Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

huta a gida, har ga Allah wannan auren nata ba wani kwanta min ya yi ba."

Daddy ya murmusa ya ce, "kar dai ki shiga tsakanisu ki zo ki ji kunya, babu ruwanki da nuna mata bakya son aurenta, babu ruwanki da nuna mata bakya son mijinta, ki tsaya a tsakiya kawai, in tayi ruwa rijiya in bata yi ba masai. A yanayin da take magana Sacin rai ne ya saka ta ce a raba auren, mu bata lokaci ta warware daga baya sai komai ya biyo baya."

Mama ta ce, "Allah dai ya kyauta kawai." Aka amsa da amin. Sai bayan sallar magriba sannan Nayla da Mama suka koma gida.

" " " " " " "

Abiy yana zaune yana amsa waya, Mama na gefensa sai Jawad kamar ko yaushe yana cewa, "To Alhaji Junaid duk abinda ku ka yanke ai daidai ne, dani da ku duk Waya ne a wajan Nayla, dukkan mu iyayenta ne, abinda ku ka ga daidai ne ku aiwatar kawai babu Sata lokaci ko jiran umarnina."

Murmushi ya sake yi ya ce, "Na baka wu™a da nama a wannan lokacin ma, duk abinda ka yanke ka ke ji a zuciyarka daidai ne ka yi kawai." Abiy ya sake cewa, "babu komai ai duk Waya ne. Allah ya zaSa abinda ya fi alkhairi." Daga haka suka yi sallama Abiy ya yanke wayar.

Mama ya kalla da take kallonsa ya ce, "´arki Nayla ce ta bar gidan mijinta ta koma gidan ™anwar mahaifiyarta." Mama ta ce, "Akan me?."
"Wai ta bar auren, ita ta gaji." Mama ta ce, "Subahanallahi! Allah ya sa ba wani abun ya yi mata ba. Kai wannan yaro an yi shaiWani wallahi."

Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba. Jawad ya ce, "Abiy akan me take so a raba auren to?." Abiy ya ce, "ta ce kawai ita bata son zaman auren a raba shi."
"To ina mijin na ta?."
"Ni ban sani ba Jawad, na basu wu™a da nama duk abinda suka yanke daidai ne. In sun raba auren daidai ne, in ba su raba auren ba ma duk Waya a wajena."

Mama ta ce, "Wannan aure babu abinda zai raba shi, in sha Allah Nayla sai ta cigaba da rayuwa a cikin sa!" Mama ta faWa tana kallon Abiy.

Abiy da Jawad duk kallonta suka yi cikin mamakin kalamanta, ganin suna kallon ta da alamun mamaki akan fuskarsu sai ta ce, "Yarinya ™arama da ita ace ta zama bazawara? Ina amfanin wannan auren tun farko amma ta dage sai da aka yi?. Bana so a raba auren nan saboda an lalata mata ™uruciyarta, tana yarinya da ita a ce ta zama bazawara abin sam bai yi ba. Duk wacce take amsa matsayin uwa a wajanta bazata so auren nan ya mutu ba."

Jawad ya ce, "ni kam Mama ban ga aibun hakan ba, in hakan shine mafi alkhairi Allah ya tabbatar, abinda ya kamata ki ce kenan." Ta harari Jawad ta ce, "Baka da hankali ai, baka san meye zawarci ba. Dan rashin hankali auren da bai wuce wata shida ba ace ya lalace?."

Abiy kallon ta yake yi kamar mai karantar wani abu, ta kalle shi suka haWa ido ya dau™e kai ba tare da ya ce mata komai ba. Shima Jawad Win shiru ya yi yana mamaki, ko meyasa Mama bata son auren Nayla ya mutu oho, tun farkon aure ita kaWai ce mai goyan bayan auren har yanzu. Ya rasa meyasa take haka, yau kaga tana goyan bayan auren, gobe ka ji tana kushewa.

Mama tashi tayi ta bar wajan zuwa Wakinta. Hannu na rawa ta kira waya ana Wauka ta ce, "Ke komai yana shirin lalacewa, Aziza wai Nayla ta bar gidanta ta koma gidan ™anwar mahaifiyarta, kuma na san halin dangin babar nan nata, sonta suke yi kamar su Wiga mata rai, tsaf zasu iya kashe auren nan ban cimma burina ba. In auren nan ya mutu yanzu ribar me na samu? Bayan kyau da Naylan ta ™ara yi a gidan? Tunda aka fara irin wannan yajin so nake a cigaba daga nan har a tashi duniya."

Aziza ta ce, "kwantar da hankalin ki Yayata kuma ™awata, Yanzu Ina ita Nayla Win?."
"Tana Kano na faWa miki."
"Shikenan ki kira ta, ki karya mata zuciya da kalaman da zata sake lulawa cikin duniyar qaunarsa. Ki kashe mata zuciya, ki tayar mata da tsumin soyayyarsa. ˜awata ki yi mata laga-laga da zuciyata, ki dasa mata raunin da zata ji tana so ta koma masa. Daga nan in ta koma ya kamata mu yi wani abun da zamu jefawa yaron tsanarta a zuciyarsa, yadda ubanta ya ce kar ta zo masa gida shi Omar Win ya dinga cin ubanta kinga bata da wajan zuwa."

Mama ta ce, "Aziza na san Sa'adatu farin sani, babu lallai ta bar kalamaina su yi tasiri a zuciyar Nayla."

"Haba Zeenatu kamar ba ke ba? Ki gwada sai ki zo ki bani labari. Ai tunda har aka Waura auren nan wallahi baza mu bari a raba shi ba, in aka raba ma kenan itace da riba ba mu ba. Duk wahalar da Bilkisu ta ba ki shikenan ta tafi a banza? Matar nan har shara da wanke-wanke ta saka ki da cikin Ahmad wata tara. Ba tausayi balle imani kuma mu sai mu bar ´arta ta yi walwala a gidan miji?. Ni fa na so mai mata ta aura, da ace yana da mata zuwa zamu yi mu haWa kai da uwar gidan, in ta kama mu biya uwar gidan ta dinga cin uwar Nayla yadda zata girbi abinda uwatta ta shuka."

Mama ta sauke numfashi ta ce, "Aziza ina son Nayla, amma bana son Nayla tayi walwala a gidan aurenta. Yadda na assasa auren nan har aka yi bazan ™yale ya lalace a banza ba, zan iya yin komai dan ta koma masa."

"Ki samu ta koma Win, in ta koma zamu canja taku ne, domin kuwa akwai wani malamin su ™awata ban taSa zuwa wajansa ba amma akan wannna maganar zamu je. Za a yi aiki akan mijin nata, a sake jefa masa dabi'ar shaye-shaye da wannan faWan daban yadda zai ci uba ta da hujja."

Mama ta yi dariya ta ce, "Aziza ke muguwa ce wallahi." Aziza ta ce, "Baza ki gane ba Zeenatu, uwarta ta wahalar da ke sosai, har ni da nake ´ar zaman Waki ba ™yale ni tayi ba. Shegiya mai ruwan aljanu, ana cikin kabari ana girbar abinda aka shuka, an bar mu a duniya muna walwala da jin daWi, ga kuma ´arta a duniya zata girbar mata abinda ta shuka kafin ta she™a barzahu."

Mama ta ce, "in na tuna lokacin da nake nakuWar Ahmad tana kallona ina juyi jini yana gudu yana bin ™asa amma baiwar Allah nan ta Wauke kai ta kuma ™i sanar Abiy abinda yake faruwa. Ba dan Allah ya kawo ku a lokacin nan ba da yanzu Ahmad bashi da rai. Ke ba a banza Alalh ya Wauki ran Bilkisu ba, barinsu a duniya ma mugun iri ne wallahi. Sai bayan ta gama aikata sharrinta wai yafe mata, an™i a yafe Win."

Aziza ta ce, "kuma a haka zamu bar ´arta tayi zaman aure lafiya?. Ai Allah yana so ki Wauki fansa ne shiyasa ya Wauki ranta ya bar ´arta a hannunki, duk abinda ta aikata miki sai gashi ta mutu ta bar ´a Waya tilo da ta mallaka a hannunki. Sai abinda ki ka ga dama zaki yi mata, kin ma yi ™o™ari da kika iya rainon Nayla wallahi."

"Ina son Nayla na faWa miki, ina jinta kamar Jidda. Biyayyar da Nayla take yi min Jidda bata yi min ita wallahi, kuma na ri™eta tsakani da Allah da zuciya Waya, kawai burina ta girma a zo wannan gaSar, bana so ta ji daWin aure ko kusa Aziza."

"Zaman aure mai daWi ai sai Jidda da Jalila, su ne zasu yi rayuwar aure mai kyau da farin ciki amma ba Nayla ba. Yanzu ki kira ta ki yi mata laga-laga daga nan sai ki bani labari." Sallama suka yi Mama ta kashe wayar ta kira number Nayla kai tsaye.KRB3P030
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla tana zaune ita da Mama Sa'adatu da Salma da Yaya Zahra kiran Mama ya shigo wayarta. Kallon wayar tayi kamar bazata Wauka ba sai ta Wauka, da yake wayar na nesa da ita sai ta saka a speaker ta ce, "Mama Ina yini." Mama ta ce, "Nayla kina lafiya? Ya na ji muryarki haka?." Nayla ta ce, "kaina ne yake ciwo Mama, Ina Jalila? Yaushe Twiny zata dawo?."

Maa ta ce, "Nayla ba wannan ba. Yanzu Abiy yake faWa min abinda ya faru, da gaske kin bar gidanki Nayla?." Nayla ta ce, "eh mama."
"To akan me Nayla? Me ya faru, meyasa baki faWa min ba?. Ba na ce duk abinda ya faru ki dinga sanar dani ba?."
"Mama ni kawai na bar auren ne."
"Akan me zaki bar auren bayan kina son mijinki?  Ko dai zuga ki ake yi akan ki kashe aurenki?."

Nayla ta ce, "A'a Mama, da kaina na gaji kawai." Mama ta ce, "to ki faWa min abinda yake yi miki mana har kika gaji Win, dukanki yake yi?." A gajiye Nayla ta ce, "ni bai taSa dukana ba" ta faWa kamar zata yi kuka.

Mama ta ce, "kin ji ko, ni na san kina son mijinki gashi nan muryarki har ta fara yin rawa. Nayla kar ki sake auren nan ya mutu, in ki ka bari hakan ya faru kin rasa masoyinki wanda ki ke so na har abada. Omar shine wanda ki ke so, shine wanda ki ke qaunar zama dashi a matsayin mijinki, na Wauka zaki jure duk ™abalalen da zaki fuskanta a gidansa ki rike aurenki amma tun ba a je ko ina ba kin fara barin gida?. Haba Nayla, meyasa baki yi min waya kafin ki bar gidan ba?."

Hawaye ya sakowa Nayla ta ce, "Mama ni kawai...." Mama ta katse ta ce, "na faWa miki ha™iri zaki yi ki jure ko me yake miki, Nayla ko da dukanki yake yi jurewa zaki yi saboda kina sonsa. In auren nan ya mutu ai sai Abiy ya yi mana dariya, tun farko kin san baya so ya yi ha™uri ne dan ke, in kuma Omar ya sake ki zai ce daman ai ya faWa miki kika ™i ji. In ki ka yi ha™uri a hankali komai zai wuce, da zarar kin fara jin daWin auren shikenan zaki yi rayuwarki cikin farin ciki. Amma barin gida ki tafi yaji wannan ba Wabi'a mai kyau bace, tunda nake da Ummanki bata taSa yaji ba nima kuma haka, a ina ki ka gado wannan hali Nayla?."

Nayla tayi shiru bata ce komai ba dan bata san me zata ce ba. Mama ta ce, "abinda nake so da ke ki koma gidan mijinki kawai, in akwai abinda ki ke so ki faWa min sai na aiko miki dashi." Nayla ta ce, "babu abinda nake so." Nayla taji Mama Sa'adatu taSata, ta kalleta taga tana yi mata alamar da ta yanke wayar, sai ta ce, "Mama kaina ciwo yake yi zan kwanta."
"To ki kwanta, gobe zan kira ki da safe ki tabbatar da kin koma kin ji?."
"To Mama" ta faWa tana yanke wayar ta ajjiye a gefe.

Yaya Zahra ta ce, "kan bala'i! Me matar nan take nufi ne wai?." Salma ta ce, "Nayla ki yi ha™uri, Mama babarki ce, amma wallahi Yaya Zahra tun lokacin auren nan na lura kamar da saka hannun Maman su Jidda akan abinda ya faru, to bazan ce komai ba tunda uwa take a wajan Nayla, ga kuma yadda mu ke da Jidda. Amma wallahi tana da hannu a lamarin nan."

Calmly Nayla ta ce, "Kai Salma, kawai tana bani goyan baya ne tun a lokacin amma ba dan wani abun ba." Mama ta kalli Nayla ta ce, "Daman duk abinda ya faru tambayarki take yi?." Nayla ta ce, "eh amma ba ko yaushe ba, tana tambayar lafiyar da nake ciki ne kawai, ni kuma in da damuwa sai na faWa mata." Mama ta ce, "ba laifi bane dan kin faWa mata damuwarki ba Nayla, Zeenatu uwa take a waja ki tunda ita ta raineki. Amma meyasa take so ki zauna a gidan Omar? Meyasa bata tambayi ra'ayinki ba?."

Nayla ta ce, "Tun farko Mama ta san abinda yake zuciayata, ta taSa ji muna hirar nida Salma da Jidda. Itace  take bani ™warin guiwa akan zan iya aurensa. Hatta lokacin da Abiy ya tambaye ni Mama ce ta saka na ce amsa masa da gaske ne Ina sonsa, sannan itace ta turo ni Kano a lokacin da Abiy ya yi fushi. Kawai tana supporting abinda nake so ne ba wani abun ba, ta na kuma guje min faWan Abiy shiyasa take yin abinda take yi ba dan ta cutar da ni ba. Mama tana sona sosai, tana yi min abinda ko Jidda bata yiwa."

Mama ta ce, "daman mun san tana sonki Nayla, waye zai ce babarki bata sonki?. A yanayin yadda take baki goyan baya akan Omar na tabbatar da son da take miki. Amma ki bani labarin abinda ya faru, na taSa tambayarki amma lokacin a ruWe ki ke baki bani amsa yadda nake so ba, yanzu ki faWa min."

Nayla ta ce, "shine ai na faWa miki Mama, ta bani goyan baya sosai har turo ni Kano duk Mama ce tace nazo. Ban san meyasa zuwa na Kano ya Satawa Abiy rai ba, amma har message ta ce na tura masa na ban ha™uri."

Mama ta girgiza kai ta ce, "kuma kin tura Win?."
"Ma tura masa, daman ha™uri na bashi ha™urin tun a gida, na kuma ce na ha™ura zan zaSi guda Waya a cikin masu neman auren nawa. To ban san me ya yiwa Abiy zafi a kalamai na ba, dan ni dai na san iya message Win na da nayi masa shine abu na ™arshe da ya haWa ni da Abiy."

Mama ta ce, "Allah sarki Zeenatu, ai mutuniyar kirki ce tana sonki sosai. Amma kin gane Nayla, ko dan gaba ba a faWar matsalar gidan miji Nayla, koda Ummanki tana raye in ta tambayeki matsalar gidanki ba a faWar damuwa ko Sacin rai, farin ciki ake faWa a Soye damuwa. In kin ga an faWi damuwa to tayi miki girman da baza ki iya warwareta da kanki ba, to a sannan sai iyaye su shigo ciki. Ki kiyaye daga yau kin ji?."
"To ni da za a raba auren Mama?" ta faWa ido na cikowa da hawaye."

Mama ta ce, "ai zaki sake wani auren ko?." Nayla bata ce komai ba Mama ta ce, "kar ki damu, ki yi abinda zuciyarki take so ki zaSi wanda yake sonki ba kike so ba. Nayla da ki zauna da namijin da baya ™aunarki gwara ki zauna da namijin da ke ce bakya ™aunarsa. Zai kyautata miki, zai baki farin ciki saboda yana hangen gaba zaki so shi. In kuwa kece ki ke so baya sonki ko wacce bola ya kwaso ke ce, babu daraja balle mutuntawa da farin ciki, duk abinda zaki yi baza ki burge shi ba dan ba sonki yake yi ba. Amma ki yi tunani ki kuma cigaba da addu'a, in akwai sauran zama tsakaninku Allah zai daidaita, in babu Allah ya haWa kowa da rabonsa. Kar ki tursasa zuciyarki yin abinda bakya son dan farantawa wani rai ba, rayuwarki ce, ke zaki zauna a ciki ba wani ba."

Nayla ta Waga kai cike da gamsuwa da maganar Mama ta ce, "to Mama." Mama ta ce, "Yauwa, Salma zauna da ita, Zahra zo mu je na baki sa™on ki wuce dare ya yi" ta faWa tana tashi ta fita daga Wakin ita da Yaya Zahra.

Nayla ta kifa kai a kafaWar Salma, Salma ta ce, "ki yi ha™uri, ki ta addu'a kamar yadda Mama ta ce." Nayla ta ce, "Salma na rasa meyasa nake sonsa har yanzu, zuciyata ta kasa karSar laifin da ya yi min."

Salma ta ce, "kar ki yi kuka, na tabbatar da zai fahimci kuskurensa zai kuma zo kamar yadda su Daddy suka ce. Amma sai kin yi ha™uri, hakan da ki ka yi shine daidai, ta haka zamu tabbatar da mahimmacin da ki ke dashi a wajansa. A haka zamu gane shin ya Wauke ki matsayin matarsa ko bai Wauka ba, ki yi ha™uri ki ta addu'a."

"Salma in kuma bai zo ba fa?."
"Zai ma zo."
"Hmmm baki san wannan ba, bana ji a jikina zai zo Salma, inda ace yana sona zai iya yin komai a kaina, dan yana girmama abinda yake so na gani akan Didi. Amma tunda har ya furta na tabbatar da bazai zo ba Salma, Didin ma da yake ™aunarta ba ™yaleta ya yi ba balle kuma ni." Salma ta ce, "Kar ki damu zai zo in sha Allah."

Nayla ta sauke numfashi ta ce, "In bai zo ba ma shikenan ai, ni dai bazan koma ba." Salma ta ce, "ki kwantar da hankalinki don Allah, gabaWaya hankalin Hajja ya tashi da ta ji ance kina gida, in kina tayar da hankali haka ya ki ke so mu kasance? Kowa ya damu dake kina gani." Nayla ta ce, "shiyasa nake alfaharin kasancewata a familyn nan, kowa yana matu™ar ji da ni. Har Ya Abbas da nake ganin kamar ala™ar mu ta ™are bai canja min, duk ya damu da damuwata, dana motsa zai ce sannu Nayla, kina son wani abu."

Salma ta ce, "to kin gani, ki yi ha™uri damuwarki ce ba ma. Kuma Ya Abbas ai Yayanki ne, dan yace yana sonki baki aure shi ba kawai sai ya canja miki? A zamanin jahiliya ake wannan ai. Kira Twiny mu yi hira."

Nayla ta ce, "™yaleta kawai, Didi ma nake so na kira naga kiranta tun jiya,  amma sai gobe zan kirata." Salam ta yi murmushi ta ce, "to na baki labari?." Nayla ta kalle ta ta ce, "Ina jinki." Ta yi dariya ta ce, "yarinya in baki wasa ba nan gaba kaWan zaki fara kirana da Anty." Kallon da ta ga Nayla tana yi mata alamun ™arin bayani ya saka tayi dariya ta ce, "Yaya J, tun saudia da azumi yake ta shige min, ashe ashe" ta faWa tana ™yal™yalwa da dariya.

Nayla ta wara ido cikin tsantsar farin ciki ta ce, "Are you serious? Salma da gaske ki ke? Yaya J Wina na Kaduna shine yake sonki?." Salma ta harare ta ta ce, "To Waga min murya su Mama su ji, Ina faWa miki a sirrinace zaki yi min handsfree?." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Salma na ji daWi, na kasa Soye farin cikina. Wayyo Allah, wallahi kun dace da Yaya J, Yaya j ™arshe ne wajan kirki Salma, please ki yi accepting Winsa."

Salma tayi murmushi ta ce, "Iya excetiment Win fuskarki ya bayyana min abinda yake zuciyarki. Zan yi tunani akan Yayan na ki na gani, Amma fa ke kaWai ki ka sani, kar ki faWawa Waya munafukar ™anwar tasa."

Nayla tayi dariya sosai mai nuni da farin cikin da take ciki ta ce, "Ai wallahi sai ta ji labari." Salma daman burinta ta saka ta farin ciki sai ta ce, "Babbar matsalar ma in na amince masa duk ™annensa sun raina ni, bazan ba ku umarni ku bi ba, taya zan amince bayan jira ku ke duk abinda ya faru bayan auren na faWa mu ku?" Ta faWa tana kashe mata ido Waya. Dariya suka yi a tare suka tafa Nayla ta ce, "™annen ango, aminan amarya." Salma ta mi™e ta ce, "Ke na gudu, gobe zan dawo in sha Allah."

Nayla ta ce, "To amaryar Yaya J." Ta harareta ta ce, "Don Allah kar ki faWa masa fa." Nayla ta ce, "bazan faWa masa ba, amma zan faWawa twiny."
"Munafukai" ta faWa tana fita daga Wakin tana jiyo dariyar Nayla daman kuma abinda take so tayi Win kenan.
KRB3P31
Arewabooks@nanahaleemq11.
     Mama da Yaya Zahra tunda suka fita suke tattaunawa akan batun Maman su Nayla. Yaya ta ce, "Mama anya ba itace ta saka mahaifin Nayla ya yi fushi har ya aura mata yaron nan ba?."

Mama ta ce, "baza ku yi zarginta ba Zahra, Zeena ta so Nayla, ta kuma raineta bisa amana da kuma zuciya Waya. Ta yi mata tarbiyya irin wacce ta yiwa ´arta, ta ™aunace ta kamar yadda ta ™aunaci na ta, in ta so cutar da Nayla zata cutar da ita tun kafin ta kai girman haka. Bana shakku ko zarginta akan wani abun na cutarwa akan Nayla, abinda ya saka na dasa mata ayar tambaya akanta; meyasa take nuna mata zaman ta Omar shine mafita kawai?."

Yaya ta ce, "Haka ne Mama, amma abinda ki ka ce Win shine nima ya tsaya min a rai kenan." Mama ta ce, "share batun kawai, bara mu jira mu ga abinda zai faru."
"Ni so nake ma auren ya mutu wallahi, Nayla sam ba ajinsa ba ce, ki duba wani gida da aka ajjiye ta kamar gidan kaji."
"Kar dai ki faWa ta ji, wallahi tana son yaron nan har yanzu, kawai ya yi mata abinda ya karya mata zuciya ne shiyasa ta zaSi haka. Dan haka ki iya bakinki, in ta koma masa zata dinga tunawa da abinda ki ka faWa a kansa."

Yya Zahra ta ce, "ikom Allah, ko meye abin so oho?. Ina jin kyaunsa ne ya Wauki hankalinta." Mama ta ce, "Barr Nass ´ar gidan Senator haka ta haukace a kansa, farin jini gare shi kawai." Ta yi dariya ta ce, "farin jini a wajan Wan daban? kuma farin jinin ma na yara kyawawa masu asali irin su Nayla?. Kuma sunayen su daga N ya fara."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Wannan hasahen naki ne, ki wuce ki tafi dare ya yi" ta faWa tana fita itama Yaya Zahra ta haWa kan yaranta suka wuce gida.

Washe gari bayan Nayla ta kammala breakfast sai ga Salma, hakan ya yi mata daWi dan tun jiya take farin ciki saboda labarin da ta bata, ganinta ya saka suka shige Waki suna hira. Wayar Nayla ce tayi ™ara ganin sunan Didi ya saka tayi murmushi ta Wauka ta ce, "Tuba nake Didi, na so na kiraki jiya dare ne ya yi aallahi."

Didi daga can Sangaren ta ce, "Nayla kin Waga min hankali, na kira baki Wauka ba kuma baki kira ni ba. Lafiya dai ki ke ko?."
"Lafiya lau Didi. Ina kwana."
"Wallahi ba lafiya nake ba, amma yanzu da na ji maganarki lafiya lau."

Murmushi Nayla ta yi ta ce, "Tuba nake." Didi ta ce, "Kina gida ne? Ina birkitaccen mijin na ki?." Nayla ta murmusa kaWan ta ce, "Didi bana gida, Ina gidan Mama tun shekaran jiya." Didi ta ce,"Mama Sa'adatu?." Nayla ta ce,"Ita."

"Amma dai lafiya ko?." Yadda tashin hankali ya bayyana a muryar Didi ya saka Nayla yin murmushi ta tausasa murya ta ce, "Lafiya lau Didi." Didi ta ce, "Lafiya lau zaki tafi gidan Mama har ki kwana biyu? Me Omar ya yi miki da ki ka koma?. Kar ko Soye min komai Nayla, in kuma na zo gidan to." Nayla ta ce, "ki yi zamanki Didi, kina fama da kan ki bai kamata kina zirga-zirga ba."

"To faWa min gaskiya Nayla, kin saka gabana sai faWuwa yake yi." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Babu abinda ya yi min Didi, hasali ma ni ko magana bata haWa mu dashi ba." Tana ji Didi ta sauke ajiyar zuciya, kafin ta yi magana Nayla ta ce, "Kawai zaman auren na mu ne ya zo ™arshe, na faWa masa ya karSi numberta a wajanki ya turo min sa™on saki ba lallai sai ya rubuta ba."

Didi ta sauke numfashi ta ce, "Kin yi daidai Nayla, kin yi abinda ko wacece a matsayinki abinda ya kamata tayi kenan. Ki yi ha™uri Nayla! Ki yi ha™uri!" Didi ta faWa muryarta na sha™ewa.

Nayla ta ce, "Didi meye na bani ha™uri kuma?."
"Nayla ban san me zan ce miki ba, kin Wauke ni tamkar Yayarki, Hajja ta Wauke ni jikarta, kun yi min komai a rayuwa amma da abinda zan saka muku kenan. Nayla...." Sai Didi ta kasa magana saboda kukan da ta ji ya taho mata sai kawai ta yanke wayar.

Nayla ta damu sosai, ta kira Didi bata Wauka ba ta kalli Salma ta ce, "Kuka fa na ji Didi tana yi Salma." Salma taja tsaki ta ce, "Ai dole ta yi kuka, wannan ™ani nata ya zamar mata

Please Login or Register in order to submit comment