Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta girgiza kai ta ce, "a'a ba magana zan yi ba daman." Omar ya bita da shu'umin kallo ya ce, "sai kin faWa." Nayla dariya ta sake kubce mata ta ce, "Allah babu."

Omar ya ce, "wa zaki yiwa wayo? Tsaf na fahimci karatunki, na san inda tunanin ki ya tafi. Ban da abin ki Jidda shima inda kike tunani kamar baza a iya kyautarsa ba, tunda dai nace komai ki ke so zan bayar ai sai ki gwada......" Nayla ta rutse ido ta katse shi ta ce, "Ka rufa min asiri, ka bar maganar nan" ta faWa tana dariya sosai.

Omar ya murmusa ya ce, "an™i a barta. Murmushi tayi ta kawar da waccan maganar ta ce, "Zan je na Wauko bed Win Musliha." Mayar da ita jikinsa ya yi bai ce mata komai ba itama bata ce ba.

Yana jin daWi in tana kwance a ™irjinsa, yana jin farin ciki da nutsuwa tare da kwanciyar hankali a duk lokacin da ya haWa jiki da ita, koda yana cikin damuwa da zarar ta kwanta a jikinsa sai ya ji komai ya yaye. Ya kan tuna abinda ya manta a lokacin da ya saka Nayla a ™irjinsa, ya kan samu ilimi na iya sarrafa harshe a lokacin da take kwance a jikinsa, ya kan ji kamar shi kaWai ne kawai a duniyar saboda yadda ko ina na jikinsa ke amsawa. Sai da ya gaji da kansa ya cikata ta fita ba jimawa ta dawo ta Wora Musliha akan gadonta shi kuma ya jata suka kwanta.

Omar ya shiga yamutsa ta yake yi yadda yake so, ™hamshinta ya gama ruWa shi, yayi tasiri wajan sakawa ya fita daga hankalinsa, da™yar ta samu ya nutsu ya kalle ta ya ce, "yaushe zaki gama hidimar haihuwar."

Nayla tana kwance a jikinsa tana dariya ta ce, "wai hidimar haihuwa, jego ake cewa."
"To shi Win."
"Nima ban sani ba, sai jinin ya tafi."
"Allah ya shiga tsakanina dashi."
"Kai YaMar, ai ko na gama ban warke ba."
"Ciwo ki ka ji?."
"Ciwuka ma, har fa Winki aka yi min."
"Wancan lokacin ma ai an yi miki Winkin ko? Lokacin aka ce na yi Sarna na raba ki biyu." Dukansa tayi tana dariya ta ce, "Bana so."

"Ai ba ™arya na yi ba, haka aka ce an yi miki Winki, kuma nima na gani."
"Ka ga me?."
"Šinkin mana, naga inda na farka aka Winke, ni da basu Winke bama da yafi min." Ta Soye fuska a ™irjinsa ta ce, "in ba a Winke ba ai da matsala, aure zaka ™ara ka barni." Yayi dariya kaWan ya ce, "babu wata matsala, daman ba kaWan ya yi min na farka ba? To meye na matsala kuma?. Daman ni na farka kuma zan cigaba da amfani da kayana.."

"kana bani kunya Rouhii." Ya taSe baki ya ce, "Aikin kenan ai, da an yi magana ki ce kunya. Magana ta baki kunya, a aikace ki ji kunya, a waya kunya, ko yaushe a cikinta ki ke. Ko meye ma kunyar oho. Duk yadda naso na rage miki kunyar nan kin ™i ko? Shikenan zan kama ki ne" ya faWa yana kissing wuyanta.

"Šazu Didi ta ce min ka je wajan Abiy."
"Uhum, yana gaisheki."
"Ina amsawa." Ta yi shiru tana jira yayi magana bai yi ba sai ma sake ri™ota jikinsa da ya yi yana lumshe ido alamun bacci zai yi. "Rouhi!."
"Uhum."
"Meyasa Abiy ya kiraka?." Ya buWe ido ya kalle ta yana Waga riga ya ce, "Sai da dalili zai kira ni?." Ta ce, "A'a."
"Amma ki ka tambaya?." Shiru tayi bata ce komai ba ya ce, "akwai dalilin zan faWa miki, yanzu bacci zan yi." Zata yi magana ya saka ta tayi shiru duk da ba haka ta so ba.KRB3P103

Abiy bai faWawa Senator yadda suka yi da Omar ba, sai da ya kira shi ya tabbatar masa da yana gida sun dawo da Narma a safiyar ya saka shi ya je gidan kai tsaye. A falo suka zauna shida Mum da kuma Senator.  Abiy ya ce, "Sen na samu Omar da maganar bayan ka tafi, na kira shi har gida kuma ya amsa ya zo." Dad a ™agauce ya ce, "Ya amince?." Abiy ya girgiza kai ya ce, "Bai amince ba, ya ce min shi bashi da ra'ayin aurenta kuma bazai aureta ba, yana kallon ta matsayin wacce ta shigo rayuwarsa ta fuskar silar rabonsa kuma ta fita."

Mum a sanyaye ta ce, "amma Narma tana cikin wani yanayi saboda shi."
"Duk na faWa masa, amma ya ce gaskiya bashi da ra'ayi kuma bazai yi ba." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu haka zamu bar Narma a cikin wannan yanayi mara daWi? Yau da safe mu ka dawo daga asibiti ko magana bata yi ba har yanzu, Ina jin tsoron rasa Narma Captain" ya faWa cikim rauni yana kallon Abiy.

Abiy ya ce, "Ha™uri za ayi a cigaba da yi mata addu'a Allah ya kawo mata mafita." Dad ya yi shiru cikin tunanin rabon da ya yiwa Narma addu'a har ya manta, bai taSa tsayawa yace zai yi mata addu'a akan abinda yake damunta ba. Sai kuma ya yi tsaki ya ce, "illar neman alfarma a wajan ™ananun mutane kenan, in ba dan kar na rasa Narma ba me zai kai ni wajansa balle har ya yi min wannan wula™ancin?."

Abiy yayi murmushi ya ce, "Ka san meye matsalar? Ka ™i shi a lokacin da ka ke ganin shi ba kowa ba ne, ka wula™anta shi, ka nuna masa bashi da wata daraja tunda bashi da ilimi kuma ga yanayin da yake rayuwa a lokacin. Ba ka hango abinda zai iya faruwa a rayuwarsa ta yanzu ba, baka hango zai iya zuwa ya wuce matakin da ka ke kai a rayuwa ba. Ai ilimi ba shine cigaban rayuwa, mutane nawa mu ke dasu wanda basu da ilimin amma sun fi masu ilimin capacity?. Yanzu shi ka duba shi, iyakacinsa secondary school, amma a yanzu haka akwai masu Digree da masters a ™ar™ashinsa wanda yake biya salary da aljihunsa. To a nan waye ya yi nasara kenan? Masu ilimi ko kuma wanda Allah ya sakawa albarka a lamarinsa?."

Dad ya yi shiru bai ce komai ba Abiy ya ce, "ita rayuwa ta duniya a duk yadda ka samu kan ka baka raina mutum, dani, da kai, da kowa ba mu san me zai faru gobe ba, dan haka baza mu yanke hukunci akan abinda zai faru a rayuwar wani ta gaba ba. Inda a lokacin ka amince ka bashi aurenta a lokacin kana da damar da zaka mayar dashi yadda ka ke so, kana da kuWi, kana da iko, zaka iya saka shi ya zama daidai da ra'ayinka. Kuma inda ka yi hakan a lokacin da siyasarka ka sake gyarata, tunda ku ´an siyasa a ko yaushe kuna neman abinda mutune zasu gani su yaba koda ku bai mu ku ba. Yanzu koda yana son Narma bazai karSi aurenta ba, saboda zai ga da da yake a yadda yake baka bashi aurenta ba, sai yanzu da ya taka wani matsayi a rayuwarsa. Da mutuwa, da aure, da arzu™i, da rabo ai ba a yiwa wani gorin rashinsu, domin kuwa lokaci kowa yake jira, in dai akwai rai bazai tsallakeka ba."

Dad ya sauke numfashi ya ce, "Wannan ya wuce Captain, yanzu zamu kalla."
"Na faWa maka abinda baka sani ba....a lokacin da na karSe shi a hannunka suka zo har gida suka yi min godiya da sauran abinda ya biyo baya. Ashe nima yarinyata Nayla ta shiga irin abinda Narma ta shiga a kansa, ma'ana tana yi masa tsananin son da bana tunanin Narma ta yi masa irin shi."

Dad ya kalle shi da mamaki ya ce, "Nayla dai?." Abiy ya ce, "tabbas ita."
"Kaga kenan asiri yake yi musu ko?." Abiy ya ce, "har yanzu kana kan batun asiri ashe? Har yanzu baka amimce Allah ne yake sakawa bawansa soyayyar wani a duk lokacin da ya so hakan ba?."

Sen ya yi shiru bai ce komai ba, Abiy ya ce, "Babu asiri, haWuwar jini ce kamar yadda na faWa maka a baya. Su mata suna son namiji irinsa mai kyau a zahiri da halitta irin ta sa. Sannan yanayinsa da komai su ya burge su, baka isa ka canja musu zuciya ba, Allah ne ya saka musu babu yadda zasu yi. Su kansu kasa sarrafa kansu suke yi balle wani ya sarrafasu."

Abiy ya kuma cewa, "Duk da a lokacin raina ya Saci akan abinda Nayla ta yi, amma daga baya na zauna nayi nazari naga ™addararta ce a haka, kuma dole sai ta faru. Nayla ta zama matarsa tun a wancan lokacin, tun bashi da gidan da zai zauna da ita ta amince zata zauna dashi na kuma yarje mata ina yi mata addu'a. Yanzu batun da nake maka Nayla ta haihu dashi, gidan da bai mallaka ba yanzu ya mallaki gidan da ko kai da kanka sai ka zauna a ciki ba ´arka ba."

Mum da mamaki da al'ajabi ta ce, "Like seriously? kana so kace yarinyar da mu ka gani tare dashi a airport ´arka ce?." Abiy ya girgiza kai ya ce, "itace, wannan ganin da ki ka yi musu zasu tafi Saudia su yi umra." Mum ta ce, "Kaga da zai amince ya auri Narma abin ya zo da sau™i, tunda ´arka ce baza a sha wahala da ita wajan amincewa ta zauna da Narma ba."

Abiy ya ce, "shiyasa na kira shi da kaina na yi masa magana amma ya ce a'a. Mijinki ya sanni, bazan yi masa ™arya ba, bazan yi masa ™arya akan abinda ban yi ba. Da gaske na yi magana dashi amma ya ce shi sam bazai amince ba. Ba haihuwarsa nayi ba balle nayi masa dole, ko wanda na haifa ban yi musu dole ba balle shi."

Dad da mamaki ya gama cika masa zuciya ya sake cewa, "Da gaske Nayla ´arka itace matar Omar Tiger?." Abiy ya Waga masa kai Sen ya ce, "Da gaske kuma tun a baya ka bashi aurenta?."

"Kamar yadda ka ji na faWa. Ni ban raina shi kamar yadda ka raina shi ba, na bawa ´ata abinda take so wanda na ke fatan zai ya kawo mata farin ciki da take burin samu a gidan aurenta. Kuma tun kafin ya zama haka take cikin walwala da farin ciki, babu abinda ta nema ta rasa a tare dashi. Yana yi mata son da baya yiwa kansa, ya kan iya sadaukar da komai na rayuwarsa a kanta, saboda kawai yana sonta sosai. Ko a lokacin da aka yi auren ko Waya ban ga laifinsa ba, laifin Nayla na gani. Amma kai a lokacin da yaje wajanka laifinsa ka gani ba laifin ´arka ba."

Dad ya Wan taSe baki yana girgiza kai ya ce, "Shiyasa bazai amince da Narma ba, saboda ´arka yake aure. Zai ga in ya auri Namra baza ka ji daWi ba." Abiy ya yi murmushi ya ce, "Ko kaWan ba haka bane, Narma itama ai ´ata ce, zan iya yi mata fighting na nemar mata da farin ciki kamar yadda zan yiwa Nayla. Da a bashi aurenta baya sonta gwara a ha™ura, tunda har ya furta gwara a ha™ura a yi mata addu'a. In kuwa mu ka dage akan sai anyi auren ko an yi auren bazata zamu wani farin ciki da take neman samu ba."

Abiy ya gyara zama ya fusankaci sanata sosai
ya ce, "Ko da nan gaba ba a raina mutum akan matsayin da yake kai, ba lallai sai ta hanyar neman aure ba, ta ko wacce hanya kar ka wula™anta wanda ka ke ganin bai kai wani matakin da ka ke so ba. Kamar yadda baka san me zai faru gobe ba a rayuwarka ba, haka baka san abinda zai faru a rayuwar wani ba. Allah yana sakawa sama ta dawo ™asa, farin ciki ya koma ba™in ciki, ba™in ciki ya dawo farin ciki, ba™i ya koma fari, haka zalika fari ya koma ba™i. Duk Wan adam ba ya kaucewa rabonsa, da zarar rabonka ya kira ka babu makawa sai ya same ka. Dukkan mu ai ba rana Waya muka farka muka ganmu a matakin da muke kai ba, a hankali rayuwar ta fara tafiya har muka zo yanzu. Ba a fara gini daga sama, daga ™asa ake farawa, a hankali sai ayi nisan zango. Komai yana da sila, komai yana da mafarki, komai yana da farko, komai yana da ™arshe."

Dad ya yi ajiyar zuciya kawai bai ce komai ba. Abi ya ce, "ku bata shawarar yin addu'a, ta koma ga Allah tana faWa masa kukanta zata ga canji a rayuwarta sosai." Dad ya girgiza kai bai ce komai ba, amma kalaman Abiy sun shiga zuciyarsa. Abiy ya ce, "Sen da kai da matarka ku dinga yi mata addu'a, ku cigaba da nema mata sau™i wajan Allah a hankali komai zai zama labari." Mum ta yi ajiyar zuciya ta ce, "haka ne, thank you." Abiy ganin haka ya mi™e ya ce, "Ni zan wuce Kaduna yanzu." Har bakin mota Sen ya rako shi Abiy ya shiga aka ja motar ya tafi ya bar shi cikin tunanin neman mafita.

    Bayan Kwana biyu.

Har aka kwana biyu Narma bata san labarin Omar ya™i yarda ba, sai da ta samu lafiya sannan Dad yake sanar mata dan ya rasa me zai ce mata gwara kawai ya faWa mata a huta. Dad ya ce, "Bazan miki ™arya ba Daughter, Omar ya ™i amincewa, har wanda yake jin maganarsa na je na samu amma ya ce shi sam baya so. Kuma wanda na samu da maganar ashe in law Winsa ne."

Narma a sanyaye ta kalli Dad ta ce, "Hakan yana nufin bazan zama matarsa ba?." Dad ya ce, "kusan hakan Narma, gwara ki yi ha™uri ki bar wannan tunanin ya wuce a rayuwarki. Ki cigaba da addu'a, zaki tafi Saudia ki je can ki zauna kina faWawa Allah damuwar ki." Narma ta yi shiru tana kallon wani waje daban kafin ta mi™e ta shiga Waki. Ganin bata nuna wani tashin hankali ba sai hankalinsu Mum ya kwanta suke fata da addu'ar Allah ya sa ta bar komai ya wuce su huta da wannan tashin hankali.

Safna ta kira a waya kasancewar ta zo Kano itama ta ce ta zo gidansu yanzu ta same ta. Ba jimawa Safna ta shigo Wakin Narma ta mi™e tsaye ta saka mayafi ta ce, "Zo ki raka ni waje." Safna ta ce, "ina?."

"Ki zo mu je." Tare suka fito falon Dad ya kalle su ya ce, "ina zaku je?."
Narma ta ce, "yanzu zamu dawo Dad, mu je" ta faWa tana yin gaba dole Safna ta bi bayanta ta shiga mota Narma ta shiga gaba suka fita daga gidan.

      A wannan lokacin Omar yana zaune sanye da kaya track suit kalar purple, Nayla tana zaune a kusa dashi haka Didi ma tana zaune dan ta zo duba shi kwana biyu ya yi rashin lafiya. Marmerh na jikinsa a kwance, Musliha tana hannun Didi tana bacci. Falon yayi shiru babu mai magana dan ya ce kansa ciwo yake baya son hayaniya.

Idanunsa a kulle suke kansa ya yi nauyi sosai ya yi shiru kamar babu shi a wajan. BuWe ido ya yi ya kalli Didi kamar zai yi magana sai ya fasa, ta ce, "me zaka ce?." ˜aramin tsaki ya yi kawai bai ce komai ba ya mayar da ido ya rufe. Nayla dai tana gefe tana danna waya hankalinta gabadaya yana ga waya, Umma Saroot tana yi mata bayanin kayan gyaran da ta bayar aka kawo mata irin nasu na mutanen Chad.

Didi ta katse shirun ta ce, "Omar zamu je Chad, akwai rasuwar da aka yi a can ya kamata a ce mun je mu ma." BuWe ido ya yi ya kalle ta ya ce, "Ina ne kuma Chad?."
"˜asar Chad mana, asalin ™asarsu Maman mu." Omar ya taSe baki ya ce, "A matsayinki na wa zaki je? Wa ki ka sani, waye ya sanki?. Didi kin cika shishshigi wallahi, ina guje miki shan duka wata ran" ya faWa murya a ™asa saboda kansa da ya yi nauyi.

Didi ta ce, "ai har da kai zamu je ba ni kaWai ba. Kakanin mu duk a can suke, kafin Kakarmu ta bar duniya na taSa ganinta sau biyu da ta zo nigeria, amma kai baka taSa ganinta ba. Akwai danginta a can sosai, ana son a sake ™arfafa zumunci ne, zamu je a madadin maahifiyarmu." Ya zuba mata ido har ta gama bayanin sannan ya taSe baki ya ce, "Sai kin dawo, amma babu inda Marmerh zata je. Danginki ne ai ba danginta ba."

Didi ta ce, "Sai mun dawo dai, ka daina batun Marmerh; har kai da Nayla da Musliha." Kallon baki da hankali ya yi mata, ko damar magana ma bata samu daga gare shi ba balle ya tanka mata, dan a ganinsa maganar bata da amfani. Didi a sanyaye ta ce, "Omar meyasa baza ka bari ya wuce bane? Ina guje maka ganin illar ri™o wallahi. Me za a yi maka da zuciyarka zata yi sanyi? Me za a yi maka da zai saka ka manta baya ka fuskanci gaba?." Omar da mamaki ya ce, "ikon Allah, ya ki ke so nayi musu? Goya su zan yi ko me zan yi?. Kin ce bana magana dasu yanzu ina yi, to me zan yi?."

"Ka saki jikinka dasu kamar kana tare da Mama, ka saki jikinka dasu Kawu kamar kana tare da Baba. Har Gombe mun je ziyara amma ka ™i zuwa. Don Allah ka yayyafawa zuciyarka ruwan ™an™ara ka ri™e danginka, wallahi baka da kamarsu a duniya."

Sake taSe baki ya yi, sai kuma ya haWe rai ya ce, "Har yanzu ina kallo wu™alancin da suka yi miki a lokacin da muka je gidansu, mu mun je da ™arfin guiwa muna ji a ranmu mun je dangin mahaifiyarmu, ashe dukkansu taron tsinstiya ne babu shara...."ya sake cewa, "Su kuma tsofaffin munafukan har yanzu akwai shatin dukan da suka yi min a jikina, yadda wannan tabon bai Sace daga fatata ba haka na zuciyata ma bazai Sace ba. Dan ma sun raina min hankali, a rasa yarinyar da za ace ina nema sai wannan koWaWWiyar, na tsani ganin fuskarta wallahi, Tsaf zan talitseta da mota wata ran. Ki basu shawara, duk inda suka san zamu haWu su daina bi wallahi, kamminta suna nan tsaf a idona, in muka gauraya za a yi Satacciya."

Didi ta yi masa banza bata tanka ba, tana ro™on Allah ya kawo ranar da zuciyar Omar zata yi sanyi, tana faWawa Allah ya kawo silar da Omar zai sauka daga wannan dokin zuciyar. Zata so taga ranar da zai yi sanyi ya karSi danginsu. Nayla kam bata ce tak ba kuma tana jinsu.

BuWe ™ofar falon aka yi aka shigo da sallama, tunda aka yi haihuwa ba a saka lock Win ™ofar saboda masu zuwa barka, kuma gate Win gidan ba a hana shiga sosai. A tare suka kalli wanda suka shigo gabaWayansu, gaban Nayla ya yanke ya faWi ta zubawa Narma ido tana kallon ta da tsananin mamaki.P104

     Didi mamakin ganin ta take yi, shi kam Wauke kai ya yi ya mayar da ido ya rufe yana ji kamar ya tashi ya zaneta, sun takura masa ya rasa ya zai yi da su. Narma ganin Didi a zaune sai ta samu ™arfin guiwa ta ™araso kusa da Didi ta tsuguna ta Wora kanta a cinyar Didi ta fashe da kuka. Dukkansu sun yi shiru babu wanda yake magana, sai kukan da take yi a hankali amma kana jin sautinsa.

Omar gajiya ya yi da jin kukan, a fusace ya ce, "Ke!." Ba ita kaWai ba hatta Nayla da Didi sai da suka firgita, Musliha da Marmerh da suke bacci suka buWe ido a firgice. Cak Narma ta tsaya da kukan ta kalle shi ta ga ita yake kallo da alama ita yake yiwa tsawar, ya ce, "Meye na kukan!?." Shiru ta yi ta kalli Didi murya na rawa ta ce, "Didi ki taimaka min, ki taimaka min zan iya rasa hankalina."

    Didi ta kalli Nayla da take kallonsu ta kalli Omar da ya mayar da ido ya rufe ta sake kallon Narma ta ce, "Narma me ki ke so nayi miki?." Narma tace, "Didi Faruk!." Didi ta kalli Omar ta sake kallon Narma ta ce, "Narma ya kamata ki manta dashi, rayuwar da aka yi a baya baza a yi ta yanzu ba."

"Amma Didi kin san ba laifina bane ba ko? Kin san bani da laifi akan abinda ya faru."
"Na sani, na san da gaske ki ke sonsa, amma ina so ki san wani abun in ya wuce ya riga da ya wuce kenan har abada. Wata damar tana zuwa sau Waya tak a rayuwa, da zarar ta wuce shikenan bazata dawo ba."

Safna da take tsaye a sanyaye ta ce, "Didi ki taimakawa ™awata ki saka baki Omar ya amince da ita, wallahi har a asibiti ta kwanta saboda soyayyarsa. Yau ne kawai ta samu lafiya ta zo inda yake." Didi ta kalli Safna ta ce, "wanne irin taimako zan yi mata? Ga Omar a zaune ai, ni babu ruwana a cikin wannan maganar."  Safna cikin dauriya ta kalli Omar ta ce, "Don Allah Omar ka amince da ita, wallahi tana tsananin sonka, ban taSa ganin Narma cikin rauni ba sai bayan ta fara sonka. Wallahi in ta rasa ka zata iya shiga wani hali, dan zuciyarta tayi rauni akan soyayyarka."

Safna ta kalli Nayla da take kallonsu ta ce, "Ki yi ha™uri Madam, mun rasa mafita ne, shiyasa mu ka zo gidanki ba tare da izini ba." Nayla bata ce komai ba Narma kawai take kallo, tabbas Narma ta canja itama ta gani, duk ta yi wani iri kamar ba ita ba, gayun nan da take ji dashi yanzu duk babu. Didi ta ce, "Omar ka yi magana." Bai buWe ido ba ya ce, "Me zan ce? Mahaifinta ya same ni na faWa masa bana ra'ayi, duk da haka bai ha™ura ba ya sanar da Abiy, shima ya kira ni na ce bana ra'ayi" ya buWe idanunsa ya kalli Didi ya ce, "yanzu kuma an kawo maganar wajanki, to me ake so nayi?."

Narma cikin rauni da sanyi ta ce, "Ina so na ji daga bakinka ne, dan na san baza ka guje ni ba." Ya tashi zaune sosai ya gyara Marmerh da take jikinsa, ya kalli Nayla ya ga ta zuba masa ido tana kallo, ya Wauke kai ya kalli Narma ya ce, "Gaskiya ki ke so na faWa miki?."

Ta Waga kai alamun eh, ya Wan cize baki kana ya ce, "Ni Omar bani da ra'ayin ™ara aure a rayuwata, in ma ina da ra'ayi bakya cikin matan da zan iya aura. Ban so ki ba kuma bana sonki, kin shiga rayuwata ne saboda haka Allah ya ™ulla, tunda ki ka fita kuma komai ya ™are...." Ya nuna ta da yatsa ya ce, "Yadda nake rayuwata kema ki je ki yi taki, ki daina bibiyata, ki daina zuwa inda nake!" Ya faWa yana kallon ta.

     Didi ta kalle shi jin kalaman sun yiwa Narma tsauri, a cikin wannan yanayi da take ciki da rarrashi ya kamata ayi mata magana ba da yadda Omar ya yi ba. Narma ta tsayar da kuka cak ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa a guje, cikin tsananin rauni da sanyi ta ce, "Da gaske baka soni ba? Da gaske baka sona?."

"To wacece ke da zan miki ™arya har ki ke so ki tabbatar? Amsa min wacece?." Narma ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai, ta Wago a hankali taga ita dai yake kallo alamun ta bashi amsa sai ta ce, "matsayin wacce ka fara so a rayuwarka."

Dogon tsaki ya ja ya kawar da kai yana girgizawa, haushi yake ji wata banzar bazawara tana cewa wai ita ya fara so, ya sake juyowa ya ce, "Ni Omar bana sonki, ban so ki ba, kuma bazan so ki ba. Kin shiga rayuwata kuma kin fita, shigarki rayuwata ya jawo canji a cikin ta ina gode miki a kan hakan. Wata™ila da ban san mahaifinki ba da haka bai faru ba, wata™ila da baki zo Kano an haWa ni dake ba da haka bai faru ba, wata™ila da baki ce kina sona ba da

Please Login or Register in order to submit comment