Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

™adangaren bakin tulu, ta karshi ta kar tulu, ta bar shi ya Sata ruwa. Ana murna an rabu da targaWe sai karaya ga ta samu."
"Hmmm" Nayla ta ce kawai bata ce komai ba.

Salma ta yi ™o™arin sake kawar mata da damuwa suna ta hira har Ummimi ta shigo suna labari. Mama ce ta shiga Wakin bayan sallar azahar ta ce, "Nayla kina da ba™uwa." Kafin Nayla tayi magana Didi ta bayyana a Wakin fuskarta cike da damuwa.

Nayla ta mi™e tsaye ta ce, "Didi sai da ki ka fito don Allah? Ki daina takurawa kanki fa,ki duba yanayin da ki ke ciki mana." Didi ta ri™e hannunta ta ce, "Nayla fitowar ce ta zamar min dole, dole nazo na same ki."

Zama suka yi a kan gadon, Didi ta kalli Mama da take tsaye ta ce, "Mama don Allah ayi ha™uri da abinda ya faru, wallahi ban san ma tana gida ba sai Wazu da muke yin waya. Don Allah ku yi ha™uri, Nayla bata cancanci zuwa gida a irin wannan yanayin daga gare mu ba, don Allah Mama...." Mama ta dakatar da ita ta ce, "Haba Aisha, wannan magiyar ta meye haka?. Mu da ke duk an zama ´an uwa, kallon jikar Hajja mu ke yi miki meye na wannan magiyar haka?. Kuma ai naga ba laifi aka yiwa Nayla Win ba balle ki ce zaki bada ha™uri."

Didi ta yi murmushi ta ce, "Mama na san halin Omar kamar yunwar cikina, wata™ila wani abun ya yi mata da ta kasa jurewa." Mama ta ce, "Nayla ta ce babu komai kawai ta gaji ne tana son ya saketa ta auri wanda ya ke sonta, tun farko ya nuna baya son auren nan ban san dalilinsa na karSar auren ba. Dan baya so ai baza ka yi masa dole ba, itama kuma yanzu ta ce bata so kinga an huta kowa baya so sai a rabu lafiya. Don Allah ki daina wannan magiyar haka, Ummimi zo ki kawo mata abinci" ta faWa tana fita Ummimi tabi bayan ta.

Didi ta sauke kai ™asa cikin sabuwar kunya da nauyi Mama, da ace ana canja mutum ya dawo yadda ka ke so tabbas da ta canja Omar. Ta ri™e hannun Nayla ta ce, "Nayla na san a zama ki da Omar ya yi miki abubuwa marasa daWi, bai Wauki auren ku da mahimmaci ba balle ya baki mahimmaci kamar ko wacce matar aure. Ina baki ha™uri akan hakan, ba wai a madadinsa nake baki ha™uri ba, Ina baki ha™uri ne saboda laifin da yayi, matsayina na ´ar uwarsa ya zama dole na bada ha™uri akan laifinsa. Ki duba yanzu yadda Mama ta tarbe ni, har nan Wakin aka kawo ni saboda ba a Wauke ni matsayin ba™uwa ba, ´ar gida ce ni zan iya shiga ko ina. Mama ta hana ni bada ha™uri ta ce nima jikar Hajja ce, ta kuma ce azo a kawo min abinci. Nayla ta ya zan ji daWi ace Wan uwana wanda mu ke ciki Waya dashi yake wula™anta jinin Hajja na ji daWi a zuciyata?" Ta fada muryarta na rawa saboda hawayen da ya taru a idanunta.

Nayla ta ri™e hannunta ta ce, "Didi ni baki min komai ba, Shima kuma bai yi min komai ba, na yanke hukunci ne saboda ya ce har abada bazai so aurena ba. Kin ga in na zauna dashi ni zan cutu, shiyasa na yanke wannan hukunci ko da bazai min daWi ba."

Didi ta ce, "to ko akan wanna kalaman nan na Omar ai ya zama dole na baki ha™uri, da ana canjawa mutum zuciya da na canjawa Omar ta sa." Salma ta ce, "Didi ki daina kuka don Allah, kina third trimester bai kamata ace kina saka damuwa haka a zuciyarki ba."

Ta kalli Salma ta ce, "Salma Omar ne fa, Omar ne ya faWawa Nayla haka in ban damu ba ya zan yi?."
"Ai ba ke kika faWa  ba, kuma shima dan ya faWa ai abinda yake ransa ya faWa ba wani abun ba. Kinga yanzu ta ce itama ba taso ba shikenan ba?."

Didi ta yi murmushi kawai ta goge idanunta ta kalli Nayla ta ce, "Kin yi daidai Nayla, kin yi daidai da ki ka dawo gida, don Allah ki saka Daddy ya maka shi a kotu, ya saka ayi masa hukuncin da za a kai shi gidan yari ayi masa horo mai tsanani."

Nayla ganin yadda Didin take magana bilha™™i da gaskiyarta sai tayi dariya sosai ta ce, "To Hajiya Didi." Didi ganin tana dariya ya saka ta ce, "Ba wasa nake yi ba, inda zan samu abinda zan yiwa Omar wanda zai ji a jikinsa da zuciyarsa wallahi sai na yi. To komai baya bashi tsoro, komai baya Waga masa hankali abinda yake gabansa kawai yake yi. Yanzu an karSo sakin?."
ÿþ

Salma ta ce, "A'a, Daddy ya ce zai bashi lokaci in yazo da kansa to, in bai zo ba kotu zata aika masa da sammaci. Abba ya ce babu wanda zai je nemansa, in ya damu zai zo, in ba damu ba kotu zata kira shi."

Didi tana girgiza kai ta ce, "sai dai sammacin kotun ya riske shi, zuwan Omar nan ba abu ne da nake ganin zai yu ba. Amma da zai yu zan fi kowa farin ciki, daga wannan lokacin zan samu abinda nake nema wanda zai taSa zuciyarsa da jikinsa."

Salma ta ce, "meyasa ki ka ce haka?."
"Salma indai Omar ya zo gidan nan ko ya nemi inda Nayla take wallahi yana sonta, ni kuma da wannan son zan yi amfani wajan hukunta shi sai na tabbatar da auren ya ™are."

Salma tayi murmushi haka ma Nayla ta ce, "Didi kina ji, yanzu mu nar zancen kawai, ki daina cewa zaki bani ha™uri bana jin daWi wallahi a zuciyata, ke Yayata ce, zaki ta ya ni ya™in neman saki a gare shi ba bani ha™uri ba." Didi tayi murmushi ta ce, "Haka ne Nayla, amma Ina tsananin jin kunyar tsatson hajja."

Ummimi da ya shigo da tray na abinci ya hana Nayla magana, suka yiwa Didi dole ta ci abinci, da Salma ta lura hirar Omar na taSa Nayla shiyasa ta kawar da ita suka fara hirar duniya kamar komai bai faru ba. Driver Mama ne da kansa ya tafi mayar da Didi bayan ta gama suka yi sallama da Mama ta tafi.

Fans kuna ganin zuwan Omar zai yu kuwa.....?KRB3P032
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla haka ta cigaba da zama a gidan Mama tana samun kulawa ta musamman, ita kuma ta dage da addu'a akan Allah ya kawo mata mafitar da zuciyarta zata iya Wauka. Maman su Jidda ta dame ta akan yaushe zata koma sai ta ce mata ta kusa komawa. Ta cigaba da zuwa aikinta kamar babu abinda ya faru, dan ta yi ™o™arin danne abinda yake zuciyarta saboda su Mama da suke tsaye a kanta wajan kulawa kar ta dinga sage musu guiwa.

Omar kuwa gabaWaya ya rasa abinda yake damunsa, hatta ma'aikatansa duk sun rasa gane kansa dan gabaWaya ko zuwa ya daina duk abinda ake so sai dai ayi masa waya. Duk da daman ba mutum ne mai yawan wasa ba, amma in yana cikin farin ciki da walwala ana ganewa, yadda fuskarsa ta ke a cushe da kuma rashin yin magana ya saka suka tabbatar da akwai abinda yake damun Ogan na su.

Ga shagunan cikin kasuwa da ake ta shirin buWewa an buWe, amma ba a zauna dashi ba balle a san tsarin da yake so ayi. Ya hana kowa ganinsa saboda shi kansa bai san abinda yake damun zuciyarsa ba. Ko Didi tun daga ranar basu sake magana da ita ba ko a waya, bata neme shi ba shima bai neme ta ba amma tana ransa.

Har aka yi kwanaki biyar da tafiyar Nayla ya rasa abinda yake masa daWi, gidan kuwa tunda ya bar gidan bai sake komawa ba yana kulle ya tare a gidansu gabaWaya.

Yana zaune a gida su da magriba ya yi shiru yana aikin tunani, zuciyarsa ta yi masa nauyi sosai, ya kuma san rashin magana da Didi ne ya kawo hakan, abinda yake bashi mamaki bai taSa jin nauyin zuciyarsa har haka ba, ya rasa wanne irin tunani ma ya kamata ace ya yi.

Goje ne ya shigo gidan da sallama ya amsa a ciki yana kallonsa, ya ce, "Damisa ka ce zaka aiko da wannan kayan ba a kawo ba, tun safe muna jira har yanzu shiru." Ajiyar zuciya ya yi mai ™arfi ya ce, "zan Wauko yanzu."
"Godiya mu ke" ya faWa yana fita.

Lumshe ido ya yi ya buWe idon, a bayyane ya ce, "Wai me yake damun zuciyata ne? Me nake ji haka mai matu™ar zafi da ciwo?. Anya ba wani ciwon ne yake damuna ba?." Babu mai bashi amsa ya sauke numfashi ya mi™e ya Wauki key Win gidan ya tafi.

Yana buWe falon gidan ™hamshi mai daWi ya doki hancinsa, ya ja numfashi ya sauke yana bin falon da kallo a hankali. Duk da akwai duhu a falon hakan bai hana shi ganin abinda yake ciki ba. Wani irin bugawa zuciyarsa take yi,har sai da ya kai hannu ya dafe zuciyarsa yana rutse ido da ™arfi. A hankali ya buWe ido yana jan numfashi da™yar, ya sake kallon falon yana hakki kamar wanda ya yi gudu haka yake sauke numfashi. Takawa ya ke yi zuwa tsakiyar falon yana jin bugun zuciyarsa na sake ™aruwa jikinsa na sake yin sanyi.

Šakinsa ya buWe ya shiga a sanyaye ya Wauko abinda zo gidan Waukowa. Kallon inda Nayla ta zauna ranar da take ciwon kai yayi, sai ya ga kamar ita Win ce har yanzu a zaune a wajan. Rufe ido ya yi ya buWe ya sake kallon wajan sai ya ga babu kowa a wajan, ya dafe kai cikin rashin sanin abinda zai yi. Daga Wakin ya fito yana kallon ™aramin falon da ya kasance mazauninta yana ji a zuciyarsa kamar tana ciki a zaune.

"YaMar!" Sautin da ya ji a kunnensa kenan, ya juya da sauri amma bai ga kowa ba bai kuma ji daga inda aka yi maganar ba. Ta bayansa ya sake jin sautin, "YaMar don Allah na je!.?" Omar ya juyowa da hanzari amma still babu kowa a wajan ko wadataccen haske babu. Kalle-kalle ya ke yi a falon amma bai ga kowa ba amma komai yana nan yadda yake. Shiru ya yi yana sake ™arewa wajan kallo, ya rufe ido ya buWe har lokacin numfashi yake saukewa kamar wanda yayi gudu.

Fita ya yi daga gidan ya kira Goje ya bashi abinda suka nema sannan ya sake komawa gidan, haka kawai yake ji baya so ya bar cikin gidan domin jin zuciyarsa yake a karye, yana jinsa kamar kwalin da babu komai a cikinsa iska na jansa.

A hankali yake takawa har inda ta saba zama yana kallon wajan cikin rashin sanin dalilin da ya saka yake jin abinda yake ji. Kallon Wakin ya yi sai ya tuna cikin azumi da yaran nan suka shigo gidan, da yadda ya ji ihunta har tsakiyar zuciyarsa. Kai tsaye Wakin nata ya buWe a hankali ya kunna hasken Wakin yana kallon Wakin.

Komai yana nan tsaf dashi, kallon inda ta diro daga kan gadon ta taho wajansa a guje tana neman agaji yake yi. Rana ta biyu da ya shiga Wakin a rayuwar da ya yi a gidan kenan, ya ™arasa jikin madubin Wakin yana kallon sauran tarkacenta da suke ajjiye a wajan.

Kamar wanda ya farka daga bacci, ya yi firgigit ya kalli Wakin ya kalli kansa a madubin ya ce, "Wai me nake yi haka? Me yake damuna ne?" Ya faWa yana sake ™arewa kansa kallo amma bai ga alamun canji a tare dashi ba, shi Win ne dai a tsaye a Wakin Nayla.

Fita ya yi daga Wakin da sauri, yana zuwa tsakiyar falon ya sake jin an kira sunansa kamar yadda Nayla take kira. Cak ya tsaya ya waiwayo amma babu kowa, ya dafe kansa ya fita daga gidan da hanzari dan ya lura aljanu sun cika gidan.  Duk yadda ya so yakice damuwar abin ya faskara, shi ba Wan uwa ne dashi ba balle ya faWa masa ya bashi shawara, shi ba mahaifiya ba, shi ba mahaifin ba, shi ba aboki ba. Didin dai itace kawai mafitarsa.

Washe gari da yamma ya bi umarnin zuciyarsa ya kira Bashir ya ce yazo su je gidan Didi. Sai da suka je ™ofar gidan sannan ya Wauki waya ya kira ta.

Didi tana zaune a falo tana tunaninsa, tayi kewarsa sosai, basu taSa irin wannan dogon fushin ba sai wannan lokaci. Ta san tana Sata masa rai ya yi kwana biyu bai kulata ba, amma ba a taSa yin sati Waya bai neme ta ba sai wannan lokacin. Ganin kiransa ya bata mamaki da farin ciki, ta Wauka da hanzari ta saka a kunne ta ji ya ce, "Ina ™ofar gidanki."

Didi da hanzari ta mi™e ta ™araso ta buWe masa ta tarar yana magana da Bashir kafin Bashir Win ya tafi ko gaisuwa ma basu yi dashi ba. Kallon ta ya yi kamar yadda take kallonsa, in ba gizo idonta yake mata ba sai ta ga ya rame amma kuma fuskarsa ta yi haske sosai.

Didi ta ce, "™araso mana." Bai musa ba ya ™arasa har cikin gidan ya zauna ta kawo masa ruwa da lemo ta zauna a gefe ta ce, "Ka sha ruwa." Šan ™aramin tsaki ya yi ya ce, "bana son sha." Didi ta bi shi da kallo ya yi shiru bai ce komai ba.

"Didi!" Ya kira sunanta ba tare da ya kalle ta ba. Didi ta ce, "Na'am Omar."
"kin Sata min rai kuma kina fushi dani." Didi ta ce, "ni ba fushi nake yi da kai ba, kaine ka daina kirana balle ka ji lafiyata." Kallon fuskarta ya yi ya ce, "amma kin san laifinki ne ko? Duk abinda ya faru ke ki ka jawo."

Didi a sanyaye ta ce, "na ji, ni ban yi dan ranka ya Saci ba gaskiya na faWa maka. Kaine ka Sata min rai da wannan hargagin naka har na mareka ban sani ba, amma ka yi ha™uri." Kallon ta ya sake yi ya lumshe ido ya buWe ya kasa furta komai.

Didi ta ce, "Baka da lafiya ne? Na ga ka rame amma kayi haske." Omar ya kifta idanu ya ce, "Nima ban sani ba Didi, nauyi nake ji a zuciyata sosai. Na Wauka rashin magana dake ne ya kawo hakan shiyasa nazo na ganki, amma gashi ina magana dake Win ina ji kamar ana ™ara min nauyin a zuciyata. Anya ba wani ciwon ne ya kama ni ba?."

Didi ta ce, "to me ya kawo hakan? Wani abun ya faru ne?." Omar ya Wan juya hannunsa ya ce, "ni ban sani ba." Didi ta bi shi da kallo ta ce, "Allah ya kawo mafita. Babu wani ciwo da ya kama ka kawai fushin da ka ke yi dani ne ya kawo hakan, haushin na yi maka faWa har na mareka a gaban matarka duk shine ya kawo hakan. Amma yanzu a hankali zaka ji ka dawo daidai, musmaman ita matar ta ka da ka ce baka so ta bar gidan ta baka space Win da ka ke nema a rayuwarka. A ganina ai babu sauran damuwa kuma Omar."

Kallon Didi yake baya ko kiftawa musamman da ta sako zancen matarsa sai yaji wani abu ya soke ji a zuciyarsa, har ta kai ™arshen maganar kallonta yake yi sannan ya ce, "yanayin nan yana damuna Didi, ban taSa jin kaina a wannan yanayin ba tunda Allah ya halicce ni."

Didi ta ce, "zaka daina ji musamman in ka saukewa kanka nauyin da yake wuyanka. Iyayen Nayla suna jiran takardar sakin ´arsu daga gare ka, ya kamata ka je ka kai musu takardar sakin ka hutawa kan ka itama ta huta tayi aurenta a inda aka san mahimmacinta ake kuma ™aunarta. Da zarar ka yi hakan shikenan zance ya ™are,
zaka cigaba da rayuwarka lafiya lau fiye da baya."

"Didi na zo nan ne dan na ji sau™in abinda yake damuna, na Wauka in na zo nayi magana dake komai zai wuce zan warware na daina jin abinda nake ji amma ban daina ba. Maganganunki sai na ji kamar ma nauyi suke sake ™ara min."

Didi ta yi murmushi ta ce, "To Omar me zan yi maka? Gaskiya ce nake faWa maka. Kai ka ce baka son yarinyar nan, baka son aurenta baza ka taSa so ba har abada. Har wallahi ka ce, kuma na san duk abinda ka yi rantsuwa a kai gaskiya ne a zuciyarka baka canjawa, shiyasa nake faWa maka abinda ya kamata ka yi ka saukewa kan ka ha™™in da yake wuyanka. Ka saki yarinyar nan itama ta huta da igiyar aurenka da yake kanta, ta cigaba da rayuwarta ta yi aure ta auri wanda yake son zama da ita. In ka aikata hakan zaka daina jin nauyin da ka ke ji."

Zuba mata ido ya yi yana kallo bai ce komai ba, itama sai ta yi shiru bata sake magana ba har mintina biyar sannan ta ce, "ka zuba min ido kana kallona baka ce komai ba." Sai a sannan ya janye idanunsa daga kanta ya yi ajiyar zuciya ya kulle ido ya buWe ya ce, "ban san me zan yi ba."
"Sakinta zaka yi."
"Ita wa?."
"Nayla mana."
"Hmmm!" Ya furta yana kallon wani wajan daban. In ta furta kalmar sakin nan sai yaji kamar ana soka masa kibiya a zuciyarsa, dafin dake jikin kibiyar yana tafiya har cikin jininsa yana zaga ko wanne sashi na sassa jikinsa.

"Yaushe zaka je ka kai musu takardar sakin?."
"Ni babu inda zan je, babu wanda ya isa ya saka ni na je inda ban yi niya ba" ya faWa a fusace yana kallonta. Didi ta ce, "ai kuwa zasu aiko maka da sammaci daga kotu. Ni na rasa wannan abu irin na ka, kace baka sonta ba sai ka saketa ba?." Ya kalle ta da idanunsa da suka fara canja launi ya ce, "Meyasa ki ka ce min ko mahaifinta ne ya ce na saketa kar na aikata hakan? Kin manta ke kika ce min haka?."

Didi ta ce, "ni na faWa, na kuma san ba wai ka amince bane kawai ka ji ni ne. Kuma yanzu ni na ce ka saketa Win ai, in da ni na hana yanzu ni na ce ka saketa." Shiru ya yi bai ce komai ba, ya kalle ta zai sake magana sai ya yi shiru. Didi ta yi murmushi ta ce, "Omar shiru ba shine abinda ya kamata ka yi, ni so make ka saukewa yarinyar nan auren ka da yake kanta ta huta wallahi."

Banza ya yi mata bai kula ta ba ganin haka sai bata sake magana ba. Ido taga ya rufe ya buWe ya sake kallon ta ya ce, "ki ™yale ni don Allah" ya faWa yana Wauko waya ya kira Bashir ya ce in ya gama ya dawo su tafi.

Didi ta ce, "ba fa zan ™yale ka ba Omar, dole na saka ka yi abinda ya kamata." Ya taSe baki ta ya ce, "kin san da haka meyasa ki ka yi min dole na karSi auren?."

"Na Wauka zaka so ta da zuciya Waya, nayi tunanin zaka zauna da ita ka ri™eta amana, ka bata farin cikin da take burin samu a gidan mijinta. Amma sai na ga ba haka ba, sai na ga har yanzu baka kallon ta a matsayin matarka, in na yi magana sai ka ce ai dole aka yi maka ba so ka ke yi ba. Tunda har yanzu baka jin zaka iya karSarta matsayin matarka gwara a rabu Win ya fi alkhairi."

"Za a rabu Win, sai sanda na yi niya babu wanda zai min dole a lokacin da ban ga dama ba" ya faWa Wan ya Soye yanayinsa. Didi ta murmusa ta ce, "Hakan ne ya kamata, ni na Wauka ma a ranar ka furta mata ka huta da wahala ai." Mi™ewa tsaye yayi ya ce, "Magana da ke ma damuwa take ™ara min, dana sani ban zo ba." Didi ta mi™e tana dariya ta ce, "ai na faWa maka, in dai ba abinda nace ka yi ka aikata ba baza ka dawo daidai ba, kuma ka ga daman ba idda ce a kanta ba, in ka saketa aurenta zata yi ta huta. Akwai masu sonta sosai, harda Wan uwanta da yake sonta kuma a gidansu take zaune."

"Mtsw!" Yaja tsaki yana barin falon. Murmushi ta yi ta ce, "Allah ya sa hasashe na ya zama gaskiya" ta faWa tana biyo bayansa amma ta samu har ya fita. Da Bashir suka gaisa sannan suka bar unguwar.

Omar da ya koma haka ya dinga juya kalaman Didi, bai san meyasa kalaman suka yi masa nauyi har baya so ya ji ta furta kalmar saki ba, in ya tuna da kalmar sai gabansa ya faWi ya ji a zuciyarsa bazai iya furta wannan kalmar ba gabaWaya. Furzar da iska yake yi ya dafe zuciyarsa yana jin yadda zuciyarsa take bugawa, ya cize baki yana jin rauni yana mamaye masa zuciyarsa. Ya shiga damuwa sosai fiye da yadda yake tunani, haka kawai ya ji ranar a gidan yake son kwana, ya sake komawa duk da Wan kiran da ake yi masa a gidan.

A Wakin Naylan ya kwanta yana jin kewa mai tarin yawa a zuciyarsa, amma bai san kewar ba ce tunda bai taSa jin yana kewar wata halitta a duniya ba, ya Wauki hakan a matsayin nauyin zuciyarsa take yi masa, bai kawo kewarta yake yi ba ko kaWan.

Wasa-wasa har kwana biyu Omar ya tare a gidan a kuma Wakin Nayla, sannan ko yaushe cikin jin muryarta yake tana kiran sunansa. Ya shiga damuwa sosai wacce ta haifar masa da kasala da kuma zazzaSi mai shegen zafi. Kansa ya yi masa nauyi saboda ciwo, ya rame lokaci Waya sai haske da ya sake yi, dan shi daman zama waje Waya yana saka shi haske.

Bashir ya kira a waya yana zaune a falon ya aike shi siyo magani saboda yadda yake jin zazzaSin na ratsa ™asusuwan jikinsa. Bayan ya kawo masa ya sha, Bashir ya tsaya yana ta yi masa sannu bai taSa ganin Ogan na sa a wannan yanayi ba.

Bashir shi ya sanar da Didi Omar ba shi da lafiya, da daddare mijinta ya kawo ta dan ta duba shi. Da ta shiga falon a zaune ta tarar dashi idanunsa a rufe, ta kalle shi da kulawa ta ce, "Sannu Omar, ashe baka da lafiya ban sani ba."

Tashi zaune ya yi sosai suka gaisa da mijinta kana ya kalle ta ya ce, "ZazzaSi ne kawai." Didi ta ce, "Wannan ya wuce kawai, kalli yadda ka koma fa, ka je asibiti?." Kai ya girgiza alamun a'a ta ce, "Zama ai ba naka bane, asibiti ya kamata ace ka je. Ka rame, fuskarka ta bayyana rashin lafiyarka a fili."

Juyawa ta ga ya yi yana kallon falon kafin ya kalle ta ya ce, "Wai baku ji ana kiran sunana ba?." Didi ta kalli AbdulHamid kafin ta kalle shi ta ce, "ni ban ji komai ba."
"To meyasa ni nake jin muryarta tana kiran sunana? Ko dai aljana ce daman?." Didi ta ™yalk™yale da dariya ta ce, "Ko kuma aljanun ne suka ji sunan yayi musu daWi suke kiranka ba." Share maganar ya yi bai ce komai ba ta ce, "Omar kwanaki na ta tafiya har ta kwashe kwana takwas a gida, yaushe zaka je ka kai mata takardar ne?."

A fusace ya ce, "ni ban san meyasa ki ka damu haka ba, ki ™yale ni mana duk lokacin da na ga dama zan yi ai na faWa miki. Meyasa ki ke min naci a kaine? Na tsani wannan kalmar nan da ki ke faWa, bana jin daWinta meyasa baza ki gane ba!?." Didi ta ce, "masifaffe, Allah ya baka ha™uri, tuna maka nayi dan ka sauke abinda yake wuyanka."

˜aramin tsaki ya yi ya kalli AbdulHamid ya ce, "Ka yiwa matarka magana ta daina bana so, ta ™yale ni in nayi ra'ayi zan yi ai."

Abdulhamid ya ce, "To Omar." Kallon gefensa yake yi bayan ya dafe goshinsa, zuciyarsa kamar ana gasata a tukuba haka yake ji. AbdulHamid ya

Please Login or Register in order to submit comment