Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dani" ta faWa hawaye yana sakko mata.

Didi ta ce, "Nayla na rasa yaushe zaki daina ji da autanci, wannan ai ™aramin abu ne, zama zaki yi ke da shi ki bashi ha™uri ba shikenan ba?." Nayla ta ce, "Didi bana kyauta masa ne, ina cutar dashi ni kaina na sani." Didi da mamaki ta ce, "Kina cutar dashi kuma Nayla? Ta wacce hanya kenan?." Nayla ta yi shiru tana wasa da hannunta cikin jin nauyin maganar da zata furta. Ganin hakan sai Didi ta ce, "kar ki damu in baza ki iya faWa min ba, amma ki samu ku daidaita dashi in ya dawo."

Nayla tayi ajiyar zuciya ba tare da ta Wago ba ta ce, "Didi haka kawai bana so ya taSa ni, in ya taSa ni sai naji kamar zan mutu. Shi kuma tunda ya fahimta ko hannuna bai sake ri™ewa ba sai ana e gobe zai yi tafiyar nan" ta Wago ta kalli Didi ta ce, "Wallahi ban san meyasa ba, ban sani ba ko wata cutar ce ta kama ni."

Didi ta bita da kallo tana zargin wani abu ta ce, "Kuma babu ciwon kai ko zazzaSi?."
"Babu komai, gwara ma dai jiri, ina yawan jiri sosai, in na tashi sai naji kamar zan faWi amma bana jin komai." Didi ta girgiza kai ta ce, "Da mota ki ke?." Ta Waga kai alamun eh ta ce, "Bara na kire YallaSai a waya sai mu je asibiti a faWawa likita."

    Cike da gamsuwa Nayla ta Waga kai, Didi ta shiga Waki ba jimawa ta fito da hijjabi Nayla ta Wauki Marmerh suka tafi. Nayla ta ce, "Akwai asibitin da Twiny take zuwa, akwai likitoci sosai bara mu je can." Can suka wuce Nayla ta ajjiye motar suka shiga ciki suka biya kuWin ganin likita aka nuna musu inda zasu je.

     Šakin Nayla ta shiga ta yiwa likitan bayani ya rubuta mata scaning ya ce ta je ta yi. Tare suka je suka biya kuWin da Didi aka nuna mata Wakin scanning Win ta shiga. Ba jimawa aka gama ta fito aka kawo mata result har inda take, ta mayarwa da likitan a lokacin suka shiga Wakin tare da Didi.

Dr ya buWe result Win ya kalli Nayla ya ce, "Hawwa kina da ciki na sati huWu, duk abinda ki ke ji shine ya saka ki ke jinsa. Ba abin damuwa bane wannan yanayin da ki ke ji, daga kin fita daga first tremister komai zai wuce" ya faWa yana mi™a mata takardar.

Nayla kasa magana tayi ta zubawa likitan ido kawai tana kallo, kafin ta kalli Didi da take murmushi sai kuma ta sunkuyar da kai cikin kunya. Magani ya rubuta mata ya bata suka fito ita da Didi ta kasa cewa komai. Mamaki take yi wai ciki ne da ita, babu abinda take ji in ba wannan damuwar ba sai kuma jirin da take ji ba, ashe daman ana iya yin ciki babu laulayi?.

Didi kamar tafi Nayla farin ciki, ta kasa Soye muryarta sai addu'a take yi. Suna shiga mota ta ce, "da na iya tu™a motar ai da bazan bari ki tu™a ba wallahi. Alhamdu lillah, burina a duniya yana ta cika, zan ga Wa ko ´ar da Omar zai haifa." Nayla ta kifa kanta akan sitiyarin motar tana jin kunyar Didi mai tsanani. Didi tayi dariya ta ce, "shi yana can yana fushi bai san abinda yake so ne ya samu ba, dole na yi masa babban albishri."

Nayla ta Wago da sauri ta ce, "Don Allah Didi kar ki faWa masa, ki bari ya dawo." Didi ta ce, "To ai da ki ka shiga wajan likita ya kira ni wai bakya Waukar waya na ce bakya jin daWi muna asibiti, duba wayarki zaki ga kiran."

Kamar jira yake yi tana kallon wayar kiransa na shigowa ta Wauka kafin ta yi magana ya ce, "Jidda Didi ta ce min bakya jin daWi an je asibiti, me ya same ki? Kina lafiya dai ko? Me suka ce yana damunki?. Ki yi magana mana, na kira Didin bata Wauka ba." Nayla jin ya rikice yana jero mata tambaya sai ta ce, "malaria ce aka ce tana damuna."

"Amma da sau™i dai ko? Kwantar dake suka yi ko ruwa aka saka miki?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Babu komai fa Rouhi, magani kawai suka bani."

"In akwai damuwa ki faWa min, kuma meyasa baki faWa min baki da lafiya ba har ki ka ce min kin tafi gidan Didi? Kin san baki da lafiya ina ke ina Waukar mota?. Sannan ba na ce duk inda zaki je ki dinga bari a kai ki ba? In aka sake ™o™arin cutar dake fa?. Meyasa ki ke yi min haka ne Jidda?."

Jin ya fara yi mata faWa sai ta ce, "Ka yi ha™uri."
"Wannan ai ganganci ne, kin san baki da lafiya sai ki Wauki mota ki bar gida? Meyasa baza ki ha™ura ba?. Na hana ki fita ke kaWai amma bakya ji, yanzu da wani abun ya same ki fa?." Nayla ta ce, "to ai nace ka yi ha™uri." Ya yi tsaki ya ce, "ina Didi?." Nayla ta ce, "gata" ta faWa tana bawa Didi wayar.

Didi ta karSa tana ji kamar ta sanar masa amma tunda Nayla ta ce bata so gwara ta ™yaleta ta faWa masa. Ya ce, "Didi don Allah ki kula da ita, kin tabbatar zata iya driving?." Didi ta ce, "Gaskiya nima bana so tayi, bara na kira Tukur ya zo nan ya tafi da motar."

Tsaki ya yi akwai ya kashe wayar, Didi ta kalli Nayla tana dariya ta ce, "A haka ma bai san ciki ne dake ba." Nayla ta yi murmushi, Didi ta kira Tk tayi masa kwantace ya ce gashi nan zuwa. Suna zaune a motar ba jimawa ya zo, Nayla ta fita ta koma baya ya shiga motar ya ja suka tafi.KRB3P084
Nana haleema.

Sai da aka sauke Didi a gida sannan aka wuce da Nayla gidan Mama. Da suka je ya ajjiye motar ya bata key ya koma a napep ita kuma ta shiga ciki. A falo ta samu Mama da Abbas da Khaleefa, Mama ta bita da kallo ta ce, "har kin dawo?." Nayla ta ce, "eh Mama, jiri nake ji" ta faWa tana zama kafin ta gaishe da su Abbas. Mama ta ce, "Sannu, rana ce ta saka ki jiri, dan yau ta buWe sosai, kuma kamar bazata buWe ba saboda hadarin da ya haWo Wazu."

Nayla ta mi™e ta shiga ciki takardar hannunta ta faWi bata sani ba. Khaleefa da yake kusa da ita ya Wauka yana cewa, "Nayla kin yarda da takarda." Nayla ta shiga ciki bata ji shi ba. Ganin hoton scaning a sama sai ya ja hankalinsa ya buWe takardar, ya kalli Mama ya ajjiye bai ce komai ba. Mama ta kalla ta ga alamun takardar scaning ce ta ce, "A'a Nayla bata da lafiya? scaning taje daman?" Ta faWa tana buWewa tana ganin abinda yake jiki.

Murmushi ta yi ganin abinda yake rubuce a jiki, a lokacin Nayla ta dawo tana cewa, "Mama na yarda takarda......" Maganar ta tsaya ganin result Win a hannun Mama. Mama ta mi™a mata ta ce, "gata nan." A sanyaye ta karSa ta koma ciki da sauri cikin jin kunya. Mama bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin ta tashi ta shiga wajan Nayla.

A zaune ta same ta, Mama ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla sannu." Nayla ta sunkuyar da kai cikin kunya ta Wagawa Mama kai. Mama ta ce, "babu abinda ki ke so?." Nayla ta ce, "Babu Mama."
"Kin tabbatar? In akwai ki faWa min kinga ba ke kaWai ba ce." Nayla sai ta kifa kanta a jikin Mama cikin jin nauyin maganar. Mama ta yi dariya ta ce, "ni tunda ki ka zo nake kallon ki kamar mai ciki, ashe shi Win ne. Allah ya inganta Nayla ya raba lafiya." Bata ce komai ba tana jikin Mama.

Mama ta ce, "To meye na kunyar? Kinga Wago ki faWa min abinda ki ke so." Nayla ta Wago ta ce, "babu komai Mama."
"Kin tabbatar?." Ta daga kai alamun eh Mam ta ce, "duk abinda ki ke so ki faWa min." Nayla ta amsa sannan Mama ta fita.

Cikin lokaci kaWan kowa ya san da batun cikin Nayla, har Mama ta Kaduna sai da ta ji labari, Nayla dai bata san waye ya faWa mata ba sai kiran Mama ta ji tana cewa duk abinda take so a kawo mata daga Kaduna ta faWa mata.

Har Abiy sai da ya kira ta ya yi mata ya jiki, ana ta murna kamar a kanta za a fara samun jika. Hajja kuwa kamar ta fi kowa farin ciki, itama waya take sakawa a bugawa Nayla ta ce ta faWi abinda take so. GabaWays ta zama ´ar gata, kowa burinsa ta ce ga abinda take so. Ita kuma cikin bai saka mata wannan kwaWayin ba, normal take harkokinta sai sai jiri da nauyin da kanta yake yi, wani lokacin sai kuma ri™ewar mara.

" " " " " " " " "

"Safna kalli ki ga, kalli Safna, wallahi he's the one, he's my love Faruk, wallahi shine" Narma ta faWa hannunta yana rawa tana nunawa Safna wayarta da take hannunta. Safna ta kalli abinda take nuna mata ta kalle ta cike da takaici ta ce, "You're out of your senses Narma, How come this classy, rich and handsome guy Win zai zama wannan thug Win?. Kin manta waye Faruk Win na ki ne? Haba ki dawo nutsuwar ki mana, wannan ba shi bane."
ÿþ

Narma ta dafe kai ta ce, "look, sunansa Omar kalli ki ga abinda aka rubuta, and he live in Kano, kalli fuskarsa mana. Wallahi shine, ko a ina na ga Faruk zan gane shi" ta faWa tana zooming fuskar Omar tana nunawa Safna.

Safna ta yi tsaki ta ce, "Ai sai ki yi, dan kawai wannan ya kasance Omar shikenan sai ya zama shine Faruk Winki?." Narma a sanyaye ta ce, "Shima fa Omar ake ce masa, ni ce nake cewa Faruk."

"Narma ki dawo nutuswarki don Allah, duk kin bi kin haukace akan wannan Wan daban. Ta ya wannan zai zama shi? Ki kalli shigarsa da matsayin da ya samu da waWanda suke gefensa ki ce he's the one?. Ki dawo hankalinki malama, ina ya ga ilimin da zai kawo wannan matakin? And ina ya ga hankali da nutsuwar da zai yi abin kirki haka?. Na faWa miki zan duba miki inda yake amma duk kin bi kin tayar da hankalinki."

Sai jikin Narma ya yi sanyi ta kalli Safna ta ce, "Amma suna kama sossi Safna, ni ban yarda ba shi bane ba wallahi."
"Sai ki yi ai, in zaki dawo hankalinki ki dawo, wannan ba shi bane, zan dai je na nemo miki wancan nakin mu gani. Abu Waya na sani, an tabbatar min da ya yi aure!."

Narma ta dafe ™irji cikin faWuwar gaba ta ce, "Ya yi aure?."
"Yess, ana zancen an yi one year ma da auren"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Safna ni fa?."
"Narma bana ce ba, in har yana sonki ai kin ce you're ready to be his second wife right?." Narma ta Waga kai alamun eh Safna ta ce, "Okay don't be nervous, in sha Allah komai zai dawo daidai."

Narma ta ce, "to" ta faWa a sanyaye cikin bugawar zuciya. Sai ta bawa Safna tausayi, mace mai aji da kyau da kuWi itace Allah ya saka ta a wannan jarabawa ta soyayya. Narma da sai ka kai wani mataki ma take buWe dm Winka balle ka yi mata waya ta Wauka ko ka yi mata magana kai da ita. Amma kalli yadda Allah ya juya sama ta dawo ™asa, haukan sonsa take yi shi kuma bai ma san tana yi ba, ya yi aurensa ya manta ma da ita a rayuwarsa. Rarrashinta Safna ta dinga yi har ta Wan dawo daidai kafin ta saka ta su fita su Wan zaga garin Abuja dan ya dawo nutsuwarta.

Satin Omar biyu a China sannan ya sanar da Nayla zai dawo, Nayla murna kamar zata yi me ta rasa ma abinda zata yi. Har gyaran jiki ta yi, duk Mama na kallon ta dan ita tsoro take ji ina mai ciki ina gyaran jiki? kar a je a zubar da shi.

Bayan ta gama kwalliyar ne Mama take cewa, "Nayla Omar zai dawo kin sha ™unshi da gyaran kai ga gyaran jiki, yanzu dai kina da ciki komai a hankali ake binsa, in ba haka ba tsaf za a zubar dashi." Nayla sai taji kunya sosai bata iya kallon Mama ba ita kuma ta fita ta ™yaaleta.

Omar kuwa a Abuja ya sauka kamar yadda ya tafi ta Abuja, yana zaune a airport yana jiran jirgin da zai kawo shi Kano ya zo. Yana zaune cikin manyan kaya na yadi coffee colour, kansa babu hula sai gashinsa da ya kwanta, ya Wora ™afa kan Waya yana danna waya ga trolly bag Winsa a gefe. In ka kalle shi sai ka sake kallo saboda yadda ya kame ya yi kyau, ya zama irin rich handsome guys Win nan.

"Faruk!." Ya ji an faWa daga bayansa, ya tsaya cak da abinda yake yi dan a kaf duniya ya san wacece ta taSa kiransa da wannan suna, kuma tana faWa fuskarsa ta zo idanunsa dan ya san itace Win. Ya maze bai motsa ba kamar ba shi ta kira ba, sai ta ce, "Omar!." A hankali ya Wago ido ya kalli idanunta. Narma ta ja doguwar ajiyar zuciya, fuskarta ta nuna yanayin da zuciyarta take ciki, hawaye suka ciko idanunta ta ce, "Safna na faWa miki Faruk Wina ne, kalle shi ki ga."

    Safna da take tsaye a bayanta ta kalli Omar da ya mayar da kai ya cigaba da abinda yake yi kamar bai ga Narma ba, ta Wan yi tsaki ta ri™e Narma ta ce, "Narma please! haba meyasa ki ke ™o™arin haukacewa ne? Kin ga wani a waya kin ce shine, yanzu kin ga wannan ma kin ce shine, maza nawa ne zasu koma miki Faruk Win?." Narma a sanyaye ta ce, "Kalle shi ki gani, shine wanda na ce miki, shine a cikin wayar kuma shine Faruk Win.." ta dawo da kallon ta gare shi ta ce, "Faruk baka gane ni ba? Narma ce fa."

Sarai Omar ya ganeta kawai bashi da lokacin dai zai kulata ne, a ganinsa in ya yi mata magana kamar ya ci amanar matarsa ne, amma wani Sangare na zuciyarsa ya ji tausayinta sosai, musamman kalaman ™awarta. Tausayinta ya ratsa zuciyarsa, jin yadda muryarta take rawa kamar ba ita ba ya dake shi.

Safna ta kalli Omar ta ce, "ka yi ha™uri, wani saurayinta ne da mahaukacin so, duk wanda ta gani sai ta ce shine, ka yi ha™uri please" ta kalli Narma ta ce, "Narma mu je" ta faWa tana jan hannunta.

Narma ta turje ta ce, "Babu inda zan je, shine wanda nake nema kuma shi na gani yanzu" ta dawo kusa da Omar ta ce, "Baka gane ni ba? Faruk say something please, ka yi magana kafin zuciyata ta buga. Na jima ina neman ka, na jima ina so na ganka, Faruk please!" Ta faWa tana haWe hannayenta tare da zubewa a wajan.

Omar ya rasa abinda zai yi, tausayinta yake ji sosai, ya san zafin so, ya san ya ake jin soyayya shiyasa yake jin tausayinta yana yin tasiri a zuciyarsa. Musamman yadda take kuka ta kuma zube a gabansa ga mutane da suke ya wucewa tunda rana ce kuma waje ne na kowa da kowa. In ya nuna ya gane ta me zai ce mata?, bai san mai zai furta mata ba gwara ya yi shiru. In kuma ya nuna bai gane ta ba ya kyauta mata kuwa?. Omar ya rasa me zai yi mata, a hankali ya kalle ta suka haWa ido, yadda idanunta suka red, jijiyoyin kanta suka tashi ya sake karya masa zuciya, ya Wauke kai daga kallon ta ya ce, "Kina ji, ba wanda ki ke nema bane" ya faWa yana mi™ewa tsaye ya ri™e trolly bag Winsa zai bar wajan.

Hannunsa ta ri™e da sauri ta ce, "Wallahi kaine, Muryarka ta tabbatar min da kaine. Ko a cikin mutanen da ban san adadinsu ba in na ganka na san kaine, ko maganar ka na ji na san kaine Faruk. Me nayi maka ka ke ™o™arin yi min wannan hukuncin? Meyasa ka ke ™o™arin wula™anta zuciyar da ta gama narkewa a soyayyar ka? Meyasa ka ke ™o™arin cutar da zuciyar da ta jima da cutuwa akan soyayyar ka?. Please Faruk, ka tausaya min kafin na rasa hankalina a kan ka."

Omar ya tsaya cak yana jinta, jikinsa ya yi sanyi sosai ya kasa motsawa. Ajiyar zuciya ya yi ya zame hannunsa daga ri™on da ta yi masa, bai ce komai ba zai wuce ta. Sake tsayawa a gabansa tayi tana kallon fuskarsa gabanta yana faWuwa, kallon fuskarta ya yi suka sake haWa ido, ya Wauke kai ganin yadda hawaye yake a kwance akan fuskarta idanunta sun sake yin ja. Hannayenta ta haWe waje Waya cikin wani yanayi na kewa da soyayya ta ce, "Please Faruk, allow me to hug you!." Jin abinda ta ce a lokacin ya janye ido daga kanta, tausayinta ya kama ratsa zuciyarsa, baya so raunin da yaji ya bayyana akan fuskarsa.

Ya sake raSata zai wuce ta ce, "ina sonka, ina so na aure ka. Faruk a yanzu babu wanda ya isa ya raba ni da kai." Baice komai ba ya wuce ta dan in ya cigaba da tsayawa zata karya masa zuciya shi kuma ba haka yake so ba.

Narma zata bi shi Safna ta ri™e ta cikin masifa ta ce, "Haba don Allah Narma, kawai daga ganin mutum sai ki ce shine wanda ki ke nema? Wannan ya yi miki kama da Omar Win Kano ne? Ko kuma nan Kano ne da zaki ce ai shine?. A Abuja ki ke, a Abuja ma a cikin airport, wanda ki ke magana a kai me zai kawo shi airport?. Ki dawo hankalin ki Narma, ki daina yi mana shirme, kina gani ana ta kallon mu kamar wasu cartoon. Ni da na sani ma ban ce ki rako ni ba" ta faWa tana jan hannunta da ™arfi suka bar wajan. Ita kuwa Narma tunanin ta yana ga Faruk Winta, duk abinda ya yi mata da abinda ya ce bata damu ba, burinta ya cika ta ganshi ta kuma tabbatar shine. Saura burinta na aurensa, dan a wannan lokacin bazata Waga ™afa ba.

Omar kuwa a haka ya shiga jirgi duk sai ya ji ta sake bashi tausayi sosai, jikinsa ya yi sanyi har yana tuna yadda take kuka. Bai bari tausayin ya yi tasiri a zuciyarsa ba, ya watsar da tunanin ya jawo tunanin matarsa yana tuna irin yanyin da zai same ta in ya koma gida.KRB3P085
Nana haleema.

A Kano suka sauka ya kira Bashir yazo ya Wauke shi suka tafi. Sai da suka fara zuwa gidan Didi kamar wancan lokacin dan zuwa lokacin yamma tayi sannan suka wuce gida. A gaggauce ya shiga saboda bai yi sallar la'asar ba ga magriba ta gabato, kai tsaye ya shiga Waki da niyar yin alwala amma sai ya tsaya yana kallon Wakin.

Decor aka yi masa mai matu™ar kyau da Waukar hankali, an rubuta welcome back Rouhi da flowers masu kyau da ™hamshi. Murmushi ya yi ya kalli table Win da yake Wakin ya ga harda cake ya girgiza kai ya ce, "ko kina ina? Na ga cake ban ganta ba."

A hankali ta fito daga bayan labule ya bita da kallon ™urilla ganin ta canja masa gabaWaya, ta sake haske ga wata cikar jiki da ta sake yi na musamman. Nayla ta tako tana murmushi tana kallonsa. Murya a raunane ya ce, "rowar ganin ki ki ke yi min in na dawo ko? Wancan lokacin ma Suya ki ka yi."

"Sannu da dawowa Rouhii!" Ta faWa tana shiga jikinsa ya sanya hannu ya rufe ta a jikinsa ya yi ajiyar zuciya mai ™arfi kana ya ce, "Don Allah indan kina yi min addu'a akan Allah ya sa na ™ara sonki ki daina, Ashiq son da nake miki yana neman fin ™arfin tunanina. Kullum soyayyar ki ™aruwa take a zuciyata, shiyasa nake neman alfarma in kina addu'a ki daina kar ta zauce" ya furta a hankali yana ri™e da ita a jikinsa ita kuma tana hasahen yanayin da zai kasance in ya san tana da ciki.

"Rouhi I missed you."
"Likewise Ashiq." Bata Wago ta kalle shi kamar ko yaushe ba, amma yana bata mamaki in ta faWi abu ya bata amsa bayan ya ce shi bai iya ba, gashi in zata kwana tana tambaya akai bazai bata amsa ba. 

Sun jima a haka kafin ya Wago ta ya yi mata peck a goshi ya ce, "ban yi sallar la'asar ba Ashiq."
"Na haWa maka ruwa yana nan yana jiranka."
"Na gode Masoyiya" Abinda ya ce kenan ya shiga bai saurare ta sai ta taya shi ba saboda sallah.

Tana zaune a falo ya fito dan lokacin har an yi magrib, ya zauna a kusa da ita ya kalle ta ya ce, "Ni na ga kin rame, rashin lafiyar da ki ka yi ne ya jawo haka?" Ya faWa yana saka hannunsa a wuyanta yana shafa ™ashin da ya gani. Nayla ta kalle ta shi tana ganin kamar ana canja mata shi, ya ™ara haske sosai fuskarsa ta canja ya yi wani irin kyau mai Waukar hankali.

A hankali ta ce, "Mijina baya nan ba dole na rame ba? Ni wai wannan kyaun da ka ke ™arawa na meye?." Yana kallon ta ya ce, "Na kewar ki ne."
"Shine zai ka ™ara kyau kuma?" Ta faWa tana kallonsa da shagwaSa.
"Eh mana, tunda bakya ganina ai dole ki ga na yi kyau. Ina tambayar ki baki bani amsa, ya naga kin rame?."

Nayla ta ce, "Tunanin ka ne wallahi." Ya zuba mata ido bayan ya ri™o hannunta ya ce, "Tunani ki ka saka har haka Jidda?."

"Ni kaWai na san yadda na yi kewarka Rouhi" ta faWa tana kwanciya a jikinsa ya ce, "Bana tunanin kina jin abinda nake ji." Zame jikinta tayi ta ce, "abinci Rouhi." Bai musa ba ta kawo masa suka ci tare suka yi sallar i'sha tare. Šakinta shiga ta Wauko cake Win da ta yi da kanta ta yanka ta bashi ya ci itama ya bata yana cewa, "kina ta zirga-zirga ko?."

Nayla ta ce, "da kaina na yi fa, ko decor Win ma da kaina nayi, kayan na siya kawai. Ya za ayi na bari masu decoration su shigar min Wakin mijina?." Kallon ta ya yi yana Wan taSe baki ya ce, "uhum ka ga mai miji." Dariya ta yi ta saka sauran cake Win a fridge ta dawo ta zauna a kusa dashi. Shi kuma baya son zaman da take yi a inda yake, yanayin shigar jikinta da ™hamshin ta haukata shi yake yi, gashi daman kwaWayinta ya dawo, kuma bai manta da yanayin da ya barta ba, baya son yin abinda zai takura ta shiyasa yake kamewa amma ta kasa ganewa.

A jikinsa ta kwanta ya yi shiru bai ce mata komai ba, jin shirun yayi yawa sai ta Wago tana kallonsa, zai yi magana ta hana shi maganar ta hanyar fara kissing Winsa, ya mayar da ido ya rufe yana jin abinda take yi masa amma ya kasa bata haWin kai, baya so sai ya birkice kuma ta janye jikinta. Nayla a zuciyarta take jin zata iya a wannan lokacin baza ta bashi kunya, amma shirun da ya yi mata baya taya ta sai ta sare, duk ™arfin guiwar da take ji dashi ya gusshe, ta kalle shi ta ga idanunsa a rufe suke. Ajiyar zuciya ta yi kamar yadda ya yi, ta mi™e ta bar jikinsa hankali ta shiga ciki.

Shima tashi ya yi ya shiga Waki ya zauna ya

Please Login or Register in order to submit comment