Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan abinda ya faru da Narma bata ga ya shiga wannan yanayi ba. Ta Wan ja da baya kar ya maketa ta ce,  Omar Ina sonka, bazan yi maka abinda zai cutar da mai ba. Ban saka ka karSi auren nan saboda na Sata maka ba, na saka ka karSa ne saboda& ..

Wata irin zabura yayi ya zo daf da ita ya ce,  saboda ki faranta min? Kina so ki ce kin saka karSa ne saboda ki faran ta min rai Didi? Ya girgiza kai ya ce,  Auren nan bazai taSa faranta min ta rai, kin haWa kan ki da mi™iyina a duniya kin aurar dani kamar wani ´ar tsanar roba. Yanzu zasu dinga ji a zuciyarsu sun zama kamar dole a rayuwata saboda su suka karSi aurena. Kuma wai kin san maganar amma ki ka yi min shiru, har ki ke cemin kar na baki kunya ashe akan wannan ne. Wallahil azim baki kyauta min ba, in na ce bana jin haushin ki ™arya nake yi, in ba dan ke Win ba ce wallahi ko wacece yanzu tana gadon asibiti in ma ban zama silar barinta duniya ba. Amma kema Win ma ki yi baya-baya a yanzu, yadda nake jin zuciyata wallahi zan iya sha™e ki.

Didi bata taSa jin tsoronsa ya shiga ranta kamar yau ba, yadda yake hayayya™o mata lamarin ya firgita ta sosai. Ta dake bata nuna masa ba, ta ri™o hannunsa ta ce,  Ka tsaya ka saurare ni. Yanzu ka Wauka ni ce a matsayin Nayla, aka aurawa wani ni kamar yadda aka aura maka, zaka ji daWi ace sake ni daga Waura aure da kwana bakwai kawai?.

 Gwara ace auren ya mutu yanzu akan ace ya jima. Ai wallahi in kece sai an raba auren, babu wani a duniya da zai aurar dake ba da sanina ba kuma na amince ki cigaba da aurensa. To in ma wai kina yi min misali da kan ki ne dan ki saka min wani tunani ki daina, dan kina sake tunzura ni ya faWa tana janye hannu ta daga jikinsa dan wallahi haushi take bashi.

 Yarinyar nan itace wacce ta shiga ta fita aka karSo ka daga wajan Sen, ba dan ita ba da wata™ila har yanzu kana can a hannunsu. Wanne irin karamci ne mahaifinta bai yi mana ba da muka je? Wanne irin tarba ce bamu samu daga gare shi ba ehe?. Da aka zo aurena a gidan kakarta aka yi komai, daga ™arshe ma kakarta ce tayi min kayan Waki. Meyasa zamu saka musu ta hanyar sakin ´arsu Omar?. Kana da halin da zaka ri™eta a yanzu, in da Omar Win baya ne da bashi da aikin yi nima wallahi bazan amince ba, saboda na san baza ka iya ri™e aure ba, amma Omar Win yanzu daban ya ke da na dah.

 Ka ji matsalar, har an fara yi min gorin ba ni ne nayi miki kayan Waki ba wata bare ce a gefe. Inda ni nayi ai baza ki kalle ni kina faWa min wannan har ki kafa hujja dashi ba. Kuma da ki ke zancen ita ta shiga ta fita aka karSo ni daga Abuja ni na saka ta? Na je na ce tayi min ne Didi?.

 Ba kai ka ro™a ba ni na ro™a, dan haka in na ro™a abu kamar ka ro™a ne. Banza ya yi mata ya juya mata baya yana jan numfashi. Didi ta ce,  Auren nan itama ba a son ranta ya faru ba, babu wanda ya san dalilin mahaifinta na aura mata kai a ™aramin lokaci, Meyasa baza ka fahimta ba?.

Jiyowa ya yi yana kallon ta ya ce,  meye ma sunan garin su?.
 Kaduna.
 Daga Kaduna kawai ya Wauko ™afa ya zo Kano, da kuma yazo Kanon sai ya rasa inda zai je sai gida waWancan munafukan mutanen nan, kuma kaf ´a´an da suke dasu ya rasa da wa za a Waurawa ´arsa aure sai da ni. FaWa min in ba shirya abin nan aka yi ba me aka yi? Haka kawai zuciyarsa zata faWa masa ya aura mata Omar ne?, Na san ´arsa ne?, Ko na taSa zuwa gidan su nace Ina sonta?, Ko kuma magana mai ™arfi ta taSa shiga tsakanina da ita ne?. Amsa min Didi.

Didi ta ce,  ™addarar aurenku ce ta kawo hakan, kuma shi yayi haka ne saboda dalilinsa wanda bamu sani ba, wata™ila hukunci ya ke yiwa ´arsa.

Ya wara hannaye tare da harWe su a ™irji y ce,  Ni kuma gani mai ba™in halin duniya wanda dani kaWai za a haWata ya zama mummunan hukunci a rayuwarta ko Didi?. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  mun gama maganar nan da kai, Zaka ri™e aurenta babu saki koda mahaifinta ne ya ce ka sake ta kar ka saketa, ka ri™eta a hankali komai zai canja.

 Hmmm! Shine abinda ya ce kenan yana kawar da kansa gefe cikin matu™ar takaici. Didi ta ce,  Yanzu ka Wauko rigar ka da ka jefar, ka saka hular ka kazo mu je gidan da zaku tare kai da amar& .. kallon da ya yi mata shine ya hanata ™arasawa. Ya ce,  ™arasa mana Didi, Ina jinki.
 Omar Yayarka ce ni fa, ka dinga sanin irin abinda zaka yi min.
 Ai ina gab da daina kallon ki matsayin yayar tawa, dan babu abinda zaki sake saka ni nayi kuma a yanzu.

Didi a raunane ta ce,  ni dai don girman Allah ka saka kayanka mu je gidan da aka kai amaryarka, don Allah ka zo mu je kar ka ce min baza ka je ba.
 Au ni ne ma zan bita wani gida ba ma ita zata zo ba ko?. To bara kiji, na rantse da girman Allah baza ni ba, gwara na yi miki kankat ki ji, wallahi babu inda zan je.

Ajiyar zuciya Didi tayi cikin damuwa, tunda har ya rantse ta san bazai je ba wallahi sai ta shiga damuwa fiye da wacce take ciki. Ta kalle shi ta ce,  shikenan, naji baza ka je yanzu ba, amma in anjima sai mu je zan zauna har lokacin mu je tare. Kallon banza yayi mata dan bazai amsa ba, ya share ta ya cigaba da abinda yake yi.

 Omar in baka je yau ba babu daWi, amarya ce fa Omar, amarya fa. Tunda ka rantse ka ce baza kaje yanzu ba, zan zauna na jiraka har zuwa anjima sai mu je ta sake faWa kamar zata yi kuka dan damuwar Omar tsaf zata sakata hawaye

Bar mata wajan ma ya yi alamun bata bu™atar amsa, har zai gota ya juyo ya ce,  naji ana batun wani gwajin jini, Ina so ki sani babu wanda ya isa ya saka ayi min wani gwaji, gwara ki faWa musu kar azo ace za a Wauki jinina, dan wallahi sai na cakawa yaron da aka turo allurar yana faWa ya shige Waki ya barta a wajan a tsaye cikin rashin sanin abinda zata yi.

Didi cikin tsananin damuwa ta ce,  Ya Allah ka kawo min mafita, rigimar Omar yawa gareta. Wayarta taji tana ™ara ta duba ta ga AbdulHamid ne ta san yana waje yana jiranta. Numfashi ta fesar ta fita daga gidan ba tare da ta Wauki wayar ba.

A mota ta same shi ta shiga ta zauna tana sauke numfashi. Ya kalle ta ya ga yanayinta babu daWi ya ce,  Ya dai?.
Sai da ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Omar gab yake da sakawa jinina ya hau YallaSai, ka ga masifar da yake zazzaga min kamar shine gaba ni?. Ya yi murmushi ya ce,  Ai dole yayi masifa fa, aure irin wannan baka shirya ba ai dole yaga kamar ba a kyauta masa ba.

 Yanzu maganar da nake maka ya rantse da Allah bazai je gidan amaryar ba, kuma daman na san bazai yi min alfarma biyu a yau ba. Na farko na tilasta masa ya furta ya amince da auren a gaban iyayenta, tunda har ya amsa musu ni kaina na san bazan iya ta™wara shi ya je gidan ba a yanzu, sai kuma wani lokaci. Gashi suna zancen gwajin jinin da ake yi na aure, ya ce na faWa musu aka turo wani ya Webi jininsa sai ya chaka masa allurar.

Dariya sosai AbdulHamid ya yi ya ce,  Kai Omar yana da bin dariya wallahi.
 Dariya ma ya baka?.
 Dariya ya bani mana. Amma yanzu ya za ki yi? Ya kamata ace yaje gidan amaryar tunda har ya amince da auren.

 Ya ce wai ba ma ita zata biyo shi ba shine zai bita? Ashe ba za a je ba. AbdulHamid ya murmusa ya ce,  Wannan amarya dai taga ta kanta, irin wannan miji mai zafin zuciya da zafin kai irin Omar zama dashi ai sai mai ha™uri. Ga kuma yadda auren ya zo yana gani kamar an bashi ita sadaka, sai dai mu yi fatan Allah ya sa ya ri™eta hannu biyu, amma zata sha wahalarsa na wani lokaci.

Didi ta ce,  wallahi tausayi take bani, sannan kunyar iyayenta nake ji. In ba ™addara ba wallahi tafi ™arfin Omar nesa ba kusa ba, yanzu haka aikin gwamnati take yi duk da dukiyar da mahaifinta yake da ita. Ga kyau masha Allah kamar ita tayi kanta. Shi ba abin farin cikinsa bane ya tsinci dami a kala? In aurota zai yi ina ya ga abinda zai kashe ya aureta?. AbdulHamid ya ce,  Ki bar zuciya da abinda take so, haka ki bar zuciya da abinda bata so. Ita tana sonsa, shi kuma baya sonta, kowa shi kaWai ya san abinda yake ji a ransa.

 Shiyasa take baki tausayi, inda ace bata sonsa da kaina zan saka ya saketa kawai a warware auren, amma tana sonsa sosai tana burin mallakarsa a matsayin mijinta. Shiyasa na™i bashi damar sakinta, ba dan na ba™anta masa nayi hakan ba sai dan saboda soyayyar da take yi masa. An ce ™iyayyar namiji tafi ta mace zafi, har gwara ace itace bata so akan ace shine baya so. Aka yi rashin sa a namijin ma irin Omar! Karkataccen mutum mai shegen ri™on tsiya. Tunda nayi masa faWa a gabanta yake jin haushinta, ashe itace matarsa dukkan mu bamu sani ba. Wallahi lamarin Omar yana damuna sosai.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce,  kar ki damu, ki tayi masa addu a komai zai zama daidai. Kuma zancen ™iyayyar namiji duk zance ne kawai wuyarta dai ya fara sonta, daga lokacin da Allah ya saka masa sonta a zuciyarsa wallahi duk wannan wahalar da yake bata sai ta fanshe cikin ruwan sanyi. Ke ai kin fini sanin komai, kin san halin ku na mata da lagon maza da ku ka haddace a kan ku. Ki yi masa addu a kawai, in yaso gobe sai na dawo dake mu kai shi gidan amaryar. Yanzu ita da wa zata kwana?.

 To bana ce ba, amma muje gidan yanzu nayi magana da ita, gwara na faWa mata gaskiya kawai kar na Soye mata ai ta san halin Omar Win.
 Eh ki faWa mata, amma kar ki yi amfani da kalaman da zata ji babu daWi. Ki yi magana yadda zata fahimta, in yaso ko gida zamu wuce da ita ta kwana sai mu tafi, in yaso goben in kika rarrashi Damisar sai mu dawo.

Didi ta ce,  Damisar gaske, in ji Hajja tace carbin ™wai janka sai mai nutsuwa, to shi Omar mai nutsuwar ma hargitsa shi yake yi. Murmushi yayi ya ja motar zuwa ™ofar gidan dan babu nisa sosai, in da ™afa ne yafi nisa, in a mota ne gidan babu wahalar zuwa.

A ™ofar gidan ya ajjiye motar tare da kashe motar, Didi ta kalli gidan tana sauke numfashi. Gate Win gidan fari ne mai Waukar ido, ™ofar gidan da haske sosai gidan ya yi kyau kana gani kasan sabo ne. Wajan bashi da jama a sosai duk da Waya unguwar ne amma wajan gidan su Didi ya fi mutane akan wajan gidan Nayla. BuWe motar Didi tayi ta shiga gidan zuciyarta sam babu daWi.

Gida yana da wajan ajjiye miota guda Waya sai hanya mai girma wacce za siya ajjiye babura har gida biyu. Kana ganin gidan ka san sabo ne ba a jima da gama shi ba, komai sai Waukar idanu yake, ga wasu flowers da suka fara tasawa daga gefe an zagaye su anyi musu ado da ™ananun fitila a ciki. Sai ka hau steps guda biyar wanda aka zagaye su da staircase silver, ga chandelier light da ta haske ™ofar falon mai kyau.

Falon ta buWe ta shiga, yana girma amma ba sosai can ba sai dai ya yi kyau matu™a, kai kana ganin falon kasan kuWi da masu kuWi ne suka haWa shi. Ya sha kujeru na alfarma, ga 85 inchs plasma an Worata akan tv stand mai kyau da girma, ga turkish carpet da ya mamaye tsakiyar falon an Wora masa center table a kai. Daga can gefe ga dining room an saka dining table mai guda shida, ya sha adon show glass cabinet, an saka plates, mugs da glass cups. Kusa da dining Win fridge ne babba mai tsaho da girma. Daga can ™arshen falon an saka cabinet Win da aka yi ado turaren wuta da humra, an yi ado da fitila a ciki sai kawowa suke suna Waukewa. Didi da yake ta san gidan bata tsaya ™are masa kallo ba kai tsaye Waya ™aramin falon ta shiga.

Shi da yake bashi da girma kujerun sa basu kai waWancan girma ba, shima akwai tv da carpert komai ya fito tsaf gidan ´an gayu.

A zaune ta tarar da Nayla da Salma da kuma Jidda suna ta rarrashin Nayla da take zubar da hawaye. Sallamar Didi ya saka suka kalle ta tare da amsawa, ta zauna kusa da Nayla ta dafata ta ce,  Nayla har yanzu kukan ne? Jikinki da zafi, Salma ki yi mata allura.

Salma ta ce,  na yi mata, sai tayi bacci zata ji daWi.
 Sannu kin ji Nayla, Allah ya ™ara miki lafiya. Kiyi ha™uri kin ji?. Hawaye ya sakko daga idanunta ta share hawayen tana numfashi.

Didi ta kalli Salma da take kallon ta itama, kafin Didi ta ce wani abu Salma ta ce,  Ina angon? Ya ™i zuwa ko?. Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce,  A a yanzu zai ™araso shiyasa nazo, kin san hali basai na faWa ba, zuma ne sai da wuta. Salma ta murmusa kawai bata ce komai ba. Nayla jin zaizo sai ta mi™e kawai ta shiga bedroom bata ce komai ba.

Didi ganin ta shiga ciki ya saka Didi ta sauke murya ™asa ta ce,  Tsakani da Allah Omar bazai zo yau ba, ya ce ya karSi auren a yau bazai kuma yin wani abun a yau ba. Salma kin dai san halinsa kema, ni Win ma ba barina yayi ba. Na faWi haka ne akwai saboda bata da lafiya, kar na faWi abinda na faWa miki taji babu daWi a zuciyarta. Yanzu ya za a yi? Ko zata bi ni mu je gidana ta kwana? Kin ga ai babu daWi a ce ta koma gidan Hajja ko gidan Daddy ko?.

Jidda cikin damuwa ta ce,  gaskiya babu, ko mu tafi gidana ta kwana kawai?. Didi ta ce,  a a Jidda, mijin ki zai yi mamakin ganin amarya a tare dake. Masalaha kawai ta bi ni Win muje ta kwana, ba a barta ta kwana ita kaWai ba ko?.

Salma ta girgiza kaita ce,  gaskiya Omar bai kyauta mana ba Didi, ki yi ha™uri da abinda zance. Omar ya daina ganin kamar sadaka aka bashi Nayla, Allah na tuba ba dan wannan abin da ya faru ba wallahi Nayla ba sa ar aurensa bace, Nayla matar manya ce ba ta ™ananu ba wallahi. To ™addara ta riga fata, da kuma sharrin so.

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce,  na sani Salma, na sani ki daina bani ha™uri gaskiya ki ka faWa ai ba ™arya ki ka yi ba. In ba dan sharrin soyayya ba ina Nayla Ina Omar? Ba tsarar aurensa bace, tazarar su na da matu™ar yawa.

 Nayla Win ce ya kamata ace tana wannan abinda yake yi ba sai shi. Gaskiya ni haushinsa nake ji wallahi, meyasa bazai karSi ™addara a yadda tazo ba? Ita Nayla ba ™addarar ta ™arba ba har take zaune a gidan nan? Salma ta faWa a Wan fusace dan haushin Omar take ji sosai.

Jidda ta ce,  duk ba wannan ba, meye mafita?.
Didi ta ce,  Ku lallaSata tazo mu je gidana mu kwana, ni kuma zan saka Omar ya dawo gidan nan gobe in sha Allah. Salma ta ce,  Didi babu tabbacin dawowarsa.
 Gaskiya babu tabbas Salma, za a kai ruwa rana dashi a wajan dawowa gidan nan, musamman in ya san daga hannun waye gidan nan ya fito. Amma zan yi maganinsa, zai zo in sha Allah.

Salma ta ce,  Ku je kawai ni zan kwana nan, zan faWawa Hajja bata da lafiya ne shiyasa akace na kwana saboda zan saka mata ruwa. Daman kamar na san hakan zai faru na ce Mima ta kwana a gidan Hajja, dan haka ba wata damuwa.

Didi ta ce,  kina ganin hakan ya yi?.
 Ya yi Didi, kar ki damu. Kema duk ya saka ki a damuwa da zullumi da fargaba. Didi ta ce,  Hmmm bari kawai Salma, baza ki gane ba kawai, amma ni kaWai na san waye Omar. Amma in sha Allah silar wannan auren shine silar canjin halayyarsa. Ina so ya so Nayla fiye da komai a duniya, ita kuma duk wannan hawayen da yake sakata a lokacin nake so ta fanshe.

Suka yi dariya Jidda ta ce,  Wallahi nima Didi Ina ji a raina auren nan nasu ba mai mutuwa bane, haka Allah ya ™addarar zuwansa shiyasa hakan ya faru. Amma dai zama da Omar Win ne sai an shirya.

Didi ta murmusa ta ce,  Allah ya sa hakan, in hakan ya tabbata ba wani shirin da zata yi, a hankali zata mayar dashi yafi ruwa sanyi. Suka amsa da amin suka fito ita da Jidda. A harabar gidan suka tsaya Didi ta ce,  Salma kwana ku biyu babu hatsari?. Salma ta ce,  unguwar su Tiger ce fa, kuma matar tiger Win ce a gidan kar ki manta.

 Amma waye ya san ita matarsa ce? Ko na yiwa su Bashir magana wani yazo yana zagawa?. Salma ta ce,  kar ki damu, babu abinda zai faru in sha Allah. Didi ta amsa suka fita ta shiga motar AbdulHamid, Jidda ta shiga ta mijinta suka bar cikin unguwar.KRB3P003
Arewabooks@nanahaleema11.

Salma a sanyaye ta koma bayan ta rufe gidan yadda ya kamata, tana shiga falon ta kulle falon ta shiga bedroom Win da Nayla ta shiga ta kwanta. Tana shiga Nayla ta Wago kai ta kalle ta ta ce,  Baki wuce ba?. Salma ta zauna ta ce,  a na zan Kwana ai.
 Hajjan fa?.
 Na tura Mima ta faWa tana zare Wankwalin kanta.

Nayla tayi ajiyar zuciya tare sa lumshe idanunta. Gata daina gidan wanda take matu™ar so take kuma ™aunar rayuwar dashi a matsayin matarsa amma shi baya nan yana wani wajan daban, sai an lallaSa shi ma sannan zai iya zuwa gidan. Meye amfanin ma son da take yi masa oho, gashi duk wannan abubuwan da suke faruwa bata jinta daina sonsa, sai dai wani lokaci tashin hankali ya kansa ta ji komai ya fita daga ranta amma da ta nutsu soyayya sa zata motsa.

 Nayla ki samu ki yi bacci, ko zaki ci abinci?. Nayla ta girgiza kai alamun a a kana ta ce,  a ™oshe nake Salma, bacci nake so yazo ya ™i zuwa gabaWaya. Salma ta ce,  zai zo in sha Allah. Wutar solar ce a gidan nan ko nepa?. Nayla bata amsa ba ita kuma fita dan ta duba. Tunani kala-kala Nayla tayi shi kafin bacci ya Wauketa saboda kanta da ya yi mugun nauyi bata san lokacin da tayi bacci ba.

Washe gari bata farka ba sai sha biyu na rana, ta buWe ido ta ganta a sabon gida ba gidansu ko gidan Hajja ba. Ajiyar zuciya tayi ta mi™e zaune a lokacin Salma ta shigo ta ce,  Mrs Omar kin tashi? Ga ruwan wanka can mai zafi na juye miki a boket sai ki je ki yi wanka. Kin san gidan babu water heater, babu bathtub, babu shower glass sai dai bokitin. Kuma Mama ta yi ™o™ari har bokiti an ajjiye miki a ciki.

Nayla ta kalle ta itama ita take kallo, Salma ta ce,  ki tashi ki yi wanka zaki fi jin daWi, kayan ki na saka miki a wardrobe in an kawo sauran daga Kaduna sai ki ™arasa sakawa dan wannan basu da yawa gaskiya. Akwai Sabon brush da toothpaste suna ciki duk na ajjiye miki. Kai ta girgiza ta mi™e tsaye ta saka slippers Win da yake bakin toilet Win akan doormate ta shiga.

Sabo da irin toilet Win gidansu masu shegen girma sai ta ga wannan Wan ™arami, duk da bashi da ™an™anta, yana da girma amma a idonta ™arami ne sosai. Har towels da bathrobes akwai a ciki, ga washing machine babba a gefe, an yi ™aramin bathroom cabinet me kyau a gefe an jera mata towels, bathrobes, showerl gels, soaps, shampoos da sauran kayan banWaki. Harda ™aramar hand dryer a ajjjiye a gefe.

Abin ya bata mamaki ganin shower gel Win da take wanka dashi a banWakin, bata tsaya godon tunani ba tayi wanka tare da alwala ta fito. Lokacin Salma ta sake shigowa Wakin Nayla ta kalle ta ta ce,  Salma na ga shower gel Wina, waye ya siyo?.

Salma ta ce,  ni ce na shiga sahad kafin ki tashi, bana so ki nemi komai ki rasa har ki ji babu daWi a zuciyarki shiyasa na siyo komai na amfani. Har pad na siyo miki na ajjiye saboda ko amfaninta zai tashi kusa. Murmushi Nayla ta yi ta ce,  na gode masoyiya. Murmushi itama tayi ta ce,  bathroom Win naki mai kyau wallahi, ya burge ni, kin san ina son bathroom mai komai fari. Matsalar kawai babu water heater, amma akwwi tank ina jin gidan akwai borhal, in kika kunna shower ruwan sanyi ne zai antayo.

Nayla bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Salma ta ce,  Yanzu dai ki shirya ki yi sallah ga abinci.
 To ta furta a ta™aice tare da zama tana kallon Wakin.

Kai da ganin furniture Win Wakin ka san masu tsada ne, sai Waukar ido suke yi kasancewar su sababbi. Šakin yana da madaidaicin girma dan ya cinye komai kuma bai matse ba ya yi yadda ake so, ga kuma center carpet a tsakiyar Wakin a Wora ™aramin table a kai wanda aka yi masa ado a kai. Daga can ™arshen Wakin akwai ™aramar cousion guda Waya wacce take kusa da carpet Win da aka ajjiye. Ga cabinet na ajjiye takalmi da jaka a gefe.

Duk ta san tsarin Mama ne wanann, amma tayi matu™ar mamaki da aka iya tsara komai a cikin kwana biyu kamar an jima ana shiryawa hakan. Wardrobe Win ta kalla ta ganta a gefe mai ™aton mudubi a jikinta. Saman Wakin ta kalla ta ga fanka ce gata nan tana ta aiki har lokacin bata Wauke ba. Salma da take tsaye tana kallonta ta ce,  gidanki ya yi kyau ma sha Allah, ki gama sai mu fita har gate ki gani.

Mai ta shafa wanda ta san shima Salma ce ta siyo ta shirya cikin atampa Winkin da saba ko yauahe, ko bubu ko Tbubu ko kuma Ashape.

Please Login or Register in order to submit comment