Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya Saci sosai" ya faWa ya yanke wayar ganin Abiy ya taho. Yana shiga motar Jawad ya ce, "Abiy mu biya gidan Hajja mu tafi da Nayla?." Abiy ya ce, "tare muka zo da ita?." Jin abinda ya ce sai ya yi shiru amma zuciyarsa gabaWaya babu daWi akan abinda Abiy ya yi, to babu yadda zasu yi ne dole su yi shiru kamar yadda ya ce. Fita suka yi daga gidan bayan sun bawa mai gadi abincin suka Wauki hanyar Kaduna.

Nayla kuwa da suka je gidan Didi bata nan sai kawai suka wuce gidan Jidda, suna zaune a Jawad yayi mata waya duk sun ji abinda ya ce. Ta kalli Twiny ta ce, "Yaya J ne yau yake yi min wannan faWan, yanzu waye zai kai ni Kaduna?." Twiny ta ce, "ke share shi, gobe sai ki tafi. Haka kawai sai yaja Abiy ya yi miki faWa daman gashi Abiy na fushi."

Nayla ta ce, "yanayin maganar Ya J da Sacin rai ciki sosai Twiny, ko dai naje na hau motar haya na koma?."
"Ki share shi, gobe da safe sai ki tafi." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya sa Abiy bai yi fushi da tahowa ta Kano ba, Allah ya sa ya fahimce ni ya yafe min laifin da nayi masa." Suka amsa mata da amin. Hira suke ta janta da ita amma ta kasa sakin jikin saboda bata da walwala ko kaWan, yamma nayi suka wuce gida a motar gidan Hajja da Salma ta kawo su.KRB2P021

Su Abiy da suka koma gida bai cewa kowa komai ba sama ya hau ya barsu a wajan a tsaye. Mama ta kalle su ganin fuskar su Wauke da damuwa ta ce, "Wai ne ya faru ne? Me kuka je yi Kano?." Jawad ya kalle ta ya ce, "dangin wannan yaron Omar muka je, abin mamaki Abiy ya bada auren Nayla, dan yanzu haka Nayla matarsa ce." Mama ta wara idanu waje a zahiri, a baWini kuma farin ciki ne ya mamaye mata zuciya ta ce, "Aure kuma? Auren Nayla da Wan daban aka yi?."

Yaya ya ce, "Wallahi shi aka yi Mama, Abiy ya™i faWa mana dalilinsa, sannan kuma ya hana mu tamabaya. Yanzu zancen da nake miki an Waura auren su ita dashi, kuma ko sani Omaar Win bai yi ba, haka Nayla Win ma bata sani ba."

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Meyasa mahaifinku ya yanke wannan hukunci? Me Nayla tayi masa haka?. Ko dan ta tafi Kano ne ya saka ya yanke wannan hukuncin?." Jawad ya ce, "itama bata da mutunci ai Mama, ban da rashin hankali da shirme meye na barin gida a akan wannan maganar? Na rantse da Allah in ta dawo sai na zaSa mata kamanni."

Mama ta ce, "bara naje na samu Abiy Win naku naji dalilin sa na aikata wannan Wanyen aiki." Yaya ya ce, "Yauwa Mama, in da hali a kira yaron kawai ya sake ta tunda daman bai san anyi auren ba. In yaso ni a bani Nayla mu koma Lagos ta koma zama a gidana, nayi alqawari zan kula da ita babu wata damuwa irin wannan da zata sake kunno kai." Mama ta girgiza kai ta hau sama da sauri wajan Abiy. Sallar magriba ta samu yana yi sai ta zauna tana zaman jiran ya idar suyi magana.

Koda ya idar lazimi ya fara ta san kuma baya gamawa sai za a yi i'sha gashi ita ta ™agu tayi magana dashi. Mama ta ce, "Don Allah Abiy ka katse lazumin nan muyi magana. Ta ya za a aurawa Nayla wancan yaron?. Bai kamata a biye mata a aikata abinda take so ba." Ko motsi bai yi ba balle ta saka ran zai bata amsa. Mama ta ce, "Abiy don Allah kace wani abu, ka dakatar da lazumin nan muyi magana don Allah."

Ban ma bai kula ta ba Mama ta zauna tayi tagumi tana kallonsa. Gajiya tayi da zaman ta tashi ta fita shi kam bai ma kalle ta ba. Sai da ya kammala yaji ana kiran sallar i'sha sannan ya tashi ya fito dan zuwa masallaci.

Koda ya dawo a falo ya tarar dasu gabaWaya da alama zaman jiran sa suke yi. Wucewa yayi ba tare da ya zauna ba suka bishi da kallo ganin ya shiga ciki. Jawad ya ce, "Mama don Allah kije kuyi magana ya bar mu cikin tunani." Mama ta ce, "maganar ce baya so shiyasa ya wuce bai kula mu ba, amma bara na sake zuwa naji" ta faWa tana hawa saman ta barsu a ™asa.

Tana zuwa ta same shi ya zauna akan kujera yana kallon tv, ta zauna a kusa dashi ta ce, "abinci fa?." Ya girgiza kai kawai alamun baya ci. Mama ta ce, "maganar dai da baka so ita zanyi Abiy. Meya faru ka yanke wannan hukunci akan Nayla?. Naji bata kyauta ba amma da ka sani baka yi haka ba." Bai ce mata komai ba itama sai tayi shiru bata sake magana ba.

Katse shirun tayi da cewa, "bata kyauta ba abinda tayi na barin g1da, bata kyauta ba maganar da tayi ta ce zata kashe kanta akansa amma Abiy bai kamata ka biye mata ba, Nayla yarinya ce ™arama bata da hankali har yanzu." Abiy ya kulle ido ya buWe ya kalli Mama ya ce, "gobe ku shiga kasuwa, duk abinda ake siyawa amarya ku siya mata. Duk abinda za ayi ayi shi a gama ba sai ance za ayi order daga wata ™asa ba. A siyi komai gobe zuwa ranar Sunday nake so tafi gidan mijinta" yana faWar hakan ya tashi ya bata waje.

Mama ta ce, "meyasa haka...." Katse ta yayi ta hanyar cewa, "kar ki shigo ki dame ni" yana faWa ya wuce Waki. Mama tayi wani mayaudarin murmushi ta ce, "an gama." Canja yanayinta tayi ta sakko ™asa wajan su Yaya da Jawad suka bita da kallo ganin yanayinta ya nuna musu alamun rashin nasara. Ta kalle su ta ce, "yace gobe na shiga kasuwa na siyawa Nayla duk abinda ake siya na aure, wai zuwa jibi zata tare." Yaya ya ce, "Mama sai kika ce masa me?" Ya faWa kamar zai yi kuka.

Mama ta ce, "bai bani damar magana ba, ya kuma kalle ni yace kar na dame shi ya shiga Waki ya bar ni a falo." Jawad ya ce, "wai me yake damun Abiy ne har haka? Me Nayla tayi masa da ya canja lokaci guda don Allah?."
"Bata kyauta ba Jawad, abinda tayi ba tarbiyyar da ya baku bace gabaWaya. Amma shima yayi gagagwar yanke hukunci, Nayla yarinya ce ´ar ™arama ba babba ba."

Yaya ya ce, "kome tayi ai bata cancanci haka ba, irin wannan aure kamar bata da gata kawai an Wauketa an bashi ba tare da yana so ba? Babu kuWin aure, babu komai hatta sadaki biya masa aka yi. Ko da yake bai ma sani ba." Mama ta ce, "ka wuce gida dare yayi, in yaso gobe zai kuzo mu ji in zai yi mana magana." Jawad ya ce, "ai wallahi gobe in bata dawo ba da kaina sai naje na dawo da ita, shashasha mara hankali da tunani" ya faWa yana fita daga falon shima ya bi bayan sa.

Mama shiga Waki ta Wauki waya ta saka a kunne kafin ta ce, "Yauwa, in zaka iya ka sake hacking account Winta na WhatsApp ka sake turawa Abiy sa™o. In zai yu zan turo maka irin abinda da zaka tura masa yanzun nan." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta ce, "karka damu, na tura maka kuWin ka harda na data ka ™ara." Yanke wayar tayi tana kallon wani wajan daban tana Wan dukan wayar da hannunta.

Murmushi tayi ta ce, "kwanciyar hankalina shine auren nan ya tabbata, babu ta yadda za ayi na bari a warware shi tunda an riga da an Waura. Yadda ban ji daWi zaman gidan nan ba, yadda Bilkisu ta wahalar dani a rayuwar gidan nan Nayla ma sai ta WanWana irin abinda na WanWana. Muje dai zuwa" ta faWa tana yanke wayar ta shiga banWaki zuciyarta fes take dan ta san ta zama silar aurawa Nayla wanda baza ta taSa jin daWin zaman aure dashi ba.

" " " " " " "

      Didi tana barin gidan Kawu gidan su ta wuce ta samu Omar Win a zaune ya dawo daga masallaci yana zaune akan kujera ya Wan zame kansa na bayan kujerar ya Wora ™afa kan Waya kamar yadda ya saba. Kallon sa take yi ganin yayi mata kyau gashin kansa ya kwanta kamar na jariri, idanunsa a rufe gashin idanunsa sun kwanta a ™asan idanun.

"Omar Lafiya?" Ta faWa tana zama daga gefen sa. BuWe ido yayi ya ce, "Didi! Saukar yaushe?."
"Yanzu na shigo, baka da lafiya ne?."
"Ciwon kai ne yake damuna tun safe."
"Amma ka sha magani?."
"Na sha" ya faWa yana sake lumshe idanunsa bai ce mata komai ba.

Didi kallonsa take yi tana haWa kalaman da zatayi amfani dasu wajan sanar dashi abinda ya faru amma ta kasa, ta rasa ta ina zata kamo zaren, ta rasa da wacce kalma zata yi amfani wajan sanar dashi abinda yake zuciyarta akansa. Ajiyar zuciya tayi hakan ya saka ya buWe ido ya kalleta ya ce "Lafiya dai?." Didi ta kalle shi sai taga idanunsa sun yi ja alamun yana jin ciwon kan sosai ta ce, "ciwon kan ne dai?." Ya Waga kai alamun eh.

Lumshe ido tayi ta sake buWewa tana kallonsa ganin ita yake kallo, ya sauke ™afa Waya ™asa ya kalleta sosai ya ce, "kar ki damu da kaina na ciwo, ki faWa min abinda yake faruwa. Naga kin canja alamun damuwa, meye?." Kai ta girgiza ta ce, "Babu komai Omar, Tambayar ka nake so nayi kawai."

"Akan son tambayata kawai kika koma haka?." Kallon sa tayi sai bata amsa ba ya ce, "Ina jinki."
"Omar na isa da kai? Na isa na zaSa maka abu ka karSa hannu biyu?." Wani irin kallo yake yi mata na me ya kawo wannan tambayar kafin ya ce, "me ya kawo wannan tambayar? Wani abun ya faru ne?."

"Babu abinda ya faru, ka amsa min tambayata."
"Akwai abinda ya faru, kawai bakya so ki faWa min ne. Ni kuma Ina so na san meye abinda ya faru kafin na amsa miki."
"Kawai ka amsa min Omar."
"Me zan amsa?" Ya tambaya yana kallonta. Didi ta rausayar da kai ta ce, "na isa da kai? Na isa na zaSa maka abu ka karSa?."

Omar ya bita da kallo yana so ya gano dalilin tambayar amma bai gane ba, ya Wan Wauke ido yana kallon wani wajan daban kafin ya ce, "kin isa."


Didi ta ce, "Koda matar aure ce? Koda Wauko mace nayi a yanzu nace maka na saka an Waura maka aure da ita zaka karSa ta?." Omaar ya bita da kallon mamaki ganin ba da wasa take yi kamar yadda ta saba ba, sannan ya ga damuwa a kwance a fuskarta, sannan ya tabbatar da akwai abinda take so ta faWa masa kafin wannan. Didi ta ce, "ka yi shiru kana kallona." Omar yayi ajiyar zuciya ya ce, "dalilin wannan tambayar nake so naji."

"Ni dai ka amsa min kawai" ta faWa tana kallon sa. Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta kafin ya ce, "eh to, kin isa ki zaSa min Win tunda kece zai karSa babu yadda zanyi. Amma kin san kin bani ita ne ba dan Inaso ba, kuma zama da wacce bana so bazata taSa jin daWin zama dani ba har abada. Kin fi kowa sanin halina, bana son ganin abinda ban saba gani a tare dani ba." Didi gabanta ya yanke ya faWi tsoro ya mamaye mata zuciya ta ce, "amma zaka iya zama da ita a matsayin matarka dai ko? Babu tsawa, babu tsoratarwa, babu razani, babu harara ko?."

Gyara zama yayi ya shafa kansa zuwa gashin fuskarsa, ya Wan sosa girar sa da yatsa Waya kana ya ce, "gaskiya bazan iya zama da ita matsayin mata ba, zan dai zauna da ita a gida Waya matsayin zaSinki, amma gaskiya ba dai a matata ba."

Kallon sa take yi ta kasa magana dan ya kashe mata baki, ya katse shirun ya ce, "me ya kawo wannan maganar wai? Aure zaki yi min ne?." Jin yana ™o™arin gano ta sai ta girgiza kai ta ce, "Kusa hakan, bana son zaman ka kai kaWai a gidan nan shine nake tunanin zaSar maka mata na aura maka."

"Kar ki wahalar da kanki bana bu™ata, bana so in kika yi ma zaki Sata lokacin ki ne, ko wacece ita zaki Sata mata lokaci da rayuwarta ne dan ni ban shirya aure ba. Gwara ki bari taje ta auri wani daban da dai ace ta aure ni, zaman aure da wacce babu ita a rayuwara tun farko babbar matsala ce. Na hutar dake, bance ina so ba, dan haka ki bar maganar nan."

"Baza ka iya kallonta a matsayin matarka ba saboda ni?".
"Haba Didi! Na faWa miki ban so a bar maganar nan, in ma kina niyar yi ne kar ki yi na hutar dake bana bu™ata, zama ni kaWai baya damuna kinfi kowa sanin haka. Wacce mace zaki Wauko ki kawota cikin rayuwata ba tare da sanina ba? Don Allah ki adana wannan tunanin, kar kuma kiyi wannan gangancin in ba haka ba zan ta Sata miki rai, ki ™yale ni!" Ya faWa a kausashe yana kallonta dan ta katse batun shi ya gaji da wannan kalaman nata.

Ajiyar zuciya tayi ta rasa da wacce hanya zata yi masa magana ya fahimta, me zata ce masa ne wai? Ta ce masa mahaifin Nayla ya zo ya baka auren ta? To Akan wanne dalili ya aura masa ita? Meyasa yayi hakan?. Ganin ta tafi duniyar tunani sai taji ya murza yatsunsa a kusa da fuskarta sun bada sauti, ta kalle shi ya ce, "Ki faWa min damuwar ki Didi!" Ya faWa cikin kakkausar murya yana kallonta. Didi ta buWe ido tana kallonsa ta ce, "babu komai na faWa maka, zaman ka haka ne bana so, ya zama dole na nema maka matar aure koda baka so."

"Didi ki daina ™o™arin raina min hankali mana, na sanki na san halin ki kar ki manta da wannan. Wallahil azim akwai wani abu a zuciyarki, ki sanar dani damuwarki in kuma baza ki faWa min ba kice baza ki faWa ba." Didi ta kulle ido ta buWe sai ta tashi tsaye ta ce, "Akwai abinda zan Wauka a kitchen, na san ba amfani kake yi dashi ba ni kuma ina so. Gwara na haWa kayan na ajjiye kar na manta" ta faWa tana shiga cikin kitchen ta barshi a wajan yana kallon ta cikin tunanin abinda yake damunta.

Da ta fito ya fita bata sake ganin sa ba, dan Waki ya shiga ya kwanta saboda ciwon kan da yake damun sa. Sai da magriba sannan ya fito yayi alwala ya same ta a tsaye a tsakar gida ta kalle shi ta ce, "zan shiga wajan Hajja." Kai ya Waga kawai tazo ta wuce shi.

        Da sallama ta shiga gidan Hajja aka amsa mata, abinda ya bata mamaki bai wuce Nayla da ta gani a zaune ba tana yi mata oyoyo. Murmushi tayi ta zauna ta ce, "mutanen Kaduna, saukar yaushe?." Nayla ta ce, "saukar jiya, kuma gobe zan koma. Har gidan ki muka je Wazu bakya nan." Jin hakan sai Didi ta bita da kallo da alama itama bata san da auren ba. To me hakan yake nufi wai? Meye dalilin Abiy na aurawa Nayla Omar ba tare da ta sani ba?.

Hajja ce ta katse mata tunani suka gaisa kafin ta kalli su Nayla ta ce, "naje gidan Kawu a can na yini sai yamma nazo nan, Meyasa baku yi min waya ba?."
"Muna ta kiran ki ta™i ta shiga shiyasa."
"Ayya, amma kun kyauta na so kun same ni." Nayla tayi murmushi ta ce, "zamu dawo wani lokacin."

Hira suka cigaba da yi da Hajja da kuma Salma dan ita dai Nayla tayi shiru bata magana. Didi ta taSata ta ce, "Nayla ya dai?." Nayla tayi murmushi ta ce, "babu komai, anyi kiran sallah bara naje nayi sallah" ta faWa tana shiga ciki duk suka bita da kallo.

Didi tausayi ma take bata wallahi, ko meyasa mahaifinta yanke hukuncin aura mata Omar oho, gashi da alama itama bata sani ba, meye amfanin yin hakan da yayi Allah ne ya sani. Duk tashi sukayi akayi sallah kafin Didi tayi musu sallama ta ce zata tafi, Nayla da Salma suka raka ta bar ™ofar g1da a nan suka ga motar AbdulHamid da alama ita yake jira.

Didi ta ce, "Don Allah kuzo ku taya ni Wauko kayan a ciki, kayan kitchen ne wanda na san ba amfani dasu zai yi ba na tattaro kayana." Salma tayi dariya ta ce, "wallahi gwara da kika Wauko" ta faWa suna bin bayanta zuwa gida. ˜irjin Nayla bugawa yake yi sosai ba kamar da suka shiga tsakar gidan, Nayla ta Wauki leda Waya Didi ta Wauki biyu Salma ma ta Wauki Waya.

Daga falon Omar ya fito sanye da ™aramar riga mai gajeren hannu mara nauyi, sai wando three quarter. Kallon sa tayi ta ce, "Omar sai da safe."
"Ki kwana Lafiya" ya bata amsa yana niyar wucewa ba tare da ya kalleta ba.
"Ya ciwon kan?" Ta tamabaya tana kallon sa. Juyowa yayi ya kalleta ya ce, "naji sau™i."
"Baka ga su Nayla da Salma ba? Baka yi musu magana ba."

Kallon su yayi, Nayla dai kanta yana ™asa Salma ce ma take iya kallonsa kamar zai yi magana sai ya fasa, ya Waga ™afa da niyar barin wajan sai ya juyo ya kalli Didi ya ce, "na rasa meyasa kike son saka ni a abinda bai shafe ni ba" yana gama faWa ya wuce ya barta a wajan.

Wani iri taji a zuciyarta, dan ita ta san yanzu Nayla matarsa ce shida ita ne basu sani ba, hakan da yayi ya tabbatar mata da karSar Nayla zai yi masa matu™ar wahala, duk ganin da yake mata gashi bai saba da ita ba. Ita ta Wauka ya saba da ita har zai iya yi mata magana, tunda shi magana da wanda bai saba ba babban tashin hankali ne a wajan sa.

Didi ta kalli Nayla bata ce komai ba sai Salma da tayi dariya ta ce, "Kema Didi ban da abin ki ina Omar inayi mana magana? Mu je" ta faWa tana yin gaba duk suka bi bayanta Nayla dai kanzil bata ce ba.

Har motar suka saka mata kayan tayi musu godiya suka gaisa da mijinta sannan suka wuce gidan Hajja. Tunda ta shiga motar shima ya lura tana cikin damuwa mai yawa, ya kalle ta cike da kulawa ya ce, "Ya dai? Akwai abinda ya faru ne?." Didi ta ce, "Akwai wallahi. Kaga yarinyar nan da kuka gaisa mai blue Win mayafi?."
"Eh na ganta."
"Itace Nayla, itace wacce ta yi silar da aka fito da Omar daga wajan Senator. Šazu mahaifinta yaje har gidan Kawu ya saka aka Waura aurenta da Omar."

AbdulHamid ya ce, "Iyee! aure da Omar  kuma!?." Didi ta Waga kai ta ce, "wallahi, yanzu maganar da nake maka ita matar Omar ce wallahi."

"Ikon Allah, to garin ya haka ta faru?. Daman suna soyayya da Omar Win ne?." Didi ta ce, "ita dai tana son Omar, na ji da kunnena suna tattauanwa a ranar Waurin aurena da kai. Ta bani matu™ar tausayi, domin soyayya bata yi mata adalci ba da ta saka ta fara son Omar. Ita ba tsararsa bace, ta wuce ajinsa nesa ba kusa ba, ko masu gadin gidansu sun fi Omar matsayi wallahi. Abinda ya bani mamaki ya kuma Waure min kai shine; mata guda biyu kyawawa, masu asali da iyaye masu kuWi da faWa a ji a ™asar nan, mata masu ilimi, aji da wayewa sune suke yiwa Oamar irin wannan soyayayar? Anya ta baki Senator ba asiri Omar yake yi musu ba kuwa?."

Abdul yayi dariya ya ce, "Wanne irin asiri ana zaune Lafiya? Kawai haWuwar jini ce. Kin san mata suna son farin namiji kyakykyawa mai saje kamar Omar Win."
"Amma haWuwar jinin su rasa da wasu haWa jini sai Omar? Mata kamar su ace sune suke sonsa ba shine yake sonsu ba?. Har gwara Narma ita ya furta min yana so, to Nayla fa da take matsayin matarsa yanzu?."
"Ni maganar auren ce ta Waure min kai, haka kawai mahaifinta ya aura masa ita kamar auren ´ar tsana?."
"Wallahi nima ya Waure min kai, abin mamakin kuma a yanayin yarinyar na tabbatar da bata san da auren ba kamar yadda Omar bai sani ba. Meyasa mahaifinta ya aura masa ita?."

"Ko ya gano tana sonsa ne?."
"Dan ya gane tana sonsa kuma sai ya Waura mata aure dashi yau kwatsam? Gaskiya akwai lauje a cikin naWi a lamarin nan." AbdulHamid ya ce, "yanzu shi Omar Win ya sani?."
"Waye zai faWa masa? Kaf duniya ni kaWai ce zan iya tunkararsa da wannan maganar, to nima Win na rasa ta wacce hanya zan faWa masa. Jurwaye mai kamar wanka nayi masa, nace masa na kai matsayin na bashi mata ya zauna da ita, ka san me ya ce?."

Ya girgiza kai alamun a'a Didi ta ce, "cewa yayi zai iya karSa tunda ni ce babu yadda zai yi, amma bazai iya kallonta matsayin mata ba, zai dai zauna da ita gida Waya matsayin wacce na ajjiye masa amma ba matarsa ba." Abdulhamid yayi dariya ya ce, "Wallahi Omar yana burge ni, yanayin ™arfin guiwarsa da gaskiyarsa tana matu™ar burge ni a halayensa. Yanzu ya zaki yi?."
Cike da damuwa ta ce, "Dole dai ni zan faWa masa, amma nima ban san ta wacce hanya ba."

"Zaki samo hanya, ki nutsu kawai, ai yana jin maganarki zai yi duk abinda kika ce masa." Didi ta ce, "hmm baka san Omar ba ne, a dai yi shiru kawai" ta faWa tana kawar da kai zuciyarta cike da tunanin dalilin auren Nayla da Omar lokaci guda haka.KRB2P022

Narma tana tsaye a tsakiyar bedroom ta idar da sallah tana ninke sallaya Ashraf shiga yana binta da kallo. In ba da sexy dress ya ganta ba bata burge shi gabaWaya, yana so ya ganta da kayan da suka bayyanar da surar ta, in ya same ta da hijjabi ko riga mai girma sai yaji haushi ya tokare masa ™irji lokaci Waya sai yaji tana bashi haushi, amma da zarar ya ganta a yadda yake so sai yaji babu abinda yake so sama da kasancewarsa da ita.

Jin motsinsa sai ta kalle shi tana zare hijjabin daga jikinta, ajiyar zuciya ya yi ganin rigar jikinta wacce tayi daidai da yadda yake so ya ganta. Iyakar rigar guiwa tana da hannu mai Wan girma kaWan amma bata da kauri sannan tana bin jiki. Zama tayi a gefen gado tana kawar da kai dan tun lokacin da ya same ta sau Waya bata sake bari hakan ya faru ba.

Murmushi yayi ya ce,  My Love zamu iya fita?. Kallonsa tayi ta girgiza kai alamun a a ya ce,  Haba my love, ki amince muje ba jimawa zamu yi ba dawo. Kullum kina g1da, tunda muka zo bakya fita. Bata ce masa komai ba yazo kusa da ita ya zauna yana ™are mata kallo, halittarta na burge shi sosai, amma yanzu abinda yake ji a kanta ya ragu da kaso mai yawa, kawai ya san yana son kasancewa da ita bayan wannan babu wani abu a zuciyarsa a kanta.

A hankali ya kai hannu ya fara shafata ya ce,  My love muje mu dawo. Ko kina so mu taje miami mu kalli ball Win messi?.
 Pls Ashraf ka ™yaleni, babu inda zanje in kai zaka je kaje amma ka daina saka ni ciki ta faWa tana kawar da kanta gefe.
 Come on my love ya faWa yana yajowata jikinsa lokaci Waya yana ™o™arin zare rigar jikinta. Da hanzari ta fincike jikinta ta mi™e tsaye ta ce,  kar ka sake wannan kuskuren, wancan ka damu dama a banza a yanzu baza ka samu ba. Ka tashi ka fita ka bani waje bana son ganinka, wallahi na tsaneka, ka fahimi bana so ganin koda fuskar ka ne.

Kallon ta yake yi jin wai ta tsane shi ya Wan buWe idanu tare da taSe baki ya mi™e shima yana kallonta ya ce, 

Please Login or Register in order to submit comment