Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai damu ba ya wuce zuwa shago. Kowa mamakin ganin sa yake yi kuma ba a ji wani tashin hankali ya sake faruwa ba, kowa mamaki yake yi da labari bai zagaye gari ana cewa Tiger ya mayarwa da kura a niyar ta ba. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi yana kuma sane da kallon da ake masa kawai babu wanda ya isa ya tunkare shi da maganar ne sai dai kallon kawai.

Nayla ranar bata je aiki ba ita da aiki sai ranar monday, tana zaune kiran Didi ya shigo wayar ta tana Wauka a gigice Didi ta ce,  Nayla lafiya ki ke dai ko? Na ji labarin abinda ya faru jiya. Ina fatan dai kina lafiya?. Nayla a kasalance ta ce,  Lafiya lau Didi, Amma a tsorace nake sosai.
 Ina Omar Win?.
 Ni ban sani ba ta faWa murya na rawa sosai.

 Ki nutsu Nayla, babu abinda zai same ki. Bara na kira Omar Win naji abinda yake faruwa ta faWa tana yanke wayar. Nayla tayi ajiyar zuciya har lokacin zuciyarta bugawa take yi dan bata taSa ji ana cewa za a yi kisa a zahiri ba sai dai a film.

Abu na social media nan da na labari ya zaga ko Ina da ko wanne gari. Arewa bloggers suna ta rubuta an kaiwa Omar Tiger babban Wan daba mai murabus hari har cikin gidan sa ana yi yunurin kashe matarsa.

A can Madina a lokacin Mama tana zaune bayan sun dawo daga sallar juma a suna zaune ita da Abiy sai ga yaran nasu gabaWaya sun shigo Wakin Abiy gashe shi. Suna zaune ana hira Mama ta Wauki waya tana dubawa.

Mama ta ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! A tare duka suka kalle ta a gigice jin salatin da tayi Abiy ya ce,  lafiya?. Mama ta kalle shi ta kalli wayar ta ce,  Jiya da daddare an kaiwa babban Wan daba na jahar Kano mai suna Tiger hari har cikin gidansa, an yi yunurin kashe matarsa Allah ya taaita Mama ta faWa cikin sigar karanto musu abinda yake da rubuta.

Jidda ta ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! Mama Twinny! Ta faWa a gigice tana wara idanu waje. Mama a ruWe ta ce,  ku kira mana wayar ta da hanzari don Allah. Yaya J da Yaya Ahmad da Jidda har rige-rigen kiran wayar Nayla ake yi cikin tsananin tashin hankali.

Abin haushin gabaWaya basa samunta sai kira ake yi amma bata shiga. Yaya J yayi tsaki ya ce,  Ba a samun ta a waya. Abiy ya bisu da kallo ganin duk sun ruWe su ga masu ar uwa, ya yi dariya ya ce,  meye duk ku ka tashi hankalin ku haka? Abinda ta aura kenan daman, kuma kun san haka zata iya faruwa ko yaushe, to meye na Waga hankali kuna salati haka?.

Yaya ya ce,  Abiy batun kisa ake yi fa, kisa fa. Abiy ya Wauke kai bai ce komai ba. A lokacin Jidda ta same ta WhatsApp call tana Wauka ta saka a speaker ta ce,  Twiny lafiya ki ke dai ko? Yanzu mu ka ga abinda ya faru jiya a social media, kina lafiya?.

Nayla a sanyaye ta ce,  Lafiya lau nake Twiny, babu abinda ya same ni.
 Kin tabbatar? Ya na ji maganar ki haka kamar kin yi kuka?.
 Bani da lafiya Twimy, stress na aiki ya saka ni a gaba ga azumi, kullum a wahale nake yini saboda gajiya ga ciwon kai. Ina Abiyna? In kin je Wakinsa ki ce ina gaishe shi ina yi masa barka da juma a. Na yi masa missed call bai Wauka ba.

Jidda ta kalli Abiy da ya duba wayarsa bayan ya ji abinda Nayla ta ce sannan Jidda ta ce,  Yana jin ki, muna tare gabaWaya Mama ta ga abinda ya faru. Kuma babu wanda ya kula a cikin mu sai yanzu, da wani abun ya same ki tun a jiyan da sai yanzu zamu sani. Yaya J ne ya ce,  Nayla kin tabbatar lafiya lau ki ke ko?. Nayla ta ce,  Lafiya lau Yaya J, Ina Yaya?. Yaya Ahmad ya ce,  Nayla gani nan, gaskiya baki da lafiya Nayla? GabaWaya voice Winki ya canja, sannu kin ji, ki samu ki je asibiti a baki magani.

 Yaya Strees ne kawai wallahi, yau kuma da yake ban je aikin ba ma Ina gida bana ji daWin jikina.
 To sannu, Allah ya ara lafiya, Allah ya kiyaye gaba. Ki yi magana da mijin na ki gaskiya a san matakin da za a Wauka, bazai yu shi da aikata laifi hukunci da oarin shafar ki ba.

Nayla ta ce,  to Yaya. Ina Anty Halisa da Amma?.
 Sun shiga masallaci ita da Jalila, Amma kuma gata nan a wajena.
 To Yaya a gaishe su, a gaishe da Mama da Abiy. Mama sai a lokacin ta ce,  Nayla kina lafiya dai ko?. Tayi murmushi ta ce,  eh Mama lafiya ta lau, ki gaishe min da Abiy.


Abiy jin tana ta ambatar sunansa sai ya ji zuciyarsa tayi rauni ya ce,  Mamana ya ibada?. Nayla jin muryar Abiy da hanzari sai ta ce,  Abiy barka da Juma a, ya ibada?.
 Alhamdu lillah Mamana, yanzu na ga kiran ki na je masallaci.
 To Abiy. Allah ya amsa ibada.
 Amin ya fita daga nan bai sake cewa komai ba. Jidda suka yi sallama ta kashe wayar. Kafin wani ya sake magana a cikin su Abiy ya ce,  Ku bani waje zan huta kafin lokacin sallah.

Duk suka mie suka fita tare da jan ofar,bayan sun fita ya kalli Mama da take hawaye ya ce,  lafiya?. Ta goge ido ta ce,  Irin zargin da ake yi min akan auren Nayla da abinda ake faWa a kaina ne yake karya min zuciya. Yanzu tsakani da Allah meye amfanin auren irin wannan mutumin? Gashi tun auren bai je ko ina ba an fara neman rayuwarta akan abinda bata san ma anyi ba. Ni ban san Nayla wacce irin yarinya ba ce da ta nace akan wannan banzan mutumin ba wallahi, ka duba yanzu tambayarta ake yi amma sai maimaita lafiya lau take yi, kar ma ta ce ba lafiya ba ace za a raba su kenan ko?.

Abiy ya ce,  to waye ya ce zai raba su?.
 A yanayin Yaya da Jawad tsaf zasu iya raba auren nan in wani abun ya same ta. Shine take ta maimaita lafiya lau take, Ina jin wannan takaicin abin har zuciyata, ina jin zafin abin nan har ohon zuciyata. A haka ma bata samu shiga a wajansa ba har yanzu, har yanzu ko kallon arzui bata ishe shi ba, har yanzu baya kallon ta matsayin matarsa ya jingine ta a gefe kamar wacce aka kai masa ita ajiya, amma sai wani lafiya lau take maimaitwa. Nayla kamar ba ni na raine ta ba, ka duba Jidda da mijinta suna nan suna ibada, gabaWaya dangi ana nan ana ibada amma ita banda ita, kuma hakan bai dame ta ba. Allah wadaran naka ya lalace Mama ta faWa tana kuka.

Abiy ya murmusa akwai bai ce komai ba ya tashi ya fita daga Waki. Mama ta goge hawayenta da ta tabbatar ya shiga ta ce,  Nayla zama da Omar ai ko bakya so. Allah na tuba ka yafe min ina asa mai tsarki ina arya ta faWa tana tashi tayi alwala ta saka babban hijjabi ta fita itama.

Nayla kuwa bayan sun gama waya Abba ne ya kira ta, shima tambayar da yayi mata kenan ta amsa da lafiya lau. Bayan ta kashe Maman Kano anwar Abiy ta kira ta, bayan ta gama da ita Mama Sa adatu, bayan ta gama Baba. Har Daddy da suke tare da su Hajja a saudia sai da ya kira ta amsar da ta bawa su Jidda ita yake basu.

Ajiyar zuciya tayi bayan ta gama amsa wayar ta ce,  Nayla ar gatan dangi, kowa kirana yake ya ji lafiyata. wanwasa gate Win ta ji ana yi a tsorace ta tashi ta saka hajjisbi ta je ta buWe.
Mama Sa adatu ta gani ta rungume cikin murna ta ce,  Mama sannu da zuwa. Mama ta bita da kallo ta ce,  Duk da mun yi waya hankalina ya kasa kwanciya wallahi, kina lafiya?. Nayla tayi dariya ta ce,  lafiya lau nake Mama ta faWa tana kulle gate Win suka shiga ciki.

Mama ta bita da kallo ta ce,  Amma yanayin ki bai gwada lafiya ki ke ba, kalle ki fa. Nayla ta zauna kusa da ita ta ce,  Mama tun jiya daman bani da lafiya, stress na aiki ga azumi ya saka min zazzaSi.

 Ayya sannu, amma dai babu abinda ya same ki ko? Mun yi waya da su Yaya ya ce na taso nazo na duba ki. Da Abbas zan turo sai na ce bara na zo da kaina, ni kaina hankalina ya kasa kwanciya duk da mun yi waya sai nake ji kamar ba lafiya ki ke ba. Nayla ta ce,  lafiya ta lau wallahi Mama. Mama ta ce,  na ga alama. Amma ya aka yi abin ya faru jiya? Su waye haka suke son cutar dake har gida?.

 Wallahi Mama ban sani ba.
 Shi bai faWa miki ba?.
 Tunda ya fita ma bai dawo ba.
 Amma naga an ce ya kai su gaban hukuma an za a hukunta su, hakan da yayi daidai ne da bai Wauki hukunci a hannaunsa ba. Nayla tayi shiru bata ce komai ba.

Mama ta ce,  yanzu me ki ke so?. Nayla ta kwanta a kafaWarta ta ce,  Babu komai Mama. Mama ta rie ta tana shafa kanta a hankali cikin tausayinta da auna. Ita kuma Nayla ji take kamar ta kanta a jikin mahaifiyarta yake, shafa kanta da Mama take yi ya saka bacci ya Wauke Nayla.

Motsawa Mama tayi sai Nayla ta buWe ido Mama ta ce,  kwanta ki huta zan tafi gida, gobe ki zo mu sha ruwa gabaWaya. Idanunta a lumshe Mama ta tashi fita amma zuciyarta babu daWi bata so ta tafi ta barta.

Nayla ta jima tana bacci har biyar na yamma, sai da ta farka tayi sallar la asar ta fara lazumi saboda lokacin amsa addu a na ranar juma a.
(Lokacin amsar addu a na bayan sallar la asar a duk ranar juma a, lokaci ne mai matuar falala kuma addu a bata da hijjabi a wajan Allah. Duk abinda aka roa a wannan lokaci Allah ya amsa sai dai a jira lokaci. Lolacon amsa addu ar yana farawa ne bayan sallar la asar zuwa magriba, babu wanda ya san taamaiman arfe nawa lokacin yake shiga, abinda malamai suka sanar damu bayan sallar la asar zuwa magriba a tsakanin haka lokacin yake farawa. Allah ya bamu iko ya amsa mana buatar mu amin.)

Tashi tayi ta dafa tea kamar ko yaushe tana tunanin bayan tea me zata dafa ta ci? Ita in tana azumi bata iya cin abu mai nauyi shiyasa sai ta rasa abinda zata ci. Irsh ta gyara ta soya,
ta soya wai duk ta ajjiye. Dawowa tayi ta zauna ta cigaba da addu a a wajan har aka yi sallar magriba sannan ta yi sallah ta ci abinci ta sha magani.

Kamar ko yaushe bai shigo ba sai bayan sallar tarawee, ta shigar da kaya kitchen ta fito kenan ya shigo. Kallon ta yayi ya Wauke kai ita kuma ta ce,  an sha ruwa lafiya.
 Lafiya. Ba zato taji ya amsa hakan ya saka ta kalle shi sai taji ya ce,  jiya na ce ki rufe ofa, meyasa baki rufe ba?. Nayla ta ce,  kaina ne yake ciwo shiyasa na manta ban rufe ba.
 Kar ki sake kuskuren barin gidan nan a buWe, duk da babu wanda zai sake shigowa.

Nayla jin yana yi mata magana a tausashe ssi ta damu damar shagwaSa kamar zata yi kuka ta ce,  Don Allah ka daina tafiya ka barni ni kaWai, tsoro nake ji wallahi. ago ido yayi ya kalle ta jin yadda take magana kamar zata yi masa kuka. Share batun yayi bayan ya Wan murza goshinsa kamar yadda ya saba ya ce,  Ya ciwon kan?. Nayla wara ido tayi jin abinda ya tambaya ta kasa bashi amsa sai kallon sa da take yi dan bata yi zaton zai tambaya ba.

Ganin irin kallon da take masa na mamaki sai ya Wauke kai ya wuce ta. Motsawar da yayi zai bar wajan ya saka Nayla ta dawo daga duniyar mamaki ta ce,  na ji saui. Bai ce komai ba ya shiga Waki ba tare da ya kalle ta ba. Nayla daWi kamar ya kashe ta, ko babu komai yana damuwa da lamarin ta tunda gashi bai manta tana ciwon kai ba, lallai ana samun cigaba ta tabbatar addu ar da take yi ce Allah ya amsa mata.KRB3P012
Arewabooks@nanahaleema11.

A yadda take kwance kallo Waya zaka yi mata ka san bata da lafiya, idanunta a kulle yake sai juya kai take cikin ciwon kan da ya fi komai damunta a yanayin da take ciki. Ashraf ne ya shigo ganin yanayin da take ciki ya ce,  Baki da lafiya, dole mu je asibiti, Ta so mu je ya faWa yana Wago ta daga kwance.

 Jikinki ya yi zafi sosai. Cikin muryar marasa lafiya ta ce,  ka yale ni kawai, bana son zuwa ko Ina.
 Sai kin je, bazai yu ki dinga zama da ciwo ba. Ina son lafiyarki ko dan na samu abinda nake so. Miar da ita tsaye ya yi ya kalli kayan jikita, Riga da wando ne dogaye a jikinta na bacci ya yi tsaki ya ce,  gabaWaya kayan ki na banza ne baki da kayan kirki a rayuwarki. Yafa mayafin mu je ya faWa yana yafa mata mayafin.

Jiri take yi hakan ya saka ya rieta suka fito, kasancewar akwai motar da yake amfani da ita ta haya a gidan. Asibiti suka tafi aka karSe ta ganin yanayin ta babu daWi, aka kwantar da ita aka fara yi mata abinda ya kamata. Yana zaune a inda aka tanada domin jira, likitan ya fito ya bishi office ya zauna ya ce,  Narma Sagir. Yadda likitan ya furta Sagir Win ya bawa Ashraf dariya ya murmusa ya ce,  yeah.
 She s is your friance?.
 No. Dr ya kalle shi ya ce,  Your mistress?. Ashraf ya ce,  she s my wife ya faWa yana kawar da kai dan bai san me za a ce masa ba.

 She s pregnant. Ashraf ya wara idanu waje ya ce,  what? Ciki wata nawa kuma?. Likitan bai fahimta ba kasancewar ba hausa yake ji ba. Ashraf ya dafe kai ya ce,  How many weeks?.
 Three weeks. Ashraf yaja tsaki cikin takaici da bain ciki ya ce,  I m not ready to be a father, so abort the baby.

 Are you sure you re not ready for that?.
 Yes I m sure. And even my wife she s not ready for that. Likitan ya ce,  okay. Sign here ya faWa yana bashi wata takarda shi kuma ya saka hannu babu Sata lokaci.

Tashi likitan ya yi ya fita Ashraf ya ce,  ni ban shiryawa haihuwa ba, tana haihuwa zata daina burge ni ni kuma ban shiryawa hakan ba. Tashi ya yi ya biyo bayan sa zuwa inda Narman take, zuwa lokacin an yi mata allurar zubar da ciki, a gabansa cikin ya fara fita Narma na juya kai saboda ciwo su kuma nurses Win suna ta yi mata sannu har cikin ya fita. Cikin lokaci kaWan aka gama gyarata aka yi mata komai yadda ya kamata ta yi bacci.

Bata jima tana baccin ba ta farka tana kallonsa, Wan ciwo take ji kaWan a mararta, sai nauyin da kanta ya yi mata, bayan wannan babu abinda take ji a jikinta. HaWa ido suka yi ya ce,  Barka da tashi. Narma ta kawar da kai tana sauke ajiyar zuciya. Nurse ce ta shigo tana tambayar ta abinda yake damunta a nan ta fahimci an zubar mata da ciki ne.

Bayan fitar nurse Win ta kalli Ashraf murya na rawa ta ce,  you have aborted my baby Ashraf?. Ashraf ya ce,  yes, saboda bamu shiryawa zama iyaye a yanzu ba, shiyasa na saka a zubar na san kema baza ki so haihuwa a yanzu ba. Narma ta ce,  ka yi shawara da ni?.
 Ai ba sai na yi shawara da ke zan yanke hukunci. Na ga dai Wan nan nawa ne ko? Ni na yi silar samun sa kuma na ce bana so, meye na ki?.

Narma bata iya magana ba sai kallonsa da take yi cikin rashin sanin abinda zata yi. Ashraf ya ce,  Ban shiryawa zama uba ba a yanzu sai zuwa wani lokaci, bani buatar na yi shawara dake wajan zubarwa ko barin sa ya rayu.
 Amma ai a jikina yake, kuma ni ce zan ji ciwo a lokacin da za a yi aborting ko?.
 Yanzu wanne ciwo ki ke ji? Abortion ki ka yi a Texas ba a nigeria ba, na tabbatar bakya jin ko wanne ciwo yanzu saboda sun cigaba wajan kawar da ciwo. So kar ki damu.

Narma ta ce,  na gaji da zama da kai, haurin da nake yi saboda wani dalili nawa ya are, zama na a Texas ya are. Wayata da ka Wauke da passport Wina dole ka dawo min dasu na bar asar nan. Wajan iyayena zan koma, dole a raba auren nan, bana son sa ko kaWan.

 Za a raba auren da zarar na kammala abinda nake yi dake, har yanzu ban gama morar ki ba shiyasa bazan bari ki yi ciki ba. Akan me zan bar ki ki yo ciki? Kina yin ciki zai canja min halittar da nake matuar sha awa a tare dake, ni kuma bana so abinda yake burge ni a jikinki ya gushe.

Narma ta kawar da kai hawaye na sakko mata ta goge ta ce,  Duk su Dad ne suka jawo min wannan damuwar, da sun bar ni da wanda nake so duk da ba haka ba. Ina son Faruk, Ina son Faruk! Ta furta a hankali tana kallon wani waje daban.  Shi Wan daban yana sonki ne?.
 Yana sona, na tabbatar bazai yi abinda zai cutar dani ba. Zan bani dukkan farin ciki, zai bani abinda nake so bazai sani ni kuka kamar kai ba.

Ya yi murmushi ya ce,  Kina da tabbacin shima son gaskiya yake yi miki? Kina da tabbas akan yana jin sonki a zuciyarsa?. Kallon sa tayi da mamakin kalamansa, ya Wage kafaWa ya ce,  eh mana, ai ke kafin ki fahimci wanda yake sonki tsakani da Allah zaki jima wallahi, saboda da yawan mu duk sha awar ki muke yi ba so ba.

 Me ka ke nufi?.
 Abinda nake nufi a bayyane yake, nima da farko na Wauka Ina sonki ne sai bayan na mallakeki na fahimci ba so ba ne. Daga lokacin na fahimci wani abu da yake a tare dake ne yake burge ni ba zuciyarki ba ya faWa yana miewa tsaye tare da kallon ta ya ce,  tunda dai kin samu lafiya zan je na same su si yi discharging na ki su haWa miki drugs mu wuce gida, bazan iya zama a nan har gari ya waye ba, kar ki manta zan daui azumi ya faWa yana fita daga Wakin ya barta tana kallonsa zuciyarta a cushe babu daWi kwata-kwata.


*Abuja.*


 Ni fa shirun nan Narma yana saka ni damuwa, ya kamata a san abinda za ayi gaskiya Mum ta faWa tana kallon Dad da yake zaune shima. Najwa ta ce,  gaskiya Mum shirun ya yi yawa, ko a waya ba a samun ta sai dai in ka kira shi. Wanne irin zaman lafiya ne wannan da zai saka ta daina amfani da waya? Kowa ya san Yaya da social media, kwana biyu har cigiyarta ake yi saboda tashin ganin update Winta.

Mum ta kalli Dad ta ce,  Ka ji ai, ya kamata a san abinda ya kamata ayi gaskiya. Ni na gaji da shirun nan ban amince lafiya lau suke ba wallahi. Zan sake komawa domin na gano halin da take ciki.

Dad ya ce,  ni kaina shirun nan ya dame ni, Narma babu waya, babu social media ai kamar babu rayuwarta ne. Gaskiya akwai abinda yake faruwa. Mum ta ce,  bara na kira shi, su na san yanzu dare ne sosai ta faWa tana Waukar waya ta kira wayar Ashraf.

Ashraf ya Wauka daga can Sangaren ya ce,  Mum barka dai. Mum ta ce,  Barka Ashraf, ina Daughter take?. Ashraf ya ce,  Bacci take yi, bata jin daWi ne muka je asibiti aka bata magani. Amma yanzu bacci take yi.

Mum ta ce,  me yake damunta haka?.
 babu komai, ciwon kai ne.
 Ina wayarta?.
 Cewa take yi bata buatar amfani da waya shiyasa kwana biyu gabaWaya ba a jinta. Ta ajjiye wayar gabaWaya ta daina amfani da ita kwata-kwata.
 In ta farka ka tabbatar ka kira ni ka haWa ni da ita, bazai yu ta ajjiye waya a daina jin ta gabaWaya ba. Ka kira ni video call in ta farka.

Ashraf ya ce,  To Mum in sha Allah. Daga nan ta yanke wayar ta kalli Dad ta ce,  gabaWaya hankalina ya kasa kwanciya da wannan Ashraf Win, Ina ganin kamar akwai abinda yake yi mata shiyasa ko yaushe in aka kira sai ya dinga kawo excuse. Anya bazan tura Najwa zuwa can?. Dad ya ce,  ki jira ayi waya da ita Win, in akwai damuwa sai a tura ta, in babu kuma shikenan.

Mum bata ce komai ba Dad ya ce,  Na san Ashraf bazai yi abinda zai cutar da ita ba, yana sonta kuma yana aunarta sosai, kuma yana da ilimi ya san abinda ya kamata ace ya yi. Mum ta taSe baki ta ce,  ashe wannan Wan daban ya yi aure, Wazu nake gani a social media wai an kaiwa matarsa hari har cikin gida. Dad shima taSe bakin ya yi ya ce,  na gani nima, ai ba abin mamaki bane ko kashe matar tasa aka ce anyi, Mahaifin da bai san darajar kansa da aansa bane zai bawa wannan mahaukacin auren arsa.

Mum ta ce,  da mun biye ta haukan Narma da yanzu itace a wannan hali. Allah ka tsare faruwar hakan ko a mafarki. Dad ne akwai ya amsa da amin ban da Najwa da ta san da gaske Yayarta tana son sasai, ta tabbatar har gobe tana aunar kasancewa dashi da zuciyarta.

******

Nayla haka ta cigaba da rayuwa a gidan mijinta Omar, magana bata shiga tsakani su har gwara yanzu, in ta gaishe shi ko ta yi masa barka da shan ruwa yana amsawa, amma kafin ta ganshi Win ma ana jimawa sai dai ta ji motsinsa kawai.

angaren business ana ta kai takalma Kaduna, ana siyarwa ana kuma bada kuWi kamar yadda Nayla ta tsara, ita da Bashir suke yi ba tare da ya san ma ana yi ba har lokacin. Haka ma aikatan su na wajen aiki suna siya sosai daga hannunta shima ba tare da san ana yi ba. Kasancewar aramar sallah ta gabato mutanen Kano kwasar takalma kawai suke yi, abinka da an Kano basu iya yayin abu ba, siyan takalman ake

Please Login or Register in order to submit comment