Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana Winkin sallah kowa guda biyu da kuWin Winki, sannan ga takalma an bamu. Kuma tsakiyar ramadan ya bada kuWi ya ce kowa ya kai gidan su, sannan ga sallamar azumi da aka yi mana mai kauri, a taya mu godiya, Boss ya yi mana komai a rayuwar nan. Nayla ta Wan yi murmushi tana aiyyana baka san ka fini daraja a wajansa ba shiyasa ka ke faWa min haka. Ta daure ta ce,  Kun gode.

 Kuma Antyn mu baki san wani abu ba ba, Boss fa mutane ne suke ganin sa haka, amma bala in sau™in kai gare shi, sannan& ..
 Kai!! Omar ya faWa cikin tswar da ta saka Bashir yin shiru yana kallonsa. Hannunsa ya juya alamun tambaya sannan ya ce,  Meye na maganar!? Ya sake faWa cikin tsawa sosai.

Bash ya ce,  Tuba nake.
 Fita! Ya faWa yana nuna amsa ™ofa Bashir ya mi™e sum sum sum ya fice.

Nayla zata bar wajan ta ji ya ce,  meye na biye masa kuna surutu? Bakya ganin Ina wajan? Sai an saka min ciwon kai?. Nayla jin yadda yake maganar a fusace sai ta kalle shi tana mamaki abinda ya fusata shi a cikin maganarta ko ta Bashir. Nayka ta ce,  ka yi ha™uri. Ta faWa ta koma ciki tana cewa,  masifaffe kawai.

Bata sake ganinsa ba sai gab da shan ruwa ta fito dining dan ranar a kai ta jera abinci saboda ta ci son ranta. Ta kuma yi aniyar yi masa tayi koda zai dizgata sai tayi, tana so ta samu lada tunda ramadan Win ya ™are, babu tabbacin zata kai mai zuwa da rai. Shigowarsa ta gani yana waya kamar ko yaushe, sai da ya gama wayar sannan ta ce,  Sannu da zuwa YaMar, Ga abincin shan ruwa na ajjiye maka, don Allah kar ka ce baka ci, kaga daga yau an gama azumi, don Allah! ta ™arasa faWa tana karyar da murya cikin shagwaSa. Yadda ta ce YaMar Win a haWe sai sunan ya bada wani salo mai dadi, ta cire harafin farko ta faWi na ™arshe, sannan ta haWe shi waje Waya da Yaya.

Omar abubuwa ne masu yawa suka haWar masa a lokaci guda suka daki zuciyarsa, sai da ya runtse ido jin abun da ™arfi kamar an saka abu mai nauyi an daki ™irjinsa. Na farko bai san meyasa indai zata ce masa Yaya Omar ba sai ya ji sunan har cikin ™ahon zuciyarsa, bai sani ba ko dan bashi da mai faWa masa Yaya ne sai ita Win shiyasa yake jin haka oho. Na biyu kuma yadda take yiwa sunan iyayi wajan faWa yana yi masa daWi, duk da ta bashi dariya dan gabaWaya bata iya furta harafin R ba, da ta ce Mar Win sai harafin R Win ya tashi kamar wani harafin daban ta faWa. Na uku yadda ta ke yi maaa shagwaSa tana wani kwaSe fuska ya dake shi sosai.

Kallon ta yayi ya ga ta sunkuyar da kai tana jiran amsarsa ya dake ya kawar da abinda yake ji ya ce,  baki faWa min kuWinki ba. Nayla ta Wago dan wallahi ta manta da batun kuWin, ta sake mayar da kai ™asa tana wasa da hannunta ta ce,  Na manta wallahi, amma zan yi lisaafin.
_Ji ta harda wallahi, ko meye na rantsuwar oho._ ya faWa a zuciyarsa ba tare da ya furta komai a fili ba.

Nayla ta ce,  Don Allah YaMar ka ci abinci yau. ˜o™arin wucewa yake yi ya ce,  na ce ina so ne? Ba na ce babu ruwanki da lamarina ba?.
 Baka ce kana so ba, kyautatawa ce nake so nayi maka. Kuma kaga yau azumin ™arshe daga yau sai wata shekarar ga masu yawan rai. Wata™ila kafin shekarar ta dawo na mutu bana duniya, ka ga ko babu komai zaka tuna ka ce ranar azumin ™arshe na last year ni na baka abinci, kaga zan samu lada a cikin kabarina. Don Allah YaMar ta faWa a sanyaye.
ÿþ

TaSe baki ya yi ya wuce ciki Nayla ta yi ajiyar zuciya cike da mamakin sa da bai yi mata masifa ba,  ki cigaba da shige masa Hauwa, in ya make ki wata ran ke kika jiyo. Sai tayi dariya ta zauna akan dining din ta lumshe ido tana addu ar gab da shan ruwa.

Hawaye ya sakko mata tunawa da shikenan ramadan ya ™are, babu tabbacin zaka kai wata shekarar gashi ka yi azumin baka da tabbacin an karSi wanda ka yi. Rauni taji a zuciyarta ta dinga hawaye tana addu a har aka yi kiran sallar magriba. Ido ta goge ta sha ruwa ta yi ajiyar zuciya ta furta,  Allah ya maimaita mana. Cincin Win da tayi ta Wauka ta saka a baki tana ci kafin ta shiga ciki da niyar yin sallah.

(Addu ar gab da shan ruwa, addu a yayin shan ruwa mustajaba ce bata da hijjabi a wajan Allah. Ba sai axumin farilla ba ko azumin nafila ne in aka kai a daure a yi addu a ko ya take. Akwai falala mai tarin yawa a cikin wannan lokaci, sannan addu a bata da hijjabi da ka yi da Allah ya amsa. Allah yasa mu dace ya amsa mana dukkan addu ar mu amin.)

Shima ruwan ya sha sannan ya fito ganin bata falon bai neme ta ba ya fita dan yin sallah. Tana zaune tana shan tea ya dawo sai ta ga kamar bashi da lafiya dan gabaWaya kamar ba shi ba, fuskarsa ta Wan yi ja kuma jijiyar kansa ta tashi, idanun sa sun Wan yi ja kaWan, ga yanayinsa babu ™arfi sosai kamar mai zazzaSi. Rauni taji ya sake mamaye zuciyarta ganin ya zauna a falon ya jingina da kujera ya kulle ido.

Nayla zuciyarta umarni take bata ta je ta kai masa abinci, wani Sangaren na zuciyarta kuma yana hanata aikata hakan. ˜arfin guiwa ta samu ta fara haWa tea, ta tuna Didi ta ce mata yana da shan madara sosai kuma yana shan sugar. Ta haWa tea Win da tosted bread ta haWa komai a tray ta tako a hankali ta ajjiye akan table Win da yake kusa dashi. Yana jinta amma bai motsa ba dan kansa ciwo yake yi sosai.

 YaMar ga abincin. Bai motsa ba balle ya kalle ta, ta koma ta zauna tana cigaba da cin nata amma gabaWaya hankalinta yana kansa har lokacin bai motsa ba. Sai ta ji abincin ya fita daga ranta ta taso tazo nesa dashi ta tsaya ta ce,  YaMar baka da lafiya? Ka ci abinci sai ka sha magani. Idanunsa a kulle bai ce komai ba amma yayi mamakin yadda ta fahimci bashi da lafiya lokaci Waya.

 YaMar! Ta sake faWa a hankali a tausashe. Idanu ya buWe ya kalle ta ganin yadda idanunsa suka yi ja sai gabanta ya faWi a rikice ta ce,  YaMar baka da lafiya ko? Idanun ka sun yi ja sosai, Ciwon kai ka ke yi?. A hankali ya janye idanun sa daga kallonta ya mayar da ido ya rufe. Sallama ta ji ana yi ta kalli wanda ya shigo da alama aiken shi ya yi shiyasa ya bar ™ofar a buWe, ta amsa sallamar. Tk ya shigo ya ce,  Sannu Damisa, ga maganin ya faWa yana ajjiye masa a kusa dashi.

Kallon Nayla ya yi ya ce,  Antyn mu mun ga sa™o, Allah ya saka da Alkahiri. Da amin akwai ta amsa dan gabaWaya hankalinta yana gare shi. Ajjiye wata ledar ya yi ya ce,  Ba a samo ayaba, amma ga apple Win nan. Daga haka ya fita daga falon.

Maganin ya Wauka zai sha da sauri ta dakatar dashi ta ce,  Don Allah ka sha koda tea ne in yaso sai ka sha maganin, babu abinda magani zai maka bayan tun jiya baka ci komai ba ta faWa kamar zata yi kuka tana kallonsa.

_Ya Allahu! Me yarinyar nan take son mayar dani ne? GabaWaya ta shiga rayuwarta na rasa meyasa nake jin maganarta har cikin kaina._ ya faWa a zuciyarsa jin maganar Nayla har cikin zciyarsa. Nayla ta Wauki tea Win ganin bai ce komai ba ta mi™a masa ta ce,  Ka sha don Allah. Ji yake kamar ya karSa ya watsa mata a jikinta, tabbas da Omar Win da ne abinda zai aikata kenan, amma yanzu ya rasa meyasa yake jin abinda yake ji akan yarinyar.

 Don Allah YaMar ka karSa! Ta sake faWa a sanyaye tana sake mi™a masa. Kamar wanda aka bawa umarni ya mi™a hannu ya karSa kamar yadda take bashi. Da yake babu zafi sosai tunda ta Wan jima da haWawa ya kai bakinsa ya sha a hankali. Duk da bashi da lafiya amma tea Win ya yi masa yadda yake so, ya yi mamakin yadda ta iya haWawa daidai da ra ayinsa.

Nayla ganin ya shaa sai taji farin ciki ya mamaye mata zuciya, rana ta farko da ya ci sha wani abun na cikin gidan bayan ruwa. Zata iya cewa abu na farko kenan ma da ya fara amfani dashi a gidan shine mug Win hannunsa.

Ri™e tea Win ya yi bai sake sha ba, ya rufe ido ya jinginar da kansa a jikun kujera. Nayla ji take kamar tayi kuka saboda rauni, ta zuba masa ido tana kallonsa kamar ta cire ciwon ya dawo jikinta, Abin ka da abinda zuciya take so.

Kafin ta yi magana ya sake shan tea Win sannan ya ajjiye. Magani ya Wauka ya Salla ya saka a baki, da sauri ta bashi ruwa a glass cup ya karSa ya sha ya ajjiye. Kulle ido ya sake yi ya yi shiru bai ce komai ba.

Nayla tea Win ta Wauke da ruwan da ya gama sha ta kai dining ta dawo a hankali ta ce,  YaMar ka ci koda irish Win nan ne aka ji daWi, ka ga baka ci komai ba tun jiya. Bai ce komai ba ta zauna nesa dashi tana kallo kamar ta dawo da ciwon kan jikinta haka take ji. Duk da ba wani shiri suke yi dashi ba in yana da lafiyar hakan bai hanata ta ji kamar ta rage masa ciwon ta hanyar kawo shi jikinta ba.

Yana kallon ta ta ™asa ido yadda ta marairaice fuska tana kallonsa, alamun tausayawa ya bayyana ™arara akan fuskarta. Mamaki ta bashi ganin yadda ta damu da ciwon sa haka, sai ya ji daWi a ransa ko babu komai bayan Didi ya samu wacce ta damu da rashin lafiyarsa a karo na farko.

Har aka fara kiran sallar i sha suna a haka, bayan an gama kiran sallar ne ya mi™e zaune sosai ya buWe ido ya mi™e ya fita. Sai sannan ta iya tashi ta yi sallah kasancewar babu tarawee tunda ga watan sallah. Tana idarwa shafa i wutir ta yi, bayan ta idar ta dawo falon ta zauna dan ya dawo a kan idanunta. Ba jimawa sai gashi ya shigo ta amsa sallamar da ya yi ta mi™e tsaye tsaye ta ce,  YaMar ya ciwon kan? Ka samu ka ci abinci zaka fi jin daWi.

Ganin ya yi shiru ya ™araso inda ya zauna ya Wauki wayarsa da ya bari a wajan da kuma wani abun a leda. Nayla ta ™arasa ta zuba masa fried rice da kazar wacce ta rage zata ci, ta ™araso a lokacin zai bar wajan ta ce,  don Allah ka ci abinci. Kallon abincin ya yi ya kalle ta ya ce,  na ji sau™i, na gode abinda ya ce kenan ya wuce ta.

Nayla sai taji daWi ya mamaye mata zuciya, ko bai ci abincin ba iya wannan godiyar da ya yi mata ta fi ya biya mata aikin hajj saboda yadda ta ji daWi har cikin zuciyarta. Murmushi tayi cikin jin daWi ta ajjiye plate Win ta shiga ciki zuciyarta cike da farin ciki.KRB3P014
Arewabooks@nanahaleema11.

Washe gari da wuri Nayla ta tashi tayi wanka ta shirya cikin Waya daga cikin lace Win da ya bata. Šinkin ya yi mata kyau Winkin doguwar riga mai faWi kuma mai kyau sosai, daga ciki wajan ™irji an kama rigar kaWan amma daga ™asa sai tayi faWi, daga baya kuma a buWe take bata kamata ba ko kaWan. Kallon kanta take yi a madubi dan tayi kyau lace Win ya amshe ta. Waya ta Wauka a lokacin ™arfe bakwai da wani abun na safe, ta yi selfie tana murmushi.

"In dai akwai masallaci a kusa gaskiya zan je sallar Eid" ta faWa ita kaWai tana kallon kanta a madubi tana murmushi. Key Win motarta ta ke nema tana dube-dube bata ganshi ba sai ta fito falo tana dubawa.

Turus Nayla tayi ganin Omar ya fito daga Waki cikin men lace fari mai ™ananun zane, kansa Wauke da  hula rantsatstsiya mai shegen kyau sai ™yalli take yi, gashin kansa ya kwanta a baya sai kyalli yake yi ya sake yin ba™i sosai. Fuskarsa a washe yana murmushi da waya a kunnensa, hakan da ya yi sai ya bayyanar da kyau da kwarjinin da Allah ya yi masa. Hatta takalmin ™afarsa fari ne, ya haska ™afarsa sosai ya fito sak a matashin Alhaji, in ka ganshi, ka kalle shi sai ka so ka sake kallonsa.

Nayla zuciyarta narkewa tayi a kallonsa ganin yadda ya yi mata kyau fiye da kullum a duniya. Ya yi kyau matu™a wanda ya wuce tunaninta har bata san ta tsaya cak tana kallonsa ba. Cikin sanyin murya taji yana cewa, "Eid bana ya shiga tarihi, Didi bata tashe ni zuwa masallaci ba na tashi har na shirya zan tafi." Maganarsa ce ta dawo da Nayla hankalin ta, ganin yadda yake amsa wayar ya tabbatar mata da Didi yake yin waya shiyasa yake murmushi.

Juyowa ya yi suka haWa ido, shima sai ya yi sak yana kallonta ba tare da ya san ya tsaya Win ba. Yadda ta ga ya yi mata kyau shima abinda ya gani kenan a tare da ita, bai lalace a kallonta kamar ita ba taji ya ce, "Gata nan." Jin abinda ya ce ta san Didi ce take tambayarta, bata gama mamaki ba taga ya mi™a mata wayarsa ™irar iPhone 14 pro max. Nayla kallon wayar tayi ta ga seconds suna tafiya ga sunan Didi a rubuce a jikin wayar.

Hannu ta saka ta karSa ta saka wayar a kunne Nayla ta ce, "Didi Ina kwana." Didi ta ce, "Kin tashi lafiya Nayla? Ya Shirin zuwa sallah, amma dai zaki je masallaci ko?." Nayla ta ce, "Ina tunanin zuwa."

"Ya kamata dai ki je Win, ai rai ne ya kawo mu. Da farko da na tambaye shi ya ce min bai san kina ina ba, ashe kuna tare."
"Yanzu na fito na ganshi."
"Na kira na tuna masa yau fa da masallaci, duk da na san aikin ki ne. Ayi ha™uri na tuna waccen shekarar ne shiyasa na kira shi."

Murmushi Nayla ta yi ta ce, "kin kyauta Didi. Babu inda zaki je anjima nazo?."
"Zan je gidan su yallaSai, a ka'idar gidan su ana haWuwa duk ranar sallah. Sai dai gobe in Allah ya kaimu."
"Allah ya kaimu Didi."
"amin. Maza ki shirya ki tafi masallaci, nima yanzu zan tafi" ta faWa tana yanke wayar.

Tunda ta fara wayar tana murmushi yake kallon ta, a rayuwarsa bai taSa ganin wacce murmushi ya ke yiwa kyau kamar ta ba, da zarar ta murmusa dimples Winta sun bayyana akan kumatunta, siraran ha™oranta masu haske sun fito waje sai yaga kamar duk duniya babu wacce murmushi yake amsar fuskarta kamar ta. Murmushi na ™awata fuskarta sosai, da zai iya da ya faWa mata ta cigaba da yi yana samun masauki mai kyau a fuskarta. Ga murmushin nata da arha ko yaushe yi take yi, amma in tayi sai ka sake kallo saboda yadda yake haska fuskarta.

Šago idon da tayi hakan ya saka ya Wauke ido daga kallonta, ta tako kusa dashi ta bashi wayar, ya kalli wayar da take mi™o masa ya mi™a hannu zai karSa idanunsa ya yi karo da zanen ba™in henna da yake hannunta. Jiya ya kula dashi a hannunta, amma da yake bashi da lafiya bai kula sosai kamar yau ba.

Kamar bai gani ba ya karSi wayar ta kalle shi ta ce, "Ina kwana, ya jiki? Ina fatan ka ji sau™i." Bai kalle ta ba ya ce, "da sau™i" ya faWa tare da motsawa zai bar wajan. Sai ya tuna bai Wauki sallaya ba, Wakin ya koma da niyar Waukowa sai ya ga sallayar bata yi masa ba duk da babu abinda tayi, ba dauWa ba komai amma bata yi ba.

Fitowa ya yi yana kiran wayar Bash yana Wauka ya ce, "Fito min da sallaya zan tafi masallaci." Kafin ya ™arasa fita Nayla ta juya da sauri ta koma ciki, ta Wauko sallaya mai kyau da laushi harda feda mata turare ta dawo ta tarar dashi zai fita daga gate Win gidan.

Tsayawa tayi ta ce, "YaMar!." Sai dai ya kulle ido ya buWe jin sunan har ™wa™walwarsa sai da ta harba. Kamar kar ya juya sai kuma ya juyo a hankali ta ™araso ta ce, "Ga sallaya." Kallon hannunta yayi da take mi™o masa ya kalli fuskarta ta ce, "don Allah" ta faWa kamar zata yi kuka.

Ganin ya™i karSa sai ta tako gab dashi ta rataya masa a kafaWa ta juya da sauri ta koma ciki har tana gudu. Murmushi ya yi ya kalli sallayar kafaWarsa itama fara kamar kayan jikinsa, ya Wauke ta daga kafaWarsa ya ri™e ya fita daga gidan.

Tana kallon sa ta window har ya fita tayi dariya ta shiga ciki a guje ta Wauko mayafi ta yafa akan ta kasancewar rigar jikinta zata yi sallah. Key Win mota ta Wauka sai kuma ta tuna akwai babban masallacin juma'a a gaban layin ba za a rasa yin sallar Eid ba. Ajjiye key Win tayi ta fito ko sallaya ita bata nema ba ta kulle gidan ta tafi a ™afa.

Ai kam babu nisa daga gidan, ta tarar har za a tayar ta shiga sahu ta samu space na wasu mata da suke tsaye ta shiga ciki aka tayar da sallah. Bayan an idar tana ta gani ana ta hotuna amma ita murmushi take yi mutanen sun burge ta. Kowa ya sha kwalliya ana murnar sallah, ko iya ganin mutanen ma ai rahama ne.  A hankali take takawa wasu mata su biyu baza su wuce sa'aninta ba suna bayan ta suna ta gulamarta.

"Na rantse da Allah itace matar Tiger, kan bala'i daman haka take kyakykyawa?. Ita kuma Wan daba take so? Amma dai ta cuci kanta, ko da yake kyaun fuskarsa ta aura."

Nayla tana jin su tayi murmushi tana cigaba da tafiya a nutse. Juyowa tayi ta kalle su duk sai suka Wauke kai cike da jin kunya bata ce komai ba ta saka key ta buWe gidan ta shiga ciki.

Nayla hutawa tayi a gida kafin ta kira mutanen Saudia tana yi musu barka da sallah. Abiy ta fara kira bayan sun gaisa ta yi masa barka da sallah ya amsa daga nan ta kira kowa har su Hajja da Salma. Bayan ta gama ta koma ta zauna tana ajiyar zuciya tana tuna abinda mata nan suka ce, taSe baki kawai ta yi ta cigaba da danna wayar ta.

Cousins Winta ne suka zo hakan ya saka ta farin ciki suka zauna suna hira suna hotunan sallah. Omar ko da ya dawo ya zo shiga ya ji hayaniya zai ya koma ya fita daga gidan gabaWaya dan shi baya son ba™i Allah ya sani, ya fi son rayuwarsa shi kaWai kar wasu su dame shi. Sai dare suka tafi ta ji daWin zuwan su sosai tare suka yi girki aka ci gabaWaya. Har glaze donut suka yi mai daWi ta saka sauran a fridge saboda ba™i.

Bayan sallar i'sha Omar ya shigo da sallama kai tsaye inda take zaune ya ™arasa yana kallonta. Nayla ta kalle shi ta ce, "Sannu da zuwa." Bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi ya ce, "Kin raina ni ko?." Gaban Nayla ya faWi ta kalle shi alamun me na yi kana ta ce, "me na yi?."

"Kar na sake yi miki magana akan kuWin nan, in na sake yi miki magana baza ki ji daWi ba." Nayla tayi ajiyar zuciya dan tayi tunanin laifi tayi masa ta ce, "ai na yi lissafin, daman so nake ka zo na faWa maka."

"Uhu hum" ya faWa alamun yana jiran cigaban maganarta ta ce, "dubu Wari biyu ne" ta faWa kawai dan bata san ne zata ce ba, ta kashe kuWi a kalla ya yi miliyan Waya da wani abun, amma saboda kar ya ga kamar ™arya take in ta faWi asalin kuWin, kuma tsakani da Allah ta yi masa shiyasa ta ce haka.

Bai ce komai ba ya wuce zai bar wajan ta ce, "Akwai abinci." Ko kallon ta bai yi ba ya wuce cikin Waki. Ta bishi da kallo ta ce, "wannan ka rasa gane kansa."

Washe gari kasancewar an tafi sallah break babu batun zuwa aiki sai ta yi niyar zuwa gidan Didi da kuma gidan Mama Sa'adatu. Didi ce ta kira ta a waya ta ke sanar da ita kar ta ce zata je ta shigo cikin gari ita da AbdulHamid. Ranar gabaWaya bata ganshi ba, ko motsinsa ma bata ji ba, duk ta damu tana so taji ko ciwon kan ne ya sake dawowa bata sani ba. Kuma ita bazata iya shiga Wakinsa ba, gwara ta zauna ta jira shi in y fito sai su haWu.

Tana zaune gab da sallar azahar ita kaWai tana cin donut din ta na jiya aka yi knocking gate Win gidan. Hijjabi ta saka akan atamfar jikinta ta fita ta buWe. Bin matan take yi da kallo kamar ta san fuskarsu amma bata gane su ba, suna yi mata kama da wanda ta taSa gani amma sai ta kasa tunawa saboda basu yi kama da hausawa ba ko a shigar su.

Šaya daga ciki ta yi murmushi ta ce, "Sannu ´ata, Don Allah nan ne gidan Omar?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "eh nan ne."
"Na san baki san mu ba, Mu dangin mahaifiyarsa ne." Nan da nan fuskar Nayla ta washe da annushuwa ta ce, "Lah sannun ku da zuwa, bismillah ku shigo."

Suka shigo ta rufe gate Win daya daga cikin mutane ukun ta ce, "Allah yasa baya nan." Nayla ta ce, "baya nan, mu shiga" ta faWa tana yin gaba suka biyo ta a baya. A falo ta sauke su da fara'ar ta kaso musu ruwa da drink harda ragowar cincin da donut, ta haWo da fruits kankana da apple harda ´ar ™aramar wu™a ta yanka apple duk ta kawo musu ta ajjiye.

Zama tayi ta ce, "Ina yini." Suka amsa da fara'a suna tambayarta anyi sallah lafiya, ta amsa da lafiya lau. Šaga daga cikin su wacce ta kasancr babba a cikin su ta ce, "Ni sunana Zainab ni Yayar mahaifiyarsa ce, dani da mahaifiyarsa uwa Waya uba Waya, ni take bi. Wannan ™anwar mahaifiyarsa ce sunan ta Aisha mai sunan Yayarsa kenan, wannan kuma sunan ta Saroot."

Nayla ta yi murmushi cike da jin daWi ta ce, "ina ta tunanin inda na san fuskar, ashe a bikin Didi ne na Wan ganku kaWan.." murmushi suka yi  wacce tayi magana ta ce, "Tun farkon auren ku muka so mu zo sai aka shiga azumi, shiyasa yau na ce tunda mun shigo cikin gari zamu zo mu gaisa. Na san duk baki san mu ba, baki san kuma labarin mu ba. Ganin da ki ka yi mana a bikin Aisha ai baki san su waye ba, kin Wan gan mu ne kaWan kin wuce." Nayla ta girgiza kai cikin girmama su ta ce, "gaskiya na ji daWi sosai."

Saroot ta ce, "mu ma mun ji daWin ganin ki, ko babu komai zamu dinga zumunci. In ba haka ba za a iya haWuwa a hanya kowa ya wuce bamu zan juna ba, hakan kuma babban abin kunya ne a gare mu." Nayla sai murmushi take yi Saroot ta ce, "ki saka min number

Please Login or Register in order to submit comment