Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta har jini ya dinga zuba, sai abin yayi mata yawa.

"Dan kinga ina sakar miki fuska shine raini zai shigo ko? In ba dan kin samu dama ba har kin isa ki bar gidan nan ba tare da na sani ba?. Kuma dan tsabar rashin hankali ki hau abin hawa na haya ki bar gidan nan ba tare da nace ki je ba. Yaushe ki ka raina ni haka?." Bakinta yana rawa tana kallonsa ganin ya canja mata gabaWaya, soyayya da tausayin da take gani a idanunsa yanzu duk ya gushe. ˜are masa kallo take yi tana tabbatar da wannan ba Rouhii ta bane, Omar Tiger ne na gidan Didi. Ganin ta™i magana ya saka ya ce, "ba magana nake miki ba!."

"Ni ban....rai....na.....ka......ba" ta faWa a rarrabe tana kallonsa
"Iskanci ne kenan? Iskanci ne ya saka ki ka fita daga gidan nan ba tare da izinina ba ko?."
"Na yi maka....text..." ta sake faWa murya na rawa.

"Da ki ka yi min text na baki amsa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "raina ni ki ka yi kenan?." Ta fashe da kukan da yake cin ranta ta ce, "A'aaaaaa!" Ta ja kalmar da ™arfi tana kuka mai sauti.

Ya girgiza kai yana nuna ta da yatsa cikin jin haushin ciwon da aka ji mata ya ce, "in kika sake wannan gangancin mai raba ni dake sai Allah, wallahi duk ranar da ki ka kuma aikata wannan ganganganci sai na saSa miki kammani ta yadda babu wanda zai iya gane ki." Ya bita da harara sannan ya ce, "ki wuce ki Wauki abinci ki ci." A zabure ta nufi inda ya nuna mata ta Wauki robar abincin da ya yi order daga Leemars_delicious tana ci tana kuka. Yana tsaye a kanta dole ta dinga tura abincin ba dan tana jin daWi ba, ya bi ciwon hannunta da kallo tausayinta yana sake shiga jikinsa. Bai nuna mata ba, sai da ta ci rabi sannan ya sake jan tsaki ya bar wajan.

Yana barin wajan ta Wora hannu a kai ta fashe da kuka ta ce, "Na shiga uku ni Nayla, na auri Wan daba!" Ta faWa cikin fitar hayyaci.KRB3P073
Nanahaleema.


      Nayla bata san lokacin da ta Wauka a wajan ba ta ji an taSa ta, wata irin zabura tayi ta mi™e sai taji an ri™e kafaWarta Didi ta ce, "Nayla ni ce, nutsu." Nayla da take a gigice ta ce, "Didi!."
"Na'am Nayla, ki nutsu. Kar ki fama ciwon hannun ki." FaWawa jikin Didi tayi ta rungumeta tana sake faahewa da kuka.

Cikin tausayinta Didi take shafa bayanta ta ce, "Ki daina kuka Nayla, ki nutsu kin ji?.." cikin kuka ta ce, "Didi jini ne a jikinsa, da daddare aka zo aka dinga buga gidan nan ana cewa in ya isa ya fito" ta Wago daga jikin Didi ta ce, "Shine....shine.....ya Wauki wu™a ya fita. Ina zaune ya dawo jikinsa duk jini, Didi jini ne a jikinsa da alamun ya yi faWa da wani. Tsoro nake ji Didi, ki Wauke ni daga gidan nan, tsoronsa nake ji. GabaWaya ya canja, baya jin tausayina, sai faWa yake yi min, har ya Waga hannu zai mare ni" ta faWa tana sake komawa jikin Didi tana kuka.

A sanyaye Didi ta ce, "Ya isa, ki nutsu ki daina kuka. Kinga baki jima da dawowa daga asibiti ba." Zaunar da ita Didi tayi ta bata ruwa ta sha tana ri™e da hannunta tana kallon ciwon da aka Winke. Sai da ta nutsu sannan ta ce, "ki yi ha™uri, ki dawo hankalinki." Nayla ta ce, "da naje gidan ki shine aka ™wace min waya, aka ji min ciwo a hannuna."
"Ki yi ha™uri, ki daina kuka" ta faWa tana dafa kafaWarta cikin rarrashi. Nayla ta koma sauke ajiyar zuciya zuciyarta tana bugawa sosai.

"Didi!" Omar ya furta cikin dashewar yana shigowa falon. Wani irin tsalle Nayla tayi ta faWa jikin Didi ta ™an™ame ta. Omar ya bita da kallon takaici, ganin yadda take rawar jiki in ta ganshi kamar ta ga abun tsoro yana bashi haushi sosai, ita bata san haushinta yake ji ba take sake tsiro da abinda take tunzura shi. Ya tako ya finciko hannunta mai lafiya, ya rabata daga jikin Didi yana girgiza ta ya ce, "Ke ni Dodo ne? Meye a jikina da yake baki tsoro!" Ya faWa yana jijjigata. Luuuu Nayla ta tafi ta kife a ™irjinsa, ya Wago ta a gigice yana bubbuga fuskarta ya ce, "Jidda!."

Didi cikin faWa da fusata akam halinsa ta ce, "ka sumar da ita hankalin ka ya kwanta. Wai me yake damun ka ne? Ciwo aka jiwa yarinyar nan fa, wannan faWan da ka ke yi mata na meye?." Bai kula Didi ba hankalinsa yana kan Nayla, ya kwantar da ita a kan kujera ya Wauko ruwa aka yayyafa mata. Ya kalli Didi a sanyaye ya ce, "Didi ta suma fa, mu je asibiti."
"Ba dole ta suma ba, wannan Waga mata murya da ka ke yi kamar ba matar ka ba. Ka san ba lafiya ce da ita ba, ka duba ciwon hannunta mana. Sai ihu ka ke mata kamar ba kai ba." Tsaki Didi tayi ta ™arbi ruwan hannunsa ta sake shafawa Nayla a fuska. Nayla ta ja numfashi a hankali, a hankali ta buWe ido tana kallon Didi.

Didi ta ri™e hannunta ta ce, "Ki nutsu Nayla, ina tare dake." A hankali take jan numfashi tana kwance a jikin Didi. Ya bita da kallo yana sauke numfashi cikin yanayin da yake nu™ur™usar zuciyarsa. Tausayinta yake ji sosai, amma haushin ta fita bai sani ba har tsautsayi ya same ta ya danne tausayin, gani yake da bata fita ba da hakan bai faru ba.

Shiru suka yi babu mai magana, Didi tana shafa kan Nayla a hankali, Omar ya jawo stand fan ya kunna mata iska tana kaWata. Sun kwashe mintina talatin a haka har bacci ya kwashe Nayla.

Sai da baccin nata ya yi nisa sannan Didi ta zame jikinta ta saka mata pillow, ta ri™e hannunsa suka dawo babban falon ta bishi da kallo ta ce, "Omar faWa ka yi shekaran jiya? Jinin wa take magana ta gani a jikinka?." Omar ya Wan yi tsaki ya ce, "ni ban yi faWa da kowa ba."
"To jinin wa ta gani a jikinka? Meyasa ka Wauki wu™a ka fita? Me wu™a take yi a gidan nan Omar?. Sannan waye ya jiwa Nayla wannan ciwon? Ya akayi waWannan abubuwan suka faru?" Ta faWa a sanyaye tana kallon sa.

Ya Waga mata hannu ya ce, "Kinga Didi, kar ki sake tunzura zuciyata na aikata abinda zan yi dana sani, ki ™yale ni naji da abinda yake raina."
"Bazan ™yaleka ba wallahi. Wanne irin faWa kayi da har matarka ta firgita da kai haka Omar? Meyasa ka ke son dawo da abinda ya wuce? Meyasa ka ke son lalata hanyar da aka jima ana gyaranta sai yanzu gyaran ya kammala?. Omar meyasa zaka biyewa zuciya?."

"Mtsww! Na faWa miki ba faWa nayi ba, ni ban yi faWa da kowa ba, ki yarda mana!" Ya faWa cikin masifa yana kallon ta. Didi ta ce, "me ya kawo jini jikinka in ba faWa kayi ba? Me ka yi da wu™a Omar?."

"To Didi faWan nayi, nayi faWan sai me?. Har gida aka zo ana yi min wula™anci, ni ake Wagawa murya har ana cewa in ban fito ba naji tsoro, ni ake cewa in ban fito ba na ja da baya. Bana taSa ja baya, bana taSa jin tsoron ko wacce halitta a duniyar nan!. Tunda da salon da suka dawo kenan mu je zuwa, ina nan yadda nake ban canja ba!. Tunda suka yi kuskuren taSa lafiyar matata babu wanda zan bari, zasu san ja da baya ba tsoro bane" Sai ya yi ™asa da murya ya ce, "Ko kura ta rame ta wuce rainin karnuka wallahi! Akan a taSa min ku zan iya salwantar da rayuwar ko waye!."

Didi ta fara hawaye ganin Omar Win shekarun baya yana ™o™arin dawowa, dan har maganarsa ta canja ta koma ta Omar Tiger da ta Wauka ya jima da mutuwa, sai gashi ya dawo yana tsaye a gabanta. Kafin ta yi magana ya ce, "Jidda suka tura a kashe, Jidda suka yi ™o™arin kashewa shine silar ciwon hannunta. Tunda aka taSa min lafiyar matata har ta zubar da jini babu wanda zan ™yale wallahi!."

Didi cikin kuka ta ce, "Omar ka rufa mana asiri, don Allah ka yi ha™uri kar ka koma rayuwar da ka bari don girman Allah!" Ta faWa cikin kuka mai sauti. Ya bita da kallo kafin ya ja tsaki ya ce, "kina nufin na bar wanda suka taSa min Jidda kenan? Sun yiwa banza ko Didi..?" Ya yi ™wafa yana girgiza kai yana binta da kallo kafin ya ce, "kin cika min kunne, bana son kuka" ya faWa yana bata waje.

Didi ta zube a wajan tayi kuka son ranta, ba kowa ne yake bata tausayi ba sai Nayla, bata san hawa da sauka ba an fara ™o™arin kashe ta a karo na biyu. Sai da ta gaji da kukan sannan ta koma wajan Nayla taga har lokacin bacci take yi. Ta kira mijinta a waya suka wuce gida dan ta san bazai saurareta a yanzu ba, zuciyarta cike da tsoro da fargaba dawowar Wabi'ar Omar.

Shima da ya koma wajan Nayla ya koma, ya zauna a gefenta ya Wora kanta a cinyarsa yana shafa kanta. Hannunta mai ciwon ya kalla yan jin wani irin ™unci a zuciyarsa, ji yake kamar Nayla bata dace da aurensa, tunda gashi ta silarsa ana neman rayuwarta a karo na biyu. Ya jima a haka a zaune kafin ya Wauke ta ya kai ta Waki ya kwantar da ita shima ya kwanta yana kallon ta. Washe gari ma haka Nayla ta farka da tsoronsa, shi kuwa baya ce mata komai dan Sacin ran da yake ji bai ragu ba.

Tunda suka gaisa ya duba hannunta ya tabbatar taci abinci tasha magani sai ya share ya cigaba da harkokinsa har ya bar gidan. Allah ya taimake ta Didi ta dawo gidan suka yini tare sai zanan ya yi mata daWi sosai.

Bai dawo ba sai dare, ya shigo da sallama dashi da mijin Didi suka fito falon. Didi ta amsa tana binsa da kallo ya zauna yana kallon Nayla da tayi la™was a jikin Didi. Didi ta bishi da kallo sai kawai ta fashe da kuka, ™aramin tsaki ya yi ya ce, "to meye na kukan?."

Didi ta ce, "Omar wu™a ka Wauka fa."
"FaWa min a inda kwana da makami ya zama haram, ki faWa min inda Waukar wu™a dan kare kai ya zama babban laifi Didi." Didi ta goge ido ya ce, "Don girman Allah Omar kar ka koma waccan rayuwar, Allah ya yi maka komai a rayuwa, ya azurta ka da mace kamar Nayla, Allah bai duba laifukan da kayi a baya ba ya haWa maka da sana'ar da ka ke ganin buWi a rayuwarka, ya haWa maka da kyautar ´a kamar Marmerh, meyasa zaka butulcewa wannan ni'imar da ya yi maka Omar? Meyasa zaka koma rayuwar da babu komai a cikinta dai ™azanta?."

Ya ja numfashi ya ce, "ni ban koma waccan rayuwar ba. Abinda ki ke tunani ba haka ba ne." Didi ta yi shiru tana kuka, jin kukanta yake har zuciyarsa hakan ya saka ya ce, "Wu™ar da na Wauka na fita ban yi amfani da ita ba, ´an sanda sun kama Wal™iya dashi da yaransa, kafin su bar ™ofar gidan nan ne suka yanki wani yaro da ya biyo su Bashir suka fito. Jinin da aka ce miki an gani jinin yaron ne dana ri™e shi kafin su kai shi asibiti, bayan wannan ni ban yi komai ba."

Bata daina kuka ba ta ce, "Omar don Allah!" Ya katse ta ya ce, "kar yi min magiya, na rantse da Allah in hukuma bata hukunta su ba sai na Wauki mataki a hannuna, wallahi Omar Win da bakya so ya dawo sai na dawo sa ™arfinsa Didi. Bazan Wauki raini da wula™anci ba, ke kin san halina, babu halittar da zan Wagawa ™afa" Ya nuna Nayla ya ce, "™o™arin kashe ta suka yi, da basu samu dama ba kalli yadda suka ji mata ciwo har sai da aka yi mata Winki. Sai da ta kwana ta yini a asibiti saboda su, ki duba yadda take a firgice babu nutsuwa saboda abinda ya faru. Wallahi tunda suka yi gangancin taSa min mata bazan bar maganar nan ba."

Didi ta sauke ajiyar zuciya tana kallon hannun Nayla ta kalle shi ta ce, "waye shi wanda ya zo Win?." Omar ya Wora ™afa kan Waya ya ce, "wani matsoraci ne, tsohuwar adawa ce, tsohuwar gaba ce, tsohuwar ta™un sa™a ce. Ya kwana biyu yana prison, yana fitowa kuma ni ya tunkaro kamar yadda ya faru cikin azumi. Shi ya yi nasara tunda ya saka an jiwa Jidda ciwo, sannan ya cutar da mutum Waya a Sangarena." Ya girgiza kai ya ce, "akwai irinsu da yawa, ni na san akwai irinsu masu jiran sa a a kaina" ya faWa yana girgiza kai yana tuna rayuwar baya.

AbdulHamid ya ce, "ba sai a kai shi ga hukuma ba? Ko prison Win ne ba sai a sake mayar dashi ba?." Omar ya kalli AbdulHamid ya ce, "Yana da iyayen gida da yawa, kamar yadda a baya nake gagarar zaman prison shima haka. Baza su bari ya sake komawa ba a yanzu. Shiyasa na faWawa Didi, in hukuma bata Wauki mataki ba ni zan Wauka" ya faWa yana nuna kansa.

AbdulHamid ya ce, "Ka yi ha™uri kar ka koma waccan rayuwar Omar, mu jira mu gani in za a Wauki matakin." Bai ce komai ba ya kalli Nayla da take lafee a jikin Didi ya Wauke kai. Ya sauke numfashi ya ce, "Kar ma hukuma ta Wauki matakin, tunda har suka taSa min matata...." Sai bai ™arasa ba yana girgiza kai cikin ™uncin zuciya. Nasiha suka dinga yi masa akan komai zai faru kar ya koma rayuwar baya yana jin su bai tanka ba.

Omar ya kalli AbdulHamid ya ce, "Ka kular min da Yayata, in ba su samu dama a kaina ba kanta zasu dawo. Kana gani abinda suka yiwa Jidda, da basu samu dama a kaina ba sun citar da ita. Da Didi, da Marmerh, da Jidda, da kai kune kaWai dangina, zasu iya huce haushinsu a kanku. Ka kula da motsinta, nan kusa kar ka bari tana fita ita kaWai har sai an warware komai." AbdulHamid ya ce, "in sha Allah babu abinda zai faru, ka kwantar da hankalinka, tunda muna addu'a babu abinda zai same mu. Addu'ar ce ta kuSutar da Nayla har abin ya tsaya a haka, in sha Allah babu abinda zai faru."

Didi a sanyaye ta ce, "Nidai ko kaina suka saka a gabas suka yanka don Allah Omar kar koma ruwa ka Wauki mataki a hannunka. Šaukar matakin shine bazai yi min daWi ba har a cikin kabarina." Ya bita da kallo kafin ya girgiza kai ya ce, "in nace miki kamar kina shan ™waya sai ki ga kamar wasa nake yi. To akwai halittar da ta isa ta saka kanki a gabas ta yanka na ™yaleta? Ai wallahi bisa ganganci aka sake ™o™arin hakan a kanun labaran na ranar sunan Omar ne zai fara fitowa. Ki daina wannan mafarkin. Hannun Jidda ma da suka jiwa ciwo sai sun biya bashin hakan wallahi" ya faWa yana kawar da kai.

Ya girgiza kai ya ce, "Da ke, da Jidda, da marmerh, da mijinki, da su Bashir babu wanda ya isa ya taSa ku na tsaya ina kallonsa. Ai ba ruwa zan koma ba Didi, cikin kogi zan faWa dan wallahi abinda nayi a baya ba komai bane akan abinda zan yi. Ke dai Allah ya kiyaye kawai, amma ko....hmmm!" Ya faWa yana girgiza kai.

Didi ta ce, "Allah zai tsare mu, babu abinda zai same mu in sha Allah. Ita Naylan Allah ya tsare ta, tunda gata a zaune a tare da mu." Ya bita da kallo ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai faru." Ta yi ajiyar zuciyar ta kalli Nayla da bata cewa komai.

Ta kalle shi ta ce, "To Omar ka nemi sulhu da wal™iyar kawai a huta mana. Ka duba abinda suka yi ™o™arin yi akan Nayla, in na nemi sulhu shikenan an huta." ˜are mata kallo yake yi kamar mai son gano wani abu a tare da, kafin ya Wan yi murmushi ya ce, "Omar baya neman sulhu, sai dai a nemi sulhu dashi. Ki ™yale ni Didi, wanda ya yi gaba baya komawa baya."

Didi ta yi shiru suna cigaba da yi masa nasiha yayi musu shiru bai ce komai ba. Sai da suka taso zasu tafi Didi ta kalle shi ta ce, "Nayla ta tsorata da kai Omar, ka rarrashe ta ka daina yi mata wannan faWan."

Ya Wan yi tsaki ya ce, "Tausayinta nake ji, ina gani kamar ban zama miji na gari a gare ta ba, ta silata ta shiga wannan yanayin, amma haushinta nake ji sosai. Ta raina ni ne kawai, dan ta ga ina yi mata dariya shiyasa ta samu wannan damar. A cikin wannan yanayin da ake ciki kawai ta hau napep ta fita ba tare da na sani ba? Dakonta fa ake yi a waje. Tk ya ce saran da suka kai mata a wuyanta suka so ya same ta, suna tsinke jijiyar wuyanta da yanzu ba wannan maganar ake yi ba. Ba dan Tk ba da me kike tunanin zai faru?."

Didi ta ce, "Ka yi mata uzuri, bata taSa shiga irin wannan yanayin ba sai wannan lokacin. Kuma ita ta Waukar fitar da tayi zai kawo mata sassaucin tsoron da take ji. Kuma tunda Allah ya yi sai ta ji wannan ciwon ko bata fita ba sai an shigo har gida an cutar da ita. Dole zaka WanWana irin abinda ka dinga WanWanawa mazajen wasu akan matansu a baya..."

Omar ya bita da kallo jin abinda take faWa, ta ce, "Eh Omar. ba dai kaji zafi a ranka ba? Ka ji ciwo da raWaWin a zuciyarka saboda abinda ya same ta ba?. To Allah ne ya WanWana maka dan kaji abinda wasu suka ji a lokacin da ka yiwa nasu, kai kanka baka san iyaka adadin matan da aka yiwa irin abinda aka yiwa Nayla ba, ba dan komai ba sai dan saboda laifin mazajensu ya shafesu. Dan haka ka nutsu kawai, mu yi fatan Allah yasa ya tsaya a haka."

Ganin ya kasa magana ya tafi tunani sai ta ce, "A firgice take Omar, tsoronka ya riga ya tsarata, ka taimaka ta dawo nutsuwarta ta daina wannan firgicewar don Allah. Ka san a ina yarinyar nan ta taso, ba sabawa da wannan tashin hankalin tayi ba shiyasa ta tsorata. Bana tunanin allura in ba ta neman lafiya ba ta taSa sokarta, yau gashi hannunta a Waure yake saboda an sare ta da wu™a. Kuma ido da ido ta ganka da jini a jikinka dole ta ji tsoro, abinda bata taSa gani a zahiri ba sai a film, dole ta shiga wannan yanayin. Ka yi ha™uri, ka yi mata uzuri, duk fushin da ka ke yi da ita a kan ta fita ka ajjiye shi don Allah."

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba. Bashir ya saka suka raka su Didi dan a yanayin da ake ciki bazai yi sake da lafiyarsu ba.KRB3P074
Nanahaleema.

Lokacin da ya koma bata falo, Wakin ta ya shiga ya tarar da ita a kwance a kan gado layi luf a kan gado, ya kunna hasken Wakin suka haWa ido ya ce, "kin ci abinci ne zaki kwanta?." Yadda yayi maganar babu wasa ya saka ta ce, "mun ci da Didi." Ya girgiza kai ya ce, "a nan kika saba kwana kenan?."

Ta mi™e zaune ta ce, "ba a nan ba ne."
"Rainin ne ko?." Ta sakko daga kan gadon bata ce komai ba ta wuce ta tafi Wakinsa. Ya sauke numfashi ya bita Wakin dan bazai iya barinta ita kaWai ba a kusa dashi zata kwanta. Sai da ya shiga Wakin ya ce, "me yake damunki?." Nayla ta ce, "babu komai." Ya taka inda take ya taSa wuyanta, ya ri™e kanta yaji babu alamun ciwo, ya duba hannunta yaga ciwon babu abinda ya same shi.

Ya bita da kallo ganin tana rawar jiki ya ce, "ke wai meye abin tsoro a jikina?." Ta sunkuyar da kai ta ce, "ka yi ha™uri." Yayi ™aramin tsaki ya bata waje ta kwanta cike da fargaba

Washe gari da kansa ya kai ta aka yi swapping sim card Win ta, bayan sun dawo suka biya asibiti aka duba ciwon, sannan ya siya mata sabuwar waya ya ajjiye mata. Jikin ta duk a sanyaye yake haka ta Wora komai na wayar saboda ta san ´an gidansu suna nemanta.

   Kwana biyu suka kwashe a wannan yanayin, bata shiga harkarsa kuma a waje Waya suke kwana, daga ina kwana babu abinda take iya ce masa, shima daga ya amsa shikenan babu wata magana. In ya riga ta tashi zai yi abinci kuma su zauna a waje Waya su ci, in ta riga shi tashi zata yi abinci itama. Zuwa lokacin waWanda ake zargi hukuma ta shiga tsakani, komai ya wuce kamar bai faru ba amma ita dashi basu dawo daidai ba, dan ita tsoronsa take ji, sannan kuma tana jin haushin faWan da ya dinga yi mata ko ciwon hannunta bai duba ba.

A haka ta je bank aka gyara mata account Winta da aka yi blocking har lokacin ba shiri suke yi ba. Ranar da aka kwana biyar da faruwar abun da daddare sun dawo daga asibiti an duba mata ciwon, ta gama shan tea ta dawo Waki ta canja kaya zuwa na bacci ta Wauki wayarta zuwa Wakinsa. Tana shiga suka haWu a hanya, suka haWa ido ta Wauke kai ta yi gefe zata wuce ya tare mata hanya, ta sake juyawa Waya side Win ya sake tare ta, ya matso kusa da ita har yana jin saukar numfashinta. Ganin ya hanata wucewa gashi ya matso kusa da kusa ita sai ta tsaya cak tana sauke numfashi a hankali. Cikin nutsuwa ya saka hannu biyu ya Wago fuskarta yana kallon idonta da suka fara taruwa da hawaye.

Kumatunta ya shafa, calmly ya ce, "Jiddana, Ashiq!" Ya furta a sanyaye yana kallonta. Fuska ta ™waSe zata yi kuka, ya Wan yi tsaki kaWan ya ce, "Kar ki yi kuka mana..." Nayla ta faWa jikinsa da hanzari ta rungume shi tightly tana kuka. Murmushi ya yi ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali cikin salo na ™auna.

Nayla cikin kuka ta ce, "Ka dana sona...ka daina sona...!." Omar ya ce, "Shiii! Ki daina magana" ya haWa yana ri™o ™ugunta ya sake haWe ta da jikinsa sosai. Sun jima a haka kafin ya sassauta ri™on da ya yi mata ya ri™e fuskarta ya fara kissing Winta slowly. Bai jima ba ya raba kansa da ita yana yamutsa gashinta yana kallon idanunta da suke zubar hawaye.

"Ki yi ha™uri!" Ya furta a hankali, ya sake kissing Win bakinta na ´an sakanni kafin ya zare bakinsa yana shafa fuskarta. Ta sake komawa jikinsa ta kwanta tana jan numfashi. Sake ri™e ta ya yi yana jan numfashi kafin ya ri™e ta har kan gado ya zauna da ita ya zauna a gefenta ya ri™e hannunta baice komai ba.

Ganin tana kallon sa sai ya ce, "Ki yi ha™uri da ni, na faWa miki ban iya Sacin rai ba, daman kuma na faWa miki zan Sata miki rai wata rana, gashi ya faru" ya faWa yana kallon ta.

Nayla ta bishi da kallo ya Wan yi murmushi ya ce, "ki daina jin tsorona Jidda, abinda ki ke tunani bai faru ba a ranar, jinin Waya daga cikin yaran da suke yi min aiki ne, lokacin da na fita sun ji masa ciwo shine na ri™e shi su Bashir suka kai shi asibiti. Amma bayan nan ko wu™ar da na fita da ita bata yi min amfani ba."

A raunane ta ce, "Ka bani tsoro Rouhii, ka bani tsoro sosai. Kar ka sake koma min Tiger, ka cigaba da zama a Rouhiina kuma YaMar Wina. Tiger zai iya

Please Login or Register in order to submit comment