Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan bai faru ba, wata™ila da ban amince har na je gidanku ba da hakan bai faru ba. Ke! Kina jina...?" Ya faWa yana Wora ™afa kan Waya ya ce, "A katse wannan maganar a wajan nan, bani da ra'ayin aurenki kawai ki ha™ura ki ™yale ni, bana son yawan maimaita magana guda Waya, tun muna shaida juna a ha™ura kafin a tunzurani." Narma hawaye ya sakko mata, cikin rauni da sanyin murya ta ce, "Ni na kasa tabbatarwa, da gaske baka sona?."

Wani irin kallo ya yi mata alamun ta ishe shi ya zuba mata ido kawai yana kallo. Didi ta fahimci wannan kallon, yanzu zai birkice ya fara masifa ya firgita kowa. Didi zata yi magana ya ce, "Ke! ni zan zauna ina yi miki ™arya? Wacece ke da zan miki ™arya?. Ina faWa miki magana kina sake dawo dani baya, dan ma kin samu lokacina da maganar!?" Ya faWa cikin faWa sosai yana kallon ta.

Didi ta ce, "Don Allah ka yi mata a hankali......."
"Bazan yi a hankalin ba, yarinya ce ita da za a tsaya ana yi mata dabara ko magana cikin magana?. Sak nake magana ke kin sani, bazan aureta ba, ta kuma daina takura min, ta je tayi rayuwata ta nayi tawa. Kar ta sake zuwa inda nake!. In na sake ganin fuskarta a kusa dani ban san abinda zan aikata mata ba" Ya faWa yana zaro idanu waje yana kallon Didi, sai kuma ya yi tsaki ya mi™e ya bar falon

     Didi ta kalli Narma da take jikinta ta ri™e hannunta cikin rarrashi ta ce, "Narma ba komai ka ke so ka ke samu ba a rayuwarka ba, wani abun zaka so shi matu™ar so amma in ba rabon ka bane dole ka yi ha™uri dashi. Wani abun zaka ™i shi matu™ar ™i amma kuma sai ka mallake shi ba tare da ka yi tunani ba. Shiyasa Allah ya ce abinda ka ke tsananin so wani lokacin ba shine alkhairi a gareka ba, abinda ka ke tsananin ™i kuma shine alkhairi a rayuwarka. Allah shine ya san abinda ba mu sani ba Narma. To ki Wauka Omar ba alkhairi bane a cikin rayuwarki shiyasa baki mallake shi tun farko ba, kuma tun farko da Omar mijinki ne da sai kin aure shi, amma ba mijinki bane shiyasa baki aure shi ba har ki ka auri wani ki ka fito daga gidansa. Baza ki taSa mallakar abinda ba na ki ba, baza ki auri mijin da ba naki ba. Abinda ya kamata ki yi addu'a, ki tsaya akan addu'a ki manta da komai sai komai ya wuce."

"Kamar yadda ya faWa miki kin shiga rayuwarsa dan ki jasa zuwa gidanku ya zama silar canjawarsa haka ne, amfaninki a rayuwarsa kenan, haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canja. Baki kasance matarsa a cikin ™addarar ku ba, shiyasa Allah bai yi ma kin aure shi ba. Tunda har Omar ya ce baya so wallahi baya so Win ne, Omar baya magana biyu, haka zakila baya faWar ™arya ya Soye gaskiya dan wani ya ji daWi. Shiyasa kalamansa suka yi miki zafi dan shi bai iya Soye-Soye ba. A lokacin da yake tunanin yana sonki ba so bane, ya samu kusanci dake ne a karo na farko a rayuwarsa. Bayan ni babu macen da wani abu ya taSa haWa su sai ke, wannan abinda yake ji a ransa shine ya Wauka soyayya ce. Amma yanzu da ya mallaki wacce yake tsananin so ya banbance tsakanin so da kusancin. Ki kwantar da hankalinki, ki yi ha™uri, ki fuskanci rayuwarki Narma."

Narma kuka take a jikin Didi a hankali. Didi ta ce, "ina faWa miki gaskiya ne a matsayina na yayarki, gwara ki san abinda zaki yi ki daina Sata lokacinki, sannan kuma daina tunanin Omar. In ki ka kuma zuwa inda yake gamuwar ku baza tayi kyau ba Narma. Zai yi miki abinda zaki ji ina ma baki san fuskarsa ba, duk yadda ki ke tunaninsa wallahi ya wuce wajan, gwara ki kama kanki ki cigaba da addu'a."

Narma ta yi ajiyar zuciya tana sauke numfashi. Didi ta ce, "Sannan Narma ki yi hankali ki daina shigar da take nuna jikinki. Shigar banza ba wayewa ba ce a ganina jahilce ne, nuna surar da Allah ya yi miki ba komai bane face tsantsar rashin sanin ciwon kai. Duk yadda zaki kasance wajan fidda saraici ai baki kai tunkiya ba, ita tunkiya yadda aka haife ta haka take yawo, kin ga kenan duk abinda zaka yi akwai wanda ya fi ka, kafin ka yi Waya an yi dubu. In kina nuna tsaraicinki baza ki samu wanda zai so ki tsakani da Allah ba, zasu so ki ne saboda abinda yake gani a zahiri a tare dake, da zarar ya aureki ya mallaka shikenan sai komai ya fita daga ransa, daman ba sonki yake yi ba sha'awa ce, ita kuma sha'awa tana gushewa ne da zarar gangar jiki ta samu abinda take maradi. Ba wai sai an neme ki a waje ne yake nuna illar shigar banza ba, ba sai anyi yun™urin yi miki fyaWe ko abinda ya yi kama da haka shine yake nuna illar fidda tsaraici ba, wani lokacin sai kin yi aure zaki fahimci illarta, domin auren sha'awa maza suke yi da masu irin wannan Wabi'ar ba na soyayya ba."

"Shiyasa nake baki shawara akan ki daina, tun kafin na san ki ni masoyiyarki ce, ina bibiyarki sosai saboda kina burge ni. Amma a ko yaushe ina cewa da Narma ta san illar nuna surarta a duniya da bata yi ba, a lokacin bani da matsayin da zan faWa miki gaskiya dan baki sanni ba, amma a yanzu na faWa miki na sauke nauyin da ya kamata ace na sauke. Surar da Allah ya yi miki ya yi miki ita ne dan ki yiwa mijinki kwalliya ba ki bayyanata ga duniya, in mijinki ya kalle ki ya yi farin ciki lada za a rubuta miki, wanda zaki je har ™abarinki ki tarar dashi. In akasin mijinki ya kalli surarki ya yi farin ciki zunubi za a rubuta miki, wanda zaki je ™abarinki ki tarar dashi."

Didi ta kuma cewa, "sannan ki daina wula™anta mutane shima ba abu ne mai kyau ba, Bazan ce kin yiwa Omar ba, amma wanda ya yiwa Omar saboda yana ganin rayuwarsa ta baya a yanzu ya ga yadda Allah ya mayar dashi, baka sanin abinda zai faru a rayuwar wani tunda ba kai ka tsara masa ba."

Didi ta yi ajiyar zuciya ganin Narma ta nutsu tana saurarenta, jikinta yayi sanyi alamun maganarta tana ratsa zuciyarta. Didi ta ce, "Ki je gida Narma, ki zauna ki tsara rayuwarki yadda ya kamata, amma ki manta da Omar. Ki dage da addu'a, na tabbatar da ace kina addu'a abin bazai yi muni haka ba. Ina baki shawarar yin addu'a Narma."

Narma ta kalli Didi ta girgiza kai tana goge idanunta ta ce, "Tabbas ina sakaci da addu'a Didi, ban taSa ro™on Allah akan ya kawo min sau™i a soyayyar Faruk ba."

"Ashsha! Kin ji matsalar, ta inda aka samu kuskure kenan Narma. Tun farko da kin mi™awa Allah kukan ki da yanzu kin manta da Omar, da yanzu kin cigaba da rayuwarki cikin farin ciki da annushuwa, da yanzu rayuwarki tayi gaba fiye sa tunanin ki. Indai kana ro™on Allah kana faWa masa abinda ya fika sani a kai zai shiga lamarin ya kuma sassauta maka. Shiyasa hausawa suka ce in so cuta ne ha™uri magani ne. Ki ri™e addu'a, a akan Omar kaWai ba, akan komai na rayuwa ki dinga addu'a a kai."

Narma ta girgiza kai ta ce, "Na gode Didi. Amma na tabbatar babu lallai na rayu a duniyar nan in babu shi."

"Kul, kar ki sake faWar haka. Babu wata halitta da in babu shi baza ka rayu ba, in har zaka rayu babu iyayenka a duniya babu wanda zaka ce dan babu shi baza ka yi rayuwa ba. Zaki manta da Omar in kin so hakan. Ki ri™e addu'a kiga in komai bai canja ba, ina nan zaki zo ki bani labari."

      Narma tayi murmushin takaici, dan ji take abinda Didi take faWa ba yuwa zai yi ba. Ta mi™e sai ta tafi zata faWi Safna tayi sauri ta tarota ta ce, "Yi a hankali." Narma ta kalli Nayla da bata ce komai ba amma kallonsu take yi, ta yi murmushi ta ce, "Ki yi ha™uri Nayla, Allah ya raya Musliha, na gode." Daga haka Safna ta ri™e ta suka fita daga falon.

Didi ta kalli Nayla da fuskar take a Waure matu™a ta ce, "Ki yi ha™uri Nayla, na san dole ki yi kishi, amma ki Wauka komai ya wuce." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta kalli Didi ta ce, "Babu komai Didi. Umma Saroot ta aiko min da kaya sosai."

"Eh ta faWa min, ta ce min ita zata gyara mai jego." Nayla ta Wan yi murmushi ta ce, "Turaren wutar mai daWi sosai, haka humra ma." Didi ta ce, "Sosai ma kuwa, ga ri™e Waki da ri™e jiki. Ni naga  kamar kina sallah, har kin samu tsarki kenan?."

     Da sauri Nayla ta waiga baya ta ga Omar baya nan ta kalli Didi ta ce, "Eh Didi, bayan yin suna babu jimawa ya Wauke." Didi ta fahimci bata so Omar ya sani sai ta ce, "Ma sha Allah, Allah ya ™ara lafiya." Ta amsa da amin kafin Didi ta ce, "Ni zan wuce gida Nayla, don Allah kar ki bar komai ya dame ki." Ta yi murmushi ta ce, "Babu komai Didi."

"Ya tafi da Marmerh, ki karSo min ita." Nayla ta amsa ta karSi Musliha ta bawa mai kula da ita sannan ta hau sama ta shiga Wakin Omar. A kwance taga Marmerh a kan gado, ta Wauko ta bata ce komai ba ta sakko ta kawo mata ita har mota, Didi ta shiga motar ta ja ta tafi.

Didi ana tafiya Nayla ta Waure fuska, ta juya ya koma gidan ta hau sama kai tsaye inda ta ganshi ta wuce. Har zata shiga Wakin nasa sai kuma ta fasa dan haushinsa taji sosai, ta Wauka zai faWa mata akan maganar Narma Abiy ya kira shi, kuma da ta tambaya sai ya ce zai faWa kuma bai faWa ba ya cigaba da harkarsa, hakan sai ya Sata mata rai, sai ta ga babu amfanin ta yi masa maganar kawai ta share shi.vKRB3P105

Narma haka suka koma gida cikin yanayi mara daWi, Mum tana ganin shigarsu ta mi™e ta ri™o Narma ta kwantar da ita a jikinta suka samu waje suka zauna Mum ta ce, "Safna ina ku ka je ne haka? Ina ta kiran ku babu wanda ya Wauki wayata." Safna ta ce, "Gidan Omar mu ka je." Mum ta ce, "What? Gidansa kuma?."

"Eh Mum, can muka je muka same shi."
"To ya aka yi?." Safna ta taSe baki ta ce, "Kusan ya wula™anta mu zan ce, wata tsawa da ya yiwa Narma sai da gabana ya faWi wallahi. Amma a haka Narma kuka take yi tana so ya saurareta amma ya™i, idonta ya kalla ya ce baya sonta ba zai aure ta ba, ta daina wahalar da kanta a akansa, shi in ya yi gaba baya dawowa baya."

Ajiyar zuciya Mum ta yi, a lokacin Dad ya shigo falon ya ji abinda Safna ta ce ya zauna Mum ta ce, "To ya Narma? Me ta ce?" Ta faWa tana taSa wuyan Narma tana jin body temperature ta. Safna ta ce, "Ni tunda muka taho nan bata ce komai ba, amma kuma dai bata kuka, wani lokacin ta kan yi murmushi kawai."

Dad ya kalli Narma ya ce, "Narma kin gani da idonki, kuma kin ji duk abinda mu ka yi dashi ko? Har baban matarsa na samu ya yi masa magana amma bai yi aiki ba." Ta kalli Dad ta ce, "Da ka amince min tun farko da haka bai faru ba Dad...." Ta ja numfashi ta ce, "amma shikenan na yarda ™addarata ce kamar yadda Yayarsa ta ce, zan yi ha™uri, in kuma ha™urin ya zama ajalina shikenan."

Mum da tashin hankali ta ce, "Akan Omar sai ki mutu?."
"Yes Mum, ina son shi son da ban taSa yiwa wata halitta a duniya ba, ina ™aunarsa matu™ar ™auna." Safna ta ce, "Baza ki mutu ba Bestie, baza ki mutu ba, zaki cigaba da rayuwa kamar kowa, zaki samu wanda zai kula da ke. Ki daina faWar wannan kalmar babu daWin ji."

Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad zan shiga Saudia, ina so naje nayi addu'a sosai. Bazan iya cigaba da zama a Nigeria ina ganin Faruk ba, zan tafi can ko zan samu nutsuwa." Dad ya ce, "Shikenan." Bata jira me zai ce ba ta wuce Waki Safna ta bi bayanta.

Dad ya kalli Mum ya ce, "Wai wannan yaron da na raina shine yake wahalar min da zuciyar yarinya haka, abin haushi abin takaici da Sacin rai. Saboda shi mu kazo Kano gashi zuwan bai yi amafanin komai ba, sai Sacin rai da ya ™ara mana, Na yi dana sanin saninsa a cikin rayuwata gabaWaya. Ban taSa kasa yiwa ´a´an abinda suke so ba sai a kansa, a kansa na Waukar mata al™awari kuma na kasa cikawa. Komai suke so ina samar musu dashi, amma na gaza bata Omar."

Mum tayi shiru kafin ta yi ajiyar zuciya ta ce, "amma tabbas nayi darasin rayuwa Dear. Duk yadda mutum ya ke kar ka wula™anta shi dan baka san ya zai zama nan gaba ba, Ban yi tunanin Wan daban yaron nan zai iya zuwa wani matakin rayuwar ba, balle har ya kai ga mun nemi alfarma a wajansa ya kasa yi mana ba. Kuma wai alfarmar ma ta auren ´armu, ban Wauka zai aikata hakan ba. Tabbas Allah ya nuna mana ba komai ka ke nema ka samu ba, duk ta™amarka akan duk abinda suke so kana samar musu dashi Allah ya nuna mana shi yake baka iko. Wannan da bai nufa ba gashi bai faru ba." Dad ya yi shiru bai ce komai ba, amma ya san tabbas abinda ta faWa haka ne, tsaki ya yi ya tashi ya shiga ciki yana tunani da tausayin ´arsa.


       Nayla haka ta kwana biyu tana Sata rai, yana lura da ita ya kuma san dalilin fushin, a ganinsa meye na fushi tunda a gabanta ya yanke hukunci, ta kuma san bazai canja magana ba meye zata wahalar da kanta tana fushi kamar wacce aka yiwa laifi. Haka suke rayuwa kafin ya fito ta ajjiye masa breakfast ta bar falon, kafin ya dawo daga office ta ajjiye masa abinci, baya sake ganin ta sai ya yi da gaske.

A ranar lahadi da yamma ya shiga falonta wanda bai cika shiga ba saboda ba™in da ake yawan yi, sannan ga wacce take zaune da ita shi baya sakewa a waje in akwai ba™uwar fuska. Kukan Musliha yaji daga cikin Wakin Nayla, kai tsaye Wakin ya wuce ya buWe sai ya ganta tana sallah. ˜arasawa ya yi ya Wauki Musliha ya fita daga Wakin ba tare da ya yi magana ba. Da faWuwar gaba Nayla ta idar da sallar, Allah ya sani bata so ya ganta tana sallah ba, shiyasa take rufe Wakin in zata yi sallah, yau ma tautsayi ne ya saka ta bar ™ofar a buWe.

A sanyaye ta mi™e tsaye ta zare hijjabin daman riga da wando ne a jikinta ´an kanti, rigar tana da tsaho har guiwa amma bata da kauri, wando kuma black jeans ne, ta saka hula ba™a sai shigar ta karSe ta kamar ba wacce take jego ba. Fita tayi zuwa falonsa, ta same shi da Musliha a zaune har lokacin tana ta kuka. Zama tayi a gefensa ya bita da kallo dan shigarta ta Wauki hankalisa sosai, ta Wauki Musliha a jikinsa, ta buWe maSallan gaban rigarta ta fara shayar da Musliha.

Shi dai ido kawai ya zuba mata yana kallonta cikin burgewa, rainon ma kyau yake ma musamman a lokacin da take shayar da ita, sai ya ji kamar ya Wauketa ya saka a Waki yana ta kallonsu. Nayla bata kalle shi ba dan ita tsoro take ji bata so ya yi mata maganar ta fara sallah, shi kuma kyaun da tayi ne yake Waukar hankalinsa, ga wani haske da ta sake yi sai ™hamshi take zubawa mai daWi shiyasa ya kafa mata ido kawai yana kallonta.

Shi ya katse shirun ya ce, "Gobe zamu kai ta passport, ina tunanin zamu yi tafiya a kwanakin nan." Nayla ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "to." Daga nan tayi shiru bata sake cewa komai ba.  Gumin da Musliha take yi a goshinta ta saka hannu tana goge mata har lokacin shayar da ita take yi bata cire ba. Bacci ta yi a jikinta, ta cire ta ta mayar da maSallan ta rufe, ta gyarata a jikinta tana gyara mata hular kanta.

Shiru ya sake ratsa tsakaninsu, kamar ta yi masa maganar Narma amma sai ta fasa, ta gama gyara Musliha har lokacin bata kalle shi ba. Shi kuma kallon ta yake yi yana murmushi a zuciyarsa, wai kishi take yi kuma take fushi dashi, ita a wajanta haka take kishin ana share miji kuma ana fushi dashi. Bayyana murmushin nasa ya yi har ta ji sautinsa, sai a lokacin ta Wago suka haWa taga sai murmushin yake yi, sai ta yi tunanin ko sallar da ya ga ta fara ne ya saka yake murmushi, dan ta san halin kayanta, tsaf ganinta tana sallah zai saka shi murmusawa dan an daWe ba a haWu ba. Gabanta ya faWi sosai dan ita bata shirya koma masa ba.

Bata iya cewa komai ba shima kuma bai ce ba, dan shi bai ga laifin da ya yi mata da take share sa ba. ˜o™arin mi™ewa ta ke yi zata bar wajan, ya daure ya ce, "Ina zaki je?." Nayla ta kalle shi ta ce, "Waki zan je."

"Kar ki tashi, ki zauna" ya faWa cikin bada umarni yana kallon ta. Fasa tashin tayi tare da yin ajiyar zuciya, sai ta sake bashi dariya ya sake yin murmushi ya ce, "Hajiya Jidda manya mata! Ranki ya daWe gimbiyar mata, sarauniya mai mulki a duniyar Omar" ya furta yana murmushi.

Bata kalle shi ba wasa take yi da hannunta, ya sake yin murmushi ya ce, "Dole sai kin saka na yi magana ne? Ni ban ga dalilin wannan fushin ba, laifin me nayi miki?." Ta kalle shi a ™ufule ta ce, "Sai yau zaka tambayi me ka yi min? Kwana nawa da yi min laifin sai share ni ka ke yi irin baka damu da ni ba balle fushina?."

Dariyar da ya ke Soyewa ta bayyana ya ce, "Jidda ni ban yi miki laifi ba, haka kawai ki Wauki fushi dani ki ka sakawa a zuciyarki, shiyasa na baki hutu ki yi fushin ki gama sai mu yi magana." Ta kalle shi tana harararsa ta gefen ido ta ce, "baka damu ma da fushin nawa ba tunda har hutu ka bani ko?." Ya juyo yana kallon ta sosai ya ce, "na damu mana, kema kin san na damu sosai." Ta kawar da kai gefe, ya saka hannu ya juyo da fuskarta yana ri™e da fuskar amma bai yi magana ba.

Murmushi ya sake yi dan wallahi dariya take bashi ya ce, "Yanzu meye kuma? Uhum....ina jinki." Ya faWa yana kallonta. Ta kalle shi ta ce, "misali a zo har cikin gidan nan a zauna a gabanka ana cewa ana sona za a aure ni, zaka ji daWi?." Ya Wan gimtse fuska kaWan ya ce, "Kina matar tawa za a ce ana sonki?."

Sai kuwa ya tunzurata, cikin fusata ta ce, "Nima ai kana mijin nawa aka zo aka ce ana sonka, gashi nan har ka haWe fuska saboda baka ji daWin maganata ba, abinda ka ji a ranka a yanzu nima shi na ji kuma ka share ni. Nima fa ina da kishin nan, amma a komai sai ka nuna kamar ka fini sanin mahimmacin kishi, yadda ka ke ji a kaina haka haka nake ji a kanka!."

Shi dai kallon ta yake yi ganin yadda take yi masa masifa kamar zata zane shi, bai ce komai ba har ta kai ™arshe. Sai da ta saka full stop sannan ya ce, "Kina jin kishina Jidda, amma asalin kishi ni nake yinsa ba je Jidda, a cikin kashi goma baki Wauki kashi Waya daga cikin kishinki da Allah ya Wora min. Ke fa ni kaWai Allah ya halitta miki a duniya, ni kuwa Allah ya halatta min mata har guda huWu, zuciyarki ni kaWai zan zauna a cikinta, ni kuwa....." a fusace ta katse shi ta ce, "mata dubu zasu zauna a cikin taka zuciyar ko? Zaka iya saka son mata dubu a zuciyarka ko!?" Ta faWa cikin masifa tana kallon sa.

Murmushi ya yi mai sauti yana girgiza kai ya ce, "Tuba nake ranki ya daWe, ni ba haka nace ba."
"To me ka ce? Me ka ke nufi da abinda ka ce? Kenan ni ban cancanci nayi kishi ba sai kai? Kaine ne ka cancanci ka yi kishin matarka, kaine mai kishi ni kuma banza ce wacce bata kishin mijinta. Wai har Abiy ya kira ka akan maganar nan amma ka kasa faWa min, inda nice nayi kwatankwacin abinda kayi min da kaf garin nan sai an ji kan mu. Amma ni da ka yi min share ni ma kayi ka daina shiga harkata, saboda kaine kawai mai kishi a duniya ni bani dashi!."

Ya saka hannu ya shafa gashin fuskarta yana wani murmushi mai Waukar hankali ya kalle ta, ganin yadda ta gimtse fuska ya sake bashi dariya ya ce, "na so na faWa miki batun zuwa wajan Abiy mantawa nayi. Sannan ita bana kawo batunta a raina, mahifinta ma da yaje ya same ni mantawa nayi da batun gabaWaya shiyasa ma ban faWa miki ba. Kuma da ta zo gidan nan Jidda ni na kawo ta? Ni ban ce tazo ba ai, kuma a gabanki tazo ban san ya akayi tasan gidan nan ba, kuma da ta zo me nace mata huh....!?."

Kawar da kai tayi gefe tana Waure fuska, ya saka hannu ya juyo da fuskarta ya ce, "FaWa min mana, me nace mata?." Bata ce komai ba ya ce, "Jidda bani da ra'ayin ™ara aure a rayuwata, bani da ra'ayin yin aure balle har nayi tunanin zan iya aurenta. Maganar sona da take yi kuma ai mun yi magana dake tun a baya, bana da bu™atar maimaita miki wannan maganar. Kuma ni ban Wauka zaki yi fushi haka ba, kin san halina, kin san abinda zan yi, kin san wanda bazan yi ba. Kuma na faWa miki komai a kanta tun farkon zamana dake, ban Wauka dan tazo gidan nan zai dame ki ba, amma sai ki ka yi fushi ki ka daina kula ni" ya ™arasa maganar cikin karayar murya yana kallon ta.gP106

Nayla ta kawar da kai kafin ta sake kallon sa ta ce, "Meyasa komai ka ke faWa min baka mantawa, amma batun Narma shi kaWai ka ke mantawa baka faWa min ba?."
"Kema gashi kin faWa, bana manta duk wani abu mai mahimmaci na rayuwata, komai da ya faru nake sanar dake. Amma ita saboda rashin mahimmacinta ne shiyasa nake mantawa Jidda."
"Uhum."
"Baki yarda ba?."

Ta kawar da kai gefe bata ce komai ba, ya zuba mata ido yana kallon ta ganin ta™i sakin fuska alamun akwai sauran damuwa a ranta. Kallon da yake aika mata dashi ne ya fara shiga zuciyarta yana yawo a jininta, ta sauke numfashi bata ce komai ba kuma ta™i yarda ta kalle shi. Can ™asan ma™ogwaronsa ya ce, "Jidda!."

Nayla ta kalle shi fuska babu walwala ta ce, "To ba kai bane ka ke share ni..? Kai ta hararata, kuma ka san ni bana son ganin idonka in kana harara ko ranka a Sace. Kuma ai ka san dole zan yi kishi ko yaya ne tunda kai mijina ne, amma ka yi min banza ko kula ni baka yi. Ka fara daina sona kawai, yanzu Musliha

Please Login or Register in order to submit comment