Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batun ha™™i ki ke yi me ki ke so nayi nata? A baki ki ke so na bata abincin ko farka cikinta zan yi na zuba mata?. Ke ki ka ce min gidansu an kaita da abinci, to me zanyi kuma? Sun nuna min ni ban isa na ciyar da ´arsu ba, sun nuna min bani da kuWin da zan iya ciyar musu da ´a shiyasa suka kaita da abincinta, ba sai ta ci abincin gidansu ba ita kaWai ba? Lallai sai na kula da abincinta!?.

Didi ta ce,  maida wu™ar Omar, abincin da aka kaita da shi daga gidansu shi ake kira da gara, a al ada ba laifi bane kuma ba anyi dan ka gaza bane al adar malam bahaushe ce. In zaka tuna kaima lokacin bikina na karSi kuWi a hannun ka nima kayan abincin na siya na je dashi, bawai dan mijina ya gaza ake yi ba sai dan al adar bahaushe ace a haka.

 Kutmar uban al adar! Ya faWa a fusace cike da jin haushi. Jin zagin da ya yayi Didi ta ce,  A uzubillah! Omar me ya yi zafi haka?.
 Ni ban Wauki hakan a matsayin wani al ada ba tunda ba addini bane, kawai an nuna na gaza ne shiyasa aka kawo ta da abinci. Sai ta aci abincin gidansu, ni ban ce ina da bu™ata ba daman ai.

Didi ta ce,  Ka dai yi min irin wannan zagin bana so. Ana nuna maka gabas kana karkacewa, kai komai abinda zuciyarka take so shine daidai?. Yanzu ya zaka yi ga azumi zamu fara, ya zakayi da abincin shan ruwa?.
 Bani da hannu ne? Zan dafa da kaina a cikin gidan mu ba a gidan haya ba.

Didi ta ce,  ai shikenan Omar. Amma ka bi komai a hankali, da zaka ji ta tawa ka Wauketa kamar ™anwarka zaman zai yi maka daWi.
 Kin ji na ce miki ina so zamana ya yi daWi ne? Ko kin ji na ce daWin zaman nake nema?. Didi ta ce,  kai dai ka sani. Amma ina so ka sani akwai ranar da zaka nemi daWin zaman, Allah Omar sai ka so Nayla fiye da son da ka yiwa Narma.

Omar ya ce,  Tunda ke kika halicce ni sai ki saka min son na ta Win. In kina yi min irin wannan maganar wallahi zan yanke ala™a da ita, gidan ma zan daina zuwa ai ba dole!. Didi tayi dariya ta ce,  Allah ya shirye ka daga haka ta kashe wayar.

Tsaki ya yi ya ajjiye a bayyane ya ce,  wai sai na sota fiye da Narma, to ita Narma har wani sonta na yi? Mtsw Didi akwai kayan haushi ya faWa yana taSe baki yana cigaba da duba kayan. Sai da ya yi i sha a unguwar ya bawa su Bash key Win gidan dan su suke kwana a ciki ya wuce can ransa duk a jagule.

Nayla bata babban falon, ta ji dai alamun ya shigo, bata yi gigin fitowa ba ma balle ta yi masa tayin abinci. Shi kuwa in ya tuna komai na gidan na ta sai ya ji zaman gidan ya fita daga ransa, shi fa a tsarinsa bai yarda da kayan Waki gidan mata su yi ba, a yadda ya tsara in zai yi aure shi zai yi komai da kansa yadda zai yi komai yadda yake so baya so ayi masa iko ba, in ya siyi komai babu wata shegiyar yarinyar da zata ce ai daga gidansu aka kawo abu kaza. Yanayin yadda auren yazo ya saka burinsa bai cika ba shiyasa ko zaman gidan baya so. A haka dai ya kwanta da ya tuna maganar Didi sai ya ja tsaki har ya yi bacci.

Bayan Kwana biyu.

*America.*

Narma ta rame sosai ta fita daga hankalinta, kai da ka kalle ta sai ka san Narma tana cikin yanayi na damuwa. Komai ya tsaya mata babu abinda take jin daWinsa a zamanta da Ashraf. Ashraf ya ™wace mata waya ya kuma hanata fita, gabaWaya kaWaici ya isheta shiyasa duk take rama.

Tana zaune a falo tayi tagumi ya shigo ya kalle ta ya ce,  Mum tana son magana dake, wallahi in ki ka faWa mata kina da damuwa sai ranki ya Saci. KarSi ya faWa yana mi™a mata wayar a lokacin kiran Mum ya shigo. Ta Wauka ta saka a kunne Mum ta ce,  Daughter me ya same ki? Ashraf ya ce min kin yi rashin lafiya, ko kina da ciki ne? Me ya samu wayarki?.

Narma jin tambayoyin da Mum take yi mata sai ta ce,  Mum lafiya lau nake. Ina Dad?.
 Dad baya nan, ya je Italy bai dawo ba. Kina Lafiya dai ko? Me ya samu wayar ki?.
 Mum na yar da wayar ne kuma kin ga layin Nigeria ne sai na dawo dole na yi swap.
 Amma ki siyo sim a nan mana ki dinga amfani dashi, shirun naki ya ishe ni.
 Babu damuwa Mum, zan yi.
 Haka nake so na ji. Zan shigo America na duba ki. Ta amsa sannan ta kashe wayar ta bashi.

Ya kalle ta ya ce,  kin taimaki kan ki da yau sai kin yabawa aya za™in ta. Narma ta kawar da kai, ba tsoronsa take ji ba ta yi hakan ne saboda duk abinda ya faru laifin su Mum Win ne shiyasa bazata faWa musu tana cikin damuwa ba. Su suka siya mata da kansu da sun yi mata abinda take so da shikenan. Gashi sun kawo ta nan ya mayar da ita tamkar se* machine, kwana biyu da aka fara azumi ne ma ya saka yake iya ™yaleta. Amma kullum a abu Waya ake.

Bayan an sha ruwa ya dawo ya bita da kallo tana zaune tana tauna tosted bread kamar bata so, ya kalleta ya ce,  ki gama malama ina da bu™atar ki. Kallon sa tayi ta ce,  kai wai babu abinda ka iya ne sai s*x?.
 Dan shi na aureki ya bata amsa kai tsaye. Narma ta ce,  kenan daman ba sona ka ke yi ba?.
 Da fari na Wauka ina sonki ne, amma daga baya sai na gane sha awarki kawai nake yi. Na tabbatar da kin bani abinda nake so kafin wannan auren da ba a kawo haka ba.

Narma ta bishi da kallo ta ce,  kenan ka yi satisfying lust Winka yanzu bani da amfani a wajan ka ko?.
 No, har yanzu ina da bu™atarki ai, ban gaji dake ba. Narma ta taSe baki ta ce,  ka ci amanar iyayena, ban yi tunanin haka daga gare ka ba. Ka san ba sona ka ke ba ka amince da aurena?.

Ashraf ya kalle ta yana taSe baki shima ya ce,  laifinki ne, ke kika jawo na aure ki da wannan niyar. A ko yaushe in na ganki sai nayi sha awarki saboda irin shigar da ki ke yi, ko yaushe nude Winki a bayyane yake, kina saka kaya half niked ga ki da sura in kika saka kayan komai sai ya bayyana sosai har hakan ya kai ni ga karyewar alwala. Ban taSa mafarki na kwanta da wata ba sai ke, saboda tayar min da hankalin da ki ke da shigarki. Har wankan tsarki kin saka ni saboda haWa jikin da nayi dake cikin shigar da ki ka saba, ko yaushe ™irjinki a bayyane yake ga ™asanki kin matse da™yar ki ke tafiya, kina motsawa jikinki na rawa, waliyi ne ni da bazan yi sha awarki ba?. Abinda nake ji a kanki shi ne ya saka na Wauka a raina sonki nake yi ashe ba so ba ne ya bata amsa yana kai abinci bakinsa.

Narma ta yi shiru domin bakinta ya mutu da kalmansa, ya sake cewa,  majority ma su sonki ba ke suke so ba halittarki suke so saboda ita suke gani a bayyane. A social media ko yaushe cikin yabon surarki ake saboda a bayyane take ga kowa. Kinga ban yi laifi ba nima dan na mayar dake abin morata ko yaushe, ke kika siya da kuWinki.

Narma ta ce,  Amma meyasa a baya baka taSa faWa min ba sai yanzu?.
 A lokaci a hakan nake son ganinki a lokacin, bana so ki Soye ko wacce halitta a jikinki shiyasa bazan taSa faWa miki ba. Zuga ki ma nake yi akan ke mai kyau ce kina jin daWi, ban yi ™arya ba kina da kyau, kina da sura mai yau Narma. Yanzu kuma na mallaki komai na jikinki, ko bargo zaki Winka ki saka a jikinki ™arewar rufe jiki bazai dame ni ba. Ni ne wanda na yi disvirgin Winki, so ban ga abinda zaki Soye min a jikinki ba, ban ga abinda zai Wauki hankalina a tare dake ba. Nayi mamaki da ki ka kasance budurwa har wannan lokacin, dan wannan shigar da ki ke yi tsaf mutum zai iya sakawa a Wauko masa ke ya yi abiinda yake so dake.

Narma kallonsa take yi har ya gama maganar, ta girgiza kai cikin ba™in ciki ta ce,  Allah ya isa. Ka raba ni da wanda nake so ka zo nan kana wahalar da rayuwata, ni ka ke kallo kana faWawa wannan maganar dan kawai ka gama cutar dani. Kuma wallahi yau duk abinda zaka yi sai dai kayi amma baka isa ka yi min komai ba, I am not your slive baka isa ka cigaba da wula™anta ni ba. Dan ka ga nayi shiru na jure kana ganin tsoronka nake ji? Don t forget, I m a lawyer, na san right Wina ina da ikon ™in yin duk abinda ya saSani da ra ayina. Ina ™yaleka ne kawai saboda ko meye ya faru su Dad ne dalili, amma yanzu na daina. Zan dawo asalin Narma da ka sani, na daina Waukar rainin hankalin da ka ke yi min ina ™yaleka. Zan bar America zan koma Nigeria in ka isa ka hana ni ta faWa tana barin a wajan ta shiga Waki.

Dariya ya yi yana shafa fuskarsa a bayyane ya ce,  ai ban gaji dake ba Narma, barinki America ai ba yanzu ba dai lokacin da na ga dama. Mu zuba mu gani ya faWa yana cigaba da cin abincin sa yana murmushi, domin kuwa shi kansa ya tabbatar da ba son Narma yake yi ba akwai sha awar take bashi. Kafin ya samu abinda yake sha awa a tare da ita sai ya Wauka so ne, amma yanzu da ya samu ya tabbatar da sha awarta yake yi babu soyayyarta ko kaWan a zuciyarsa, kuma bai ga laifin kansa ba, dan duk abinda ya faru itace silar faruwarsa.KRB3P007
ArewaBooks@nanahaleema11

Zaman Nayla da Omar babu cigaba sai ci baya, dan Omar bai ma cika zama a gidan ba, in kuma ya kwana to kafin ta tashi ya bar gidan wani lokacin bazai dawo ba sai tayi bacci. Ba kasafai ta cika ganinsa ba, dan in ya fita bai cika dawowa ba sai dare, sai dai in akwai abinda ya manta ko abinda zai yi shine yake dawowa. Ko da zasu haWu bazai ce mata komai ba itama tunda ya yi mata warning shikenan ta daina yi masa magana. Ta gaji da kula shi yana shareta ko ya harareta wani lokacin harda tsaki, ga tsoronsa da take ji shiyasa tunda ya hanata kula shi ta hanu har aka shiga watan ramadan.

Yau an kai azumin ramadan na uku kenan, kuma ya yi daidai da kwana goma sha bakwai da tarewar Nayla a gidan Omar.

Tana nan kamar yadda ta ke, bata mayar da jikinta ba kuma bata rame ba. Tana nan kamar yadda aka kawo ta da ´ar rama da kuma damuwa. Dan zaman shirun ma damunta yake yi, sai dai ta danna waya ta gaji, ta yi karatu ta gaji, ta yi bacci ta gashi abinda take yi kenan a gidan. GabaWaya zaman damunta yake yi shiyasa bata da walwala ko kaWan.

Tana zaune a falo sun gama waya da Twiny da take ™asar saudia ta je umrar azumi. Wayar ta ce tayi ™ara ganin sunana Yaya J sai ta Wauka da hanzari tana murmushi. Kafin ta yi magana ya ce,  Ina gate Win gidanki. Kamar an yiwa Nayla albishir da aljanna, ta mi™e da sauri ta saka hijjabi ta fita ta buWe gate Win ya shigo yana kallonta da murmushi.

 Yaya J ta faWa tana rungume shi cike da murnar ganin Wan gidansu. Dariya ya yi ya ce,  Nayla kin kasa girma har yanzu, ke fa matar aure ce ya faWa yana rabata da jikinsa amma ta ri™e hannunsa gam tana kwantar da kanta a kafaWarsa.
 Sannu da zuwa Yaya J.
 Yauwa Nayla. Hannunta na cikin nasa suka ™arasa falon ta zauna shima ya zauna ya ce,  parlour gidan nan na ki ya yi kyau Nayla, ya burge ni. Nayla tayi dariya ta ce,  Ina yini Yaya J.
 Lafiya lau Nayla, ya ibada?.
 Alhamdu lillah Yaya J. Ya hanya?.

Jawad ya ce,  Alhamdu lillah. Da yake tun jiya ina Kano ba yau na shigo ba. Nayla ta ce,  shine ba ka zo ba tun jiyan?. Ya murmusa ya ce,  gashi ai na zo yanzu.
 Yanzu mu ka gama waya da Twiny.
 Eh, ita kwanan ta biyar da tafiya ma ai ko?. Nayla ta Waga kai alamun eh Jawad ya ce,  Abiy fa? Kun yi waya?. Nayla a sanyaye ta ce,  na kira shi na yi masa Allah ya kiyaye, yanzu ma ma san sun sauka ko?.

Jawad ya ce,  Da yake Egypt airline suka hau kin san yana da wahalar sha ani, sai sun yi transite Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce,  Allah ya kiyaye. Ya bita da kallon tausayi a zuciyarsa, amma a bayyane ya ce,  Amin Nayla.

Ya ciro takarda daga aljihun ya ce,  Ga takardar canjin wajan aikinki, na saka wata abokiyar aikin ki tayi komai da komai. Yanzu ki yi signing a wannan takardar zan bayar a kai can Kaduna Win, gobe in Allah ya nuna mana sai ki je branch Win da yake kusa da gidan governor ki kai wannan takardar ki yi signing shikenan.

Nayla farin ciki ya mamaye mata zuciya, ko babu komai zata rabu da zaman kaWaicin da yake damunta wani lokacin. Biro ya bata da kansa ta saka hannu ya karSa ya ce,  zan bayar a kai can Kaduna Win, wannan kuma sai ki tafi da ita goben. Ta karSi wacce yake mi™o mata ta ce,  To Yaya J, na gode sosai. Na ji daWi wallahi.

Murmushi ya yi ya ce,  zan cire miki hanci keda kin gode Win ai. Ga key Win motar ki da nayi alqawari, gata can a waje an zo miki da ita, akwai laptop Winki da iPad Winki a ciki. Akwai kayan ki da Mama ta bani da dai abubuwan ma dai suna cikin motar. Nayla ta Wauki key Win da ya ajjiye kusa da ita cikin tsananin farin ciki ta ce,  na gode Yaya J Tana faWa sai kuma ta fara hawaye.

Jawad ya yi tsaki ya ce,  Allah zan yi tafiyata, ya zaki dinga yi min kuka kuma?. Ta goge idanunta ta ce,  To Yaya J na daina ta faWa tana goge idanunta.
 Babu abinda ki ke so?.
 Babu komai.
 In kawai ko meye ki faWa min. Kuma aikin gidan nan bai yi miki yawa ba kuwa?. Nayla ta ce,  za a kawo min house maid daga Kaduna, sai Mama ta dawo. Jawad ya ce,  meyasa sai Mama ta dawo? Yanzu aikin baya yi miki yawa?.

Ta ce,  Ina iyawa.
 Kin tabbatar?.
 Eh Yaya j.
 Gaskiya ki yi magana ko gidan Hajja ne a kawo miki housemaid, har wani aiki ki ka iya da zaki iya gyara gidan nan?. Bayan wannan falon akwai wani, sannan ga bedrooms. Gaskiya ki yiwa Hajja magana ko wacce zata dinga zuwa tana taya ki ta koma ne ki samu. Nayla ta Waga kai ta ce,  To Ya J. Kuma kaga gwara ma ta gidan Hajjan, damaan ni bana son mai kwana.


Jawad ya ce,  haka dai ya kamata. Yanzu abinda zai faru zan tashi na wuce, kin san ™arfe uku zai tashi, yanzu ga Waya da rabi har tayi ina da sauran awa Waya da rabi. Zan je gida a kai ni airport ya faWa yana mi™ewa tsaye. Nayla ta ce,  Yaya J Allah ya kiyaye hanya. Su Hajja ma gobe da zafe zasu tafi.

Yayi dariya ya ce,  kawai ki ce saura ke kaWai a nigeria kowa ya gudu ya barki. Dariya tayi ta ce,  Yaya J in zaka dawo fried chicken Win McDonald nake so, na bawa Twiny sa™on Albaik, na baka na McDonald, Salma kuma zan bata na KFC.

Dariya sosai ya ce,  Duk ke kaWai? Kuma ki rasa abinsa za a siyo miki sai soyayyiyar kaza?. Nayla ta ce,  ita nake son ci. Tare suka fito shi da ita suna hira har ™ofar gidan, ta buWe sabuwar motar ™irar glk ta Wauki laptop Winta da iPad Winta. Ya kalle ta ya ce,  To Nayla na tafi, ki cigaba da addu a ya faWa yana shiga mota ta Waga masa hannu ya tafi.

Gidan ta koma cike da kewa ta saka laptop Winta a chaji ta dawo ta yi sallar azahar sannan ta Wauki alkur ani ta fara karantawa. Gate taji ana bugawa abin ya bata mamaki, ta hijjabi saka ta fito tana tambayar waye. Muryar Bashir yaron Omar taji hakan ya saka ta buWe ya ce,  Antyn mu barka da rana. Damisa ne ya aiko ni na kawo wannan kayan gidan nan. Nayal ta ce,  to shigo. Ya ibada?.
 Alhamdu lillah. Ta bashi hanya ya shiga ta rufe gate Winta koma ciki.

Kaya ne da yawa a leda babba ya ajjiye yana kallon falon ganin da haske sosai sai ya ce,  Antyn mu zan iya yiwa kayan nan hoto a nan? Naga da haske sosai, in ban yi ba yanzu in anjima zan saka a nemo ni. Nayla tayi dariya kaWan ta ce,  kayi mana, babu komai.
 Godiya nake ya faWa yana fito da takalman daga ledar. Nayla hannu ta saka ta Wauki takalmi guda Waya na mace ta ce,  kai amma takalmin nan ya yi kyau sosai, kuma da gaske aikin kune wannan? Da hannu aka yi shi?.

Bashir ya ce,  ™warai kuwa Antyn mu. Wannan boss ne da kansa ya yi shiyasa ya ce na kawo shi nan sai na shago sun ™are za a fitar da su. Tun safe aiki mu keyi har yanzu. Nayla ta ce,  Gaskiya ya burge ni sosai ma ta faWa tana shafa logon takalmin wanda aka rubuta Tiger da wani style mai kyau da kuma yanayin jikin Damisar.

Nayla ta kalli wayar da ya Wauko zai yi hoton ta ce,  ko na ara maka wayata kayi hoton da ita? ta faWa tana mi™a masa wayarta. KarSa ya yi ya ce,  Godiya mu ke Antyn mu, ga iPhone 16 ai iPhone 13 baza tayi ba. Hotuna yake yiwa takalman tana kallon dan ya iya Waukar hoton sosai. Ya jima yana yi tunda suna da yawa sannan ya gama. Nayla a ™afarta ta saka takalmin yayi mata bala in kyau kasancewar jikinsa baki ne sai ya haska ™afarta sosai.

Wayar da ya mi™a mata ta karSa kawai sai ta yiwa ™afarta ta hoto ta tsaya tana kallo domin hoton ya yi kyau sosai. Bashir ya ce,  Antyn mu ayi min airdrop. Ba musu ta buWe ta tura masa hotunan suka je har wanda ta Wauki ™afarta bata san ta tura ba. Kallon hoton ya yi ya kalleta ya ce,  Antyn mu amma hoton nan ya yi kyau sosai. Zamu iya posting Winsa? Ya faWa yana haska mata hoton.

Nayla ta ce,  ban ma san na tura maka ba, amma babu damuwa zaka iya.
 Daman muna son a dinga sakawa ana Wauka a ™afar mace, to Boss Win ne shi ba wasu mata ya sani ba balle a dinga biya ana yi. Na mazan ma daman da ™afarsa ake Wauka shima kuma sai ya ga dama, in ya ga dama ya saka a Wauka in bai ga dama ba ba za a Wauka ba. Amma wannan kam ya yi kyau.

Nayla ta ce,  kuma nawa ku ke siyarwa?. Bashir ya ce,  ya danganta gaskiya, bamu cika siyar da guda Waya ba, an fi siyan kwali ko guda sha biyu. Nayla ta ce,  ya kamata ace kuna siyar da pieces saboda ga sallah ™arama nan zata zo akwai wanda zasu siya sosai. Bashir ya ce,  Gaskiya ne, amma da yake muna kaiwa kasuwa da shaguna bamu cika siyar da Waya ba. Amma zamu fara in sha Allah.

Nayla tavce,  nima ina da shop a Kaduna, ina so a haWa min masu kyau ku bawa driver da ya ke muku aiki ya kai can na tabbatar da za a siyar. Bashir ya ce,  To Antyn ku duk sanda ki ka shirya.

 Ai gobe nake so a tura, ka haWa package mai kyau na maza da mata da na yara, zan yi waya a karSa dan na tabbatar bazai kai sallah ba ya kare. Bashir ya ce,  za a yi hakan.

 Meye sunan platforms handle Win ku ke posting?. Sunan page Win ya faWa mata sannan ya ce,  duk da sunan kWa amfani, ig, x, facebook har da TikTok ma. Nayla ta ce,  zan taya ku advert in sha Allah. Ka bani number ka saboda kayan da za akai gobe. Bai yi musu ba ya bata number sa ta yi saving ta kira shi shimaya yi saving sannan ta ce,  Amma kun taSa kai advert gidan tv ko radio haka?.

Bashir ya ce,  gaskiya ba mu taSa ba.
 Ya kamata ace an kai saboda manyan mutane su gani. Ga sallah zata zo in aka yi talla yanzu abinda zai wuce yadda ake tunani. Gobe in fita zan shiga arewa24 zan ji ya tsarin sun yake, yadda muka yi dasu zan sanar dakai. Za a yi tallah a kwanakin nan koda guda biyu ne.

 An gama Antyn mu, hakan ma tunani ne mai kyaun. Nayla ta ce,  tunda ka ce wannan kayan shi ne ya ce ka kawo, Ina son guda Waya yanzu ka kawo min daga shop Win amma irin wannan nake so ta faWa tana nuna irin wanda ta saka a ™afarta.

Bashir ya ce,  ai kawai Antyn mu ki Wauka a nan, babu irin waWannan a shago. Yin su aka yi kuma ya ce ba yanzu za a fitar dasu ba. Nayla ta girgiza kai ta ce,  to na gode. Yadda mu ka yi zan yi maka waya sai a shirya wajan in zasu zo Waukar video. Amma bana son Boos Win na ku ya sani. Ya yi dariya ya ce,  babu damuwa Antyn mu, duk da dai kwana biyu yana zama sosai a shagon amma zan san abinda zan yi. Nayla ta amsa ta ce,  don Allah zaka iya shigo min da farar mota da take wajen gidan nan?.

Bashir ya ce,  zan iya. Ta bashi key Wn ta ce,  na gode. KarSa ya yi ya fita ba jimawa ta ji ya shigo da ita sannan ya dawo ya bata key Win tayi masa godiya shi kuma ya fita.

Kallon

Please Login or Register in order to submit comment