Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rufeta da faWa, a sanyaye ta mi™a masa key Win motar ta ce, "Don Allah, don Allah ba don ni ba."

Ajiyar zuciya ya yi ya bi hannunta da kallo wanda ta mi™o masa key Win, ya sake kallon fuskarta ya ga har lokacin hawaye take yi. Bai san meyasa yake jin zafin hawaye ta ba, bai san meyasa yaji ya damu da kukan da take ba. FaWa yake so ya yi mata akan kukan da take yi amma kamar an kulle masa baki ya kasa kataSus, ya zuba mata ido kawai yana kallo bai karSa ba kuma bai yi magana ba. Numfashi ya sauke ya mi™a hannu ya ya karSi key Win, sai tayi murmushi tana goge hawaye ta ce, "na gode."

Yana fita ta biyo shi ya kira Tk da yake ™ofar gidan ya saka ya buWe masa gate Win gidan. Kallon motar yake yi shi bai shiga ba kuma bai koma ciki ba, ga kuma gate Win an buWe, juyawa yayi ya kalle ta ya ga itama shi take kallo sai ya Wauke kai yana ji ko dai ya bawa Tk ya kaita ne?.

Ji ya yi bazai iya yin hakan ba ya danna remote Win jikin key Win motar, ta bada sautin buWewa ya shiga mazaunin driver. Tana tsaye ya fita da motar Tk ya kulle gate Win, ita kuma ta fito ko rufe ™ofar gidan bata yi ba kawai jan ™ofar ta yi dan ta san key Win gate Win yana jikin makullin motar.

Har tuntuSe take yi wajan shiga motar saboda sauri, ta zauna a mazaunin gaba a Warare cikin bugawar zuciya. Motar ya ja suka tafi, ta kalle shi ta gefen ido ta ga glass Win gabansa kawai ya ke gani ba ita ba.

Nayla tayi murmushi cikin jin daWi ta ce, "Asibitin getting better zamu je, a nan cikin nasarawa gra." Tafiya suke yi kawai bai ce komai ba ita kuma sai satar kallonsa take yi zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ba su taSa zama na wani lokacin tare dashi haka ba, dan zaman da suke yi kaWan bashi da tsaho shiyasa take jin tafiyar motar tayi mata daWi sosai.

Har suka je asibitin babu wanda ya yi magana, suka shiga gate Win asibitin ya ajjiye motar ba tare da ya ce komai ba. Kallon sa ta yi ta ce, "zan shiga ciki?" ta faWa a sanyaye duk da ta san amsarta. Bai amsa ba kuma bai motsa ba yana kallon gabansa, sai daga baya ya ce, "ba driver ki ka ajjiye ba, ki san zaman da zaki yi." Nayla ta ce, "to" ta faWa tana buWe motar ta fita zuwa ciki tana kiran wayar mijin Jidda.

Da shi suka haWu ya rakata Wakin da Jidda take tana shiga ta ™arasa inda Babyn ta ke tana kallo ta ce, "Ma sha Allah! Wannan Babyn kamar na Wauke ta twiny." Jidda da take zaune ta yi murmushi ta ce, "ta baby kike yi ba tani ba ko?." Nayla da take yiwa Babyn hoto ta ce, "ni na isa? Jira na gama yi mata hoto na yi posting tukunna."

Hoton ta tsaya kalla bayan ta gama ta tabbatar da ya yi kyau sannan ta tura family group Winsu sannan ta saka a status. Kafin ta gama Worawa a status Abiy ya yi reply a group Win da Allah ya rayata bisa sunna.

Murmushi tayi ta ce, "kinga har Abiy ya yi reply." Jidda ta ce, "™araso na ji Wuminki ´ar uwa, Wallahi na Wauka she™awa zanyi saboda azabar haihuwa." Nayla ta ™arasa inda take ta ri™e hannunta ta ce, "Sannu Twiny, amma kin samu lafiya ko?."
"Tun magriba fa na haihu, bai miki waya ba sai bayan na farka daga bacci." Nayla ta ce, "Allah sarki Twiny, sannu kin ji."

Jidda tayi dariya kaWan ta ce, "wai an yi min Winki, ko dariya na yi sai naji a jikina."
"Sannu my love, wallahi tausayi ki ke bani." Jidda ta sake yin murmushi ta ce, "Ke kaWai ki ka zo a daren nan? Sai da na ce masa kar ya faWa miki na san zaki ce zaki zo ga dare yayi, shine ya ce ai in bai faWa miki ba ya ci amanarki." Nayla ta yi murmushi ta ce, "wallahi kuwa ya ci amanata. Ba ni kaWai na zo ba ai."

"Drivern Hajja?."
"A'a."
"Waye ya kawo ki to?."
"YaMar mana." Jidda ta wara ido ta ce, "Mijinki wai?." Nayla tayi murmushi tana sake ri™e hannun Jidda ta ce, "shi mana." Jidda ta ce, "yaushe aka fara shiri haka babu labari? Nayla kina so ki ce komai normal yanzu?."

Nayla ta girgiza kai a sanyaye ta ce, "kawai dai ya ga dare ya yi ne shiyasa ya kawo ni." Jidda ta dafa ta ta ce, "tabbacin komai ya fara zama normal Win kenan, in ba dan haka ba Ina ruwansa dake ma?." Nayla tayi murmushi ta ce, "ba a gane kan shi ne gabaWaya Twiny, yau fari gobe ba™i, yau kirki gobe masifa."

"Na faWa miki hanyar da zaki kamo shi ko baya so amma kin ™i ji, wallahi da yanzu abubuwa sun fara daidaita."

"Twiny a haka ma alhamdu lillah, tunda har yana saurarena nayi magana ya bani amsa, in bani da lafiya ya tambayi lafiyata, ko hana ni fitowar nan yayi ya ce dare yayi yanzu kulawa ce mai girma wacce na ke girmamata a zuciyata. A hankali komai zai daidaita, amma ni bazan iya jawo hankalinsa da jikina ba Twiny, saboda zan ga kamar ba ni Win yake so ba jikina yake so."

"Waye ya faWa miki? Kawai zai fi saurin bayyana abinda yake zuciyarsa ne ta hanyar hakan. Wannan turaren da na baki da kina amfani dashi kina saka kaya masu Waukar hankali, yadda ki ke da structure mai kyau da yanzu an wuce wajan."

Nayla ta ce, "Twiny soyayyarsa nake bu™ata ba s*x love ba, wannan dabarar ta ki kusancin kawai zata kai ga jikin mu ba da zuciyarsa ba.Wallahi Twiny ji nake yi a zuciyata indai zai so ni ya zauna dani da zuciya Waya, ya bani kula da soyayyar zahiri ko kusancin mu bai ga haWa shinfida ba am okay. Allah kaWai ya san irin son da nake yi masa, Ina ™o™ari wajen Soyewa ne saboda hakan ya zamar min dole amma Ina mugun ™aunarsa" ta fada hawaye na sakko mata, ta mi™e tsaye ta Wauki Babyn Jidda ta ri™e a hannunta.

Jidda ta ri™e hannunta cikin tausayawa ta ce, "komai zai ™are in sha Allah, zai furta miki kalmar so ina jin hakan a jikina. Lokacin da na fara labour na san na yi miki addu'a, amma da ta tankama ban sani ba ko na yi miki Win ko banyi ban sani ba." Nayla ta ce, "a hakan ma alhamdulillah, shiryawa ta da Abiy kawai nake so Twiny, wai ni Naylan Abiy nice na kwashe sama da wata huWu ban ga Abiy ba, Ina azabtuwa da hakan sosai."

"Ki yi ha™uri, har yanzu bamu san me ya Sata masa rai ba, amma komai duk zai wuce." Ajiyar zuciya tayi ta goge idanunta tana yiwa Babyn wasa da kumatu. A lokacin mijin Jidda ya shigo yana ta tsokanar Nayla tana mayar masa dan sun saba tun kafin auren hira suke yi dashi sosai.

Nayla ta bashi Babyn ta ce, "Twiny zan koma, amma gobe na san kina gida ko?." Kai ta Waga mata Nayla ta ce, "bara na je, zan shigo goben tun safe in sha Allah. Na san tare zamu shigo da Salma." Jidda ta amsa suka yi sallama ta fita da sauri tana fargabar haWuwa da Omar dan ita kanta ta san ta jima sosai.KRB3P024
Arewabooks@nanahaleema11.

Omar yana zaune yana duba agogo yana mamakin zaman da tayi ta bar shi a mota kamar wani yaronta. Wayar da Bashir ya yi masa ce ta Wauke masa hankali suka jima suna waya akan abinda ya shafi kasuwancinsa yana basa umarnin abinda ya kamata da abinda ya kamata a bari.

Yana wayar yana kallon agogon motar yana girgiza kai cike da zallan takaici. Haushin kansa ma yake ji da har ya karSi motarta ya kawo ta, to daman ba dole ma ta shanya shi ba tana ganin motarta ce kamar driverta yake a wajanta.

Yanke wayar ya yi ya sake kalla ya ga mintina kusan arba'in kenan da shigarta. Murmushin takaici ya yi a bayyane ya ce, "Ni Omar aka bari jira a mota" ya faWa yan girgiza kai cikin tsananin Sacin rai. To ko Narma da mahaifinta ya biya shi yana kai ´arsa unguwa bai taSa zaman jiranta na tsahon wannan lokaci ba sai ita.

Tunda ya hango ta fito ya tsaya yana jiran ™arasowa ta, yana gani tana sauri har ta ™araso yana jira ta shigo ya sauke mata kwandon masifar da take nu™ur™usar zuciyarsa, dan bai ga abinda zai dakatar dashi wajan nuna mata kuskurenta ba.

Tana buWe motar ko ™arasa shiga bata yi ba ya fara cewa, "Ga banza Wan aikinki wanda ki ka raina, kin shiga sama da mintina arba'in kin bar ni zaune ina jiranki saboda ga yaronki. Biyana ki ke yi ko kuma a ™ar™ashinki nake aiki? Ko dan motarki ce na taimaka na kawo ki sai ki ka saka a ranki ni driver ki ne!?." Jin yadda yake magana da faWa sosai jikin Nayla yayi sanyi kafin ta yi magana ya sake cewa, "Dan kin raina min hankali kin kuma raina ni ni zaki bari Ina jira har wannan lokaci? Saboda ga wanda ki ka ajjiye kina biyansa dole ya yi miki abinda ki ke so ko?."

Nayla ido ya ciko da hawaye a sanyaye ta ce, "Don Allah ka yi ha™uri, saboda kai nake ta sauri na fito nazo mu koma, babu kowa a tare da ita haka na barta. Ka yi ha™uri YaMar, duk abinda ka ce ba haka bane, ni ban raina ka ba, ka yi ha™uri don Allah" ta faWa a sanyaye hawaye na sakkowa daga idanunta cikin tsananin rauni.

Šif ya yi kamar an tsayar da faWan na sa, ya zuba mata ido ganin yadda hawaye yake sauka Waya yana bin Waya, sai ya ji gabaWaya fusatar da yake tare da ita tana gushewa a hankali. Yanayin da ta yi masa magana ya kashe masa jiki sosai, duk karsashin faWan da yake ji dashi duk ya gudu sai rauni da ya mamaye masa jiki, ya kafa mata ido kawai yana kallon yadda take kuka da alama akwai abinda yake zuciyarta.

Kukan nata ya yi ™arfi, ya tashi daga hawaye ya koma kuka mai sauti ta ce,"Ka....yi....h™u....ri YaMar......"yadda taja ™arshen sunan tana kuka ya ba wani sabon style da ya sake jefa shi a wani yanayi na daban. Ajiyar zuciya ya yi dan gabaWaya ya sauka daga dokin fushin da ya hau, ya kunna motar suka fita daga asibitin yana tafiya a hankali.

Kukan na ta ya dame shi, tun yana jin sautinsa a kunnensa har ya koma jin sautin a zuciyarsa, babu macen da yake damuwa da kukanta sai Didi, baya so ya ga Didi tana kuka ko kaWan lokaci guda sai ya tashi hankalinsa. Abinda yake ji game da kukan Nayla yafi wanda yake ji akan kukan Didi, ratsa zuciyarsa kukan yake yi yana nutso a cikin jininsa. Bai san ya runtse ido ya buWe ba sai da ya kalli gefenta kaWan sannan ya ce "ki bar wannan kukan!." Yadda ya faWa a kausashe ya saka ta dakata tana cewa, "bana na Sata maka rai ne, bana so ka dinga yi min faWa ko kaWan."

Kallon ta ya yi suka haWa ido yaga yadda idanunta suka yi ja sai ya Wauke kai yana mamakin wannan kukan nata kamar daman akan gaSar yin take. Goge ido take yi a hankali ya sake cewa, "na ce ki bar kuka." Nayla jin ya sassauta murya sai ta ce, "to" a sanyaye tana jingina da kujerar tana kallon titi.

Sai kuma ta Wauki wayar tana duba hotunan Babyn ta yi murmushi ta yiwa hoton kiss, ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba ta ce, "YaMar ka ga hoton babyn, tana da kyau ko?" Ta faWa tana haska masa wayar.

Juyowa ya yi ya kalla kaWan ya Wauke kai bai ce komai ba. Murmushi ta sake yi ta ce, "Twiny na ta iya haihuwa, ji nake kamar na taho da babyn gida" ta faWa tana sake zooming hoton tana gani.

Shi dai bai tanka mata ba amma ya yi murmushi a zuciyarsa yana cigaba da tafiya a hankali. Wani check up suka ga ana yi a kan titin har aka zo kansu. Sauke glass ya yi kamar yadda kowa yake yi ya kalli officer Win da yake tsaye. Officer Win ya ce, "Ah Tiger na mu" ya faWa yana bashi hannu shima Omar ya bashi hannu suka gaisa.

"Daga Ina haka?."
"Unguwa" ya bashi amsa a ta™aice a kuma ™asaitance. Office ya ce, "kwana biyu, fatan komai Lafiya?." Omar ya ce, "lafiya, ya aiki?."
"Alhamdu lillah. Wannan Madam ce?" Ya faWa tana kallon Nayla da take kallonsu. Kafin ma ya bashi amsa officer ya ce, "Madam barka da dare." Nayla ta ce, "barka dai." Zai sake magana Omar ya ce, "na gode" ya faWa tana Waga glass Win ba tare da ya sake cewa komai.

Nayla mamaki tanke yi ya akayi ´an sanda suka san shi? Ko dan ya kasance mai aikata laifi ne a baya?. Shi dai bai kalle ta ba abinda yake gabansa kawai yake yi kuma tu™i a hankali kamar baya so su je gida.

Wajen tarin ´an shaye-shaye suka da suke zaune a gefen titi ga makamai a gefen su suka zo. Har ya gota sai kuma ya tsaya ganin sun tsayar da wani mai machine ya san da™yar basu ™wace masa machine Win ba kuma sun cutar dashi ba.

Baya ya yi a hankali a daidai lokacin da suke shirin cutar mai machine Win ya sauke glass ya ce, "kar wanda ya cutar dashi!." A tare duk suka juya suna tunanin wanne mai ™arar kwana ne wannan yake magana cikin bada umarni. HaWa ido da shi ya saka su yin ihu a tare da faWin, "Allah ya biya Damisa!." Kallon Nayla ya yi da take kallon sa bai ce komai ba ya Waga glass Win ya fita daga motar.

Tana ganin su suna magana kuma ta ga mutumin da suka tsayar ya tafi basu yi masa komai ba. Magana ta ga suna yi sosai har ya saka hannu aljihu ya basu kuWi yana murmushi kafin ya buWe motar zai dawo. GabaWayan su sun rako shi bakin motar yana buWewa ya ce, "To ya isa haka, na gode. A daina fitina bata da amfani, duk wanda ya shirya ya yi min magana Ina da wajan ajjiye shi."
"Godiya mu ke Damisa, Allah ya bar ka da Madam." Bai ce komai ba ya buWe ya shiga ta ja motar da sauri yana murmushi.

Kallonsa tayi ganin yana murmushi bata ce komai ba amma taa mamakin yadda ya hana su cutar da wancan, sannan gashi ya yi magana da ´an sanda ya kuma zo yana magana da abokansa na baya. Meyasa suke girmama shi har haka? Bata ce masa komai ba har suka je gida ta sauka daga motar, a ™ofar gidan suka samu yaransa suna nan, aka buWe gate Win aka shiga da motar itama ta shiga gidan.

A falo ta tsaya tana jiran shigowarsa, ba jimawa sai gashi kuwa ya shigo ta mi™a mata key ta karSa ta ce, "Na gode YaMar, Gobe in Allah ya kaimu zan je gidanta."
"Allah ya kaimu" ya faWa yana shiga ciki ta amsa da amin itama ta shiga ciki.

Kamar yadda ta ce kuwa da safe sai tafi gidan Twiny, tun safe har magriba sannan suka dawo tare da Salma gabaWaya jikin Naylan a sanyaye. Yanayin da take ciki ne ya saka Salma ta bita ciki tana ta rarrashin dan kuka take yi sosai. Ta ce, "Haba Nayla meye na kukan don Allah?." Zata yi magana Didi ta kira Nayla a waya ta Wauka ta ce, "Didi barka da dare."
"Barka dai Nayla, an samu ™aruwa."
"Eh Didi."
"Allah ya raya mana ita."
"Amin Didi."

Didi ta ce, "tana gida ai ko?." Nayla ta ce, "eh tana gida, amma gobe da zasu wuce Kaduna."
"Kaduna! Na Wauka a nan zata zauna ai."
"Ai kowa na dangin mijin yana can itama kuma kinga haka, aiki ne kawai ya kawo shi nan shiyasa zasu koma." Didi ta ce, "kai amma ban ji daWi ba, bara yallaSai ya zo ya mi™a ni na yi mata barka bazan jira har sai ta dawo daga Kaduna ba."

A sanyaye Nayla ta ce, "To Didi." Yadda Didi ta ji maganar ta san tana cike da damuwa kuma ta san damuwar bai wuce tuna gida ba, in ba dan auren Omar ba da yanzu da ita za ayi shagalin haihuwar nan amma yanzu babu ita. Sallama suka yi Didi bata tambayeta abinda ya faru ba dan ta san amsar, kuma a ganinta abinda ya faru family issue ne bai shafe ta ba.

Salma ta kalle ta bayan ta kashe wayar ta ce, "meyasa ki ke kuka don Allah? Ki yi ha™uri mana dole ne zuwa Kaduna?." Ta kalli Salma cikin kuka ta ce, "Salma Twiny fa, komai tare mu ke yi, tare muka tashi muka yi komai. Sunan ´arta ta fari ace babu ni za a yi ai dole na yi kuka."
"To ya zaki yi? Ko zaki je ne?."
"A gaban ku dai Abiy ya ce kar na sake zuwar masa gida sai ya neme ni, ta ya zan je masa gida yanzu bai neme ni ba?."

"To ki yi ha™uri, ni kukan ne bana so naga kina yi." Nayla tayi murmushi kawai ta ce, "Salma ni kaWai na san abinda nake ji a zuciyata. Mahaifina ya ce kar nazo masa gida sai ya neme ni, akwai abinda ya kai wannan taSa zuciya da sanya zubar hawaye? Tunda na zo gidan nan ko video call ban yi dashi ba, ke kin san yadda nake da Abiy dole na shiga damuwa."
"Na sani, amma ki yi ha™uri."
"Na yi Salma." Ta faWa a sanyaye ta jingina da kujera. Da™yar Salma ta rarrasheta sannan ta tafi saboda dare ya yi har an yi i'sha.

Omar duk ya ji abinda aka tattauna, yana mamakin wai meye dalilin mahaifinta na aura masa ita? Me tayi masa har ya ce kar ta zo masa gida?. Yana zaune a Waki yana tunani babu mai bashi amsa haka ya kawar da tunanin daga zuciyar sa.

" " " " " " "

Narma ta ware sosai ta samu sau™i sai dai ta zama shiru-shiru babu magana sai ta zama dole, ko yaushe tana Waki, ko aiki ta daina zuwa, bata hira da kowa sai ta ga dama. Mum ta yi mata faWan har ta gaji ta share ta itama, kuma har lokacin laifin Omar take gani shine ya saka ´arta a wannan yanayi.

Da daddare suna zaune a dining tana juya spoon Win hannunta plate Win gabanta tana yiwa abincin cin yanga. Dad ne ya kalle ta ya ce, "Daughter me yasa ki ke haka?." Ta ajjiye spoon Win ta ce, "Dad me na yi?." Dad ya ce, "kin koma wani iri ko magana bakya yi, hakan daidai ne a rayuwarki?." Kawar da kai ta yi ta ce, "Dad kawai bana son hayaniya ne."

Dad ya kalli Mum da take kallosa suka yi mata shiru bata ce komai ba. BuWe ™ofar falon aka yi aka shigo duk suka kalli wanda ya shigo suna mamakin ganinsa. Dad ya mi™e tsaye ya ce, "Ashraf! me ka zo yi gidan nan?." Ashraf ya ce, "Dad I just come here because of my wife, I need to take her out." Mum ya mi™e tsaye ta ce, "You're not serious Ashraf. Let me tell you something, Narma ta gama auren ka wallahi. Divorce paper zaka bata ko kana so baka so."

Ashraf ya ce, "Mum bazan sake ta ba, Ina son zama da matata." Dad ya kalle shi cikin fusata ya ce, "Ashraf ka fita ka bani waje, zan yi magana da babanka baza ka kuma zaman aure da Narma ba har abada." Ashraf ya kalli Narma ta da take zaune tana kallon sa ya kalli Dad ya ce, "Dad gaskiya bazan sake ta ba, Ina son matata, babu wanda zai saka na sake ta."
"Dole ka sake ni Ashraf ko baka so!" Narma ta faWa tana tasowa daga inda take tana kallon sa.

˜are mata kallo yake yi, sabuwar sha'awarta na sake kunnuwa a zuciyarsa. Tana sanye da shigarta ta ko yaushe, ya ce, "Bazan sake ki ba Narma, ko me zai faru wallahi ina tare dake matsayin miji." Narma ta ce, "Wallahi sai ka sake ni, ai ko kana so ko baka so zama da ni ya ™are a rayuwarka."

"Haka ki ke tunani kawai, amma har yanzu lokaci sakin ki bai yi ba dan ban ga wanda ya isa ya saka na sake ki ba Narma. Wato na sakeki ki komawa wancan Wan shaye-shayen Wan daba ko? To baki isa ba wallahi.

"Šan daba ya fi min kai sau dubu, Ina sonsa son da bana yi maka shi, kuma bazan yi maka shi ba har abada."
"Wannan ke ta dama kuma Narma, abinda na sani you're my wife, dole kuma ki yi abinda nake so" ya faWa yana ™are mata kallo.

Mum ce ta katse shi ta ce, "Ashraf fita ka bar gidan nan, ka cire komawar Narma gidan ka domin baza ta taSa komawa ba har abada." Ya kalli Mum ya ce, "Mum ko court bazata raba aurena da ita ba wallahi, Ina son zama da ita." Dad ya ce, "ka san kana sonta ka dinga wahalar da ita?." Narma ta ce, "Dad ba ya sona, ya faWa min ba sau Waya ba baya ™aunata."

A fusace ya juya ya kalle ta ya ce, "eh bana son ki, bana ™aunar ki kuma bazan sake ki ba!." Dad ya kalle shi cikin tsananin fusata ya ce, "you know what? It's my fault, laifina ne da na dau™i aure na baka ba tare da na yi bincike mai kyau a kan ka ba. Laifina ne da na duba relationship Wina da mahaifinka na dau™i my own daughter na baka ba tare da ka bayar da ko sisi ba. Amma yanzu dole sai ka sake ta ko kana so ko baka so Ashraf, zaman ta da kai ya kare."

Mum ta ce, "Ko kunya baya ji, in front of our eyes yake faWar baya son Narma, kuma kana expecting zamu sake baka ita ne ta zauna da kai? Ka goge wannan tunanin daga ranka Narma baza ta sake zaman auren da kai ba."
"I'm sorry Mum and Dad, bazan iya sakin ta ba kome za a yi sai dai ayi. Kuma zan Wauki matata a duk lokacin da naga dama" ya faWa yana fita daga falon.

Narma ta kalli Dad cikin kuka ta ce, "Dad kalli abinda ka jawo mana, lokacin da na ce bana sonsa baku saurare ni ba ku ka yi forcing Wina akan aurensa. Na ce ban so amma babu wanda ya saurare ni balle a fahimci bana so Win. Dad duk abinda ya same ni ku ne silar komai, duk halin da na shiga ku ne ku ka jawo, inaa da wanda nake so, na kawo shi gidan nan ku ka wula™anta shi saboda ra'ayinku, na Wauka duk abinda nake so zaku yi min amma kun kasa. It's over!" ta faWa tana hawa sama a guje tana kuka sosai.

Mum ta kalli Dad a fusace ta ce, "Duk abinda ya faru da ´ata bazan ™yale Ashraf ba wallahi, babu ruwan da abinda yake tsakanin ka da mahaifinsa, zan yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata" ta faWa tana barin dining Win itama. Dad ya yi shiru ya bisu da kallo a lokacin Najwa ma ta tashi ta hau sama, ya yi ajiyar zuciya yana ji a zuciyarsa duk abinda ya faru da Narma kamar shine sila.KRB3P025
Arewabooks@nanahaleema11.

An yi shagalin sunan a Kaduna, yarinya ta ci sunan mahaifiyar mijin suna yi mata la™aSi da Mihada. Nayla a waya take ganin komai gabaWaya ta damu da rashin zuwanta, sai da Yaya J ya kira ta ya dinga rarrashi sannan ta sake ta cigaba da harkokinta

Zaman su da Omar yana nan yadda yake babu abinda ya canja, tana fita aikin ta dawo wani lokacin ta wuce gidan Hajja ko gidan iyayenta da suke garin sai

Please Login or Register in order to submit comment