Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na cire Omaar daga raina. Mama ce taka bani ™arfin guiwa akan zai amince min na cigaba da ha™uri. Ni dai na san na tafi Kano ban tambaye shi ba amma daga nan ban san me na aikata ba. Kuma Mama ce ta saka na tafi, na nuna bazan je ba tace naje zan fi samun hutu." Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, "To ki daina kuka, tunda ke kin san baki yi komai ba ko ma meye zai bayyana in sha Allah."

Nayla ta ce, "Salma Abiy fushi yake yi dani."
"Zai daina in sha Allah."
"Ya aura min Omar, ya aurar dani ga wanda baya so, ya aurar dani ba tare da sanina ba."
"Shi Omar Win ya sani?."
"Wallahi ban sani ba, ban sani ba Salma. Ban san Ina zan saka kaina na ji daWi ba." Salma ta ce, "is okay, ki daina damun kanki kinga baki da lafiya."

Šan buga ™ofar akayi tare da shigowa. Abiy ne ya shigo da kansa ganin Salma sai ya yi murmushi ya ce, "A'a Salma, saukar yaushe?." Salma ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta su Hajja ta amsa masa kafin ya ce, "Ya jikin Naylan?." Salma ta ce, "har yanzu da zafi a jikinta Abiy."
"Zata warware in sha Allah. Kin zo a kai amarya Kano dake kenan, ai kin kyauta." Salma ta kalli Nayla da itama ita take kallo.

Abiy ya kalli Nayla ya ce, "me yake damunki?." Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka. Abiy ya ce, "ba kuka nace kiyi min ba, me yake damunki?." Nayla ta goge ido ta ce, "ciwon kai."
"Ki daina kuka shima zai daina." Kai ta Waga alamun to ya buWe ™ofar ya fita.

Nayla ta ce, "kinji ko? Wai kinzo a tafi dani Kano ya ce, Salma na shiga uku!." Salma ta ce, "baki shiga uku ba Nayla, ko meye zaizo da sau™i in sha Allah. Ki kwantar da hankali ki komai zai warware, ki cigaba da addu'a komai zaizo da sau™i." Rarrashinta Salma ta dinga yi har ta Wan saki jiki suna hira hakan ya yiwa Salma daWi a haka har dare yayi.

           Washe gari.

Saboda rashin lafiya Nayla bata iya tashi da azumi ba duk da ta saba duk sati amma baza ta iya ba. Salma ce ta ke tsaye akanta akan cin abinci da shan magani ita kam gabaWaya ta zama wani iri. Jawad ma ya sakko yana bibiyar lamarinta da jin ya ta kwana, ita kam gabaWaya bata su take yi ba, fushin da mahaifinta yake yi da ita ya fi komai Waga mata hankali.

Suna zaune a falo Abiy ya fita ita da Mama da Salma da kuma Jawad. Mama ta Wauki waya ta kira Didi bayan ta Wauka sun gaisa ta ce, "Aisha Ina ta jiran kiran ki, ya maganar mu?." Didi ta ce, "kiyi ha™uri Mama, sai dare naje na duba gidan ne shiyasa. Falo ne guda biyu, babba Waya sai ™arami Waya, sai bedrooma guda biyu."
Mama ta maimaita abinda Didi ta ce sannan ta ce, "kitchen fa?."
"Akwai kitchen da store, kitchen Win babu laifi yana da Wan girma."
"To ma sha Allah, zan fara aiko da kayan in anjima, zan bawa driver number ki sai kiyi musu kwantace a kai gidan. Zan aiko da masu Waura kayan duk sai ki yo musu bayani."

Didi a sanyaye ta ce, "to Mama." Mama ta ce, "Sai sun zo" ta faWa tana yanke wayar. Nayla da Salma duk suna jin abinda yake faruwa, Nayla ta mi™e ta hau sama Salma ma tabi bayanta. Jawad ya kalli Mama ya ce, "Mama don Allah meyasa kika fi mayar da hankali akan kayan Wakin Nayla? Auren nan kowa ba so yake yi ba, amma hankalinki gabaWaya yana ga a kai kayan Kano."

Mama ta ce, "umarnin mahaifinku ne, zan canja hakan ne?."
"Amma Mama shi kansa Abiy Win ya Wan sauka saboda rashin lafiyar Nayla, amma gabaWaya ke ta ta kayan ma kike yi." Mama ta kalle shi kamar zata yi magana sai ta fasa kawai ta tashi ta shiga Waki.

Nayla kuwa bayan sun shiga Waki kallon Salma tayi ta ce, "Wai kayan aurena ake zance Salma, wallahi komai ya fita daga raina, son Omar Win ma na neme shi na rasa." Salma ta ce, "ki yi ha™uri ki cigaba da jurewa. Amma sai naga kamar Mama murna take yi da auren nan. Ki yi ha™uri ina faWar hakan a kanta, amma daga jiya zuwa yau na fahimci kamar ita so take yi."

Nayla ta ce, "meyasa zata so? Kawai umarnin Abiy take cikawa." Salma ta yi shiru bata ce komai ba amma a zuciyar ta gabaWaya bata amince da Mama ba, gani take yi kamar da biyu take yin abinda take yi. Duk da ta san Maman bata da wani aibu da hali mara kyau, amma zuciyarta ta dasa mata ayar tambaya akanta.

" " " " " "

Abiy kai tsaye da ya shiga Kano gidan Daddy ya nufa kamar yadda yayi masa waya ya sanar dashi yana hanya. Daddy ya karSe shi hannu biyu da girmamawa aka tarbe shi da ruwa da kuma abinci. Ya sha dai ruwa amma bai ci komai ba yana zaune a falo shi kaWai an barshi ya huta. Sai da ya Wan jima da zuwa sannan Daddy da Abba da Baba suka shigo a tare gabaWaya.

Sake gaisawa aka yi kowa yana tambayar iyalan kowa kafin Daddy ya ce, "Alhaji Abdullahi mun ji batun aure kwatsam babu shiri, hankalin mu gabaWaya ya kasa kwanciya musamman da kace zaka zo kayi mana bayani." Abiy ya ce, "ni kaina ban shiryawa auren ba, yazo ne lokaci Waya dole na karSe shi."

Abba ya ce, "Amma me ya kawo shi?." Abiy ya ce, "Nayla tana son yaron, son da take masa ne ya saka ta koma kamar ba ita ba, kullum a rashin lafiya take, kullum a cikin damuwa. Da fari ban fahimta ba, amma daga baya da aka sanar dani sai na fahimci hakan. Na kira Nayla akan hakan ta tabbatar min da tana sonsa. Ni na faWa mata ban damu da kuWin namiji ba, abinda nake nema a ko yaushe hali na gari da kuma inda yaro ya fito. A take da na kirata na yanke ala™ar batun yaron, na ce ta cire daga zuciyarta, sannan a cikin masu neman aurenta tabbatar da ta fitar da guda Waya."

Abiy ya ce, "ta amsa min kamar da gaske take, na sake maimaita abinda nace amma sai na wayi gari Nayla ta taho Kano. Duk da ban sani ba kuma bata taSa fita wajan Kaduna ba tare da na sani ba balle tazo Kano, ko aiki zata taje sai ta faWa min saboda haka tsarina yake a haka suka tashi. Na yi  mamaki da naji labarin bata nan amma nuna ba na share ta. Ina nan zaune sai ga wannan sa™on ya shigo wayata Nayla ta turo min" Abiy ya faWa yana Wauko waya ya shiga number Nayla ya mi™awa Daddy.

Sai da ya jira ya gama karantawa kaf ya bawa Abba da Baba duk suka karanta duka messasges Win sannan Abiy ya ce, "raina ya Saci gaskiya akan hakan sosai, ban kuma yi tunanin zata aikata haka ba. Nan take na yanke hukuncin aura mata shi tunda haka ta zaSa, kuma tunda har take irin wannan furucin akansa aura mata shi shine mafita kar a zo a haifar da Wa mara ido. Wannan dalilin ne ya saka na aura mata shi a lokacin da nake tsakiyar Sacin rai, daga baya naji kamar ban kyauta mata ba amma na riga da na aikata."

Daddy ya girgiza kai ya ce, "Tabbas Nayla bata kyauta ba, ko waye a matsayinka dole ransa ya Saci ya aikata fiye da abinda ka aikata saboda abinda ta aikata. Amma Alhaji Abdullah anyi aikin gaggawa, Nayla yarinya ce ™arama, soyayya zata iya sakawa tayi wannan furucin ba tare da ta sani ba. Wata™ila da ka sake bata dama da hakan bai faru ba."

Abiy ya ce, "Eh to ba nace ba, ni a wajena hakan da nayi shine daidai tunda shi ta zaSa take ganin zata iya zama dashi, ni a wajena na bata shi a matsayin wanda take son kuma zaSinta." Baba ya ce, "ni babban abinda yake damuna akan auren nan ba komai ba ne face halin yaron, inda ace mutum na gari ne kamar kowa sai mu yi fatan Allah ya sanya alkhairi tunda kowa yasan matar mutum kabarinsa. Amma kowa ya san sunansa ba ta hanyar kirki ba, in na tuna hakan sai naji komai Nayla zata aikata bata cancanci a yanke mata wannan hukunci ba gaskiya, Alhaji Abdullahi."

Abba ya ce, "Shi yaron ya san da auren?." Abiy ya ce, "ban sani ba ko yanzu ya sani." Ya girgiza kai ya ce, "Mahaifinta ne kai kana da ikon yanke hukunci a kanta fiye da kowa, amma duk da haka baza mu fasa faWa maka gaskiya ba, koda ba Nayla ka yiwa haka ba in muka ji labari zamu faWa maka tunda an zama ´an uwa. Ba dan muna yayyen mahaifiyarta muke faWar baka kyauta ba, muna faWa maka ne a matsayin Wan uwan mu. Gaskiya ka yanke hukunci cikin fushi da Sacin rai, in da an bi wata hanyar ba wannan ba da wata™ila hakan bai faru ba."

Abiy yayi ajiyar zuciya ya ce, "Haka Allah ya shirya, amma har zuciyata a yanzu bana jin ban kyautawa Nayla ba." Daddy ya ce, "Shikenan Alhaji. Amma yana da kyau a zauna da yaron aji shi yana da ra'ayin zama da ita, in yana dashi shikenan tunda tana sonsa sai mu ce Allah ya basu zaman lafiya, in kuma bashi da ra'ayi zata sha wahala a zama dashi gaskiya. Kuma ga yanayin da muke ciki a wannan zamani na cututtukan da ake Wauka, ana gwajen-gwajen jini yanzu kafin aure dan tabbatar da lafiyar su shida ita, haka za'a kaita ba tare da a san matakin jininsa da abinda yake ciki ba?."


"Na bar mu ku komai a hannunku akan wannan, ku yi duk abinda ya kamata, koda auren ku ke ganin za'a samu matsala wu™a da nama yana hannunku, ku yanke hukunci ba sai an sanar dani ba." Abiy ya faWa tana kallon Daddy.

Daddy ya ce, "ai aikin gama ya gama Alhaji Abdullah, amma duk da haka zamu ™o™arta mu gani. Allah ya shige mana gaba." Aka amsa da amin suka cigaba da tattauanwa kafin yayi sallama ya wuce dan Kaduna zai koma.KRB2P025
ArewaBooks@nanahaleema11.

Bayan fitar Abiy su uku suka cigaba da tattaunawa akan lamarin Nayla, amma basu da abinda zasu yi tunda shine mahaifinta yana da ikon yanke hukunci a kanta a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama. Kasancewar Hajja tana gidan Daddy gabaWaya suka shiga suka same ta, a wajan Hajja suka samu ™anwar su Mama Sa adatu a tare da Hajjan.

Hajja ta kalle su ta ce,  Har ya tafi?. Daddy ya ce,  ya tafi.
 To ya aka yi?. Basu Soye masa komai ba suka sanar da ita Daddy ya ce,  Kuma baya dana sanin aura mata shi ya ce har yanzu. Abinda na lura dashi ransa ya Saci sosai, ya yanke hukunci cikin fushi da Sacin rai, kuma itama Nayla bata kyauta ba ban yi tunanin zata aikata haka ba. Amma mun sanar dashi zamu zauna da yaron, in ba a zauna dashi a san yana sonta ko baya sonta ba zaman gidansa bazai yi mata daWi ba. Ya ce ya bar komai a hannun mu, mu yiabinda muke ganin ya dace.

Mama Sa adatu ta ce,  Gaskiya Nayla bata kyauta ba, amma ni ban ga abinda zai saka ayi mata aure irin wannan a maganar nan ba. Hajja ta ce,  Koma dai meye shine ya haifeta, duk abinda zamu ji akan Nayla bayan a sa ne. Ku bar shi da hukuncin da ya yanke kawai, abinda zai faru mu yi mata addu a kawai zai fi.

Mama Sa adatu ta ce,  Hajja aure lokaci Waya haka? Babu sanarwa, babu kuWin aure ba lefe?. Kuma mijin ma ba wani na kirki ba, ai sai ace dan mahaifiyarta bata raye ne ya saka muka zuba ido akayi mata wannan auren. Yanzu in da ace tana da rai hakan zai faru ne?.

 Koda tana da rai hakan zai faru tunda Allah ya rubuta, kawai a bar maganar nan mu yi mata addu a. Yana girmama mu sosai, kar yaga kamar mun cika za™ewa akan lamarin iyalansa. Mu yi mata fatan Allah ya sa hakan ya zama alkhairi.

Duk suka amsa da amin ba dan hakan yayi musu daWi ba sai dai babu yadda zasu yi ne, amma da suna da iko Nayla baza ta zauna da Omar matsayin mijita ba ko kusa.

Bayan Kwana biyu.

Har ranar laraba Omaar bai san da wannan labari ba, harkokin gabansa kawai yake yi domin kuwa Allah ya dafa masa a sana ar da ya saka a gaba, sosai yake ganin alkhairi da kuma cigaba fiye da tunaninsa. Shiyasa ya mayar da hankali ya ke kuma ™aro sani akan abinda yake yi.

Kamar yadda Mama tace ta turo da kayan gidan Nayla a gama Waura komai, hatta kayan kitchen a cikin kwana biyu an zuba gida ya fito yayi tar kana kallonsa ka san gidan amarya ne. Mama ce kawai take shagalinta a wannan Sangare amma ko Abiy Win baya bi ta kai balle kuma Nayla da ta koma kurma saboda bata son magana.

A daren ranar larabar suna zaune ita da Jidda da ta zo Kaduna saboda maganar, ita Salma suna hira a kusa da Nayla, Nayla dai bata saka musu baki su ne suke hirar su ita kam abinda take tunani daban. Mama ce ta shigo falon da sallama suka amsa sallamarta, ta kalle su ta ce,  ya kamata ace an yiwa Nayla gajeren gyaran jiki, dan haka gobe mai gyara zata zo zata yi mata abinda ya samu, sannan zata yi mata ™unshi tunda jibi ne tafiya Kano.

Gaban Nayla ya faWi har sai da ta runtse idanu bata kalli Mama ba. Jidda ta ce,  Haba Mama! Wanne irin gyaran jiki a cikin wannan yanayi?. Don Allah Mama ki bar faWin haka wallahi bana son ji kwata-kwata. Ba ma fatan auren nan ya tabbata balle a dinga tunanin wani gyaran jiki ko ™unshi. Mama ta kalli Jidda ta ce,  ai kam dole za a yi, tafiya Kano ranar juma a babu fashi ranar zata tare a gidanta. Haka za a kaita babu wani gyara?.

Jidda ta ce,  Haba Mama don Allah, ki daina faWar haka mana. Auren nan fa ba so muke yi ba.
 Kece bakya so, amma Nayla tana matu™ar son mijinta ko Nayla? Ta faWa tana kallon Nayla. Nayla bata iya buWe ido ba saboda haushin Mama da ta fara ji a zuciyarta, tunda daga abinda tayi mata akan Abiy shikenan ta fara jin wani abu akanta wanda bata san meye ba.

Mama ta sake cewa,  ku dai shirya gobe zata zo tana faWa ta fita daga falon. Bayanta Jidda ta bi sai suka haWu da Jawad ya taho duba Nayla ya kalleta ya ce,  ke kuma ina zuwa?. Jidda ta ce,  Wajan Mama zan je Yaya J, abinda take yiwa Nayla gabaWaya bai kamata ba, ana cikin wannan yanayi amma Mama tana zancen wai zata kira mai ™unshi da gyaran jiki ta yiwa Nayla?. wallahi ban ji daWi ba, sai ta dinga ganin dan ba itace ta haifeta ba shiyasa take faWar haka.

Jawad ya ce,  ke ni fa na lura kamar Mama murna take yi da auren nan, gabaWaya itace abin bai dame ta ba. Jidda ta ce,  nima dai na lura daga zuwana gidan nan zuwa yanzu, ko ba murna takeyi ba bata nuna ta damu akan hakan.
 Ki ™yaleta karki bita, kije ku cigaba da rarrashin Nayla Win a hankali.
 Amma Yaya Jawad wallahi ban ji daWi ba, Nayla ta kasa magana gabaWaya, kuma ga cousin Winta Salma, zata ga kamar Mama ce take son auren nan.

Jawad ya ce,  ki ™yaleta ki je kawai, zan san abinda zan yi. Jidda ta koma ciki jiki a sanyaye ta zauna kusa da Nayla da kanta yake kafaWar Salma tana hawaye. Dafata tayi ta ce,  Twiny don Allah ki yi ha™uri da abinda Mama ta ce. Nayla ta kalleta ta ce,  Twiny me Maman tayi?. Zata sake magana ta ce,  ki bari bana so, komai Mama tayi tana yi ne matsayinta na uwa a gare ni, Don Allah karki sake cewa komai.


Jidda ta ce,  Yanzu haka zamu zuba ido a kai ki gidan Omat ba tare da soyayyarki a zuciyarsa ba?. Ni bani da tabbacin ma ya san da auren nan, in ya sani ya karSe ki ko bai karSa ba?. Salma ta ce,  abinda yafi komai tsaya min a rai kenan. Nayla bata iya cewa komai ba idanunta na kulle fuskar Omar na gilma mata a ranar Waurin auren Didi da yake tsokanar Didi.

Washe gari ranar alhamis da safe suna zaune gabaWaya a falo ana breakfast saSanin Nayla da take a gefe a rakuSe. Abiy ya kalle ta ya kalli Jidda ya ce,  kin gama shirya mata kayanta? Gobe zata tafi gidan mijinta in sha Allah. Jidda ta kalli Abiy a sanyaye ta ce,  Don Allah Abiy ka sake bata lokaci, ko zuwa nan da bayan sallah ne sai ta tare. Amma yanzu ba a shirya komai ba ace zata tare a gidan wani?. Abiy ya kalle ta ya ce,  Haka ta ce miki?.
 Ko bata faWa ba na san hakan ne a zuciyarta Abiy.
 Ke dai haka ki ke tunani, amma Nayla ba haka take so a zuciyarta ba. Ki barta taje gidan mijinta tayi ibada, zata fi samun lada a watan Ramadan Win a can.

Nayla ta Wago ido ta kalli Abiy suka haWa ido sai ta mayar da kan ™asa bata ce komai ba. Abiy ya ce,  Ku shirya komai, gobe daga nan za a kaita gidan Hajja, daga nan Hajja ta kai ta gidan mijinta. Na sauke nauyin da yake kaina a matsayina na mahaifinta.

Jidda tayi ajiyar zuciya, ta kalli Mama ta Wauka zatayi magana sai taga abincin ta ma take ci hankali kwance. Sai daga baya Mama ta ce,  jiya nayi magana da Zaliha da take Kano, tana tambayata ya aka yi haka ya faru na ce ta tambayeka. Amma ta ce zata kasancewa a gidan Hajja a kai amarya da ita.

Abiy ya ce,  Su Yaya Ashiru da su Kawun Zaria suna tayi min waya ban san waye ya faWa musu ba, na ce duk na hutar da ku hidimar biki bana bu™atar ayi komai amarya kawai nake so a kai.

Jidda ido ta ya ciko da hawaye ta ce,  don Allah Abiy ka amince ko walima mu yi a goben. Ya kalli Jidda ya ce,  lokaci ya ™ure, inda kin san kuna da wannan shirin da kin sanar dani da wuri, gobe har yaushe aka gama walima aka tafi Kano? Kin san bana son tafiya in dare ya yi.

 To Abiy a Waga tafiya zuwa ranar Sunday.
 Ke Jidda! Ya Isa, kar na sake jin wannan maganar a bakin ki kin gane? Ya faWa yana kallon ta a tsawace. Kai ta Waga tana goge hawaye. Ta kalli Nayla da har lokacin kanta yake a ™asa kafin ta mi™e ta hau sama. Jidda ma bin bayanta tayi dan bata ga amfanin zama a falon ba.

Nayla kasa kukan ma tayi ta zauna akan stool Win madubi tayi shiru. Jidda ce ta shigo ta dafata ta ce,  Nayla ki yi ha™uri, wata™ila wannna auren alkhairi ne a gare ki da rayuwarki shiyasa yazo a haka. Ta kalli Jidda da idanunta da suke a kumbure ta ce,  ta ya zai zama alkhairi bayan mahaifina baya son auren nan? Ta ya zai zama alkhairi bayan mahaifina yan fushi dani?. Salma ta ce,  Allah bazai kama ki da laifi ba, tunda ke kin san baki yiwa Abiy komai ba.

 Ku ka sani ko na aikata Win ban san nayi ba?. Jidda ta ce,  Rashin sani ne, in ma kin aikata Win baki sani ba Allah bazai kama ki da wannan laifin ba. Ki karSi wannan jarabawarki sai ki ga abin yazo ya wuce inda mu ke tunani. Knocking ™ofar aka yi tare da turowa, duk suka kalli ™ofar suka ga Jalila ce da wata mata a bayanta.

Jalila ta ce,  Ya Jidda Mama ce tace na rako ta Wakin nan, wai mai ™unshi vc. Nayla duk suka kalla kafin su yi magana Nayla ta ce,  bana bu™atar komai, ki ™yale ni kawai ta faWa tana tashi ta shiga banWaki zuciyarta kamar zata fito. Jidda ce ta sallani mai ™unshi dan basa tare da farin cikin yin wani abu ™unshi. GabaWayan su suna cikin damuwa, Soyewa suke yi suna ™o™arin ganin sun fitar da ita daga damuwar.

" " " " " "

Omar yana zaune da yaransa a falo ana tattaunawa akan sabon machine Win da suka siya. Bashir ya ce,  Tiger ana samun customers sosai daga Lagos, kuma alhamdulillah kaya in suka tafi basu taSa dawowa ba. Omar yayi ajiyar zuciya ya ce,  haka muke so. Tk ya ce,  Amma Boss wannan couples design Win da za a samu mace da namiji da zasu dinga sakawa a ™afar su ana yin hoto ana watsawa a dnoya zai fi Waukar hankali. Haka naga anayi dana je Lagos kai kaya.

Bashir ya ce,  Hakan zai yi kyau kuma zai Wauki hankali, lokaci Waya za a fi fahimtar na mace da namiji ne iri Waya. Kuma Tiger da zaka amince ™afarka ma zatayi kyau da hoton. Kallon ™afar tasa ya yi da take a bayyane dan three quater ne a jikinsa.

Omar ya ce,  kawo mu ga. Yana faWa ana mi™o masa takalmi guda Waya ya saka a ™afarsa ta haggu wacce take Waure da ba™in abun da yake ™arawa ™afarsa kyau. Bashir ya ce,  na rantse da Allah Boss yayi maka bala in kyau. Cirewa yayi ya ce,  zamu san abinda zamu yi a akan hakan.
 Allah ya biya Tiger na mu ya faWa yana duba wayarsa da take ™ara.

Šauka yayi suna magana akan takalman da ake so yana yanke wayar ya ce,  Tiger harkar social media Win nan tana yi sosai, yanzu haka daga Abuja ne ana son ™afa Wari biyu da hamsin. sun yi min magana a can ba kula ba sai aka kira ni. Omar ya Waga kai kamar baya son magana ya ce,  ayi abinda ya kamata. Ina Goje?.

Tk ya ce,  yana inda ka tura shi ™aro ilimi akan harkar nan.
 Yayi kyau, ku je a cigaba da aiki. Tk ya mi™e ya ce,  Boss nan gaba fa shagon nan kaWan zai yi mana wallahi, a haka ma shago uku aka haWe amma kayan matsewa suke yi. Bai kula shi ba sai Wora Wafa kan Waya da yayi bai ce komai ba.

 Assalamu alaikum aka faWa daga bakin ™ofa ana shigowa. Duk kallon ta suka yi suka haWa biki wajan gaisheta ta amsa ta ce,  ya kasuwa?. Suka amsa kafin su fita. Kallon ta Omar yayi ya ce,  kwana biyu me kike zuwa yi ne? Baki yi sati da zuwa ba fa. Ta zauna tana kallon sa ta ce,  ana yiwa mutum iyaka da zuwa gidan su ne?.
 Shi mijin naki ne yaga zai iya da yake barin ki yawo a kan titi.
 Laifi ne hakan?.

Bai ce komai ta kalle shi ta ce,  Magana nazo mu yi. Ya sauke ™afa ya kalleta ya ce,  maganar meye da ta saka ki fitowa yanzu?. Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, 

Please Login or Register in order to submit comment