Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duniya ta ke. Rawar sanyi take yi sosai alamun zazaaSi, ya kalle ta sai ya mike da™yar ya fita ya shiga Wakinta ya Wauko blanket ya dawo ya rufa mata ya zauna a gefenta ya ri™e hannunta yana murzawa a hankali.

Zafin jikinta ya dame shi sosai, duk da shima haka nasa jikin yake amma ta ita yake yi ba ta kansa ba. Yana cize baki ya mi™e tsaye ya duba maganin da ya taSa siya na zazzaSi ya Wauko, fita ya yi ya Wauko ruwa ya dawo inda take ya tallafo kanta ya saka mata maganin a baki ya kafa mata robar ruwan amma sai yaga ruwan yana dawowa kamar yana bawa gawa ruwa.

Hankalin Omar ya tashi fiye da Wazu, a firgice yake cewa, "Jidda! Jidda!! Ki yi magana in kina jina, kina jina....? don Allah ki ce wani abu. Kar ki saka zuciyata ta buga mana, ki yi magana, ki yi magana naji don Allah, ki ce wani abu ko zan ji daWi!" Abinda yake faWa kenan cikin fitar hayyaci. Kiran sallar asuba da ya ji ya saka shi tsayawa cak yana mamakin gudun lokacin, inda yana da ™arfi da lafiya asibiti zai kai Nayla amma bazai iya ba, bazai iya fita a wannan hali ba. tsaf sai su yi hatsari.

Wayarsa ya jawo ya shiga number Didi yana kallo amma ya kasa kira, ajiyar zuciya ya yi, bashi da wata in ba Didin ba dole ita zai kira ta zo ta taimaka masa kar Nayla ta mutu ya shiga uku. Danna kiran ya yi ta gama ringing amma Didi bata Wauka ba, ya sake kira a karo na biyu nan ma bata Wauka ba, ya ajjiye wayar yana ji kamar ya yi ta dukan kansa saboda takaici da ba™in ciki.

In ya bar Nayja a haka ta mutu ya zai yi? Wanne hali zai shiga?. Ya juya ya kuma kallonta ya sauke ajiyar zuciya ya dafe kan da yake barazanar tarwatsewa. Yana ji aka tayar da sallar asuba amma bazai iya motsi ba, yana zaune har aka idar da sallar ya kasa motsawa daga wajan.

Ana idar da sallah kiran Didi ya shigo wayarsa, da hanzari ya Wauka ya ji muryarta a firgice tana cewa, "Omar lafiya? Me ya faru?." Bai ma ji me take cewa ba ya ce, "Didi ki zo, na rasa me zan yi, ki zo ki taimaka min. Jidda zata mutu, ki zo!" Abinda yake iya faWa kenan yana lumshe idanunsa.

Wayar faWuwa tayi a hannunsa ya sunkuyar da kai ya rasa abinda zai yi. Kallon Nayla ya yi da take yadda ya barta numfashin ma baya fita, ruwan da ya taru a idanunsa suka fara sauka tamkar hawaye, hawaye yake yi na ba™in ciki da takaicin kasa taimakonta da ya yi. Yana kallon ta a kwance, ita ba sumammiya ba ita ba wacce take hayyacinta ba, ya kasa yi mata abinda zata ji daWi zazaSin jikinta ya rabu da ita, ya kasa yi mata komai. Ya kasa sakawa ta dawo daidai, ya rasa abinda zai yi mata wanda zai sakata dawowa hankalinta.

Tunda yake a duniya bai taSa zubar da hawaye akan komai ba sai a yau, ya kasa ri™e hawayensa sai da suka sauka dan yana ganin komai laifinsa ne, shine yayi gaggawa ya kai kansa inda bai taSa zuwa ba, shine ya kai su inda basu taSa zuwa ba ba tare da yana da ilimi a kai abun ba, gashi gaggawa ta kai shi ga zubar da hawaye, ya kasa yi mata abinda zata iya ko da magana ne balle kuma ta iya tashi. Ya manta ma zai yi sallah, sai daga baya ya mi™e da™yar ya yi alwala ya dawo ya yi sallar a zaune dan bazai iya sallah a tsaye ba saboda jiri, yana idarwa ya koma inda take kwance, har lokacin numfashi ta yana sauka amma a hankali.

Kiran wayarsa ya ji ana yi bai iya Wauka ba har ta katse, aka sake kira bai Wauka ba, sai aka kira sau biyar sannan ya iya jan wayar da take kife a ™asa ya Wauka. A rikice Didi ta ce, "Omar gani a ™ofar gidan, ka zo ka buWe min." Runtse ido ya yi yana tunanin ta ya zai iya fita ya buWe gate? Ciwon da yake ji tunda yake a duniya bai taSa jin irinsa ba, ji yake kamar iska tana Waukarsa tana hujijjiga shi a sama in ya tashi tsaye, amma dole zai daure ko dan saboda ita.

Yana haWa hanya ya fita, yana fita compound Win gidan ya ji sanyi na ratsa ko ina na jikinsa, ya buWe gate Win Didi ta shigo a firgice mijinta yana jikin motarsa a tsaye shima hankalinsa a tashe. Didi ta ce, "Omar lafiya ka ke? Omar!" Ta faWa da ™arfi ganin yana ™o™arin zubewa a wajan. Da sauri AbdulHamid ya shigo ya ri™e shi yana cewa, "Subahanallah! Omar Bba ka da lafiya haka?."

Didi ya kalla da idanunsa da suka koma jajaye ya ce, "Didi, Jidda!." Da hanzari ta shiga ciki shi kuma AbdulHamid ya ri™o shi suka dawo falo ya zaunar da shi yana jera masa sannu. Didi Wakin Nayla ta shiga amma bata ganta ba, ta fito ta ce, "tana ina?." Da hannu ya nuna mata Wakinsa ta buWee ta shiga. Da sauri ta ™arasa inda Nayla take tana kiran sunanta amma ta ga kamar Nayla bata numfashi. Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Me yake damunsu haka? Nayla! Nayla!" Ta faWa tana jijjigata amma ita Nayla bata san tana yi ba.

A guje Didi ta fito ta ce, "YallaSai asibiti zamu je, dukkan su basu da lafiya." AbdulHamid ya ce, "To bara mu je mota dashi, ku fito tare da ita" ya faWa tana kallon Omar ya ce, "Omar daure ka tashi mu je asibiti, daure ka mi™e." Omar ya™i tashi saboda ya san dai Didi bazata iya fitowa da Nayla daga Waki ba, to ta ya za a tafi asibiti kenan?.

Didi kuwa da sauri ta dawo Wakin Nayla ta samu doguwar riga mai Wan kauri a kayanta, ta koma Wakin ta Wora mata a kan rigar jikinta ba tare da ta cire ba. Ta fito ta kalli mijinta ta ce, "kamar a sume fa Nayla ta ke, ta ya zamu fito da ita?." Omar yayi caraf ya ce, "zan iya."

AbdulHamid ya ce, "baza ka iya ba Omar, baka da lafiya kaima, ta ya zaka iya Wauko ta?." Omar yana jinsa amma baya tunani zai iya bari shi ya Wauketa, dan in dai ba shi Win ne ya Wauke ta ba to tabbas shi ne zai maye gurbinsa, saboda ya san aikin ya fi ™arfin Didi. Shi kuwa da hakan ta faru gwara ya Waukota koda suna tafiya suna kifawa ne ya amince da hakan.

Omar ya ce, "zan iya" ya faWa yana wuce shi ya shiga Wakin ya Wauko ta kamar yarinya, da™yar da siWin goshi ya iya fitowa falon, AbdulHamid ya ri™e shi, shi kuma yana ri™e da ita a haka aka fita yana tangaWi har motar mijin Didi.

Didi ta kalle shi ta ce, "Ina key Win gidan?." Cikin gidan kawai ya nuna mata ta shiga tana ta dube-dube amma bata gani ba, key Win motar Nayla ta gani kawai ta Wauko ta fito da sauri ta kulle gidan ta shiga gaban motar suka tafi asibiti a guje. Basu tsaya bi ta kan asibitin gwamnati ba, kai tsaye ™aramin private suka wuce dan abin na gaggawa ne ana kuma bu™atar hanzari da aikin gaggawa saboda a taimaka su dawo hankalinsu.KRB3P049

Duk su biyun kwantar da su aka yi, ko wanne an saka masa ruwa yana shiga jikinsa saboda yadda jikin na su ya yi laushi dole sai sun sha ruwa. Bayan an gama daidaita komai dukkan su sun samu bacci hankali Didi ya kwanta, ta kalli nurse Win ta fito daga Wakin ta ce, "Don Allah me ya same su haka?." Nurse Win ta ce, "Ni gaskiya ban je kanta ba, shi dai jikinsa ne ya yi weak sosai, sai zazzaSi mai zafi da ciwon kai, amma yanzu ya samu bacci."

Wata Likita ce ta le™o daga Wakin ta kalli Didi ta ce, "Sister ji mana." Didi ta ™arasa kusa da ita ta kalli Didi ta ce, "mata da miji ne?." Didi ta ce, "eh."
"Ya ku ke dasu?."
"˜anina ne uwa Waya uba Waya." Ta girgiza kai ta ce, "Sabon aure ne?." Didi ta ce, "eh to, sabon aure ne."

Dr ta ce, "Akwai abinda nake expecting ne shiyasa nake tambayarki, lokacin barina aiki ya yi amma saboda su na tsaya. Ko dai they had their first night ne? Ina nufin ko dai sun kusanci juna a karo na farko ne?." Didi ta kalli Dr gabanta yana faWuwa ta ce, "it might be." Dr ta ce, "let me check" ta faWa tana komawa ta bar Didi da tunani.

Kenan in hakan ne dalilin da ya saka Nayla suma kenan? Suma fa, har ya sumar da ita saboda wannan kawai?. Tausayin Nayla ya mamaye mata zuciya, ta koma inda take zaune ta zauna ta yi shiru ta rasa abinda zata ce.

Dr da tayi mata magana ta ga ta fito daga Wakin ta kira wata sun shiga tare basu ce mata komai ba. Sun jima kafin su fito ta kalli Didi da take zaune kusa da mijinta ta ce, "Sis zo ki ji." Ba musu Didi ta mi™e ta ™arasa inda take ta kalli Didi ta ce, "abinda na yi hasashe haka ne ya faru. Amma wannan ™ani na ki anya ba maganin ™arfin maza ya sha ba? Kin ga irin aikin da ya yiwa yarinyar nan kuwa?. Gashi kuma da alama ba ta shiga ko Wan ruwan zafin nan da ake taimakawa amare ba. Duk da dai shima bashi da lafiya sosai, amma ya kamata ace an taimaka mata."

Didi ta yi ajiyar zuciya, kunya duk ta bi ta rufe ganin AbdulHamid yana wajan kuma yana ji, duk da dai sun Wan yi nisa da inda yake amma ta san zai juyo dan ba a hankali take magana ba.

Nurse Win da take tsaye kusa da Dr ta ce, "Lamarin ya dangana ga Winki, amma ba wai sosai can ba, kuma kyau samu ta kwana a nan zuwa gobe ko jibi yadda za a kula da ita in ya so sai ta koma gida." Didi a sanyaye ta ce, "Shi kuma me ya kawo nasa ciwon?."

Dr ta ce, "Ana samun irin haka musamman ga saurayin da ya Wan kwana biyu bai yi aure ba kuma bai taSa sanin mace ba, su kan tsinci kansu a yanayi na zazzaSi da ciwon kai, ciwon gaSoSi da jiri saboda kasancewar su ba™i a wannan Sangare. Wannan shine ya jawo masa na sa ciwo, dan zazzaSi ya kama shi sosai har zafin jikinsa har ya fi nata. Shi ake kira da samartaka in ji manyan mu."

Didi ta girgiza kai cike da gamsuwa Dr ta ce, "in  sun warware ta koma gidan a Wan ™ara mata hutu na at least kwana biyar zuwa sati Waya haka." Didi ta girgiza kai cikin gamsuwa ta ce, "Yanzu tana Lafiya?."

"Lafiya take, ta yi bacci. Shima kuma rashin sabo ne da zarar ya farka zai iya dawowa daidai sai dai rashin ™arfin jikin kawai, itace zata Wan yi jinya kaWan." Didi ta ce, "na gode sosai." Dr ta ce, "babu komai aikina ne" ta faWa suna wucewa suka fita daga wajan.

Didi ta dawo a sanyaye ta zauna cikin kunyar mijinta kamar ita ce ta aikata abinda aka ce. Tunanin halin da aka faWa mata suke take yi, Allah ya sani tunda Nayla ta dawo gidan Omar take tunanin wahalar da zata sha a hannunsa, haka kawai take ji a jikinta Nayla zata sha matu™ar wahala a hannunsa dan Omar bai yi kama da ragon namiji ba. Babban abinda ya saka ta ji daWi a zuciyarta tunawa da bayanin likita, godiya take ga Allah ya kasance Omar bai taSa aikata zina ba, ya gujewa saSawa Allah ya ri™e kansa har sai da aka gama faWan zamansa da Nayla har ya amince da ita ya fara sanin ´a mace a kanta. Hakan ya yi mata daWi sosai, dan yadda zamani ya lalace samarin yanzu kaWan ne basu taSa aikata zina ba, an mayar da ita ado kamar ba ita Allah ya ce kar a kusanceta ba. Amma tausayin Nayla ya gama mamaye mata zuciya, daman ko shakka bata yi akan Nayla, ta san ita Wiyar ™warai ce da ta samu tarbiyya mai kyau. Ajiyar zuciya tayi, a lokacin gari ya yi haske sosai ma'aikata na shigowa asibitin wanda suka kwana kuma duk sun tafi.

AbdulHamid ya kalle ta ya ce, "ko zan mayar dake gida ne kin bar Marmerh a hannun Umma, in ta farka ya za a yi da ita?." Didi ta ce, "to in na tafi waye zai kula dasu gabaWaya? Da ace ma ya farka sai na tafi, amma bai farka ba shima bacci yake yi."
"To yanzu haka za a bar jaririya a gida ba tare da mahaifiyarta ba? Ai sai da na ce ki taho da ita ko?."
"Ban Wauka zamu jima haka ba, bara mu gani zuwa anjima in bai farka ba sai mu je ka kaini na dawo anjima." Bai ce mata komai ba ya yi shiru itama ta yi shiru cikin tausayin Nayla mai yawan gaske.

Ganin ™arfe takwas na safe tayi Didi ta tashi ta shiga Wakin ta same su dukkan su suna bacci dan Wakin mai gado biyu ne. Ajiyar zuciya tayi ta ™arasa inda Nayla take ta dafa goshin ta taji babu zazzaSi a jikinta, ta dawo wajan Omar ta tsaya yana kallonsa.

Dariya ce ta kubce mata ba tare da ta san dallin yinta ba, haka kawai ya bata dariya har sai da ta dara ta dafa goshinsa, a bayyane ta ce, "Bana tunanin Omar ya taSa kwanciya asibiti, kai bai taSa ba ma, amma gashi yau ya kwanta. Alhaji Omar manya, komai na su na manya ne" ta faWa tana dariyar da bata san dalilin ta ba ta fita daga Wakin.

Kallon AbdulHamid tayi tana murmushi ta ce, "Ka yi ha™uri YallaSai, mu je ko?." Ya kalle ta ya ce, "da wa ki ka barsu?."
"Zan dawo anjima sai na taho da Marmerh Win."
"Bai kamata ba, ya kamata ko gidan Hajja ki yi waya yarinyar nan ™awarta ta zo."
"Ka san abinda ya faru na san ka ji me suka ce, bana son kiran mutane azo ana tambayar me ya same su, hakan babu daWi kamar fallasa sirrinsu ne."

AbdulHamid ya ce, "lalura ce ai ba wani abun damuwa ba, babu wanda ya wuce ™addara dan an sani ai ba komai bane. Haramci suka aikata ko me?." Didi ta ce, "mu je dai kawai, ance ai zasu jima suna baccin." Bai ce mata komai ba suka fita daga wajan tare.

Didi koda ta koma a gaggauce ta yi wanka ta yi girki mai sau™i da shayi da sauran abinda ta san zasu bu™ata. Bata fi awa biyu da komawa ba ta dawo ita da Umma Saroot, dan itama hankalinta bai kwanta ba dan Didin bata ce mata ga abinda ya faru ba ta ce kawai basu da lafiya. Har lokacin da suka dawo dukkansu bacci suke yi, suka basu waje suka dawo wajen Wakin suka zauna akan kujera.

Omar sai ™arfe biyu na rana ya buWe ido yana kallon Wakin yana so ya gane a inda yake a kwance. Mi™ewa zaune ya yi cikin rashin ™wari amma ya ji daWin jikinsa zazzaSin ya sauka sai dai rashin ™arfin jiki da bashi da ita. Kallon gefensa ya yi ya ganta a kwance idanunta a rufe da alama bacci take yi.

Sakkowa ya yi daga kan gadon ya mi™e tsaye a hankali yana yamutsa fuska, sai yanzu ya lura a asibiti suke ya Wan ja tsaki kaWan, a rayuwarsa bai taSa kwanciya a asibiti ma amma saboda tonan asiri Didi ta kama ta kawo shi asibiti. ˜arasawa ya yi wajan Nayla ya dafa kanta ya ji babu zafi a jikinta gabaWaya, ya taSa wuyanta nan ma babu zafi ko kaWan. Kanta ya shafa da gashin ta yake baje a kan gadon yana kallon fuskarta.

Kiss ya yi mata a goshi yana shafa fuskarta yana ganin yadda take a kumbure har lokacin, ya sauke ajiyar zuciya yana kallon ta. BuWe Wakin aka yi ya kalli wacce ta shigo, ganin Didi ce sai ya Wan yi tsaki ya ce, "Wai daman asibiti mu ka zo? Ni na ce miki asibiti zaki kawo mu?."

Didi ta ce, "ikon Allah, kai ka tashi daga ciwon ma baza ka daina masifa ba? Da ba mu zo asibitin ba ya ka ke so nayi da ku gabaWaya?." Šauke kai ya yi daga kallonta a lokacin Umma Saroot ta shigo jin maganar Omar.

HaWa ido suka yi da ita Marmerh na hannunta ta ce, "Omar ya jiki?." Ransa ya ji ya Saci matu™a, ya kalli Didi ya girgiza kai kawai bai ce komai ba amma haushinta yake ji, daga kiranta dan ta taimakawa Nayla sai kawai ta yi masa gayya? Ya tsani rashin sirri a rayuwarsa, yana girmama sirri sosai a rayuwa, wannan dalilin ya saka bai taSa tunanin aikata zina ba, saboda gani yake duk yarinyar da ya kwana da ita ba tare da aure ba kamar ™arshen rashin sirri kenan. Shiyasa ko sha'awar auren mata biyu ba ya yi, gani yake in yana raba kansa ga mata biyu kamar babu sirri a ciki. Amma daga kiran Didi ta taimaka masa ta kama ta yi masa gayya harda zuwa asibitu. Kallon Didi ya yi ganin tana kallonsa alamun ya amsawa Umma sai ya Wan yi ™aramin tsaki ya ce, "lafiya...." Kafin ta amsa ya kalli Didi ya ce, "Ya jikinta?."

Didi ta ce, "har yanzu ita bata farka ba." Šan dafe kai ya yi jin yana sara masa Didi ta ce, "ka zauna ka daina tsayawa, zata farka itama in sha Allah." Zama yayi akan farar kujerar da take gaban gadon da Nayla ta ke, ya ri™e hannunta ya kulle ido bai ce komai ba. Didi ta ce, "bara na faWawa likitan ka farka, daman sun ce in ka farka na sanar da su."

Fita Didi ta yi ba jimawa ta dawo ita kaWa,  jim kaWan sai ga likita namiji ya shigo ya kalli Omar ya ce, "Sannu ya jiki?." Omar ya Waga kai kawai bai ce komai ba. Likitan ya ce, "Abinda ya kamata ka yi yanzu shine; ka samu ka yi wanka, ka ci abinci, ka huta zaka fi jin daWin jikinka." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ita fa?." Likitan ya kalle shi ya ce, "itama muna jiran ta farka, in ta farka sai mu san abinda ya kamata mu yi."

Omar ya yi shiru bai ce komai ba likitan ya matsa kusa da Nayla yana duba ruwan da saka mata dan likitan da ta karSe su tayi masa bayanin komai kafin ta tafi.

Omar kallonsa yake yi ta ™asan ido yana jin kishi na mamaye masa zuciya, gabaWaya haushin Didi yake ji, ko meye na kawo su asibiti oho, haka kawai yanzu ga wani banza kusa da matarsa har yana maganar wai zata samu sau™i. Tsakin da ya yi a bayyane ya saka Didi ta kalle shi a lokacin likitan ya fita daga Wakin.KRB03P50

Bayan fitar likitan Didi ta bishi da kallo tana Soye dariyarta ta ce, "ko zaka kira Bashir ya zo ku tafi gida ka je ka yi wanka? Ko kuma zaka fara cin abinci?, gashi na kawo." Kallon ta ya yi baice komai ba.  Didi ta ce, "ko tea ne ka sha ka ga yanayinka har yanzu bai dawo normal ba, ga toothpaste na tawo maka dashi na san zaka ce baza ka ci abinci ba saboda baka wanke baki ba, gashi don Allah ka wanke ka sha koda tea ne in yaso sai na kira Bashir ya zo ya kai ka gida, zuwa anjima sai ka dawo lokacin ta farka."

"Kawai sai na tafi na barta a nan a kwance?" Ya faWa muryarsa a can ™asa dan kana ji ka san bashi da lafiya kamar mai mura.

Didi ta ce, "ai ni ina nan, kuma ba jimawa zaka yi ba" ta faWa tana Wauko kayan wanke bakin ta mi™a masa ta ce, "don Allah ka tashi." Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Nayla, maganganunta na daren jiya suna amsa kuwa a kunnensa. KarSar abin hannun Didin ya yi amma bai mi™e ba Didi ta ce, "ga banWakin nan" ta faWa tana nuna masa ™ofa nan ma bai kalle ta ba.

Sai da ya gaji da zaman dan kansa ya tashi ya shiga ya wanke bakin ya fito, ta bashi tea Win da ta haWa masa ya karSa yana sha yana kallon Nayla. Rabin tea Win ya sha ya ajjiye Didi ta ce, "Ga Bashir Win ya zo, ka zo ku je."
"Kar ya shigo min nan."
"Allah ya ba ka ha™uri, na ce ya jiraka a waje." Banza ya yi mata kamar ba zai tashi ba yana kallon Nayla da take kwance tana bacci a hankali.

Ya kwashe sama da mintina goma sannan ya mi™e Didi ta ajjiye masa takalmi ta ce, "ga shi nan." Bai musa ba ya saka ya fita yana takawa da™yar. Umma Saroot ta murmusa ta ce, "Omar manya." Dariya Didi tayi kawai bata ce komai ba suka cigaba da zama.

     A hankali Nayla ta buWe ido tana kallon Wakin kafin ta ware gabaWaya, zafin da ta ji jikinta ya saka ta yamutsa fuska ta ce, "wash!." Duk da muryarta tayi ™asa haka bai hana Didi ji ba, ta taso da sauri ta ce, "Nayla kin farka? Sannu." Didi ta ri™e hannun Nayla ta ce, "Nayla sannu, ya jikin na ki?." Jin muryar Didi ya saka ta kalle ta ta ri™e hannun Didi amma ta kasa magana.

Didi ta ce, "sannu, bara na kiira likita" ta faWa tana sakin hannunta ta fita da sauri. Ba jimawa suka dawo tare da wata midwife babbar mace ta ™araso kusa da Nayla ta ce, "Sannu, me yake damunki yanzu?." Nayla ta nuna kanta midwife Win ta sake cewa, "bayan shi fa?."

Da™yar Nayla ta ce, "Ina jin zafi sosai" ta faWa tana runtse ido. Midwife Win ta kalle Didi ta ce, "Ku Wan bani guri na duba ta." Ba musu suka fita, ta saka safar hannu ta duba Nayla ta zare safar ta ce, "Ki yi ha™uri, an yi miki Winki ne, zaki dinga jin wannan zafin amma in kina tsarki ruwan zafi a hankali zai ware, yanzu ki tashi ki ci abinci ki samu ki yi wanka."

Nayla hawaye ya sakko mata dan ba ™aramin zafi take ji ba, Allah ya taimaka babu zazzaSin sai nauyin da kanta ya yi mata. Midwife Win ta kira Didi ta shigo ta ce, "kina ji, kamata ya yi kawai ku tafi da ita gida, in aka je gida zata fi samu ta shiga cikin ruwan zafi a nan kin ga babu damar hakan. Duk da ba a son shiga ruwan zafin in an yi Winki yanzu, an fi so ayi tsarki da ruwan ba a shiga cikinsa a zauna ba, amma saboda yanayin ciwon da ta Wan ji da kumburi zata iya shiga, amma ba mai zafi sosai ba."

Didi ta ce, "amma ciwon kan fa?."
"Duk zafin ciwon ne ya kawo ciwon kan, da zarar raWaWin da yake mata ya Wan ragu ciwon kan ma zai daina ciwo. Yanzu bara na rubuta magani ku siya sai ku wuce gida ku je ta shigan ruwa mai Wumi ba mai zafi ba, tayi wanka ta ci abinci ta sha magani, in sha Allah zata samu sau™i."

Didi ta ce, "To na gode." Midwife Win ta ce, "sannan a faWawa mijin nata a bata lokaci ta warke gabaWaya, in ba haka ba za a fama ciwon, a bata kamar sati Waya zuwa kwana goma haka. Sannan ya kasance tana shiga warm water, ba mai zafi sosai ba irin Wan daidai kamar yadda na faWa a farko. Ko bata shiga ciki ba ta yi tsarki dashi."

Didi ta ce, "in sha Allah."
"Yauwa, ki jira na kawo miki" ta faWa tana fita Didi ta koma kusa da Nayla ta ri™e hannunta. Cikin tausayi ta ce, "Sannu Nayla." Hawaye Nayla ta share bata amsa ba ta yi shiru kawai.

Didi waya ta Wauka

Please Login or Register in order to submit comment