Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tunanin anjima zai sake dawowa cikin kansa.

Tsaki ya yi a bayyane, ko a lokacin Narma bai ji wannan nauyin zuciyar da yake ji a yanzu ba. Ya karkata hakan ga Sacin ran da maganar ta saka masa shiyasa da ya tuna sai ya ja tsaki.

Bashir ne ya shigo suka gama magana, Omarya aike shi shi kuma ya kwanta akan kujera ya rasa abinda yake masa daWi.

Bacci ne ya kwashe shi a haka sai kiran sallar azahar ya ji, ya tashi ya yi sallah yana tunanin abinda ya kamata ace ya ci. Kitchen Win ya shiga yana ™arewa komai na ciki kallo, sai kuma ya ja tsaki ya fito ya Wauki ruwa yana sha cike da jin haushi. Sai kuma ya kuma tashi ya dafa shayi ya dawo yana sha ba tare da ya saka madara ko wani abun ba.

Bayan sallar la asar Bashir da Tk suka shiga wajansa, yana kwance da ya gansu sai ya mi™e ya ce,  Ya aka yi?. Tk ya ce,  Tiger kayan da aka tura Abia state ne wai basu je ba, shine nake tambaya mai motar bai yi maka waya ba?.

Omar ya ce,  Kamar ya basu je ba? Ni babu wanda ya kira ni ya faWa yana duba wayarsa amma bai gani ba. Tk ya ce,  wanda aka turawa kayan ne ya kira ni ya ce driver bai je ba har yanzu, na kira driver a waya kuma baya Wauka amma bara& . Maganar ta katse saboda ganin kiran mai motar sai ya ce,  gashi ma yana waya. Ya faWa yana Wauka suka yi magana kafin ya kashe ya ce,  Yauwa, ya ce yanzu nan ya shiga garin zai kai masa nan da anjima kaWan.

Shiru ya yi baice komai ba. Bashir ya ce,  Damisa Didi ta sanar damu aurenka. Šago ido ya yi ya kalle shi sai ya sunkuyar da kai yana sosa kai ya ce,  Tuba nake Damisa, babbar Yaya ce ta sanar dani shiyasa na amince da batun. Kuma ta saka har a masallaci an sanar da maganar.

Da mamaki ya ce,  a masallaci?.
 kwari Boss, dan yanzu mutanen unguwa duk sun shaida. ˜aramin tsaki ya yi bai ce komai ba Bashir ya ce,  Allah ya sanya albarka Boss, mun so ranar auren ka ayi shagali na gaske, ranar Kano ta san da zaman mu wallahi tallahi. Da ranar kaf unguwar nan sun huta siyan maganin sauro, saboda zamu yiwa unguwar haya™i da ganye mai albarka Boss. Amma hakan ma normal ne, sai dai ba mu san Anty na mu ba.

 Bash ka dakata da yi min wannan maganar ya faWa yana kallonsa.
 Tuba nake, kaina biya wuya na. Šauke ido ya yi daga kallon su amma bai ce komai ba.

Sallamar da aka yi ne ya saka suka kalli wanda ya shigo. Ganin Didi ce da mijinta duk sai suka yi fara a suka gaishe su ta zauna tana cewa,  in aka ga zara za a ga wata, in aka ga Omar za a ganku. Bash ya shafa kai ya ce,  Babbar Yaya muna kewar girki mai daWi wallahi, yanzu sai dai mu dinga yawo mu rasa inda zamu ci. Tayi dariya ta ce,  ba sai ku yi aure ba, shi ogan na ku gashi nan ya yi aure ya bar ku ai.
Bashir ya ce,  Yanzu nake maganar babbar yaya, amma Damisa ya nuna baya son zancen.

 Baya so ya kai ku ku ci girkin amarya ne shiyasa. Suka yi dariya suka yi musu sallama suka tafi.

Omar ya kalli AbdulHamid ya ce,  sannu da zuwa. AbdukHamid ya murmusa ya ce,  Yauwa Omar. Kana Lafiya?. Numfashi ya sauke a hankali ya ce,  lafiya. Didi da take kallonsa ganin ya shareta kamar bai ganta ba sai tayi murmushi ta ce,  Omar ina yini. Kallon ta ya yi yaga tana murmushi sai ya sake tamke fuska ya ce,  lafiya. Dariya ta yi mai sauti ta ce,  Allah ya shirya min kai Omar.

Omar ya kalli mijinta ya ce,  matarka ta yi min laifin da na kasa mantawa, ko ya na motsa sai na tuna da abinda ta yi min, Ina so na manta amma na kasa. AbdulHamid ya ce,  Tuba mu ke yi.
 Da kai aka haWa baki kenan?.
 Babu ruwana, ni ha™uri nake baka kawai. Omar ya Wauke kai bai ce komai ba amma har lokacin yana jin haushinta.

Didi ta ce,  har yanzu haushin nawa ka ke ji?. Bai amsa mata ba kuma bai kula ta ba. Ta ce,  To Omar ka yi ha™uri, ka ji?. Nan ma bai tanka ba ya kawar da kai, sai kuma ya kalle ta ya ce,  wai har da sakawa a faWa a masallaci, ki ka tari su Bash ma ki ka faWa musu. Didi meyasa ki ke yi min haka ne?.

 Nayi haka ne saboda kowa ya san ka yi aure, sannan kar aga kana shiga gidan da matarka take a Wauka kana zuwa wani abun daban ne shiyasa na sanar. Yanzu kowa ya san kayi aure, ita kanta matar ta ka zata samu tsaro sosai.

Omar ya kalle ta ya ce,  in an zarge ni Win sai me? Ni ina tsoron ta mutu ne balle tayi rai?.
 Ka dai yi ha™uri ta faWa tana kallonsa dan bata so maganar ta yi nisa.

Didi ta ce,  in an jima zamu je gidan amaryar. Šago idanu ya yi ya kalle ta ya Wora ™afa kan Waya ya harWe yatsunsa yana kallonta ya ce,  da gaske?. Jin rainin hankalin da ya yi mata sai ta ce,  Don Allah Omar kar ka ce baza ka je ba, ka daina wahalar dani, don Allah ka je gidan nan kawai a huta.

AbdulHamid ya ce,  don Allah Omar ka amince ka je. Yanzu matsayin matarka take babu ruwan Allah da ya yadda aka yi auren nan, ha™™inta yana kan ka, ciyar da ita, shayar da ita, yi mata suttura, wajan kwanciya hatta kuWin katin waya yanzu kai Allah ya Worawa. In baka sauke wannan ha™™in ba babu ruwan Allah da baka son auren nan sai Allah ya kama ka da ha™™inta.

Omar da yake kallonsa sai ya yi wani murmushi na rainin hankali ya ce,  to ashe mijin Didi malami ne ban sani ba. Dariya ya bawa AbdulHamid ya ce,  to kira ni malamin indai faWar gaskiya zata saka na zama malami na karSa Omar. Ha™uri zaka yi ka tashi mu je ka huta da nauyin da yake kanka, itama Yayarka ta samu ta huta abinda yake cikinta ma ya huta.

Da sauri Omar ya kalle shi AbdulHamid ya ce,  eh Omar, tana da ciki. Ka kusa samun ´a ko Wa jinin Yayarka. Don Allah ka daina wahalar da ita ko dan saboda cikin da yake jikinta, kullum a damuwa take da fargabar yadda zata tunkare ka, kuma iya fargaba da tunani yana sakawa ciki ya zube Omar. Ka tausaya mata ka amince, komawa gidan kawai ake so ka yi, na tabbatar a hankali zaka sauke duk wani ha™™inta da Allah ya Wora maka.

Didi da take gefe murya a sanyaye ta ce,  Har ha™™in mu amalar aure. Wani banzan kallo ya yiwa Didi tare da harararta. Didi ta ce,  Harare ni da kyau gaskiya na faWa, har shi Allah ya Wora maka kuma in baka sauke ba kuma Allah zai iya kama ka. Banza ya yi mata bai kula ta ba dan magana da ita ma Sata baki ne.

AbdulHamid ya ce,  Yanzu ka amince?. Omar ya taSe baki ya ce,  Sai na yi tunani.
 Ka yi daga nan zuwa magriba in muna da rai.
Didi ta ce,  Sai hatun gwajin jini kuma& .. AbdulHamid ya kalle ta ya ce,  Ana ga ya™i kina ga ™ura.

Omar ya ce,  Shi gwajin jini meye amfanin sa?. Didi ta gyara zama jin ya tambaya ta ce,  ai kala-kala ake yi. Akwai na genotype wanda zaka san jinin ka wanne type ne saboda gudun samar da yaro mai ciwon sikila. Akwai na hiv, akwai na sanin jinin ka wanne group ne, shima in aka haWa positive da negative akan samu damuwa a wajan haihuwar yara, akwai na ciwon hanta, da na infection. Suna da yawa, amma in ka je za a yi maka bayani.

Jin ta yake yana girgiza kai yana yi mata kallon gaskiya kin samu matsala a kanki kafin ya ce,  To ni meye haWa ni da gwajin jini? Me ya haWa ni da samar da yaro mai ciwo?. Didi ta ce,  matarka ce fa Omar, yanzu na gama faWa maka harda ha™™in mu amalar aure a kanka, kuma za a iya Waukar ciki. Wannan ha™™in shine kan gaba a zamantakewar aure, nasan ka sani, ina sake tuna maka ne.

 Kuma da gaske ki ke?.
 Da gaske mana.
 Da ni Omar Win? Ya faWa tana nuna kansa yana kallonta. Sai yanzu ta gane gabaWaya raina mata hankali yake yi ta yi tsaki ta ce,  Omar don Allah ka bar wannan wasan kwaikwayon, ka nutsu mu yi abinda yake gaban mu don Allah.

 To na ji kina wani lissafi ne wanda zan kira shi da tatsuniya ko wasan yara. Didi zata yi magana AbdulHamid ya dakatar da ita ya ce,  a bar maganar gwajin jinin nan, ka amince da zuwa gidan amaryar kawai. Ba dan mu ba don Allah da kuma darajar cikin da take dashi, ka daina sakata a damuwa don girman Allah.

Omar ya ce,  Ai daman wallahi in dan ita ne bazan yi ba, gwara ma ta san inda ace saboda da ita ne wallahi bazan ba, dolen da take saka ni ya yi yawa. AbdulHamid ya ce,  mun gode sosai.

Omar ya ce,  shi gidan da ake zance ta ya aka samar dashi? Ko shima iyayenta ne suka bayar?. Didi ta kalle shi suka haWa ido ta ga ya tsayar da ido a kanta, Wauke kai tayi dan ta san ko ya ya tayi wani motsi zai iya kamata. Ta ce,  Haya na kama na biya. Ya girgiza kai ya ce,  anzo wajan. Ko ina sai kin nuna min bani da amfani sannan ban san abinda nake yi ba Didi, shiyasa ake yi min gori ake cewa babu abinda nake yi miki ke ki ke ciyar dani! Ya faWa a fusace yana kallonta.

Ganin ya fara fusata sai ta ce,  Dalilin da ya saka ban faWa maka ba ka ga baka san da auren ba, ita kuma iyayenta sun kira ni sun ce suna son ganin gidan da zata zauna. Ni kuma da yake akwai kuWin sana ata sai na Wauka kawai na kama hayar shekara Waya. Ba nayi dan na Sata maka rai ba ne.

 Ai kin saba, Sata min rai yau aka fara Didi?. Har ki Wauki kuWi da kuWin ki ki biya min kuWin haya kuma ki ce na naje gidan na zauna? Kema kin san wasa ki ke yi.
 Ban kai na biya maka Win ba ne Oamar?.
 Gaskiya baki kai ba, tunda ina da halin kama hayar babu ruwanki da biya min. Yanzu ki ka gama zana min samar mata wajan kwana ha™™ina ne, to ha™™in nawa ne ya dawo kan ki?.

Didi ta ce,  yi ha™uri, ni na yi ne saboda lokaci. Amma ka yi ha™uri ta faWa tana kawar dan bata so maganar tayi nisa. Juyar da fuska ya yi ya sake kallon ta ya ce,  a ina gidan ya ke?.
 Yana wancan layin na baya.
 Nawa ki ka biya?.

 Uhum? Ta faWa kamar bata ji me ya ce ba. Ya harareta ya ce,  kin ji abinda na ce ai. Didi tace,  dubu Wari biyar ne. Girgiza kai ya yi ya ce,  lallai Didi kina wula™anta ni yadda ki ke so, Kina nuna min bani da kuWi da zan iya biyan naira dubu Wari biyar. Kin raina abinda nake dashi kece mai kuWi ko?.

Didi ta ce,  Allah ya baka ha™uri ta faWa a ta™aice dan ta gaji da rigimar nan ta sa wallahi. Waya ya Wauka ya kira Bash yana Wauka ya ce,  nawa ne kuWin nan?. Shiru ya yi alamun ana bashi amsa ya ce,  Ka tura min Wari biyar yanzu ya faWa yana ajjiyewa ya kalle ta ya ce,  zan biya ki kuWinki.

Ta buWe baki zata yi magana ya ce,  wallahi kina musawa bazan je gidan ba. Ziping bakinta tayi da hannunta ta ce,  nayi shiru ranka ya daWe. AbdulHamid dariya yake yi dan shi Omar burge shi yake yi sosai ba kaWan ba, komai daga zuciyarsa yake fitowa babu ™arya balle kara.

AbdulHamid ya ce,  ranka ya daWe an yanke hukuncin zuwan?. Bai ce komai ba ya mi™e ya fita. Didi ta ce,  ka ga kalar rigimarsa ko?.
 Ai mun ci albarkarcin cikin jikinki da kafin ya amince zamu jima. Ki daina takura shi da tambaya kar ya fasa. Didi ta taSe baki kawai ta kawar da kai. Tana zaune har aka yi sallah ta tashi tayi sallah Abdulhamid ya fita.

Bayan ya dawo yana shigowa Omar ya shigo, AbdulHamid ya kalle shi ya ce,  Ranka ya daWe Damisa zamu iya tafiya?. Ya kama ™ugu ya kalle shi yana Waga gira sama tare da ™an™antar da idonsa ya ce,  saka ni a gaba zaku yi kenan?. AbdulHamid ya ce,  a a, raka ka zamu yi dai ya faWa yana dariya ™asa-™asa. Juyawa yayi ya fita Didi ta sake taSe baki AbdulHamid ya nemi waje ya zauna yana dariya.

Haka Omar ya shanya su yayi har tara na dare ta kusa yi sannan ya dawo. Yana shigowa ya kalli Didi yanayinta ya koma na wacce ta sha wahala ya ce,  Didi kina lafiya?. Ta kalle shi ta ce,  ta ya zan kasance lafiya ka shanya mu a nan Omar?.
 Mu je. Kallon sa tayi ta ce,  ™anunun kaya fa ka saka Omar, Ina laifin ka sa manya kaya?.
Ya Waure fuska ya ce,  In a fasa zuwa to. AbdulHamid ya ce,  kar ka fasa, amma da zaka saka manyan kayan ya fi mutunci.

 Gaskiya bazan saka ba!. Didi zata yi magana AbdulHamid ya ce,  shikenan mu je. Babu yadda Didi ta iya haka suka fito har ™ofar g1da. Ta kalli Omar da yake basarwa yana shan ™hamshi ta ce,  ban ga ka Wauki kaya ko kala Waya ba.

Banza yayi mata ko kallonta bai yi ba, AbdulHamid ne ya yi mata alama da ta daina yi masa magana dole ta yi shiru. Mota ya ga sun shiga ya kalle su ya ce,  ku je zan biyo ku bai jira mai zasu ce ba ya yi gaba su kuma suka biyo shi a baya.KRB3P005
ArewaBooks@nanahaleema11.

Har suka ™arasa ™ofar gidan Omar bai ™araso ba, Didi ta fito daga motar ta waiwaya tana kallon bayanta ta hango shi can nesa dasu ta ce,  tsabar rigima irin ta Omar motar ce bazai shiga ba. AbdulHamid ya ce,  kema ke ce ai, ana lallaSa shi a samu yazo kina sake tsare shi da tambayoyin da zai saka ya fasa..
 Ka dube shi fa YallaSai, haka Ango yake shigar sa don Allah?.
 Shi haka ya yi, kinga ya fitar da style.
 Kaima na san ka shaida taurin kansa ai yau.
 Gaskiya dai na shaida. Dan ba dan dani ba bazai saurare ki ba, har yanzu haushin ki yake ji.

Murmushi tayi kawai tana kallon sa yana sake matsowa inda suke har ya ™araso. Yana zuwa ya kalli Didi ya ce,  unguwar nan munafukai ne, sai kallona ake yi tunda na fito. Didi ta ce,  Ba dole a kalle ka ba, Ango guda da ™ananun kaya saunan kuma zai je gidan amarya?. Ya kalle ta ya ce,  to ko zaki tsaya na je gida na canja kayan?. Ta wara idanu ta ce,  a a yi ha™uri, hakan ma da ka yi daidai ne. Ya yi mata hararar wasa ya ce,  da kin nemi wani ba ni ba.

Didi ce ta ™arasa tana buga gate Win gidan a hankali. Salma da suke ciki tana zaune ita da Nayla suna hira sama-sama, Nayla idar da sallar i sha kenan tana zaune da hijjabi suka ji ana buga kofa. Gaban Nayla ya faWi ta ce,  mun shiga uku, waye yanzu Salma?. Salma ta tashi ta ce,  tsaya na je na duba. Nayla ta ce,  a a kar ki je. Salma ta ce,  ke babu komai fa. Ta faWa tana yin gaba ta barta a zaune tana raba idanu.

Salma na buWe ™ofa suka haWa ido da Didi sai tayi dariya ta ce,  Didi Sannu da zuwa. Didi ta ce,  Yauwa Salma. Haka ki ke buWe gidan ba tare da kin san waye ba? Gwara ki dinga tambaya in kin Wauki murya sai ki buWe. Salma ta ce,  Daman na san bazai wuce ke Win ba ce ko su Mima shiyasa na buWe kai tsaye. Sannan da zuwa.

Didi ta ce,  Yauwa. Ku zo mu je ta faWa tana kallon AbdulHamid da kuma Omar da ya jingina da mota yana kallon wani waje daban.

Salma ganin Omar sai ta ji farin ciki ya mamaye mata zuciya, kamar itace Nayla Win haka taji daWin zuwansa. AbdulHamid ya kalli Omar ya ce,  Omar mu je ko?. Sai da ya sauke numfashi sannan ya mi™e tsaye sosai ya kalli gidan sannan ta shiga.

Salma ta rufe gidan bayan sun shiga Didi ta ce,  Salma ki yi mana iso zuwa cikin gidan. Salma tayi gaba suka bita a baya ta tarar da Nayla a inda ta barta. Gira ta Waga mata tana yi mata nuni da ™ofa, sai Nayla ta kalli ™ofar ta ga Didi tana yi mata murmushi. Murmushi ta yi sosai ta ce,  Didi sannu da zuwa, tun Wazu nake ta zaman jiran zuwan ki. Didi ta ce,  Sai yanzu Allah ya yi amarya. Omar yana bayan Abdulhamid Hakan ya saka Nayla bata ganshi ba, ta Wago da niyar ta gaishe da AbdulHamid suka haWa ido da shi yana kallon ta.

Gabanta ya yanke ya faWi ta yi saurin janye idanunta ta gyara zama kamar wacce ta zauna a kan wani abu. Gaisawa suka yi da AbdulHamid kafin ya ce,  To amarya ga ango mun kawo miki shi, ayi mana afuwa Ango bai tashi zuwa ba sai bayan kwana biyu da kawo amarya, Ina fatan za a yafe mana?. Nayla dai kanta yana ™asa hakan ya saka Salma ta ce,  Zamu yafe amma sai an biya mu. Didi tayi dariya ta ce,  To Hajiya Salma za a biya indai za a yafe mana Win.

AbdulHamid ya ce,  Omar ga matarka Nayla nan ka ri™eta hannu biyu cikin tausayi da kuma amana, ka bata kulawa fiye da yadda ka ke bWa kanka kulawa. Kai Allah ya Worawa ha™™in kula da ita a yanzu, hatta wani abun da zata gani a waje taji tana ra ayin ta ci ko ta sha kai Allah ya Worawa ka siya mata tunda a ™ar™ashinka take. Don Allah ka kula da ita kar ka bari tayi kukan nisa da gida ko wani abun. Sannan&  Omar ya dakatar dashi ta hanyar cewa,  wai ba ka gama wannan maganar nan tun kafin mu zo ba? Meyasa ka ke maimaitawa kuma? Bana son dawo da abinda aya wuce, a bari kawai ya faWa cikin bada umarni yana wani lumshe idanu.

Didi ta ce,  sake tunasar sa da kai ake yi ai, yadda ake maka nasiha itama za a yi mata. Kallon Didi yayi ta harare shi ya dau™e kai dan shi baya so a maimaita masa abinda aka riga aka faWa masa.

AbdulHamid ya murmusa dan shi har ga Allah Omat burge shi ya ke yi ya ce,  Amarya Nayla, ga mijinki Omar nan ki yi masa biyayya gwargwadon yadda zaki iya. Kar ki kalli ta yadda auren na ku yazo ki kalli bautar auren da zaki yi wacce zata kai ki aljanna. Duk abinda kika yi na saSa masa saboda kina ganin ta yadda ™addarar ta ku tazo Allah sai ya rubuta miki zunubi, aure sunan sa aure indai har an shaida an bada sadaki. Komai zai zama labari in sha Allah, ki ta addu ar Allah ya baku zaman lafiya, Allah kuma ya baki hakurin zama dashi.

Kallon AbdulHamid Omar ya yi jin ya raina masa hankali, shi meyasa ba a ce Allah ya bashi ha™uri zaman da ita ba sai shi ne zai ce Allah ya bata ha™urin zama dashi?. Šaure fuska ya yi tamau kamar zai yi magana sai kuma ya fasa kawai ya mike tsaye. Didi ta kalle shi ta ce,  Ina zaka je? Baka jin ana yi muku nasiha ne?.
 Nasihar mijin ta ki ce na ji da Wan rainin hankali a cikin ta, Allah ya bata ha™urin zama dani ya ce, amma ni bai ce Allah ya bani ha™urin zama da ita ba. Ni ne mai halin banza kenan?.

AbdulHamid ya ce,  Yi ha™uri mutumina, kai ai namiji ne, na san zaka iya yin ha™urin shiyasa ban faWa ba. Ita kuwa mace ce sai an sanar da ita. Yi ha™uri ka zauna. Didi ta jawo hannunsa ta ce,  Zauna don Allah. Bai musa ba ya zauna AbdulHamid ya murmusa ya cigaba da yi musu ta™aitacciyar nasiha.

Ita dai Nayla ba ma jinsu take yi ba, hankalinta yana ga wani wajan daban, amma duk motsin Omar a kan idanunta yake yi, duk abinda ya ce tana ji. Ita kanta dariya ya bata jin abinda ya ce, bata san tayi murmushi ba a ranta tana ayyana mutum sai masifa.

Didi ta ce,  to ka gama faWar duk abinda zance ai, abinda zan ™ara dashi shine Nayla sai kin yi ha™urin da zama da Omar Sai ta kalle shi taga ita yake kallo ta ce,  ka dai na san halinka, nima ha™uri nake yi da kai balle matarka, ka daina kallona sai na faWa. Ta sake kallon Nayla ta ce,  Yana da taurin kai sosai kuma masifaffe ne, sannan yana da hargagin da zai tsorataki lokaci Waya, yana da zafin kai kullum zuciyarsa a sama. Don Allah ina so ki mayar dashi kamar ruwan sanyi, duk wannan zafin kan na sa ya ajjiye ya zama bawan ki. Bai san lokacin da murmushi ya kubbe masa ba jin kalaman Didi, wai ya zama bawanta, shi har yanzu zuciyarsa faWa masa take yi Didi tana da ´ar matsala gaskiya.

Ta kalle shi ta ce,  Omar Nayla bata da matsala ba kamar kai bace, tana da kirki tana da fara a da kuma biyayya. Ta fito daga babban gida wanda ta samu kyakykyawar tarbiyayya ta kuma ta shi cikin nutsuwa. Bana jin Nayla ko kaWan, na san ko ban ce ba ita mace ta gari ce a wajanka, don Allah kaima ka zamar mata miji na gari. Marainiya ce bata da mahaifiya, ga mahaifi ta ma ya yi mata nisa tunda ta bar asalin garin su. Don Allah ka zamar mata uwa da uba, yayanta kuma mijinta. Don Allah Omar kar ka bar Nayla ta zubar da hawaye a zaman ku da ita. Ka bata dukkan kulawar da ka san zaka iya.

Please Login or Register in order to submit comment