Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi miki kyau ne?." Nayla ta ce, "sosai ma kuwa, ka yi bacci kuwa?."
"Ban yi ba, yanzu aka idar da sallar asuba da zan kwanta sai naji bazan iya ba sai na ga fuskarki. Ga ki nan kin yi kyau sosai, daga tafiya kwana biyu naga an sake canja min ke."

Nayla ta ce, "mu kuma a nan an yi sallar 'isha, ka je ka huta in ka farka daga baccin sai ka kira ni."
"Lokacin ai kin yi bacci."
"Zan katse baccin na amsa kiranka Rouhii."
"To Ashiq zan huta." Kiss ta yi masa sannan ta ce, "Bye Rouhi." Katse kiran ta yi dan tana so ya huta ta biye masa bazai huta ba.

        Kwanakin biki yana ta tahowa ana ta shiri Nayla na ta shan soyayya da mijin ta a waya, duk inda ya je sai ya faWa mata, haka duk abinda ya siya sai ya tura mata. Haka take zama ta lalace a video call dashi ko gajiya da wayar basa yi, kewar junan su na sake damun zuciyarsu.

A cikin garin Kano aka fara events na bikin Salma, Nayla itace kan gaba komai tare ake yi da ita sai Jidda da ta shigo ciki, Sune ™annen Ango kuma ™awayen amarya. Tun daga kan masu henna, da masu kwalliya duk tare ake yi musu, Nayla dai iya ba™in henna tayi iya hannu ta ce baza ta yi ba sai mijin ta zai dawo suka dinga tsokanarta.

An yi kamu, an yi dinner aka Waura aure ranar Friday, ranar Saturday aka tafi da amarya garin Kaduna. A can Kaduna ma wani bikin aka sake yi, Nayla sai zirga-zirga take itace wajan ango itace wajan amarya. Kowa in ya ganta sai ya yi dariya ya jinjina mata ana tsokanarta ™anwar ango ™awar amaryar, gashi ta yi kyau ta sake yin haske sai aka dinga tunanin ciki ne da ita. Mama ma ta Wauka ciki ne da ita, shiyasa take hanata wani yawo, sai da ta tambayeta ta ce ita bata da komai sannan ta ™yaleta. Amarya bata je gidanta ba sai ranar lahadi da daddare, su Nayla ne yan rakiyar amarya ita da Jidda da Ummimi.

A tsakiya suka saka Salma suna ta tsokanarta tun tana ™yale su har ta fara basu amsa, sai da ango ya shigo sannan suka dawo gida ita da Jidda cikin farin ciki. Biki ya watse kowa ya koma gida ana huta gajiya, Nayla ma ta sha baccin gajiya, kiran wayar mijinta ne ya tashe ta a firgice ta duba ta ga video call ne.

Šauka ta yi ta kalle shi ta ce, "good morning Rouhii!." ˜are mata kallo yake yi dan kayan bacci ne a jikinta, rigar mai ™aramin hannu kuma bata da kauri sosai sannan bata saka komai ba sai rigar kawai dan haka ana iya ganin jikinta. Ganin ya yi shiru yana kallon ta sai ta kalli abinda yake kallo ta kalle shi sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yi kewarki Ashiq, ni kaWai na san halin da nake ciki da bakya tare dani, Kin san dai halin mijinki, mayenki ne."

Nayla ta yi kasalalliyar dariya da ta saka Omar ya lumshe ido ya ce, "Kina sake kashe min jiki Jidda, kar ki saka ni kuka mana." Ta wara ido ta ce, "wace ni na saka YaMar tiger kuka? Sai daina saka shi farin ciki." Murmushi ya yi ya ce, "kuka na nawa kuma? An ce da kare ya sunanka ya ce na nawa kuma?." Dariya ta yi sosai shima dariyar ya yi ya ce, "ko ba haka ba ne?."
"Ni dai babu ruwa."

   "Yanzu rufe jikinki in ya so sai mu yi magana, in ina kallonki a haka akwai matsala." ˜i tayi ta shagwaSe fuska tana kallonsa ya Wauke ido ya ce, "Jidda ki yi abinda na ce, Allah zan rasa nutsuwata, ki taimaka min. Kar ki saka aljanuna su tashi gashi bakya kusa balle ki yi min ru™iya." Dariya tayi sosai sannan ta ja bargo ta rufe jikinta ya kalle ta ya ce, "Wai waye ya saka ki yi wannan shigar?."

"Gajiya na yi sosai, wannan Win ma a cikin kayana na nemo ta."
"Amma wannan kayan da zaki saka a gida ba ne, akwai ´an biki, ko wata ce ta ganki a haka ai ta cuce ni." Nayla tayi dariya ta ce, "yanzu zan yi wanka."
"Ya gajiyan biki?."
"Bari kawai Rouhi, na gaji sosai."
"sannu, ai dole ki gaji, ™awar amarya ™anwar ango."

Dariya ta yi kaWan tana kallonsa ta ce, "ni ko ina dani a wannan bikin. Yau baka je kasuwar ba?." Ya Waga mata gira ya ce, "zan je sai anjima, akwai da wanda mu ke zuwa tare."
"Allah ya taimaka ya dawo min da kai lafiya."
"Amin. Na ™agu na dawo nima wallahi, duk na gaji da zaman."
"Nima na gaji da zama baka nan."
"Hmmm Kamar gaske."
"Da gaske mana, in ka dawo zan tabbatar maka da na yi matukar ™ewar ka." Murmushi ya yi bai ce komai ba ta ce, "kasan meye?." Ya girgiza kai alamun a'a ta ce, "yau na tashi da azumi, rabona da azumi har na manta, tun dai wanda muka yi tare guda uku nida kai."

Omar ya ce, "ki yi abinda ki ke so kafin na dawo."
"Don Allah meyasa baka so na yi azumi?."
"Akan me zance bana so ki yi ibada? Kawai bana so a shigar min lokacina ne. Ina so na kasance dake kuma ga azumi, kinga akwai shiga ha™™i, maimakon ki samu lada sai ki kwashi zunubi tunda ba azumin farilla bane. Ina taSa ki zaki ce azumi ki ke yi, to akan me nida ha™™ina kuma matata mallakina? Shiyasa gwara ki ha™ura kawai."

Dariya tayi zata rufe fuska ya ce, "kina rufe fuska zan kashe wayata, a wayar ma kunya ki ke ji?." Dariya ta yi sosai har ya shagala da kallon ta kafin ta ce, "Daman Didi sai da ta faWa min, ta ce da™yar in baka hana ni azumin litinin da alhamis ba, nayi-nayi ta faWa min dalili ta™i, ta ce na jira na gani in har ka hana Win zan fahimta, gashi kuwa na gane."

"Ta san ™aninta bai yi kama da mai ha™uri ba, ta san ™aninta yana da ™ulafuci akan abinda yake so. Inda zan iya zan barki kiyi ai lada zaki samu, babbar matsalar indai zan barki kiyi sai dai in na fita tun safe baza ki ganni ba sai kin sha ruwa. Dan in muka haWu, in idanuna ya faWa cikin naki ke kan ki baza ki san kin karya azumin ba. To me ya yi zafi? A dinga karya azumi da gangan? Maganin kar a yi kar a fara. Baazan iya ba, ji zanyi kamar za a zare min rai daga jikina. Ya za a yi na iya tsallake daddaWan yanayin nan na bayan sallar asuba?."

Dariya tayi sosai tana rufe ido ta ce, "kana bani kunya Rouhii."
"to ™arya nayi? Ke kan ki lokacin baya burge ki don Allah? Ki faWi gaskiya banda ™arya, aljanun da suke tashi a lokacin na san baza ki so a shiga ha™™insu su ™i tashi ba." Bata ce komai ba sai fuska da ta rufe ya yi ™aramin tsaki ya ce, "komai kunya, zan kashe wayata in baza ki buWe fuska ba." Nayla ta ce, "Kana adawa da wannan kunyar tawa, ni kuma ba ni nayi kaina ba."

"Kunyar ta gulma ce ai, inda ya kamata tazo bata zuwa. Ki tuna daren za zan yi tafiyar nan mana, mantawa ki ke yi da kunyar, sai daga baya ki fara rufe min fuska." Ido ta rufe tana dariya suka cigaba da hira cikin nishaWi da soyayya.KRB3P079
Nana haleema

Narma ta kammala idda amma har lokacin bata walwala kamar da, iyayenta sun Wauka tunda ta gama idda zata dawo kamar baya amma sai suka ga akasin haka har lokacin ware kanta take yi a cikin su.

Suna zaune a falo gabaWaya har da Yayansu Dad ya kalle ta ya ce, "Narma wai meye matsalarki ne? Na Wauka da kika gama idda zaki dawo kamar dah kina walwalarki sai na ga akasin haka. Me ki ke so ne?."

Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Abinda nake so ba samu zan yi ba shiyasa gwara na yi shiru kawai." Mum ta ce, "Wan daban nan ko?." Narma ta ce, "Mum sunansa Omar, Omar sunansa ba Wan daba ba." Mum ta ce, "na rasa me ya shiga kanki, ina ke ina wannan yaron?."

"A haka nake sonsa! A haka nake so na rayuwa dashi Mum. Shekara Waya kenan da ku ka raba ni dashi, amma zuciyata har yanzu tana tare dashi. Matu™ar baku amince min da aurensa ba baza ku taSa samuna a yadda ku ke so ba. Yadda na bi abinda ku ke so na auri Ashraf, ku ma ku yi min adalci na aure shi!."

Dad ya ri™o hannunta cikin rarrashi ya ce, "yi a hankali my love, ke yanzu kin san inda Tiger Win yake? Kuma kina da tabbacin zai karSe ki?."
"Indai zaku amince na aure shi zan nemo shi a duk inda yake, kuma zan tabbatar da na dawo da soyayyata a cikin zuciyarsa. In kuma ba ku amince ba zan iya barin gidan nan na koma Kano na rayu dashi."

Jin abinda ta ce Nabil Yayanta ya ce, "Baki da hankali." Dad ya dakatar dashi ya kalle ta ya ce, "Narma yaron nan ba type Winki bane, na rasa abinda ya shiga kanki kika kasa fahimtar matsayin da ki ke dashi. Mahaifinki fa takarar governor yake yi, meyasa zaki dinga cewa kina son wanda ko makaranta bai yi ba?."

"Dad!.....A haka nake sonsa, a haka nake so na aure shi, in zaku bani dama ku bani, in baza ku bani dama ba wallahi in na tafi baza ku sake  ganina ba. Na gaji, na gaji da wahalar da zuciyata da ku ke yi, na jure a lokacin baya, amma a wannan lokacin bazan taSa iya jurewa ba. Ko ku yarda, ko kar ku yarda zan auri Faruk ko bakwa so!" Ta faWa tana fashewa da kuka mai sauti.

Najwa ta kalli iyayen ta ce, "Mum, Dad, Yaya, don Allah ku ™yaleta ta aure shi, tana sonsa, tana ™aunarsa meyasa baza ku amince ba?. Kuma shi wanda ku ke cewa type Winta ne ga abinda ya aikata mata, Inda tun farko ta auri Omar Win da hakan bai faru ba" ta faWa tana tasowa ta ™araso inda take ta rungume Yayarta. Mum ta kalli Dad bata ce komai ba ta tashi ta hau sama. Dad ya kalli Narma ya ce, "Kar ki damu Narma, zan yi tunani a kan hakan, Ina zuwa" ya faWa yana bin Mum sama.

A Waki ya same ta ya ce, "Sai muna yi mata a hankali, kin manta Dr ya ce a daina saka ta a damuwa?." Mum ta ce, "tana maganar auren Wan daba ne fa, tana maganar in ba shi ba zata bar gidan nan, ya ka ke so mu yi mata?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "tunanin abinda ya kamata zamu yi ba fushi ba My dear, kin ga Narma yarinya ce ™arama, kuma ga abinda ya faru da ita a auren ta da Ashraf, dole tana bu™atar rarrashi daga wajena da ke, yin fushi ba na ki ba ne."

"Dole na yi fushi fa, domin bazan amince ta aure shi ba wallahi, wallahi bazan amince ba sai dai in bani da rai. Kai ko bani da rai bazata aure shi ba, aurensa kamar cin mutunci ne a gare ni."

"Calm down! Zamu san abinda zamu yi, amma ki daina nuna mata bakya so kar mu wayi gari bata nan, mu cigaba da binta a hankali sai komai ya wuce." Mum ta ce, "mu bita a hankali ta yi tunanin zamu bari ta aure shi kenan? Dear bazan iya wannan pretending Win ba gaskiya, dan ko a mafarki bazan taSa bari ta aure shi ba wallahi." Dad ya ce, "zaki iya, kina son Narma na san zaki iya." Shiru ta yi bata ce komai ba amma ko me zai faru Narma baza ta auri Omar ba sai dai ta mutu.

     Narma kuwa tana falo tana kukan, ™awarta ta yi sallama ta shigo falon. Najwa ta kalle ta ta ce, "Welcome Sis, don Allah taimaka ki kai ta Waki ko zata daina wannan kukan." Ri™e hannunta ta yi zuwa Wakin Narma ta zauna da ita ta ce, "what wrong kuma?." Ta kalle ta ta ce, "Safna Faruk, I so much love him wallahi."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Yanzu me ya faru?."
"Na faWawa su Dad in dai ba su amince na aure shi ba a wannan lokacin baza su sake ganina cikin farin ciki ba. Kuma zan tattara na bar gidan nan gabaWaya."

"Like seriously!" Ta faWa tana wara ido tana kallon ta. Narma bata ce komai ba Safna ta ce, "Narma ya kamata ki dawo hankalinki." Narma ta ce, "in dai ba auren shi na yi ba bazan taSa dawowa hankalina ba."

"Shi kin tabbatar da yana sonki ne?." Ta kalli Safna ta ce, "yana sona mana, har gidan nan ya zo saboda son da yake min su Dad suka wula™anta shi, yana matukar sona yana kuma ™aunar zama dani matsayin matarsa." Ajiyar zuciya ta yi ta kalle ta ta ce, "Narma ya kamata ki fara dawowa tunaninki ki fahimci kuskurenki, a Sangaren auren Ashraf kawai ya isa ki gane rayuwarki."

Narma ta kalle ta matsayin ban game ba ta ce, "i'm talking about your rubbish sexy dress Narma, shine babbar matsalarki wacce ta kawo ki a wannan yanayi da ki ke ciki." Narma ta kalle ta tace, "meye haWin wannan maganar da wacce ki ke yi?."

"Akwai mana, da farko kin Wauka Ashraf yana sonki ne ashe ba ke yake so ba jikinki da yake gani a bayyane yake so. Ya yi ™o™arin ganin kin bashi dama kafin ya aure ki kika ™i, amma da ya biyo ta hanyar aure ai kinga ya same ki. Narma na faWa miki tun ba yanzu ba, wannan dress Win da ki ke ba farin jini zai jawo miki ba, a cikin maza goma da zasu ce suna sonki in suna ganki da wannan shiga tara a ciki jikinki su ke so Narma. Kuma suma kamar Ashraf ne, da zarar sun samu jikinki zaki fita daga ransu tunda daman ba soyayyar gaskiya suke yi miki ba. Shi kan shi Faruk Win da kika haukace a kansa baki da tabbacin son ki yake yi, maybe shima irin Ashraf ne jikin ki yake so, da ya mallakeki......"

"Hold on Safna!" Narma ta katse ta, suka haWa ido Narma ta ce, "Faruk yana sona, Faruk ni yake so ba body structure Wina ba."  Safna ta ce, "ya aka yi kika sani? Shi Ashraf Win kin yi tunanin ba son ki yake yi ba?."

Narma ta yi shiru bata amsa ba Safna ta ce, "Baki yi tunanin haka ba saboda baza ki fahimta ba, yana yin duk abinda yake yi ne dan ganin ya mallakeki ya samu jikinki daga nan kuma ya tsallake ki tunda amfaninki ya ™are a wajansa. Narma let me give you example, ki Wauki alawa ki cire ta daga jikin ledarta kin ajjiye, kin Wauko wacce take a rufe a jikin ledarta ki ajjiye a kusa da ita. A cikin wacce aka buWe da wacce take rufe wacce ce flys zasu fi zuwa kusa da ita?."

Narma ta yi shiru bata amsa ba Safta ta ce, "ki bani amsa mana." Narma ta ce, "the opened one."
"That's the real example of you. Wannan wacce take a buWe Win kece, wannan flys Win da suka mamaye kuma mazan da suke yi miki caa, ko yaushe suna cewa suna sonki bayan ba so bane kin kasance a buWe ne shiyasa suke zagaye dake. And the closed one is Ikram, yes ikram wacce Ashraf zai aura yanzu. Yarinyar ko a social media ko yaushe jikinta a rufe yake, bata taSa buWe wani Sangare na jikinta balle wani ya gani yayi sha'awa har ya nemeta. Wannan shine dalilin da ya saka Ashraf yake matu™ar sonta saboda Allah ba saboda jikinta ba."

Narma ta ce, "yanzu so ki ke na koma saka hijjab kenan? Kuma meya amfanin halittar da Allah ya yi min in ban yi kwaliyya dashi ba?."
"Noo ni ban ce haka ba, amma kalle ni don Allah" ta faWa tana tashi tana juyawa a gabanta ta ce, "kin ga wani Sangare na jikina a buWe?."

Narma ya Wauke kai ta ce, "to ke abayar ma in zaki saka sai kin bawa wannan shegen tailor nan naki ya yi shaping Winta sannan zaki saka, a ganinki shine daidai kuma shine za a kalle ki ace ana so, kuma shine zaki fito a Barr Narma ´ar Sentor Sagir. You fail Narma, this is your failure, wallahi kin faWi indai wannan ne tunaninki. Abu mai arha a ko yaushe ya fi customers, abinda ya kasance mai tsada sai wanda ya san mahimmacin sa ne yake zuwa inda yake. Amfanin surar da Allah ya yi miki ki yiwa mijinki ado a gidansa, ki yi masa kwalliya ta Wauki hankalinsa Allah ya rubuta miki lada. Amma in ki ka buWe wani waje har wani ya gani ba, ko wani ne ya ji wani abu ransa sai Allah ya kama ki, in ya ce Allah ya isa wallahi sai ta kama ki. Maybe ha™™in mazan da ki ka Wauka ne ma ya saka komai ya canja miki."

Narma ta ce, "ni ban kira ki ki yi min wannan maganar ba, na kira ki saboda Faruk, ina so na san inda yake da kuma me yake yi yanzu." Safna ta ce, "gaskiya dai na faWa miki, in kin ga zaki gyara fine, if not zaki ta shan wahala a wajan maza. Saboda babu namijin da zai miki son gaskiya sai dai saboda jikinki." Ta koma ta zauna Narma ta ce, "ni fa ba buWe jiki nake yi ba."

"Meye marabar kayan da ki ke sakawa da tsirara Win Narma?." Narma ta Wan Wauke kai bata ce komai ba, Safna ta kalle ta ta ce, "me ki ke so na yi miki?."
"Ina so ki yi min bincike akansa, a inda yake zaune da komai da komai nasa."
"Zan yi ™o™ari in sha Allah, duk abinda na gani zan sanar dake. Amma ina so ki kwantar da hankalinki, sannan ki daina wannan dress Win dan ko a yanzu kin ga disadvantages Winsa."

Narma ta yi ajiyar zuciya tana kallon Safna ta ce, "zan daina."
"Better, shi kansa Faruk Win in ya ganki da shiga mai kyau ta musulunci zaki fi burge shi." Jin ta sako maganar masoyin ta sai ta yi murmushi ta ce, "da shigar kafirai nake yi?."

"Har gwara ta kafirai ma akan wacce ki ke yi, na sha faWa miki bakya ji, saboda su Nasreen suna zugaki suna ce miki mai figure eight kanki yana fashewa saboda ke ga mai shape ko?. Yanzu gashi kin jawowa kan ki bala'i, ni nayi mamaki ma da har ki ka yi aure ba a yi disvirgin Winki ba. Dan yadda maza suke haukacewa a kan ki tsaf wani zai yi raping Winki wallahi. Allah ya sa Tiger Win ma bai manta dake ba." Narma ta ce, "Allah yasa yana lafiya zaki ce, dan na san Faruk Wina har yanzu yana sona." Safna bata amsa mata ba ta ciro sim card Win ta mi™a mata ta ce, "Sabo ne, bani nayi register ba sister na ce. Zaki iya amfani dashi."

Narma ta karSa tana murmushi ta ce, "Thank you my friend."
"Amma wanne amfani zaki yi dashi?."
"Zan kira Faruk dashi, tunda nayi aure ya yi blocking number ta. Zan kira shi ko na yi masa message."

Safna ta taSe baki tana mamakin ko ina class Win Narma ya je oho, gabaWaya ta haukace akan wannan Faruk Win kamar shine autan maza na duk duniya. Komai Faruk, motsi kaWan Faruk, mafarki Faruk, tunani Faruk Duk ta rasa nutsuwarta ta dalilin shi, tunda ta fara sonsa har kawo yanzu bata sake samun sukuni ba.

Safna ta ce, "gabaWaya kin koma wata mara aji akan wannan Faruk Win."
"I love him so much, in ban aure shi ba ji nake zan iya rasa raina Safna."
"In kuma ya yi aure fa? Ya zaka yi?." Narma ta yi shiru tana kallon Safna alamun tunani kafin ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah ma bai yi aure ba, In ma ya yi auren na san yana sona, zai iya sakinta ya aure ni" ta faWa cikin ™arfin guiwa tana kawar da fuska gefe.

Safna da mamaki take kallon ta kafin ta ce, "oh really?."
"Yes, in ma bai saketa ba zai aure ni naje a matsayin matarsa ta biyu, amma matayina da nata a wajansa da banbanci. Yana sona sosai, yana sona fiye da wacce yake aure, zai bani mahimmaci fiye da ita. In ma ya yi auren kenan, dan na san bai yi auren ba.." Safna ta taSe baki bata ce komai ba tana girgiza kai.KRB3P080
Nana haleema.

Kamar wasa Omar har ya cinye kwanakin da zai yi, ranar da ya faWawa Nayla zai dawo washe gari gigicewa tayi saboda murna. Daman ta dawo Kano tun bayan biki da sati Waya ta dawo gida Mama ta zauna. Mama Sa'adatu ta saka aka yi mata ™unshi ta je gyaran kai aka yi mata sabon gyaran jiki, ga magani mai kyau da Mama ta dinga bata.

Ranar da zai dawo ta koma gida da masu aikin, aka gyara gidan tsaf ya yi kyau ta zauna ta yi abinci mai daWi ba mai yawa ba ta ajjiye. Ta shirya tsaf dan ta san ita zai kira ta je ta Wauko shi  an airport kamar yadda suka yi. Tun tana jiran wayarsa har ta gaji a lokacin azhar ma ta wuce, ta shirya cikin doguwar riga irin shigar da yake so ya ga tayi irinta.

    Tana zaune ta ji an buWe gate, sai ta mi™e ta buWe window tana kallonsa yana magana da yaransa, zuba masa ido ta yi ganin sa cikin shigar da taSa gani ya yi ba. Suit ce a jikinsa blue colour mai duhu, maSallan gabanta a buWe ana ganin farar shit Win da take ciki. Gashin kansa ya sake yin ba™i sannan ya sake yawa, haka gashin fuskarsa ya kwanta luf kamar jikin mage. A bayyane ta ce, "YaMar yana da matu™ar kyau." Nufo falon ta ga ya yi, sai ta Suya a bayan labule tana murmushi zuciyarta na bugawa cike da kewa.

     Sallamarsa ta ji cikin murya mai taushi, ta yi shiru bata amsa ba tana murmushi cikin kewar ganinsa. A hankali ya ce, "Ashiq! kina ina?." Ajjiye jakar hannunsa ya yi, ya shiga ciki ya duba ko ina amma bai ganta ba ya dawo falo ya ce, "Jidda kina ina?" Ya faWa yana Waukar waya yana kiranta. ˜arar wayarta ya ji da take hannunta, ta runtse ido bata so wayar tayi ™ara ba, a hankali ta ga ya tako yana zuwa inda yaji sautin wayar. A tsaye ya ganta ba tare da ya yaye labulen ba, dan wajan da take tsaye ya nuna masa akwai mutum a wajan.

   Murmushi ya yi ya buWe labulen suka haWa ido, dariya tayi mai sauti ta rungume shi ya Wagata cak yana juyawa da ita a cikin falon cikin tsananin kewarta. Murmushi yake yi ya ce, "Jiddana! na ji kin ™ara nauyi" ya faWa yana sauke ta yana kallon ta ya ce, "uhum ko kewata ma baki yi ba, kiSa ki ka yi ki ka sake yin kyau" ya faWa yana shafa fuskarta yana murmushi.

   Murmushin take yi tana kallon sa ta kasa magana saboda farin cikin ganinsa, ganin ta™i magana sai yayi pecking Winta a a goshi. Nayla ta shafa fuskarsa ta ce, "Ka yi kyau Rouhii, kayan nan sun maka kyau sosai, kamar bature." Dan taSe baki ya yi kaWan yana kallon ta ya ce, "Duk na rame saboda rashin ki ki ce na yi kyau?." ˜are masa ta shiga yi ta ga ya Wan rame idanunsa sun sake fitowa waje ta ce, "Allah sarki Rouhii, ka rame kaWan."

"Hmm na faWa miki ina kewar ki sosai Jidda." Kiran sallah suka ji ana yi, ya kalli agogo ya ga ™arfe huWu tayi ya kalle ta ya ce, "Na biya na gaisa da Didi kafin nazo nan

Please Login or Register in order to submit comment