suka sake shiga wani gate Win a nan wani mahaukacin parking space yake mai bala'in girma wanda aka tanadi rumfuna daga can gefe na ajjiye mota.

Didi kallon gidan take tana girmama girmansa da kuma ™arfin kirki irin na Nayla. Wanda ya fito daga wannan gida ba kowa ne zai yi mutunci har ya kalli na ™asa dashi ba. Ciki suke shiga Didi ta ga sai tafiya suke yi kafin a buWe wata babbar ™ofa su shiga sai gasu a wani babban falo mai bala'in kyau.

Babu kowa a falon sai mai aiki tana kunna turaren wuta Salma ta kalle ta ta ce, "Ina Mama da Nayla?." Ta ce, "Mama tana ciki, Nayla kuma tana sama bata sakko ba gabaWaya." Mama ce ta fito tana cewa, "waye yake nema na?." Ganin Salma sai tayi murmushi ta ce, "A'a Salma, ke ce tafe?." Salma tayi dariya ta ce, "Ni ce Mama." Zama suka yi har Didi suka gaisa da fara'a kamar ta san Didi kafin Salma ta ce, "Didi ce Mama, na san kina jin labarinta a bakin Nayla." Sai Mama ta sake yin dariya ta ce, "™warai kuwa in jin labarin Didi ma™ociyar Hajja ko?." Salma ta amsa ta ce, "itace. Ta zo wajan Abiy ne."

Mama ta ce, "ai kuwa yana falon sa kuma fita zai yi, maza jeki ki rakata dan na ji yana cewa cikin Zaria zai shiga, kuma ya kai yamma ko dare bai dawo ba." Salma ta mi™e tana cewa, "Nayla fa?." Mama ta ce, "tana sama yau ko sakkowa ma bata yi ba, bata jin daWi shiyasa ko aiki bata je ba. Jeki zan tasota sai tazo ta same ki." Tare suka fita da Didi da Salma. A harabar gidan wani Sangaren daban suka shiga, Salma ta buWe ™ofar da ta san nan ne falon Abiy na waje.

Ai kuwa yana zaune shi kaWai da alama ya gama cin abinci suka shiga falon da sallama, Jawad ne ya fito daga kitchen Win falon da ruwa a hannunsa ya ajjiyewa Abiy a gaban sa. Abiy ya amsa sallamar sai ya murmusa ya ce, "A'a Salma, ke ce tafe?." Salma ta ™arasa ta zauna a kan carpet ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta Hajja da Daddy ta ce duk suna lafiya lau. Da Didi suka gaisa lokaci Waya ya gane ta, Salma ta ce, "Abiy Didi ce." Abiy ya ce, "Aisha dai, Ai na gane ta." Didi tayi murmushi tana sunkuyar da kai.

Salma ta ce, "ta ce na rakota wajan ka shiyasa muka taho yau. Tare mu ke da Omar ™aninta ma yana waje a tsaye." Abiy ya ce, "yana waje a tsaye? Kun yi wannan doguwar tafiya a barshi a waje? Jawad jeka ku shigo tare." Jawad ya tashi ya fita ba jimawa suka dawo tare da Omar harda driver Hajja. Gaisawa suka yi da Drivern kafin ya tashi ya fita Omar ya gaishe da Abiy cikin yanayin sa na kadaran kadahan.

Abiy da murmushi yana kallon sa ya ce, "Lafiya lau Omar, ya hanya?."
"Alhamdu lillah" ya amsa a ta™aice dan jinsa yake a takure. Wani irin girma yake ji Abiy ya yi masa a jikinsa da zuciyarsa, shiyasa gabaWaya ya kasa sakewa ya kuma kasa haWa ido da Abiy.

Didi ta ce, "Abiy mun zo mu yi godiyar alkhairin da aka yi mana, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna. Babu abinda zamu saka maka dashi sai addu'a. Ga Omar ya dawo cikin alfarmarka, Allah ya sa a fi haka, Allah ya kare ka, Allah ya shirya maka zuri'arka, Allah ya ™ara maka lafiya da tsahon rai mai amfani." Abiy yana ta murmushi cikin jin daWin addu'arta ya ce, "Amin ya rabbi. Tun daga Kano har Kaduna ku ka taho?."

Didi ta ce, "ai ya zama dole ne, dole mu zo mu yi godiya."
"Har gida kin je kin yi min godiya a lokacin, sai da ku ka sake Wauko hanya ku ka zo?." Didi ta yi murmushi Abiy ya ce, "Babu komai ai yiwa kaine. Kuma kafin na taimaki Omar ai shi ya taimake ni, na rama alkhairi da alkhairi ne kawai."

Omar wani iri yake ji a jikinsa, ba saba yiwa mutane godiya ya yi ba balle ya san irin addu'ar da zai musu, duk sai ya rasa abinda zai ce yake jin bakin sa kamar an Waure tamau. Gashi yana ji a jikinsa ya kamata yayi magana amma ya rasa me zai ce. Zai yi magana kenan Nayla ta shigo falon ba tare da ta lura da Didi ko Omar ba, a shagwaSe ta shigo ta san Abiy yana nan dan kawai Mama ta ce mata Abiy na kiranta bata san su waye a ba.

"Abiy" ta faWa tana ™arasowa inda yake. Ya kalle ta ya ce, "Mamana kin tashi? Tun Wazu aka ce bacci ki ke yi, ya zazzaSin?" Ya faWa yana ri™o hannunta ya zaunar da ita kan kujera yana taSa wuyanta. Abiy ya ce, "har yanzu jikinki da zafi. Mamana baki da lafiya gaskiya yana da kyau ki ga likita, gabaWaya kin rame sai yawan ciwo a kai akai-akai. Zan yi magana da likitan da zaki gani ki je gobe ya duba ki a san abinda yake damunki. Jiya Maman ki ta ce min harda ciwon ™irji ko?." Kai ta Waga alamun eh har lokacin idanunta a lumshe yake kafin ya ce, "Jawad gobe zai kai ki wajan likita, na lura kece bakya son zuwa."

"Hajiya Nayla" Salma ta furta tana kallon ta. Da sauri ta buWe ido tana kallon mutanen da suke zaune a falon. Dam! Gabanta ya buga haWa ido da suka yi da Omar da yake zaune daga gefe ya Wago kenan suka haWa ido. Wara idanu tayi ta kalli Abiy ta sake kallon su Salma ta ce, "Salma, Didi?." Didi tayi murmushi ta ce, "Na'am Nayla." Sai kuwa tayi ihu ta tashi a guje ta koma kusa da Didi ta ce, "Didi yaushe ku ka zo? Shine ba a faWa min ba?. Wai ko mafarki nake yi ne?."

Didi ta ce, "ba mafarki ki ke yi ba Nayla, ni ce yau a Kaduna." Nayla ta ce, "ikon Allah. Kuma Mama bata faWa min ba fa, ta ce min kawai Abiy yana nemana, ashe ku ne kuka zo. Sannu da zuwa."
"Yauwa Nayla, ya jikin na ki?."
"Da sau™i" ta faWa tana sauke da ido ™asa farin ciki yana mamaye zuciya ta ganin masoyin ta a zaune a falon gidan su.

Abiy da yake kallon ta yana murmushi ya ce, "ki tashi ki je ki saka a haWa musu breakfast sun yi tafiya mai nisa." Mama ce ta shigo falon da sallama ta ™araso ta zauna suka sake gaisawa da Didi shi dai Omar bai iya kallon ta ba sun gaisa kawai dan in akwai abinda ya tsana bai wuce gaisuwa ba.

Abiy ya kalli Mama ya ce, "wannan shine wanda ya taSa taimakon Nayla a Kano shekarun baya....Kin tuna?." Mama ta ce, "Allah sarki na gane shi." Didi ta bawa Mama abinda ta taho musu dashi Abiy ya ce, "harda wahala? Ku da ku ka yi tafiya mai nisa har sai an yi tsaraba?." Didi murmushi ta ke yi ta ce, "Babu komai Abiy." Abiy ya ce, "mun gode sosai, Allah ya bar zumunci."

Didi ta amsa da amin tana murmushi, ta ji daWin yadda Abiy ya karSe su wallahi, ta kuma fuskanci gadon kirki Nayla tayi daga wajansa. Mama ta kalli Nayla da ta kwantar da kanta a kafaWar Didi tana kallon Omar ta gefen idanu ta ce, "Nayla ki je ki saka a haWa musu abinci su ci ko?." Nayla ta Wago a sanyaye ta ce, "To Mama." Abiy ya ce, "Mamana jikin ne?." Ta girgiza kai ta ce, "A'a Abiy, murnar ganin Didi ce kawai."
"To maza ki je a haWa musu abinci, sun yi doguwar tafiya."

Bata mi™e ba gani take in ta tafi bazata cigaba da kallon Omar ba, shi kam ko kallon inda take ma bai yi ba balle ya yi magana. Abiy ya ce, "amma dai sai gobe zaku koma?." Didi ta wara idanuta ce, "A'a, anjima kaWan zamu koma in sha Allah." Abiy ya ce, "Toh, ai na Wauka zaku kwana ku huta gajiya ai. Shikenan ni daga nan zance ya kiyaye hanya, zan shiga Zaria bazan dawo na zame ku ba gaskiya. Allah ya kiyaye hanya na gode da girmamawa." Omar ne ya buWe baki kamar mai koyan magana ya ce, "Amin. Mun gode sosai, Allah ya ™ara girma."

Lumshe ido Nayla tayi jin kalaman Omaar idanunta suna cika da hawaye saboda tsantsar bugawar da zuciyarta take yi. Salma na lura da ita haka Mama duk motsin ta akan idanunta take yi. Abiy ya ce, "amin Omar, Na gode sosai. Mamana ki raka su falo su huta." Nayla ta amsa ta mi™e ta ce, "Didi ku zo mu je" ta faWa a sanyaye. Didi ta mi™e Salma ma ta mi™e Abiy ya ce, "Omar ku je tare, Jawad raka shi zai fi sakewa." Jawad ya amsa yana mi™ewa shima suka shiga ciki.

˜aramin falon ba™i aka shigar dasu mai kyau madaidaici. Nayla ta kunna a.c bayan ta kunna hasken falon ta fita daga falon ita da Salma. A kitchen Salma take ce mata, "Nayla don Allah ki nutsu, sai rawar jiki ki ke yi kina bayyana feeling Winki a fili." Sai kawai ta rungume Salma ta fashe da kuka tana cewa, "Salma Omar ne a gidan mu, Omar ne a zaune shaida Abina suna magana. Salma na kasa tantance adadin farin cikin da nake ji, ji nake kamar zuciyata zata buga saboda murna Salma. Omar Wina yana nan lafiya, Allah na gode maka, Allah na gode maka" ta faWa cikin kuka sosai.

Salma ta ce, "to ki yi ha™uri ki bar kuka mu kai musu abincin in ya so sai mu yi magana." Nayla ta Wago daga jikin Salma tana share hawaye ta ce, "Salma ki yi addu'a Allah kar ya Wora miki soyayya irin wacce ya Wora min, akwai azaba ba kaWan ba Salma. Na kasa yin lafiya cikin kwanakin nan kuma duk saboda tunaninsa." Tausayi ta bawa Salma matu™a, idon Salma ya kawo ruwa amma bata yi kuka ba ta daure ta yi mata shiru bata tanka mata ba.

A haka suka zuba abincin a flaks, doya ce da ™wai da sauce sai dankalin turawa soyayaye da kuma soyayyen ™wai. Ga farfesun naman rago da aka yi shi mai ruwa, sai shayi da manyan slice bread da gwangwanin madara da na milo da sugar.

A kan table suka ajjiye sannan Salma ta koma ta kawo ruwa da lemo masu shegen sanyi ta ajjiye. Didi ta kalli Nayla da take tsaye kana ganin ta ka san tayi kuka ta ce, "Nayla jikin ne?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "A'a Didi, kaina ne yake ciwo shiyasa."
"Sannu, Allah ya ™ara lafiya. Ki je asibiti a duba ki." Kai kawai ta Waga dan ™irjinta ya yi mata mugun nauyi, ga Omar dai tana kallonsa amma kewarsa take ji kamar ta je ta rungume shi haka take ji.

Shi kuwa Omar yana jin su amma baya Wagowa waya yake dubawa ba tare da yana yin wani abun a wayar ba. Fitar Salma da Nayla ya saka Didi ta ce, "kai kuwa Omar ko sannu ai ka ce mata ko? Itace silar fitowar ka daga hannun Sen na faWa maka. Ko ya jiki ai ya kamata ka ce mata zata ji daWi." Shiru ya yi bai ce komai ba, gabaWaya a takure yake jin kansa cikin jin nauyi wanda bai san dalilin faWuwar hakan ba.
Salma da Nayla sun jima basu dawo ba har kusan mintina talatin kafin su dawo, Didi ce kawai ta sha tea amma shi ruwa kaWai ya sha bayan nan bai sake Waukar komai ba.

Nayla ta kalli Didi ta ce, "Didi har kin ci?." Didi ta ce, "na sha tea Nayla, in zan yi tafiya bana son cin abinci wallahi." Nayla tayi murmushi tana satar kallon Omar da ya ajjiye ruwan da ya sha a lokacin.
"Yaushe zaki zo mana Kano?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "ai sai bikinki, aiki ya saka ni a gaba ya hana ni zuwa ko ina. Ni dana sanin ma fara aikin nake yi wallahi."

Didi tayi dariya ta ce, "Allah ya kaimu, ya taimaka miki." Ta amsa da amin wajan ya yi shiru babu mai magana. Didi ce ta sake cewa, "Salma an kaiwa driver abincin?." Salma ta ce, "na tabbatar ma ya cinye yanzu." Didi ta yi murmushi suka sake yin shiru. ˜arar wayar Nayla ce ta katse shiru ta kalla ta ga Abbas ne ta kalli Salma ta ce, "Yayanki ne." Salma tayi dariya ta ce, "yayan mu dai, kema ai yayanki ne. Baza ki Wauka ba?." Nayla ta ce, "ana babbakar giwa waye zai je ™aure zomo?."

Salma ta murmusa cikin tausayin ´ar uwarta ta ce, "Gaskiya ne." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Nayla zan shiga banWaki." Salma ta ce, "mu je na raka ki." Didi ta mi™e ta fita ita da Salma aka bar Omar kawai da Nayla a zaune. Wani irin yarrr Nayla take ji a jikinta, gashi dai kamar bai san tana zaune ba amma wani irin suka zuciyar take yi ga farin ciki da yake mamaye zuciyarta. Ganin ba ita yake kallo ba kawai sai ta zuba masa ido tana

Please Login or Register in order to submit comment