Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rasu. Kuma ni ai ba ba™uwa ba ce ba Didi, zaman ki a nan zai yi min daWi fiye da yadda ki ke tunani, na tabbatar in ki ka zauna a ranar zan fara jin daWin zaman gidan nan. Don girman Allah ki kwana a nan Win, in kuma ba haka ba mu koma can gidan sai mu kwana tare.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Ubana ma ai ya yi min dole, harda rantsuwa kuma yana faWa min baya karya masa rantsuwa, dole na amince ko bana so. Nayla tayi dariya jin daWi ta ce,  YaMar ya kyauta, ya yi daidai. Yanzu me zaki ci?. Didi da murmushi ta ce,  haWe min kai zaku yi kenan? Shi yana tsaye ™i™am kamar soja. Nayla ta ce,  ni dai yanzu ki faWa min me zaki ci?.

 Keda baki da lafiya ina ke ina girki? Ki bari in zan ci zan girka da kaina. Nayla ta zaro idanu ta ce,  ki yi girki a gidan nan? Ai bazai yu ba Didi. Yanzu ki ka ce matsayin uwa kike a gare mu, kuma sai na bari ki yi girki? Lallai bani da kunya ta faWa tana dariya kafin ta ce,  Ni fa ganin ki har ya saka na daina jin ciwon kan ta faWa tana tashi ta shiga ciki.

Didi ta bita da kallo tana murmushi kafin ta kalle shi ta ce,  yarinya bata da lafiya baka damu ka sani ba ko Omar? Yanzu in wani babban ciwon ne fa? In wani abun ya same ta wallahi kai kanka baza ka ji daWi ba. Ka gyara zaman nan naku don Allah, ba dan komai ba ko dan saboda lafiyarta. Bai ce komai ba amma shi kansa bai ji daWi ba a ransa, in ya tuna yadda ta dinga lallaSa shi tana bashi tea hakan yana yi masa daWi a lokacin, shima zai so ya kula da lafiyarta kamar yadda ta kula da tashi.

Basarwa ya yi yana kallon Didin ya ce,  nima ai bani da lafiyar yana gama faWar hakan ya wuce zuwa Waki.

Didi tashi tayi ta bi Nayla kitchen ta same ta a tsaye kamar mai nazari, ganin Didin sai ta ce,  Yauwa Didi, me zan girka miki?. Didi tayi murmushi ta ce,  duk abinda ya yi miki.
 A a, ina so na san abinda ki ke so, meye favorite Win ki?.
 Ki dafa Omar s favorite, nima Ina so. Nayla tayi ´ar dariya ta ce,  har na tuna lokaci da ki ke faWa min yana son jellof rice, pasta, indomie and awara. Yanzu ni me zan dafa?.

Kafin Didi tayi magana ta ce,  okay, let me prepare some delicious jellof rice for my Didi ta faWa tana Waukar waya tana danne-danne. Ba jimawa ta ajjiye ta ce,  kin ce jellof dWin mai kifi ko?. Didi ta yi murmushi ta ce,  ba sai kin saka ba, a ina za a samu yanzu?.

 Akwai inda nake order, yanzu zaki ga an kawo min. Didi ta bi kitchen Win da kallo cikin burgewa, yana nan tsaf dashi sai ™hamshin turaren wuta yake yi ta ce,  kitchen Winki very neat Nayla. Murmushi tayi bata ce komai ba ta fara haWa kayan girki.

Gyaran kayan miya ne bata ™auna, ta Wan yamutsa fuska ta ce,  I hate this wallahi, a gida ko me zan dafa bana gyarawa sai dai a yi min. In ba haka ba sai dai na ha™ura da cin ko meye. Sai ta bawa Didi tausayi, ta san Nayla ´ar gata ce ajin ™arshe, komai yi mata ake yi a gidansu amma gashi ta ™are rayuwarta a haka. A sanyaye Didi ta ce,  kawo na gyara miki. Nayla ta wara ido ta ce,  So ki ke unborn ya fara jin haushina tun yana ciki? A a bari zan yi da kaina. Waya aka yi mata sai ta kalli Didi ta ce,  Kin gani, rider Win ne yake kira yanzu zasu kawo.

Šaukar wayar tayi tana bashi address, ba jimawa ya sake yi mata waya ta fita ta je ta karSa ta dawo. Didi ta kalle ta bayan ta ajjiye tana buWewa ta ce,  meyasa ki ke siya da kuWin ki? Ai ha™™in Omar ne ya siya ba ke ba.

Nayla ta ce,  Didi ni ba siya nake yi ba fa, dan ni bai dame ni ba gabaWaya. Kuma ni bana siyan abu sosai, da azumi ne akwai na siya kaji shima sai gab da azumin zai ™are sannan na siya.
 Duk da haka dai Nayla. Nayla tayi mumurshi bata ce komai ba, Didi ta karSi gyaran kifin ta dole ta ta bata ba dan ta so ba.

Viniger ta bawa Didi ta karSa ta gyara kifin su na ta hira cikin nishaWi. Šan ri™e kai Nayla tayi alamun ciwo Didi ta ce,  ciwo ko? Sannu Nayla. Na ce ki ji ki huta amma kin ™i, gaskiya ya kamata ki je asibiti a duba aga meye yake kawo miki wannan ciwon kan, kina yawan yinsa. Nayla ta ce,  Ranar Mondy zan je in sha Allah, Ko ma azumi bazan Wauka ba ranar.

 Ai gwara haka, Allah ya ™ara Lafiya.
 Amin Didi.
 Kina da ™o™arin azumi Nayla, kina burge ni sosai saboda kina da ri™o da ibada sosai.
 Bana jin wahalar azumi, na riga na saba in ba ban yi ba bana jin daWi. Yanzu haka na gama sitta shawwal kuma har wanda ake bina na yi.

Didi ta ce,  kin yi ™o™ari sosai. Allah ya kar nan gaba Omar ya hana ki azumin litinin da Alhamis Win nan, ko da yake ma ai kina wajan aiki ba yini ki ke a gida ba. Nayla da mamaki ta ce,  Kawai sai ya hana ni ibada Didi?.
 Eh mana, baki san maza suna hana mata yin azumi ba?.
 Na sani, akwai cousin Wina itama haka take kamar ni, amma da tayi aure ta daina. Har ta kan cemin tana so ta cigaba amma mijinta ya hanata
 Ashe ma kin sani Didi ta faWa tana ajjiye abinda yake hannunta.

Nayla ta ce,  To wai Didi meyasa suke hana azumi? Ba sa so ana yin ibadar ne ko me?. Didi tayi ´ar dariya ta ce,  ba haka bane, kawai saboda shiga ha™™in su ne. Nayla ta Wan yi jim kafin ta ce,  Kamar ya shiga ha™™i? Kawai dan mutum yana azumi sai ya shiga ha™™in wani?.

Didi ta sake yin dariya ta ce,  Zamu jira mu gani, in har Omar ya hana ki yi zaki fahimci me nake nufi, in ma bai hana ki Win ba ma zaki gane.

Nayla ta ce,  no, ina so na sani yanzu.
 Zaki sani Nayla, faatana da burina Allah ya daidaita zaman ku. Nayla tayi ajiyar zuciya Didi ta cigaba da taya ta aiki tana murmushi. Zata so ganin ranar da Nayla da Omar zasu zama ma aurata kamar kowa, zata so ta ga irin so da ™aunar da Omar zai nuna mata, zata so ta ga tattali da riritawar da Omar zai gwadawa Nayla. Kuma zata iya rantsewa Omar yana daga cikin mazan da zasu iya hana Nayla yin azumi, ba dan komai ba sai dan za a shiga ha™™insu. Haka kawai take ji a ranta hakan zai faru, ba dan Omar Win ya faWa mata ko wani dalili ba, haka kawai ta san da™yar hakan bai faru ba.

Nayla ta kalli Didi ganin tana murmushi ta ce,  Didi wallahi you re so beautiful. Didi tayi dariya ta ce,  Nayla ban da tsokana.
 Allah kuwa, Da na ga Anties Win ku sai na tabbatar da gadon kyau ku ka yi dan dukkan su ma sha Allah. Ashe ma halfcast ne ku
tunda dangin Mama ´an Chad ne, Shiyasa ku ke da kyau. Kin san anyi analysis babu wanda ya kai halfcast kyau a duniya.

Diid tayi dariya ta ce,  Omar dai yana da kyau amma ba ni ba.
 Ai kuna kama dashi sosai, ana ganin ki a san ke jinin shi ce.
 Kama ta jini ba, amma Omar da mahaifiyar mu yake kama completely. Manyan idanu kawai ya fita, idanunta na da girma sosai itama kawai na shi ya fi nata ne sosai. Tana da kyau sosai, tana da kyaun da ake kira kyau shiyasa Omar da ya gadota ake kallonsa in ya shiga waje. Zan nuna miki hotonta zaki gani.

Nayla tayi murmushi ta ce,  Allah ya gafarta musu. Didi ta amsa da amin suka cigaba da hira har suka gama girkin tsaf suka wanke kayan.

Didi ta kalle ta ta ce,  Tunda naga har wata apron ki ke sakawa a kitchen Win, cire ta mu je mu ci abincin. Nayla tayi murmushi tana kwance igiyar apron Win ta ce,  bana son Sata kayana ne.

Didi ta ce,  jeki ki shafa turare a jikinki da hannunki ki dawo. Nayla bata musa ba ta fita taje ta dawo. Tana dawowa ™hamshin turaren ya shiga hancin Didi tayi murmushi ta ce,  turaren kam akwai ™hamshi, kin san kifi yanzu sai ya ma™ale miki a jiki. Na kai abincin falo na ajjiye, na ji dawowar Omar daga masallaci ya shiga Waki. Ki je ki ce masa ya zo mu ci abinci.

Nayla ta wara idanu waje ta ce,  na je ina Didi?. Didi ta ce,  Wakinsa mana, ki je ki ce na ce ya fito ya ci abinci. Nayla ta ce,  A a Didi, ke dai ki je da kan ki. Didi ta ce,  kina matarsa baki je ba sai ni zan je na ce ya zo?. Nayla ta ce,  eh gaskiya, ni bazan iya ba.

Diid ta ce,  to umarni nake baki matsayin yayarki, ki je ki ce masa ya zo ya ci abinci. Nayla kamar zata yi kuka ta ce,  Didi ba ya cin abincin gidan nan, in na yi masa tayi wula™anta ni yake yi yayi min banza ko kallona ba ya yi, ina jin babu daWi shiyasa na daina cewa ga shi. Kuma ni ban taSa shiga Wakinsa ba wallahi!. Didi jin har tana saurin rantsuwa ya saka ta dariya ta ce,  Nima ban ce kina shiga Wakinsa ba ai Nayla, Amma ki je ki faWa masa ma tabbatar yau bazai wula™anta ki ba, Kawai ki je.

Nayla tayi rau-rau da ido ta ce,  Didi don Allah&  Didi ta katse ta ce,  just go Nayla. Nayla ta Wan yi shiru tana tunanin ta yadda zata aikata abinda Didi ta ce, ta Wan sauke numfashi kana ta ce,  to bara na Wauko hijjab. Didi ta dakatar da ita ta ce,  hijjab Win me zaki saka? Wajan mijinki fa zaki je.

 Ban saba zama babu hijjab ba, kuma ni ban taSa zuwa wajansa babu hijjab ba gaskiya.
 Haba Nayla, Ina ganin ki mai wayo, mai ilimi ya zan same ki da haka? Dan zaki je wajan mijinki sai kin saka hijjab?. Wuce ki je ba sai kin Wauko komai ba, daga baya ma tattauna wannan katoSarar ta ki. Nayla ta yi ajiyar zuciya tana kallon Didi kamar ta yi kuka, tare suka fita daga falon, Didi ta nuna mata Wakim alamun ta je. Nayla bata da zaSin da ta wuce fara takawa zuwa Wakin Omar.

Didi ta bita da kallo tana murmushi ta ce,  in sha Allah kafin kwana biyun nan zan saka ki rage wani abun da ki ke yi Nayla, zan san yadda zan yi kusancin ku ya ™aru fiye da yanzu. KRB3P017
Arewabook@nanahaleema11.

Nayla ayatul kursi kawai take karantawa a zuciyarta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta Wan ™wan™wansa ™ofar a hankali. Omar yana zaune akan stool na gaban mirror ya Wora ™afa kan Waya yana kaWawa kamar wani basarake idanunsa a lumshe, shi kansa bazai ce ga abinda yake damunsa ba haka nan yake jinsa uncomfortable.

Yana ji ana ™wan™wasa ™ofa amma bai motsa ba dan ya san hakan bai taSa faruwa ba tunda ya fara kwana a gidan. MurWa handle Win ya ji anyi an buWe kofar tare da jin motsi alamun an shigo.

BuWe ido ya yi ya kalli wajan suka haWa ido da ita tana tsaye tana raba idanu. A hankali ta ce,  YaMar Didi ta ce ka zo ta faWa murya na cracking sosai alamun tsoro ko tilastawa a yanayinta.

Shi kam kallon ta kawai ya tsaya yi, she looks so good in her dress, bazai yi ™arya ba tayi masa kyau a idon sosai, shiyasa ya tsayar da ido yana kallonta kamar ranar ya fara ganin ta. A hankali ya janye ido ya ce,  haka ake shigowa wajan mutane babu sallama? Ya faWa muryarsa a can ™asa sosai.

Nayla ta ce ,  kayi ha™uri, na manta ne?.
 Na ce kin yi laifi ne?. Nayla ta girgiza ka alamun a a ya ce,  to meye na bani ha™uri?.
 Ka yi ha™uri ta sake faWa tana sauke kai ™asa. A zuciyarsa murmurshi yake yi amma a kan fuskarsa akasin haka ne. ˜aramin tsaki ya yi hakan ya saka ta fita da sauri kamar wacce aka biyo.

Didi tana zaune ta ga yadda ta fito ta ™araso har waige take yi. Didi ta ce,  ki nutsu mana Nayla, Omar babu abinda zai miki na cutarwa. Wannan tsoron na sa da ki ke ji nake so ki rage don Allah, in ba haka ba nan gaba zai cutar da ke a zaman auren ku wallahi. Zaki zo kina dana sani dan tun farko kin Wora kan ki akan matsanancin tsoronsa, shi kuma a haka zai tashi.

Nayla ta girgiza kai ta ce,  Didi baki san waye YaMar ba, kallon fuskarsa ma abin tsoro ne. Didi cikin tsokana ta ce,  inye ka ji wani suna na masoya, YaMar! An cire harafin farko an yiwa sunan ado sai ya bada wani style mai kyau. Lallai Nayla kina shagwaSa Omar.

Nayla tayi dariya tana rufe fuska da hannunta kafin ta buWe ta ce,  Allah Didi ni ko a gida haka nake, Ko Yaya Jawad bana cewa Yaya Jawad Yaya J nake ce masa. Haka cousins Wina duk yanke sunayen su nake yi, hatta Yaya Abbas da Yaya Ab nake ce masa kafin na daina. Tunda ya ce yana sona muka daina mutunci, da muka haWu da azumi ne naga bai nuna min komai ba, mun gaisa kamar yadda muke yi kafin ya ce yana sona.

A daidai nan Omar ya fito yana takowa zuwa wajan da Didi take zaune. Ya ji abinda Nayla ta ce a kunnensa amma bai nuna yaji ba yana tunkaro su kamar baya son taka ™asa.

Ganin sa sai Didi ta ce,  Dan mutum ya ce yana sonki sai ku daina mutunci?. Ni ki bani labarin samarin ki. Nayla bata san ya fito ba dan bata ji motsin sa ba hakan ya saka ta yin ™aramar dariya ta ce,  Hmm Didi nayi samari kam, wani lokacin har bana son fita saboda da™yar na je na dawo ba a yi min magana ba, ni kuma na tsani magana a kan hanya. Wasu ma fa dan son iyawa da za™ewa har gida wajan Abiy suke zuwa kai tsaye kafin su same ni, suka saka Abiy ya tayar min da hankali akan maganar aure.

Diid ta ce,  na san kuma akwai wanda ki ke so a cikin su ko?. Nayla ta kalli Didi sai a lokacin ta ga Omar da yake tsaye ya harWe hannayensa a ™irji ya zuba mata idanunsa masu shegen kaifi yana bin ko wanne lungu na jikinta da kallo.

Sai ta Wan ji tsoro kaWan ta yi shiru bata amsawa Didi tambayarta ba. Didi ta kalle shi ta ce,  ka zauna mana, ka fito ka hanata cigaba da bani labari. Bai musa ba ya zauna yana kallonta ta gefen idanunsa. Didi ta ce,  Ina jin ki, kafin zuwan maganar Omar wa kika yi niyar zaSa a cikin su?. Nayla ta kasa bata amsa ta yi shiru bata ce komai ba. Didi ta Wan yi tsaki ta ce,  wai dan ya fito sai ki daina bani labari? To Ina ruwan Omar shi? Kawai ki cigaba da faWa min, da wa ki ka zaSa a matsayin abokin rayuwarki?.

Kafin Nayla tayi magana ya ce,  Don Allah Didi ya isa haka, in bakya son fitowa ta meyasa ki ka saka aka kira ni? Ya faWa murya a ™asa yana kallonta.

Didi ta ce,  zan dawo kan ka ne, yanzu hira mu ke yi ai. Ya ce,  A bar hirar, bana son ji. In kuma za a yi a bari na tashi.
 To ubana, saboda kai kawai sai mu daina hira?. Tsaki tayi kaWan ta kalli Nayla ta ce,  ina jin ki, waye zaSinki?. Nayla ta sauke numfashi ba tare da ta kalle shi ba ta ce,  daman tun farko bana tunanin zan iya auren Ya Abbas, shi kuma& 

A kausashe Omar ya katse ta ya ce,  Na ce a bar hirar! An san hirar da za a yi kenan meye na kira na? Ya faWa yana kallon Didi. Didi ta taSe baki ta ce,  to meye haWin ka da hirar mu? Laifi ne dan mun tuna baya?. Harara ya sakar mata ya ce,  to na ce a daina!. Didi ta ce,  sannu ubana, wannan bada umarni kamar kai ka haife ni?. Kawai dai mun yi shiru da maganar ba dan ka hana ba ta faWa tana harararsa tana murmushi ™asa-™asa.

Abin mamaki kamar kishi take gani a tare dashi, tabbas kishi ne, in ba kishi ba meye na damuwa dan suna hirar samarinta bayan ta san halinsa?. Murmushin jin daWi tayi, in hakan ya kasance zata fi kowa murna, kuma tunda ta fahimci baya so zata san abinda zata sake yi da zata saka ya magantu.

Didi ta ce,  abinci na ce ka zo mu ci. Ya kalli warmers Win abincin ya kalle ta ya ce,  bata faWa miki bana cin abinci ba?.
 Tofa! yaushe ka daina cin abinci ban sani ba?.
 Bana cin abincin gidan nan, kema kin sani ai ko?.
 Yau zaka ci. Wani murmushi ya yi ya kalle ta yana Wage gira tare da ™an™antar da ido ya ce,  dole zaki yi min?.

 Ban kai nayi maka dolen ba Omar?. Ya Wora ™afa kan Waya ya ce,  kin kai, kawai kin je ™arshe ne, kin ™ure ni a yanzu. Dan haka bana tunanin akwai abinda zaki sake yi min dole a kai na amince na karSa. Didi ta ce,  Balle ma ba dole zan yi maka ba Omar, darajar zuwa na gidan nan matsayin ba™uwa zaka duba ka daure ka ci. Hausawa sun ce ba™on ka annabin ka.

Šan shafa kansa ya yi ya kalle ta ya ce,  To bani da ra ayin cin abincin gaskiya. Didi ta ce,  ka daure ka yi ra ayi kaji YaMar. Kallon ta ya yi jin sunan da ta faWa, sai ya ji bai ji abinda yake ji a zuciyarsa ba a duk sanda Nayla ta faWi sunan. Šauke kai ya yi ya ce,  Didi bazan ci ba. Didi ta ce,  Zaka ci Omar, Abinda ka ke so matarka ta girka maka kuma ka ce baza ka ci ba? Ta faWa tana tashi tana serving Winsa.

Matarka, shine abinda ya maimaita a zuciyarsa ya kai kallonsa ga Nayla da kanta yake ™asa tana wasa da zoben hannunta kamar bata falon. Šauke kai ya yi a lokacin Didi ta mi™a masa plate Win ta ce,  Don Allah ka karSa ka ci.

 Didi ni fa na faWa miki bazan ci abincin gidan nan ba, ki bari duk lokacin da ya ™are na siyo da kuWina sai na ci. Amma yanzu bazan ci ba.
 Meye ka ke yi haka ne? Yanzu saboda ni baza ka ci ba Omar? Ai shikenan na gode ta faWa tana ajjiye plate Win a gefe ta ce,  Nayla zo mu ci tare. Nayla ta kalli Didi tana mamakin kalamansa, kenan daman abincin gidan ne bazai ci saboda ba shi ya siya ba? Kenan zai fara ci a duk ranar da ya siya da kuWinsa?. To akan me? Laifi aka yi masa ko me?. Ta girgiza kai tana mamakin hali irin nasa.

Didi ta katse shirun, cikin raunin murya ta ce,  Wai ni na bawa Omar abu ya ™i ci, shikenan ai babu komai. Dama mahaifiyar mu na raye da na kai mata ™arar Omar wajanta na ce baya yi min abinda nake so, abinci kawai na bashi ya ce bazai ci ba Didi ta faWa a raunane dan ta saka shi ya sakko ya ci. Baza ta so Nayla ta gama shan wahala tayi girki kuma ya™i ci ba, ba lafiya ce da ita ba ta daure tayi girkin bai kamata ace bai ci ba.

Yana jin ta bai motsa ba amma ™hamshin abinci shi kansa ya shiga zuciyarsa har ya ji yana so ya ci Win. Ajiyar zuciya ya yi ya ce,  Didi& !
 Kar ka sake kirana, ka ™yale ni kawai. Plate Win da ta ajjiye yaja gabansa ya dau™i spoon yana juya abincin ba tare da ya ci ba.

Banza tayi masa bata ce komai ba dan tana magana zai iya fasawa, Nayla kuwa kallon sa take yi tana jinjina ™aunar da yake yiwa Didi da har saboda ita ya sakko zai ci abincin gidan. Ajiyar zuciya ya sake yi harda rufe ido kamar wanda zai ci guba, ya buWe idon kamar mai tunani kafin ya iya kai spoon Win bakinsa. Abincin ya yi masa matu™ar daWi, kuma tabbas favorite Winsa ne yana matu™ar ™aunar abinci da kifi sosai. Yafi damuwa ya ci kifi musamman grill talapia akan ya ci nama ko kaza.

Babu wanda yake magana a cikin su, Didi tayi shiru bata son ta faWi abinda zai saka ya daina cin abincin dan ta san halinsa. Tana kallonsa, abincin ma cin isa ake yi masa, kamar baya so haka yake taunawa. Didi girgiza kai take yi tana tunani ita kaWai, abinci ma ya yi zuciya baya ci saboda kawai yana ganin an raina arzu™insa da aka kawota dashi, ina ga ranar da ya san gidan da yake zaune gidan Kawu ne? Ai tana tunanin sai babbakata da ranta, gidan kuwa ta san daga ranar bazai sake taSa koda ™ofar gidan ba.

Rabin abincin ya ci, daman ta san abincin ya yi masa yawa, shi ba mutum ne mai cin abinci lokaci Waya ba, sai dai ya ci anjima ya sake ci. Ajjiyewa ya yi ya sha ruwa bai ce mata komai ba ya Wauki waya yana dannawa a nutse. Nayla a takure take cin abincin dan bata saba ci a gabansa ba, duk sai ta takura hakan ya saka da wuri ta janye hannunta ta daina ci.

Didi ta kalle shi ta ce,  Ka ce min kana son magana da ni jiya a waya. Ya girgiza kai ya ce,  akan ribar da aka samu ne, an samu riba sosai ba kaWan ba Didi. Didi tayi murmushi ta ce,  Alhamdu lillah! Allah ya cigaba da dafa mana Omar.

Omar ya ce,  Amin. Me ki ke ganin ya kamata a fara yi? Ranar juma a a masallaci ana huWba kafin a tayar da sallah an faWin mahimmacin yiwa iyaye da suka rasu abinda zai dinga kai musu lada kabarin su. To ni dai na tambaya nawa ake yin borhal an faWa min

Please Login or Register in order to submit comment