Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke awa ce, kuma Yaya ce a gare shi. In bai kyautata miki ba wa zai kyautatawa?."

"Amma Nayla akwai abubuwa da yawa a gabansa, ya zai kwashe kuWi ya siyo min gold?."
"Tunda ki ka ga ya yi ya san abinda yake dashi ne. Don Allah ki daina kuka Didi, in kina kuka zai ga kamar baki murna ba." Ta goge idonta ta ce, "bara na je na same shi."

Nayla ta ce, "A'a Didi, ki bar shi kawai kar ki gode tunda ya ce baya so." Didi ta ce, "Amma Nayla ta ya zan kasa gode masa?."
"Ya san kin gode Win ai, saboda haka ya ce miki shi Marmerh ya bawa, baya so ki yi masa godiya shiyasa ya ce ba ke ya bawa ba, don Allah ki yale shi kawai." Didi ta zauna tana goge ido tana sake kallon Wan kunnen cikin farin ciki.

Nayla fita tayi kamar yadda ya fita, Didi ta biyo bayan ta suka same shi a zaune a mota da Marmerh a hannunsa. Ganin sun fito sai ya fito ya bawa Didi ita AbdulHamid ya ce, "Omar Allah ya cigaba da shiga lamarinka, Mun gode sosai."
"Abokinka mai gida, har ka turo min number sa" ya faWa yana kallonsa ba tare da ya bashi waccan amsar ba. Abdulhamid ya ce, "yi hauri na manta ne."

Omar ya ce, "hmmm matarka ta koya maka halin Soye-Soye, tashi zamu yi daga gidan nan da lokaci kaWan, bazan cigaba da zama a gidan da ake yi min alfarma ba." Didi dai tana tsaye tana kallonsa tana murmushi da alfahari a zuciyarta.

Kallon ta ya yi kamar zai yi magana sai ya Wauke kai bai ce komai ba, ya shiga mota Nayla ta shiga ya ja motar yana murmushi. Ya san in ya biyewa Didi kuka zata yi masa shi kuma kuka ne baya so. Yana so ya saka Didi farin ciki a rayuwarsa, yana so ya ga tana dariya shiyasa yake jin daWi a duk lokacin da ya zama silar dariyarta. Cikin farin ciki ya cigaba da tafiya bayan ya rio hannun Nayla.KRB3P067

Rayuwa tana ta tafiya Omar da Nayla zaman su abin burgewa, ko yaushe cikin nunawa juna kulawa da soyayya suke tunda ta ajjiye aiki yanzu babu inda take zuwa sai ta kama take fita. angaren sana'ar Omar ba a cewa komai, albarka sai samuwa ta ke yi daga inda ba a yi tunanin zuwan ta ba, alkhairi kawai ake samu ta ko ina, dan yanzu shagunansa sun sake yawa sannan sun canja inda suke aikin sun koma babban waje, ma'aikata sun sake yawa. Kasancewarsa mutum ne mai kyautatawa ma'aikata da basu hainsu akan lokaci ya saka ake tururuwar son yin aiki dashi, sai dai yana da sharaWin babu wasa da aiki.

Ranar Sunday Nayla tana zaune a Waki da daddare sai ga kiran wayar Mama Sa'adatu. Nayla ta Wauka suka gaisa Mama ta ce, "Kin san bikin Yayanki Abbas ya kusa ai." Nayla ta ce, "Ummimi ta faWa min, na ce ashe akwai shagali, ga na Salma ga na shi."
"Sosai kam."
"Allah ya nuna mana."
"Amin. An kai kayan lefenki gidan Daddy Wazu."

Nayla da mamaki ta ce, "Kayan lefena kuma Mama? Wanne irin kayan lefe?." Ta yi dariya ta ce, "Da alama baki sani ba kenan, to ai mijinki ya haWa miki lefe Wazu muna zaune sai ga Yayarsa da wasu mata masu kama da shuwa, ta ce mana an uwan mahaifiyarsu ne sun kawo kaya wai lefen aurenki. Suna can a ajjiye kaya ba kaWan ba kaya masu uban yawa da tsada."

Nayla ta ce, "Wallahi ban sani ba Mama, ni ko da wasa bai faWa min ba, ban ma san labarin ba ban da yanzu."
"Shiyasa ai na kira na faWa miki. Daddy ya ce min na aika a kwashe a kai gidan ku Kaduna, Ni na Wauka ma ke kika yi masa maganar ya yi miki lefen."

"A'a wallahi Mama, ko da wasa ni ban taSa wannan maganar ba, ni wallahi na manta ma da batun wani lefe a duniyar nan."
"To shi bai manta ba kam, na yi matuar mamakin kayan da aka zuba a ciki, na ce Allah ya arawa nema albarka. Kaya dai suna nan a ajjiye, inda ki ka san lefen Salma aka kawo, hatta kayan kwalliya an zuba."

Nayla ta ce, "ikon Allah, ban sani ba." Mama ta ce, "Ya baki mamaki, Zan saka a Wauko hoton kayan a turo miki ki gani. Kaya sun yi kyau Nayla, sai ki yi masa godiya dan ya kashe kuWi wallahi ba kaWan ba." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "To Mama." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar.

"Wai kayan lefe" ta maimaita da mamaki dan bata Wauka zai faru ba. arasa saka kayan ta yi, ta saka kaya riga da siket an kanti, rigar tana high neak amma daga irji a Wan tsage take, sannan bayan ta a buWe yake. Siket Win kuma mai tsaga ne daga baya har cinyarta, kayan sun zauna ajikinta komai ya yi mata daidai. Gashin kanta ya sha gyara, ta gyara ta Waura aramin Wankwali. Ta gama shafa turare kenan ta ji ya shigo gidan, ta ajjiye abinda yake hannunta ta fito falon ta ce, "Welcome Rouhii" ta faWa tana arasawa ta Wan yi hugging Winsa kaWan kafin ta janye jikinta ta kalli fuskarsa ta ce, "ka gaji da yawa ko?."

Omar ya kulle idanunsa ya buWe ya ce, "na gaji." Ta ce, "sannu, mu je ka yi wanka yanzu sai kazo ka ci abinci." Bai musa mata ba suka tafi tare yana ta yaba kwaliyyarta ita kuma hakan ke yi mata daWi, shiyasa ko bata yi niyar yi ba in ta tuna in dai ya gani sai ya yaba sai ta yi. Wajan yabon kwalliyarta da abincinta yana sakawa ta ara aunarsa.

Tare suka fito bayan ya shirya ta kawo masa abinci, bai i ci ba ya ci bayan ya gama ya kalle ta ya ce, "Abubuwa suna neman yi min yawa Ashiq, bani da hutu ko kaWan, nan su kira ni a waya can su kira ni a waya. Gobe za a buWe shago a garinku, babu plan Win zuwa Kaduna a tsarina gobe, dole Bashir zan tura aje a san abinda za ayi."

Nayla ta ce, "Sannu Rouhi, Allah ya cigaba da saka mana albarka a duk abinda ka saka a gaba, Kuma in sha Allah na Kaduna ba za ka samu matsala dashi ba, yaron a gida mu ya tashi bashi da wata matsala."
"Amin ya rabbi. Amma ina shan wahala ko a iya amsa waya ne, gobe akwai bain da zan yi ina tunanin ma nan gidan zasu same ni, kinga bani da lokacin zuwa Kaduna."

Nayla ta ce, "na ce ka naWa ni na zama personal assistant Winka amma ka i, ka ga da ba sai na wakilce na zauna da bain ko na tafi Kadunan ba?." Ya Waga ido ya kalle ta cikin harara ya ce, "kawai sai na sallama ki ko wanne banza yana ganar min mata? Lalacewar tawa bata kai haka ba. Amma zan shigo dake ta dole, tunda naga na fara bai turawa dole sai kina kusa." Dariya tayi sosai ta ce, "Ba wani nan, kana fa jin turancin nan kawai baka son yin ne, inda ka damu dashi da yanzu ka kai inda baka Wauka zaka kai ba a iyawa." Ya taSe baki bai ce komai ba kafin ya gyara zama ya ce, "kina ji."

Nayla tayi dariya dan ta san indai zai ce kina ji Win nan magana mai mahimmaci ce, ta gyara zama ta ce, "ina ji."
"Me ki ke ganin zan iya a yanzu? Gida nan zan siya ko kuma na fara gina nawa?, Ko kina ganin na siyi babban waje da kuWin sai ayi lissafin nawa za a kashe in za a haWa babban company?. Nan yana neman yi mana kaWan, ma'aikata sai aruwa suke yi, wani so yake ko a mai goge-goge ne a Wauke shi. Kuma Alhamdu lillah tunda ana samun alkhairi bazan i Waukar ma'aikata ba."

Nayla ta ce, "ginin ya kamata ka fara yi, kafin a gama kaga an samu wasu kuWin sun sake shigowa in ya so daga sai a san ya za a yi a yi samar da company." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "To a ina ki ke so a yi ginin?."
"Wannan kai zan tambaya, kaine Wan Kano ai ba ni ba." Ya yi murmushi ya ce, "in sha Allah za a duba."

Nayla ta rio hannunsa ta ce, "YaMar!." Ya kalle ta bai yi magana ba ta ce, "Wai daman kayan lefe ka ke haWa min?." Ya Wan murmusa kaWan ya ce, "eh mana, Didi ta ce haka ake yi tun kafin haihuwar Marmerh tayi min mgaganar. Sai daga baya na dinga bata kuWin a hankali har aka tara da yawa aka siya aka huta."
"Amma Rouhii ni.....!" Ya katse ta ya ce, "kar ki faWi wani abu, in kaWan suka yi miki Jidda zan iya arar da abinda na mallaka a kan ki, In akwai abinda ki ke so ki faWa min sai a kawo miki."

Nayla ta ce, "A'a, ba kaWan suka yi min ba Rouhii, Mama sai yabon kayan take yi , kawai na ga nida kai mun zama Waya ai, meye na kwashe kuWi ayi min kayan lefe?."
"Na faWa miki kuWin sun jima a wajan Didi, sai yanzu ne ta yi takai amma ni na jima da bata kuWin. Ki yi hauri na san kin fi arfin kayan, babu yawa ki yi amfani dasu, amma ban gama ba, in sha Allah ko me kike so koda a asar waje ki ke so a yi miki kaya ke kaWai a duniya zan kai ki a yi miki. Ki cigaba da taya ni addu'a kawai."

Ta kwanta a jikinsa ya Wora hannunsa a bayanta ta ce, "Na gode Rouhii, na gode. Allah ya bar m1 tare har aljanna."
"Amin, abinda ya kamata ki ce kenan daman tun Wazu, kuma daman ina jin haushinki." Nayla ta kalle shi ta ce, "haushina kuma?."

"Eh, mun je gidan tv nan sun zo sun sake Waukar mana tallah tunda yanzu abubuwa sun cigaba. Sai yanzu na fahimci kwanakin baya da ki ka ce min dubu Wari biyu ki ka kashe raina min hankali ki ka yi, ko a lokacin kin kashe kuWi ya yi miliyan Waya."

Nayla ta yi dariya ta ce, "to ai kaima kaine da bincike, dan mata ta yiwa mijinta abu duk sai ka bi ka damu sai da ka biya ta? Ina sane na ce maka haka ai, ko addini akwai taimako a tsakanin miji da mata ai."
"Na sani, amma abin ya yi yawa sosai. KuWin sun yi yawa sosai, dan haka zan dawo miki ragowar kuWinki."
"Wallahi bazan karSa, in kuma ka dawo dasu baka Wauke ni matsayin abokiyar sirrinka ba."

Omar ya kalle ta ya ce, "harda wallahi?." Ta murguWa baki, ya yi murmushi ya sumbace ta a kumatu ya ce, "zan saka miki da wannan alkhairi in sha Allah, zaki zama gimbiyata a ko ina." Nayla ta ce, "ko a yanzu ni gimbiya ce, mijina babu abinda baya yi min." Murmushi ya yi baice komai ba. Ta kalle shi ganin fuskarsa ba yabo ba fallasa ta ce, "sai na tuna lokacin da ka ga ana haska tallan a tashar, ka tsare ni da ido kana hararata, nace maka nayi ne saboda kai Yayana ne ka yi min kallon banza ka ce ba a lissafoni a cikin wanda iyayenka suka haifa ba."

an taSe baki ya yi, ya saka hannunsa a gashin kanta ya ce, "an lissafo ki Win ne? Daga ni sai Didi aka haifa, ko kina ciki...?."
"Bana ciki, amma sai ka yi min kara."
"Ban iya kara ba ai. Kuma ke da kin kasance anwata ai da an shiga uku, soyayyar da nake miki ba ta Yaya da anwa ba ce, soyayyar mata da miji ce, wacce zamu shiga Waki mu kulle ofa..." ya yi asa da murya tare da kai bakinsa kunnen ta ya ce, "Soyayyar da zaki saka Omar haukacewa ce, wacce zai zubar miki da hawaye saboda auna, wacce zata saka aljanun dare su tashi."

Dariya ta yi tare da rufe fuskarta, ya buWe cire hannunta daga kan fuskarta ya ce, "kunya ko?." Ta rufe ido ruf tana dariya. Murmushi ya yi ya ce, "shiyasa tun a lokacin na ce miki ke ba anwata ba ce, ina anwa ina ganin hawayen Omar?." Dariya ta sake yi ta Soye fuskarta a irjinsa tana juya kai tana cewa, "To naji, ka daina faWa kunya ka ke bani." Bai ce komai ba sai sumbatar kanta da ya yi yana cigaba da shafa bayanta a hankali.

Nayla ta Wago ta kalli fuskarsa ta ce, "ina so zan je Kaduna." Ya kalle ta shima ya ce, "yaushe?."
"Ko zuwa jibi haka."
"Waye zai kai ki?."
"Driver Hajja."
"Kwana zaki yi?." Nayla ta ce, "kwanaki ma in da za a bani dama." Ya tallafi haSarsa yana kallonta ya ce, "har nawa?." Ta ce, "a'a abinda ka ce."
"Abinda ki ka ce dai, tayawa zaki yi na ji in zan iya siyarwa."

Ta yi dariya ta ce, "Kamar sati Waya haka? Kaga akwai bikin Ya J ana ta shiri." Ya wara idanu ya ce, "Sati Jidda? Ina laifin kwana biyu?." Nayla ta kalle shi cikin sanyin jiki ta ce, "Kwana biyu kuma Rouhii? Kwana biyu ya yi kaWan, rabona da kwana a Kaduna na manta." Ganin ta yi maganar a sanyaye sai ya sauke ido daga kallon ta ya ce, "To Jidda, bazan hana ki kwanakin da ki ke so ba, in satin zaki yi ki kawai."

Jin yadda ya yi maganar irin babu yadda zai yi Win nan sai ta ce, "A'a zan yi kwana biyun." Ya kalle ta yana Wan buWe ido ya ce, "ni dai ban hana ki ba."
"Amma a zuciyarka ba haka ka ke so ba."
"In zaki biye ta zuciyata ko kwana biyun bazan bari ki yi ba, na saba da rayuwa dake kwana biyu babu ke zan zama mara gata ne a duniya. Dan haka ki yi abinda ki ke so na baki dama, in kika biye min a ranar zaki je ki dawo, in na iya hauri ki dawo washe gari."

Nayla ta kalle shi jin abinda ya ce, tasan da gaske yake, ta san shi ba mutum ne mai Soye abinda yake zuciyarsa ba. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "To YaMar na gode." Kai ya Waga mata kawai bai ce komai ba. Nayla ta bishi da kallo ta ce, "Sai naga kamar kana fushi."

Ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "Dan zaki gidanku sai na yi fushi? Haba son kan nawa bai kai haka ba." Ta kwanta a kafaWarsa ta ce, "amma na ga ka canja."
"Hmm Jidda kenan! Sati Waya babu ke nake hangowa kawai, tun kafin ki tafi kewarki ta cika min zuciyata." Ta ce, "Nima haka Rouhii, bana so na yi nisa da kai." Bai ce komai ya zagaya da hannunsa ya rie ta amma bai yi magana ba.

Kamar yadda ta ce ranar talata da safe ta gama shiryawa tana tsaye ya shigo Wakin, ya jingina da ofa tare da harWe hannayensa a irji yana kallonta. Ita kanta sai ta ji kewarsa na ratsa zuciyarta, tunda ta dawo gidan yake gwada mata soyayyar da duk inda ta je ba tare dashi ba dole zuciyarta da gangar jikinta su san ta yi nisa da abin aunarta. Itama ta san zata yi kewarsa sosai, ta saba da kalolin soyayyar da ya saba mata masu tsayawa a rai, yin sati Waya babu shi zata shiga halin kewa. Ta tako da sauri ta shiga jikinsa bai Sata lokaci ba ya rie a tsam-tsam ya ce, "Zan yi kewarki Jidda, ba dan bai da zasu zo anjima ba ni zan kai ki da kaina."

Ta ce, "nima zan yi kewarka Rouhi, har na fara kewarka tun kafin na tafi."
"Allah ya kai ki lafiya ya dawo min dake lafiya. Amma magana ta gaskiya zan yi kewarki fiye da yadda ki ke tunani, zan shiga halin maraici gaba da baya Ashiq. Ina tausayin gangar jikina da ta saba rayuwa dake, ko ya zata kasance a cikin kwanakin nan ban sani ba."

agowa ta yi daga jikinsa ta sumbace shi a fuskarsa ta ce, "Nima zan yi kewarka, zan yi aljanun dare" ta faWa tana Waga masa gira. Dariya ya yi mai sauti ya buWe idanunsa ya ce, "Allah da gaske? FaWa min adadin kewar da zaki yi." Sai kuma ta rufe ido ta koma jikinsa ta kwanta cike da jin kunya. Itace ta saka sunan aljanun dare, in ita da Omar Win suna kashe juna da soyayya sai ta ce Omar yana maganganu da rawar jiki kamar wanda aljanunsa suka tashi, shima ya ce itama kamar mai aljanu.

Ya Wago ta ya ce, "sai kin faWa min adadin kewar da zaki yiwa aljanunki." Dariya ta yi bata ce komai ba, ta kalli idanunsa sai ta sake yin dariya ta ce, "zan dawo da wuri in sha Allah." Murmushi ya yi ya sumbace ta a goshinta ya ce, "Mu je." Tare suka fito ta shiga mota suka wuce ta bar shi da kewarta.KRB3P068
Nana haleema.

Da wuri suka shiga Kaduna, kowa ya yi mamakin ganinta dan babu wanda faWawa zata zo. Abiy ma sai ganin ta ya yi, ya nuna tsananin farin cikin ganin ta suka gaisa kafin ta shiga wajan Mama. Nayla har Wakin Mama ta shiga ta ce, "Mamana kina ina? Na yi kewarki." Mama ta kalli Nayla ta ce, "Gani nan Nayla, saukar yaushe?." arasa tayi ta rungumeta ta ce, "Na yi kewarki sosai Mama. Laifin me nayi miki bakya Waukar wayata kuma bakya kirana? Hankalina ya tashi, shiyasa na zo na ji laifin da na yi miki."

Mama ta yi murmushi ta ce, "ki je ki ci abinci ki huta zamu tattauna." Nayla ta fita tana cewa, "Shikenan Mama ina dawowa." Wanka ta yi ta shirya ta sha baccin gajiya, basu haWi da mutanen gidan ba sai bayan sallar i'sha. Ta fito ta zauna kusa da Mama ta ce, "Ya J angon Salma." Da mamaki ya ce, "Ke kuma saukar yaushe?."

Ta kwanta a jikin Mama ta ce, "tun Wazu."
"ina ki ka baro Omar Win?."
"Gida mana."
"Lallai Hajiya Nayla, wannan kyau haka ai sai na kasa gane ki." Dariya tayi sosai ta kalli Abiy da yake ta murmushi ta zuba abinci tana ci suna ta hira da Jalila da Jawad har suka gama.

Nayla ta ce, "Abiy ka taya ni bawa Mama hauri, na yi mata laifi ko wayata bata Wauka, duk na damu wallahi." Mama ta kalle ta a sanyaye ta ce, "ni nace miki kin yi min laifi ne Nayla?."
"To Mama bakya Waukar wayata kuma bakya kirana, in ba laifi na yi miki ba me nayi miki?." Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "ni na yi miki laifi ai Nayla, ki yi hauri ki yafe min." Nayla ta ce, "Mama ni kika yiwa laifi? Ni babu abinda ki ka yi min Mama, Don Allah ki daina faWar haka" ta faWa dan a tunaninta akan zuwa gidanta da ta yi ne.

Mama ta ce, "Nayi miki laifin ne ai Nayla, kunyarki ma nake ji shiyasa gabaWaya ko wayarki bana iya Wauka saboda ban san ne zan ce miki ba Nayla. Har bana so na haWa ido dake saboda irin abinda na yi miki."

Nayla ta yi sak jin abinda Maman ta ce, ta taso ta dawo kusa da Mama ta rie hannayen Mama ta ce, "Mama me ki ke faWa ne haka? Me kika yi min da zaki kasa Waukar wayata? Mama ni fa arki ce, laifin me zaki yi min?." Mama ta rie hannayenta ta ce, "na yi miki Nayla, nayi miki, amma don Allah ki yafe min. Duk abinda ya faru a lokacin aurenki da Omar ni na haWa, ina so ki aure shi saboda wani buri nawa da na saka a zuciyata, shiyasa ki ka kasa gane kan mahaifinki a lokacin, saboda ni nake Wora shi akan abinda ma bai faru ba, ki yi hauri kin ji Nayla."

Nayla ta fara hawaye jin kalaman Maman babu daWin ji ta ce, "Mama ni ko me ki ka yi min ba laifi bane a wajena, kuma lokacin ai kina so ki samar min da abinda nake so ne shiyasa ki ka yi haka, kin yi dan farin cikina ne ba dan ki cutar dani ba." Mama ta ce, "A'a Nayla dan cutarwa nayi hakan, na raine ki na baki tarbiyya da rayuwa mai kyau, amma ina burin ki yi aure a gidan da zaki sha wahala Nayla. Kuma bani da wani dalili mai arfi akan hakan sai akan abinda ya wuce, saboda wani saSani da ya shiga tsakanina da mahaifiyarki a shekarun baya. Kuma kafin ta rasu ta nemi afuwata tun kafin ma a haifeki, ta nemi tafiya na yafe mata mun zauna lafiya mun cigaba da rayuwa. Amma shaiWan ya saka ni har nake so na ga kema kin shiga irin saSanin da ya shiga tsakanina da maahifiyarki. Ki yi hauri Nayla, don Allah ki yi hauri. Na gane kuskurena a lokacin da mahaifinki ya ganar dani, na kuma yi nadama, har zuwan da na yi gidanki ma ki yafe min kin ji?."

Nayla ta gigice bata ma jin me Maman take cewa, hangowa take yi Mamanta na neman afuwarta, ganin hakan take kamar babban saSo ne a wajanta. Ta ce, "Don Allah Mama ki bari bana jin daWin wannan maganar da ki ke yi, Kuma ai Allah ne ya addara faruwar komai baki da hannu a cikin duk abinda ya faru. Don Allah ki daina bana so." Mama zata sake magana Nayla ta ce, "don Allah Mama ki bar maganar nan, ki yi hauri ki bar maganar bana son ji ko kaWan" ta faWa tana toshe kunnenta tana kuka.

Abiy da yake jinsu ya ce, "Zo Mamana." Ba musu ta koma kusa da Abiy ya share mata hawaye ya ce, "Ki nutsu."
"Abiy kana ji me Mama take cewa fa, in ma laifin ta yi min ba uwata ba ce meyasa take neman afuwata? Wanne laifi Mama zata yi min da zata ce kunyata take ji har na dinga kiranta tai Wauka?."

Abiy ya ce, "neman afuwarki yana da kyau tunda laifi tayi miki Nayla, amma tunda kin ce bakya son ji shikenan." Nayla cikin muryar kuka ta ce, "Ni bana so."
"To ai an bari" Abiy ya faWa cikin rarrashi dan ya san halinta.

Jawad dai bai ce komai ba sai ma tashi da ya yi ya fita Jalila ma ta tashi ta bar wajan. Nayla ta kalli Mama ta ce, "Mama ni baki min komai ba don Allah ki daina faWa, in kina so nayi farin ciki ki daina cewa na yafe miki."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Na daina Nayla."
"Baza ki sake in Waukar wayata ba?."
"Bazan sake ba Nayla."
"Kuma a Wakinki zan kwana."
"To Nayla" ta faWa da murmushi tana kallonta amma a zuciyar ta gabaWaya babu daWi, ta rasa me ya kai ta har ta yi oarin cutar da Nayla wacce ta raina da kanta. Ina ta tuna hakan sai zuciyarta karye ta fara zubar da hawaye.

Nayla tashi ta yi ta shiga Waki, Mama ta kalli Abiy ta ce, "na san ban kyauta ba da na biyewa zuciya, amma yanzu wallahi na yi nadama bazan sake oarin aikata abinda na yi ba, ka yi hauri. Tun ranar da aka yi maganar nan ban samu arfin guiwar baka hauri ba sai yau." Abiy ya ce, "ta ya zaki bani hauri kin koma wasan Suya da mutanen gidan?."

Mama ta kalli Abiy tana hawaye ta ce, "Kunya ce Abiy, kunyar haWa ido da kai nake yi, kunyar su Jawad lulluSe ni take yi da zarar na ji maganarsu balle na haWa ido dasu. Nayi kuskure, na so na aikata abinda zan bar baya da ura, duk da na aikata Win amma na gane kuskurena wallahi. Ka yi hauri ka yafe min."

"Ni baki min laifi ba ai, in ma kin yi Allah ya hukunta ki tun ba a je ko ina ba, iya kunyar aanki da ki ka ji babbar jarabawa ce a gare ki, baza su taSa mantawa da wannan abun da ki ka aikata ba har abada. Na Waga miki afa tun farko saboda na san ke ar adam ce, dole ki yi kuskure a wani Sangaren. Amma

Please Login or Register in order to submit comment