Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli Didi ya yi murmushi itama murmushin ta yi sannan ta ce, "Omar me ka ke ji a zuciyarta ka? Anya baza ka je asibiti ba?." Kamar jira ya ke tayi magana sai ya Wago ya ce, "Nima tunanin da nake yi kenan, ya kamata naje na ga likita wannan yanayin bana lafiya bane, wata™ila na kamu da ciwon zuciya."

"To kai meye a zuciyar taka da zai saka maka ciwo Omar?"AbdulHamid ya faWa yana kallonsa. Omar ya kalle shi ya ce, "Komai ma akwai."

Abdulhamid ya ce, "Ba sai ka je wani asibiti ba, zama ya kamata ka yi ka tuna daga yaushe ka fara jin haka, in ka tuna rana da lokacin sai ka tuna me ka rasa a lokacin wanda kafin ka fara jin wannan yanayin yana tare da kai, bayan ka rasa shi ka fara jin abinda ka ke ji. Ko da ace wayarka ce ka tuna ita ka rasa daga lokacin da ka fara jin hakan da zarar ka sake mallakar wayar zaka daina jin abinda ka ke ji, duk abinda ka binciko ka ga shine silar shigarka wannan yanayi to tabbas kana matu™ar ™aunarsa Omar!, kana yi masa soyayya ba ta wasa ba, soyayya ka ke yi masa wacce baza ka iya ha™uri da rashinsa ba."

Omar ya zuba amsa ido yana kallonsa ko ™ifta ido baya yi. AbdulHamid ya ce, "in mun tafi ka zauna kayi tunanin, duk abinda ka rasa a lokacin zaka fahimci maganata gaskiya ce."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya kalli Didi da take kallonsa ta ce, "abinda ya kamata ka yi kenan, ta haka ne kaWai zaka samo maganin damuwarka." Omar a raunane ya ce, "to zan yi. Amma ina neman alfarmarki don Allah kar ki sake yi min maganar yaushe zan kai takardar saki, ki ™yale ni na gama da abinda yake gabana kafin komai ya biyo baya. Ta lafiyata nake yi, wannan yanayin ya canja ni gabaWaya ko aiki bana iya yi. An buWe shaguna har guda huWu amma babu wanda na iya zuwa na gani saboda wannan abinda yake damuna. Rauni ba bai yi daidai da zubina ba, ni ba mutum mai rauni bane wallahi, ki bari na samo abinda ya saka zuciyata rauni in ya so sai mu yi magana. Ni nace bana son aurenta kuma ni zan raba shi."

Didi ta ce, "To Omar na daina." Kai ya girgiza bai ce komai ba Didi ta ce, "ga abinci nan na kawo maka in ka ci sai ka sake shan magani, Allah ya kawo mafita." Bai amsa ba AbdulHamid ne ya amsa da amin suka tashi suka tafi dan su bar shi yayi tunani.KRB3P033
Arewabooks@nanahaleema11.

A mota AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, "Omar bazai iya sakin yarinyar nan ba, yana matu™ar ™aunarta wallahi, yana yi mata soyayyar da bai san yana yi mata ba."

Didi ta ce, "na so na fahimci hakan, amma kuma in na tuna waye shi sai naga anya zai yu kuwa?. Ka duba har yanzu shi baya kawo ta cikin damuwarsa, tunda gashi ka ji ya ce shine yace baya so kuma shi zai raba. Ni ban Wauka yana da hankalin da ya san ko nida kai ya furtawa ya saketa ta sa ku ba, ya ™i furta kalmar koda wasa."

AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "yana da hankali da ilimi fa, ta ya zai aikata hakan? Saki ko baka je makaranta ba indai kana social media yadda malamai suke wayar da kai a kansa ai zaka sani. Balle ga makarantar da ki ka ce yana attending online, ko ya manta wani abun zai tuna indai yana bibiyar karatun. Ki zuba ruwa a ™asa ki sha, Omar yana sonta wallahi, baza ki bini bashin rantsuwa ba, Omar bazai iya sakin yarinyar nan ba."

Didi ta yi murmushin jin daWi ta ce, "in hakan ya kasance zan fi kowa murna da farin ciki. Amma anya Omar zai je gidansu Nayla kuwa? Har yanzu bai amince da soyayya ba fa."

"Ai daman a yanzu bazai amince ba, sai ya sake ji a jikinsa sannan zai damu. Ke wacce damuwa ki ka taSa ganin ta saka shi rauni haka har da zazzaSi?." Didi ta ce, "Wallahi babu, ko lokacin yarinyar nan Narma bai koma haka ba, ya cigaba da rayuwarsa normal kamar komai bai faru ba, amma ita kaga harda ciwo. Shine nake tunanin a tsakanin Narma Da Nayla Win wa yake so?."


"Wacce tunaninki ya baki."
"To abun ne da Waure kai, na farko ka ga Narma itace wacce ya furta min yana sonta, amma ko kusa bai shiga irin wannan damuwar ba. Ita kuma Nayla itace ya ce baya so amma ya shiga damuwa mai tarin yawa har ta haifar masa da rauni da ciwo. Kamata ya yi ace akan Narma ya shiga damuwa tunda ita yake so ba wai Nayla ba."

Didi ta yi shiru ta sake cewa, "Kenan dai Nayla yake so da gaske ba Narma ba, amma meyasa a baya ya ce yana son Narma?." Ya ce, "Wata™ila wani abun ne daban ba soyayya ba."

Didi ta ce, "Bayan ni a duniya Narma itace mace ta farko da Omar ya samu kusanci da ita, magana da ita a waya da komai ma a duniya. Amma meyasa ko lokacin da ya ce yana sonta ko waya tayi masa sai ya ga dama yake Wauka? ko da suka rabu ban ga alamun ya damu ba, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi akan sana'arsa. Amma ita kuma Nayla...." Sai kuma tayi shiru bata ™arasa ba.

AbdulHamid ya ce, "ki bar wannan lissafin, Omar yana sonta kawai ki yarda, ita waccan labarinta ya wuce ta shigo rayuwarsa ne dan ta zama silar canja shi, amma asalin wacce yake ™auna wannan ce. Labarin zuciya ai a tambayi fuska, kina kallonsa kin san tsananin kewarta da son da yake mata ne ya mayar dashi haka, har rama yayi ga ciwo da yake fama dashi. ina shiga falon muna haWa ido dashi na san Omar ya faWi a ™asa warwar wallahi" ya faWa yana murmushi.

Didi ta yi murmushin farin ciki ta ce, "Naji daWin wannan abun abun wallahi, Omar na son Nayla. Na rasa inda zan saka kaina saboda farin ciki." Abdulhamid ya yi murmushi yace, "ke dai kawai ki tabbatar da ya je gidan su."
"0n sha Allah" ta faWa cikin zumuWi tana murmushi.

" " " " " " " "

     Yadda ya ke zaune zai tabbatar maka da ransa a matu™ar Sace yake, ya zubawa waje Waya ido yana kallo kafin ya daki table Win gabansa ya ce, "Wallahi sai Narma ta dawo wajena, babu wanda ya isa ya saka na sake ta wallahi." Abokinsa da yake gefensa ya ce, "calm down maza, haba wannan ba ajinka ba ne."

A fusace Ashraf ya ce, "har ni Dad Winta yake cewa wai in ban sake ta ba zasu kai ni court, ka ji rainin hankali. Ai zama da Narma yanzu na fara shi wallahi, ban gaji da zama da ita ba, a bari duk lokacin da na gaji da morarta sai na saketa. Amma yanzu ban kammala ba tukunna." Dariya sosai abokin nasa ya yi ya ce, "To wai kai ka san baka son Narma meye na damuwa kuma haka?."

"Saboda ban gama abinda na aure ta dan shi ba. Yarinyar nan ta wahalar dani, babu ta hanyar da ban biyo mata ta amince dani ba ta ™i. Ban taSa jin sonta a zuciyata ba, haka ban tana jin ina qaunarta ba. Da fari dai na Wauka soyayya ce, amma daga baya na tabbatar da sha'awarta kawai nake yi. Har gobe ina da bu™atarta wallahi, sai yanzu ma tabbatar da Ikky itace wacce nake so ba Narma ba."

Sharif ya murmusa ya ce, "To na ga ai ka samu abinda ka ke so har na watanni da yawa, har yanzu baka kashe ™ishin da kake ji a kanta ba?."
"Sharif na kashe, sam bata wani burge ni sai in amfanin ta ya tashi, amma ni kaWai a san abinda yake jikinta. Ni ne mutum na farko da tayi tarayya dashi, ina da tabbacin har gobe babu wani ni sai ni Win kawai. Ban gama da ita ba har yanzu, ban gama da mallakarta ba har yanzu, babu wanda ya isa ya aureta sai na gama abinda nake so."

Sharif ya ce, "to ai matarka ce har yanzu." Ashraf ya ce, "iyayenta sune suke so su raba mu kuma wallahi ba su isa ba." Sharif ya ce, "Mtsw! Ni fa tun daga kan ka da Narma shikenan mata masu shiga half niked Win nan basa burge ni, da zarar na ji sun burge ni zan saka a raina ba soyayya bace jikinsu ne kawai ya burge ni. Ka duba Ikky da ka ke magana yanzu, yarinya mai hankali ko yaushe cikin shiga mai mutunci da rufe jikinta take, amma ka rufe ido ka ce kai sai Narma saboda surarta da ka ke gani a bayyane. Yanzu gashi ka tabbatar itace wacce ka ke so, Narma kuma jikinta kawai ka ke so kuma ka samu."

Ashraf ya ce, "Kai ka san sau nawa Narma ta karya min alwala? Ka san sau nawa Narma ta saka ni wanka ban shirya ba?. Haka zata saka kaya jiki a bayyane ta zo tayi hugging Wina, don Allah wanne yanayi ka ke tunanin zan shiga?" Ya ™arasa faWa yana dariya.

Sharif ya yi dariya sosai ya ce, "i'm sorry, she's your wife dole zaka ji kishi, but yarinyar nan she's too sexy." Ashraf ya ce, " Sorry for what? Do you think i have been jealous of what you've said about her? Mtsw shirme. Wallahi sam bana kishin Narma, ban jin wani abu a zuciyata a kanta in dai ba sha'awa ba. Yadda ka yi maganar Ikky yanzu na fi jin haushi a kanta."

"Ita Ikky kana sonta ne ba surarta ka ke so ba, ita kuma Narma ba ita kake so ba jikinta ka ke so. Na tabbatar iri ka ma su son jikin Narma suna nan da matu™ar yawa saboda Narma she's too hot. Wacce ka ke so ita zaka yi kishi ba wacce ka ke sha'awa ba daman ai" Sharif ya faWa yana kallon sa.

Ashraf ya ce, "ni yanzu zan sake komawa Abuja, dole a dawo min da matata, in na ™ara ko da wata biyu ne tare da ita sai mu rabu na dawo wajan Ikram Wina."

"Ka san Sen bazai baka wanna damar ba."
"Nima kuma bazan sake ta ba wallahi, sai dai ayi bala'i da masifa."
"Kar ka yi haka Ashraf, da mahaifinka da mahaifinta abokai ne matu™a. Kuma mahaifinka gov ne, kar ka yi wani abun da zaka Sata masa harkokinsa. Ko yanzu ka rabu da Narma ai ka ci riba." Ashraf ya ce, "Yadda take ta™ama da bata sona so nake na nuna mata ikona a kanta, wallahi so nake sai tayi shekara biyu sannan na saketa."

Ya yi dariya ya ce, "Wannan ai mugunta ce, tunda ka samu abinda ka ke so ba sai ka share ba kawai." Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "za dai mu ga abinda ya kamata ayi" ya faWa yana Waukar wayarsa ya cigaba da dannawa.

" " " " " " "

Kamar yadda AbdulHamid ya bawa Omar shawara ya yi nazari ya tabbatar da Nayla ce abinda ya rasa a lokacin da ya fara jin wannan yanayi, kenan dai ita yake so meye?. Shi dai ya san ba haka ake jin so ba tunda ya taSa son Narma a baya, amma ba haka ya ji a kanta ba gabaWaya yanayin bai kai haka ba.

To in har abinda ya ji akan Narma shine so meyasa bai shiga yanayin da ya shiga a yanzu ba? Sannan ita Nayla me yake mata kenan? ˜inta yake yi ko kuma wani abun ne daban?. Babu mai bashi amsa sai kawai ya share maganar ya danne zuciyarsa yana ™o™arin cigaba da harkokinsa amma ya gaza hakan.

Bayan kwana biyu da zuwan Didi da daddare suka sake zuwa, yana gidan shi kaWai a zaune amma yanzu aikin yanka fatar takalmi yake yi. Tunda suka gaisa da su Didi yana yanka takalmin sai ya ma rasa ta yadda zai yi kawai ya ajjiye.

AbdulHamid ya ce, "Ya jikin?." Omar ya ce, "na samu sau™i." AbdulHamid ya ce, "Ka samo abinda ka rasa Win kuwa?." Omar ya sauke numfashi ya ce, "Ni babu abinda na rasa balle na ce shi nake so, kawai ina jin mutuwa zan yi shiyasa nake jin wannan yanayin. An ce daman in zaka mutu kana ji a jikinka, wata™ila ita Win nake ji" ya faWa cikin gaskiyarsa.

AbdulHamid ya ce, "A'a Omaar, ka dai sake tunani, akwai wani abun bayan wannan." Omar ya ce, "to meye? Na rasa gane me nake ji Win." Didi ta kalle shi a nutse ta ce, "Meyasa ka ke zaune a gidan nan? Na Wauka kana gidanmu ne ai." Omar ya ce, "kawai ina so na zauna a nan ne."
"Kana kewar matar gidan kenan?." Kallonta yake yi ko kiftawa baya yi kafin ya janye ido ya ce, "amma meyasa ki ka ce haka?."

Didi ta ce, "Wanda ake kewa shi ake zama a inda yake saboda a dinga tunawa ana ganin kamar yana tare da kai. In kana kewar mutum kana kallon hotosa in baka dashi har inda yake zama kana gani, kana zuwa ka zauna inda mutum yake zama dan ya rage maka abinda ka ke ji a zuciyarka. Shiyasa nake tunanin ko kewarta ka ke yi."

Omar ya Waga kai sama ya sauke, ya kalle ta sai ya sauke kai ™asa ya furzar da iska ya ce, "indai har haka ake jin kewar wani tabbas ina kewarta, in ba a Wakin da take kwana na kwanta ba bana jin daWi ko kaWan. Ina kewarta Didi, ina kewarta sosai!" Ya faWa yana girgiza kai alamun tabbatarwa. Didi ta yi murmushi mai nuni da zallan farin cikin da ya mamaye mata zuciya, ta kalli mijinta shima ita yake kallo.

Ta sake kallon ta ce, "in dai har kana kewarta
kenan kana sonta?." Kallon Didi ya sake ya yi yana juya ™wayar idanunsa akan fuskarta kamar mai neman wani abun a kan fuskar tata. Ganin ya zuba mata yana ™are mata kallo sai Didi ta ce, "Eh Omar, sai kana son mutum ka ke jin kewarsa irin wannan."

Šan ™aramin tsaki yayi ya ce, "ni kewarta na ce ina yi ba so ba, bana sonta kamar yadda na faWa miki a baya. Na yarda ina kewarta kamar yadda ki ka ce, amma ba wai so ba." Didi ta sake yin murmushi mai sauti ta ce, "Omar kana sonta, so ba Wan kaWan ba, soyayya mai yawa ka ke yi mata."

Sai ta fusata shi ya mi™e a firgice ya ce, "na ce miki bana sonta, bana son aurenta dole ki ka yi min na karSa! Meyasa ki ke maimaita ina sonta bayan ni ba haka nake ji zuciyata ba?."

AbdulHamid ganin yadda Omar Win ya birkice sai ya ™arasa kusa dashi ya dafa kafaWarsa ya ce, "Kwantar da hankalinka, koma ka zauna." Omar ya zauna yana cewa, "matarka ce take son tarwatsa min ™wa™walwa, na ce mata ba sonta nake yi ba dole sai ta ce ina sonta ne?" Ya ™arasa faWa a sanyaye yana kallonsa.KRB3P034
Arewabooks@nanahaleema11.

Didi ta bishi da kallo sannan ta yi dariya tana Soye farin cikin ta ta ce, "to meye na fusatar dan na ce kana sonta?." Dafe kai ya yi da hannunsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Didi ta tausasa murya ta ce, "Na san ka so Narma a baya ko? Sannan....." katse ta ya yi  ya ce, "Shiyasa na ce miki ba sonta nake yi ba, saboda abinda na ji akan ´ar Senator daban itama na ta daban. Kuma ke kika tabbatar min da ina son Narma, kinga kenan ita wannan ba sonta nake yi ba."

Didi ta ce, "Ka nutsu ka bani amsar tambayar da zan yi maka don Allah."

"kar ki tambayi abinda zai Sata min rai."
"To YaMar" ta faWa tana kallonsa dan ta ga reaction Winsa. Ai kuwa da sauri ya kalle ta ya ce, "Maimaita abinda ki ka ce." Didi ta ce, "cewa na yi YaMar." Lumshe ido ya yi ya buWe yana kallon wani wajan daban ya ce, "meyasa ke ban ji komai a raina ba da kika faWi wannan sunan nan? Ita kuma duk sanda zata faWa sai gabana ya faWi" ya juyo ya zubawa Didi ido tare da zaro su waje ya ce, "Na shiga uku! Anya Didi ba da aljanna kika haWa ni zama ba?."

AbdulHamid da yake kallon dramar Omar ya yi dariya Didi ma murmushi ta yi ta ce, "ta ya gabanka zai faWi dan na faWi sunan da matarka take kiran ka dashi? ni fa jininka ka ce ba mata ba, taya zaka ji irin abinda ka ke ji a lokacin da matarka ta faWa?."

Shiru ya yi yana sauke numfashi a hankali, a tausashe  Didi ta ce, "Omar na san ka so Narma a baya, abinda nake so na tambayeka shine; lokacin da ka ke tsakiyar sonta ka ji irin abinda ka ke ji a yanzu a kan Narma?." Kai ya girgiza alamun a'a yana kallonta, ta ce, "lokacin da ku ka rabu ka ji irin wannan yanayin a zuciyarka?." Nan ma ya girgiza mata kai alamun a'a.

"Ka yi kewarta kamar yaddaka yi kewar Nayla?, zuciyarka ta buga a lokacin kamar yadda yanzu take bugawa? Ka ji rauni a lokacin kamar yadda ka ke ji yanzu? Ka yi zazzaSi kamar yadda ka yi yanzu?. Ka jure zama da Narma kamar yadda ka jure zama da Nayla? Ka ji zafi a zuciyarka in wani ya yabi wani abu na Narma kamar yadda ka ji zafi a lokacin da aka yabi ™afar Nayla?." Omar ya yi tsitt yana sauraren Didi yana kuma kallon ta. Ajiyar zuciya Omar ya yi ya girgiza kai ya ce, "A'a duk ban ji ba."

"Amma ka ji kishi da wani ya biyo Nayla ya ce yana sonta, ka ji zafi da ka ga ™afarta na zaga social media ana yabonta, ka ji babu daWi a lokacin da nake hirar samarinta. Ka damu da rashin lafiyarta har jikinka ya yi sanyi kana so kaji ya take, ka jure zama da ita sama da ko wacce mace a duniya, zuciyarka ta karye akan rashinta har ka ke jin kanka kamar kwalin da babu komai. Haka ne ko Omar?." Omar ya yi ™aramin tsaki cikin gajiya ya ce, "Haka ne Didi, ki kai ™arshen maganarki na gaji da wannan tambayiyon."

Didi ta ce, "Omar ba son Narma ka yi ba." Ya Wago ya sake kallonta kafin ya musa ta ce, "Ta ya zaka WanWana karayar zuciya bayan Narma itace take sonka ba kaine ka ke son ta ba? Itace mace ta farko da ka samu kusnaci da ita shiyasa a lokacin ka Wauka sonta ka ke yi amma ba so bane. Zaka WanWana karayar zuciya da rauni ne in ka rasa wacce ka ke so Omar!" Ta faWa tana kallonsa kamar yadda yake kallonta.

Abdulhamid ya ce, "hakan yana nufin kana son matarka so mai yawa Omar, duk abinda ka ke ji a yanzu shi ake kira da tsananin so. Baza ka taSa dawowa daidai ba in dai baka je ka dawo da ita ba."

Omar ya yi shiru yana sauraren su, jin maganarsu yake yi kamar film ko kuma tatsuniya. Ta ya zasu ce masa wai Nayla yake so ba Narma ba? Bayan ya san Narma ita ce akace ya so ta? Shi abinda yake ji akan ta daban, abinda ya ji akan Nayla daban. Ta ya zai banbance soyayya da kuma abinda Didi take faWa? Shi gabaWaya sun saka shi a tsaka mai wuya.

Omar ya kalli Didi ya ce, "Didi ba sonta nake yi ba, na yarda dai ina kewarta kamar yadda ki ka ce, ina kewarta sosai na yarda da wannan amma ba wai ina sonta ba, ki bar zancen nan don Allah." Didi ta ce, "shikenan na bari Omar, ka yi tunanin maganar da na faWa maka, in ka tabbatar ba haka bane tana gidan ™anwar mahaifiyarta ka je ka sallame ta."

Ya lumshe idanu ya ce, "Na faWa miki ki daina yimin zancen nan amma kin ™i ji." Didi ta ce, "kai da ka ce baka sonta meye na damuwa dan ina znacen zaka sake ta? Kaga....." jajayen idanunsa ya zuba mata hakan ya saka ta yi murmushi kawai bata ™arasa ba.

AbdulHamid ya ce, "Ka yi tunani Omar, in kana bu™atar shawara ™ofa a buWe take zaka iya kirana. Wata shawarar namiji yana da bu™atar tattaunawa da Wan uwansa namiji, na san baka da aboki shiyasa nake so na zamar maka aboki Omar."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "to" ya kalli Didi ya ce, "na gode, ku je g1da kawai" ya faWa yana jingina da kujera yana tunani. Didi bata sake cewa komai ba dan ta riga ta gama dashi gabaWaya. Ta san ko ya zai motsa sai ya tuna da kalamanta, a cikin kalamanta kuma dole ya samo gaskiya.

Omar kansa ya kulle ya kasa tunanin hakan ya saka ya tashi shima ya fita daga gidan saboda in ya zauna tunani zai saka kansa ya yi bindiga.

Nayla ta kwashe sati biyu cif a gida, duk kauce-kaucen Omar ya tabbatar da maganar Didi gaskiya ce. Abin ya wuce gizo da take yi masa mafarkinta kawai yake yi, indai zai kwanta ya tashi sai ya yi mafarkinta. Zuciyarsa na bugawa a kanta ya kan rasa inda zai saka kansa, sai ya ruWe ya rasa inda zai je ya samu sassauci. GabaWaya ya susuce yana gab da zama zararre akan Nayla. Ya yarda da Nayla yake so ba Narma, sai yanzu ya tabbatar da inda ace abinda yake akan Nayla shi yaji a lokacin Narma da babu halittar da ta isa ta raba shi da ita, kamar yadda ta nemi ya gudu da ita tabbas zai iya aikata hakan. Sai dai kash! Ba akanta yake jin wannan yanayi ba, akan Nayla yake jinsa!.

Babban abinda yake Waure masa kai shine in dai son Nayla yake yi ita Narma me ya yi mata a baya? Sonta ya yi ko tausayinta yaji ko kuma meye bai sani ba.

Hankalinsa ya gama kaiwa ™arshe wajan tashi, ya tsayar da tunaninsa waje Waya ya kuma yarda da gaske dai Nayla yake so ba wai da wasa ba. Abin ka ga soyayyar farko, in yana tunaninta jikinsa har karkarwa yake yi saboda azabar da zuciyarsa take yi masa, fatar jikinsa har Waukar zafi take yi saboda yanayin da zuciyarsa take ciki. Nauyi ™irjinsa yake yi masa sosai, har ya kai ya kawo in ya motsa yana jin zafi a ™asan zuciyarsa. In ya yi tari sai ya ji numfashinsa yana neman tsayawa cak, sai ya ja numfashi da ™arfi sannan yake samun sassaucin nauyin da yake yi.

Ranar asabar bayan sallar azhar ya kasa jurewa, ya rasa ya zai yi ya kasa cin abinci tun safe. Ya haWa tea amma ya kasa sha ruwa kawai yake zubawa cikinsa. Ya kasa cin komai, baya sha'awar cin komai balle ya nema ya zuba a cikinsa, duniyar yake ji ta yi masa zafi tana juya masa. Nayla kaWai yake so ya gani, itace abincin da idanunsa da zuciyarsa take marari, muryarta yake so ya ji ta furta sunan da ta saba faWa masa. Ya tabbatar da ya ji wannan suna daga bakinta duk abinda yake ji a zuciyarsa zai daina ji. Ganin yana neman kashe kansa da tunani sai ya kira Didi a waya dan tunda tazo basu sake magana ba, tana Wauka kafin su gaisa ya ce, "Didi meye abu na gaba?."

Didi ta ce, "Ya naji magnarka haka, Omar ko ka je asibiti a duba ka?."
"Didi gab nake da zaucewa wallahi, tafasa jinina ake yi kullum" ya faWa a sanyaye." Didi ta ce, "Allah ya kawo mafita Omar."
"Ina tambayarki, meye abu na gaba?."
"kamar me kenan?."
"A ina zan sameta?."
"Ita wa kenan?."
"matata!" Ya faWa kansa tsaye ba tare da wani tunani ba.

Didi ta yi dariya mai sauti ta ce, "ban gane abu na gaba ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Me aka ce zan yi?." Didi ta ce, "akan dawowarta?."
"Uhum."
"Gidan iyayenta zaka je."
"Ina ne gidan? Ki tura min address Win gidan zan je."

Didi ta

Please Login or Register in order to submit comment