Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mijinta yana da son yara sosai. Omar ya mi™e tsaye ya ri™o hannunta ya ce, "Ashiq da me zan biya ki ne? Kina ta bashi farin ciki a cikin rayuwata da duniyata, dame zan saka miki?. Cikina na uku kenan da kika Wauka, duk da wancan bai zo duniya ba amma shima ciki ne ko?." Yadda ya ™arasa maganar kamar yaro sai ya bata dariya ta ce, "ciki ne mana."

"Jidda ni rasa me zan miki da zai saka ki farin ciki, komai naki ni ki ke barwa." Ta yi murmushi ta ce, "Ai ni zaman da ka ke yi tare dani, da soyayyar da ka ke nuna min ita kaWai kawai ta ishe ni. Bana da bu™atar komai daga gare ka, soyayyarka kawai ta ishe ni. Ina jin kaina kamar gimbiya a duk lokacin da na tuna ni ce wacce ka ke so, ina ji babu kamar ni kaWai ce a cikin matan duniya, saboda soyayyar da ka ke min."

Sumbatar ta ya yi, ya ri™e fuskarta ya ce, "Allah ya saka min soyayyarki ban san lokaci ba, ina ji in na rasa ki bazan iya cigaba da rayuwa ba Jidda. Ina yi miki son da ban san adadinsa ba, ina miki son da zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan na zauna dake kawai. Amma duk da haka ina jin kamar akwai gurbin da ban cike miki ba, ki faWa min ko meye zan yi miki Jidda."

"Ko wanne gurbi ka cike min shi Rouhi, duk abinda nake so na mallaka daga gare ka. Soyayyarka kullum ™ara ™aruwa take yi, yadda ka ke nuna min tsantsar so kullum sake gaba yake yi, yadda ka ke nuna min tsantsar kula da soyayya ni ya fi min komai Rouhi!. Burina kawai kar ka yi min kishiya...." Ta ™arasa faWa a shagwaSe tana kallonsa. Dariya yayi tare da kissing Winta cikin tsananin shau™i da soyayya, cikin ™aramin lokaci suka fara gwadawa junan su soyayya mai tsayawa a zuciya, sun nunawa junansu tsananin soyayya mai yawan gaske wacce zata yi wahalar mantawa a rayuwar su.

Tana kwance a jikinsa ta Wago ta kalli fuskarsa taga idanunsa a lumshe kamar yadda ya saba ko yaushe ta ce, "Rouhi." Ya buWe ido ya kalle ta ta ce, "Mama ta ce na bata Musliha ta je Kaduna ko na sati biyu ne tayi sai ta dawo, amma na ce sai na tambaye ka in zaka bari. Zaka bari taje?."

Wani irin abu ya ji ya tsaya masa a zuciyarsa, ya zuba mata ido kawai yana kallo dan bai Wauka zata yi masa zancen za a tafi da Musliha wani waje ba. Ta san baya son yin nisa da ita, baya son ya yi nisa da ´arsa amma take yi masa zancen zuwa Kaduna kuma bai isa ya ce a'a ba. To ta ya zai ce a'a bayan babarta ce tace a kai mata ita? In shine shima bazai iya hana Didi ba, duk da zai ta yiwa Didi mita amma zai bata saboda itace uwa a gare sa, kamar yadda Mama take uwa a wajan Nayla.

Nayla ganin bai yi magana ba sai ta ce, "Rouhi in bazata je ba kana da ikon da zaka ce baza ta je ba, kar ka damu bazan ji komai ba. Lokacin da muna yara Mama ta ce Abiy baya bari a kai mu ko ina sai da izininsa, ko ni kai tsaye Mama bata cewa nazo sai in shi ya bar ni. Kana da ikon da zaka ce baza ta je ba Rouhi."

Ya yi ajiyar zuciya a sanyaye ya ce, "Jidda ina jin Musliha a kusa da zuciyata, Allah ya sani bana so tayi nisa da ni ko kaWan. Marmerh daman na san bani na haife ta ba, mahaifinta yana da ikon kai ta duk inda yake so ban isa na ce a'a ba. Amma Musliha...." Ya faWa yana ri™e hannunta ya ce, "Bana son yin nisa da ita Jidda, ita jinina ce, bazan iya jure tashon kwana sha huWu ban ganta ba....." ya sauke numfashi ya ce, "Amma bazan hanata ba, wajan Maman ki zata je, bazan ce baza taje ba, amma sai dan babu yadda zan yi."

Nayla ta bisa da kallo tana mamakin rashin kara irin tasa akan Musliha, wai sai dan babu yadda zai yi, ko kunya bai ji ba yake faWa mata haka bayan yasan gidansu zata je, yadda yake maganar irin an yi masa dolen nan. Lokaci Waya fuskarta ta canja itama, cikin rashin jin daWi ta ce, "A'a Rouhi kar ka damu, ba sai ta je ba. Nima na san ba ka son nisa da ita shiyasa ban amsawa Mama ba, na ce mata sai abinda ka ce." Ya shafa fuskarta ganin ta canja alamun bata ji daWi ba, ya san daman baza ta ji daWi ba, shi kam bazai Soye mata abinda yake ransa ba, bai saba Soyewa ba kuma bazai fara ba. Ya ce, "A'a Jidda, taje Win kema zaki samu hutun kula dasu. Daman Marmerh Abbanta ya ce zasu je garin su, itama Musliha in ta je Kaduna zaki huta ki raini abinda yake cikinki. Kar ki damu na amince ta je Win."

Nayla zata yi magana ya ce, "na ce taje, kar ki damu." Ta langwaSar da kai tana kallonsa ta ce, "Amma kamar baka so, har ka canja fuska kamar nace zan kaita inda za a cutar da ita, ko ina nace zan kaita ba gidanmu ba ban Wauka zaka Waure fuska ba. Kar ta tafi kazo kai tayi min faWan nan naka mara full stop, gwara a ha™ura tunda baka so." Ya yi murmushi yana shafa fuskarsa ya ce, "Ina so mana, gidan ku fa zata je. Ki shirya mata kayanta kawai. Yaushe zata tafi?."

"Gobe nake so."
"Allah ya kaimu." Ta amsa da amin. Yayi murmushi dan kawar mata da wancan rashin jin daWin ya ce, "Allah mai iko, kin ga tafiyar mu Mexico honeymoon zamu je ko?."
Ta yi ´ar dariya ta ce, "Honeymoon da ciki?."
"Eh mana, ai ya fi armashi." Tayi dariya ta ce, "to visa da ka yi musu fa?."
"Basu da rabo" ta kwanta a jikinsa suna hira kafin bacci ya Wauke su.

Washe gari kuwa aka haWa kayan Musliha aka sanar da Mama zuwanta. Bai iya bawa driver ya kai ta ba, da kansa ya kaita ya kuma dawo a ranar. Da daddare Marmerh ma ta tafi wajan mahaifinta ya rage sai su kaWai. A cikin gidan suka cigaba da shan soyayyar su kafin ranar Sunday su Waga zuwa Mexico.

Zuwan su Mexico ya buWe sabon shafin soyayya da tattalin juna, gabaWaya a honeymoon houseboat suka tare, jirgin ruwa mai Wauke da falo da bedroom harda kitchen. Ko ina glass ne a ta ciki kana kallon ruwa da jiragen ruwa da suke yawo a tsakiyar ruwan.

Zaman wajan ya yiwa Nayla daWi sosai, ta ji daWi matu™a, soyayya da sha™uwa ta sake wanzuwa a tsakaninsu. Sun sha yawo a ™asar Mexico kamar ba aiki ne ya kai shi ba. Ya tara hankalinsa da tuaninsa a kan Nayla, ya shagwaS ta, hatta wanka shine yake yi mata. Babu abinda take yi, girki shi zai yi ko ya siyo. Sun sangarce gabaWaya, tafiyarsu Marmerh da Musliha tayi musu daWi domin sun raya juna a cikin kwana goma sun kafawa juna tarihi a zuciyarsu. Kwanan su goma suka dawo bayan sun kallama abinda ya kai su a cikin ™asar.

Jama'a kamar wacce aka yiwa turare..? Novel ya™i ™arewa, gaskiya addu'a ake yi min=Ø)Ş>Øyİ

Ready to say goodbyes>Øyİ
Nana haleemad'şd'şKRB3P125

Kamar yadda ya faWa bayan dawowar su da kwana uku ranar juma a aka buWe company bayan gayyato manyan mutane masu matsayi. Gwamnan Kano da Sarkin Kano, da manyan mutane da ake ji dasu duk sun halacci taron buWewa. Turawa da ´an China duk sun halacci buWe kafataran company mai matu™ar girma da kyau, dan floor goma yake dashi.

Nan da nan labari ya zaga duniya da hotunan company. Ana ta saka albarka, ana yabo ana kuma burin son jin cikakken tarihin mallakin wannan company, wanda ya samu nasara cikin ™aramin lokaci a rayuwarsa. ³an uwa da abokan arzu™i ana ta taya su murna, a ranar sai kashe wayarsa ya yi saboda kiran waya da yake shigowa har bai san me zai yi ba.

Bayan an buWe company aka haWa dinner wacce za a yi don zama da mutane. Na haWa dinner gaggaruma wacce ta samu halartar manyan mutane. Ya so ya ce Nayla bazata je ba amma ta tubure sai ta je, ta dinga ™unci tana yi masa hauka-hauka har ya amince zata je. Zuwan su wajan dinner da shi ita, da Marmerh da Musliha da aka saka musu kaya iri Waya sai abin ya sake bawa mutane sha awa. (Can na gano ´an Kiran Rabo comments section an yi baje baje ana cin kaji, ´an Arewapen kam har sun fi ´an whatsapps za™ewa).

Hotuna kam ya dinga yawo a duniya ana faWar dacewa da kuma kyaun da suke dashi. Babu wanda yake fahimtar Marmerh ´arsa bace saboda kamar da take yi da Didi, ita kuma Didi dashi take kama. Ranar mutuwar Didi ta dawo masa sabuwa dal? ya dinga jin kewarta a zuciyarsa har sai da ya zubar da hawaye, domin da Didi tana nan da da ita za a yi komai cikin tsananin farin ciki. A haka dinner ya watse kowa ya kama gabansa.

A zaune ya zo ya samu Nayla da laptop Winta a gaba tana ta dannawa, ya zauna kusa da ita ya ce,  Aikin me ki ke yi haka?. Ta nuna masa screen Win laptop Win ta ce,  Gmail Winka nayi log in, mail aka samu daga ™asar Malaysia shine nake so na yi replay. Da mamaki yake kallon ta ya ce,  to sai ki yi replay with out my consent? Me suka ce?. Ta kalle sa tana turo baki ta ce,  abu ne na cigaba, ka jira su yi approving zaka gani ta faWa tana cigaba da typing.

Ya ri™e hannunta ya hanata cigaba da danna keyboard Win ya ce,  in bani da niyar yi fa? Abubuwa suna neman yi min yawa kar ki sake Wauko min wani aikin. Iya wannan ma na gode Allah. Nayla ta shagwaSe fuska tana kallon sa ta ce,  ni meye amfanina?.
 Ai na faWa miki baza ki dinga zuwa company ba.

 Nima ban ce zan je ba ai, amma ina daga gida zan dinga yin abinda ya kamata. Ka bar min Sangaren Malaysia a hannauna, zan iya handling komai ina daga nan ba tare da naje ko ina ba. Ya yi ajiyar zuciya yana binta da kallo tare da girgiza Sai ya ce,  Jidda ciki ne dake, ta ya zan bari kina zirga-zirga?.
 Babu inda zan dinga zuwa fa YaMar, kawai zan dinga taya ka aiki ne daga nan. In aikin ya yi maka yawa sai ka dinga tura min. shikenan fa

 Wai dole ne sai kin yi aikin nan?.
 Ina so nayi ne. Ajiyar zuciya ya yi baice komai ba, ya yi shiru ya kawar da kai. Nayla ta kalle sa ta ce,  in baka so na sai daina ta faWa a sanyaye tana mayar da fuskarta kalar tausayi. Murmushi ya yi kaWan ya ce,  ni na isa na ce haka? Ki yi abinda ki ke so Ashiq. Kawai bana so ki dinga wahalar da kan ki ne. Murmushi ta yi cikin jin daWi ko amsar ™arshe bata bashi ba kar ta jawo wata maganar ta ce,  godiya nake yi.

Kallon ta yake yi yana tuna abubuwan da suka faru a aurensa da ita da abinda ya biyo baya. Ta Wago ta kalle shi ta ce,  C.E.O exclusive Footwear by Tiger da kansa. Ya Wan cize bakinsa kaWan ya ce,  Ban taSa jin wanda ya iya faWar exclusive Win nan kamar ki ba, Wan sake faWa na ji. Ta yi dariya ta yi masa peackin cheek Winsa ta ce,  na ™i Win.
 Didi ce ta saka masa suna, itace take cewa ya kamata ace company ku yana da suna. Na dinga mamaki da ta ce company, gashi ya zama company a lokacin da bata duniya. Allah ya gafarta mata.

Nayla ta ce,  Amin ya rabbi. Ya kalle ta ya ce,  baza ki faWa ba?. Ta yi dariya ta ce,  Exclusive!. Ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce,  wai Omar Win Didi ne a wanna matakin ya kalli Nayla da take kallonsa ya ce,  Omar Win da baya jin magana, Omar Win da ko takardar kammala secondary school ba shi da shi, Omar Win da ya kasance mai zubar da jinin mutane, Omar Win da ya zauna a prison, Omar Win da marasa jin Kano suke jin tsoronsa saboda tsagerancin da yake dashi. Omar Win da bashi da kowa, Omar Win da ya rayu babu iyaye babu dangi, Omar Win da ya rayu cikin bahaguwar rayuwa, Omar Win da ake yiwa kallon Wan iska, Omar Win da ake ganin babu matakin da zai iya kaiwa a rayuwarsa& .. ya ja numfashi kana ya ce,  in ba Allah ba waye zai yi min wannan Jidda?. Ta kwanta a jikinsa ta ce,  Allah ne mai bayarwa a duk lokacin da ya so, ya hana a duk lokacin da ya so. Ya girgiza kai ya ce,  Haka ne Jidda. Amma ina mamakin yadda rayuwata ta juya daga ba™i zuwa fari, ko da yake ikon Allah ba abin mamaki ba ne.

 Daddy! Aka daga bayan su, suka shigo a guje su biyu suka faWo kansu. Nayla ta mi™e tana yatsine fuska ta ce,  Wayyo Marmerh kun buge min cikina. Da hanzari ya ce,  Marmerh me ku ke yi haka? Ya kalli Nayla ya ce,  Kina lafiya? Babu abinda ki ke ji?. Ta girgiza kai ta ce,  Babu komai, kawai na Wan ji zafi ne ta ri™e kunne Marmerh da Musliha ta ce,  Ku daina gudu, ko yaushe cikin gudu. Suka yi dariya suna sake kwanciya a jikin baban su.

Ya kalli Nayla sannan ya kalli Marmerh ya ce,  Kun ci abinci?. Marmerh ta ce,  mun ci Daddy. Ni ina so naci shawarma Daddy.
 To za a siyo miki yanzu. Ta yi dariya tana cigaba da wasanta. Omar ya Wauki waya ya bada umarnin a siyo a kawo masa gida. Ya kalli Nayla kafin ya yi magana aka kira wayarta, ta Wauki wayar ta saka a kunne, abinda ake ce mata ya saka ta kashe wayarta shiga instagram.

Sai ta fita da sauri ta shiga YouTube ta ce,  An yi update Win interview Winka, bara naje kalla na gani. Tashi ya yi ya shiga Waki ´a´ansa suna biye dashi, ita kuma tana kallon hirar da aka yi da mijinta. Murmushi take yi tana kallo yana amsa tambayar Waya bayan Waya cikin kamewa da cikakkiyar nutsuwar da Allah ya bashi, baza ka kalle shi ka ce shine Omar tiger na shekarun baya ba, dan gabaWaya ya canja.

 Kamar yadda mutane suka sani sunana Omar Usman Omar, ana ta kokwanto a duk lokacin da aka ce wannan Omar mai compony Exclucive Footwear By Tiger shine dai tiger da aka sani na shekarun baya. Tabbas ni Win ne ba wani ba, duk wanda ya san sunan tiger a shekarun baya tabbas wannan Omar Win shine a zaune a gaban ku. Allah yana arzuta mutum a duk lokacin da ya so a kuma ko yaushe, Allah yana bada duniya ga kowa ciki harda wanda basu amince da bauta masa ba. In Allah ya yi nufin Waukaka da azurta ka ilimin boko ko rashinsa bazai taka rawa a wajan ba, mutanen mu da yawa suna kallon wanda bashi da ilimin boko babu inda yake zuwa a rayuwa, babu matakin nasarar da zai taka, babu wanda zai san sa sai dai ya ™arasa rayuwarsa a yadda ya fara. Ilimi yana da matu™ar amfani a wannan duniyar, ilimi ya zama matakin ko wacce nasara a rayuwa, ilimi yana ™arawa mutum girma da matsayi da daraja a duk inda ya je.

 Ba yawan ilimin ba albarka ake nema, kamar yadda ake ta yaWa magana a kaina, wasu su ce ™arya ne wasu su ce gaskiya ne zan faWa da kaina a yanzu. Ni Omar ina tabbatarwa da duniya bani da koda takardar kammala secondary school har yanzu. Na yi karatu daga primary har ajin ™arshe secondary school, amma ban zauna na rubuta jarabawa ba. Da taimakon Yayata na yi karatun da™yar, bana son makaranta ko kaWan, itace ta dage a kaina kamar ita karatun zai amfana har sai da na kai ajin ™arshe a secondary school kafin na daina zuwa.

 Allah ya saka min albarka a karatun da nayi duk da ™an™antarsa, ya bani nasara da Waukaka a lokacin da ban kawo hakan ba. Ban gama koda secondary ba, amma a yanzu ina da wanda yake da matakin karatu na Phd a ™ar™ashina yana aiki ina biyansa. Ban ce ilimi ba shi da amfani ba, ina nuna muku albarkar da Allah yake sakawa akan abinda ya nufe ka dashi komai ™an™antarsa, in Allah ya saka maka albarka zaka kai inda baka yi tunani ba.

 Komai yana da sila a rayuwa, ko wanne rabo akwai ta hanyar da yake kiran mutum. Ni nawa rabon ya kira ni ta hanyar mace kuma na amsa. Kafin lokacin in za a shekara ana cemin ai ga abinda zai faru dani a gaba bazan yarda ba saboda ban yi koda wasa hasashen haka a rayuwata ba. Amma daga lokacin da na amsa kiran rabon, sai da rabon ya riske ni na manta da komai, canji ya zo min a rayuwata, na ajjiye duk abinda nake yi wanda ya kasance bashi da kyau na kama abinda nake da ™warewa a kai. A cikin shekarun da basu wuce uku na baya ba na fara aikin sarrafa takalmi, a cikin shekaru biyu baya nayi aure, a cikin shekara biyu baya na fara samun nasarar da ban yi tunanin zan same ta ba. Kafin a rufe shekara biyu na kai matakin da babu wani Wan Nigeria da ya taSa kaiwa.

 Shawarata ga matasa masu Wabi a irin ta Tiger, su ajjiye makamansu su kama karatu ko abinda suke da sani a kai. In kana ta™ama da wani Wan siyasa a ™asar nan saboda yana karSarka hannu biyu, ko yana yi maka kyauta ta ban mamaki, ko yana fito da kai daga wajan ´an sanda, ina so ka san na Wan lokaci ne, amfani yake da kai domin gina rayuwarsa da ta ´a´ansa, kai kuma yake tarwatsa ta ka rayuwar. Duk wani Wan siyasa da zai amfani da kai a tafiyarsa yana kallon ka matsayin mahaukaci, yana kallon ka matsayin dabba wanda bai kai darajar Wan adam ba. In kuma kuna ganin maganata ™arya ce ka je gidan Wan siyasar da yake baka goyan baya a duk Sarnar da ka ke yi ka ce kana son ´arsa da aure!.

Ready to say goodbye>Øyİ
Nana haleemad'şd'şP0126

Nayla ta tsaya tana kallon sa ganin ya yi wani murmushi, kafin ya girgiza kai ya ce,  A lokacin zaka tabbatar da matsayin da ka ke dashi a wajansa, soyayyar da yake nuna maka ta gaskiya ce ko akasin haka& .Zubar da jinin juna da ake yi ba daidai bane, ta addaci ne. Mutum ya kashe Wan uwansa saboda kawai basa shiri wannan babban zunubi ne, kashe-kashe juna da ake yi da tayarwa da ´an unguwa hankali saboda dalili mara tushe babban laifi ne a wajan Allah. Duk wanda ka kashe ha™™in mutuwarsa yana rataye a wuyanka, sannan sai Allah ya yi muku hisabi da kai dashi a ranar tashin alqiyama.

Ya ja numfashi ya cigaba da magana,  Duk wani matashi da yake son barin wannan faWace-faWacen, ya kuma shirya fita daga harkar ´an siyasa, ™ofa a buWe take a gare ni, ina da aikin da zan bashi wanda zai ri™e shi ya ri™e iyalansa ya kuma taimaki yaransa su yi karatu kar su tashi a irin rayuwar da iyayen su suka tashi.

 Na yi wannan rayuwar, na san kuma ya take, duk da Alhamdulillah, ina godewa Allah a ko yaushe da ya kasance duk tantirancin da Tiger ya yi, duk suna da tambari da sunana yayi a garin Kano, na kai wani mataki da duk tantirancin da wasu suke ji dashi in aka ganni watsewa ake yi saboda tsagerancin da nake dashi, duk da wannan hali nawa ban taSa kashe mutum ba. Na san dai na zubar da jinin mutanen da ban san adadinsu ba, wasu na saka su a jinyar da sai sun gwammace mutuwa suka yi, wasu na raba su da wani sashi na jikinsu, wasu na illata jinsu ko ganinsu. Da taimakon Allah da addu ar Yayata komai ya canja, na daina faWa na koma kai ™ara ga hukuma. Ina ro™on duk wanda wannan rashin hankalin nawa ya taSa haWa ni dashi ko ya haWa ni da wani a cikin danginsa, don Allah a yafe min kuskuren da na aikata cikin hauka da tsantsar rashin sanin darajar kaina.

 Ku ajjiye faWa da shaye-shaye, ku zo ku rungume iyawar ku, ko wanne Wan gaban yana da baiwa a duniya, akwai abinda nake dashi wanda baka dashi, akwai abinda ka ke dashi wanda bani dashi. Baza ka san baiwar da Allah ya yi maka kana zaune a gida, baza ka san baiwar da Allah ya yi maka kana ri™e da makami ba, baza ka san baiwar da Allah yayi maka kana gusar da hankalinka ta hanyar shaye-shaye ba. Zaka fahimci baiwarka ne in ka tashi ka mayar da hankali akan iyawarka, daga wannan lokacin zaka ga rayuwarka na canjawa tana zuwa matakin da baka yi tunanin zuwa ba.

 Kamar yadda na ce ina da vacancy da zan bawa duk wanda ya nutsu yake son mayar da rayuwarsa irin ta mutane. Zan taimaka masa wajan cikar burinsa, zan tallafa masa domin barin gurSatacciyar rayuwar da yake ciki. Wacce babu komai a cikinta sai ™azanta, fansa, bibiyar rayuwa da kasancewa cikin fargaba.

Nayla kasa ™arasa ji ta yi saboda kuka, kuka take yi sosai kamar wacce aka yiwa mutuwa, ta shiga comments section ta ga irin yabo da addu ar da miji ta yake samu, Didi kuwa tana ta shan addu ar samun rahamar Allah a kabarinta. Sannan ana jinjina masa akan yadda ya rayu da gwagwarmayar da ya sha, dan kaf labarinsa ya bayar har harin da aka kawo mata da rasuwar Didi. Mutane da yawa sun Wauki darasi alqawarin yin amfani da labarinsa wajan zama madubi a rayuwarsu.

Da gudu ta tashi zuwa Wakinsa, sai ganin ta ya yi ta shigo a guje ta rungume shi tana kuka mai ™arfi. Calmly ya ce,  Jidda meye haka? Ciki gare ki fa, in kika faWi fa?. Kuka take yi a jikinsa tana cewa,  Allah ya cigaba da taimaka maka, Allah ya Waga ka ka wuce matakin da ka ke kai yanzu. Allah ya baka abinda ka ke nema ya ji™an iyaye da Didi. Murmushi ya yi ya amsa da amin ya ce,  kema Allah ya saka miki da alkhairi, labarin Omar incomplete ne without you. Allah ya bar mu tare Jidda. Ta amsa da amin tana jikinsa tana kuka.

Ya Wagota ya goge mata ido ya ce,  Bana so naga kina kuka nan Jidda. Ina da kyautar da zan baki, kin shirya?. Nayla ta ce,  ko yaushe cikin baki kyauta ka ke, yanzu& ..
 Shiiii! Zo mu je ki gani ya faWa yana jan hannunta suka fito ta balcony, ya nuna mata wata ba™ar mota mai shegen kyau da tsada da take ajjiye a car park ya ce,  Tayi kyau?.

Nayla ta ce,  sosai ma kuwa. Ya Wauko key Win ya ce,  mallakin ki ce Jidda, KarSi key Win. Nayla ta kalle shi bayan ya saka mata key Win a hannuta

Please Login or Register in order to submit comment