Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa, ina wani aiki yanzu." Yarom ya amsa ya fita.

Ya samu Sen a zaune ya ce, "Boss ya ce ka jira shi yana zuwa." Da mamaki yake kallon yaron ya ce, "ka faWa waye ya zo nemansa?."
"na sanka ne da zan faWa masa waye?."
"Ka koma ka ce masa Sen Sagir ne yazo."
"Umarninsa nake bi ba naka ba, in kai shugaban ™asa ne ba sanata ba abinda yace shi zan yi" ya faWa yana wucewa ya bashi waje. Sen cike da ™unar rai ya bi yaron da kallo, sai yanzu yake dana sanin rashin tahowa da escort, da tare suke dasu babu abinda zai hana bai saka an yiwa yaron dukan tsiya ba.

       Sen ya gama zuwa wuya, sama da mintina talatin yana jiran Omar bai ce ya shigo ba. Sai wuci yake shi kaWai yana ™wafa, Allah ya taimaka wajan ba public waje bane da ya shiga uku da jin kunya. Narma kaWai yake hange a idanunsa, in ba dan haka ba da yanzu ya saka an tashi wajan, amma ita yake tunawa shiyasa yake yin sanyi. Bashir ne ya zo wucewa ya ga babban mutum kamar Sen yana jiran Boss Winsu. Ya bishi da kallon mamaki, bai yi magana ba ya shiga wajan Omar. A tsaye ya samu Omar yana Waukar wayarsa da key da alama fita zai yi. Bash ya ce, "Tiger kana da ba™o a waje."

Omar ya Wan dafe kai ya ce, "na manta, ka ce ya shigo" sai ya kalli agogo ya ce, "duk da dai sauri nake yi." Bashir bai faWa masa waye ba ya Wauki abinda ya kawo shi wajan Omar Win ya fita.P099

      Da sallama aka shigo ya Wago tare da amsawa idanunsa suka haWu da na Sen Sagir. Omar ya gyara zama yana kallonsa da matu™ar mamaki amma bai ce komai ba, ya ™araso ya zauna yana kallon Omar kamar yadda yake kallonsa, Hannu ya mi™awa Omar alamunsu gaisa, ba musu Omar ya bashi hannu suka gaisa. Yangance Sen ya ce, "Ya aiki? Ka barni ina jira for more than 40mints." Omar ya ce, "Alhamdu lillah.... Ban san da zuwan ka ba, so dole zaka jira na gama abinda nake yi." Sen ya yi ajiyar zuciya, bai bari maganar ta yi tasiri a ransa ba, Narma kaWai yake gani hakan ya saka ya ce, "Tiger nazo tun daga Abuja kawai saboda na ganka."

Omar ya Wan taSe baki ya ce, "zaSe ya kusa ko? Kamar saura ´an kwanaki kaWan na ji ana cewa ko?." Sen ya kalli Omar suka haWa ido sai Omar ya ce, "Yanzu ba wancan tiger Win da ka sani ba bane, wannan Tigers Footwear ne. In ma kana neman wanda zasu yi maka aiki kamar yadda ka saba zaka iya zuwa bakin titi suna nan suna zaman jiran zuwanka, in maganar da ta kawo ka kenan ina da ba™in da zan yi" Omar ya faWa yana cigaba da duba abinda yake gabansa.

Sen ya daure ya ce, "Ba wannan maganar ce ta kawo ni ba."
"Ina jinka, but don't waste my time, ina da ba™i suna jirana."
"Omar na zo ne akan batun Narma." Da sauri Omar ya kalle shi kana ya ce, "Driver take nema ne?."

Sen ya kalli Omar jin ba™ar magana yake faWa masa a fakaice, amma saboda Narma da halin da take ciki sai ya kawar da maganar Omar ya ce, "Omar wannan ya wuce ya kamata ka manta komai ya wuce. Narma ta shiga damuwa a kanka, tana matu™ar sonka, in ta rasa ka zata shiga damuwa sosai. Please Omar ka amince ka karSi auren Narma, this the first time da nake ro™on wani a rayuwata, i beg you for that, ka amince ka auri Narma in ba haka ba zata iya samun matsala."

Omar ya zuba masa ido yana kallonsa cikin mamaki da al'ajabi, wato yanzu ya zama mutum kenan, tunda da ya ce kallon dabba yake masa, ya ce ma gwara dabba akansa. Yanzu ya tashi daga jahili kenan ya dawo mai ilimi tunda gashi a zaune a cikin office Winsa yana kallonsa yana faWa masa ya auri ´arsa, yanzu ya tashi daga wanda bai zai kaiwani mataki a rayuwarsa ba ya dawo mai matsayi a idon sanata. Soyayyar da ake i™irarin yayi asiri yanzu ta dawo ta gaskiya tunda gashi ana cewa ya aure ta. Omar ya dinga binsa da kallo yana tuna abinda ya faru a baya, hakan ya saka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. In ba dan ma yana so ya nuna masa banbancin da da yanzu shi ya isa ya iya haWa ido dashi?.

Sen ba tare da jin nauyi ba ya ce, "Gab take da kamuwa da heart attack Omar, ka amince da ita ka aureta zata zama matarka ta biyu, dan ta zo a sencond wife Winka ba wani abun damuwa ba ne."

Omar ya girgiza kai cikin dubun mamaki, ya yi wani irin murmushi na rainin hankali ya kalle shi ya ce, "Sen Sagir Sani Shatima, yau kaine ka ke neman alfarma a wajan Omar? Ka manta waye Omar ne a wajanka?."

Sen ya ce, "ka ji na ce komai ya wuce ai, ni dai burina ka amince ka auri Narma please ." Omar ya jingina da kujerar office yana Wan motsawa a hankali tana juya shi kaWan-kaWan ya ce, "to abin ne yake bani mamaki, ka manta kace dabba ta fi ni wajan ka? Ka manta kace ko a mai gadin gidanka bazan zo ba balle sirikin ka?. To ya aka yi aka haihu a ragaya? Ko dai Satan kai ka yi kazo wajena? Dan na san ba ni Omar Win ka ke nema ba."

Sen ya yi shiru bai ce komai ba Omar ya ce, "Wannan Omar Win ba shi da ilimin da zai auri ´arka, ´arka tana matakin masters ko? ³arka tana juya kuWin masu yawa ko? ³arka tafi ™arfina sai dai na zo a mai gadinta ko?. Ina so ka tuna  wannan Omar Win fa ko takardun secondary bashi dasu har gobe, kai da kan ka ka ce baka Waukar mutum aiki a gidanka sai yana da takardar digree ko masters, to ya aka yi ka ke so ka bawa ´arka jalihin mutum irin Omar?."

Sen ya ce, "Please Omar! Abinda ya faru ya riga ya wuce, ka manta mu kalli abinda yake present a yanzu."

Omar ya sake yin murmushi ya ce, "Shine nake mamaki ai Sen Sagir, ta ya zaka amince ka bawa ´arka wanda babu matakin rayuwar da zai iya kai wa?. Ka ce wanda ba shi da ilimi babu inda yake zuwa sai dai rayuwarsa ta ™are a kan titi kuna cigaba da amfani da rayuwarsu wajan gina ta ku rayuwar da ta ´a´anku. Shine amfanin mu kawai a wajanku, ya aka yi ka zo kana son irin wannan namijin ya auri ´arka?."

Sen ya yi ajiyar zuciya yayi ya ce, "Omar ka daina wannan maganar, yanzu magana ake ta ceton rayuwar yarinyata, tana sonka, tana ™aunarka, tana so ya rayu dakai a matsayin mijinta. Na amince ka aure ta ko dan ceton rayuwarta." Omar ya yi murmushi yana kallonsa yana girgiza kai cike da mamakin Wan adam ya ce, "Senator Sagir Sani Shatima kenan...." ya sake yin ´ar dariya ta rsinin hankali ya ce, "tambayarka nake so na yi." Ya kalle shi alamun ina ji, Omar ya ce, "waye ni?." Sen ya ce, "Omar mana."
"Ina nufin waye ni..Kai ba Senator ba ne? So nake ka faWa min ni waye kamar yadda ka faWa min a wancan lokacin."

Sen ya ce, "Omar ne kai, C.E.O Exclusive Footwear." Omar ya yi murmushi yana girgiza kai  ya ce, "A'a, Tiger ne wannan, Wan daba, Wan shaye-shaye, mara aikin yi, wanda yayarsa take Waukar Wawainiyar rayuwarsa saboda ya gaza. Mara ilimi ne, jahili, wanda ya yiwa ´arka asiri, wanda bazai je ko ina a rayuwa ba, Ko ba haka ka ce ba?."

Sen ya yi shiru bai ce komai. Omar ya ce, "Haba Sen, yanzu shi ka ke so kace zaka aurawa ´arka? Ko dai ka yi Satan hanya ne kana neman wani Omar Win ba ni ba?." Nan ma ya yi shiru bai ce komai ba. Omar ya Waure fuska sosai, ya canja daga lokacin fara'a ya dawo lokacin rashin mutumci ya ce, "Alhaji Sagir zan ce ko Malam Sagi..?"

Ya sake girgiza kai ya ce, "ina so ka sani ba lallai sai kana da ilimin boko zaka kai wani mataki a rayuwarka ba, meye ilimin bokon....? Turanci ko?. Ina so ka sani akwai masu Digree da masters Win da ka ke ta™ama dashi a ™ar™ashina a cikin wajan nan, ni da ka ke kallo bani da ilimi ni ne nake biyansu albashi a duk wata. Ni Win dai da kake kallo matsayin wanda ba zai je ko ina a rayuwa ba ni ne dai na kai matakin da kai baka je shi ba. Ba kai kaWai ka taSa yin senator a Nigeria ba, amma ni ni ne kaWai akan matakin babu wanda ya taSa kaiwa a kaf africa ba nigeria kaWai ba, duk wanda zai samu matsayin da na samu a yanzu a bayana yake, ko babu komai sai an ce ai Omar ne ya fara kafin wannan. Ko a iya haka Allah ya bar ni Alhamdu lillah, ya gama yi min komai a rayuwa, balle kullum sake cigaba nake yi."

Omar ya Wan yi murmushi ya nuna shi da ya yatsa ya ce, "Dama ba nace ka kasance a raye ba? Ka Wauka wasa nake yi ko?. To gaka da rai a gaban Omar a zaune ka zo neman alfarma..." ya faWa yana girgiza kai yana smilling.

"Kazo aurawa Omar ´arka amma ka hana Tiger ´arka saboda kana kallonsa a ™as™ance ko?. Ina so na faWa maka wani abu Sagir, ´arka Narma bani da bu™atarta a cikin rayuwata, ta je ta auri daidai da rayuwarta mai ilimi wanda yake ri™e da babban compony kamar dai ita. Ni ka bar ni na cigaba da rayuwata da wanda suke daidai ni ita taje tayi rayuwarta. Bani da bu™atarta a cikin rayuwata, ta shigo rayuwata ne dan ta jani na je gidanka ka faWa min maganar da raina zai Saci na zubar da shashancin da nake yi a baya. Amfanin Narma kenan a rayuwata, kuma in na tuna da hakan ina gode mata har a zuciyata amma ba dan ina kallonta da wani matsayi ba. Ban taSa son ´arka ba, ta zama silar amsa kiran rabo na ne shiyasa har amince na je gidanka ba tare da na tantance soyayya da burgewa ba. Dan haka kar a sake zuwar min da wannan maganar, bani da bu™atar aurenta kuma bazan yi ba, ta samu daidai ita ta aura!."


Sen Sagir ransa ya kai ™arshe wajan Saci, mamakin Omar yake yi da yake faWa masa magana kamar bai san matsayinsa ba. Ya kalli Omar ya ce, "Dan ma ka samu kamar ni na zo ina yi maka zancen ka auri yarinyata shine ka ke faWa min magana?." Omar ya sake Waure fuska ya ce, "shiyasa nace ka bar ta bani da bu™ata, a kai kasuwa in tallanta ka ke yi, ni baza ka samu damar na taya ba balle har na siya. Meye ma sunanka......Sagir ko? Ina so ka sani a office Win Omar ka ke, ka san irin maganar da zaka faWa min, kar ka ja raina ya Saci na nuna maka asalin waye ni yanzun nan. Bana son hayaniya, dan haka bismillah..." ya faWa yana nuna masa ™ofa ba tare da ya kalle shi ba.

Sen ya girgiza kai cikin Sacin rai tare da yin ™wafa, zai fita kenan Omar ya ce, "ka je ka samu a karya asirin da na yiwa ´arka, dan bazata taSa samun Omar ba koda zata mutu. In ta mutu bani da asara, asara kai ta kama bani ba." Sen ya girgiza kai ya fita daga office Win ransa a Sace. Omar tsaki ya yi, ko kaWan babu Sacin rai a tare da shi, babu komai a zuciyarsa a haka ya cigaba da harkokinsa.P100

Omar bai jima an office Win ba ya koma gida, sai ya tarar ana ta aikin naman suna, ´an aiki suna ta aiki ya yi mamaki dan shi ya Wauka an gama. Ta baya ya shiga har samansa ba tare da kowa ya ganshi ba. Farin ciki yake ji a zuciyarsa sosai, ko babu komai yau Allah ya nunawa Sanata in ya yi nufin yiwa bawansa abu babu wanda ya isa ya hana, Allah ya nunawa masa shima yana da tasa baiwar, akwai kuma inda yake da ™warewa a kai wanda shi bashi da ita. Gashi shine ya zauna a gabansa yana neman alfarmar ya auri ´arsa, ko a yanzu Allah ya Wauki ransa ya gama yi masa komai.


Nayla ta ga dawowarsa, daman ta yi kwalliya cikin material tayi Waurin Wankwali tayi adon gashi a baya, in ka kalle ta baza ka ce itace ta haihu ba saboda yadda jikinta yayi kyau ya kame waje Waya. Falon nasa ta shiga da sallama hannunta Wauke da plate ta ajjiye akan table ta ce, "YaMar sannu da zuwa." Jin maganarta sai ya juyo yana kallon ta, ta bai san ya zuba mata ido ba saboda yadda kayan suka yi mata kyau, gashi dai basu nuna jikinta ba amma sun yi mata bala'in kyau, sun haska fuskarta.

   Kai ya Waga mata bayan ya janye idonsa daga kanta, ta Wan tura masa plate Win soyayyen naman da yake ta ™hamshi yake yi ta ce, "Ga naman suna." Kallon plate Win ya yi yaga harda yaji a gefe ya Wauke kai ba tare da ya Wauka ba, abinda bai dame shi ba kenan shi a rayuwarsa, da rayuwar nama da babu duk Waya ne. Komawa ta yi ta kawo masa lafiyayyen zoSon mai sanyi wanda tayi order a wajan leemars_delicous a jug, ta zuba masa a glass cup ta ajjiye masa ta ce, "ka ci naman sunan Didi."

TaSe baki ya yi ya ce, "ina take?."
"Wanka ake yi mata."
"Okay" ya faWa yana Waukar zoSom bai ce komai ba. Nayla ta rasa wacce irin zuciya ce da Omar, in ya yi fushi kamar shi kaWai aka fara yiwa laifi a duniya, sai ta sha wahala yake sakkowa, shiyasa wani lokacin take share shi yayi ya gama yazo ya same ta.

"YaMar wai baka daina fushin ba?." Har zuciyarsa ya ji maganarta, ya lumshe ido ya buWe yana shan zoSon bai ce komai ba. Mi™ewa ta yi ta fita dga falon sai bita da kallo. Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "na rasa meyasa bana iya dogon fushi da ita, in Didi ce tayi min wannan laifin sai nayi kwana uku bana kula ta, amma ita kwana Waya duk na damu" ya faWa tana shafa kansa cikin kewarta. Ba jimawa ta dawo da abinci ta ajjiye masa ta zauna kusa daahi ta ce, "na zuba maka abincin?."

      Ya kalli idanunta itama tana kallon nasa bata Wauke ba, ba shi shiri ya Wauke kai yana jin shock Win idanunta har cikin ™wawalwarta. Hannunsa ta ri™e ta ce, "YaMar don Allah ka yi ha™uri, na san nayi laifi amma bazan sake ba." Yadda take murza yatsunsa tana shagwaSa ya saka ya lumshe ido ya furta, "Ashiq!" Ba tare da ya san ya yi ba. Jin ya yi magana sai ta sake langwaSar da kai ta ce, "Please!."

      Sake kallon tsakiyar idanunta ya yi ya tafi da idon kamar zai rufe sai ya buWe a cikin nata, wannan Wabi'a ta sa tana kashe ta, ta yi saurin sauke ido ™asa ta ce, "Please Rouhi!." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba. Nayla ta Wauki plate ta zuba masa abinci tana ri™e da abincin ta ce, "Rouhi ka ga har yanzu ba lafiya ce dani ba." ˜arar wayarta ya saka ta Wauke kai daga kansa ta kalli wayar shi kuma yana kallonta, sai ya ga fara'arta ta ™aru ta ce, "Didi ce Rouhi, daman ta dawo ne?."

"Hello Didi" Shiru ta yi tana murmushi kafin ta ce, "Ina falon YaMar, ki shigo." Murmushi ya ga tana yi cikin farin ciki, yana jin daWin yadda take matu™ar qaunar Didi, hakan yana burge sa sosai, yana kuma ™ara mata ™ima da matsayi a zuciyarsa.

      BuWe ™ofar aka yi Didi ta shigo ri™e da Marmerh, Nayla ta mi™e ta taka a nutse ta rungume Didi cikin muryar ganinta. Didi ta ri™e ta tana murmushi ta kalle ta ta ce, "Ma sha Allah, wallahi kamar ba ke kika haihu ba, kin yi kyau ga wani ™hamshi na musamman da ki ke yi."

"Saukar yaushe Didi?."
"Šazu da safe."
"Amma shine baki huta ba ki ka fito?."
"Waye yake ta hutu...? Ina Musliha Win?." Nayla ta ce, "tana ciki, bara na karSo miki ita." Didi ta ce, "bara na koma na karSota dai" ta faWa tana juyawa ta koma. Nayla ta kalli Marmerh da ta ke zaune Ware-Ware a kan cinyar Omar.

Nayla ta ce, "Marmerh baki ganni ba?.." juyowa tayi ta yi dariya irin ta yara, Nayla ta yi murmushi tana kallon Omar da yake ta zuba murmushi yaga rabin ransa.

      Didi ce ta dawo Wauke da Musliha ta ™araso inda Omar yake tana kallonsa, ba dan Marmerh da take wajansa ba bata ma san yana falon ba. Ta Wan yi murmushi ta ce, "Alhaji Omar ba magana?." Ya kalle fuskarta, ba yabo ba fallasa ta ya ce, "ai na ga ba tani ki ke yi ba, ita da take son ganina ai ta zo inda nake" ya faWa yana nuna mata Marmerh.

     Didita yi ´ar dariya ta ce, "Alhaji Omar! Halin dai tana nan" ta faWa tana bashi hannu alamun su gaisa. Bai musa ba ya saka hannunsa a cikin nata kafin ya cire ya ce, "Hajiya Didi." Sai ta yi dariya ta zauna tana kallon Musliha ta ce, "Ma sha Allah tabarakallah, A zahiri ta fi kyau. Na jima ina tunanin irin yaran da zaku haifa yadda zasu kasance saboda kyau. Kalli dai Musliha kamar na sace ta, ni na rasa da wa take Kama wallahi, sai naga kamar fuskar Umma Saroot."

"A dangin wa zata yi kama da ita?." Ta ji Omar ya faWa ba tare da tayi tunani ba. Ta Wago ta kalle shi ta ce, "A dangin Mamanka." Kafin ya bata amsa ta kalli Nayla ta ce, "Sannu Nayla, Allah ya raya mana ita Allah ya yi mata albarka. Na gode Nayla da ki ka amince aka saka sunana, wallahi kwana nayi ina kukan farin ciki." Nayla ta Wan Sata rai ta ce, "Didi wannan godiyar ce bana so wallahi, tun kina can ki ke yi."

"Ai dole Nayla, sunana guda fa aka saka, in ba mai ™aunata ba ya za a yi hakan ya faru?." Nayla tayi murmushi ta ce, "To muna da wacce ta fiki ne?." Didi ta yi murmushi ta ce, "Babu Nayla."
"To kin ga ai daidai mu ka yi."
"Allah ya cigaba da baku zamana lafiya, ya tabbatar da farin cikina rayuwarku."

"Amin ya Allah Didi." Kallon Omar ta yi da yake ta biyewa Marmerh tana masa kwaranci, ta iya kiran Daddy raWau in ta ganshi, har mamakin yadda ta saba da Omar take yi.

Dariya Didi tayi ta ce, "su Omar Tiger an zama uba, Allah ya raya mana ita, Allah yasa silar haihuwarta yasa kayi hankali ka daina abinda bai kamata ba." Sai a sannan ya kalle ta sai ya yi wata dariya wacce ta Wauki hankalin Didi da Nayla, duk suka zuba masa ido suna jiran su ji dariyar ta meye, sai ya kuma ya gimtse fuska amma fuskarsa a sake take sosai.

Didi ta ce, "Wannan dariyar ta me ye?." Ya girgiza kai ya kalle ta ya ce, "Zan faWa miki amma sai ni dake, magana ce ta ´an uwa." Nayla tayi dariya sosai dan ta san da ita yake, Didi ma dariyar tayi tana jin farin ciki a zuciyarta.

Ta sake kallon sa ta ce, "Umma Saroot ta bani labarin yadda ka karSesu Omar, haka Kawu ma ya ce da ya kiraka ka Wauka har kun gaisa. Naji daWin hakan sosai, burina da rage ka daidaita da ahlinmu." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ta ce, "Saura ka je ka yiwa Kawu godiyar gidan da ka zauna." Nan ma bai ce komai ya yi mata banza. Nayla aka yiwa waya tayi ba™i dole ta mi™e ta basu waje.

     Da kallo ya bita har ta Sace sannan ya yi ajiyar zuciya, ya kalli Didi ta ™asan ido da take kallonsa ya ce, "Meyasa nake iya dogon fushi da kowa amma ban da ita? Ko ke ina iya yin sati ban kula ki ba, amma ita ´an awannin kawai duk sai na damu, daurewa kawai nake yi."

Didi ta yi dariya sosai ta ce, "To ita ai matarka ce, baza kaso kaga tana fushi ba ko kaWan,ita rayuwarka ce Omar. Kusancin mata da miji ai ba ™arya bane kuma ba wasa ba ne, balle kai da ka ke matu™ar sonta." Ya kalli Didi ya ce, "inda ki ka san na haWWiyetaa na huta, kamar na yi mata sabon rai ta haWa biyu haka nake ji Didi." Didi ta ce, "to ai kaga baza ka haWa ni da ita ba, kowa yana da matsayinsa a wajanka. Kuma Nayla ta cancanci ka sota ai Omar, ta sadaukar da komai nata saboda kai."

"An fara yi min gorin da aka saba, nima ai na sadaukar da komai saboda ita" ya faWa yana ri™e hannun Marmerh. Didi ta ce, "Amma ba kamar ta ba, ta tashi cikin gata amma ta amince ta yi rayuwa da kai."
"Kar ta amince Win mana."
"Da yake ta haifa maka ´a ai dole kace haka, lokacin da soyayyarta tayi ™o™arin kai ka kushewa ai baka ce haka ba."
Ya Wan yi murmushi tare da yin ajiyar zuciya, ya kalli naman gabansa ya ce, "baza ki ci ba?."
"Wannan naka ne ai."
"Kin san ba damuna ya yi ba, ko son ci bana yi. A nan zaki kwana amma dai ko?."
"Kwana kuma Omar? A'a dai."
"Amma tunda aka gama gina apartment Winki baki taSa kwana ba."

Didi tayi dariya ta ce, "Zan kwana Omar. Bara na koma wajanta." Bai ce komai ba ta tafi ta barshi da Marmerh.KRB3P101

Dad rai a Sace ya koma, tunda Mum ta ganshi gabanta ya faWi dan yanayinsa kawai ya nuna mata bai amince ba. Bai tsaya a falo ba bai kuma bari Narma ta ganshi ba ya shiga Waki ya zauna yana jin zuciyarsa a wuya. Mum ce ta shigo ta rufe ™ofa ta kalle shi ta ce, "Me ya faru? Me ya faru my dear?." Dad ya kalle ta ya ce, "Ni yaron nan zai kalla ya dinga faWa min maganar banza da wofi? Ni zai dinga kallo yana cewa baya son Narma bazai aure ta ba?."

Mum ta ce, "Wai Omar Win har ya samu damar faWa maka wannan kalaman? Me yake ta™ama dashi? Ko dan mun je wajansa da neman ya auri Narma shine zai samu damar faWa maka wannan maganar?." Dad ya ce, "idona yake kallo yana faWa min maganar banza. Daman can na san bashi da kunya kuma bashi da tsoro, Amma ban Wauka abin nasa ya kai haka ba, tunda har na je na yi magana dashi na Wauka zai amince. Ni ya kalla ya ce a kai Narma kasuwa bazai aureta ba."

Mum ta ce, "abinda nake gudu kenan, mu yada girman mu a wajansa kuma ya zuba mana ™asa a ido. Wannan soyayya da Narma take masa Allah ya tsine mata albarka, duk itace ta jawo mana, ba dan haka ba da yanzu muna nan hankalin mu a kwance babu wata damuwa." Dad ya yi ajiyar zuciya ransa na sake Saci yana girgiz kai. Mum ta ce, "To yanzu ya zamu yi da Narma? Ya zamu yi da ita?."

Narma ce ta shigo Wakin duk suka juya suna kallon ta, suka ga hawaye take yi ta zube a wajan akan guiwarta ta ce, "Dad ya ce bazai aure ni ba ko? Ya ce baya sona ko Dad?. Baya sona....haka ya ce baya sona....ya ce baya son Narma.....Narma ce baya so. Dad da ka amince dashi tun farko da yanzu nice matarsa....da yanzu nic cemu ka

Please Login or Register in order to submit comment