Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masoyi ko wanda ka ke so. Ni kuma na yi miki kyautar wannan sunan Jidda. Ke ce wacce nake so, sannan duk lokacin da na kira ki dashi zan tuna da mahaifiyata haka take kirana. Ke kaWai ki ka cancanci suna,  Ashiqaty!." Ganin tana ta murmushi sai ya ri™e hannunta yana murmushi yana kallon fuskarta.

"Na gode!" Ta furta a hankali ba tare da ta  kalle shi ba. Ya Wora yatsunsa akan goshinsa kamar yadda ya saba, ya Wan shafa kaWan ya Waga gira guda Waya yana kallonta ya ce, "in ki ka gode min ni me zan yi mikikenan?." Bata ce komai ba ya ce, "ke kika cancanci a gode miki Jidda, Omar bai cancanci godiya ba."
ÿþ

Kai ya Wan dafe jin ya Wan sara masa lokaci Waya, ta kalle shi ta ce, "kanka yana ciwo?." Ya kalle ta yana lumshe ido ya ce, "ba sosai ba." A sanyaye ta ce, "Didi ta ce baka ci abinci ba, ka ci abinci." Ya Wan murmusa ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "ta ya zan iya cin abinci bayan na zama silar shigarki halin da baki taSa shiga ba Ashiq? Bana tunanin zan iya cin komai in dai ba lafiya na ga kin samu ba" ya faWa yana juyowa yana kallon ta.

"Ai na ji sau™i, ka je ka ci abincin."
"Zan ci Jidda."
"To ka je." Ya yi murmushi ya ce, "Zan ci, amma sai kin kalle ni." Nayla ta rufe ido da hananyenta cikin tsananin kunyarsa. Omar ya yi murmushi ya ce, "Omar ya yi sa'ar mallakarki a matsayin matarsa Jidda, ina alfahari da hakan." Nayla dai murmushi take yi farin ciki take ji, ji take kamar ta taka rawa amma babu dama. "Ina zuwa" ya furta yana tashi ya fita ta bi shi da kallo tana murmushin jin daWi. A bayyane ta ce, "Ko ina Waure fuskar ta sa ya tafi oho" ta faWa tana murmushi dan ya canja mata, ya koma mata wani daban ba wanda ta sani ba.

    Omar yana fitowa falon ya kalli Didi da take kallonsa, gani t yi ya rame shiyasa ya bata tausayi a lokacin. Ya ce, "bani abincin Didi, kaina ciwo yake yi." Didi ta ce, "dole kai ya yi ciwo ai, Bara na kawo maka." Ta faWa tana tashi ta kawo masa ya zauna yana ci, kuma ya ji daWin abin sosai duk da shima bakina babu daWi.

Yana gama ci ta ce, "ga maganinka nan ka sha." Bai musa ba ya sha maganin ya kalli Marmerh da take hannunta ya yi murmushi ya ce, "ban ga Marmerh ba sai yanzu." Didi ta ce, "kana ta matarka ta ya zaka ya Marmerh?."

Murmushi ya yi ya ce, "bani ita." Bata musa ba ta bashi ita ya ce, "zan yar miki da ita Didi, Wauketa." Didi ta yi murmushi ta ce, "ka ri™e ta bazata faWi ba." Fuskarta yake kallo yana murmushi, ya Wuka ya yi mata kiss a goshi yana jin son yarinyar na zaga ko ina na jikinsa.

Ba tare da ya kalli Didi ba ya ce, "Didi ban taSa Waukar jariri ba sai ita, ban taSa jin son abu yana shiga zuciyata lokaci Waya ba sai ita Didi. Ina sonki Marmerh Didi, ban sani ba ko dan sunan mahaifiyata ne da ita, ko kuma dan ´ar Didina ce.....amma Allah ya sani ina sonta" ya sake faWa yana shafa kumatunta. Murmushi Didi tayi dan itama ta sani, daga haihuwar ta zuwa yanzu kuWin da Omar ya kashe mata ba kaWan bane. Kuma haka kawai zai kira ta a waya ya ce yana gaishe da Marmerh.

Didi ta ce, "To Omar ai ´arka ce, dan ka sota ba laifi ka yi ba."
"Kamar in na ce ki bar min ita zaki iya" ya faWa cike da tsokana yana kallon ta. Ta yi dariya ta ce, "Zan iya mana Omar, Indai babanta zai baka kuma Nayla zata Wauka gaka ga Marmerh nan. Bata da wani uba in ba kai ba, dan na bar maka ita ko a jikina."
"Hmm!" Kawai ya ce yana murmushi yana kallonta.

KarSarta Didi ta yi ya mi™e ya fita, ta biyo bayansa ta ce, "Omar!." Tsayawa ya yi ya kalle ta ya ce, "ni fa zan wuce gida dare yayi." Omar ya ce, "To, amma ki bari na saka Bashir ya mayar dake."
"Yauwa, kira shi. Sannan..." sai ta yi shiru tana kallonsa ya ce, "uhum...ina ji."

Ta sauke numfashi ta ce, "Likita ta ce a bawa Nayla hutu na kwana biyar zuwa sati Waya ko kwana goma. Ta samu ciwo sosai har Winki sai da aka yi mata, tana bu™atar hutu sosai, in ba haka ba zai zama kamar an fama ta ne. Kuma ka tabbatar tana shiga ruwan Wumin nan kamar yadda ka ga na yi, an ce ana so ta shiga kamar sau biyu a rana har sai ta warke. Kuma don Allah in wani ne ya baka wani maganin ka sha har hakan ya faru don Allah kar ka kuma sha, ka ga ka cutar da yarinya bata ji ba bata gani ba" ta ™ara faWa a sanyaye.

    Wata irin kunya ya ji ta lulluSe shi a karo na farko a rayuwarsa, babu halittar da ya taSa jin kunya a duniya sai Didi, shi bai san ma kunyar ba, bai san ya ake jinta ba amma yau kam ya ji kunyar Didi matu™a, musamman bayaninta na farko. Duk yadda ya so ya basar da kunyar amma sai ya kasa, ya Wan Wauke ido daga kanta ya kawar da kai bai ce komai ba. Didi bata lura da yanayinsa ba dan ita kam bata ji kunyarsa kamar yadda tasan baya ji ta ta, ta saba dashi kuma in ba ita Win ba waye zai faWa masa?.

Jin ya yi shiru ta ce, "baka ji me na ce ba ne?." Ya Waga kai ya ce, "na ji mana."
"Yauwa, sannan ga maganinta nan shima ya zama tana sha ko yaushe, Kaima ga naka nan dan har yanzu baka dawo daidai ba." Ya Waga kai bai ce komai ba.

Jin ta yi shiru sai ya juyo ya kalle ta ya yi murmushi ya ce, "Na gode Didi. Allah ya bar zumuncin dake tsakanina dake, Allah ya saka miki da alkhairi. In ba ke Win ba bani da wanda zai share min hawaye kamar haka, Marmerh ko wata Waya bata yi ba amma kin fito tun asuba har yanzu baki koma ba. Na gode Didina!."

Murmushi ta yi tana harararsa cikin wasa ta ce, "ai ba dan kai na yi ba, saboda Nayla nayi. Ka san ´ar da™ina ce tun kafin ka aureta, tun kana yi mata tsawa kana zare mata wannan manyan idanunna naka kana ritsa ta da wu™a. Ka daina gode min, ba dan kai na yi ba dan ita na yi, in dan ta kai ne ko kallon ka na yi."

Yayi murmushi mai sauti ya shafa fuskarsa, ya kalle ta itama dariya take yi kafin ta ce, "Mijina ya kamata ka godewa Omar ba ni ba, ya Wauke ka tamkar ™aninsa yana shiga hidimarka kamar yadda nake shiga. Ba kowa ne zai dinga barina ina zirga-zirga a kan ka haka ba. Tun da cikin Marmerh nake yawo a kanka saboda lokacin aurenka ne da Nayla, ya zo ya girma aka samu damuwar da har ta bar gida, yanzu na haihu kuma ga abinda ya faru. Shi zaka godewa ba ni ba Omar, ina alfaharin samunsa a rayuwata, jinkirin aurensa ya zamar min alkhairi."

Omar ya girgiza kai ya ce, "Haka ne, Zamu zo har gida mu gode." Ta yi murmushi ta ce, "ya dai kamata. Sannan don Allah Omar ka godewa Umma itama." Ya kalle ta bayan ya Wage gira ya ce, "Wacece Umma kuma?." Ta san sarai ya gane wacce take nufi, amma da yake nema take yi sai ta ce, "Umma Saroot, ba dan ita ba da wa zai dinga kula da Marmerh in ina kula da ku? Wallahi ta yi hidima sosai."

Ya taSe baki bayan ya Waure fuska kamar ba shine yake murmushi ba ya ce, "na saka ta ko na gayyace ta? Ke na gayyato ai ba ita ba, dan haka ni babu godiyar da zan mata."
"˜anwar babarka ce fa."
"Ai ba babar tawa ba ce ba ko?."
"Haba Omar, itafa ko lokacin tana sonka wallahi, sunan da Maman mu take faWa maka shi take kiran ka dashi. Ko ta ce Habibi ko ta ce Ashiq kamar yadda Mama ke faWa, Don Allah ka ce mata ka gode ko iya haka ne zata ji daWi."

Omar ya ce, "Daman ai babbar ce shegiyar." Didi ta wara ido ta ce, "Yayar babarka ce fa, haka bai kamata ba. Wallahi zuciyar nan taka ce take haWa ni da kai, ka bar komai ya wuce ka kasa. Inda a kafirai ka zo baza ka karSi musulunci da wuri ba."

TaSe baki ya yi ya share zancen kar ma ta Sata masa rai ya ce, "Nawa aka kashe asibiti?." Didi ta ce, "zan duba na gani."
"Ki faWa min kawai, bana son wanann zagaye-zagayen nan naki."
"Ikon Allah! Na ce zan duba ko?."
"In ma baki duba ba zan tura abinda na yi niya. In kinga dama ki yi amfani dasu, in baki dama ba ki zubar!" Ya fada yana wara idanunsa a kanta.

Dariya ta yi sosai tana kallonsa, dariyar ta ta ta Waauki hankalinsa ya tsaya yana jiran ™arin bayani. Ta tsayar da dariyar ta ce, "ka san ne na tuna?." Ya girgiza kai alamun a'a, ta girgiza kai tana ´ar dariya ta ce, "Lokacin da aka yi ™o™arin raping Nayla, ka dawo da ita gida kana ta yiwa mutane masifa, ashe ashe kanka ka ke yiwa tanadi. Kalle ka, sai murmushi ka ke yi kamar ba Omar Tiger ba, ni nasan ungulu bata jewar banza" ta faWa tana dariya ta wuce ta bar shi a wajan. Shima dariyar ya yi ya girgiza kai, kuma abinda ta faWa Win gaskiya ne shi bai ma kawo hakan a ransa ba.

Abinda ya bata mamaki lokacin da suka fito ita da Umma ta ga ya kalli Umma ya ce, "an gode." Sai ta ga Umman ta ruWe tana ta murmushi Didi taji daWi a ranta sosai, a karo na farko da magana mai daWi ta haWa shi da dangin babarsa kenan. Ba jimawa Bashir ya zo ya Wauki motarsa ya tafi mayar da Didi gida.KRB3P053
Arewabooks@nanahaleema11.

Omar wajan Nayla ya koma amma sai ya tarar tayi bacci, ya yi murmushi ya ™arasa ya rufe mata jikinta ya fito ya shiga Wakinsa. Yan nan kaca kaca yadda suka bar shi, ya shafa kansa yana kallon Wakin yana tuna abinda ya faru da abubuwan da suka biyo baya. Kai tsaye frame Win da ta kafa ya kalla wanda ya zama silar faruwar komai, ya ™arasa yana kallon frame Win yana kallon yadda zanen tiger Win yayi bala'in kyau.

    Barin wajan ya yi ya kalli kettle Win da ya ajjiye, sai ya duba hannunsa ya ga inda ruwan zafi ya Wan zuba, wajan ya Wan tashi har ya yi ba™i. Fara gyara Wakin ya yi, ya Wauke bedsheet Win da ya cire ya kai banWaki ya buWe washing machine Win ciki ya saka, ya dawo ya buWe wardrobe ya Wauko asalin bedsheet Win da aka saka da ta tare a gidan wanda aka wanke ya shinfiWa. Cikin lokaci kaWan ya gyara Wakin kamar mace, ya yi ajiyar zuciya yana kallon agogo. Kiran sallah ya ji ana yi, ya shiga banWaki ya yi alwala ya fito ya fita zuwa masallaci. Har ya dawo bacci take yi bai tashe ta ba ya zauna dan har lokacin ba shi da wani ™arfin jiki yadda ya kamata.

    Nayla bata farka ba sai bayan sallar i'sha, da ya dawo daga sallah ya tsaya suna magana da Bashir sannan ya shigo ciki ya tarar itama ta idar da sallah tana zaune akan sallaya. ˜arasowa ya yi inda ta ke zaune, a lokacin ta mi™e ta zauna a kan gadon a hankali, shima ya zauna a kusa da ita ya ce, "Bacci ba ya yi miki wahala." Sunkuyar da kai ta yi bata ce komai ba ya ce, "Me zaki ci?." Nayla ta yi shiru bata amsa ba, ya sake maimaitawa a hankali ta ce, "Babu."

Omar ya ce, "ki dai tuna." Nayla ta ce, "bana jin cin komai, amma....." sai ta yi shiru bata ™arasa ba, ya zuba mata ido yana kallon ta ya ce, "uhum, ina jinki." Nayla ta ce, "Ina sha'war shan fura da nono." Ya girgiza kai ya ce, "to zaki samu, ki jira na je na kawo miki...." Ta Waga kai alamun to, ya sake kallon ta ya ce, "Na so abinci ki ka ce kina so, da na dafa miki da kaina, amma ki bini bashi" ya faWa yana murmushi ya tashi ya fita.

Nayla ta yi ajiyar zuciya ta bishi da kallo tana mamakinsa, gabaWaya ya canja mata, ya tashi daga Omar Win gidan Didi ya koma mata wani daban wanda bata san shi ba, ya koma mata kamar wani ruwan sanyi, ya koma mata kamar abokin wasanta, ko yaushe cikin murmushi yake kamar ba shine kullum fuska a Waure yana harararta ba. Ko dan ya saka ta jinya ne ya koma haka bata sani ba.

Babu jimawa ya dawo da leda a hannunsa, ya shigo Wakin ya zauna ya ce, "to gashi" ya faWa yana buWe robar ya mi™a mata. Mi™o hannu tayi zata karSa sai ya ga hannun nata kamar yana rawa, ya dakatar da ita ya ce, "barshi ba sai kin ri™e ba, zan baki da kaina." Kamar yadda ya ce Win kuwa shi ya bata furar da kansa, ta sha da yawa dan kaWan ta rage ya ajjiye. A sanayaye ta ce, "kai baka so?." Kai ya girgiza bai ce komai ba, Nayla ta ce, "meyasa?." Ya kalle ta suka haWa ido ta sunkuyar da kai ya ce, "Bana jin yunwa."

"Don Allah ka sha, kaima baka da lafiya."
"Ni waye ya ce miki bani da lafiya?."
"Ni na san baka da lafiya, har maganarka ta canja kamar wanda yake mura."
"Tunda baki da lafiya nima bani da lafiya, amma yanzu bana jin yunwa ban sani ba ko anjima."

    Shiru tayi bata ce komai ba tana wasa da hannunta, ya kalle ta sai ta suka haWa ido sai rufe ido kafin ta buWe a hankali ta ce, "Ban ga wayata ba yau gabaWaya." Kan madubin Wakin ya kalla ya ga wayar, ya tashi ya Wauko mata ya mi™a mata bai ce komai ba. KarSa tayi ta ga kiran Salma da na Jidda har da na Mama da Ya J. Nayla ta girgiza kai ta ce, "ana ta yi min waya" ta faWa tana ajjiye wayar a gefenta.

Shiru ta ji bai ce komai ba itama haka. Shirun ya ratsa Wakin kafin ya ce, "Yaunzu ya jikin? Didi ta ce min na tabbatar kina shiga ruwan zafin nan kuma kina shan magani. Ki faWa min in kin samu sau™i?." Nayla ta kulle ido bata ce komai ba, dan ya bata kunya musamman da ya saka Didi a maganar. Shiru ya biyo ba ya bai ce komai ba itama bata ce komai ba.

A hankali ta ce, "Ya Didi ta je gida? Ka kira ta?." Ya Waga kai ya ce, "uhum na kira ta, tana gaisheki." Ta Waga kai bata amsa ba, ya lumshe ido ya buWe a kanta yana ™are mata kallo. Abin mamaki yake bashi, wai shi da wata mace yanzu babu wani sauran abinda ya rage, ya zama ita ta zama shi, ga tarin soyayayr da yake mata wacce bai san adadin yawan ta ba. In aka ce hakan zai faru a rayuwarsa zai ce ™arya ne, amma gashi ya faru cikin ruwan sanyi, kuma jikinsa da zuciyarsa sun karSi abun hannu biyu.

     Šago ido ta yi jin shiru ya yi yawa ta kalle shi suka haWa ido alamun kallon ta daman ya ke yi, ta yi saurin sunkuyar da kai. Murya a ™asa ya ce, "meyasa baki son kallona?." Tayi shiru bata amsa ba ya ce, "meyasa." Jin ya maimaita sai Nayla ta ce, "bana iya kallon idanunka, kuma kunyarka nake ji" ta faWa tana rufe fuska da hananyenta.

Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "kunya!...." Ya sake murmusawa ya ce, "A karo na farko a rayuwata na ji wani abun kunya, ban taSa ji ba sai Wazu da Didi take min bayani akan Sarnar da na yi a jikinki. Sai na ji nauyinta sosai, amma daga nan komai ya wuce."

Kalamansa ya sake bata kunya sosai, ta runtse ido cikin kunyarsa da kuma kunyar Didi da kunyar abinda ya faru. Bai lura da yanayin ta ba ya Wan yi murmushi ya ce, "Ni fa a kanki na aikata abubuwan da ban taSa aikatawa ba a rayuwata. Tunda ki ka shiga rayuwata abubuwa suke ta faruwa dani wanda basu taSa faruwa ba sai a kan ki kawai." Ta Wago a hankali ta kalle shi ya Waga gira ya ce, "Na lissafa miki?."

Kai ta Waga alamun eh, ya matsa kusa da ita ya ri™e hannunta cikin kasalalliyar murya ya ce, "ke ce mace ta farko da Didi ta taSa yi min faWa a gabanta...." Ya dakata da maganar saboda ´ar dariyar da Nayla tayi alamun ta tuna.

Bata yi magana ba sai Wauke kai da tayi ya ce, "Da gaske kece ta farko, ni ba a yi min faWa a gaban kowa musamman baki. Abu na biyu kuma na ce zan Wauki mataki a kanki akan hakan amma sai na kasa aikatawa, amma da wata ce ba ke ba har abada bazata sake marmarin zuwa gidanmu ba, kin dan waye Tiger a baya ba sai na faWa miki ba. Abu na uku; a kanki Didi ta ce na fita na bata waje, hmm...! lokaci daga Abuja na dawo, ko sannu da zuwa bata ce min ba. Na ji haushinki sosai, ina mamakin meyasa ki ke shiga rayuwata ne har haka?. Na uku; a kan ki ta ce min ina shirme, kuma ke ce ki ka yi min korar shaiWanu ban Wauki mataki ba."

³ar dariya Nayla ta sake yi tunawa da abinda ya faru, sai ya dakata da maganar yana kallonta ganin tana dariyar da ta Wauki hankalinsa. Ya yi shiru bai ce komai ba, ta kalle shi suka haWa ido ya ce, "Kuma tun farko kece wacce Didi take yawan saka ni a lamarinta, haka kawai in ki ka shigo ki ka fita sai ta fara labarinki, sai na ji haushi na ce wai wannan wacece ne da zata ™wace min Yayata?. Ke ce mace ta farko da ki ka fara bani kyauta na karSa har na yi amfani dashi, kin bani kyutar azurfa gata a hannuna, kin bani kyautar turare har yanzu na kasa ™arar dashi saboda son da nake masa, kin bani kyutar riga wacce da ita na kwanta a asibiti a jiya."

Hannunsa ta kalla ta ga azurfar kuwa tana nan, ta Wora hannu a kai ya ri™e hannayen nata ya ce, "Kece mace ta farko da na fara jin nauyi da girman iyayenta a duniya, a gaban Abiy na kasa samun sukuni, nauyinsa ya rufe min idanu, na rasa abinda nake ji. Ke ce mace ta farko da ki ka fara kirana da Yayaaaa!" Ya Wan sauke numfashi kaWan ya ce, "Ya ilahii......!har yanzu na kasa manta lokacin da mu ka je g1danku, ki ka ce Yaya Omar Allah ya kiyaye hanya, a daidai lokacin hawaye ya sakko daga idanunki kuma kina murmushi. Kin tuna?."

Wasu hawayen ne a idanunta, ta Waga kai alamun eh ba tare da ta kalle shi ba ya ce, "kina lissafawa dai? Ni na Sata a lissafin."

Bata bashi ba amsa ba ya ce, "kece mace ta farko bayan Didi da na ci abinda ta sarrafa, Didi ta faWa min lokacin da ki ka dafa awara na ci har naji tayi min daWi. Jidda ke ce mace ta farko da na karSi aurenta, ke ce mace ta farko da na zauna da ita a gida Waya, kece mace ta farko da na ke shiga lamarinta har na saurereta. A kan ki na fara jin kishi tun ban san ina sonta ba, ke ce mace ta farko da na kwana a gado Waya da ita, ke ce mace ta farko da na damu akan rashin lafiyarta, ke ce mace ta farko da na ji a raina in wani abun ya same ki bazan ji daWi ba" ya sauke ajiyar zuciya ya matse hannayenta, ya sake yin ™asa da muryarsa sosai ya ce,

"Ban taSa karya rantsuwa ba, in na rantse na rantse kenan bana canjawa, shiyasa ban cika yawan rantsuwa a rayuwata ba, dan babu halitttar da ta taSa karya min rantsuwa. Ke ce mace ta farko da rantsuwar ta karye ta dalilinki. Ke ce mace ta farko da na ji a raina in na rasa ta bazan iya rayuwa ba, ke ce mace ta farko da na furta mata kalmar ina sonki, ke ce abu na farko da na ce na bar shi amma na kasa bari, ke ce ta farko da nake tsananin ™auna, nake ji kamar na mayar da ke zuciyata. Ashiqaty!" Ya furta can ™arshen ma™ogwaro yana kallon idanunta.

Shiru ya sake yi yana kallon ta, zuciyarsa na cigaba da antayo kalamai kan harshensa ya ce, "Ke ce ta farko da na san meye so a kanta, na banbance soyayyar burgewa da soyayyar gaskiya a kanki. A kan ki na fara sanin mace, da ke kaWai na taSa haWa jiki Jidda, ke kaWai ce ki ka san waye Omar in and out. Kuma ke ce wacce na taSa bawa ha™uri a duniya Jidda!."

Lumshe ido tayi ta kwanta a jikinsa dan farin cikin ya yi mata yawa tana so ta jita a jikinsa a wannan lokacin, ya rungumeta sosai yana shafa bayanta a hankali cikin salo na ™auna. Ya sake yin shiru bai ce komai ba, idanunsa a lumshe yana ji kamar ya buWe ™irjinsa ya saka ta ya huta da bugawar da zuciyarsa take yi masa. Ya buWe ido ya ce, "abu nawa na lissafa?." Nayla ta ce, "nima na Sata a lissafin, amma dai sun fi fifty." Dariya ya yi kaWan ya ce, "to duk ta dalilinki ya faru, na ™ara miki da wani ma guda Waya....a kan ki nake ta yawan murmushin, ko Didi albarka."

Murmushi ta yi tana daga jikinsa yana shafata a hankali cikin salo na soyayya da kwantar da hankali da nuna tsansar kulawa a gare ta. Shiru ya biyo baya, ta yi luf a jikinsa ko motsin kirki bata yi. A hankali ya ji ta ce, "ban Wauka zaka saka azurfar da na baka ba, lokacin da na ganta a hannunka na yi mamaki sosai. Ban Wauka zaka yi amfani da abinda ya fito daga hannuna ba, ganin haushina ka ke ji." Cikin shau™in ™aunarta ya ce, "Haushin na ki shine soyayyar Jidda!. Wannan soyayyar da nake miki ba wacce aka samu a kwanan nan bane. Ni na san ta jima a zuciyata, ban fahimta ba ne sai bayan kin bar ni, kishin kuwa tun shekara goma baya."

    Ta Wago ta kalle shi ya Waga gira sama ya ce, "eh mana. Na kuSutar dake daga wanda suka ke ™o™arin yi miki fyaWe, na ji zafi a raina har ta kai ga na yi amfani da wu™a dan hukunci. Jidda daga wannan ranar na fara fitar da jini daga jikin wani, a ranar na yanke masa ´an yatsunsa saboda ya yi ™o™arin taSa min ke. Tsananin kishinki da na ji a lokacin shine ya kai ni ga aikata hakan. Ban fahimta ba, ban kuma gane ba, amma na tabbatar da daga wannan lokacin soyayyarki ta samu gurbi a zuciyata. Tunda aka samu kishi tabbas akwai soyayya, yadda hankalina ya tashi na dinga yiwa Hajja faWa ni kaina abin ya bani mamaki. Kuma gashi lokacin da ™uruciya a tare dani, amma na ruWe a kan abinda aka yi ™o™arin yi miki, in ba soyayya ba meye Jidda!?." ya ™arasa faWa yana kallonta.

Ya Wan taSe baki kaWan yana kallon ta ta ™asan idanu ya ce, "Ashe faWan da na yi akan abinda ya ke mallakina kuma halak Wina ne,

Please Login or Register in order to submit comment