Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashe na suturta jikinki ne da rigar jikina saboda abinda na rufe Win nawa ne ban sani ba." Kunya ya bata mai nauyi, ta koma jikinsa ta rufe fuska tana murmushi. Murmushin shima ya yi ya ri™e ta yana lumshe ido, bai ce komai ba sai ™hamshin ta da yake sha™a wanda ya zauna daram a jikinta.

Shifa ya Wauka zancen Didi ne da ta ce kalamai suna fitowa daga zuciya, amma yanzu ya tabbatar dan baya sanin mai zai furta sai bayan ya furta Win.

Shiru ya tsara tsakaninsu, sun jima a haka yana shafa kanta zuwa bayanta idanunsa a rufe itama kuma na ta idon a rufe. Gently ta ji ya ce, "™arin wani abu Waya! A kan ki Omar ya fara kwanciya a asibiti. A yadda Allah ya halicce ni ban cika rashin lafiya ba a rayuwata, amma a kan ki nayi zazzaSi da ciwon ™irjin damuwar barinki gidan nan, sannan jiya na kwanta a asibiti saboda ke. Ki ™ara a lissafi." Murmushi tayi ta sake kwanciya a jikinsa ya cigaba da shafa kanta har ya gama maganar idanunsa na kulle.

"Jidda!."
"Uhum!."
"ki yi ha™uri idan son da nake miki yayi yawa, ki yi ha™uri in soyayyar da nake son gwada miki ta girmi ™wa™walwarki. Ban taSa jin irin wannan soyayyar a baya ba, shiyasa na baki kaina gabaWaya dan bana son na kwantanta irin zaman kaWaicin dana yi a baya. Tabbas zaki iya ganin za™ewata tayi yawa Jidda, ba dan komai ba sai don ke Win kin zama komai a gare ni da rayuwata."

Šago ta ya yi daga jikinsa, ta kalle shi kamar yadda yake kallonta ya ce, "in zamu kwana ina faWa miki mahimmacin da ki ke dashi a rayuwata lokacin ya yi mana kaWan, ko da zamu kwana mu yini mu sake kwana bazan kai ™arshe ba, kawai ki saka a ranki Omar yana sonki, zai rayu dake a duniya, yana fatan rayuwa dake a aljanna."

Murmushi ta yi cikin tsananin farin ciki da ™aunarsa amma bata ce komai ba. Ya tashi tsaye ya ya fita bai ce mata komai ba, bai jima ba ya dawo ya yi shirin kwanciya ya ce, "na shigo?." Rufe ido ta yi da sauri dan rigar jikinsa ™arama ce ita kuma kallonsa ma tsoro yake bata.

A hankali ta Waga kai, ya tako ya shigo ya kwanta a gefenta bayan ya kashe hasken Wakin ya matso da ita jikinsa ya kwantar da ita a ™irjinsa. Gabanta ya faWi sosai, tsoron abinda ya faru jiya ya dawo mata a zuciyata, sai ta yi niyar mi™ewa zaune ya mayar da ita. Calmly ya ce, "bazan yi abinda zai cutar dake ba, na san abinda yake ranki Jidda, a jiyan ma yazo ne ba tare da an shiryawa hakan ba. Ki nutsu!." A sanyaye ta koma ta kwanta amma har lokacin a tsorace take dashi.

"Nifa har da yayanki na yi kishi, da ki ka rungume shi a gabana sai dai naji faWuwar gaba. Kin san ban iya Soye abu a rai ba shiyasa nake faWa miki, amma kishi na yi ba haushi na ji ba." Dariya tayi sosai jin yadda yake maganar a yangance, kuma ba tayi zaton zai sake magana ba sai gashi ya yi, sai abin ya bata dariya, wai kishi na yi ba haushi na ji ba.

Shima murmushin ya yi, a lokacin ya tuna  yayi kishi da Jawad, kuma yana so ya faWa mata kar ya manta. Dan shi bai iya Soye abu a rai ba, kuma yanzu ya na ganin babu wacce ta cancanci ta san duk abinda yake zuciyarsa kamar ita. Bai sake cewa komai ba sai shafa bayanta da yake yi a hankali duk da ya san babu lallai ta yi bacci tunda bata jima sosai da ta shi ba.

"YaMar!" Ta furta a hankali tana kwance a jikinsa ya ce, "Uhum!."
"Lokacin da mu ka je Kaduna, da Abiy ya ce ka dawo masa dani fa?."
"Zan dawo Kano ni kaWai na bar ki a can."
"Ka ce baza ka iya rayuwa babu ni ba....?"
"Rayuwar zata yi min wahala, amma gwara na barki a can da na dawo da ke baya so."

Nayla ta ce, "meyasa?." Ya yi ajiyar zuciya kaWan ya ce, "Zan faWa miki, amma yanzu ki kwanta ki huta." Nayla ta ce, "ni bana jin bacci." Ya ce, "ai baki da lafiya."
"Ni dai ka faWa min."

"Tunda na ce zan faWa miki zan faWa, amma yanzu ki huta." Shiru tayi bata ce komai ba sai daga baya ta sake cewa, "To Narma fa!?." Idanunsa a kulle ba tare da ya kalle ta ya ce, "Wace haka?." Ta kalli fuskarsa, sai ya buWe ido suka haWa ido a cikin ™aramin hasken Wakin, bata bashi amsa ba ta koma ta kwanta a jikinsa shima kuma bai sake cewa komai ba. Ta dole ya saka bacci ya Wauke ta yadda yake yamutsa mata gashin kai da shafa bayanta bata san ta biye masa bacci ya kwashe ta ba.KRB3P054

A haka suka yini cikin kula da tattali da soyayya mai tsayawa a rai. Babu inda Omar ya je, ko sallah tare suke yi da sun idar ya cigaba da rarrashin masoyiyarsa. Iya kallon da yake yi mata kwantar mata da hankali yake yi, balle in ya buWe baki ya ambaci sunanta sai ta ji kamar babu wata macen a duniya bayanta.

Bayan sallar i'sha tana zaune a falon da ta saba zama tana shan alawar tom tom, idanunta a rufe ta jingina da kujera ta Waga kai sama kamar mai tunani. Bata jin daWin jikinta ko kaWan, ji take kamar iska zata kwasheta ta watsar a wani waje. Ga raWaWin da take ji a cikin jikinta, dauriya kawai take yi amma a takure take.

Motsinsa ta ji a kusa da ita yana, ya zauna a kusa da ita sosai ya ce, "Gata nan." Jin abinda ya ce sai ta buWe ido ta kalle shi kamar yadda yake kallon ta. Ta Wan gyara zama kaWan ta Wauke kai daga kallonsa. Muryar Didi ta ji daga wayar ta ce, "bani ita mu gaisa." A sanyaye ta ji ya ce, "tana jin ki." Didi ta ce, "Nayla!." Nayla a raunane ta ce, "Na'am Didi, ina yini."
"Lafiya lau Nayla, ya jikin na ki?."
"Da sau™i Didi."
"Allah ya ™ara lafiya."
"Amin. Ina Marmerh?."
"Gata nan tana bacci."

Omar kallon ta kawai yake yi, ™hamshin alawar da take bakinta yana shiga hancinsa saboda kusancinsa da ita. Ya lumshe ido yana kallon bakin ta da take motsa shi cikin rauni da shagwaSa. Ta buWe baki zata sake yiwa Didi magana ya haWe bakinsa da nata, wayar hannun Nayla ta suSuce ta faWi a kan carpet, ta zaro ido waje jin yana shanye alawar da take bakinta a nutse. Gabanta faWuwa yake yi, ta motsa kaWan ko zai cikata amma bai sake ta ba sai sake ri™e fuskarta da ya yi.

Omar idanunsa a lumshe yake, za™i da yajin tom tom Win da take bakinta yake haWWiyewa a cikin salo na soyayya da shau™inta da yake mamaye masa jiki. Nayla ™irjinta bugawa yake yi, tsoro da fargaba suka mamaye mata zuciya. Jikinta ya fara rawa ba tare da ta shirya ba, hawaye ya fara sakkowa daga idanunta. Šumin hawayenta ya ji a kan fuskarsa, ya buWe ido ya kalli fuskarta yaga hawaye take yi amma idonta a rufe yake. A hankali ya zame bakinsa ya haWe goshinsu waje Waya a lokacin kukanta ya samu damar fitowa.

Kuka take yi mai sauti jikinta yana rawa, ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali tana cigaba da kukan. Yadda jikinta yake rawa ne ya saka shi ya matse ta a jikinsa yana so ya samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali. A hankali kukan nata ya ragu, ta Wago daga jikinsa tana jan numfashi idanunta a rufe saboda kunyar da take ji.

Fuskarta ya Wago yana kallo, ya saka hannu ya share mata hawaye ya ce, "Ina ma Omar zai zama hawayen da suke sakkowa daga idanunki, ina ma ni ne hawayen da yake fitowa daga idonki ya samu masauki a kan kuncin. Inda na kasance a haka da zan fi kowa farin ciki, dan na san zai rage min kewar ki da nake ji a zuciyata. Zan kasance a cikin idonki kullum, sannan in na tashi fitowa zan sakko akan kyakykyawar fuskarki!" Ya faWa yana ri™e da kumatunta yana shafawa da yatsa Waya.

Bata buWe ido ba tana jin abinda yake faWa, a tsorata take dashi sosai, zuciyarta bugawa take ji tsoro ya mamaye ko ina na jikinta. Kafin ta yi magana ya ce, "Me ki ke so ki ke kuka? Me yake damun ki?." Kawai sai ta sake fashewa da kuka ta kwanta a kafaWarsa ta ce, "Ni Kaduna zan je wajan Abiy!." Bai Wagota daga kafaWarsa ba sai hannunta da yake cikin nasa ya ce, "Bakya son zama dani?." Ta girgiza kai alamun a'a sannan ta ce, "Wajan sa nake son zuwa" ta faWa cikin kuka.

A hankali ya Wago ta yana kallon yadda hawayen suke sauka Waya na bin Waya, matso da fuskarsa ya yi kusa da ta ta, ya sanya harshe ya lashi hawayen cikin sacan biyu. Jin Wumin harshensa sai ta buWe ido suka haWa ido, ya Waga mata gira Waya sai ta mayar da ido ta rufe gabanta yana cigaba da haWuwa.

A taushashe ya ce, "Yanzu ki ke so ki tafi Kadunan?." Da sauri ta Waga kai alamun eh. Ya yi murmushi mai sauti ya ce, "Ni kuma sai ki bar ni da wa?."
"Didi" ta bashi amsa murya tana rawa cike da tsoro. Murmushi ya sake yi, ya fuskanci a tsorace take matu™a kuma bai ga laifinta ba. Ya ce, "Da yake bakya sona ko?." Ta buWe ido ta kalle shi sai ta sake fashewa da kukan shagwaSa ta ce, "Na gaji, na gaji wallahi. Zafi nake ji, jikina ciwo yake yi min, jiri Waukata yake yi. Ka kaini gida wajan Abiy don Allah!" Ta sake faWa cikin kuka sosai.

A jikinsa ya kwantar da ita yana shafa bayanta da shigar rarrashi, tana ta jan numfashi a ™irjinsa tana zubar da hawaye. Bai yi mata magana ba sai da ta nutsu sannan ya Wagota daga jikinsa ya zaunar da ita, ya sakko kusa da ™afarta ya mi™e akan guiwarsa tare da dafa guiwarta ya ce, "Har yanzu da akwai zafin?." Ta Waga masa kai alamun eh. Ya yi ajiyar zuciya cikin tausayinta ya ce, "na sake haWa miki ruwan zafin?." Ta no™e kafaWa kamar yarinya ta ce, "Shima da zafi, ni bana so."

GabaWaya ta ruWa shi, ya rasa me zai yi mata, ganin tana hawaye Waga masa hankali take yi dan ya san shine silar faruwar hakan. Ya sake numfashi cikin taushin murya da sanyi ya ce, "To me ki ke so Jidda? Ko mu koma asibiti?." Nan ma ta girgiza kai alamun a'a. Ya ce, "to me zan yi miki?."
"Ka kaini wajan Abiy."
"Dare ya yi Jidda."
"To ka kaini wajan Hajja" ta faWa tana buWe ido tana kallonsa.

Ajiyar zuciya ya sake yi yana kallon ta, mamakin kansa kawai yake yi, dan ko Didi bazai tsaya yana faWa tana ja ba, amma yau ga Jidda ta saka shi a gaba da rigima kuma bai ji komai ba sai ma son samar mata da abinda take so yake yi. Omar ya ce, "Jidda dare ya yi yanzu, har ™arfe tara ta yi." Ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "na baki abinci?." Ta girgiza kai alamun a'a, ya ce, "A'a Jidda, zaki ci abinci sannan ki sha magani." Ta sake no™e kafaWa ta ce, "ni bakina babu daWi, bana son cin komai."

"A'a, sai kin ci abinci" ya faWa yana tashi daga inda yake ya fita. Bai jima ba ya dawo da mug Win tea ya zauna a kusa da ita yana bata. Da™yar ta sha rabi, ya bata maganinta tasha ya cigaba da kallonta. Kallon sa ta yi sai kuma ta Wauke kai, ta mi™e tsaye tana runtse ido tare da furta, "Ouhchh wayyo Allah!" Ta gaWa cikin muryar kuka. Mi™ewa ya yi da sauri yana kallon ta, cikin tausayinta ya ce, "Jidda sai an kuma haWa ruwan nan, sai kin shiga zaki ji daWi." Ta girgiza kai alamun a'a, ya Waga kai alamun eh ya ce, "Zaki yi Jidda, mu je" ya faWa yana du™awa ya Wauke ta cak zuwa cikin Wakinta.

A gefen gado ya sauke ta, bai ce mata komai ba ya fita. Tana ganinsa yana ta hidimar haWa mata ruwa kamar da safe. Sai da ya gama ya ™araso inda take ya fara Salle maSallan gaban rigar jikinta. Da sauri ta ri™e hannunsa suka haWa ido ya ce, "zan kai ki banWaki ne." Ta girgiza kai ta ce, "zan iya."
"Baza ki iya ba, tafiya ma da™yar ki ke yi. Ki bari na kai ki."
"a'a" ta faWa a hankali.

Omar ya ce, "to na cire miki kayan?." Nan ma ta girgiza kai ya ce, "Jidda baki da ™arfin jiki, ki jira na yi miki kawai" ya faWa yana cire hannunta daga kan nasa ya cigaba da buWe rigar. Da sauri ta ce, "Nidai ka bari, bana so."
"Jidda!" Ya faWa yana kallon idonta. Ta girgiza kai bata ce komai ba. Bata ankara ba ya saSule rigar ya rage daga ita sai pink colour bra. Ihuu ta yi da ™arfin da ya rage mata ta ce, "Na ce bana so, ka ™yale ni!." Omar a hankali ya Wan buWe ido ya ce, "shiiii! Shikenan ya isa, bazan cire wannan ba, mu je sai ki cire da kan ki" ya faWa yana Wan jan hannun bra Win.

Šaukarta ya sake yi ya kaita banWakin ya fito ya barta zuciyarsa cike da tausayinta. Wayarsa ya Wauko a falo ya yi nufin kiran Didi dan ya ji meye matsalar da take jin zafi har yanzu. Ba tare da tunanin komai ba ya kira ta.

Didi tana Wauka ta ce, "Omar muna waya Wazu ta katse, ya aka yi?." Ya Wan yi shiru kamar mai tunani kana ya ce, "meye matsalar? Har yanzu tana jin zafi." Didi ta Wan yi jimm kafin ta ce, "Allah ya sa ba sake fama ta ka yi ba." A Wan fusace ya ce, "Mtsww! da yake ga mara hankali ko? Ko faWa miki aka yi bana sonta?."
"Kana sonta ka yi mata abinda ka yi?."
"In kin san Sata min rai zaki yi na kashe wayata."

Didi ta yi dariyar sha™iyanci ta ce, "Alhaji Omar mai matar so..." tsaki ta ji ya kuma yi zai kashe wayar sai ta ce, "Sai a hankali zata daina jin ciwon. Ka tabbatar tana shan magani, tana cin abinci, tana shiga cikin ruwan nan. Indai tana yi zata warke in sha Allah."

"Daga nan zuwa yaushe kenan?."
"Zuwa sati Waya."
"Har sati Waya tana fama da wannan ciwon?."
"Waye ya jawo mata?" Ta faWa tana katse shi. Banza ya yi mata bai amsa ba ta ce, "ka ce ina gaishe ta, amma ka tabbatar tana shiga ruwan. Kuma akwai tsoro a tare da ita, ka yi ™o™arin kawar da tsoron daga zuciyarta." Bai ce komai ba ya yanke wayar.

A lokacin Nayla ta fito sanye da bathrobe jikinta na Wigar ruwa. Da hanzari ya tako ya Wauke ta ya ajjiye ta akan gado har lokacin hannunsa yana kan cinyarta. Kanta yana ™asa, kunya da tsoro sun yana hana ta sakat, musamman yanzu da hannunsa yake jikinta ga yanayin rigar wankan da ta saka. Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "kin ji sau™i?." Ta girgiza kai alamun a'a. Ya Wan yi murmushi tunawa da maganar Didi, ya kalle ta cikin taushin murya da sanyi ya ce, "Jidda babu abinda zan yi miki, ki saki jikinki. Bazan sake yi miki komai ba sai kin warke."

Ta langwaSar da kai ta ce, "ai bazan warke ba." Ya yi dariya mai sauti, ya kalle ta yana tabbatar da tsoro ne kawai a zuciyarta shiyasa take haka. Omar ya shafa fuskarta yana murmushi ya ce, "Shikenan na ji. Yanzu me zan yi miki?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "kaya zan saka." Ya le™a fuskarta ya ce, "na Wauko miki?." Ta Waga kai alamun eh. Ya mi™e ya ™arasa wajan wardrobe Win ta ya buWe, kayan bacci suna rataye a cikin hanger ya Wauko mata doguwar riga ya kawo mata.

Ta karSa ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "don Allah ka je falo in na saka kayan sai ka dawo." Jin yadda take maganar a sanyaye sai ya ce, "To Jidda. Amma ina so ki tuna ni da ke babu sauran hijjabi, babu abinda zaki Soye min, komai na gani." Nayla toshe kunneta ta ce, "ni dai ka je!." Murmushi ya yi ya fita ya bata waje. A gaggauce ta saka rigar, ta mi™e tana takawa a hankali tayi shafe-shafen da ta saba sannan ta dawo ta kwanta ko bathrobe Win bata mayar ba.

Sai da ya tabbatar ta gama sannan ya shiga ciki, yana shiga hasken Wakin ya kashe ya ™arasa ya kwanta a kusa da ita. Jawota jikinsa ya yi, sai ta motsa zata bar jikinsa ya kai bakinsa kusa da kunnen ta ya ce, "Jidda ki nutsu! Na faWa miki babu abinda zan yi miki, don Allah ki nutsu, ki daina jin tsoro." Ta ™am™ame shi a jikinta cikin rauni ta ce, "ka yi al™awari?." Ya yi pecking Win ta a kunnenta ya ce, "Na yi al™awari Jidda. Ki nutsu kin ji?." Ta Waga kai alamun to ta gyara kwanciya a jikinsa tana lumshe ido.

Bayan wasu kwanaki.KRB3P055

Dad yana zaune a hakimce yana waya rai a Sace yana cewa, "Ai kawai ba sai ka zo ba, magana ce da zamu yi ta a waya. Auren Ashraf da Narma bana bu™atarsa kwata-kwata, gwara ka saka shi ya sake ta hakan zai fi."

Daga cikin wayar gwamna ya ce, "A'a Shatima, ba haka ya kamata a yi ba, ka bari na shigo Abuja mu tattauna in ya so sai mu tsayar da magana. Yanke hukunci a waya ai bai yi ba." Sen ya ce, "ni na nemi ayi auren nan kuma yanzu na nemi ya saketa. Ashraf ya yi disappointing dina, I trust him, that's why na Wauki auren Narma na bashi without any event or something related to marriage, amma sai ya dinga wu™alanta Narma, har ya kai ga ya saka an yi aborting Babynta. Ai kawai auren nan ya ™are, itama bata so, gwara ka saka shi ya sake ta kawai."

Gwamna ya ce, "bai kyauta ba gaskiya, Amma ina so mu zauna mu yi magana sosai, a ganina abin zai fi akan mu tattauna a waya."
"Kana jina? I don't want to our relationship to fall apart because of our children's marrige. That's is why I just want to him to divorce her." Gwamna ya ce, "gaskiya ne, shikenan Sen zan turo shi zuwa anjima zai sake ta in sha Allah. Ka bawa Narma ha™uri."

Dad ya ce, "kar ka damu, wannan abinda ya faru ba zai taSa friendship Win mu ba." Sallama suka yi Dad ya kashe wayar ya kalli Mum da ta shigo a lokacin ta zauna ya ce, "Zai turo shi in anjima zai kawo divorce paper ta Narma." Mum ta yi murmushi ta ce, "hakan shine daidai. Mun samu Narma ta dawo hayyacinta bazan so na sake rasa ta ba."

Narma ce ta sauko daga sama, Dad ya kalle ta ya ce, "Zo nan Narma." Ba musu ta ™arasa inda yake ta zauna. Da farin ciki akan fuskarsa ya ce, "Yau Ashraf zai kawo divorce paper Winki." Murmushi ta yi a yangance ta ce, "glad." Dad da mamakiya ce, "ahh....! is that all you have to say? Ina tunani zan ga fuskarki with so excitement sai na ga akasin haka."
"Dad you pushed me into this marriage knowing I don't love him, yanzu kuma auren yana ™o™arin ™arewa, What did you expect me to say Dad?."

Dad ya ri™ota ya ce, "Haba Narma, na Wauka wannan duk ya wuce kuma, yanzu mu yi facing abinda zai faru nan gaba bayan ya sake ki. What country are you planing to go for your phd?." Narma ta yatsine fuska ta ce, "Dad, I'm not ready for a phd right now, In fact I'm even not interested in further studies. My masters digree is sufficient for my career goals."  Mum ta ce, "but why Narma?."
"Kawai Mum, i'm not interesting."
"Amma zaki iya karatun zai Webe miki kewa."

Narma ta ce, "bana so." Dad ya ce, "is okay." Narma ta cigaba da danna wayarta bata ce komai ba tana ji suna tattauanwa.

Kamar yadda mahaifin Ashraf ya faWa kuwa ba jimawa Ashraf ya zo gidan da alama yana cikin garin Abuja, har cikin falon ya shigo ya samu Narma ce kaWai a zaune tana danna waya. Kallon ta ya yi itama ta kalle shi ta Wauke kai kamar bata ganshi ba, ya zauna yana binta da wuala™antaccen kallo kafin ya ce, "Finally I've divorced you after satisfying my desires, so u have no further use for me. Here's your divorce paper" ya faWa yana mi™a mata takardar sakin.

Dad da Mum da suke jin abinda ya ke faWa Mum ta ™araso ta ce, "ya yi kyau Ashraf, har cikin gidansu ka ke zuwa kana faWa mata wannan maganar banzan? Gaskiya baka da mutunci baka san mutunci ba." Ashraf ya kalli Mum da take sakkowa daga sama, kafin ya yi magana Dad ya ce, "shikenan ko? So get out!."

Ashraf ya ce, "Dad zan fita, but let me make you know one thing; in dai a kan tarbiyyar shigar da ku ka Wora Narma a kai kenan babu wanda zai aureta tsakani da Allah. I married her for her physical appearance, and now I've gotten what I want. Dan na sake ta bazan ji komai ba, daman ba ita nake so ba. Da farko na Wauka ina sonta, sai bayan na aureta na gane ikram nake so, Narma kuma jikinta nake so da ya kasance a bayyane ko yaushe......" ya dawo da kallonsa ga Narma da take kallonsa ya ce, "Dan haka ki yiwa kan ki faWa, if not zaki ta aure kina fitowa wallahi, kowa da ya samu abinda yake so a tare dake kamar ni zai gama dake, da zarar ya gama da ke kuma saki ne zai biyo baya."

Dad ya fusata sosai ya ce, "Ashraf get lost!." Ashraf ya Waga hannu sama alamun surrender ya ce, "Na tafi, bye my ex wife" ya faWa yana mata bye-bye ya fita daga falon. Šaukar paper da ya ajjiye Mum ta yi ta karanta ta kalli Dad ta ce, "Dan wula™anci har saki uku." Dad ya ce, "ai gwara haka, gwara da ya yi haka dan ya tabbatar da baza ta sake komawa gare shi ba."

Ya kalli Narma da bata ce komai ba ya ce, "shikenan ko? Na raba auren da na haWa ko Daughter?" Ya faWa yana smiling. Narma ta kalle shi fuska babu walwala ta ce, "Dad do you want to me to be happy?."
"absolutely my Love! your happiness means everything to me. I want you to be happy and fulfilled in life."
"Please allow me to married Faruk, I'm still have strong feelings for him. If you refuse it like you did previously, it will deeply affect my happiness." Mum ta ce, "Tiger again! Narma what are you saying?."

"Gaskiya Mum, ina faWar gaskiya ne kuma shine abinda yake zuciyata" tana faWar haka ta bar falon ta hau sama da gudu. Mum ta ce, "har yanzu bata bar tunaninsa ba fa, wai wannan wanne irin bala'i ne haka? Wanne irin asiri ya yiwa yarinyar mu?." Dad da ya yi shiru ya kalle ta ya ce, "kar ki damu, da ta sake dawowa daidai zata dawo hankalinta. Ki nutsu, kema kin san auren ta da shi ai ba abu ne da zai yu ba, itama faWa take yi amma ta san ta fi ™arfinsa, ba sa a aurenta ba ne."

Mum ta ce, "Narma da gaske take Sen, Narma da gaske take, kana jin yadda take magana ka san daga zuciyarta ne." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya hau sama shima, amma yana tunani a zuciyarsa ya zama dole ya samar mata de farin ciki ko ta wacce hanya ne. Kamar yadda ya Sata mata yana so ya faranta mata ta hanyar yi mata abinda

Please Login or Register in order to submit comment