Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye.KRB3P010

Nayla tana juyowa suka haWa ido dashi yana tsaye yana aiko mata da kallon tsakiyar ido, haka kawai sai gaban ta ya faWi, tayi saurin kawar da kai daga kallon sa a lokacin wanda ya sauke ta ya tafi. Tk da yake ™ofar gidan ya ™araso ya ce, "Antyn mu kawo na shigar miki da ita." Ba musu ta bashi key Win ta ce, "na gode sosai Tk." Gidan ta shiga ta zauna akan kujera zazzaSi gabaWaya ya mamaye mata fatar jikinta.

Da™yar ta iya samu tayi wanka ta canja kaya zuwa doguwar riga ta shan iska wacce take a tattare da roba a ™irji, ta saka hula ta kwanta akan kujera tana mayar da numfashi saboda zazzaSi ne a jikinta sosai. Bata tunanin zata iya koda dafa tea saboda yadda take bata jin daWi ko kaWan.

Sallamarsa ta ji kamar ko yaushe a ciki bata fito sosai ba, ta Wago ta amsa ya ™araso har inda take ya ajjiye key Win motarta da tk ya bashi akan table Win da yake kusa da ita. HaWa ido suka yi ta Wauke kai ya tsaya kafin yana kallon ta ya ce, "shi wannan Win waye?."

Babu zato babu tsammani taji maganarsa, hakan ya saka ta Wago ta kalle shi ba tare da tayi tunanin ita yake kallo ba. Janye idonta tayi ta mi™e zaune gabanta yana faWuwa matu™a ta ce, "Colleague Wina ne." Kamar bai ji me ta ce ba, yayi shiru yana zagawa da idanunsa ko ina na jikinta. Nayla ta diririrce ganin kallon da yake yi mata, murya na rawa ta ce, "Abokin aikina ne, bani da lafiya bazan iya driving ba shine ya kawo ni sai cleaner ya dawo da motar."

"Shi cleaner Win bazai kawo ki ba sai abokin aikin ki?." Da sauri ta sake kallon sa jin abinda ya sake faWa, fuskar nan ta sa tana Waure matu™a sannan babu a alamun wasa a tare dashi. Nayla gabanta faWuwa yake yi dan bai taSa tsayawa sun yi doguwar magana shida ita haka ba, ta sunkuyar da kai ta ce, "da a can zan bar motar sai daga baya aka yi tunanin cleaner ya kawo." Shiru ya yi yana kallonta ko motsin kirki baya yi, ya kafa mata ido kawai yana kallo ba tare da ya san asalin abinda yake nu™ur™usar zuciyarsa ba. Wanda ya ajjiyeta a motar kawai yake gani a idonsa, bazai ce ga abinda yake ji ba amma ya san zuciyarsa tayi nauyi sosai.

Nayla da taji shiru ta Wauka ya fita, hakan ya saka ta kalli inda yake suka sake haWa ido tayi saurin Wauke kai jikinta har tawa yake yi.

Sa™on Didi ya ajjiye mata ya ce, "Kar na kuma ganin hakan!" Ya faWa cikin kakkausar murya. Nayla saboda tsoro bai barta ta iya bashi amsa ba hakan ya saka shi ya ce, "sa™on Didi" abinda ya ce kenan ya bar wajan.

Nayla ta yi sauke ajiyar zuciya mai tsaho ta ce, "na kuSuta!. Iko Allah to shi wannan mutum me ya ke nufi ne? Kishi yake yi ko me oho?." BuWe abinda ya ajjiye mata take yi tana cewa, "nima ba a son raina hakan ya faru ba ai, babu yadda zan yi ne matan office Win duk sun tafi saboda matan aure ne ana sauri aje ayi girki."

"Wow!" Ta furta ganin pack mai kyau ta sako mata awara manya-manya wacce taji sauce har da mayonnise da aka zuba mata. Nayla tayi murmushi ta ce, "Wayyo Allah! na huta cin komai in an sha ruwa." Sai kuma tayi murmushi ta ajjiye pack Win ta ri™e haSa ta ce, "wai yanzu kenan kishina yake yi?..." sai ta girgiza kai ta ce, "A'a dai Nayla, ta ya zai yi kishin ki bayan ba sonki yake yi ba?. To amma meyasa ya nuna ya ji haushi har ya ce kar ya sake gani?." Sai ta sake yin ™aramar dariya ta ce, "Dole Twinny ta ji labari, addu'ar da suke yi min Allah yana karSa."

Tana zaune tana wannan tunanin aka yi kira ko addu'ar kusa da shan ruwa bata samu ba. Ruwa ta Wauko ta sha ta Wauki awarar guda Waya ta ci tana lumshe ido saboda tayi mata daWi. Sallah ta tayar bayan ta idar ta shiga kitchen ta haWa tea ta dawo tana sha tanacin awarar da tayi mata masifar daWi. Tana gamawa ta sha paracetamol ta zauna tana hutawa. GabaWaya abinda ya faru ya ™i fita daga kanta, ta lura kwana biyu yana iya yi mata magana ko dan ya saba da ganin ta ne dai oho.

Aiki take so tayi ta turawa ogan su amma baza ta iya ba saboda ciwon kai, tana nan zaune a wajan har aka yi i'sha ta tashi tayi sallah aka tayar da sallar tarawee. Bayan an idar da hijjabin jikinta ta fito babban falon dan ta Wauki alkur'anin ta da ta bari a kan table. Shigowarsa ta gani ta amsa sallamar da yake yi kamar baya so, wucewa take niyar yi ya ce, "tsaya."

Babu musu ta tsaya bata juyo ba kuma bata dawo baya ba. "A kausashe ta ji ya ce, "Ni zan zo na same ki kenan?." Jin abinda ya ce sai ta dawo da baya dan daman gudun kar ta yi laifi ya saka bata dawo ba. Leda ya ajjiye mata babba mai girma sosai ya nuna ledar da hannunsa ya ce, "ki Wauka" abinda ya ce kenan ya wuce Waki ya barta a wajan. Nayla ta Wauki ledar ta shiga zuwa ™aramin falon da ta saba zama dan ta fi sakewa a can.

BuWe ledar ta yi ta fito da laces masu shegen kyau guda uku, sai atampa guda uku, sai veils masu shegen kyau da tsada gida uku, ba™i da milk da blue kalar lace guda Waya, sai kuma takalma ™afa uku. Nayla kallon kayan take yi kawai tana murmushi a zuciyarta na jin wani farin ciki na mamaye ko Ina. Farin ciki ya gama mamaye zuciyarta, ji take yana zaga jininta yana shiga ko wanne lungu da sa™o sa jikinta.

A bayyane ta ce, "shine ya siya min kayan sallah? Kenan ya karSe ni matsayin matarsa? Allah na gode maka, Allah na gode maka da ka ke karSar addu'ata." Ita kaWai take surutai tana fito da kayan daga cikin ledar. Hannu na rawa ta shiga WhatsApp zata kira Salma voice call ta bata labari sai kuma ta dakata saboda kiran Didi da ya shigo.

Da murmushi ta Wauka suka gaisa Nayla ta ce, "Didi an kawo min awara mai daWin gaske, gaskiya na gode sosai ita kawai na ci. Daman yau na dawo da zazzaSi daga wajan aiki."
"Amma dai kin samu lafiya ko?."
"Eh ya sauka, daman gajiya ce."
"Allah ya ™ara lafiya."
"Amin Didi. Na gode sosai."

Didi ta ce, "kar ki damu Nayla. Yau ya kawo min ziyara ya kuma kawo min kayan sallah, ki ta ya ni yi masa godiya Allah ya ™ara arzu™i." Nayla ta yi murmushin jin daWi da annushuwar da take jin zuciyarta ta ce, "Amin Didi. Nima yanzu aka ajjiye min nawa, kaya masu kyau Didi naji daWi sosai." Diid ta ce, "To ya yi min ma balle ke matarsa? Allah ya cigaba da daidaita ku kawai, amma na faWa miki daman tun a baya da zarar kun saba shikenan komai ya ™are. Yana da matu™ar wahalar sabo ne kawai, amma da an saba wallahi sai kin yi mamakinsa, dan gani zaki yi kamar an canja shi gabaWaya."

Nayla ta yi murmushi cikin gamsuwa da abinda Didi tace dan itama ta fahimci haka. Didi ta ce, "A taya ni godiya." Nayla tayi murmushi Didin ma haka kafin ta ce, "Amma zaki samu Winki dai ko?."

"Didi bani da tailor a nan Kano ai, da dai akwai wanda zai kai min Kaduna ne tailor na ko ana e gobe sallah zai Winka min. To nan ban san kowa ba." Didi ta ce, "Ko Salma ki tambaya ta haWa ki da nata, ni na san nawa Winkinsa bazai miki ba, kin saba da na ku na manya." Nayla tayi dariya ta ce, "Haba dai Didi, in dai ya iya Winki ai shikenan."
"Ki tambayi Salma in zai miki sai ki bashi, in bazai miki ba sai na tambayar miki nawan in za a samu."

Nayla ta ce, "in sha Allah." Didi ta ce, "kinga tallan companyn na ku ake yi a arewa, Wazu nake yi masa maganar yake raina min hankali. Wai wanne talla? Na ce ban sani ba." Nayla tayi dariya mai sauti ta ce, "bai sani Win ba ai Didi. Tsakani da Allah ni da Bashir muka tsara komai na je tashar muka yi komai ba tare da ya sani ba. Kuma da yake ba kallon tv yake yi ba shiyasa bai san ma ana talla ba." Didi taji wani daWi ya mamaye mata zuciyarta, kana jin maganarta ka san taji daWin maganar Nayla ta ce, "Yanzu Nayla da kan ki ki saka aka yi tallan nan kuma ke kika Soye masa?."

Nayla ta ce, "Don Allah kar ki faWa masa, kin san halinsa ya ce na daina shiga harkarsa, in ya san ni na bada advert Win bazai ji daWi ba ™arshe ma ya ce a daina haskawa. Ni kuma nayi tsakani da Allah saboda kayan nasa suna da kyau sosai, advert shine zai saka su zaga ko ina a san da company."

"Amma kuWin da kika kashe da yawa, kwanaki naji ana zancen tallah nan ana kashe kuWi sosai."
"Babu komai Didi, duk cikin cigaban mu ne ai."
"Allah Sarki! Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya ki ya saka soyayyarki a zuciyar Omar."

Nayla tayi murmushi ta ce, "Amin Didi, Don Allah kar ki faWa masa." Didi ta ce, "ya kamata ace ya sani, ai abin arzu™i ne ai."
"A'a don Allah, na faWa miki ne ma saboda kar ki sake yi masa zancen bana so ya fahimci ma ana yi tunda ba kallon tv yake yi ba." Didi ta ce, "Shikenan Nayla bazan faWa masa ba, Allah ya biya ki ya baku zaman lafiya na har anda."
"Amin Didi. Yaushe zaki zo?."
"Ai sai cikin sallah in sha Allah."
"Ina so nazo kafin azumin nan ya fita."
"Allah ya kawo ki."

Nayla ta ce, "Amin ya rabbi." Didi ta ce, "ki fa isar da sa™ona, ki ce na ce ina godiya sosai." Tayi ´ar dariya ta ce, "a'a Didi ba da ni ba." Didi ta ce, "kina bada mata Nayla, Allah rashin sakewa nan da baya yi da laifin ki. Amma bara ayi sallah zan zo mu tattauna."

Nayla ta ce, "Didi ai marmari daga nesa ne." Suka yi dariya a tare kafin Didi ta kashe wayar Nayla ta cigaba da kallon kayan. Sai a lokacin taga kuWi a cikin kaya har dubu hamsin. Nayla ta wara ido tana irga kuWin ta ce, "Lallai su Damisa manya, an san a bada kayan sallah da kuWin Winki."

Salma ta kira a waya aka yi sa'a suna tare da Twiny hira ta bar™e a tsakaninsu tana basu labari da nishaWi su kuma suna ta tsokanarta.

Dawowarsa da taji ya saka ta kashe wayar ta tashi ta saka hijjabi ta fita da niyar yi masa godiya. A zaune ta same shi yana cin Apple da take hannunsa. Zama tayi a Wan Warare ta ce, "Na ga sa™o na gode Allah ya saka da alkhairi." Bata ji ya amsa ba daman ta san baza ta ji ba ta mi™e tsaye a lokacin Bashir ya shigo da kaya masu yawa.

Ajjiye kayan ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Antyn mu an sha ruwa lafiya." Tayi murmushi ta ce, "Lafiya lau, ya ka ke?."
"Lafiya lau." Daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce zuwa kitchen. Bash ya kalli Boss Win nasa sai ya ga kamar harararsa yake yi ya Wauke kai ya ce, "Tiger an kai kayan Abuja." Omar ya ce, "ya sanar da ni."

Bash ya ce, "Damisa muna ta samun alkhairi cikin kwanakin nan sosai, wani abokina ya ce ya kamata mu yiwa companyn register saboda ba a san inda zai je gaba ba." Omar ya kalle shi ya ce, "nayi wannan tunanin nima, amma ban san ya abin yake ba."
"Nima ban san a ina ake yi ba, amma in na tambaye shi zan sanar da kai, tunda har an fara karSar kaya ana sakawa a store gwara mu dinga yiwa takalman kwali da Rc number da komai."

Omar ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "in ka samu ka sanar da ni." Nayla da take tsaye ta fito daga kitchen ta ji abinda aka ce ta ™araso ta ce, "Zan iya magana?." Kallon ta ya yi kafin ya ce wani abu ta ce, "Rc number a nasan wani ma'aikatan da suke aiki a ™ar™ashin CAC inda ake yin number kenan, zan iya sakawa ayi number ba sai an nemi wani ba."

Bash ya ce, "shikenan faWuwa tazo daidai da zama Antyn mu, abu ya zo har gida." Kallon da Omar ya yi masa ne ya saka shi ya mi™e ya ce, "Damisa na koma company, sai ka shigo. Antyn mu sai da safe." Bai jira ta amsa ba ya fita saboda kallon da yake yi masa ya san ba kyau.

Bai motsa ba kamar bai ji ma abinda ta ce ba, ganin haka sai ta koma tana mamakin hali na wannan bawan Allah. Shi kuwa Omar gabaWaya haushi ta bashi, meye dalilin ta na zuwa yana tare da wani tana magana?, Ya saka ta ne ko kuma dole sai tayi magana Bashir yana wajan?. Tsaki ya yi yana nan zaune har goma na dare sannan ya mi™e ya shiga Waki. Kaya ya canja sannan ya sake fitowa ya same ta a tsaye tana Waukar ruwa a fridge har lokacin hijjabin yana jikinta.

Kamar zai yi magana sai ya fasa kawai ya fita dan ba a gidan zai kwana ba zai je ya saka su a gaba dole ayi aikin ko ba so. Har zai fita kuma sai ya da fasa ya dawo ya kalle ga ya ce, "ki rufe ™ofa." Abinda ya ce kanan ya fita. Nayla gabanta ya faWi a bayyane ta ce, "ba dai ba a nan zai kwana ba?." Sai kuma ta ce, "wata™ila zai dawo sai dare." Maimakon ta je ta rufe sai ta koma ciki ta kwanta saboda kanta na ciwo sosai.

Omar kuwa aiki ya saka ana yi sosai a company saboda sun karSi kuWi mutane kuma babu kaya sosai a ™asa ga sallah na zuwa. Ganin idanunsa dole ya saka ake yi ko ba a so, ya bada kuWi aka siyo abinci kar ma wani ya ce yunwa yake ji.

Da yake daren azumi ne kuma goman ™arshe mutane suna ta kai kawo ana tafiya masallaci baza ka ce dare ya yi ba. A lokacin Goje ya shiga shagon ya kalli Omar da yake zaune yana kaWa ™afarsa. Goje ya ce, "Damisa akwai matsala." Ya kalle shi alamun me ya faru. Ya ce, "Wannan yaron Kb wanda ka yi silar zuwan sa prison ya fito, ya kuma yi alwashi a akan ka ko matarka. Ya samu labarin auren ka yanzu haka an sanar dani sun taro mutane zasu tunkari gidan."

Omar kallon sa yake yi kawai jin abinda aka faWa masa, a hankali ya ce, "Meye sahihancin maganar?."

"Darr Damisa, bazan kawo abinda ban tabbatar ba. Na faWa ne dan mu kwashi kayan aiki mu je mu nuna musu zaren ba kalar yadin bane." Omar ya mi™e tsaye sai Tk da Bash ma suka mi™e ya Waga musu hannu yana kallon su ya ce, "a tabbatar da an gama aikin nan a daren nan, kar wanda ya biyo ni." Goje ya ce, "Amma Damisa zuwan mu yana da mahimmaci."
"Kar wanda ya biyo ni!" ya faWa yana nuna su da yatsa tare fita kai tsaye ya nufi gidan.

Nayla tana kwance a Waki ta ji wata ™ara mai ™arfi da hanzari ta mi™e zaune tana raba idanu, ta sake jin ™a™ar alamun ana ™o™arin buWe gate Win gidan da ™arfin gaske. Gabanta ya faWi ta dafe ™irji ta ce, "Lafiya ake dukan gate Win nan haka? Kai ashe na manta ban kulle ba" ta faWa tana mi™ewa da™yar saboda ciwon kai ta fito a hankali kamar munafuka.

Tana zuwa falon aka sake dukan ™ofar da ™arfin har lock Win ya cire tunda iya shi kaWai ne a jiki bata saka key ta kulle ba. Shigowar mutane take ji ana cewa, "Wallahi yau ko shi ko matarsa sai Waya ya ba™unci lahira. Ya yi silar zuwa mu prison shi ya zo yana zaune ya ma yi aure yana jin daWin rayuwa, na rantse da Allah bai isa ba yau sai ya ba™unci lahira." Nayla ta zaro ido gabanta ya faWi jikinta ya hau rawa a lokacin ta ji ana taSa ™ofar falon. Tsalle tayi ta koma da baya cikin matu™ar tsoro ta gudu ciki ta shiga Waki ta shige can ™arshe jikinta na matu™ar rawa tana hawaye.

Motsi da ta ji a Wakin ne ya saka ta Wagowa a razane ™irjinta ya buga ta sake zabura cikin tsananin tsoro kamar wacce ta zauce.KRB3P011

Nayla a gigice take matu™a hakan ya saka suna haWa ido da Omar da ya shigo Wakin a karo na farko ta diro daga kan gadon a hanzarce, cikin sacannin da bai wuce biyu ba ta zo inda yake ta ri™e shi jikinta na rawa tana faWin,  Tsoro nake ji, tsoro nake ji ka taimaka min zasu kashe ni. Yadda jikinta yake rawa zai tabbatar da gaske a tsorace take bata cikin nutsuwarta. Ta ri™e masa riga gam hannunta sai rawa yake yi sosai.

A karo na farko da hannunta yazo jikinsa shima na sa hannun ya je jikinta, duk da shima baya cikin nutsuwa hankalinsa a tashe yake yana tunanin ko wani abun ya same ta ya dawo gidan, sai da yaji haWuwar hannunsu a waje Waya a jikinsa da zuciyarsa, duk da hannun nata rawa yake yi amma hakan bai hana shi jin ba™on yanayi a tare dashi ba.

 Babu abinda zai same ki, ki nutsu ya furta a tausashe yana kallon yadda take kuka sosai kanta ko Wankwali babu. Gashin ta yana cure a tsakiyar kanta ta Waure shi da ribbon. Kamar ma bata ji me yake faWa ba har lokacin bata cikin nutsuwarta saboda tashin hankalin da taji yana ™o™arin tunkaro ta, kasheta fa taji ana zancen za a yi, to ba dole hankalin ta ya bar jikinta na wani lokaci ba.

Nayla har lokacin hawaye ta ke yi tana ri™e dashi ta ce,  Tsoro nake ji, zasu kashe ni. Sun Salla gate sun shigo, Ka taimaka min ta sake faWa a tsorace sosai tana ri™e hannayensa duka biyun tana waige-waige. Abinda ya ji ya ratsa hannunsa mai kama da jan wuta shine ya saka shi yi mata tsawa ya ce,  ba na ce ki nutsu ba! Ki saurara da wannan shirmen! Ya faWa da ™arfi ba tare da ya sani ba saboda shock Win da ya ji ya ratsa hannayensa ya shiga har cikin jininsa ya zaga sa™on ya tafi har ™wa™walwarsa lokaci guda.

Firgigit Nayla tayi ta tsaya cak tana kallonsa har lokacin jikinta bai daina rawa ba amma ta saki hannunsa babu shiri. Kallon ta yake yi kamar yadda take kallon sa tana share hawaye ya ce,  babu abinda zai same ki, ki nutsu ki daina yi min shirme ya faWa yana fita ya bar ta a wajan jiki na karkarwa.

A gefen gadon ta zauna tana ajiyar zuciya, tsoron da take ji ya ragu ganin Omar Win yana nan amma har lokacin a tsorace take ta kasa sakewa gani take kamar zasu dawo su kashe ta Win.

Shi kuwa harabar gidan ya fita zuciyarsa na yi masa zafi akan abinda aka yi masa, yana fitowa harabar gidan ya tarar da Bash da Goje da Tk suna jiran fitowarsa. Yana ganin su ya ce,  bana ce ku zauna kar ku fito ba?. Goje ya ce,  Haba Damisa, an shigo har gonar mu kuma mu zauna muna kallo?. Tsaki ya yi ya ce,  to da ku ka zo me zaku yi?.

 Umarnin ka mu ke jira, wallahi yau baza su kwana lafiya ba. Azumin gobe sai dai su yi shi a kabari. Hayaniya yake jiyo daga waje ya ce,  su waye a waje?. Bash ya ce,  masoya ne, sun Webo kayan aiki suna jira ka ce wani abun.

Tsaki ya sake yi ya fita zuwa wajan dan ganin abinda yake faruwa, yana fitowa ya ga matasa da makamai an taru ana jira ya fito, yana fitowa suka fara hayaniya wannan yace wannan wancan ya ce wannan. GabWaya baya fahimtar abinda ake faWa hakan ya saka ciki cikin tsawa ya ce,  ya isa! Ya isa!.

Duk suka yi shiru ya kalle su ya ce,  ban ce kowa ya yi wani abun ba, ban ce kowa ya aikata wani abun ba. Kar wanda ya yi musu komai, a bari hukuma tayi aikin ta. Ina sake maimaitawa, kar wanda ya Wauki doka a hannunsa. Šaya daga cikin matasan ya ce,  Madugu har gida fa, har gida suka zo aka yi mana ba daidai ba kuma ka ce mu bari?. Kaima wasa ka ke yi baza mu ™yale su ba wallahi. Ranmu fansa ne a gare ka Damisa, zamu iya Satawa da kowa mu shirya da kai wallahi.

Omar ya ce,  ni dai na ce kar wanda ya yiwa kowa wani abun, in kuma ba haka ba duk wanda ya aikata saSanin abinda na ce zai haWu da fushina mai yawa. Kowa ya wuce ya tafi ya yi alwala ya tafi masallaci ya yi sallah. Wani zai sake magana cikin tsawa ya ce,  Na ce ku bar nan ko!. Dukkan su barin wajan suka yi ya kalli su Bash ya ce,  ban ce kowa ya aikata wani abun ba, haka zalika ban bawa kowa umarnin tura wasu su yi wani abun ba, ku ™yale ni ni nasan matakin da zan Wauka.

Tk ya ce,  Amma Damisa& .
 Shiru! Na ce a ™yale ni ya faWa a tsawace yana kallon sa dole ya yi shiru suka fita shi kuma ya koma ciki. Kamar ya shiga Wakin ya duba ta amma sai ya fasa ya yi zaman sa yana kaWa ™afa cikin Sacin rai mai yawa.

Wai shi za a zo har gida aka yiwa wannan wula™ancin, in ba dan kura tayi lafiya ba ai da gobe garin Kano an wayi gari jini ya Sata ko Ina, azumin gobe jama ar Kano da jini zasu sha ruwa. Babbar sa ar da suka yi Omar Win dah dana yanzu akwai banbanci, in ba dan haka ba da duk sai dai iyayensu su haifi wasu, koda bai Wauki mataki da kansa ba za a Waukar masa. A bayyane ya ce,  ko ya ya kayi ™o™arin zama mutumin kirki sai an yi abinda za a saka ka koma na banza.

Tsaki ya yi ya fita yana kallon gate Win ya mayar ya rufe dan ba Salla shi suka yi duka suka yi masa har lock Win ya zare. Ko key bai saka ba ya dawo ya zauna a kan kujera yana kaWa ™afa yana tunanin irin hukuncin da ya kamata ya yi musu. Yana wanna tunanin ya ga ™arfe uku na dare ta yi ko ina sallah ake yi. Kawai sai ya tashi ya yi alwala shima ya tayar da ta sa sallar.

Nayla kuwa baccin wahala ta yi alarm Win wayar ta ne ya tashi ta, ta tashi da nauyin jiki da ciwon kai daman dashi ta kwanta gashi tayi kuka kuma bata samu baccin kirki ba, alawala tayi ta tayar da sallar tahajjud.

Washe gari sai ™arfe goma na safe ya tashi, kasanacewar juma a ce manyan kaya ya saka ya fita, kai tsaye police station Win da ya saka kai yaran ya wuce. Da yake Dpo da suka saba ne suka tattauna ya ce masa za a Wauki mataki mai ™arfi, zuwa ranar monday za a tura su kotu bisa tuhumar tayar da faWa har cikin gida al™ali yanke musu hukunci.

Omar ya san za a yi hakan shiyasa

Please Login or Register in order to submit comment