Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bai wuce har yanzu kana fushi da ita ba. Abiy ya ce,  magana ta ™are, cigaba da lissafin. Suka cigaba da abinda suke yi.

Mama da ta koma Waki ita kanta ta kasa nutsuwa, ba haka taso ta ga Nayla ba, taso ta ganta cikin damuwa sosai amma sai ta ga akasin haka. Taso ta je ta ga Omar ya yi mata dukan tsiya sai taga babu alamun koda cizon sauro a jikinta balle alamun duka, taso ta je ta ga fuskarta a kumubure, fatar jikinta a yayyake amma sai ta ga kyau da ™yalli ma fatar take yi. Gashi yanzu Abiy ya fara zargin bata faWar alkhairi, tunda ya fara faWar hakan kenan ya karSi auren na su hannu biyu. Ba yanzu take so ya amince da auren ba, ko da zai amince tafin so sai Nayla tasha ba™ar wahala a hannun Omar, amma yanzu tun ba a je ko ina ba ya fara faWar haka dole ta damu. Zagaye take yi tana tunanin ya zama dole ta samo mafitar da Nayla zata sha wahala sannan Abiy ya sake tsanar auren, sai ta yi hakan burinta zai cika, a yanzu abinda yake faruwa ba shi take so ba.

" " " " " " " "

Mum da Dad da Najwa sun dira Texas saboda yadda hankalin su ya kasa kwanciya a kan Narma. Sun je estate Win da suka san suna nan amma basa gidan. Hankalin Mum ya sake tashi da™yar Dad ya lallaSa suka koma inda suka sauka. Bayan sun koma Mum cike da damuwa ta kalli Dad ta ce,  ni wallahi jikina yana bani wani abun ya samu Narma, ka kira Ashraf Win mu ji suna ina.

Dad bai musa ba ya kira Ashraf whatsApp call, Ashraf bai fahimci Dad yana America ba tunda whatsApp call ne ya saka shi ya Wauki wayar. Yana Wauka Dad ya ce,  Ashraf kuna ina ne? Ga mu a estate Win da ku ke amma gidan babu kowa. ˜irjin Ashraf ya buga ya kalli Narma da take kallon sa ya ce,  Eh Dad, mun canja estate ne.
 Turo min location Win yanzu.
 Okay Dad ya faWa yana yanke wayar.

Narma ta kalle shi bayan ya yanke wayar ta Wauke kai bata ce komai ba, ko murnar zuwan iyayen nata ma bata ji ba dan a ganin ta duk su suka saka ta a cikin wannan hali da take ciki. Da sun amince ta auri wanda take so duk da ba haka ba ai.
Ashraf bai nuna ya wani damu sosai ya turawa Dad location Win inda suke. Ya juyo ya kalle ta ya ce,  Ko da su Dad sun zo babu wanda ya isa ya raba ni dake wallahi, sai na gama fanshe wahalar da ki ka bani kafin na rabu dake ki je ki auri Wan daba. Narma bata ce komai ba ta Wauke kai dan gabaWaya yanzu ta zama shiru-shiru, duk rashin kunyar nan da take ji da ita ta gudu.

Kusan mintina ashirin da tura musu location Win aka fara danna door bell, Ashraf ya mi™e ya buWe suka fara haWa ido da Mum. Kallon da take yi masa ya saka ya Wauke kai daga kallon ta, Dad ya yi hugging Winsa ya ce,  Ashraf mun zo babu notice ko?.
 Babu komai Dad, ku shigo. Shiga suka yi falon Narma na zaune a kan kujera ko motsawa ma bata yi ba.

Mum ce ta kalle ta ta kalli Dad da shima ya kalleta ta ce,  Narma baki gan mu ba ne?. Kallon su tayi ta sake Wauke kai bata ce komai ba. Dad ya wara idanu ya ce,  Narma me yake damunki? Kin yi rashin Lafiya ne?. A guje suka taho inda take kawai sai ta fashe da kuka.

Dad ya zauna a gefen ta Mum ma haka, suka sakata a tsakiya suna tambayarta abinda ya same ta. Bata ce komai ba kuka kawai take yi Mum ta kalli Ashafe ta ce,  Asharaf me yake damunta ne? Me ka ke yi mata da ta koma haka duk ta rame uhum?. Meyasa ko yaushe ba a samun ta a waya?. Ashraf ya ce,  Mum ta samu miscarriege ne fa. Dad da mamaki ya ce,  miscarriege! Yanzu Ashraf miscarriege ta samu baka kira ka sanar da mu ba? Meyasa ka Soye mana?.

Mum kallon Narma take yi ta ri™e hannunta ta ce,  yaushe hakan ya faru?. Ashraf ya ce,  Dad na so na sanar da ku itace ta ce bata so na faWa mu ku kar hankalin ku ya tashi. Dad ya kalle ta ya dafa kanta sai ya ce,  har yanzu jikinta da zafi sosai.

Narma cikin kuka ta ce,  Dad kun raba ni da Faruk Win, kun aura min wannan. Na tsane shi bana sonsa na gaji da zama dashi. Kuma ba miscarriege na samu ba, he aborted my baby! Ta faWa tana hawaye.

Mum a razane ta ce,  What! Abortion?. Narma ta ce,  Yes Mum, da kansa ya saka aka cire cikin ya ce he s not ready to be a father shiyasa ya zubar da cikin. Ya mayar da ni s*x machine, always on it. Ya ™wace wayata, ya canja mana estate, ya canja password na ™ofa saboda kar na fita. Rayuwa nake kamar a prison, na gaji! ta faWa tana kwanciya a jikin Mum tana kuka.

Mum ta kalli Ashraf da yake zaune ya wani basar kamar ba laifinsa ake faWa ba, ta kalli Dad da yake kallon Ashraf Win shima cikin ™unar rai. Mum ta ce,  na faWa maka daman jikina yana bani Narma tana cikin matsala ka ce min ba haka ba. Kana ji ai yanzu, har zubar mata da ciki ya saka anyi, baiwa aka kawo masa ko kuma sonta ne baya yi?.

Dad ya kalli Ashraf cikin Sacin rai ya ce,  Ashraf duk abinda ta faWa kana aikatawa?. Asharaf cikin rashin damuwa ya ce,  Dad har yaushe muka yi auren da za a ce an samu ciki? Ni ban shiryawa hakan ba shiyasa aka zubar da cikin. Kuma da take zancen na mayar da ita s*x machine, to dan me na aure ta?.

Mum ta buWe baki tana kallonsa jin da yadda yake magana, ta kalli Dad da shima shi yake kallo cikin tsananin takaici da mamaki. Dad ya ce,  Ashraf sakamakon ™aunar da na nuna maka kenan? Sakamakon yarda da amince maka da nayi na baka amanar ´ata kenan? Yanzu abinda zaka saka min dashi kenan ko?. Ka ajjiye min yarinya kana wahalar da ita shine daidai a wajan ka?. Ashraf ya ce,  Dad ni ban wahalar da ita, itace take wahalar da rayuwarta. Kuma ko yaushe cikin yi min zancen wancan banzan Wan daban take yi, ta kalle ni ta ce ta tsane ni shi take so ba dole raina ya Saci ba.

Narma ta sake kallonsa ta ce,  na tsane ka, bana sonka Omar nake so. Kuma Allah ya isa virginity Wina, Allah ya isa babyna da ka zubar min. Ka jira sai na yi shari a da kai!.

A firgice ya taso yazo inda take, ba zato ba tsammani suka ga ya tsinke ta da mari ya ce,  ko wacce irin shari a zaki yi dani baki isa na sake ki ba, ban gama amfanar jikinki ba, ki bari duk sanda na gama sai na& . Marin da ya sauka a fuskarsa ya hana shi ™arasawa. Ya juyo ya kalli Dad da yake wuci cikin Sacin rai ya sake marinsa. Kafin ya dawo daidai Mum ma ta mare shi a Waya Sangaren cikin tsananin tasafar zuciya.

Kallon su yake yi su duka biyun cikin mamakin da ya hana shi magana. Dad y ce,  Ashe baka da mutunci ban sani ba? Ashe baka da tarbiyya?. A gabana ka ke Waga hannu ka mari Narma? Har kana cewa baka gama amfani da jikinta ba?. Ashraf ya ce,  Dad Narma itace mara tarbiyya ba ni ba, bata girmaman ni a matsayina na mijinta, shiyasa raina yake Saci ko yaushe.

Mum ta kalle shi da dan ita ta kasa magana, takaici da ba™in ciki sun yi mata yawan da ta kasa buWe bakinta tayi magana. Narma ta ce,  ba yau ya fara mari na ba Dad ya saba, ya mayar dani kamar slive Winsa ko yaushe abinda yake so yake yi. Dad ya ce,  Tunda abin naka haka ne ka sake ta yanzu, auren ya ™are gabaWaya ai babu dole. Ashraf ya kawar da kai gefe ya ce,  ni bazan iya sakin ta ba, kuma babu wanda zai saka na sake ta.

Mum zata yi magana Dad ya hana ta ya kalli Narma ya ce,  Ina passport Winki?. Narma ta ce,  yana wajan shi. Ya kalle shi ya ce,  Wauko min passport Winta. Ashraf ya ce,  bazai yu na Wauko ba, haka kawai ku zo ku Wauke min mata ba, bazan iya Waukowa ba.

Dad ji yake kamar ya dinga dukan Ashraf har sai ya fitar masa da jini. Ya danne zuciyarsa ya ce,  Ashraf in baka Wauko min passport Win nan ba sai nayi reporting Winka a ™asar nan bisa cin zarafin ´ata da ka ke yi. Ya san Dad zai iya, kuma in hakan ya faru abin bazai yi kyau ba dan a ™asar America yake ba a nigeria ba, tsaf zasu Waure shi bayan tara da zasu saka ya biya. Hakan ya saka ya shiga ya Wauko ya mi™a masa har wayar Narma. Dad ya kalli Najwa da ta kasa magana ya ce,  Wauko abinda ki ka san nata ne ku zo mu wuce.

Ashraf yana ji yana gani aka haWa trolly bag Win Narma suka ri™e hannun ´arsu suka fita da ita. Da kallo ya bisu yana girgiza kai cikin takaici da ba™in ciki, dan yayi alwashin bazai sake ta ba sai ya gama morar surarta yadda yake so, sai ya gama lalata komai babu abinda zai rage mata wanda zata cigaba da bayyanawa har wasu mazan su shiga irin halin da ya shiga lokacin da suke soyayya, sai ya tabbatar da ya gama lalata komai nata sannan hankalinsa zai kwanta.KRB3P016
ArewaBooks@nanahaleema11.

Tunda suka koma hotel Win da suka sauka babu wanda ya iya cewa komai. Mum tana zaune kusa da Narma an haWa mata tea tana bata a baki, duk suna zaune kowa ya zuba mata ido cikin tausayi da soyayya. Sai da ta shanye tea Win sannan ta kalli Najwa ta ce,  kin Wauko maganinta?. Najwa ta amsa da eh ta bawa Mum maganin nata ta bata ta sha. A kafaWar Mum ta kwantar da ita tana shafa kanta a hankali.

Mum ta ce,  ki yi ha™uri Daughter, ba mu san rayuwar da ki ke yi a wajan Ashraf ba kenan, mun Wauka rayuwar soyayya ce ashe wahala yake baki. Ki yi ha™uri. Narma ta ce,  ai na ce muku bana sonsa tun farko amma ku ka ™i saurarena, aka aura min shi ba tare da yarda ta ba, aka turo ni nan ba tare da na amince ba. Ni gabaWaya ba a kyauta min ba, an lalata min rayuwa gabadaya Mum.

Dad ya ce,  ki yi ha™uri my love, bamu Wauka haka abin zai zama ba, mun turo ki nan saboda ki samu peace of mind ba mu Wauka haka lamarin zai lalace ba. Muna ganin Ashraf yana sonki shiyasa mu ka haWa ki dashi, a ganin mu zai baki fari mai yawa.

 Ashraf baya sona Dad, baya sona. Ya faWa min da kansa, satisfying lust Winsa kawai ya ke yi kaina. Ba sona yake yi ba, ya aure ni ne saboda ban bashi goyan bayan abinda yake so kafin ya aure ni ba shiyasa kawai.

Dad ya ri™e hannunta ya ce,  calm down, muna tare dake a yanzu babu abinda zai sake faruwa dake. Za a raba auren tunda haka abin ya zama. Narma ta mi™e zaune ta ce,  Da gaske zaka raba auren Dad?.
 Da gaske nake Narma, za a raba auren ko da baya so.
 Zaka bar ni na auri Faruk?. Dad ya kalli Mum da take kallonsa ta ri™o Narma jikinta ta ce,  Ki nutsu mu koma gida sai mu yi wannan maganar.
 Za ku yarda ya aure ni? I love him so much, da shi na aura bazai min haka ba, he loves me zai kula dani da rayuwata sosai.

Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce,  ki nutsu mu gama maganar nan, yanzu ke matar aure ce ki daina maganar Faruk, ki jira ya sake ki sai mu ga abinda za a yi. Kwanciya tayi jikin Mumta rufe ido a hankali har ta yi bacci.

Mum zare ta tayi daga jikinta kwantar da ita suka fito zuwa falo su ukun. Najwa ta ce,  Gaskiya Dad bai kamata a ™yale Ashraf ba, ya kamata a Wauki mataki a kan sa. Ka duba halin da ya saka ta a ciki. Mum ta ce,  ya zama dole ya sake ta, kuma ka kira mahaifinsa ka sanar da shi abinda ya aikata. Dad ya ce,  Tunda har mun zo mun Wauko ta duk magana ta ™are, zamu samu lokaci a nan dan ta huta tare da mu daga nan sai mu koma gida. In mun koma zan kira mahaifinsa domin ya saka ya sake ta.

Mum ta ce,  Hakan ya fi wallahi. Najwa ta ce,  Yaya Nabil yana ta faWa, ya ce da ya san haka ne sai ya biyo mu. Dad ya ce,  kar ku damu, ai komai ya ™are.

 Amma Dad ya batun Faruk Win? Tana sonsa sosai, zaka amince mata ta aure shi?. Mum ta ce,  kar na sake jin maganar nan a bakin ki, hauka ake yi an faWa miki ko wasan yara ake yi?. Dad ya ce,  Najwa auren ta da Tiger ba abu ne da zai yu ba, beside shi ya ma yi auren sa, bana so a sake dawo da maganar nan. Itama zata manta da batun komai zai wuce.

Mum ta ce,  duk ba shine ya jawo komai ba? Da bai yi mata asiri ya shiga rayuwarta ba ai da duk ba haka ba. Wajan Narma Mum ta koma dan gani take yi kamar wani abun zai same ta.

" " " " " " " "

Nayla da Omar haka suka cigaba da zama irin yadda suka saba, babu magana mai ™arfi ganin sa ma sai tayi sa a tunda in ta fita bata dawowa sai yamma shi kuma baya shigowa sai dare. A haka su Hajja suka dawo, da yake shigowar dare suka yi washe gari da Nayla ta tashi saga aiki kai tsaye gidan Hajjan ta wuce.

A nan ya tarar da su Mama Sa adatu sun zo barka da zuwa, ana ta ba™i a gidan ana yi mata barka da dawowa. A nan tayi zaman ta ita da Salma suna hira har dare sannan ta koma gida da tsarabar ta harda ta Omar ma Hajja ta bayar.

Da ta koma da Tk ta haWu shi ya shigar mata da motar ita kuma ta shiga cikin gidan da sallama. Abinda bata saba gani ba ta gani, shine a zaune a falo amma lissafi ya ke da alama kuma lissafin ya sha kansa sosai. Sallamar da ya amsa ma bai Wago ba lissafi yake bugawa da wayarsa yana sake duba littafin da take tunanin a ciki yake rubuta komai. ˜arasowa ta yi ta kalle shi ta ce,  Ina yini. Bai kalle ta ba ya ce,  lafiya. Daga nan ya Wauka zata ™yale shi ganin abinda yake yi sai bai sake cewa komai ba.

Nayla ta ce,  Na je gidan Hajja na yi mata barka da zuwa. Yayi mata banza bai ce komai ba, Nayla ta ce,  ga sa™o ta ce a baka.
 Bakya ganin abinda nake yi ne!? Lallai sai kin yi magana!? Ya faWa a faWace yana kallonta. Nayla da ta firgita a sanyaye ta ce,  yi ha™uri, Hajja ce ta ce na baka ta faWa tana ajjiye masa ledar ta tashi ta koma ciki.

Tsaki ya yi ko kallon ledar bai yi ba ya cigaba da abinda yake yi yana mita a zuciyarsa. Sai da ya gama ya lissafa ribar da aka samu daga fara aikin zuwa yanzu, da abubuwan da aka kashe, da wanda aka siya ya ga an samu riba fiye da tunaninsa. KuWin sun ninka sun sake ninkawa, domin kuwa tabbas sai ya fitar musu da zakka, babu abinda zai cewa Allah sai godiya domin kuwa lokaci kaWai ya kai inda bai yi tunanin zuwa ba.

 Ya kamata na samu Didi na ji abinda ya kamata ayi ya faWa a bayyane cikin tsananin jin daWi, ko a mafarki bai Wauka zai mallaki abinda ya mallaka yanzu ba. Shiyasa yake ™o™arin kyautatawa ma aikatansa ko yaushe, shiyasa suke son aiki dashi dan bayan albashi haka kawai zai yi musu kyauta. A bayyane ya sake cewa,  Zan tambaya naji kuWin sun kai tsahon lokacin da za a fitar da zakka. Kallon abinda ta ajjiye ya yi kamar bazai Wauka ba sai kuma ya Wauka bai buWe ba ya tashi ya shiga Waki zuciyarsa cike da farin ciki.

Bayan Kwana biyu.

Ranar ta kama rana asabar, Nayla tana gida babu aiki tana kwance a Waki ciwon kai ya dameta. Mai aikinta ce tayi mata komai har tea ita ta dafa mata sannan ta tafi tunda ba kwana take yi ba.

Bata san yana gidan ba har azahar ashe ranar bai fita ba yana cikin gida yana hutawa. Ta fito falo tana shan tea ta ganshi ya fito daga Waki suka haWa ido. Tunda ya yi mata tsawa ranar da ra dawo daga gidan Hajja basu sake haWuwa ba sai yanzu. Nayla ta ce,  Ina yini. A iya lallaSansa ya amsa, ba dan kallon sa take yi ba baza ta fahimci ya amsa ba.

Fita ya yi bakin gate, lokacin rana ta buWe sosai har sai da ya kare fuskarsa da hannunsa saboda ranar, hango Didi yayi a cikin adaidaita sahu a zaune tana jiransa, ya ™araso inda take ya ce,  wai baza ki shigo ba?. Didi ta ce,  sauri nake yi, bani key Win gidan mu

 Me zaki yi a ciki?. Didi ta ce,  YallaSai ne ya yi tafiya, ka san kuma yanayin unguwar ta mu bazan iya zama ni kaWai ba, shine ya ce na taho cikin gari in ya dawo sai na koma. Bani key Win na tafi na tsayar da mai mota. Ai su Bashir ba a nan suke kwana ba ko? Na ji kwnaaki ka ce min sun daina zama a gidan.

Wani irin kallo yake yi mata na ta ma raina masa hankali ya ce,  wai kina nufin a can zaki dinga kwana?. Didi ta ce,  eh mana.
Omar ya harare ta ya ce,  Meye amfanin nan da baza ki zo ba?. Didi ta wara ido da mamaki ta ce,  Omar ni fa Yayarka ce ba ™anwa ba, kawai sai nazo gidan ka da ka ke zaune da matarka na zauna? Haba wannan ai bai dace ba. Ka bani key Win naje na gide na zauna, in kuma baza ka bani ba na tafi gidan Hajja.

Ya girgiza kai cike da jin haushi jin amsar da ta bashi ya ce,  Oh! zaki iya zama a gidan Hajja, Hajjan da babu dangin uwa da uba amma baza ki iya zama a gidan da nake biyan kuWin hayarsa ba ko?. Dariya Didi ta yi tana tunanin wannan wacce irin Wabi a Omar yake da ita, wato bazai ce gidansa ba sai dai gidan da yake biya kuWin haya zai ce.

Didi ta ce,  Gaskiya bazan zauna ba, tunda muna da na mu gidan zan je can na zauna. Omar ya Waure fuska yana girgiza kai ya ce,  wallahi indai baki shiga gidan nan kin zauna ba bazan sake kwana a cikin sa ba har abada. Kin ji kuma na ce wallahi, babu wata halitta da ta taSa karya min rantsuwa a duniya. Kin san kuma zan iya yin abinda na ce, amma in kina ganin bazan iya ba ki tafi Didi ya faWa yana bar wajan.

Didi ta ce,  Innalillahi wa inna ilahir raji un! Wannan wanne irin yaro Allah ya haWa ni dashi?.

 Hajiya sauri nake yi ki sallame ni mai adaidiata sahun ya faWa yana kallonta. Didi ta ce,  yi ha™uri ta faWa tana Wauko kuWi ta bashi ta fito daga ciki ta rasa mafita.

Allah ya sani bata son kwana a gidan dan gani take yi zata takurawa Nayla ita kuma bata son faruwar hakan. Matsayin uwa take a wajansa, haka kawai sai ta shiga gidansa ta ce zata kwana bayan tana da inda zata iya kwana?. In kuma bata shiga ba tunda ya ce ya daina kwana a gidan wallahi ya daina, ta san halin kayanta in and out, ita kuma so take aurensa da Nayla ya daidaita, in bata shiga ba yadda ya rantse ya kenan?.

Ajiyar zuciya tayi ta Wauki ™aramar jakarta ta ™arasa bakin gate Win. Ashe yana tsaye daga ciki yana kallonta, ™iris yake jira ta tafi ya shiga ya tattaro kayansa dan bazata karya masa rantsuwa ba. Kafin ta ™arasa sai gani tayi ya buWe mata gate Win tare da karSar jakar hannunta dan cikin jikinta ya fito sosai.

Harararsa ta yi ta ce,  Wallahi ka cika rigima, ina ni ina zama a gidan nan don girman Allah? Wannan ™arfa-™arfa da me tayi kama?. Wato a nan ka ja tunga kana jiran tsammani ko?. Shi dai bai kula ta har cikin falon. Nayla tana tsaye a Inda take har lokacin tana goge dining glass Win.

Jin muryar Didi ya saka ta juyo ta ce,  Didi! sannu da zuwa ta faWa da fara a tana takowa tazo inda Didin take. Didi ta bi ta da kallo ta ce,  Nayla baki da lafiya ne?. Nayla ta yi murmushi ta ce,  Eh Didi, ciwon kai ne yake damuna sosai.
 Ga fuskarki nan har ta Wan kumbura kamar wacce ta yi kuka. To ki je asibiti mana wannan ciwon kai yan damun ki.
 Ranar Monday kafin na tafi aiki zan biya in sha Allah. Sannu da zuwa.

Didi ta ce,  Yauwa Nayla, Zauna kar jiri ya Wauke ki. Nayla ta zauna kusa da Didi ta ce,  Sannu da zuwa Didi. Didi ta amsa ta kalli Omar da yake tsaye ta ce,  Bata da lafiya shine baka faWa min ba?. Kallon Didin ya yi ba tare da tunanin komai ba ya ce,  ban sani ba.

Didi ta ce,  ta ya zaka sani tunda baka so ka sani ba?. Ta sake kallon Nayla da take murmushi ta ce,  Wai fa YallaSai ne ya yi tafiya zai yi kwana biyu baya cikin gari, shine nazo ya bani key Win gidan mu naje na zauna. Nayla ta Wan buWe ido ta ce,  ke kaWai a gidan? Meyasa baza ki zauna a nan ba?.

Didi ta kalli Omar da yake tsaye har lokacin, ta kalli Nayla ta ce,  Nayla Omar fa ™anina ne, ke ma ™anwata ce, ta ya ina matsayin uwa a wajan ku zan Wauko ™afa na zo gidan nan na ce zan kwana don Allah?.

Nayla tayi dariya ta ce,  Didi to meye a ciki? Mahaifiyar Mama tana kwana gidan mu na Kaduna kafin ta

Please Login or Register in order to submit comment