Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar duniya Aisha?. Aisha da gaske kin mutu kenan!?" Ya faWa cikin kuka mai nuni da tsantsar ruWanin da zuciyarsa ke ciki. Omar cikin wata irin murya mai Wauke da rauni da sanyi ya ce, "Didi bata mutu ba, ka daina faWar wannan kalmar!."

Kallon Omar ya yi ya ce, "Omar ba a wasa da mutuwa, da gaske Aisha ta bar duniya, da gaske ta mutu!." Nayla jikinta ya fara rawa ta ce, Yaya AbdulHamid yanzu muka gama magana da ita fa, itace ta ri™e min hannu. Kaga....kaga......Kaga.....ruwan da ta shanye, itace ta shanye wannan ta ce min zafi take ji" Nayla ta faWa a rikice tana Waukar robar da Didi ta sha ruwa. AbdulHamid bai iya magana ba saboda kukan da ya ci ™arfinsa sosai kamar mace, ya du™a a wajan tana kuka sosai cikin rashin mafita.

   Omar kam kallon Didi ya yi ya buWe fuskarta yaga idanunta a rufe ya runtse ido ya ce, "Kana neman ka wartsawa min zuciya, Didi bacci take yi ba mutuwa tayi ba. Didi bacci ki ke yi ko? Wai mijinki ya ce kin mutu ni kuma ban yarda ba, likitoci ma ™arya suke yi, ki yi magana su fahimci da ranki, ki tashi dan su tabbatar idanunki biyu Didi!" Ya fada cikin wani irin rauni da mutuwar jiki wanda bai taSa jin irinsa ba a duniya.

Nayla kuwa wani irin bugawa zuciyar take yi, kanta ya yi bala'in sarawa, mararta ta Waure tamau. Didi ta mutu shine abinda take maimaitawa a zuciyarta, ta kalli Marmerh da take zaune tana shan alawar da Omar ya bata, sai kawai Nayla ta zube a wajan a sume jini ya fara fita daga jikinta.

Likitan da yake tsaye a guje ya fita aka kira nurses mata uku aka Wauki Nayla aka fita daga ita daga Wakin cikin gaggawa. Omar dai ya ji faWuwar abu amma bai san meye ba, sannan ya ji kukan Musliha amma bai san daga ina kukan yake zuwa ba, sannan ya ji an kira shi da Daddy bai san a inda ya ji maganar ba. Hannun Didi ya ri™e a kasalance da rauni ya ce, "Didi da gaske ne wai? Kin mutu Win?." Sai kuma ya zabura ya kalli AbdulHamid ya ce, "Zan kaita wani asibitin, ban amince da abinda aka ce a nan ba."

AbdulHamid ya aro nutsuwa da jarumtar ya mi™e tsaye ya goge idanunsa ya dafa Omar ya ce, "Omar mutuwa Waya ce tak a duniya, tunda aka furta ta tabbata ne. Yayarka ta amsa kiran wanda ya halicceta, ka dawo nutsuwarka!."

Omar ya tsayar da ido kawai yana kallon AbdulHamid jin abinda ya ce, wai Yayarsa ta amsa kiran mahaliccinta, jin maganar yake kamar saukar arabu a cikin kansa da zuciyarsa. Jikinsa rawa ya fara yi, ya yi baya kamar zai faWi AbdulHamid ya yi saurin ri™e shi, Omar ya mi™e tsaye sosai ya kalli Didi, ya kalli AbdulHamid, ya kalli Musliha da take kuka a kusa da gawar Didi, ya kalli Marmerh da take gefe tana kallonsa tana kiran sunansa.

"AbdulHamid....!" Ya faWa cikin wata irin murya jikinsa na rawa sosai." AbdulHamid ya ce, "Ta mutu Omar, maganar da muka da ita a Wazu maganar ™arshe ce. Ta mutu!" Ya faWa hawaye na sakko masa.

Wata irin ajiyar zuciya Omar ya yi, ya sake komawa kusa da Didi yana kallon fuskarta, ya Wora hannunsa a goshinta ya ce, "Didi...!" Sai ya kasa ™arasa maganar saboda wani abu da ya taso daga zuciyarsa ya tokare ma™ogwaronsa ya hana maganar fitowa. Kansa ya yi bala'in sarawa amma ya dake ya saka hannunsa a daidai ™ofar hancinta ko zai ji tana numfashi amma bai ji komai ba. A ™irjinta ya kifa kansa yana juya kai ya rasa abinda zai yi, ya kasa banbance a wacce duniyar yake, ya kasa banbance abinda yake ji a cikin zuciyarsa. Kalmar ta mutu shine abinda yake ji a kunnensa cikin murya mai amo.

AbdulHamid ya dafa shi daga baya ya ce, "A Wazu da ta bar gidanka ta dawo gida, ta sanar dani kana ta yi mata gorin rashin kwana a inda ka gina mata. Cikin wasa da dariya ta ce in ta mutu a kaita gidan a shirya....." sai ya kasa faWa saboda kukan da ya taho masa ya fashe da kuka yana rufe fuskarsa da hannayensa.

Marmerh ce ta zo inda yake tana kallonsa sai ta nuna amsa Didi ta ce, "Abba Ummi" ta faWa tana nuna Didi da fuskar ta take a buWe. Ri™e Marmerh ya yi rauni na sake mamaye masa zuciya yana kuka sosai. Likitan da suka fita da Nayla ne ya shigo a nurse ya ce, "Ku yi ha™uri, mun san an taSa ku, yau an saka muku rauni da ciwo a zuciyarku, ku karSi jarabawa ku amince da ™addara. Ku nutsu ku Wauke ta ku kaita gida ku yi mata gatan da ko wanne mamaci yake nema, kuka dole, amma ku jure addu'ar ku ita take da bu™ata a yanzu."

Sai a lokacin Omar ya Wago idanunsa da suka ™an™ance sun koma jajaye, shi so yake ma ya yi kukan amma ya kasa sai wani abu da yake ji na sukar zuciyarsa, ga wani abu mai yaji da ya mamaye masa jiki har idanunsa yake jin yajin. Magana yake so ya yi amma kamar an rufe masa baki ya kasa furta komai. AbdulHamid ya mi™e ya goge ido yana ri™e da Marmerh ya ce, "Haka ne, mun gode sosai, Yanzu zamu tafi da ita."

"Allah ya gafarta mata, ya sa aljanna ce makomarta ya bata ikon amsa tanbayar kabari." Wani hawayen ne ya sakoowa AbdulHamid ya girgiza kai yana amsawa da amin. Likitan ya ce, "akwai patient kun bari, tana kwance a sume har yanzu." Kai ya Waga kawai bai iya cewa komai ba.

Omar ya kalla ya ce, "Ka yi ha™uri Omar, zamu je da ita zuwa gidan ka kamar yadda ta sanar da ni. Bara na kira su Kawu" ya faWa murya na rawa hannunsa na rawa yana laluben waya y Wauko ya fara sanar da ´an uwa.

     Shi dai Omar yana tsaye kawai har lokacin hannunsa na cikin nata ya rasa abinda ya kamata ya yi. Yana tsaye ya zuba mata ido yana kallo yana mamaki wai ta mutu, ya kasa yarda da maganar balle ya amince ta bar duniya. A haka su Kawu da Baba Adamu suka zo cikin tashin hankali da ruWani.

Omar yana ji yana gani aka gama abinda za a gama aka basu gawar Didi. Kawu Mamman ne a gefensa dan ya lura baya cikin hankalinsa duk inda ™afarsa ta kai kawai jefa ta ya ke yi. Baba Adamu kuwa Musliha na hannunsa sai kuka take yi, da™yar aka samu number Mama Sa'adatu aka sanar da ita halin da ake ciki.

Kafin wani lokaci a cikin daren mutuwar ta ratsa ko wanne sashe na dangi, dangin Nayla kowa ya sani duk sun shiga ruWani saboda mutuwar ta zo babu zato babu tsammani. Mama Sa'adatu tana kuka ta wuce asibiti wajan Nayla tunda ance tana can a kwance.

Gidan Omar ya cika da dangi musmanan dangin su Didi da kuma dangin AbdulHamid. Kafin gawar ta isa mutane sun cika gida tunda kowa ya tambaya sai ace a gidan za a yi jana'izarta. Aka shiga da gawarta falon gidan aka kwantar da ita..

Omar dai kallon ikon Allah kawai ya ke yi amma bakinsa ya rufe ruf ya kasa magana sai kallo da ido. Danginsa sai aikin bashi baki suke yi amma sai dai ya kalle su kawai dan ya zama kurma ya kasa cewa komai.

A Daren shi da AbudlHamid ne suka yi mata wanka, yana yi yana le™a fuskarta ko zai ga ta buWe ido amma ko motsa idon nata baya yi balle ta buWe. Ya taSa zuciyarta wai ko zai ji tana bugawa ya ji shiru babu abinda yake motsi a jikinta. A haka suka shirya Didi, ™arfin shiryata Win ma AbdulHamid ne Kawu Mamman da yake ta ya su.

Aka gama shirya ta ya zauna a gefen ta ya zuba mata ido kawai yana kallonta cikin farin kaya tana kwance a mi™e samSal. Ko motsa ido baya yi a kanta, sai Kawu ya taSa shi sannan ya yi ajiyar zuciya. Kawu ya ce, "Ka maimaita Innalillahi wa'inna ilahir raji'un a zuciyarka."

Ya bi kawu da ido kafin ya Wauke idon ya sake kallon Didi. A haka Omar ya kwana cir a kusa da ita, tunda ya zauna a wajan sallar asuba ce kawai ta saka shi ya motsa, shima sai da suka mi™ar dashi ya tafi zai kifa suka ri™e shi yana dafe kai sannan ya iya yin alwala ya yi sallah. Yana idarwa ya dawo ya buWe fuskarta wai ko zai ga ta farka amma bai ga alamun ta motsa ba, ya shafa fuskarta ya koma ya jingina da kujera tare da lumshe idanunsa.KRB3P114

Mutuwar ta ratsa ko ina, social media ta cika da hoton Omar da Didi da sauka Wauka a madina, wanda ya dafata tana gefensa sanye da abaya ta yi dariya. Jidda ce ta fara Wora hoton a status, kafin ka ce kwabo ya zaga inda ba a yi tunanin zai zaga ba. Duk inda ka bi zaka ganshi an rubuta Allah ya yiwa Yayar Omar Usman, C.E.O Exclusive Footwear by Tiger rasuwa, Za a yi jana'izar ta ™arfe tara na safe a gidansa.

Gida ya cika dam da mutane da ba a san su ba ma, mutanen Kaduna duk sun zo kowa ka kalla zai kaga fuska tayi ja alamun an sha kuka.

Har karfe takwas da rabi Omar yana zaune a gaban gawar, yana kallo wannan ya shigo ya yi mata addu'a ya fita shi dai bai motsa ba kuma bai ce komai ba har lokacin. Tausayi yake bawa kowa, iya kallon yanayin da yake ciki ma kuka yake saka mutane saboda kowa ya san wacece ita a wajansa, an san matsayi da girma da take dashi a gare shi. Kowa ya san Omar aka yiwa mutuwa shiyasa ake matu™ar tausayinsa musamman rashin maganar da baya yi.

A haukace Nayla ta faWo falon jikinta na wani irin rawa kayan jikinta sun Saci da bushshen jini, ta rame lokaci Waya ta koma kamar zararriya. A gaban gawar ta zube guiwa biyu hannu na karkarwa ta buWe fuskar Didi sai ta fashe da kuka. A hankali ta ce, "Didi bata mutu ba, bacci ta ce min zata yi, bacci ta ce min zata yi fa. Ku saka ta farka bata mutu ba, hannuna ta ri™e ta ce min Nayla bacci nake ji, bacci take yi ba mutuwa tayi ba" ta faWa tana kallon mutanen falon wanda duk ´an uwan Didin ne harda Hajja a zaune tana kuka.

Nayla ta mi™e a firgice ta Wauko iv da Didi ta kawo a ajjiye akan table hannu na rawa ta ce, "kun gani, jiya ta kawo da kanta ko awa ashirin da huWu ba ayi da zuwan ta ba. Kun gani, a nan..a nan......ta zauna muna hira, A nan ta zauna...wallahi a nan ta zauna." Ta faWa murya na rawa matu™a haka jikinta ma rawa yake yi.

Kuka ta saka mutanen falon Mama Sa'adatu da take biyw da ita ta ce, "Nayla ki nutsu, ki nutsu don Allah" ta faWa tana kuka tana ™o™arin ri™ota. Fizge jikinta tayi ta zube a gaban Omar ta saka hannu biyu ta jijjiga kafaWunsa ta ce, "ka faWa musu bata mutu ba, Didi bata mutu ba, bacci ta ce zata yi fa, daga fitarka kai da Yaya AbdulHamid ta ce na bata ruwa zafi take ji, daga nan ta ce min Nayla bacci zan yi. Wallahi Didi bata mutu ba, ka faWa musu ni na faWa sun ™i yarda dani......" ta faWa tana kuka sosai.

Omar kallon ta kawai yake yi bayan wannan babu abinda ya iya aikatawa, ya dubawa Nayla ido kawai kafin ya lumshe idon ya buWe yana ji ina ma shine ya samu damar da ta samu na zubar da hawaye, da ya fi kowa farin ciki dan nauyin da zuciyarsa take yi masa ya san tabbas zai ragu.

Hajja ta kalli Mama Sa'adatu cikin kuka ta ce, "Sa'adatu ki Wauke Hauwa'u daga wajan nan." Mama ta taka zuwa inda Nayla take ta mi™ar da ita tsaye ta ce, "ki yi ha™uri Nayla, kowa lokaci yake jira, nata lokacin ya yi yanzu." Ta kalli Mama ta ce, "Lokacin ta bai yi ba, ba fa mutuwa tayi ba bacci take yi wallahi. Ni fa ta cewa na bata ruwa, na bata ruwa ta ce min zata yi bacci, ya zaku dinga cewa min ta mutu bayan bacci ta yi? Ku daina faWa bana so" ta faWa tana janye jikinta daga na Mama ta sake komawa inda Didi take kwance.

"Didi! Didi!! Didi!!" Ta faWa sau uku sai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin gawar cikin fitar hayyaci. Mama Sa'adatu da Maman Nayla ta Kaduna suka ri™o Nayla suna bata h™kuri cikin tsananin tausayi.

A lokacin karfe tara na safe ya buga, Kawu ya mi™e ya ce, "Lokaci ya yi, mutane suna jira a Wauko ta, Omar tashi mu je!" Ya faWa yana ri™o Omar. Omar ya mi™e tsaye yana bin wanda suka shigo da makara da kallo. A akan idonsa aka saka Didi a makara aka fita da ita daga falon.

"Didi!" Nayla ta faWa cikin jan numfashi kafin ta yi baya ta zube a kan carpet, mutanen falon aka yi kanta gabaWa amma Nayla ko numfashi bata yi.

A kan idon Omar ta zube amma sai ya rasa gane me hakan yake nufi, Kawu ya ja hannunsa suka fita. Sai da ya kare fuska da hannunsa
saboda hasken da ya gani, ga mutane kowa shi yake kallo shi dai kallon su kawai yake yi. A nan aka yi sallah aka wuce zuwa ma™abarta.

Nayla kuwa asibiti aka koma da ita daman gudowa tayi babu wanda ya sani, aka jona mata ruwa da taimakon gaggawa dan numfashinta ya tsaya cak ga rashin jini da babu a jikinta dan ta zubar da jini sosai.

A cikin gidan aka zauna ana karSar gaisuwa, AbudlHamid ya yi namijin ™o™arin jurewa yana ta karSar gaisuwa, Omar dai yana zaune da kayan jiya a jikinsa. Ya san dai in aka mi™o masa hannu yana bada hannu a gaisa bayan nan babu abinda yake iya yi yana dai zaune kamar mara hankali.

Har rana ta fito sosai baya iya cewa komai, a lokacin Baba Adamu ya taso ya kamo hannunsa bai musu ba ya mi™e tsaye zuwa wajan da babu mutane sosai, ba jimawa sai ga Mama Zainab a wajan ya kalle ta ya ce, "Yaron nan yana cikin wani yanayi, yana bu™atar ya ci abinci Zainab."

Mama Zainab ta kalli Omar da jajayen idanunta ta ce, "Sannu Omar." Bai iya tanka mata a hankali ta ce, "Matarsa ma na asibiti a kwance, kasan yanayin da ake ciki" ta faWa murya na rawa sosai. Baba ya ce, "Dole ayi wani abun, shima ko a kai shi asibitin kawai."

Omar gajiya ya yi da tsarguwa ya cire hannunsa daga na Baba yana takawa a hankali zuwa inda zai bi ya hau samansa ya hau saman bai sake kallon kowa ba. Da ya hau saman ma tunani ne yake neman tarwatsa masa zuciyarsa, ga zafin da yake ji a zuciyarsa da fatar jikinsa har tiriri yake ji yana tasowa yana mamaye masa zuciya. Jin zafin ya dame shi ya saka shi shiga banWaki ya kunna ruwan sanyi ya tsaya ruwan na sauka a jikinsa ba tare da ya cire kayan ba.

Waje Waya yake kallo a banWakin, duk inda ya kalla babu abinda yake gani sai fuskar Didi tana murmushi. Ko ya ji sautin muryar tana kiran sunansa bayan nan babu abinda yake iya ganewa. Kamar zautacce haka ya koma, ya fito ba tare da ya cire kayan ba ya zauna yana rawar sanyi saboda sanyin ya yi masa yawa amma baya so ya cire.

Bai san lokacin da ya Wauka a haka ba ya dai ji ana buga ™ofar Wakin bai iya motsawa ba a lokacin aka buWe aka shigo. Baba Adamu ne da Mama Zainab suka shigo Wakin da sallama, ya kalle su bai ce komai ba kuma bai motsa ba. Baba Adamu ya ce, "Subahanallah, Omar me ya same ka haka?." Bai ce komai ba yana dai zaune sai ya dafe kai da hannayensa saboda ciwon da suke yi masa kamar zasu tsage.

Mama Zainab kasa ri™e kuka tayi ta fita tana kuka sosai, ba jimawa Baba ya fito yana yi mata faWa akan zata sake tayar masa da hankali in tana kuka a gabansa. A lokacin ya fito ya saka jallabiyya fara mai gajeren hannu suka sauka tare saboda nema sa da ake yi in an zo.

    Haka aka kwana uku Omar baya cikin hankalinsa, abun kullum sake gaba yake yi dan baya magana, in an yiwa Didi addu'a dai yana iya motsa bakinsa ya ce amin amma tun a asibiti ba a sake jin muryarsa ba. Zaman makoki ake yi mai capacity, kowa a danginsu Omar bada gudunmawa yake yi na abinci da abin sha. Mutane zuwa kawai suke yi wasu ba a san su ba kawai suna shigowa ne.

Nayla har lokacin tana asibiti ta farfaWo amma ta kasa nutsuwa, jininta ya hau ga kukan da yake yi kullum. Jidda da Salma ne a wajan ta in Mama bata nan, Musliha na wajan su suna ta rarrashi amma bata iya dainawa har sai an yi mata allurar bacci. A ranar kwana na ukun ne ta Wan samu nutsuwa, kukan ya ragu sai ciwon kai da yake damunta. In ta rufe ido ta tuna Didi ta mutu sai ta ji zuciyarta ta buga ta sake gigicewa.

    A ranar kwana na huWu suka dawo gida, tana shiga falon gabanta ya faWi ta tuna inda Didi ta zauna ranar da zata mutu sai kuka ya sake cin ™arfinta. Abiy da kansa ya yi mata nasiha yana bata ha™uri amma ta kasa daina kukan jikinta ya zama wani iri ta koma kamar ba ita ba. Bayan ta zauna ta Wan nutsu Musliha tana hannunta Marmerh ta shigo da gudu ta faWa jikinta ta ce, "Mummy ina Ummi?." Nayla ta zubawa Marmerh ido hawaye suka sakko daga idanunta.

Umma Saroot ta ce, "Nayla ki yi ha™uri, wannan damuwar da kika saka a ranki ciwo zasu saka miki, wanda ya bar duniya ya mutu bazai dawo ba, ita ta dace tunda ta samu yabo da kyakykyawar shaida, na tabbatar mala'iku sun Wauki abinda mutane suke cewa da shi zasu yi amfani. Addu'a ya kamata ki dinga yi mata kin ji?." Ta ri™e Marmerh a jikinta ta kalli Umma ta ce, "Umma bacci ta ce min fa zata yi, hannunta yana cikin wannan hannun nawa" ta faWa tana kallon hannunta.

Umma Saroot ta ce, "na sani Nayla, amma ikon Allah ai ya fi gaban wasa. In lokacin mutum ya yi baya ™ara ko second Waya a duniya yake mutuwa, lokacinta ya yi a lokacin da ta ce miki bacci zata yi."

"Meyasa zata mutu yanzu? Meyasa?."
"Haba Nayla me ki ke faWa haka? Kar hankali ya gushe ki yi saSo fa." Hawaye suka sake sakko mata, Marmerh tana jikinta har lokacin ta kasa sakinta. Hajja ta ce, "Hauwa ki tashi ki je ki duba Omar, an ce ya hau sama tun Wazu bai sakko ba." Umma Saroot ta ri™e Marmerh, Nayla ta mi™e a sanyaye ta hau saman memories Win Didi na dawo mata tana kuka.

Halin da ta tarar da Omar a ciki ya saka ta sake gigicewa, domin kuwa yana kwance shima kamar yadda Didi take. Ta ™arasa inda yake a gigice tana jijjiga shi da iya ™arfin da ya rage mata amma baya motsi kamar yadda Didi bata motsi. Ido ta wara tana girgiza kai kafin ta kwasa a guje ta tana haWa steps zata kifa ta sakko tana hakki ta ce, "Shima baya motsi, shima baya numfashi irin Didi, shima yana kwance, baya motsi." A firgice take maganar hakan ya saka hankalin mutanen wajan ya tashi sosai.

      Nayla ta sulale ta zauna a wajan tana sake maimaita abinda ta faWa, tana ganin su Umma sun hau saman da sauri ita dai ta kasa motsi. Tana gani su Baba Adamu da AbudlHamid suka hau saman, ba jimawa sai su Kawu da cousins Win Omar an hau sama gabaWaya. Šauko Omar aka yi cak aka fita dashi ta ™ofar da zata fitar da kai compound Win gidan ba tare da an shiga ta falo ba aka wuce asibiti.P115

KarSar gaggawa aka yi masa, aka shiga ceto ransa domin yana cikin mayuwancin yanayi. Sun jima a kan Omar kafin a samu a daidaita komai likitan ya fito repection inda suke zaune ya ga dukkansu kallon sa suke yi alamun ™arin bayani. Dr ya ce, "Akwai abinda yake damunsa ne? Ina nufin abinda ya jefa shi a cikin wannan yanayin. AbdulHamid ya ce, "™warai akwai, Yayarsa Allah ya yiwa rasuwa."

"Allah sarki, Allah ya gafarta mata." Aka amsa da amin likitan ya ce, "gaskiya jininsa ya hau sosai, sannan akwai yunwa a tare dashi wacce ta taimaka wajan sakin jikinsa da galabaitar dashi. A yadda na fahimta akwai rashin bacci, shima ya taimaka wajan hawan da jininsa ya yi."

Baba Adamu ya ce, "Yanzu ya jikin nasa?."

"Numfashinsa ya dawo daidai a yanzu, an saka masa ruwan da zai daidaita blood pressure Winsa. Sannan an yi masa allurar bacci wacce zata saka shi bacci na dogon lokaci, mun yi isolating Winsa a special room wanda ba a hayaniya wajan saboda ana bu™atar ya yi bacci ™wa™walwarsa ta dawo daidai. Sannan an saka masa nasogastric tube (NG tube), wacce za a dinga bashi abu mai ruwa ta cikinta yana zuwa har cikinsa, kamar tea ko kunu da sauransu. Yunwar da take damunsa ta wuce drip ya yi masa magani gaskiya. So za a samu mutum Waya da zai dinga shiga yana bashi abincin amma ban da hayaniya, in bai samu baccin da ake so ba zai iya samu taSin ™wa™walwa."

A tare kowa ya yi ajiyar zuciya likitan ya ce, "kar ku damu, da ya tashi daga baccin in sha Allah za a samu canji sosai." A tare suka haWa baki suka ce, "Allah ya sa."

   Tsakanin dangin Baba da dangin Maman su Omar har rige-rigen kula da Omar ake yi, kowa ya ce shi zai zauna saboda halin da Nayla take ciki itama bazata iya kula dashi ba. Da™yar aka bar autan su Kawu a asibitin duk suka koma gida saboda masu zuwa gaisuwa.

Nayla ma tana gida su Mama sun sakata a gaba tana cin dafaffiyar hanta wacce aka dafata da alaihayu, da™yar take iya kaiwa bakinta ta tauna, da tunanin Didi ya faWo mata sai aga hawaye yana zuba daga idonta. Marmerh da take gefe tana bacci ta kalla ta shafa kanta tana kuka ta goge ido tana cigaba da ci a hankali.

    Salma ta dafata ta ce, "Nayla don Allah ki daina kuka, addu'a take bu™ata yanzu." Nayla ta kalle ta ta ce, "Salma hannuna yana cikin nata, ashe ta mutu ban sani ba. Ta juyo ta ce min nima fa ina son Omar ba ke kaWai ke sonsa ba, sai ta yi murmushi ta yi dogon salati ta rufe ido. Ni gani nake kamar ba mutuwa tayi ba suka je suka binne ta."

Jidda ta ce, "Haba Nayla, ki daina furta wannan maganar mana, Ana wasa da mutuwa ne? Lokacin ta ya yi wannan maganar itace ta ™arshe da zata yi miki. Don Allah ki kwantar da hankalinki, sai kin nutsu zaki iya kula da mijinki, shima yana asibiti."

Ta kalli Jidda da take maganar zata yi magana Mummynsu Salma ta ce, "Don Allah Nayla ki nutsu, rashin nutsuwar da baki da ita ne ya saka ki ke a nan da kina tare da mijinki. Yana can a kwance, in baki nutsu ba ta ya shi zai nutsu?."

Hawaye ya zubowa Nayla ta ce, "To Mummy, in na tuna da Didi ne sai zuciyata ta karye."
"Ha™uri zaki yi, an san zaki ji zafi a zuciyarki amma daurewa ake yi, addu'a take da bu™ata ba wannan koke-koken ba." Nayla ta goge ido ta kalli Marmerh da ta tashi daga bacci ta ce, "Mummy Ummi." Nayla ta ri™eta

Please Login or Register in order to submit comment