Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakawa zuciyata tayi bindiga, Tiger tsawa yake yi min, Tiger baya sona, Tiger tsorata ni yake yi. Rouhi ne yake sona, shine baya aunar ganin kukana, shine baya so na shiga damuwa ko kaWan. Ka cigaba da zama a haka, don Allah ka daina rikiWewa kana koma min wancan kaji!" ta faWa tana Wora hannunta a gashin fuskarsa.

Murmushi ya yi tare da pecking Winta a goshi yana kallon ta da murmushi ta ce, "saura iris Tiger ya sa na gudu Kaduna, kuma in na gudu bazan dawo ba!" Ta arasa faWa da shagwaSa tana kallonsa. Murmushi yake yi mata wanda yake kashe mata jiki kana ya ce, "Tiger yana sonki Jidda, Omar ma yana sonki. Koda kin gudu Kaduna da kaina zan je na Wauko ki."

"A'a, Rouhii ne yake sona ba tiger ba. Shi fa tsawa yake yi min, kuma ya ce min Naylaaaa!. Rouhi kuma Jidda yake ce min ko ya ce Ashiq. Tun a gidan Didi Tiger baya sona, amma YaMar yana matuar ji da ni" ta faWa tana kallonsa.

Fuskarta yake shafawa a hankali kafin ya rie hannunta da aka ji mata ciwo ya ce, "ke kika jawo Ashiq, ke kika Wauki tsoro ki ka saka a zuciyarki har in nazo kusa dake kike rawar jiki. Yanzu Ashiq kina ganin zan ji daWi in naga bakya so nazo kusa dake? Uhumm zan ji daWi?."
"Ni Damisa nake tsoro ba Rouhii ba, Damisa ne bana so yazo kusa dani ba Rouhi ba. Ga Rouhiina a kusa dani yana rarrashina" ta faWa tana turo baki gaba."

Bakin nata ya rie yana murmushi yana kallonta ya ce, "Jidda kin Sata min rai, ana cikin irin wannan yanayi kawai ki tafi gidan Didi? Kuma ba ma ki Wauki mota ba, ki ka hau keke napep kika tafi ke kaWai. Ga ruwa anyi a ranar, ga yamma, ga adadin abubuwan da suka faru. Why Jidda...!" Ya faWa yana kallon ciwon hannunta. Ya sake kallon fuskar ta ya ce, "kalli sakamakon fita babu izinina abinda ya jawo miki, da baki fita ba da jini bai zuba a jikinki ba."

Ganin murmushin ya gushe daga kan fuskarsa sai ta rausayar da kai ta ce, "ka yi hauri, wallahi tsoron gidan na dinga ji. Tunda na ganka da jini a jikinka shikenan na rasa nutsuwata, sai nake gani kamar wani abun zai same ni a gidan nan. Kuma wallahi na kira ka baka Wauka ba, sai na yi maka message na faWa maka. Kuma na san baza ka hana ni zuwa gidan Didi ba shiyasa na tafi."

"Da ki ka fita Win me ya faru? oarin kashe min ke aka yi Jidda, kai tsaye kashe ki suka yi niyar yi ba wannan ciwon ba. Har waya aka wace miki, kina tunanin wannan abinda ya faru dake Win zai saka naji daWi a zuciyata?."

"Ka yi hauri, bazan sake ba."
"Jidda kin san da cewa duk motsinki akan idanunsu yake? Ina da maiya masu son ganin bayana, ina da abokan gaba da muka cutar da juna a baya suna so su Wauki fansa a kaina ko a kan ahlina. Kina fita daga gidan nan aka bi bayanki, ba dan Allah ya taimaka Tk ya gani ba da me zai faru? Da bai je a lokacin da ake oarin sukar ki a cikin ki fa?. Iya wannan ciwon da suka ji miki basu cuce ni ba Jidda?" ya arasa faWa cikin rauni yana kallon ta.

Nayla a sanyaye ta ce, "ka yi hauri." Ya sauke numfashi ya ce, "Jidda hannunki aka yanka da wua fa, jini ya Sata jikin ki gabaWaya..." ya yi shiru yana girgiza kai ya ce, "na faWa miki wani abu..? Ni Omar na zubar da harkar daba saboda Didi, na watsar da makamaina saboda ita kawai. Duk wani wanda muke tare ya san Didi ce raunina, na yarda na cutu indai zata zauna lafiya. An kawowa Didi hari ana neman rayuwarta ko lafiyarta sau babu adadi, wannan dalilin ya saka na hana kowa shiga gidanmu, sannan duk wanda zai shiga za a sanar dani. Wannan shine dalilina na ko ina Didi zata je ana biye da ita, hatta lokacin da take zuwa makaranta ana yi min gadinta ba tare da ta sani ba. Saboda lafiyar Didi ban taSa zuwa wani waje na kwana ba, duk dare sai na dawo gida wajanta saboda kar wani abun ya same ta. Akwai masu jin haushina da zasu wuce akan Didi in basu samu dama a kaina ba...."

Ya yi shiru yana kallon ta kafin ya Wauke ido daga kanta, ya sake kallon ta ya ce, "Saboda kar a cutar da ita na daina cutarwa da kowa danginsa, na zubar da makamaina na dawo gida na zauna a tare da ita. Ba dan ina jin tsoro ba, ba dan na ja da baya ba, ba dan an fi arfina ba, ba dan anyi nasara a kaina ba, sai dan saboda kar wani abun ya same ta."

Ya murza yatsun hannunta ya ce, "Yanzu ba Didi ce kaWai dangina ba, har dake, kuma kece a kusa dani a yanzu ba ita ba, ke zasu fi kawowa hari fiye da kowa. Kina ganin abinda ya same ki dai, duk hakan ya faru ta dalilina. Anya zan yafewa kaina abinda ya faru Jidda!?."

Nayla ta girgiza kai tana kallon sa ya ce, "baki san hawa ba, baki san sauka ba, bake kika aikata laifin ba, lokacin da na aikata ban sanki ba, lokacin da na aikata baki sanni ba, lokacin da na aikata ban taSa kawo batun aure a zuciyata ba balle na san zan aure ki. Amma gashi hukunci ya sauka a kanki, ciwo ne a hannunki a matsayin sakamakon laifun da na aikata. Jidda ban kyautawa Abiy da ya bani amanarki ba, sannan zaman aurena dake bashi da wani amfani a gare ki sai cutarwa."

Ya dame hannunta gam ya ce, "bana so na rasa ki Jidda, bana so wani abun ya same ki ta dalilina. Na gaza kula dake, na gaza baki kariya har aka ji miki ciwo aka zubar miki da jini. Ke ba kalar macen da zata shiga tashin hankali bace, sai yanzu nake sake tabbatar da baki dace da auren Omar ba! Baki dace ba Jidda!." Nayla ta ce, "YaMar babu wanda ya wuce addara."

"Ganganci ne wannan ba addara ba Jidda, ni na kai kaina tun farko, da ace ban aikata laifuka masu yawa a baya ba da hakan bai faru ba. Sau biyu kenan ana neman rayuwarki, sau biyu ana zuwa gidan nan dan a cutar dake, anya na zama miji na gari a wajanki kuwa Jidda!."

Ta rie hannunsa itama ta ce, "Rouhii!" Bai bari ta arasa ba ya ce, "Ta silar laifukan mijinki ake neman rayuwarki, ana so a cutar dake dan a biya bashin da mijinki ya ci a shekarun baya. Ni ba miji na gari ne a gare ki ba Jidda, ban amsa wannan sunan ba" ya faWa yana jan numfashi dayar cikin unar abinda ya faru.

Nayla ta ce, "Wannan ba komai bane, ya riga ya wuce ai. Kuma Allah ya rubuta dole sai hakan ya faru, ko da ban aureka ba wannan ciwon da naji yana cikin addarata."

"Bai wuce ba, lokacin da hakan ya faru a cikin azumi na Wauka ya wuce sai gashi ya sake faruwa.." ya juyo ya kalle ta ya ce, "akwai irinsu da yawa Jidda, ni kaina ban san adadinsu ba. Suna nan suna fakon rayuwata, in basu samu ba su nemi taki ko ta Didi. Ba iya Waliya ko Kb ne kaWai ba, akwai su da yawa Jidda, za a cutar min dake a wani wajan da bana nan, za a iya biyan bashin da na Wauka dake ko Didi Jidda. Shiyasa ban cancani na amsa sunan miji na gari a gare ki ba. Muryarsa tayi asa sosai cikin rauni da bugawar zuciya ya ce,  Jidda na fara wani tunani akan zaman aurena dake, bana son cutar dake, bana so ki rasa rayuwarki ko lafiyarki ta dalilina" ya ja numfashi ya ce, "Jidda!" Ya faWa yana jan sunan nata cikin wani yanayi tare da kallon idonta kamar yadda take kallonsa nasa gabanta ya faWuwa tana jin tsoron abinda zai fito daga bakinsa.KRB3P075
Nana haleema.

Ganin ya shiru yana kallon idonta bai ce komai ba sai ta daure ta ce, "me ka ke shirin faWa?" Ta faWa tana zare ido waje. Ya Wauke ido daga kallon ta yana jin irjinsa yana bugawa sosai, idanunsa har tara ruwa yaji suna yi saboda tashin hankali. Ya sauke numfashi ya ce, "Bazan iya rabuwa dake ba Jidda, rabuwa dake kamar rabuwa da numfashina ne."

Ta yi murmushi tare da ajiyar zuciya ta ce, "me ya kawo batun rabuwa kuma?." Ya sake kallon idonta ya ce, "Jidda bana so a cutar dake, bana so wani abun ya sake samun ki. Shiyasa...." Ta katse shi ta ce, "shiyasa ka ke tunanin rabuwa dani?."

Ya girgiza kai alamun a'a bai ce komai ba. Ta ce, "daman akwai damuwar da zamu shiga har ka yi tunanin rabuwa dani YaMar?." Ya matsa kusa da ita sosai ya ce, "bana so naga kina yin koda ciwon kai Jidda, har dini aka yi miki a hannunki. Jidda ciwo nake ji a zuciyata wallahi."

Ta haWe rai tana kallonsa ta ce, "akan wannan aramin dalilin sai ka yi wannan tunanin? Ashe daman soyayyar da ka ke yi min iyakacinta kenan?." Ganin ta haWe rai alamun bata ji daWi ba sai ya murmusa ya rie fuskarta ya fara kissing bakinta cikin salon soyayya da son kwantar mata da hankali. A hankali ya zare bakinsa da nata yana rie da fuskarta ya ce, "ina sonki, ina aunar ki. Rabuwa da ke daidai yake da rabuwa da raina." Cikin shagwaSa ta ce, "to shine ka ke wancan tunanin?."

Ya sauke numfashi ya ce, "tsoron nake ji, da ace wani abun ya same ki ta dalilina gwara na mayar dake wajan Abiy kin cigaba da zama cikin kwanciyar hankali. Rashin ki zai yi min illa, rashin ki zai cutar dani, rashin ki zai zama ajalina Ashiq. Amma gwara na rasa raina da ace wani abun ya sake faruwa dake!."

Ta sauke numfashi cikin son kwantar masa da hankali ta ce, "in sha Allah babu abinda zai faru, da izinin Allah komai ya are, ka daina damuwa. Kuma don Allah ka daina yi min magana irin wannan, bana so."

Omar ya sauke ajiyar zuciya yana kallon ta cike da damuwa ya ce, "Dole na damu Jidda, kalli hannunki fa, ciwon yayi girman da sai da aka Winke shi. Har abada da wannan tabon zaki rayu har ki bar duniya, iya kallon wannan tabon na hannun ki ba aramin ciwo zai saka min a zuciyata ba, saboda na san ni ne sila. Baki da tabo ko kaWan a jikin ki, amma ta silata gashi kin samu tabo mai girma. Wallahi ban taSa jin na damu akan abinda na aikata a baya ba sai yanzu. Kuma nima haka nayi, matar mutum ko ar uwarsa da bata ji ba bata gani ba a kanta zan mu Wauki fansa, duk da ban taSa kisa ba, amma na..." sai ya kasa arasawa ya sake jan numfashi yana kallon ta ya ce, "ina hasashen yanayin da zan kasance in wani ya yi irin abinda nayi a baya Jidda, ban san a wanne yanayi zan kasance in aka sake cutar dake ba."

Nayla ta rie fuskarsa cike da damuwa ta ce, "Rauni nake gani a fuskar mijina, mijina bai yi kama da namiji mai rauni ba." Ya lumshe ido ya buWe ya ce, "Nayi rauni Jidda, raunin zuciyata ne ya bayyana akan fuskata Jidda, wallahi zuciyata tayi rauni sosai. In na tuna ta silata kika kwana a asibiti da ciwo a hannun ki sai naji duniyar tayi min zafi. Wannan shine dalilin da na kasa sakewa dake, gani nake kamar za a cigaba da cutar dake in na cigaba da amsa suna mijinki" ya faWa yana rie hannunta gam.

Nayla ta ce, "in sha Allah babu abinda zai faru, ka kwantar da hankalinka, Allah yana tare damu." Ya bita da kallo kafin ya Wauke ido daga kanta ya ce, "Rayuwarki bata dace da rayuwa a nan ba Jidda, ina jin tsoron kar wani abun ya sake samun ki, ina jin wannan tsoron a zuciyata. Sai yanzu na sake gasgata maganar Didi da take cewa baki dace dani ba!." Nayla a sanyaye ta ce, "YaMar ka daina faWar haka, yana cutar dani."

"Jidda har suma ki ka yi fa saboda tsoro, kika kwanta a asibiti saboda ciwon da aka ji miki. In aka sake cutar dake da wanne ido zan kalli Abiy?."

"Babu abinda zai kuma samu na, ka daina damuwa don Allah." Ya lumshe ido ya buWe ya kalle ta ya ce, "Ki yi hauri, na kasa kula da lafiyarki har aka wace miki waya, na kasa kula dake har aka yanke ki jini ya zuba daga jikin ki. Ki yafe min, aurena ne ya saka kika shiga yanayin da ki ka shiga, da baki aure ni ba da hakan bai faru ba."

Ta saka hannunta a tsakanin kafaWarsa ta rie shi tare da kwantar da kanta a jikinsa ta ce, "Ka daina faWar haka, bana jin daWi ko kaWan. Kuma ciwon da naji addara ce." Ya Wan lumshe ido ya buWe yana ji zuciyarsa na bugawa sosai.

Nayla ta ce, "Ya jikin wanda suka jiwa ciwo?."
"Ya ji saui, yana gida."
"An kama su ko?."
"Uhum, amma bazai jima ba zai fito. Yana da manyan da suka tsaya masa, baza su bar shi ya jima a gidan yari ba."
"Ko ya fito bazai yi mana komai ba, ka daina damuwa."

Numfashi ya sauke baice komai ba, yana jin zuciyarsa babu daWi akan abinda ya faru, ya san duk ta silarsa ta shiga yanayin da ta shiga. Sai yanzu yake jin raWaWin da iyaye da an uwan wasu suka ji a lokacin da yake cutar da yaransu. Sai da ya ga Nayla a kwance a gadon asibiti sannan ya tabbatar da ba aramin cutar da an uwan wasu suka yi ba. Gashi Allah ya fara saka musu, ya cutar da matar wani an cutar da matarsa, ya zama silar zubar jinin wata shima an zubar da na matarsa, ya zama silar kwanciya a asibitin matar wani shima ga tasa ta kwanta. Addu'a yake yi da fatan Allah yasa abun ya tsaya iya haka, in kuma sakayyar zata cigaba da bibiyarsa Allah yasa ta tsaya a kansa ba sai ta tsallaka kan Nayla ko Didi ba.

Nayla ta kalle shi ganin ya yi shiru yana tunani, ta zame ta zube guiwa a asa ta ce, "zan iya roar ka alfarma?." Ya Waga mata kai alamun eh, ta rie hannunsa ta ce, "Don Allah ko me zai faru kar ka ce zaka koma rayuwar da ka bari a baya, ko meye zai tunkaro mu ka karSi addara kar ka tunzura ka koma rayuwar baya Rouhi. Ko da zasu kashe ni, ka yi min alawarin baza ka cutar da kowa ba."

Ya yi murmushin gefen baki yana kallon ta ya ce, "ke kin san bana yin kara, bana faWar abu dan na burge wani ko wata. Wallahil azim duk wanda ya sake oarin cutar dake sai dai a haifi wani ba shi ba, wannan da aka yi na yale tunda an kama wanda ya aikata, amma in aka maimaita wallahi bazan yale ba. Jidda ko ban kashe shi ba sai nayi masa abinda zai ji ina ma ya mutu. Daga ranar kundin laifukan Omar Tiger da aka rufe za a buWe sabo, domin kuwa laifukan da na yi a baya ba komai bane akan wanda zan yi. Hmmm kedai Allah ya kiyaye kawai, amma zancen alfarma indai wannan ce bazan yi miki ba Jidda!."

Bata ce komai ba dan ta san bazai yi Win ba, ta rausayar da kai ta ce, "ni kuma hakan bazai yi min daWi ba." Bai ce komai ba ya girgiza kai kawai, ta ce, "sannan wannan wuar da ka ke kwana da ita ta meye?." Ya kalli idonta ya ce, "ko a addini dan na kwana da makami ba laifi bane, tunda na tare a gidan nan take kusa dani, duk Wan iskan da ya kuma kawo min wargi sai dai uwarsa ta haifi wani. Na daina sharewa, na daina kai maganar ga hukuma, zan koma Omar Win da suka sani a baya."

"Baza ka koma ba in sha Allah, babu abinda zai sake faruwa balle har ka Wauki mataki."

Shiru yayi bai ce komai ba, ta dawo ta zauna a kusa dashi. Fuskarta ya rie ya ce, "Akwai abinda yake damunki? Akwai abinda yake yi miki ciwo?. Hannun yana ciwo har yanzu?."
"Ba ya ciwo Rouhi, ya daina kamar ban ji ciwo ba. Lafiya alau nake." Yayi mata peck a goshi yana girgiza kai bai ce komai ba.

Sun jima a haka a zaune kafin ya ce, "ki kwanta Jidda, dare yayi." Ta kalle shi ta ce, "ta ya zan iya bacci bayan mijina baya cikin walwala?."

"Bana ciki Jidda, bazan taSa samun sukuni ba tunda aka fara haka. Tunani nake yi kar na fita na barki ke kaWai a gidan nan a sake cutar da ke."

"Haba Rouhii, ya zaka bada ni? Don Allah ka nutsu, ka manta da komai mu cigaba da rayuwarmu. Tunda muna addu'a Allah zai cigaba da kare mu, kariyar Allah ce ta saka ciwon ya tsaya a iya hannu, mu cigaba da addu'a kawai."

Ya zuba mata ido yana kallon ta kamar mai neman wani abu, sai ta ce, "Please!." Ya Wan yi murmushi da son kawar mata da damuwa ya ce, "kin daina jin tsoron nawa?." Ta yi murmushi ta ce, "Tiger nake jin tsoro ba Rouhii ba." Ya girgiza kai yana murmushi ya ce, "Ina sonki Jidda, ina aunar rayuwa dake. Ki yi hauri a yadda kika same ni, rana ta farko da nake jin nadamar abubuwan da na aikata a baya, da ban aikata ba da na kasance miji na gari a wajanki!."

Ta yi murmushi tana shafa gashinsa tana kallon idonsa ta ce, "Wallahi kai miji na gari ne Rouhi, babu abinda na nema na rasa a tare dakai akan me zaka dinga kiran kanka da wannan suna?."
"Jidda na kasa baki kwanciyar hankali, har suma ki ka yi a irjina saboda tsoro, ga tabon da aka yi miki wanda na tabbatar dashi zaki je lahira. A hakan ne na samar miki da kwanciyar hankali Jidda?."
"Suman da nayi firgici ne kawai, amma ba dan ka kasance akasin miji na gari a gare ni ba."

Ya zubawa bakinta ido har ta gama kana ya ce, "zan saka miki da alkhairi in sha Allah, wannan Sacin ran da na saka ki, da firgici, da tsoro, da ciwon da kika ji zai maye gurbinsa da farin ciki in sha Allah Jidda. Ki cigaba da hauri dani kawai, ina da Wabi'un da basa yi miki daWi, na san ina juyewa na koma miki wanda bakya so, amma wallahi ke ce rayuwata. Ina sonki, ina aunar zaman ki cikin kwanciyar hankali, ina so na rayu dake, ina tsananin kishinki!. Dan a cikin haushin fitar ki da naji harda kishin Tk da ya rie hannun ki, har yanzu ko magana bana iya yi masa, duk da ba da wani abun ya aikata ba, ya yi ne dan ceton rayuwarki amma na gaza fahimtar hakan!."

Nayla ta yi murmushi ta ce, "ni shaida ce akan duk abinda ka faWa YaMar. Amma ka yi hauri ka manta da batun Tk, kamata ya yi ka sake rie shi hannu biyu ba ka daina kula shi ba. Shi ne ya ceci Ashiq Winka, ka daina jin haushinsa don Allah."

Ya sauke numfashi yan kallonta, ta yi murmushi ta ce, "duk da fushi ka ke yi dani a cikin kwanakin, baka iya barina da yunwa, sai ka tabbatar naci abinci, in baka siyo ba sai ka dafa min. In na ci abincin sai ka tabbatar na sha magani ka ke bari nayi bacci. Ina jinka in ina bacci kana taSani dan ka tabbatar lafiya nake. Iya wannan ya isa ya tabbatar min da mahimmacina a rayuwarka."

Ya yi murmushi ya ce, "ni ba fushi nake dake ba, kece ki ke fushi dani har ki ke jin tsorona, shiyasa na baki lokaci ki dawo nutsuwarki ba dan kin yi laifi ba. Ta ya zan yi fushi dake bayan ni ne mai laifi? Ina da son ayi min adalci a rayuwata, shiyasa nake yiwa kowa adalci, in nayi fushi dake ban yi miki adalci ba."

Ta zuba masa ido bata ce komai ba, shima kallon ta yake yi kamar zai haWWiye ta saboda aunarta da tausayinta da yake ji. Muryarsa ya kai can asa yana shafa fuskarta ya ce, "na saka ki kuka ko, Ashiq Wina?." Ta shagwaSe fuska cikin muryar shagwaSa ta ce, "shiyasa na ce ni bana so kana komawa Tiger, nafi son Rouhiina" ta faWa tana karya murya. Yayi murmushin da yake kashe mata jiki ya ce, "Tiger ya tafi, amma zai dawo wani lokaci. Kafin ya dawo ga Rouhinki ki yi abinda ki ke so, Jiddana!" Ya faWa yana lumshe ido kamar mai jin bacci."

Kafin ta yi magana ya ce, "Na yi kewarki Jidda!" Ya faWa a kunnenta cikin kasalalliyar murya. Ta kalle shi ta ce, "Nima nayi kewar ka Rouhii." Ya anantar da ido ya ce, "Ki nuna min, ki saka aljanun wannan dare su tashi" ya faWa da salon da ya bata dariya har ta fara kissing Winsa cikin kewa da soyayya. an zame kansa ya yi ya ce, "baki da lafiya Jidda, kar na wahalar dake."
"Ni haka na ce maka bani da lafiya?."
"Ni na san babu."

Ta kalli idanunsa ta ce, "Ni lafiyata alau" ta arasa faWa cikin salon da ya saka shi lumshe ido yana buWewa akan fuskarta. Ya matso da fuskarsa kusa da ta ta ya ce, "ciwon ki fa, babu matsala?." Bata ce komai ba saboda yadda yake bin wuyanta da hancinsa yana sauke mata numfashi mai zafi hannunta yana cikin gashin kansa.

Kissing wuyanta ya yi ba tare da ya Wago ba ya ce, "Ashiq!." Nayla dayar ta iya buWe baki ta ce, "Uhum."
"Bani da kuzari mai yawa, zaki taimaka min?." Ta buWe idanunta ya kalle ta da ido ya Waga mata gira tare da haWe bakinsa da nata cikin tsananin kewa da soyayya.KRB3P076
Nana haleema
#Thebeginingofsuccess!

Haka suka cigaba da zama cikin soyayya da aunar juna, abinda ya faru ya saka Omar ya ara ninka kulawar da yake bata. Ko fita ya yi baya jimawa zai dawo, in kuma ya kira wayarta aka yi rashin sa a bata Wauka ba lokaci Waya sai hankalinsa ya tashi ya dawo gidan. Baya iya bari ta fita ita kaWai, duk inda zata je sai ta jira ya kaita in ba haka ba sai dai a fasa. Ya shiga damuwa akan abinda ya faru, shiyasa yake kiyaye duk wata hanya da za a sake cutar da ita. Da yake abin bai baza duniya kamar wancan lokacin ba ba kowa ne ya san ya faru ba.

Cikin ikon Allah babu abinda ya sake faruwa, tun yana jin fargaba har ya daina ya sake suka cigaba da rayuwarsu. Wannan sabuwar kulawar da yake bata sai ta sake zama ar gata a wajansa, kulawa yake nuna mata zalla wacce babu sirki a ciki. Ko sau Waya ka je gidan zaka tabbatar da irin aunar da Omar yake nunawa Nayla, baya iya Soyewa ko kaWan, ko yaushe cikin faWa mata sirrin zuciyarsa yake baya iya yin shiru.

angaren kasuwancinsa sai dai ace alhamdulillah, kuWi ne suke shigo masa ta ko ina kuma suna fita. Harka ta buWe ta ko ina, dan zuwa lokacin ya siyi bus da machine na kai kaya, sannan yaransa uku duk ya siya musu machine na hawa.

Babu wanda yake aiki a arashinsa baya jin daWin zama dashi, sai dai yana da faWa wanda duk yaransa sun saba da faWansa, in yana yi ma wani lokacin basu cika damuwa ba saboda sabo, amma kyautatawa kam yana yi sosai. Naira biyar in ta shiga account Winsa sai Nayla ta sani, baya iya Soye mata samunsa haka in asara aka yi itama zata sani. Duk ribar da za a samu da abinda zai siyawa Didi da Marmerh, ya canjawa Didi waya da sauran kayan amfani musamman a Sangaren sana'arta. Marmerh kuwa

Please Login or Register in order to submit comment