Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana shan wahala a hannunsa wani lokacin ne oho.

Ganin yana kallon ta sai ta ce, "Didi zan faWawa." Bai hanata ba ta kira Didi ta faWa mata komai. Didi ta dinga murna tana addu'a Nayla na biye mata. Shi kan ya rasa gane wacece tafi wata farin ciki a cikinsu, Nayla ko Didi?.

Bayan ta gama murnar ta zauna ya kalle ta ya ce, "Jidda!." Ta kalle shi jin da yadda ya kira sunanta ta san serious abu ne, ta ce, "Na'am."
Ya kafa mata idanu ya ce, "Meyasa yanzu bakya so na taSaki?." Ta sunkuyar da kai a hankali ganin yana kallonta, gabaWaya sai muryar ta gushe akan fusksrta. A sanyaye ta ce, "yaushe na ce bana so?." Ya Wan taSe baki ya ce, "Sai kin faWa min zan fahimci hakan?." Ta kalle shi zata yi magana ya ce, "yanzu ma gashi kin bar jikina ina fara taSa ki, bayan da ba haka ki ke ba, akwai abinda ya canja ne? Akwai abinda nake gaza yi miki ne yanzu?."

Nayla ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, "A'a."
"To Meyasa?." Ta Wan yi shiru cikin rashin sanin amsar da zata bashi ta ce, "Babu komai, ka yi ha™uri bazan sake ba." Ya Waga kai ya ce, "Na yi ha™urin, amma in da damuwa ki faWa min kar ki cuci kanki." Ta girgiza kai ta ce, "Babu komai."
"Okay" ya faWa yana tashi yana shiryawa.

Ita kanta abin na damunta sosai, gashi tana tsananin kewar mijinta amma da ya fara taSata sai taji kamar za a rabata da numfashinta, komai ya tsaya mata cak har sai ta bar kusa dashi take jin daWi.

Shima a nasa Sangaren tunanin da yake yi kenan, me ya gaza mata har take gudunsa haka? Me yake yi mata wanda bata so da zarar ya taSa ta sai ta zabura kamar wacce wutar lantarki ja ta?. Raini ne ko kuma son da yake nuna mata ne ya jawo raini? Ko kuma dan ta ga yana bu™atarta a kai a kai shiyasa hakan? Jan aji ne ko wula™anci?. Juyowa ya yi ya kalle ta ya ga jikinta ya yi sanyi bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi.KRB3P082
Nana haleemaa

       Ranar alhamis da daddare faWa suka yi da ita kaca-kaca, ya yi fushi ya ™yaleta dan yana ganin kawai raina masa hankali take yi da wannan sabon salon da ta Wauko, yana kuma ganin nuna mata da yake yi yana bu™atarta shiyasa take yi masa haka, wata™ila jan aji ne ko wani abun a wajanta. Dan bazai manta ba, a cikin mazan da suka zauna a China ya ji Waya daga cikinsu na maganar, yana cewa mata in suka ga ana nuna ana bu™atarsu ana jin daWin tarayya dasu wasu suna rainawa mijin hankali, su dinga jan aji har wasu su ce sai an biya su.

     A lokacin bai Wauki abin da mahimmaci ba, kuma bai saka musu baki ba dan ba sabawa ya yi dasu ba, amma a yanzu ya ji a ransa tabbas dan yana sonta yana bu™atarta ya saka take yi masa haka. Ya san baza ta yi haka dan kuWi ba sai dai jan ajin, kuma zai nuna mata shi Wan halak ne, bazai sake sauraronta a wannan Sangare ba.

Nayla haka ta kwana duk ta damu, tayi kuka har ta gaji amma ta kasa gane abinda yake damunta. Tana ji a ranta tana so ta samu na gaba da ita ta faWa masa ko taje asibiti, yanayin yana cutar da ita kuma yana cutar da mijinta.

    Da safe juma'a bai nuna mata yana fushi da ita ba, dan a wajansa komai Sangarensa daban, dan tana nuna masa wani hali a wancan Sangaren bazai shafi wani Sangaren na zamansu ba. Tare suka ci abinci har ya shirya ya tafi masallaci, bai jima baya dawo ya kalle ta ya ce, "Zo ki zaSar min kayan da zan saka."

Tare suka je ta Wauko masa sabuwar suit Win da ya siyo, ya kalle ta ya ce, "ta yi? ni da kayan hausawa zan saka." Ta Waga amsa gira duk da nauyinsa take ji sosai, ta ce, "tana yi maka kyau, ka saka ta". Bai musa ba ya mi™a hannu zai karSa, ™in bashi tayi tana warwarewa alamun ita zata shirya shi.

Bai hanata ba, ta shirya shi ta fesa masa turare, ya Wauki comb zai gyara gashin kansa ta karSa zata fara gyara masa ya zare shi daga hannunta ya ce, "ki barshi, zan yi da kaina." Sak Nayla tayi, jikinta ya sake yin sanyi dan ta san fushin jiya ne ya jawo haka, ta koma ta tsaya ya gama abinda yake yi ya kalle ta ya ce, "na yi kyau?." Murmushi ta yi ta ce, "ka yi kyau sosai." Murmushi ya yi kawai ta bi shi da kallo, in ba dan yana fushi da ita ba babu abinda zai hana bai rungumeta ba.

Cikin rauni ta ce, "Ka yi ha™uri Rouhii, wallahi....." dakatar da ita ya yi ta hanyar Waga mata hannu, ya Wan daure fuska ya ce, "na ce miki kin yi min laifi ne?." Ta ce, "A'a."
"To meye na bada ha™urin?."

Shiru ta yi bata ce komai ba. Share batun ya yi yana gyara maSallan rigarsa ya ce, "da wanne yare zan yi magana? Ni ba turanci nake ji ba, ba kuma yaren China nake ji ba." Sai ya bata dariya ta ce, "ka yi magana da yaren ka, suma ai da yaren su suke magana. In ban da nigeria ma ai ko wacce ™asar da ta cigaba da yaren su suke amfani." Murmushi ya yi ya ce, "ki kasance active, kin san kece transilator Wina."

Murmushi ta yi ta ce, "An gama."
"Zan tafi" ya faWa yana kallon ta. Tare suka fito harabar gidan, da yake motar tana ™ofar gida sai ya kalle ta ya ce, "ki koma, ki ta yi min addu'a."
"In sha Allah Rouhii, sai ka dawo." Fita ya yi ba tare da ya ri™e koda hannunta ba. Nayla ta fara hawaye dan ta san fushi yake yi da ita shiyasa tun daren jiya bai sake kai hannunsa jikinta ba.

      Jiri ne yake Waukarta ta koma falo ta zauna tana jin kanta na juyawa sosai. Ta yi shiru tana tunanin mafita, kunya take ji ta tambayi Mama Sa'adatu ko Mamanta ta Kaduna, dan maganar akwai nauyi sosai, ta ya ya zata iya ce musu da zarar mijinta ya fara taSata da niyar aikata wani abun sai ta ji kamar zata mutu? Ta ya zata iya faWa musu wannan maganar?. Ajiyar zuciya tayi dan bazata iya ba gwara ma ta je ta ga likita kawai.

Bayan ta tafi da jimawa ya kirata a waya, tana Wauka ya ce, "Jidda wa ki ka sani lawyer a nan Kano?." Nayla ta ce, "Yaya Muhammad, Wan Daddy ne."
"Tura min number sa yanzu, da gagggawa." Da to ta amsa ta kashe wayar ta tura masa number ta yi shiru tana jiran tsammani.

     Daga nan bai sake yi mata waya ba har bayan magriba kuma bai dawo ba. Duk ta damu tana kiransa amma bai Wauka ba, so take ya dawo kawai ta ji ya aka ™are. Tana wannan tunanin ya shigo gidan da sallama, abin mamaki shida Yaya Mahmmad Win ne wanda take k1ira da Yaya Babba, kaf jikokin Hajja shine babba shiyasa suke ce masa Yaya Babba.

Da mamaki ta ce, "Yaya Babba! Yau kai ne a a nan?." Yayi murmushi ya ce, "dole ki ganni a nan, na zo na taya ki murna." Kallon sa tayi ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, "me ya faru?."
"Zaki ji daga bakin mijinki, Ni dai ina tayaki murna Allah ya sanya alkhairi." Ya kalli Omar ya ce, "Omar zan wuce." Tare suka sake fita da Omar suka barta a wajan, duk ta ruWe tana jira ya dawo. Ba jimawa ya dawo, ta matso inda yake amma sai ya yi baya yana kallonta, bata damu ba ta ce, "Rouhi me ya faru? Ka faWa min don Allah."

Takardar da take aljihunsa ya mi™a mata,
hannu yana rawa ta buWe tana karantawa. Baki ta rufe da hannunta tana sake wara ido a takardar kafin ya ga ta zube ta yi sujjada a wajan ta Wago zata shiga jikinsa ya Wan kauce ya ce, "baki ce Alhamdu lillah ba!."

Jikinta ya yi sanyi ganin ko taSa shi ya™i bata damar yi. Abin ya yi mata yawa ga damuwa ga farin ciki, haka ta daure ta ce, "Na faWa da na yi sujjadar godiya ga Allah. YaMar contract na aiki da company ka suka nema har na shekara Waya fa, ai dole na ce Alhamdu lillah."

Murmushi ya yi yana girgiza kai ya ce, "Kamar wasa ba, wai Omar ne zai yi aiki da babban company na ™asar China. Sun ga products Win mu ya yi musu suna so a dinga fita dashi zuwa ™asar su. Ni ban san abinda zai faru ba kenan, kin san komai na su mai ™a'ida ne shiyasa na tambaye ki lawyer. Sai da Yayanki ya je aka saka hannu aka jima ana ta cike-cike sannan komai ya kammala."

Nayla hawayen farin ciki ya sakko mata ta ce, "Allah mun gode maka, Allah ka cigaba da saka mana albarka a duk abinda muka saka a gaba."
"Amin Ashiq!." Wayarta ce ta fara ™ara ta duba ta ga sunan Salma ta Wauka Salma ta ce, "Ke Nayla kinga yadda hotunan mijinki da ´an China suke trending? Wai ashe contract ya samu da su shine ko labari?." Nayla ta ce, "Salma yanzu abin ya faru, dawowarsa gida kenan."

Salma ta ce, "Maza ki duba wayarki zaki ga abin mamaki." Katse kiran Salma ta yi tana shiga instagram da abinda ta fara karo kenan. Ta karanta caption Win a bayyane tana cewa, "Mutum na farko Wan africa, Wan nigeria, bahaushe ya saka hannu a yarjejeniya tsakaninsa da ™asar China. Sun ™ulla yarjejiya akan zasu dinga karSar products Winsa suna kaiwa ™asar China." Kallonsa ta yi ta ce, "Rouhii kaine mutum na farko a kaf africa da aka taSa bawa wannan damar, kaine na farko fa Rouhii, kaine na farko."

     Gangar jikinsa bu™atarta jinta a jikinsa take yi, rungumeta yake so ya yi tsam-tsam tayi kukan a ™irjinsa amma baya son aikata hakan dan ™arshe shine zai kwana a ciki. Ya dake bai nuna mata ba ya ce, "Sun faWa Jidda, da ni suka fara signing wannan contract Win a kaf Africa. Fatana Allah yasa mu fita kunyarsu."

˜arar shigowar message ya ji, ya kalli wayar ya ga kuWin da aka turo masa a acc ya haskawa Nayla wayar ya ce, "alert Winsu ya shigo." Kalla ta yi ganin yawan kuWin ta wara idanu ta ce, "Numbers Win sun rikice min, nawa ne?." Dariya ya yi ya ce, "ke da kike ´ar boko ma kenan, balle ni."

"Didi ta sani?."
"Yanzu zan faWa mata."
"Mu je gidan tare kawai." Zai yi magana sai ga kiran Didin yana shigowa, ya yi murmushi yana Wauka ta ce, "Omar zo ka buWa mana ga mu mun zo." Murmushi ya yi ya ajjiye wayar ya kalle ta ya ce, "ki saka hijjab." Ba musu ta tashi ta Wauko shi kuma ya fita. Didi tana shigowa ta rungume Nayla, itama kuka take yi sai ta saka Nayla kuka.

Omar gaisawa suke yi da AbdulHamid yana yi masa murna kafin ya karSi Marmerh da take hannunsa. Sun saba da yarinyar sosai, ta fara dariya shi kuma yana yi mata wasa cikin ™aunarta. Nayla daman kuka biyu take yi, ga na damuwa ga na farin ciki, Didi ta Wagota daga jikinta Nayla ta ce, "Nayla ina ta ya ki murna, Allah ya taya ri™o ya tabbatar da alkhairi." Nayla ta ce, "Amin Didi, nima ina taya ki murna, Allah ya sa silar nasarar kenan." Ta yi murmushi ta ce, "Amin."

Ta kalli Omar ta ce, "Ina ta jiran wayarka shiru, sai yanzu YallaSai yake nuna min hotunan ka da ´an China a waya, ga takarda an saka hannu. Allah ya cigaba da dafa maka Omar, Allah ya cigaba da shiga lamarinka Omar." Murmushi ya yi ya ce, "Amin Didi, Duk kin ruWe, ki zauna don Allah." Didi ta ce, "ba dole na ruWe ba Omar" ta faWa tana zama akan kujera shima ya zauna da Marmerh a hannunsa.

Didi ta kalle shi ta ce, "Yanzu sai me..." kafin ta ™arasa aka kirata a waya, ta duba ta ga Mama Zainab ce ta yi murmushi ta ce, "´an uwa sai kira na suke yi a waya, iya wannan ma abin alfahari ne." Šauka tayi tana amsawa, itama Nayla Abiy ne ya kira ta yana kashewa ya kira Omar. Omar da ya Wauka murna dai Abiy yake taya shi daga nan ya kashe sai ga Yayan Nayla ma ya kira shi.

      Zaman falon gabaWaya amsa waya yake yi shida Nayla, sai da akayi kiran sallah sannan suka fita shida AbdulHamid aka bar su Didi. Kafin su dawo Nayla ta kawo abinci, Omar yana zama Didi ta ce, "yanzu sai meye abu na gaba?." Omar ya ce, "Sai zuwa gobe zan san abinda za a yi." Didi da fara'a da alfahari ta ce, "Allah ya kaimu." Ya amsa da amin daga nan bai sake cewa komai ba, Marmerh tana hannunsa ta yi luf a jikinsa har ta yi bacci.

      Nayla da ta dawo daga rakasu Didi zama tayi suna waya da Jidda tana faWa ta shiga comments section taga ´an matan da suke son mijinta. Bata bi ta kan maganar ´an comments section ba hoton ta tsaya tana kallon, yana tsaye a tsakiyar ´an China, su biyu suna gefensa kowa ya ri™e takardar aka yi hoton. Ya yi matu™ar kyau sosai, in ka kalle shi sai ka sake kallo saboda yadda ya yi kyau kamar ba shi bq. Ajiyar zuciya ta yi ta tashi ta shiga Waki.

Kaya ta canja zuwa na bacci ta shiga Wakinsa ta same shi a zaune yana duba waya ta shiga ta zauna ya kalle ta amma bai ce komai ba. Nayla ta ce, "YaMar!." Kallon ta ya yi bai ce komai ba ta ce, "ka yi ha™uri."
"Laifin me ki ka yi?" Ya faWa ba tare da ya kalle ta ba. Kafin ta yi magana ya ce, "kinga lokacin farin ciki ne yanzu, ki adana damuwar nan taki mu fuskanci abinda yake gaban mu."

Nayla ta ce, "amma fushi ka ke yi dani."
"Ni ba fushi nake yi dake ba. Mun yi magana da Didi tace ya kamata ayi sadaka da saukar alkur'ani, dan haka zata yi abinci za a yi sadaka, sannan akwai wannan malamin da na baki labari, na samu Wansa na ce ayi saukar alkur'ani sannan na bada kuWi na ce ayi sadaka. ˜auyensu Bash inda ´an uwansa suke suna da bu™atar ruwa sosai, shima na tura kuWin yanzu za a yi musu ruwa guda biyu. Šaya da niyar Allah ya ji™an iyayenmu nida ke, Waya kuma sadaka akan abinda ya faru da wanda ma zai faru gaba."

Nayla ta girgiza kai cikin gamsuwa ta ce, "Hakan ya yi, Allah ya amsa mana ya ji™an iyayen mu."
"Amin. Sai me ki ke ganin za a yi? Na san baza ki iya aiki mai yawa ba shiyasa nace Didi abincin."
"Duk Waya ne."
"Me ki ke ganin ya kamata bayan wannan?."

Nayla ta ce, "Ai duk abinda ya kamata Win ka yi, amma akwai asibitin nan na cikin gari mun taSa zuwa da Hajja wani lokaci da nazo Kano, akwai masu bu™ata sosai, sai ka ga mutum yazo ga rashin lafiya amma babu kuWin magani."

Omar ya ce, "to me ki ke ganin za a yi?."
"Mu shiga gobe da daddare, duk mara lafiyan da yake ciki mu basu sadaka, wani ko kuWin abinci ba shi dashi. Ko mutum biyar aka taimakawa mun gode Allah." Omar ya girgiza kai ya ce, "Allah ya kaimu goben."

"Amin ya Allah. Shiyasa ka ke cigaba a rayuwar ka, duk abinda ka samu ka farantawa wani da abin da ka samu wallahi Allah bazai barka ba, sai ya ninka maka ninkin abinda ka samu. Allah ya dafa maka Rouhii."

"Amin Ashiq!. Na tashi da yin sadaka gaskiya, ban sani ba a jinina abin yake ko kuma dan Didi ce ta raine ni ban sani ba. Didi akwai ta da taimako, ta yarda ta rasa inda wani zai samu, ko kuWinta kenan tana iya yin kyautarsa ta ce Allah zai bata wani, shiyasa nima na buWe ido da yi. Kuma Malamina marigayi Malam Salahudeen a duk sanda na je wajansa yana faWa, duk abinda na samu kar naci ni kaWai na kyautatawa na kusa dani, kuma na bawa wanda bashi dashi. Tun bana Waukar nasihar saboda yadda nake a lokacin har ta shiga jikina. Yanzu ina ganin amfaninta sosai, kuma zan iya cewa itace silar nasarata a rayuwa."

Nayla ta ce, "Gaskiya ne, Allah ya cigaba da bamu ikon taimakawa wanda bashi dashi." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Amin ya rabbi. Mutanen Kaduna sun yi min waya suna ta taya ni murna" ya faWa yana kallon ta da murmushi. Ta yi murmushi ta ce, "Abin murnar ne ya samu, dan ma ´an mata suna ta tanka min kai, ni kam ina ta faWa tabarakallahu asanul khaliqin!."

   Šan girgiza kai ya yi ya ce, "kin kyauta." Ganin yadda ya amsa mata kawai ta san ba a ´an kirkin yake ba. Ya mi™e tsaye ya ce, "Bacci zan yi." Nayla ta ce, "nima haka." Tare suka kwanta amma hannunsa bai zo inda Nayla take ba, zuciyarta na son kasancewa dashi amma gangar jikinta bata so. Da kanta ta matso jikinsa ta kwanta bai hanata ba ya ™yale ta dan bazai neme ta ba sai dai ta neme shi.

       Labari ya baza duniya, ana ta cecekuce ana ta yiwa Omar fatan alkhairi da nasarar da ya samu. Abinda yake trending kenan a media a kwanakin, ba kamar hoton Omar da yake Waukar hankali, kallon farko zaka yi masa ka fassara shi a Wan gata gaba da baya, saboda kyuan da Allah ya yi masa. Abu kamar wasa ig account Winsa ya cika da dms, kuma yawanci duk mata ne, shi abin ma dariya yake bashi ko buWewa baya yi balle ya ce zai basa amsa.KRB3P83
Nana haleema

Bayan kwana biyu da yin abun ranar Monday Nayla ta tashi da azumin godiya ga Allah, ta yi mamaki da ta ce masa zata yi azumi bai tanka ba ya ce Allah ya bada ikon yi, a nan ta tabbatar da ™warai fushi yake yi da ita. Sai ta ™ure yake ri™e hannunta, amma hugging ko kiss duk ya daina, hakan yana damunsa shi kansa balle ita da take ganin laifi tayi masa.

   Bayan ta sha ruwa ya shigo falon ya zauna ya kalle ta ya ce, "Kin sha ruwa lafiya?."
"Lafiya lau."
"Ina tunanin jibi zan koma China tunda akwai visa, akwai takardar da zan saka hannu a can, kuma akwai kayan da zan siyo saboda zamu fara tura musu kaya a wannan watan." Nayla ta kalle shi ta ce, "Jibin zaka je?."

"In sha Allah."
"Ka siyi ticket Win ne?."
"A'a ban siya ba, yanzu maganar zuwan ta tashi ke na fara faWawa."
"Allah ya kaimu."
"Amin." Ta sake kallon sa ta ce, "tare zamu je din?." Kallon ta ya yi na wani lokaci, kafin ya janye ido ya ce, "A'a, ina yi miki batun tafiya jibi kina zancen tare zamu je?."

Nayla a sanyaye ta ce, "Amma ka ce baza ka sake tafiya ka bar ni ba." Ya Wan shafa kansa ba tare da ya kalle ta ya ce, "in na je dake yanzu amfanin me zaki yi min? Damuwa zaki ™ara min kawai." Kallon sa tayi da mamaki, kafin ta yi magana ya ce, "A ina zaki zauna in na tafi?." Muryarta ta fara rawa sosai ta ce, "Wajan Hajja."
"Baza ki je Kaduna ba?." Ta Waga kai alamun eh hawaye na sakko mata.

      Sai ta karya masa zuciya, yana matu™ar ™aunarta yana kuma tsananin bu™atarta amma ya rasa abinda ya yi mata take gudunsa, shiyasa yake bata space bai sani ba ko akwai dalilin ta na yin hakan. Kusancinsu cutar dashi ya ke yi, shiyasa yake baya baya da ita. Ita kuma sai ta ke gani kamar ya canja mata ko ya daina sonta bayan ba haka bane, shi kaWai ya san halin da yake ciki na rashinta.

A hankali ya ce, "Meye na kukan?." Kamar jira take ya tanka ta fashe da kuka mai sauti, ya yi ajiyar zuciya ya taso ya zauna a kusa da ita ya ce, "Jidda!." Bata kalle shi ba ta kwanta a jikinsa bashi da zaSin da ya wuce ya ri™eta a jikinsa amma shi kaWai ya san illar da hakan zai masa.

Bayanta yake trapping a hankali ya ce, "ki bar kuka Ashiq, ko kina so na yi kuka ne nima?." Ta girgiza kai tana kuka ta ce, "ka....dai....na....so....na....Rouhi!."
"Shiii! Har abada bazan daina sonki ba Jidda, da sonki Allah ya halicce, da sonki zan bar duniya, da sonki zan tashi har a aljanna. Babu wani dalili da zai saka na daina sonki, ina baki space ne kawai."

"Ka yi ha™uri!."
"Baki yi min laifin komai ba Jidda, ki daina kukan mu yi magana." Ta Wago daga jikinsa tana kallonsa, ya share mata hawaye ya yi mata kiss a goshi, ta lumshe ido jin Wumin lips Winsa a fuskarta, rabon da ya yi mata haka har ta manta. Fuskarta ya ri™e ya ce, "Kinga tafiyar gaggawa ce ta same ni shiyasa baza mu tafi tare ba, amma in sha Allah tafiya ta gaba tare zamu yi dan na san yanzu zan dinga shiga ™asar a kai a kai."

Ta Waga kai alamun to ya ce, "To ki yi murmushi mana." Bata yi murmushi ba ta zuba masa ido musamman lips Winsa da ta missing sosai, a hankali ta ta matsar da bakinta kusa da na shi ta fara kissing a hankali. Runtse ido ya yi jin tana sake birkita masa nutsuwa, ya san abin yana yim nisa jikin zai fara rawa ta gudu. Kiran sallah aka yi ya saka shi ya janye jikinsa da hanzari, ya kalle ta ya ce, "Ki kwantar da hankalinki, zan je nayi sallah na dawo" ya faWa yana mata kiss a kumatu ya tashi ya fita.

   Nayla tausayin kanta take ji, tana son mijinta tana kewarsa amma ta rasa abinda yake yi mata daWi, ta rasa me yake damunta har ya canja ta haka. Ranar ya sakar mata fuska duk da daman bai daina yi mata fara'a ba, sai dai rashin kai hannunsa jikinta da ba yayi, kuma bai yi ™o™arin yi mata komai ba itama bata nema ba a haka dai suka yi bacci.

   Kamar yadda ya faWa ranar talata da safe ya hau jirgin abuja ya sauka a airport na Abuja, sai ™arfe  Waya na rana hau jirgi suka bar Nigeria. Nayla tana gidan Hajja har jirginsu ya tashi, gidan babu daWi saboda babu Salma sai ´ar ™anwar Hajja itama kuma ta girma sosai.

Zaman gidan baya yi mata daWi kawai sai ta tafi gidan Mama Sa'adatu, gabaWaya bata son zama a Kaduna da can zata je haka kawai bata son zuwa. A gidan Mama Sa'adatu ma bata da walwala ta fi ganewa ta keSe kanta a Waki ita kaWai bata son hayaniya.

    Bayan kwana uku da tafiyarsa ya tura mata hotunan abinda ya faru a can da hoton da aka Wauka kamar yadda aka Wauka a Kano. Ta taya shi murna amma ko a status bata sakawa saboda mata. Amma da ta shiga X sai ta ga ana ta sake Worawa ana addu'a, masu cewa ya burge su suna yi masu addu'a suna yi. Gajiya tayi da zaman ta Wauki mota ta tafi gidan Didi bayan ta faWa masa ya barta da™yar. Da maganar abinda ya faru Didi ta tare ta itama ya tura mata hotunan, Didi kuwa an saka a status tana addu'a da fatan alkhairi.

     Bayan sun gama gaisawa da maganar Omar Didi ta kalle ta a nutse ta ce, "Nayla sai nake gani kamar kina da damuwa ko?." Nayla ta yi shiru kafin ta ce, "ina da damuwa Didi." Didi ta ce, "me ya faru?." Nayla ta ce, "Rouhii ne yake fushi

Please Login or Register in order to submit comment