Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin son abu ya shiga zuciyarsa farar Waya ba sai son yarinyar, ji yake sonta na shiga zuciyarsa sosai kamar shine mahaifinta. Ya yi murmushi yana kallon ta ya kalli Didi ya ce, "Kamar ku Waya." Didi ta yi murmushi tana kallon sa shima yana murmushi yana kallon yarinyar.

"Didi Wauke ta, hannuna yana rawa kar na ´ar da ita, ban taSa Waukar jariri ba sai ita." Didi ta Wauke ta ta ajjiye a gefe ya bita da ido yana murmushi. Karaf suka haWa ido Saroot ™anwar Mamansa, tunda ya shigo ya san sune a Wakin shiyasa ko kallon inda suke ma bai yi ba, amma sai da ta saka suka haWa ido.

Mama Zainab ce ta ce, "Omar barka da safiya, ashe kuma anyi ´ar kuma? Allah ya raya ta." Tsam ya tsuke fuska duk murmushin da yake yi ya gushe lokaci Waya. Didi ta kalle shi ta ce, "Omar ana yi maka magana." Bai saurare ta ba ya Wauke kai, baya son yayi abinda zai Sata masa farin cikin da zuciyarsa take ciki da ya basu mamaki wallahi. Kuma da laifin Didin, dan ta raina masa hankali ace har sun riga shi zuwa inda ta haihu? Za su gamu ne da ita bara ta warware. Girgiza kai ya yi tare da cize baki bai ce komai ba Didi dai tana lura dashi.

AbdulHamid ne ya shigo ya ce, "Sun bada sallama, zamu iya tafiya gida." Omar ne ya mi™e ya fita aka fara haWa kaya suka fito gabaWaya. Sai da suka shiga mota har iyayen nasa sannan suka tafi a motar AbdulHamid.

Omar shida Goje suka tafi dan gida zai wuce, a hanya ya ga wani baby shop sai yayi tunanin bai siyawa Didi da babyn komai ba ya zo ransa, nan take ya saka Goje ya tsayar motar suka shiga ciki. Duk abinda ya gani ya burge shi sai ya Wauka, a haka suka yi siyayya mai yawa suka biya kuWin aka saka a bayan mota suka wuce gida.KRB3P038
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla bata san Didi ta haihu ba, da safen bayan sun kammala breakfast suka wuce gidan Daddy kamar yadda ya ce su zo. Lokacin da suka je su Abba da Baba har sun zo aka zauna a falo ana tattaunawa akan batun Omar kafin a kira Nayla. Nayla gabanta faWuwa yake yi, ta shiga falon da sallama aka amsa ta nemi waje ta zauna.

Daddy ya ce, "Hauwa kamar yadda na faWa a kwanakin baya, zamu bashi lokaci in ya zo da kansa zamu karSe shi mu tattauna, in bai zo ba zamu kai maganar kotu a raba auren. Jiya ya zo ya same mu, kuma mun gamsu da dukkan bayanansa. Kamar yadda na ce jiya yau zauna dake domin ki faWa mana abinda yake zuciyarki akan mijinki. Ya zo jiya har kun gaisa dashi, abinda nake so dake ki faWi abinda yake ranki babu wanda zai yi miki dole a cikin mu, kina da ra'ayin cigaba da zama dashi ko kuma a kashe auren kamar yadda ki ka ce da farko?."

Nayla ta yi shiru bata ce komai ba sai sunkuyar da kai da tayi, Abba ya ce, "kar ki cuci kan ki, ki faWi asalin abinda yake zuciyarki. Zaki iya cigaba da zama dashi matsayin mijin ko a'a?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "Abba a bani lokaci na yi tunani."

Abba ya ce, "Lokacin me za a baki? Ba fa neman aurenki yake yi ba matarsa ce ke, kawai sai mu cigaba da ajjiyeki a gida da auren sa a kanki?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba Daddy ya ce, "meyasa ki ke so a baki lokaci?." Nayla ta ce, "ina so na yi tunani ne."

Abba ya ja tsaki ya ce, "ke ba wasan yara mu ka zauna yi a nan ba, mijin naki dan zaki koma masa sai kin yi tunani?. Kin ga malama ki tsayar da magana in zaki koma ki ce eh, in baza ki koma ba ki ce a'a, bana son shirme da Sata lokaci." Mama Sa'adatu ta ce, "To Yaya Ali a bata damar tunanin mana, dan dai kwana biyu ai ba wani abun ba ne ba." Ya Harare ta ya ce, "Daman ai duk shirinki ne, har kin yanke ma kwana biyu ko?." Daddy ya ce, "A bata lokacin Ali. Mun amince an baki kwana biyun ki je ki yi tunanin ki dawo ki faWa mana."

Abba ya ce, "Kai ka biye musu, tunanin me zata yi  banda Satawa kai lokaci?." Daddy ya yi murmushi ya ce, "yi ha™uri ka ™yale su, tashi ki je Nayla." Ta mi™e ta tafi a sanyaye. Abba ya bita da harara ya ce, "munafuka, tana son mijinta amma da yake ta samu goyan bayan uwar banza wai sai ta yi tunani, ko tunanin me zata yi ma oho."

Mama Sa'adatu ta ce, "A bar mu mu yi abinda mu ke so, wancan lokacin ba mu samu damar yin kwalliyar amare ba, wannan mun samu sai abarmu mu yi ai. Kuma Yaya gaskiya ya kamata ayi mata lefe fa, yana da rufin asirin da zai iya yi mata lefe."

Daddy ya ce, "Wannan ba dole ba ne ba ai, in yana da ra'ayi ya yi, in babu ni bazan ce ya yi ba saboda ba farilla ba ne. Kuma ko kayan dubu nawa zai siya mata kafin ya siya mata tana dashi, dan haka babu wani batun lefe. Gwajin jini kawai zai kawo min dan na tabbatar da lafiyarsa, itama kuma Nayla Khalid zai duba min nata dan tabbatar da lafiyarsu kafin ta koma gidansa." Hira dai suka cigaba da yi akan maganar kafin Abba da Baba su tafi.

       Nayla da ta shiga ciki babu ™awar hirarta Salma dan haka sai ta shiga Waki tana danna wayarta. Kiran Didi ne ya shigo wayarta, ta Wauka da sallama suka gaisa Didi ta ce, "amaryar mu."
Nayla tayi dariya ta ce, "Didi kina bani kunya." Didi ta yi murmushi ta ce, "Kin ´a fa." Nayla ta wara ido ta ce, "da gaske? Wai kin haihu kenan?." Didi ta ce, "na haihu Nayla, na haifi mace jiya da daddare."

"Wayyo Allah na! Amma shine baki faWa min ba sai yanzu Didi?."
"Yi ha™uri, da yake cikin dare ne sosai sai yanzu da muka dawo gida na samu wayar har na kira ki." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Gani nan zuwa yanzu Didi, gani nan" ta faWa tana kashe wayar ta fito falo.

Mama ta kalla ta ce, "Mama Didi ta haihu, zan je gidanta." Mama da fara'a ta ce, "yaushe? Me aka samu?."
"Mace, jiya da daddare."
"Ma sha Allah, Allah ya raya ta."
"Amin Mama. Ni zan tafi gidan."
"Waye zai kai ki?."
"Da kaina zan je."
"A'a bara a kai ki, ki ce mata ina yi mata barka kafin nazo." Mummy ma sa™on da ta bayar kenan, Nayla a guje ta fita driver ya Wauke ta zuwa gidan.

Nayla a can ta tarar da su Mama Saroot sun ji daWin ganinta, suna zaune sai ga matan su Kawu da cousins Winsu mata ana ta yi mata barka da haihuwa. Didi ta ji daWin haWuwar iyalansu, tana ji ina ma Omar yana nan shima ya shiga cikin ´an uwa, amma ta san koda yana nan bazai zauna a wajan ba. Umma Saroot ce zata zauna da Didi a gidan kamar yadda ake yi. Babu wanda yake maganar Omar sai hira da suke yi, Nayla sai hoto take yiwa Babyn.

Har yamma Nayla tana gidan, zuwa lokacin dangin Babansu Didi sun tafi saura Umma Saroot kawai wacce zata zauna da Didin a gidan. Umma Saroot ta shiga Waki itama ya rage daga Didi sai Nayla a zaune sai babyn da take hannun Nayla. Didi bata yi mata maganar Omar ba itama bata yi mata ba, hira kawai suke yi kafin su ji ana buga gate.

Nayla ce ta tashi ta je ta buWe, ganin Bashir ne da Goje sai ta yi dariya suka gaisa suka shiga ciki. Kaya suke ta shigowa da su Didi ta bisu da kallo ta ce, "waWannan fa?." Bashir ya ce, "Tiger ne ya ce a kawo miki." Didi tace, "Nayla buWe min na gani don Allah." Nayla ta buWe kayan ta ja su ta mi™awa Didi tana fitowa dasu ta ga gabaWaya kayan jarirai na mata a ciki.

Didi ta ce, "waWannan kaya kamar za a buWe shago haka? Ku ku ka siyo?." Goje ya ce, "da kansa wallahi, tun a hanyar dawowa daga asibiti Wazu muka ga wani shago na siyar da kayan ya ce mu shiga. Duk abinda ya yi masa sai da ya Wauka." Didi ta ce, "Omar yana da matsala wallahi, wannan kayan Allah kaWai ya san nawa ya kashe" ta faWa tana jawo waya zata kira shi. Su dai sallama suka yi mata ta yi musu godiya tare da basu tukwici. ˜in karSa suka yi, sai da ta nuna Sacin rai sannan suka karSa suka tafi.

Umma Saroot da ta fito a lokacin ta kalle ta ta ce, "To Aisha meye matsalar dan ya yi miki wannan siyayyar?." Didi ta ce, "Umma kayan sun yi yawa sosai, kalli fa don Allah, kamar wacce take siyar da kaya? Bara na kira shi" ta faWa tana kiran wayarsa a karo na biyu.

Umma Saroot ta ce, "saka a speaker ina son jin dramar ku." murmushi Didi tayi ta saka a speaker, daga can Sangaren yana Wauka ya ce, "Didi." Didi ta ce, "Omar an kawo min kaya."
"Uhum na ´ata ne."
"Amma Omar kayan nan sun yi...." Katse ta ya yi ya ce, "sun yi kaWan ko? Daman ai ban gama ba."

Didi ta ce, "ni ban ce sun yi kaWan ba, ka san kana da abubuwa a gaban ka, ka manta maganar da muka yi jiya amma ka kwashe ka yi wannan siyayar da kuWin?."
Omar ya ce, "Haka na ce miki kuWin na kashe? Kuma in ma su Win na kwashe nayi laifi ne? Ke kan ki Wazu cewa ki ka yi Omar ga ´arka, kenan nayi laifi dan na siyawa ´ata abinda na fi ™arfinsa?." Didi ta ce, "ba laifi ba ne."

Omar ya ce, "in ma a wajanki laifi ne a wajena ba laifi ba ne. ³ata ce kamar yadda ki ka ce, a karo na farko a rayuwata na samu wanda zai ce min Uncle ko ta ce min Baba, na samu wacce zan faWawa duniya ´ata ce babu wanda zai yi musu akan hakan. A ganina ko abinda na mallaka na kwashe na yi mata siyayya da su ban faWi ba Didi." Didi hawaye ya sakko mata ta goge ido ta ce, "Omar!." Jin maganarta na rawa ya ce, "wai kuka ki ke yi? Didi kenan, wahala bata ishe ki ba. Baki fara kuka ba kuwa, tunda har ki ka haifi ´ata wallahi yanzu ki ka fara kuka Didi."

"Omar na gode, Allah ya ji™an iyayen mu ya bar zumuncin mu har abada."
"Amin Didi. Amma ni ba ke na yiwa ba balle ki yi min godiya, in kuma na kika sake yi min godiya kin nuna min ´ar tawa da kike faWa bai kai zuciya ba."
"Bazan sake ba."
"Ya fi miki dai. Amma da ki ka tashi addu'ar kin yi mantuwa, ki tuna bayan Allah ya ji™an iyayen mu, bayan zumunci akwai wacce ya kamata ki saka."

Didi ta yi murmushi ta ce, "wacce kenan?." Ya Wan yi ™aramin tsaki ya ce, "Sai an yi magana ki ce na san halin ka fiye da kowa a duniya, amma gashi kin kasa gane abinda nake nufi" ya faWa cikin kwaikwayon muryar Didi.

Didi ta yi murmushi ta ce, "Allah ya bar ka da matarka Nayla." Murmushi ta ji ya yi mai sautin gaske ya ce, "na yarda a duniya babu wanda ya zan Omar kamar ki. Amin Yayata, Na gode da addu'arki, ki kula min da ´ata zan zo na ganta."

Didi tayi murmushi tana kallon Nayla ta ce, "Allah ya kawo ka." Omar ya amsa yana yanke wayar. Umma Saroot ta ce, "Aisha Allah ya bar zumuncin ku da Omar har abada, Allah ya wanke masa zuciyarsa ya daina jin abinda yake ji akan dangin mu da na mahaifinsa. Omar mutum ne mai kirki da ™aunar zumunci, mu muka lalata komai amma in sha Allah komai zai wuce."

"Amin Umma, in sha Allah komai zai wuce." Ta girgiza kai tana goge hawaye ta ce, "ana kirana a waya" ta faWa tana shiga ciki. Didi ta kalli Nayla ta ga tana murmushi har lokacin Babyn tana hannunta ta ce, "Nayla duk da Omar akan katanga yake amma mijinki ne, ki taya ni yi masa godiya." Nayla murmushi kawai tayi amma bata tanka ba, zuciyarta kuwa farin ciki take ji kamar ta taka rawa. Sai bayan sallar magriba sannan driver ya dawo ya Wauke ta suka koma gida.

Tun daga ranar Nayla kullum sai ta zo gidan Didi, Didi bata taSa yi mata maganar Omar ba itama bata yi mata. Dangin su Nayla kuwa kamar dangin Didi haka suka dinga tururuwar zuwa yiwa Didi barka. Hajja da kanta sai da ta je da kayan barka masu matu™ar yawa, da su yajin jego, da kayan amfanin mai jego.

Mama Sa'adatu ma kaya ta kawo mata masu matu™ar yawa harda lace da atampa. Haka Mummyn su Salma kowa ya yi mata kyauta wacce ta saka Didi zubar da hawaye saboda farin ciki. Nayla kayan da ta kai mata sai da Didin ta dinga faWa tana cewa bazata karSa ba sun yi yawa da™yar dai ta amince ta karSa.39
    A ranar litinin Nayla ta Wauki hutu saboda Mama ta ce ta Wauka saboda shirin da suke yi. Gyaran jiki Mama ta ke ta yiwa Nayla, kasancewar ta fara cikin kwana biyu ta sake yin haske da kyau fatar ta ta sake yin laushi sosai.

Har lokacin babu maganar da ta sake haWata da Omar, duk ta damu tana ganin kamar daman baya so ta dawo. Shi kuwa ya bada lokacin ne kamar yadda iyayenta suka ce, sai dai ya kai result Win gwajin jinin kamar yadda Daddy ya ce masa. Kuma da ya je kai musu ya sake samun tarba mai kyau a wajan Daddy har sai ya yi mamaki sosai, sai dai Daddy ya ce masa ya ™ara ha™uri Nayla zata dawo in sha Allah.

Haka aka yi sunan ´ar Didi wacce ta ci sunan mahaifiyarsu ake yi mata la™abi da Marmerh. An yi shagalin suna sosai, Didi ta zama ´ar gata domin dangi na ko wanne Sangaren sun zo an yi shagali sunan Marmerh.

Marmerh kuwa kayan da ta samu daga haihuwar ta zuwa suna Didi bazata iya lissafa su ba, ta samu kaya da kuWi da atamfofi. Har lokacin Omar bai sake zuwa gidan ba, amma kullum sai ta tura masa hotunan Marmerh dan a yanzu hoton ta ne ma akan screenlock Win wayarsa. Yana matu™ar son yarinyar kamar shine ya haifeta haka yake ji, ya kan tsaya yana kallon hotonta kawai yana murmushi.

Washe garin sunan yana zaune yana duba wayarsa kawai hannunsa ya kai kan status Win Didi. Ya ga hotunan suna ne na jiya ta saka, ya dinga bi a hankali yana gani yana ya taSe baki saboda ganin danginsu wanda baya ™aunar gani. Har ya wuce ya dawo ya sake wara idanunsa yana kallon Nayla ta yi murmushi tana ri™e da Marmerh a hannun. Ajiyar zuciya ya yi ya zuba mata ido yana gani yana murmushi shima.

Screenshot hoton ya yi sannan ya fita daga WhatsApp Win ya kira Didi a waya. Tana Wauka ya ce, "Didi ki goge hoton da ki ka saka a status yanzu, ta ya zaki Wauki hoton matata ki saka a duniya tana gani? Ki goge yanzu sai mu yi magana." Yana faWa ya yanke wayar. Ba jimawa ya sake kira ta ce, "To Omar na goge."
"Na gani. Kar ki sake Wora hotonta a status. Ina Marmerh?."
"To ubana. Ga Mamerh tana bacci a kusa dani."
"Ki shafa kanta a madadina, zan zo na ganta."

Didi ta yi murmushi ta ce, "To sai ka zo, tunda dai kana ta cewa zaka zo baka zo ba." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba Didi ta ce, "ya dai?." Omar ya ce, "dama ta zo gidanki jiya?." Didi ta ce, "kaima ka san ta ya za a ce bazata zo sunan Marmerh ba?." Ya girgiza kai cike da jin haushi ya ce, "tana ta zuwa inda take so ba tare da izinina ba." Didi ta yi murmushi ta ce, "To ai ita kaga...." ˜aramin tsaki ya yi ya ce, "kar ki kira abinda zai Sata min rai don Allah."

Didi ta ce, "shikenan Omar, amma yanzu ya ake ciki da maganar?." Omar ya ce, "Ina gab da kasa jurewa Didi, na yi ha™urin, nayi juriyar amma abin yana neman yafi ™arfina." Didi ta ce, "ka kira ta a waya?." Ya girgiza kai kamar tana gabansa ya ce, "tunda aka ce na bata lokaci shine na bayar, bana son yin abinda za a ga rashin kyautawata shiyasa ni ko waya ban kira ta ba."
"Kana kewarta sosai ko?."
"Fiye da yadda zan faWa miki Didi, ban san me zan ce miki ki gane ba." Didi ta ce, "to ka je gidan ka same ta mana."

"Didi ban son na je ayi min wani abun raina ya Saci wani abun ya faru, a karo na farko ina gudun Sacin raina a wani waje."
"Ranka bazai Saci ba in sha Allah, ka je ka sameta."

"Didi gaskiya bazan je ba." Didi ta ce, "to ai shikenan, sai ka cigaba da jiran tsammani" ta faWa dan ta san bazai iya jurewa ba. Katse kiran ya yi ya nemo number Nayla da har lokacin bai yi saving ba, ajiyar zuciya ya yi kawai ya kira number.

     Nayla a lokacin tana zaune an gama turara mata jiki kenan ta ga ana kiranta, kamar baza ta Wauka ba sai kuma ta Waga ta ce, "Hello." Shiru ya yi bai amsa ba jin saukar muryarta har cikin ™wa™walwarsa. Tsaki ya ji tayi ta katse wayar ya kifa wayar a kirjinsa yana lumshe idanunsa.

Nayla tana katse wayar Mama ta shigo Wakin ta kalle ta ta ce, "Daddy yana ta faWa wai kin yi shiru, na ce masa kin amince kawai muna Wan gyare-gyare ne, yana ta faWa ya ce ki koma a wannan satin."

Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama ta ce, "Ko baki son komawa ne?." Nayla ta yi shiru Mama ta ce, "Nayla faWa min abinda yake ran ki, kin ce kin amince amma yanzu ina ganin kamar baki son komawa." Nayla ta ce, "Mama har yanzu ko waya bai sake yi min ba balle ya zo, Ina ganin kamar baya so na koma."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Yana so mana Nayla, dan bai yi miki waya ba ko bai dawo ba ba hakan yana nufin baya sonki ba. Tunda har yaje gaban iyayenki yana sonki wallahi, wata™ila bai neme ki ba saboda lokacin da aka ce za a baki." Nayla ta ce, "Mama ni sai nake ganin kamar baya so ne kawai." Mama ta shafa kanta ta ce, "Kar ki damu yana sonki, yana kuma so ki koma da ra'ayin kan ki ba dan tilastawa ba." Nayla ta goge idanun ta bata ce komai ba.

  Da yamma Salma da Jidda suka zo gidan suka dinga rarrashinta amma ta kasa fahimta ita gani take yi kawai ba sonta yake yi ba tunda bai neme ta ba. Salma ta ce, "kema kin cika rigima wallahi, kin san halin mijin nan naki meye zai dame ki? A ganina ai tunda har ya kalle ki ya ce bazai sake ki ba, sannan ya faWa a gaban su Daddy me zai dame ki kuma?." Nayla ta ce, "gani nake kamar...." Jidda ta katse ta ce, "Haba me ki ke so ya yi miki kuma? Ke ki ka ce sai an baki lokaci, an baki lokacin kuma kin damu."

Nayla ta yi shiru bata ce komai ba. Wayar ta ce ta yi ™ara ta duba ta ga number ce sai kawai ta Wauka ta saka a speaker ta ce, "Hello."
"Ina cikin gidan da ki ke, zan iya ganin ki?." Gabanta ya faWi ta kalli su Jidda da suke kallon ta ta ce, "waye ya ke magana?."
"Ki zo zaki gani" yana faWa ya yanke wayar Nayla ta bi wayar da kallo.

Sai kuma ta yi ihu ta faWa jikin Salma suka rungume ta Jidda ta ce, "Wai ke nufin ki Omar Win ne?." Nayla ta ce, "wallahi shine Twiny, ko a mafarki zan gane maganarsa." Jidda ta ce, "to ga abinda mu ke faWa miki ya tabbata." Murmushi ta yi tana goge idanuta.

Salma ta ce, "ya aka yi ya san kina gidan nan? Sananan kuma ya aka yi ya san gidan nan?." Nayla ta ce, "ban sani ba." Jidda ta ce. "yanzu dai a faWawa Mama zuwansa sai ki je ki sha kalaman soyayya ki dawo." Murmushi ta yi ta kalli Mihada da take gefe tana bacci ta shafi fuskarta.

Salma ce ta faWawa Mama batun zuwan Omar ta aika ta ta ce taje ta shigo dashi. Salma ta yi mamaki gani sa a mota a zaune a wajan gate Win gidan dan bai shigo ba. Salma ta ce, "Barka." Kallon ta ya yi sarai kuma ya gane ta, da™yar ya buWe baki ya bata amsa. Salma ta ce, "Mama ta ce ka shigo." Omar bai ce komai ba ya fita ya bi bayanta zuwa gidan. Salma sai gulmarsa take yi a zuciyarta har suka shiga cikin gidan.

Yadda suka gaisa da Mama abin ya burge shi sosai itama ta saki fuska sun gaisa sosai, aka kawo masa ruwa da lemo da bowl wanda aka zubo cincin a ciki da kayan motsa baki. Ba jimawa Nayla ta shigo da sallama ya amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan yana so ya yi mata warning akan fitar da take yi babu izininsa, in ya kalle ta tsaf zai kasa aikata abinda ya zo aikatawa.

"Ina yini" Nayla ta faWa a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Baki tambayi waye ba amma kin fito, in da ba ni Win bane ba fa?." Nayla ta Wago ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba sai wani basarwa take yi fuskarsa a Waure.

Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai ta ce, "Salma ta sanar dani." Omar babu walwala akan fuskarsa ya ce, "Meyasa ki ke fita ba tare da na sani ba?."

Sai a lokacin ya kalli fuskarta ya ga abinda yake matu™ar Waukar hankalinsa akan fuskarta, yadda take kifta idanu kamar mai jin yaji a cikin idom, ganin motsawar idonta yana sakawa ya tsayar da idonsa ™yam a kanta. Šago ido tayi ta kalle shi ta ga ita yake kallo, ya buWe Wan idanunsa akan fuskarta ya ce, "meyasa?."

Nayla ta sauke kai ™asa, ta daure ta jure dan tana son gwada yanayinsa ta ce, "har yanzu ai ban gama yanke hukunci zama da kai ba." Kai ya girgiza ya ce, "kafin ki yanke Win har yanzu matata sunan ki, kinsan abinda zaki yi ai." Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Omar ya zuba mata idanu dan gani ya yi ta ™ara yin kyau sosai, umarnin zuciyarsa kawai ya bi saboda ya kasa jurewa sai da yazo ya ganta, gashi ya zo sai wani shan ™hamshi take yi masa.

"Yaushe zaki dawo?." Ba zata taji maganar kuma a hankali ya furta sai ta kalle shi ya Waga mata gira alamun ina jinki. Nayla ta kawar da kai dan gabaWaya fuskarsa babu walwala kamar ba shine ya je gidan Daddy yana murmushi ba. Nayla ta ce, "bana tunanin zan dawo saboda ka riga da ka gama cire min son zama da kai a zuciyata, gabaWaya ka karya min zuciya."

Kallon ta ya yi yana mamakin kansa, wai shine zaune a gaban wata mace tana faWa masa kalaman da ba su yake da ra'ayin ji ba. Lallai soyayya ta canja shi, abinda ta rage a halayensa kaWan ne ya rage. Omar ya yi shiru bai ce mata komai ba, sai da aka Wan jima kaWan sannan ya ce, "baki ha™uri ba?." Ta Waga kai ta kalle shi ta ce, "ha™urin nake so na yi amma na kasa, tun daga ranar da ka je gidan

Please Login or Register in order to submit comment