Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kasa magana sai kuka.

Jidda ce ta Wauke Marmerh ta ce, "Marmerh muje na baki cocholate?." Marmerh ta ce, "Ummi za ni." Jidda ta ce, "zan kai ki, amma ki fara sha ko?." Ta Waga kai sai kuma ta ce, "da daddy." Murmushi Jidda tayi, hawaye na zubo mata itama ta fita da Marmerh kamar yadda Musliha take hannun Salma.

Da™yar aka samu Nayla ta sakko ™asa saboda masu zuwa gaisuwa, in Omar baya nan dole ita za a nema. Nayla dai kallon mutane take yi har lokacin itama bata dawo daidai ba shiyasa ba a tura ta asibitin ba. A haka aka akayi kwana bakwai da rasuwar Didi, gida ya watse har lokacin Omar yana asibiti bai tashi ba.

Ranar kwana na takwas da yamma aka kai Nayla asibitin, Musliha da Marmerh suna wajan Umma Saroot dan ita a wajan Nayla take kwana.

Šakin da Omar yake ta shiga ta ganshi a kwance yana sauke numfashi a hankali, shafa kansa tayi da gashi ya taru gashin a kwance, kallo Waya zaka yi masa ka san ya rame sai haske da ya sake yi musamman fuskarsa da ™afarsa. Hawaye ta goge tana kallonsa ta zauna a gefensa tana kallo ™irjinta ma bugawa matu™a. A asibitin ranar ta kwana ita da Umma, wannan dare ya tuna mata Didi, dan da ace tana da rai tare zasu kwana da ita suna kula dashi. Ta sha kuka son ranta ta share hawaye tana yiwa Didi addu'a a zuciyarta.

     Washe gari da safe Nayla tana gefe a zaune a gefensa, Umma Saroot na gefe ita Marmerh da Musliha suna bacci Omar ya buWe ido. A hankali ya juyo ya kalli Umma Saroot da take zaune suka haWa ido sai ta ce, "Omar ka farka? Sannu" ta faWa tana mi™ewa zuwa inda yake.

Nayla ta kalle shi suka haWa ido, yadda idanunsa suka koma sai da gabanta ya faWi, ta ri™e hannunsa ta ce, "Sannu." Ido ya lumshe a hankali, ya jima a haka kafin ya sake buWe idon ya kalli Nayla muryarsa dashe matu™a ya ce, "Abinda ya faru mafarki ne ko gaskiya? Nayi mafarki wai Didi ta rasu, da gaske ne?."

Sai kawai Nayla ta fashe da kuka, ta Wora kanta a hannunsa hawayenta na sauka a hannunsa. Omar ya kafa mata ido yana kallo kafin ya kalli Umma Saroot da take tsaye tana goge hawaye ya ce, "Meyasa ku ke kuka? Ba mafarki na yi ba kenan? Ni na ri™e Didi aka sakata a kabari da gaske?."

   Da sauri Umma ta fita daga Wakin tana kuka, sai da ta daidai kanta sannan ta kira likita kamar yadda ya ce in ya farka a sanar dashi. Kallon Nayla ya yi da take kuka ya ce, "Hajiya ki daina kuka, zaki sake tayar masa da hankali. Kwanciyar hankalinsa ake da bu™ata yanzu." Nayla ta share hawaye likitan ya ce, "sannu." Bai iya motsawa ba likitan ya ce, "Akwai abinda yake damunka?."

Omar ya nuna kansa ya ce, "kaina na ciwo sosai, ™irjina ya yi nauyi kamar an Wora dutse."
"Sannu, damuwa ce tayi maka yawa, in ka sassautawa kanka zaka ji sau™i, Zaka iya tashi zaune?." Omar ya girgiza kai alamun a'a saboda baya jin ™arfi ko kaWan. Likitan ya ri™e babban Wan yatsansa na ™afa yana matsawa a hankali ya ce, "kana ji ina matsa ™afarka?." Omar ya Waga kai alamun yana ji, ya ri™e Wayar ™afar ma ban ma ya ce yana ji.

Hannunsa ya ri™e ya matsa nan ma ya ce yana ji likitan ya ce, "Zaka iya tashi, gwada." Omar ya motsa da™yar sai ya koma ya zauna ya ce, "kaina!."
"Sannu, in ka zauna zaka ji daWi." Da™yar ya mi™e ya zauna yana jan numfashi da ™yar. Bp Winsa ya auna ya ga jinin ya Wan sauka amma ba sosai ba, ya kalli Omar ya ce, "Kana da bu™atar ka yi wanka sannan ka ci abinci, zaka ji daWi sosai a jikinka." Omar ya lumshe ido bai ce komai ba likitan ya fita dan kawo magani.

   Umma Saroot ya kalla ya ce, "Ina Didi take? Ban ganta ba." Ya faWa dan shi manta maganar da aka yi a farkon tashinsa. Shiru tayi bata amsa ba ya kalli Nayla da take ta ajiyar zuciya ya ce, "Didi bata zo ba?." Nayla ta zuba masa ido bata ce komai ba. Murmushi ya yi kaWan ya kawar da kai gefe.

A lokacin su Kawu suka zo harda su Mama Zainab, su Kawu ne suka saka shi dole ya yi wanka aka kawo kaya daga gidan aka bashi tea Wan ya sha. Bayan ya gama ya yi sallolin da suke kansa ya koma ya zauna. Omar duk ya zama wani mai sanyi, komai aka ce masa kai yake Wagawa baya iya mayar da martani balle musu.

Da ya sha tea ya ji daWin jikinsa, sai nauyin da ™irjinsa yake yi masa kawai. Washe gari aka sallame shi bayan an yi masa hoton ™irjin da yake ta kuka da ya yi masa nauyi. Omar ya zama dan gata wajan dangi, kowa nuna masa ™auna yake yi, Nayla ta zama ´ar kallo tana gefe kawai.

     A hankali ta shiga Wakin ta same shi a tsaye yana kallon hotonsu tun lokacin da suke yara wanda ya Wauko daga gidansu. Jin shigowar Nayla ya saka shi ya kalle ta ya ajjiye hoton yana kallonta kamar yadda take kallonsa. Ya yi ajiyar zuciya ya kalli hotonsu shida ita da suka yi a madina ya ce, "Da gaske Didi ta rasu?."

Nayla ta Waga masa kai ta ce, "Didi ta tafi ta bar mu." Ya dafe kai yana salati ya ce, "Meyasa a lokacin da ta ri™e hannuna a asibiti na cire hannun na tashi? Meyasa ban zauna ri™e da ita har ta mutu ba?. Meyasa Didi zata mutu bayan ni ya kamata na fara mutuwa? Ta san ya rashinta zai yi min illah?. Jidda Didi ce uwata, Didi ce ubana, Didi ce yayata, Didi ce ™awata. Ta ya zan iya jure rashinta? Ta ya zan yi!" Ya furta a sanyaye yana kallon Nayla da ta fara hawaye.

Nayla ta taka zuwa inda yake ya sake kallonta ya ce, "Didi ce ta raine ni, itace komai nawa. Yau magana ake ta kwantanta goma a kabari, ni kuma gani ina rayuwa a duniya. Anya na yiwa Didi adalci Jidda!?."

Nayla ta kasa magana sai kuka da take yi, ya sake cewa, "Meyasa da ta ce tana son jin Wumin ™aninta ban rungumeta ba Jidda? Meyasa na bari ta bar duniya da kewar hakan a ranta? Na tabbata inda ni ne baza ta bar ni ba, zata saka ni a jikinta ta samar min da abinda nake so, amma ni na gaza!" Ya faWa yana kallon window cikin tsananin rauni.

Sai kuma ya juyo ya ce, "Da wannan hannun nawa na ri™e Didi aka sakata a kabari, ni...ni nayi mata wanka. Kenan ta tafi kenan? Ta tafi har abada bazan kuma ganinta ba?. Meyasa Didi zata mutu? Ta sha wahala dani, sai yanzu da lokacin jin daWi yazo zata tafi ta barni? Meyasa na bari ta rasu Jiddaaaa....meyasa?" Ya faWa da rauni sosai muryarsa rawa. Nayla ta kasa ri™e kukanta, ta saki kuka mai ™arfi sosai, ta taka a guje ta faWa jikinsa ta rungumesa. Wata irin runguma ya yi mata mai ™arfin gaske, ya matse ta gam a jikinsa kamar zai shigar da ita jikinsa.

"Didi ta tafi ta barni, ta tafi ta bar ni Jidda. Shikenan ni da ita baza mu sake ganin juna ba, bazata sake bani shawara ba, baza mu sake faWa ba, baza mu sake zama waje Waya ba Jidda, bazan sake kwana biyu ban kulata ba, baza ta sake bani hannu mu gaisa ba, bazan sake jin muryarta ba, bazan sake ganin dariyarta ba Jidda!. Shikenan komai ya ™are, shikenan....!" Ya fashe da kuka mai sauti yana sake matse Nayla a jikinsa hawaye na ambaliya daga idanunsa.

"Didi....didi...ta...."ya kasa magana saboda kuka, itama Nayla kuka take yi ya matseta ya hanata motsi a jikinsa, jikinsa na rawa kamar yadda muryarsa take rawa. Dukkansu kuka suke yi cikin rauni da bugawar zuciya, ji suke kamar a ranar Didi ta mutu, ji suke yi kamar babu wanda ya kai su ™unci da ba™in ciki a wannan lokaci. Sun kwashe mintina talatin a haka, tsayuwar sam bata ishesu ba saboda basa cikin hankalinsu.

Omar tunda ya fara kuka bai daina ba, kuka ya ke yi da zuciyarsa da gangar jikinsa, ya matse Nayla a jikinsa, jikinsa yana rawa kamar an jona masa wutar lantarki. Nayla ce ta motsa ta Wago daga jikinsa ta ri™e hannunsa zuwa kan kujera, ta ri™e kafaWunsa ya zauna sannan itama ta zauna a kusa dashi, ya sake kwantar da kansa a ™irjinta tana shafa a kansa a hankali.

Hawayensa a fatar jikinta yake sauka, ta yi shiru bata ce komai ba kamar yadda bai ce ba, sai dai ya rage sautin kukan sai hawaye da yake yi kawai wanda ya™i tsayawa. Ya Wago ya kalli Nayla yana lumshe ido saboda ciwon kai, ta goge masa hawayen idanunsa ya girgiza mata kai ya ce, "kar ki tafi ki barni kamar yadda Didi ta tafi kin ji Jidda. In kika barni haukacewa zan yi koda ban mutu ba. Ki bari na rigaki mutuwa kin ji? Ki bari na fara mutuwa kafin ke. Ke da Didi kawai nake da su kawai, ita ta tafi saura ke, kar kema ki tafi ki barni Jidda....in kika tafi haukacewa zan yi...." Ya faWa a rikice yana sake rungumeta a jikinsa sabon kuka na cigaba da zuba daga idanunsa.KRB3P116

A wannan yanayi bacci ya Wauke su dukka su biyun, basu tashi farkawa ba sai lokacin sallar la'asar. Nayla ta kalli fuskarsa da ta koma ja, idanunsa sun kumbura, gashi ya rame, gashin fuskarsa ya sake taruwa. Kallo Waya zaka yi masa ka san baya cikin hayyacinsa.

Nayla ta saka hannu tana shafa fuskarsa da take wuyanta har lokacin. A hankali ya buWe jajayen idanunsa ya kalle ta ta ce, "ana kiran sallah." Kai ya Waga bai ce komai ba, ta mi™e tsaye sai tayi kamar zata faWi ya ri™o hannunta da niyar ri™eta amma sai ta faWa kansa dan bashi da ™arfin iya ri™eta. Mi™ewa tayi daga jikinsa ta ce, "kazo ka yi alwala."

Hannunsa ta ri™e ya mi™e suka yi alwala suka yi sallar la'asar ya koma ya jingina da bango ya yi shiru baya cewa komai.

Nayla ta kalle shi cikim tsananin tausayi ta ce, "addu'a zaka dinga yi mata, wannan tunanin ba shine mafita ba." Ajiyar zuciya ya yi mai nauyi ya furzar da iska waje ya ce, "Ina Marmerh?." Nayla ta ce, "suna wajan Umma." Mi™ewa tsaye ya yi, ta mi™e itama ya ce, "zan je na ganta."

Hannunsa ta ri™e ta ce, "mu je tare." Tare suka fito har zuwa falon Nayla, suka samu Marmerh tana ta tsalle-tsalle tana yiwa Musliha wasa. Rauni ya sake mamaye zuciyar Omar, hawaye ya suka cika masa idanu. Marmerh ta juyo ta kalle sa sai gabansa ya faWi, rana ta farko da ya amince Marmerh da Didi take kama. Marmerh tana ganinsa ta yi dariya ta tawo a guje ta faWa jikinsa ta ce, "Daddy!." Šaukarta ya yi a kafaWarsa yana kallon fuskarta cikin ™auna da tausayinta da yake ji.

Marmerh ta ce, "Daddy, Ummi zani." Omar ya rufe ido ya buWe a raunane ya ce, "Marmerh Ummi ta rasu" Nayla ta ce, "Haba YaMar, ya zaka faWa mata haka kai tsaye? Duk da bata san mutuwa ba amma bai kamata...." Kallon Nayla ya yi sai bata ™arasa faWa ba, ya ce, "™arya ki ke so na yi mata? Na ce mata Mamanta tana da rai zata dawo in anjima?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "bazan iya saka mata rai akan abinda bazan iya bata shi ba har abada, gwara na faWa mata gaskiya."

Umma Saroot ta kalle su cikin rauni ta ce, "Ga abinci Omar, zauna ku ci don Allah." Ya Wago ido ya kalle ta, maganarsu ta ™arshe da Didi tazo zuciyarsa, ya lumshe ido ya buWe ya sake yin ajiyar zuciya ya kalli Umman kamar zai yi magana sai ya fasa. Umma ta matso ta ce, "Ku zauna don Allah." Nayla ta jawo hannunsa suka zauna, ta Wauki Musliha amma ba ita take so ta Wauke ta ba, shi take mi™awa hannu.

Ya karSe ta itama ya haWasu su biyu a jikinsa yana kallonsu. Umma ta zuba musu abinci Nayla ta karSa tana juyawa cokali bata ci ba shi kam bai ma karSa ba. Umma ta ce, "Omar." A hankali ya kalle ta ta ce, "ka ci abinci don Allah." Ajiyar zuciya ya yi ya karSa ya fara ci a hankali ba dan yana jin daWi ba, ko rabi bai ci ba ya ajjiye.

Kan Marmerh yake shafawa a hankali yana cewa, "Zan kula da rayuwarki, bazan taSa bari ki yi kukan rashin mahaifiya ba Marmerh. Zan sadaukar da duk abinda nake dashi dan na zauna dake kawai, zan miki gata a duniya, zan baki duk abinda ki ke so, bazan bari rayuwarki ta wula™anta ba, bazan bari ki san ba ni ne na haifeki ba Marmerh!. Zan tabbatar da kin samu nagarta a duniya, zan baki gatan da koda Didi tana da rai iya abinda zata yi miki kenan, bazan bari maraici ya taSa rayuwarki kamar yadda ya taSa ni ba, zan zama gatanki gaba da baya Marmerh, zan sadaukar da duk abinda nake dashi dan inganta rayuwarki! Ya faWa hawaye masu zafi suna sakkowa daga idonsa.

Sai Marmerh ta saka hannu tana goge masa ido, ya yi murmushi tare da sumbatarta a goshi, ya sumbaci Musliha da take kallonsa ya ce, "Zan kula da rayuwar ku gabaWaya in sha Allah, Allah ya bani aron ran da zan baku rayuwa mai kyau, Allah ya bani aron ran da zan kula da rayuwarku. In kuma nima na bi Didi kafin na samar muku da rayuwa mai kyau Jidda tana nan" ya faWa yana kallon Nayla. Suna haWa ido ta fashe da kuka ta kwantar da kai a kafaWarsa tana kuka. Umma Saroot ma kuka take yi gabaWaya ba su lura da Mama Zainab da Aisha da Baba Adamu a tsaye ba.

Mama Zainab ta ce, "Omar ku daina kuka, addu a." A hankali ya Wago ido ya kalle ta ya ce, "baza mu daina kuka ba, har abada!." Baba Adamu ya dafa shi ta baya ya juya ya kalle shi ya ce, "Sai ha™uri Omar. Ka daure ka cinye wannan jarabawar, kar ka sare lokaci guda. Allah ya ji™an Aisha ya gafarta mata, halinta na gari ya bita, Allah ya sa zaman kabari ya fi mata zaman duniya daWi."

"Amin& .amin ya Allah" ya furta yana lumshe ido tare da ajiyar zuciya. Yana ji ashe haka ake jin daWi in aka yiwa wanda ka rasa addu a?.

Marmerh ya kalla da take ta tsokanar Musliha tana yi mata wasa. Omar ajjiye Marmerh ya yi ya ajjiye Musliha ya mi™e tsaye Baba Adamu ya ce, "ina zaka je?."
Omar ya ce, "ba nisa zana yi ba, zan dawo yanzu."
"Amma baka da lafiyar da zaka iya fita kai kaWai."
"Zan iya, bazan jima ba zan dawo."

Mama Zainab ta ce, "A a Omar, kar ka fita wani abun ya same ka." Ya yi murmushi yana kallonsu yana jin wani iri a zuciyarsa, Didi da Nayla ne kaWai masu damuwa dashi, yau ssi ga dangin mahaifiyarsa suna tsoron kar ya fita wani abun ya same shi. Ya lumshe ido ya ce, "kuma tsoron kar nima na mutu ko? Suka kalle shi gabaWaya cikin rauni, ya girgiza kai ya ce,  Kar ku damu, Allah zai bani aron rai har sai na inganta rayuwar Marmerh" ya faWa yana fita daga falon. Nayla suka dinga bawa ha™uri ita dai jinsu take yi amma da ta tuna wani abun sai kuka.

Omar kuwa saboda ganganci da kansa ya ja mota, kai tsaye ma™abarta ya wuce ya je kabarin Didi ziyara. Addu'a yake mata yana kuka yana ji kamar ya tone kabarin ya fito da ita. Ya fi awa Waya a gaban kabarin sannan ya tashi ya shiga mota ya jima a zaune kafin ya tafi. Tafiya yake yana tunanin ya bar Didi a can shi kuma gashi a cikin mota yana tafiya, Didi bata duniya shi kuma yana duniya, sai ya ji kamar bai kyauta mata ba. Hawaye yake gogewa yana tafiya ya wuce gidan Didi.

A ™ofar gidanta ya ajjiye motar ya tsaya yana ™arewa gidan kallo. Jikinsa ya shafa yana nemn wayarsa, sai ya tuna bashi da waya bai ma san inda wayar take ba gashi yana son magana da AbdulHamid, kuma bazai iya shiga cikin gidan ba. Ana haka sai ga AbdulHamid ya fito Omar ya zuba masa ido, shi kansa AbdulHamid Win ya rame sosai kana kallonsa ka san yana cikin yanayi na damuwa. Omar ya sauke glass a sanyaye ya ce, "Mijin Didi."

AbdulHamid ya kalli Omar sai ya yi murmushi duk da gabansa ya faWi, Omar ya fito daga motar yana kallonsa AbdulHamdi ya ™araso inda Omar yake. Hannu Omar ya bashi suka gaisa ya ji jikin Omar zafi zau ya ce, "Omar baka da lafiya me ya fito da kai?." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "na jima a nan ina jiranka, bani da waya balle na kira ka, kuma bazan iya shiga gidan nan ba."

AbdulHamid ya yi murmushi ya ce, "Allah ya gafartawa Aisha."
"Amin ya Rabbi. Yanzu ma naje kabarinta na gaishe ta, amma ban ji ta amsa kamar ko yaushe ba. Tana cewa lafiya lau Alhaji Omar, da tana da rai da yanzu ta ce Omar me ya same ka, mu tafi asibiti" Omar ya yi murmushi hawaye na sake taruwa a idanunsa ya ce, "Amma yanzu ta tafi ta barni, ta bar duniya ni kuma ta bar a cikinta ko tausayin bata ji ba. Ko ta ya rayuwa zata yi min daWi bata tare dani oho, bata yi wannan tunanin ba ta mutu ta bar ni.

Sai kalamansa suka karyawa AbdulHamid zuciya ya goge ido ya ce, "Mutuwa bata bari wani dan wani ai Omar, dan ka rasa wani ba hakan yana nufin ka rasa farin ciki ba ne. Omar ya goge idanu ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Alfarma nazo nema a wajanka, ban sani ba ko zaka iya yi min."
"Ko wacce irin alfarma ce zan yi maka Omar, ka faWi komai da yake zuciyarka. Yadda Aisha zata yi maka duk abinda ka ke so nima zan yi Omar.

Omar ya girgiza ya ce, "Marmerh....! Marmerh nake so ka bar min ita ta dawo hannuna da zama. Na san abu ne mai wahala a gareka amma ka duba raunin da nake ciki na rashin Yayata, na san kai matarka rasa ni kuwa duniyata na rasa gabaWaya. Ka san itace komai nawa, ka san bani da kowa sai Didi. Zaman Marmerh tare dani zai Wan rage min wani abu kaWan daga cikin kewarta. Ka amince don Allah ka bani ita!."

AbdulHamid ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Omar ya ce, "Don Allah kar ka ce a a, nayi maka alqawarin zan bata tarbiyya mai kyau, zan inganta mata rayuwarta ba dan kai baza ka iya ba. Ina so na nuna mata ™aunar da baza ta yi maraicin uwa ba, kuma ba dan kai baza ka iya ba. Ka taimaka min don Allah!." AbdulHamid ya kalli Omar yaga gabaWaya ya canja, ya yi sanyi da rauni kamar bashi ba, gashi ya rame matu™a. Ya ce, "Shikenan Omar, na baka ri™on Marmerh."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya kalle shi ya ce, "na gode, na gode sosai." Ya yi murmushi ya ce, "babu komai, na san zaka kula da rayuwarta sosai, Allah ya baka ikon kula da ita."
"Amin..amin& Na gode sosai."
"Sai batun gadon yayarka, na fara tartara abinda na san ta mallaka domin a sauke mata nauyi."

Omar ya ce, "ka yi duk abinda ya kamata." AbdulHamid ya ce, "in sha Allah, Ka koma gida baka da lafiya." Omar ya Waga kai ya shiga mota ya tafi. AbdulHamid ya bishi da kallo cikin tausayi, ya jima bai ga Wan uwan da ya fita daga hankalinsa saboda mutuwar yayarsa ba sai Omar.P117

       Omar bai shiga gida ba sai da ya yi sallar magriba, a harabar gidan nan suka haWu da su Bashir suna jiran sa. Ganinsa duk suka taho suka gaishe shi ya amsa suna sake yi masa gaisuwa. Ya kalli Bashir da ya kasance shine manager, shine mai kula da komai in baya nan ya ce, "Bashir ka cigaba da kula da komai, duk abinda kaga ya dace ayi, in ya zama dole na sani sai ka kira ni." Bashir ya amsa a sanyaye, bai taSa ganin Tiger a cikin wannna yanayi ba, sai ya bashi tausayi ya wuce su ya shiga ciki.

Da Umma Saroot suka haWu, tana tsaye da hijjabi ta juya baya tana magana da masu aikin gidan magana. Kallonsa ta yi a sanyaye ta ce, "Omar ka dawo? Ya jikin?." Ya girgiza kai ya ce, "naji sau™i sosai. Fita zaki yi?." Tsayawa tayi tana kallonsa, sai ta yi saurin kawar da mamakinta ta ce, "Gida zan koma Omar, tunda ka samu lafiya."

"Meyasa zaki tafi? Kafin ta bashi amsa ya ce,  ko an Sata miki rai?. Ta girgiza kai ta ce,  Babu abinda aka yi min Omar, kawai zan koma ne. Omar ya ce,  Ki zauna don Allah" ya faWa a sanyaye yana kallon ta. Zata yi magana ya ce, "don Allah!."

Sanyi da daWi ya mamaye zuciyarta tayi murmushi ta ce, "To Omar, zan zauna zuwa wani lokaci."
"na gode Umma!" ya faWa yana wuce ta ya hau sama. Murmushin farin ciki take yi ta Wauki waya tana kiran ´an uwan tana basu labarin abinda Oamar ya yi mata.

Bai iya kuma fita ba a Waki ya yi sallar i'sha, Nayla ta kawo masa abinci har cikin Wakin ta zauna a kusa dashi ta ce, "ka ci abinci." Ya kalle ta ya ce, "har yanzu ™irjina bai daina nauyin nan ba, da na zubar da hawaye ya ragu amma akwai saura."
"Sai a hankali ai zai daina, ka cigaba da addu'a. Ga wayarka Wazu Baba ya bani bayan fitar ka." KarSa ya yi ya ajjiye a gefe.

Nayla ta ce, "ka ci abincin." Da kanta ta bashi ya Wan ci kaWan ya ce ya ishe shi, bata matsa masa sai ya cinye ba ta bashi magani ya sha. Wuyanta ya taSa ya ce, "kema baki da lafiya, kin rame sosai."
"Na samu sau™i, rashin ™arfin jiki ne kawai da bani dashi." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na je gidan Didi."

Ta kalle shi ya Waga kai ya ce, "Gidanta na gaskiya da gidanta na duniya, na kai mata ziyara kabarinta na gaisheta amma banga murmushinta ba, kuma ban ji sautin muryarta ba. Na yi mata addu'a ina kuma fatan addu ar ta iske ta."

Nayla ido ya ciko da hawaye ta ce, "amma baka faWa min mun je tare ba?." Ya kalle ta cikin sanyi ya ce, "Zaki iya zuwa?."

"Na taSa raka Abiy kabarin Ummana amma an jima sosai, shima yana zuwa ziyara duk ranar juma'a har yanzu. Nima zan je na yiwa Didi addu'a, in zaka je ka dinga faWa min." Ya ri™e fuskarta ya share mata hawaye ya ce, "in sha Allah zan faWa miki." Nayla ta bi fuskarsa da ta koma ´ar ™arama da kallo ta ce, "ka tuna maganar Didi ta ™arshe?." Ya Waga kai alamun eh ta ce, "ka cika mata burinta don Allah, ka yi abinda zata yi farin ciki a cikin kabarinta."

Ya ce, "Zan yi Jidda! Wallahi zan yi!. Zan ri™e kowa kamar yadda take so, zan bar komai ya wuce bazan sake tuna komai ba. Zan ri™e su kamar iyayena, zan nemi shawararsu da albarkarsu da komai, zan kuma nemi su yafe min, zan cika birin Didi in sha Allah!. Da ace na san mutuwa zata yi da na bar komai ya wuce tun tana duniya, da ace na san zata mutu bazan ™i amincewa da abinda take

Please Login or Register in order to submit comment