Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sama da abinda ta ce.

Mun ta ce, "Why Ashraf? Ka kira shi mana yazo a yi magana a Waura musu aure kawai a wuce wajan. In ta tabbatar tayi aure zata manta dashi gabaWaya." Dad ya yi shiru yana tunani kafin ya fara oarin kiran waya.

A lokacin aka yi sallama aka shigo falon. GabaWayan su kallon wajan suka yi ga mamakin su Ashraf ne. Zama ya yi a kan kujera sannan ya ce, "i'm sorry na shigo without notice. I'm so worried about Narma Dad, bana samun ta a waya komai ya lalace gabaWaya." Mum ta kalle shi ta ce, "maganar ka mu ke yanzu. Ka san wannan Wan daban ya yi mata asiri ko?."
"Yes Mum, ta yi min maganarsa tun kwanakin baya wai shi zata aura." Dad ya ce, "har yanzu asirin nan bai sake ta ba Ashraf. Daman tunani nake akan wani hukunci da na yanke, ban sani ba ko zaka yi accepting."

Ashraf ya ce, "Ina ji Dad."
"Zaka iya amincewa da auren Narma a yanzu? I mean cikin week Win nan a Waura muku aure ku bar Nigeria after some days sai ku dawo ayi biki?." Ashraf ya yi murmushi ya ce, "why not Dad, na amince ko yanzu a Waura auren." Mum ta yi murmushi ta ce, "thank you my Son, You've saved her life. That man was driving her crazy! Wahalalle kawai mai asiri."


Ashraf ya murmusa ya ce, "Mum Narma means the world to me, I would take any risk and do whatever it takes to keep her safe. Wannan ba komai bane ki daina yi min godiya." Dad da murmushi ya ce, "ya ka ke ganin za a yi abin? Zaka yi inviting friends Winka ko a'a?."
"I will, but some, ba kowa zan faWawa ba sai close friends Wina. Sai cousins da sauran su dai."
"Good. Zan yi magana da governor in sha Allah a week Win nan komai zai are."
"Thank you so much Dad." Dad ya murmusa kawai babu yadda zai yi ne shiyasa ya ke aikata haka amma shi ma ya san bai kyautawa Narma ba, bata shirya ba kawai ya Waura mata aure ai babu daWi, to bashi da mafita dole ya yi hakan.


KRB2P015
Arewabooks@nanahaleema11.

An kai amarya gidan ta mai kyau ana ta yabon kyaunsa saboda ko ina a gidan yayi kyau sai dai babu mutane sosai a kusa da ita amma kyau kam gida ya yi kyau. Jinkirin auren ta bai tashi a banza ba ya zame mata alkhairi domin kuwa da gidanta da lefen ta komai ma sha Allah.

Su Nayla gida suka dawo suna sauka a ofar gidan Hajja suka hangi Omar a zaune a ofar gidan Didi akan farar kujera ya Wora afa kan Waya yana kaWawa. Nayla murmushi tayi ta Wauke kai ta shiga gidan Hajja bata sake kallon sa ba.

Shi kuwa Omar kewa yake ji sosai a zuciyarsa, ya rasa abinda zai yi ya ji daWi. Ya san Didi kuka zata yi in suka haWu shiyasa ya gudu bai bari sun haWa ba dan baya son ganin kukanta. Gidan yake son shiga amma in ya tuna bata nan sai yaji babu amfanin shigarsa gwara yayi ta zaman a ofar gidan in yana ganin mutane zai fi jin daWi. Bai san ya damu da Didi ba sai yanzu, bai san haka Didi take da tasiri a gare shi ba sai yanzu, bai Wauka zai yi kewarta har haka ba sai ya tabbatar da bata nan.

A kan idanunsa su Nayla suka shiga gidan Hajja ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da zama a wajan. Sai sha biyu na dare sannan ya iya miewa ya shiga gidan, kewarta ta damu zuciyarsa sosai, haka ya zubawa ido yana kallo kamar zai ganta ko ya ji muryarta, ga tausayin Narma zuciyarsa. Tabbas yana jin tausayin Narma amma babu abinda zai mata in ba ya nisanta kansa da ita ba shiyasa ya aikata abinda ya aikata. Da wannan tunanin ya kwanta yana tunanin Didi bacci ya Wauke shi.

Washe gari.

Nayla haka ta tashi da nauyin jiki tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atampa mai kyau. Falo ta fito wajan Hajja ta zauna a kan kujera ta ce, "Hajja Baba Salisu ya taho yazo zamu wuce gida." Hajja ta bita da kallon tuhuma ta ce, "Hauwa me ya ke damunki ne haka?." Hajja ta kalli Salma da ta fito tana shan tea ta ce, "Salma me yake damun ar uwarki?."

Salma ta zauna ta miawa Nayla cup Win tea Nayla ta karSa ta ce, "na gode." Salma ta kalli Hajja ta ce, "Hajja bana ce ba, ni ma dai haka nake ganinta. Kawai ki ta yi mata addu'a." Hajja ta ce, "Me ya ke damunta? In ba zaku faWa ba zan kira babanta na tambaye shi. Ya ina tambayar ku kuma ce min babu komai? Ina ganin duk wani motsin ku fa, yadda ku ke yin komai a sanyaye na tabbatar akwai abinda yake damunta." Nayla ta ce, "Hajja babu komai ba wani abun bane, shima Abiy Win haka yake cewa kuma na faWa masa babu komai."

"Mu in baki faWa mana ba ai Salma da Jidda sun sani." Salma ta ce, "Hajiya ni ban san komai ba gaskiya sai dai ko Jidda" ta faWa tana miewa ta bar wajan. Hajja tayi musu banza bata sake magana ba amma tayi kuWurin tambayar Abiy abinda yake damun Nayla.

Lokacin da Baba Salisu yazo sai da ta kai masa abinci kamar ko yaushe, ta dawo daga kai masa abincin idanunta ya sauka akan masoyinta yana tsaye suna magana dasu Bashir suna nuna masa wasu kaya a leda. auke ido tayi tana takawa a sanyaye ta shiga gidan Hajja ba tare da ta sake kallon sa ba dan gabaWaya hankalinsa baya kanta. Bata jima da shiga ba ta gama haWa abinda tazo dashi ta kai mota, Baba yana gama cin abincin ya huta tayi musu sallama Salma ta rakata har bakin mota ta shiga suka tafi.

" " " " " "

Amarya Didi ta wayi gari a gidan miji cikin aminci da kwanciyar hankali, ganin abun take kamar a mafarki wai itace tayi aure bayan shekarun da ta kwashe ba tare da auren ba. Tana girmama ikon Allah da kuma lokaci da mutane suke faWa sai yazo komai zai faru. Tabbas ta amince da aure lokaci ne, duk yadda ka kai ga son yinsa in lokacin yin bai yi ba baza ka yi ba. Kamar mutuwa ce, duk yadda ka kai ga yin jinya in lokacin mutuwar bai ba babu inda zaka je, amma da zarar lokaci yayi kamar iftawar ido anyi an gama. Ita kam taga tasirin hauri, taga tasirin miawa Allah lamarinta, taga tasirin in sanya damuwar rashin aure a zuciyarta. Gashi fa lokacin yayi har ta wayi gari a gidan mijinta kamar almara.

Tana zaune a falon ta gabaWaya kewar Omar ta cika mata zuciya, AbdulHamid ya shigo falon da sallama ta amsa ya ce, "Omar Win kike tunani ko?." Didi tayi dariya ta ce, "wallahi, ina ta tunanin ko ya ci abinci." Ya yi dariya ya ce, "banda abin ki Omar ai ba yaro bane ba" ya faWa yana zama kusa da ita.

Didi ta ce, "baka san halin Omaar bane, baya son cin abinci sai ance masa gashi, ko ance gashi Win sai yaga dama. Bara ba kira shi" ta faWa tana Waukar wayata kira shi. auka taji anyi ta ce, "Assalamu alaikum." Daga can Sangaren Omar ya ce, "Wa'alaiki Salam, Hajiya Didi amarya."
"Alhaji Omar anin amarya." Dariya Omar ya yi ya ce, "ya naji maganar ki a dashe? me ya same ki?."
"Babu komai, mura ce kawai." Omar ya ce, "Kin sha ruwan sanyi kenan, shi bai san in kika sha ruwa mai sanyi kina tari ba ya bari ki ka sha?."

AbdulHamid da yake surarensa ya yi murmushi amma bai ce komai ba. Didi ma murmushin tayi ta ce, "jiya shine ka gudu ko?." Omar ya ce, "ni ai bana guduwa, kawai na Suya ne saboda ban son damuwa." Didi ta ce, "HaWuwa dani Win ne damuwa?."
"Kukan da zaki yi min shine damuwa, a haka ma kin barni da tunani inaga kin saka ni gaba da kuka?." Didi tayi dariya ta ce, "To yaushe zaka zo?."

"Zan zo, Zan zo ko dan na yiwa mijin ki huWuba ya san wacce yake aure, akwai gaSar da zan tabbatar masa da Yayar Damisa yake aure." Didi da AbdulHamid suka yi dariya gabaWaya AbdulHamid ya ce, "To Alhaji Omar ina nan jiran ka, Allah ya kawo ka."

Murmushi shima ya yi Didi ta ce, "ka ci abinci? Har sha biyu na rana tayi, Allah ya sa ka karya." Omar ya ce, "ban ci ba, ban jima da tashi ba. Yanzu dai nake tunanin abinda zan ci."
"Ka tashi ka yi girki mana, akwai abinci a kitchen da gas da komai ka dafa ka ci don Allah."
"To Didi zan ci."
"Ka kuma shiga gidan Hajja kayi mata godiyar abubuwan da suka faru."
"Didi nifa bana son godiyar nan kin sani."
"Ta zamar maka dole ne Omar, ta zama dole kaje kayi mata godiya." an tsaki ya yi ya ce, "to zan je."

Didi ta ce, "zan kira ka in anjima naji in kaje." Da to ya amsa a taaice ya kashe wayar ta kalli AbdulHamid tana murmushi. Shima murmushin yayi ya ce, "Kina ji da Oamar kamar yadda yake ji dake." Didi ta ce, "to mu kaWai Allah ya bawaa iyayen mu, kuma iyayen na mu su ma babu."
"Gaskiya ne. Allah ya ara muku zumunci." Ta amsa da amin tana murmushi yana ta tsokanarta da sunan amarya ita kuma tana murmushi cikin jin nauyi.

Bayan Kwana biyu.

*Abuja.*

Najwa tausayin Narma take yi sosai, gashi ana ta batun Waura aurenta a ranar kuma bata sani ba. Duk tayi wani iri kamar ba ita ba kana kallon ta kasan tana tattare da damuwa mai yawa. Najwa ta fita wajan mahaifinsu ta zauna ta ce, "Dad don Allah kar a Waura auren nan, ku yaleta taji da abinda yake damunta mana don Allah. In kuka aura mata Ashraf yanzu ba shi take so ba, ku yaleta taji da damuwarta."

Mum ta kalle ta cikin harara ta ce, "kin fi mu sanin abinda ya kamata ne?." Najwa ta ce, "A'a Mum, Amma ina guje mana danasani a nan gaba." Dad jikinsa ya yi sanyi, maganar Najwa gaskiya ce amma bashi da zaSi ko mafitar da ta wuce wannan, kuma dole ita zai bi dan samar mata da lafiya da kwanciyar hankali ta kuma manta da batun Omaar gabaWaya a rayuwarta.

Dad ya ce, "Najwa ki bar zancen nan, aure za ayi shi yau in Allah ya kaimu. Sannan bance ki faWa mata ba." Najwa ta tashi ta bar wajan cikin tausayin Narma sosai.
Narma tana zaune tana shan tea a falon sama tayi wanka ta saka ananun kaya riga da wando, wando iyakarsa guiwa sai riga mai baya a buWe. Najwa wajanta ta dawo ta zauna bata ce mata komai ba itama bata ce ba tea kawai take sha a hankali.

Sun jima a haka kafin suji ana hayowa sama ba tare da ta kalli wajan ba ya dai jin motsin mutane. Muryar Dad ta ji yana cewa, "gata nan ma a zaune." Kallon wajan tayi sai ta ga gwamna Katsina ne da Ashraf da kuma minister sai Dad da Mum da Nabil. Bata yi oarin miewa tsaye ba Dad ya karaso ya zauna kusa da ita mahaifin Ashraf shima ya zauna ya ce, "Daughter ya jikin na ki?."
Murmushi tayi ta ce, "Da sauki Daddy. Ina yini."
"Lafiya lau. Ina fatan babu abinda yake damun ki?."
"Babu komai Dady" ta faWa tana Wauke kai daga wajan.

Ya ce, "ma sha Allah, Allah ya ara lafiya." Ta amsa da amin tana ji suna maganar da ita ba ganewa take yi ba kafin duk su sauka ya rage daga Dad sai Mum sai ita a wajan. Dad ya kalle ta ya ce, "Narma yanayin damuwa da tashin hankalin da kike ciki, yau ciwo gobe lafiya shiyasa muka yanke hukunci a kanki." Da sauri ta kalli Dad ta ce, "ka yarda da Omaar?." Mum ta yi tsaki ta ce, "waye wani Omaar? Daughter ki nutsu mana, ki daina zancen wannan banza."

Shiru tayi bata ce komai ba. Dad ya ce, "Ashraf shine saurayinki wanda zaki aura a baya, kina sonsa shima kuma yana sonki. Wannan dalili ya saka yau Win nan mun Waura auren ku ke dashi, zaku tafi America ku je ku huta in kika nutsu sai a dawo ayi biki gabaWaya." Kofin da take shan tea ne ya suSuce daga hannunta ta kalli Dad murya na rawa ta ce, "au....re...Dad?."
"Yeah Aure, an Waura miki aure keda Ashraf yanzu. Kuma gobe in anjima zaku tafi america ku huta daga baya sai ku dawo."

Narma kallon mahaifin nata take yi ba tare da ta iya cewa komai ba, muryarta rawa take yi haka jikinta ma rawa yake yi cikin tsananin tashin hankali. An aura mata wani ba Omaar ba? Kenan yanzu bata da hope Win aurensa ake so ace ko me?. Ganin yadda jiki ta yake rawa ya saka Mum ta rieta calmly ta ce, "Calm down my daughter! Kar ki damu Ashraf yana sonki kuma zai kula dake yadda ya kamata. Mun yi haka ne saboda ki dawo nutsuwarki bama so mu dinga ganin ki cikin damuwa."

Murya na rawa ta ce, "Mum in dai bakwa sona cikin damuwa meyasa baza ku aura min Faruk ba? Meyasa baza ku amince na aure shi ba?. Bana son Ashraf, Faruk nake so dashi nake so nayi rayuwar aure ba Ashraf ba, don Allah ku ce wasa ku ke yi min ba ku yi min aure dashi ba, please Dad you're just kidding me right?" ta faWa tana haWe tafukan hannayenta waje daya alamun roo.
Mum ta ce, "Zaki manta dashi a hankali, asirin da yayi miki zai bar jikinki saboda tasirin auren da aka yi miki. Kar ki damu ki nutsu."

Narma kuka take yi sosai zuciyarta nayi mata zafi, shikenan an rabata da Oamar Winta kenan? Shikenan yanzu bata da damar aurensa tunda gashi an aura mata wani ba shi ba. Tuna hakan ne yake sakawa ta ara arfin kukanta cike da unar zuciya. Rarrashinta suka dinga yi amma tai ta daina sai kawai Dad ya kira Ashraf ya ce ya hayo saman, yana shigowa saman ya samu tana wannan kukan duk sai jikinsa ya yi sanyi.

Dad ya kalle shi ya ce, "ka rarrasheta" abinda ya ce kenan suka bar musu wajan shi da Mum. Ashraf a hankali ya taka zuwa inda take ya Wagota daga kan kujerar ya haWata da jikinsa ya rungumeta tsamtsam yana shafa fatar bayanta a hankali kasancewar rigar bayanta a buWe yake. A kunne yake raWa mata yana cewa, "Shiii! relax my wife, i'm here for you, stop craying."

Kuka take yi sosai a jikinsa shi kuma ya matse ta ya hanata koda motsin kirki sai kukan da take yi. "Ki bar kuka my wife Ina tare dake a ko yaushe, bana so ki dinga zubar da hawayenki. Ina sonki zan zauna dake a ko wanne yanayi ki ke, don't be nervous about this early marriage. I'll take care of you, i promise i'll always be there for you and make you happy. I love you so much my love, I love you! I love you! you're my heart, you're my life, you're my world. Stop crying, please..." a kunne yake raWa mata cikin salo mai Waukar hankali da son rarrashi yana sake hura mata iska a cikin kunnenta tare da sake matse ta a jikinsa.

Narma duk tana jinsa amma bata daina zubar hawaye ba, imagination take yi wannan kalaman da yake faWa mata ace Faruk Win tane yake faWa mata da bata san farin cikin da zata yi ba, hango kanta take a rungume a jikinsa ya matse ta yana faWa mata wannan kalaman. Nan take tsigar jikinta tashi ta runtse ido zuciyarta na bala'in bugawa har shi Ashraf yana jin bugun zuciyar a jikinsa.

Ido a kulle tana daga jikinsa ta ce, "I love him, I love Faruk. Dashi nake so nayi rayuwa, shi nake so na aura. Bana son zama da kai, dashi nake so na zauna......!" ta furta cikin wata irin murya mai nuni da raunin da yake tare da ita. Maimakon ya ji haushin kalamanta sai ya zaunar da ita akan kujera ya zauna a gefenta ya rie hannunta ya ce, "ina jin irin abinda ki ke ji, komai zai wuce na tabbatar da kina sona soyayyata zata dawo a cikin zuciyarki. Ina so kawai ki nutsu ki bani dama zan saka ki manta dashi a cikin rayuwarki gabaWaya."

"Bazan taSa mantawa dashi ba, shi nake so ba kai ba, shi nake so na aura ba kai ba, dan haka ka yale ni" ta faWa tana miewa da sauri ta shiga Waki tare da kulle ofa ta saka key. Bai yi oarin binta ba sai ma murmushi da yake yi, tunda dai an aura masa ita koma me zata yi daga baya ne.

Narma tana shiga a kan gado ta zube tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya, lokaci Waya kanta yayi nauyi sosai saboda ciwo idanunta suka tasa saboda kuka. Sai da tayi kukan mai isarta sannan ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya. A sanyaye ta Wauki waya ta nemo number Omar da tayi saving da my Faruk ta kira. Bata da tabbacin zai Wauka ko bazai Wauka ba, ta yi shiru tana jiran tsammani.

it taji ta katse alamun bai Wauka ba ta ajjiye wayar a gefe tana kallon sunansa cikin bahagon yanayi. Kamar a mafarki sai ga kiransa na shigowa ta zabura ta Wauki wayar hannu yana rawa ta kai kunnenta. Kafin ya yi magana ta ce, "Hello...hello...my Faruk kaine ka kira ni?......Wayyo Allah! yau ya kira ni, Allah na gode maka. My Faruk Ina kewar ka Ina so na ganka..." abinda take faWa kenan a ruWe kana ji kasan bata cikin yanayi mai daWi.

Omar da yake jinta bai ce komai ba ta sake cewa, "My Faruk su Dad suna son kashe ni, wai sun Waura min aure da wani ba kai ba, mutuwa kawai zan yi....!" Ta faWa cikin kuka mai ban tausayi. Omar ya lumshe idanu jin abinda ta ce, maganar tayi masa daWi kuma bata yi masa daWi ba. angare Waya yaji daWin aurenta kodan ta daina takura masa ta daina damun kanta a kansa ta san ita matar aure ce. angare Waya kuma bai ji daWi ba saboda tausayinta, ya san tana sonsa, aura mata wani a wannan yanayi bazai mata daWi ba.

Narma ta ce, "ni da kai nake so na rayu, bazan iya rayuwa da kowa ba sai kai. Don Allah ka amince nazo na zauna da kai, ni kai kaWai nake so nayi zaman aure dashi ba wani ba. In na zauna da Ashraf mutuwa zanyi! Bana sonsa, kai nake so da kai zan rayu......!"

"Narma! Ki nutsu" ya furta a hankali cikin murya mai taushi. Numfashi taja kamar ya saka mata pause ta dakata da kukan sai ajiyar zuciya da take yi. Ya sake cewa, "Kin ce an Waura miki aure ko?." Kamar tana gabansa ta Waga kai ta ce, "eh, amma bana sonsa, ni kai...." Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa, "Matar aure ce ke, furta kina son wani ba mijinki ba babban laifi ne. Kina jina?."
"Ina ji" ta faWa murya na rawa sosai.
"Waye ni a wajanki?."
"Wanda nake matuar so, wanda nake so na rayu dashi har a aljanna."
"Na isa nace ki yi abu ki yi? Na isa na ce ki bari ki bari?."

Narma ta ce, "har ka yi yawa ma Faruk! Har ka yi yawa wallahi. Zan iya sadaukar maka da raina da rayuwata." Ya Wan yi jimm kafin ya ce, "to ki rie aurenki, ki yi abinda iyayenki suke so ki zauna da mijinki..." Katse shi ta yi ta ce, "Amma bana sonsa, bana aunarsa ta ya zan iya zama dashi?."

Omar ya ce, "ki koya, ki koyi sonsa zaki iya. Ina faWa miki gaskiya matsayina na Yayanki, in na ce miki Ina kallon ki matsayin wacce nazo gidan ku a matsayin mai sonki a yanzu arya nake miki, gwara na faWa miki gaskiya ki rie aurenki ki daina tunanina a cikin rayuwarki. Narma Allah bai rubuta ni da ke zamu zauna a inuwa Waya matsayin ma'aurata ba, ki karSi Waddara hannu biyu Allah ne ya tsara ba ni ko ke ba. Iyayenki da kike gani kamar basu kyauta miki ba ba laifin su bane, babu ni a cikin rabon ki Narma, babu ni a cikin addararki saboda haka ki kwantar da hankalinki yi fuskanci rayuwa."

Narma hawaye take yi, ta san gaskiya yake faWa mata amma zuciyar baza ta iya Waukar kalamansa ba, zuciyarta bugawa take yi sosai ta runtse ido tana jin kalamansa kamar saukar ruwan zafi a zuciyarta, ta wani Sangaren kamar saukar ruwan sanyi a zuciyarta.

"Wataila akwai Omar a ciki rayuwarki ta gaba, watala babu. Ni dake babu wanda ya isa ya amsa kiran rabon da ba na shi ba. Dan haka ki nutsu, ki rie aurenki ki daina tunawa da kin san mai suna Omar a rayuwarki. Ina yi miki fatan alkhairi da fatan samun rayuwa mai albarka" ya sake faWa cikin taushin murya wacce take ratsa zuciyar Narma.

Kai take girgizawa tana hawaye ta ce, "A'a Faruk, kar kace haka don Allah, bazan iya rayuwa babu kai ba, Ina sonka, ina son rayuwa dakai. Na san kaina kana jin abinda nake ji, ka amince min kawai nazo na rayu dakai ta ko wanne hali."
"Matar aure ce ke, Zancen na amince dake bai tashi ba. Kuma ni babu abinda nake ji a kanki kema ki daina ji a kaina, Ki manta dani ki kalli rayuwar aurenki zai fi miki kwanciyar hankali. Indai da gaske zan saka ki abu ki yi kamar yadda kika ce to ki rie aurenki, ki kuma manta dani!."

Jin tana kuka mai sauti ya saka Omar ya ce, "Ina yi miki fatan alkhairi, sai anjima" yana faWa ya yanke wayar ta kifa kai akan wayar tana kuka sosai. Sai da ta gaji da kanta sannan ta dakata, kanta ya rie sosai saboda kuka ta koma sauke ajiyar zuciya. Bata san haka soyayya take ba, bata san haka ake ji a soyayya ba, bata san haka azaba da raWaWin soyayya yake ba da bata yi gangancin fara son Omar ba. Numfashi take saukewa a hankali a hankali cikin rashin sanin abinda zata yi.

KRB2P016
Arewabooks@nanahaleema11.

Tana ji ana buga ofar bata buWe ba sai daga baya ta tashi ta buWe, Najwa ta gani ta kalleta ta ce, "Ya ki shirya before magrib zaku wuce." Rungume Najwa tayi tana cewa, "Bana so Najwa! Bana son Ashraf, Ni Faruk nake so!. Ya zanyi? Ya ake so nayi da raina?." Najwa hawaye ya cika mata ido amma bata yi ba ta ce, "ki yi hauri." Ajiyar zuciya take yi a hankali kukan ma ya daina zuwa idanunta sai kanta da ya yi nauyi sosai.

Idanu a kulle ta ce, "Nayi magana da Faruk, ya ce wai na rie aurena na manta dashi. Hmmm ki ji fa Najwa, taya zan iya mantawa dashi? Shi ne wanda naso kuma nake so har yanzu. Ya kasa gane irin yadda nake ji a kansa." Najwa ta ce, "Gaskiya ya faWa miki Ya Narma, mantawa dashi Win shine yafi alkhairi a gare ki da kuma shi kansa. Yanzu kina da aure ya zama dole ki manta dashi, addu'a zaki dinga yi a hankali komai zai wuce." Bata ce komai ba ta bar jikin Najwa ta koma ta zauna a gefen ta dafe kanta.

Najwa da kanta ta jawo trolly bag ya fara haWa mata kaya a ciki. Komai da ta san zata yi amfani dashi ta zuba tayi zipping bag Winta ta ajjiye ta fita. Bayan sallar la'asar Najwa ta sake dawowa ta tarar ta idar da sallah kalle ta ta ce, "Ya Narma ki tashi ki shirya." Kallon Najwa tayi kamar zata yi magana sai bata ce komai ba, kalaman Omar ne suke yi mata yawo a zuciyarta. Mum da Dad suka shigo Wakin a tare, Dad ya kalle Narma a tausashe ya ce, "Daughter ki tashi ki shirya zaku wuce America." Kallon Dad tayi da idanu ta da suke a kumbure

Please Login or Register in order to submit comment