Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"iya tea Win ma ya isa."

Tea Win ya karSa ya koma ya zauna daga can arshen Wakin ya zauna dan gaskiya bazai iya fita ya bar Nayla ba. Mama ta saka aka bawa Nayla dafaffen naman rago da aka shi da romo mai yaji kaWan ta ce ta ci. Ta kuwa ci Win amma ta fi shan ruwan, ta ajjiye bayan ta gama ta Wora mata Babyn a cinya ta ce, "To bismillah, ki shayar da ita yunwa take ji itama." Nayla kamar zata yi kuka ta kalli Omar da ya kalle ta, suna haWa ido yayi mata wata inkiya da ido yana sipping tea da yake hannunsa yana ifta idanunsa. Dariya ta kama Nayla, amma sai ta Wauke ido daga kansa ta kalli Mama ta ce, "Mama ai ban iya ba."

Shigowar Jidda Wakin ya hana Mama magana, ta taho ta rungume Nayla ta Wauki Babyn tana kallonta ta ce, "kin ci amanata." Nayla ta ce, "yi hauri." Suka gaisa da Mama dan ita bata ma ga Omar ba dan yana can arshe sai ka kula zaka ganshi dan Wakin yana da girma.KRB3P097
Nana haleema

Mama ce ta nunawa Nayla yadda zata shayar da ita, Nayla ta yi yadda tace sai zuba shagwaSa take yi ita zafi take ji, ita ta gaji waye-waye. Duk Waga idon da zata yi ta kalle shi sai sun haWa ido, da sun haWa ido kuma sabuwar inkiya zai yi mata wacce ita dashi kaWai suka san me hakan yake nufi. Mama bata yaleta ba sai da ta tabbatar yarinyar ta oshi sannan ta karSeta aka kwantar da ita. Jidda hoto ta dinga yiwa yarinyar ta tura family group Winsu.

Omar bai jima ba sai ya fita, fitarsa Jidda ta gani dan bata san yana nan ba. Mama ta saka Nayla ta yi wanka ta saka doguwar riga wacce Mama ta taho mata da ita ta kwanta a kan gadon bacci ya sake Wauketa. Duk suka fito waje saboda ta samu ta yi baccin yadda ya kamata.

Omar sai da ya koma ya ga kiran Didi WhatsApp call, ya yi murmushi ya kirata ta ke tambayar mai jego ya ce ya barta asibiti. A gaggauce ya shirya shima, ya yi wanka ya canja kaya ya dawo asibitin dan bazai iya zaman gidan ba sam.

Washe gari ranar sallah, ji yake ko sallar ma bazai iya zuwa ba, amma ganin Mama na kula da ita sosai sai ya je ya dawo daga masallacin kai tsaye ya dawo asibitin. Da yake asibitin kuWi ne akwai ma'aikata suna ta aikinsu, ya shiga Wakin Nayla da sallama a nan yaga jama'a sun aru harda waWanda bai sani, abinda ya bashi mamaki ganin dangin mahaifiyarsa, ya bisu da kallo dan ya san aikin Didi ne. Gaisawa kawai suka yi ya fito ya zauna sai ga Mama Saroot da Mama Zainab sun fito suka kalle shi a raWaWe suka ce, "Omar an samu aruwa, Aisha ce take sanar damu, Allah ya raya."

"Amin. An yi sallah lafiya?." Mamaki ya hana su magana suka zubawa juna ido, dayar Mama Zainab ta ce, "Lafiya lau, Allah ya raya abinda aka samu, ance sunanta Aisha ko?." Ya Waga kai Mama ta ce, "Allah ya raya mana, yasa ta yi halin mai sunanta." Ya amsa da amin sai suka samu arfin guiwar zama a asibitin dan suna tsoron kar ya yarfa su a gaban sirikai.

Sai da aka kwana biyu a asibiti sannan aka bada sallama, da kansa ya rio hannun Nayla suka fito tana takasa a hankali Babyn na hannun Mama Sa'adatu, sai Mummy Maman su Salma. Mota suka shiga aka wuce gidan sa kai tsaye.

Kai tsaye sama aka saka ta ta hau yadda baza ta sake sakkowa ba, duk wanda ya zo sai dai ya hau saman. Tana falon a zaune, bayan Mama ta saka ta yi wanka ta shirya cikin atamfa baza ka ce ita ta haihu ba. Nayla ta saka Jidda ta Wauko kayan Babyn ana Waurawa, baby beds da baby swing aka ajjiye a falon. A ranar su Mama suka zo daga Kaduna harda Abiy da Salma da kuma Jawad da su Jalila.

Farin ciki a wajan Nayla sai da tayi kuka, ta rie Abiy dan bai taSa zuwa gidan ta ba sai yanzu. DaWi take ji da ta gashi a gidanta, ta saka aka yi musu hoto shida ita duk ta ruWe kamar bata taSa ganinsa ba. Bai jima ba ya tafi bayan ya bada kayan baby da kuma kayan ita kanta Naylan. Mama kuwa basu tafi ba sai dare, Salma ma sai dare sosai sannan suka tafi. Jalila kam ta ce kwana zata yi suna tare tana rie da Musliha tana yi mata hoto.

Mama Sa'adatu bayan tafiyar Maman Kaduna ta kalli Nayla ta ce, "Nayla zan koma gida yanzu, amma gobe da safe zan dawo. Zan zauna har sai an yi suna daga nan Baba Hafsatu zata zo ku cigaba da zama har ki samu lafiya." Nayla ta ce, "To Mama."

"Ki kula sosai, ban da yawan zirga-zirga kin ga baki da lafiya kuma an miki Winki. Wai kin aru a wajan haihuwar ne har aka yi miki Winki?." Nayla ta girgiza kai tana turo baki ta ce, "A'a, kawai an yi min ne, cosmetics ne." Mama ta rie haSa ta ce, "Gaskiya ne an daWi miji, kin kyauta." Nayla ta yi murmushi Mama ta tafi aka barta da Jalila da Ummimi.

Nayla falonsa ta shiga da Musliha a hannunta, ta same shi yana zaune a akan kujera yana duba waya, ganinta sai ya ajjiye wayar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wai haka ake haihuwar a hana ka ganin matarka? Zo ki zauna" ya faWa yana tashi tsaye ya karSi Musliha sannan ya zaunar da ita. Nayla ta ce, "To ka ga bai ake ta yi shiyasa, yanzu ma motsin ka na ji nace ko mijina ya ci abinci?."

"Wa nake dashi da zai bani?."
"Baka ci ba kenan?."
"Ban ci ba." Nayla ta ce, "to bara na nemo maka." Ya dakatar da ita ya ce, "Wasa nake yi, har falon nan Mama ta saka aka kawo min abinci, na zama Wan gatanta, bata barina da yunwa."

Murmushi ta yi ta ce, "Na ji daWin haka." Ya zuba mata ido ya ce, "Wai ba a gama jegon ba?."
"Tab ai sai nan da kwana arba'in."
"Ko kuma sai an tashi duniya ba" ya faWa cikin baar magana yana harararta. Nayla tayi dariya kaWan tace, "Allah da gaske nake."
"Kedai ayi shiru kawai, amma wallahi baza ki kwana arba'in ba."
"Harda wallahi?."
"Kuma kin san bana rantsuwar banza ba." Ta yi dariya ta ce, "Wazu an kaiwa Hajja Musliha."

Ya yi murmushi mai sauti yana girgiza kai ya ce, "ai gwara da aka kai mata ita."
"Murmushin na meye?."
"Na Hajja ne."
"Da ta baka aurena?."

Omar ya sake yin ar dariya ya ce, "da aka bani auren ki a gidanta." Nayla ta murmusa ta ce, "tijarar da ka yi a gidan fa?." Ya shafa fuskarsa yana tuna lokacin, ya sake yin murmushi ya ce, "ta rashin sani ne, ai ban san haka sirrin yake ba, ban san haka abun yake da Wankaren zai ba." Nayla ta sake yin murmushi ta ce, "baka da kunya."

Ya Wan sunkuyar da kai tare da Wago ido ya kalle ta ya ce, "itama mai jin kunyar tayi ciki ta haihu, kuma ba a ruwa tasha cikin ba." Nayla ta sake yin murmushi ta kwantar da kanta a kafaWarsa ta ce,"Yaushe Didi zata dawo ne?."
"Har sai an yi suna."
"Kai amma ban jiwa Didi daWi ba." Murmushi ya yi akwai suka cigaba da hira.

Haka aka cigaba da karSar bai an barka, dangin babansu Omar duk sun zo kuma suna haWuwa babu wanda yake nunawa wani abu, sai yaga dama na zai kula su, hakan ya saka gobe ma wasu suke zuwa. angaren su Umma Saroot kusan a gidan take yini kullum tunda itace bata da aure a cikin su, ko yaushe kusan tana nan tana bawa Nayla irin ta ta kulawar ta mutanen Chad, musamman Sangaren turaren wuta da humra da gyaran jiki.

Ranar suna aka raWawa yarinya suna Aisha ake yi mata laabi da Musliha. Shanu uku aka yanka na ranar suna, aka yi decoration a harabar gidan dan gidan babba ne no need a fita event center, aka Wauko masu hoto da masu video da masu kiWan warya. Abinci kuwa ba a magana, dan komai da komai leemars_delicious ce tayi, kowa sai yabawa yake yi saboda daWin abincin.

Taro aka yi gagarumi, tun daga farkon gidan banner hoton Musliha ne har arshe, a cikin wani gado na glass aka saka ta duk wanda ya zo ya ganta a ciki ba a Waukarta tana ciki tana bacci. Kafin a fara taron Nayla ta takura masa akan za a yi musu hoto da video, ya nuna baya so ta dage da magiya har ya amince, aka kira mai hoto da videographer aka yi musu a cikin gida shida ita da Musliha kafin a fara taro.

Kafin a gama taro tuni hotuna sun yaWu a duniya, masu hoton wajan da masu video suna ta Worawa a duniya ana saka c.e.o exclusive footwear with his wife on their daughter's naming. Mutanen suna ta tofa albarkacin bakinsu, musamman yanayin kyaun da suke dashi sun dace da junan su sosai.

Omar bai gani ba sai bayan an tashi daga taron kowa ya watse sai an uwanta. Ran maxa ya Saci, aljanun tijararsa da rashin mutunci suka motsa. Nayla tana zaune kawai ta ganshi a falon ta, kafin ta buWe baki ya nuna mata wayarsa ya ce, "meye wannan?." Nayla ta kalli wayar ta ga hotonsu ne, ta kalle shi zata yi magana ya ce, "da izninki aka yi posting kenan?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a ban sani ba, kawai sun yi ne saboda aikin su ne."

"Oh aikin su ne Wora matan mutane ba tare da izni ba? Aikin su ne dan sun yi maka hoto sai sun yaWa a duniya?."

Ganin ya fusata ya fara faWa sai tayi asa da murya ta ce, "suna yi ne saboda advert, amma...."
"Amma me!? Da hoton naki da na ata za a yi advert Win Jidda!?." Tayi ajiyar zuciya jin yadda ya fara yi mata halin, tsawar da ya yi mata har tsakiyar kanta, bata so maganar ta yi nisa sai ta ce, "ka yi hauri."

Ya girgiza kai cikin fushi ya ce, "Dole ki ce na yi hauri ai, dole ki bani hauri tunda sun riga sun yi, blog sama da goma sun yi reposting dole ki bani hauri Jidda." Nayla ta kalle shi da damuwa ta ce, "ban san zasu yi ba, da nace kar a yi."

"Yanzu ma ki saka su goge, yanzu ba anjima ba su goge hoto da video, ai ba da iznina suka yi posting ba. Ni ba shashasha bane da zan bar hotunan ku a duniya suna yawo da sunan wayewa ba, bana ra'ayi, daman ni ba wayayye bane, dan haka bazan yi aikin wayayyu ba. Bana so a cire yanzun nan, in ba haka ba wallahi zan yi ararsu!. Ai ba ni na ce su saka ba, kema ba ke kika ce su saka ba. In ba su goge ba kotu ce zata raba mu!." Jin yadda yake yi mata faWa sosai harda zancen zai yi ararsu sai tayi sanyi dan ta san laifinta ne, da ta ce kar ayi posting da ba a yi ba. A sanyaye ta ce, "To zan ce musu." Ko kallon ta bai sake yi ba yana fita cikin unar zuci.

Salma da take zaune ita da Jidda dan sun fito lokacin da ya fara faWan, Nayla ta kalle su da damuwa ta ce, "Yanzu ta ina za a fara goge hotunan don Allah?."

"Kema laifin ki ne Twiny, kin san halin mijinki da sai ki ce kar su yi posting." Nayla ta kalli Jidda ta ce, "Wallahi mantawa nayi Twiny, ban Wauka abin nasa zai zo da haka ba."

Salma ta ce, "ki kira su ki ce su goge." Nayla ta ce, "kin san adadin mutanen da suka yi reposting kuwa? Kuma ni tsorona an TikTok wallahi, gwara an Ig zasu iya gogewa, amma an tiktok sai a hankali." Jidda ta ce, "haka zaki yi musu magana tunda baya so, sannan sai ki je ki bashi hauri." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Hmmm Twiny ke baki san shi ba ne, amma Salma ta san waye shi ai. Wallahi in ransa ya Saci wanda ku ka sani a baya yake komawa, baya Waga min afa ko kaWan."

Salma ta yi dariya ta ce, "Tiger yana dawowa kenan. Amma ki je dai ki bashi hauri, Yayanki ma in ni ce aka yi posting pics Wina na shiga uku, ba ya aunar posting a social media da hotunana, wai ba tallata yake yi ba." Jidda ta ce, "Nima dai bana so wallahi, ban Wauki nuna hotuna na da mijina da sunan wayewa ba sam." Salma ta ce, "mu dai zamu wuce, ki je ku arke da Tiger lafiya, Allah ya sa kar ya yi kaca-kaca da naman jikinki. Jidda mu je" ta faWa suna fita suka bar Nayla da ajiyar zuciya.KRB3P098
Nana haleema

A zaune ta same shi a falo ya rufe ido, ko da ya ji shigowarta bai buWe ba daman ta san bazai buWe ba, ta zauna a gefensa ta ce, "Rouhi ka yi hauri, nayi mata magana zata goge yanzu in sha Allah." Bai buWe ido ba ya yi mata banza, zata sake yin magana aka kira shi a waya.

Ya buWe ido ya kalli mai kiran ya ga Farid China da haka ya yi saving, ya Wan yi tsaki sannan ya Wauka ya saka a a speaker. Daga can Sangaren ya ce, "Omar ashe yau ake sunan babyn ka shine babu labari? Yanzu na gani a tiktok, gaskiya matarka she is so cute wallahi, kun dace, damn....." it ya kashe wayar ya cillar da ita akan kujera.

Nayla ta sake tsorata dan ta san an kuma tsokano shi, in bai yi niyar magana ba ma yanzu ta san sai ya yi. Ya kalle ta bayan ya tashi zaune sosai ya ce, "Hankalinki ya kwanta ko? Hankalinki ya kwanta kin ji daWi a zuciyarki an ga hotonki an ce kina da kyau, sai ki je ki siyi abin sadaka ki rabawa yara." Nayla ta kalle shi a raunane zata yi magana ya Waga mata hannu ya ce, "kar ki ce min komai, ban ce ki yi min magana ba. Ba hakan ki ke so ba? In ba hakan ki ke so ba meyasa ki ka aikata!?."

Ta sunkuyar da kai tayi shiru dan bata aunar wannan faWan na sa, faWa ne wanda bashi da full stop in ya fara, bai san kara ba kuma baya Waga mata afa.

Omar ya cigaba ya ce, "iya afarki ce ta fita a duniya nace miki bana so aka daina, amma da yake kina so a ga fuskarki sai kika iriro da za ayi hotuna. Na ce bazan yi ba, ki ka yi min magiya na tsaya aka yi saboda tarihi kamar yadda kika ce, amma sai ki ka bada dama aka yaWa min hotunan matata a duniya. Ke kin san me nake ji kuwa? Kin san lokacin da na ga afarki ana yabonta a duniya me naji?. Ji nayi zan iya aikata komai a lokacin, zuciyata tana bugawa, gangar jikina tana rawa matua saboda kawai an yabi afarki. Yau fuskarki da surarki ake yabo..." ya faWa yana watsa hannayensa cikin tsananin kishi da Sacin rai.

"Har wanWanda ba sa jin hausa abokan kasuwancina sun kira ni suna cewa sun ga matata. Hankalinki ya kwanta an ganki ko Nayla!? To ta shi ki tashi ki bani waje!." Nayla ta kalle shi da sauri jin da sunan da ya kirata, zata iya irga sau nawa ya kira ta da Nayla, dan baya faWa kwata-kwata. Kuma ta san baya taSa ce mata Nayla sai in ta Sata masa rai, a lokacin ne yake mantawa da Jidda ko Ashiq ya kirata da sunanta.

A raunane ta ce, "wallahi Rouhi ban ce ayi posting ba, na san laifina ne da ban yi magana na ce kar ayi ba, amma ban san zasu yi ba."
Kamar zai dake ta ya yo kanta da faWa a hargitse ya ce, "Amma kin san babu ta yadda za a yi ayi mana hoto nida ke ace baza a yi posting ba ko!? Likers suke nema, kuma matuar aka Woraki dole a samu likers har da comments. Meyasa baki wannan tunanin ba!?" Ya faWa a fusace yana zare mata idanu waje.

Sak ya koma mata Tiger, kallon Tiger take masa lokacin da ya Wora mata wua a wuyanta yana zare mata ido, kallon tiger take masa wanda ta ganshi da jini kaca-kaca a jikinsa. Jikinta ya yi sanyi sosai, a hankali ta sake cewa, "na yi kuskure ka yi hauri, amma yanzu na yi mata magana zata goge in sha Allah." Ya kalle ta cikin hararar da ta saka ta yin shiru, ya yi wafa tare da jan tsaki ya girgiza kai bai ce komai ba.

Nayla ta duba wayarta ta nuna masa ta ce, "ka gani har ta goge ma." Ya Harare ta da jajayen idanunsa ya ce, "Ko ki matsar da wayar nan daga kusa dani ko na fasata, kuma wallahi in na fasa bazan siyi wata ba, kema kuma baza ki siya ba, na kuma ce wallahi." Nayla ta janye wayar ta ajjiye a gefenta, ya bita da kallon up and down ya ce, "Dan ta goge mutane nawa ne suke dashi? Mutane nawa ne suka saka su ma? Ko duk zaki bi su ki ce su goge ne?."

Yadda ya kafe ta da ido shine ya saka ta sauke ido asa bata ce komai ba. Yaja dogon tsaki ya ce, "Kawai kin riga kin cuce ni, kin yi min abinda bana ra'ayi kuma bana so. Duniya gabaWaya a kan hotonki take magana, ni ba banza ba ne da zan ji alfahari dan wani ya yabi matata ba......" ya Wauke ido daga kanta, kafin ya sake kallon ta ta ce, Ki ta shi ki bani waje na ce ko!?."

Nayla zata yi magana cikin tsawa ya ce, "in kika yi min magana sai na fasa miki baki, ki bar wajan nan ko na nuna miki asalin waye ni!." A hankali ta mie ta bar falon bata ce komai ba, ya yi tsaki ya Wauki wayarsa ya shiga TikTok, bai yi seconds biyar yana scrolling ba ya yi karo da video sa shida Nayla da kuma Musliha.

Kishi da haushi suka sake kama shi ya furzar da iska ya cillar da wayar. A haka ya kwanta cikin takaici da Sacin rai, in dai zai farka sai ya duba wayarsa, amma baya jimawa yana scrolling zai ga ga abinda baya so, arshe kashe wayar ya yi cikin bain ciki da takaici.

" " " " " " " "

Cikin wanda suka ga video Nayla da Omar harda Narma, Narma ta ruWe ta saka hotunan a gaba tana kuka. Dad da yake zaune a kusa da ita ya rie hannunta ya ce, "Haba Narma meye haka kuma? Baki yarda da abinda nace miki bane ba wai?."

Narma ta ce, "Dad kalli matar shi, kalli yadda yake farin ciki kana gani ka san yana sonta. Dad ni ce baya so, Dad bazai aure ni ba, shikenan mutuwa zan yi." Ta faWa cikin kuka mai tsanani. Mum ta kalle ta cikin tausayi ta dafata ta tace, "ki yi hauri Daughter, kin ga saboda ke mu ka zo Kano dan a same shi a yi magana, in kina wannan kukan sai ki saka mu ga kamar har yanzu kina ganin bamu kyauta miki ba."

Dad ya rie hannunta ya ce, "Zan je na same shi da kaina nayi masa magana, na tabbatar zai amince ya aure ki tunda yana sonki yana aunarki, na tabbatar zai amince ya aure ki in sha Allah, so don't be nervous." Ta kwantar da kanta a kan kafaWar Dad ta ce, "Dad da gaske zai amince?." Dad ya ce, "zai amince ya aureki, I promise you zan san yadda zanyi ya amince ya aure ki daughter. Kar ki damu ki kwantar da hankalinki."

Ta goge idanunta tana cigaba da kallon hoton Nayla da Omar zuciyarta na bugawa sosai. Hankalinta ya gama tashi gani take yi bazai amince ya aure ta ba tunda yana da matarsa mai kyau gashi har ta haihu.

Washe gari da safe Dad da Mum suna zaune suna breakfast Narma ta fito taja kujerar dining ta zauna, Dad ya kalle ta kafin ya yi magana ta ce, "Morning Dad." Dad ya ce, "Ya ki ka tashi Daughter?."
"Fine" ta faWa tana haWa tea tana sha bata sake cewa komai ba. Dad ya ce, "nayi waya an tabbatar min da yanzu yana office, in na fita zan je na haWu dashi."

Narma ta Waga kai kawai bata ce komai ba. Mum ta ce, "ki kwantar da hankalinki dear, komai zai zama daidai." Kai ta Waga bata ce komai ba ta mie da mug Win hannunta ta hau sama.

Mum ta kalle shi a raunane ta ce, "Dear anya yaron nan zai amince da auren Narma?."
"Zai amince in sha Allah, kar ka damu in sha Allah zai amince. In bai amince ba ya zamu yi da Narma? Ai sai ta samu heart attack." Mum ta yi tagumi ta ce, "wallahi na damu sosai, bana son wani abu ya samu Narma wallahi."

"Saboda ita zan je na same shi amma bayan haka ke kin san bazan je ba, amma zan je saboda mu san abinda zai faru, Na san bazai i amincewa ba tunda yana sonta. Kuma a matsayin da yake dashi yanzu abin alfaharinsa ne ace yana da inlaw kamar ni." Mum ta girgiza kai ta ce, "to ba dole ma ya amince ba, ai dole ya amince ya aureta ko baya so." Shiru ya yi ya girgiza kai bai ce komai ba ya mie ya fita.

Omar da safe koda ya tashi shiryawa ya yi ya fito falo ya tarar an ajjiye masa kayan breakfast. Zama ya yi yana ci, a lokacin Nayla ta shigo da sallama hannunta Wauke da Musliha. Sallamar ya amsa ya kalle ta ya watsar kamar bai ganta ba, ya mia mata hannu alamun ta bashi arsa. Ba musu ta bashi Musliha, sai ya yi murmushi yana kallonta domin kuwa Allah ya zuba baiwar kyau a fuskar Musliha. Nayla ta ce, "Ina kwana."


Kallonta ya yi ya Wauke kai a daile ya ce, "Lafiya." Daga nan ya yi shiru bai ce komai ba. Nayla ta ce, "YaMar har yanzu fushi ka ke yi?." Bai kula ta ba ya gama abinda yake yi, ya sumbaci goshin Musliha ya mie tsaye ya zo inda take ya ajjiye mata ita a jikita, ya kalle ta suka haWa ido na wani lokaci kafin ya janye idonsa ya Wauki key na mota ya sauka daga saman.

Ajiyar zuciya ta yi tana binsa da kallo ta ce, "na shiga uku kuma fa ai, shi bai san ayi abu ya wuce ba, yayi ta fushi kenan kamar tsohon arne. Zai yi ya gama ya dawo ya same ni." Tashi ta yi ta shiga nata falon dan bata san abinda zata yi masa ba kuma.

Omar ko da yaje a haWaWWen sabo office Winsa na karSar manyan bai ya zauna, office Win yana da girma sosai, Wauke da kujeru set Waya masu kyau da kuma kujeru na zaman office. Da awards da ya samu a jere akan wani dogon table, ga hotonsa da manyan mutanen nigeria da wajenta.

Babu abinda babu a office Win, tv, dispenser, fridge, kettle ta dafa tea, microwive da komai na amfani akwai. Buga ofar aka yi ya ce a shigo, aka shigo da sallama ya kalli yaronsa alamun arin bayani ya ce, "Boss akwai wani babban mutum da ya zo nemanka." Omar ya Wan yi jim kafin ya ce, "Waye?."
"Kamar Wan siyasa ne."
"Ya jira ni ina

Please Login or Register in order to submit comment