Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk abinda yazo zuciyarsa, hakan ya saka ya kulle ido ya buWe ya ce, "Jidda!." Wani irin dum Nayla taji a zuciyarta, a karo na farko an kira ta da Jidda, duk da ta san sunanta ne amma ba dashi ake kiranta ba. Bata san ta Wago ta kalle shi sun sake haWa ido ba, tsayar da ido tayi a kansa na na wani lokaci kafin ta sauke ido asa.

Omar ya sake tausasa murya ya ce, "Ki yi hauri!." Ba Nayla ba, shi kansa da ya bada haurin sai da ya ji sautin a zuciyarsa, fit ya ji kalmar ta fita ba tare da ya shirya ba. Bai taSa bawa wata halitta hauri daga zuciyarsa ba sai ita, itace mace ta farko da yake furta mata kalamansa suke fitowa daga zuciyarsa har kan harshensa

Nayla ta rufe ido ta buWe tana jin kamar ana Waureta da igiya, ta kasa koda motsin kirki sanyin da take ji yana mamaye jikinta kamar mai zazzaSi. Omar ya sake cewa, "Na Wauka barinki a inda nake shine zai zama maganin matsalata, amma da na zauna bakya nan sai na fahimci kece maganin matsalar. Ina so ki dawo mu cigaba da rayuwa ba irin wacce mu ka yi a baya ba, Da gaske nake ina so ki dawo rayuwata Jidda!

Nayla ta muguWa cikin sanyin murya ta ce, "Ba zan dawo ba, bayan kace dole aka yi maka ka zauna dani."

Omar ya yi murmushin farin ciki, ji yake kamar ya jawo ta jikinsa amma bashi da wannan arfin guiwar. Ya kalli fuskarta da take a asa ya ce, "in ji waye ya ce haka?." ago kai tayi ta kalle shi ta shagwaSe fuska ta ce, "kaine ka ce." Sake kashe masa zuciya tayi da salon maganarta, ya runtse ido da arfi yana murmushin da yai barin fuskarsa ya ce, "a baya haka ne Jidda, amma a yanzu ba haka bane."

Nayla ta kawar da kai cikin dakiya da dauriya ta ce, "ni bazan komai ba, Ina jiran saon saki daga gare ka. Bazan iya cigaba da zama da kai a haka ba, bani da daraja a idanunka, bani da ko wanne mahimmaci a gare ka. Ko lamarinka na shiga cewa ka ke yi baka saka ni ba na tsaya a iya matsayina. Ka kalle ni ka ce baka sona baka son zama dani, ka ce ka tsane ni, ka tsani aurena, babu abinda zai saka ka so auren. Gwara a haura kawai, bazan iya zama da wanda baya sona....baya son aurena ba. Na san ba da sanin ka aka aura maka ni bani, sadakata aka baka shiyasa ka samu damar faWar duk abinda ya zo bakinka......" ta kasa arasa maganar saboda kukan da ya taso mata. Ta share hawaye ta ce, "Ka bawa su Daddy takardar sakin, ni bazan sake zama da kai ba" ta faWa tana tashi tsaye zata tafi.

Miewa tsaye shima ya yi, rauni yake ji a zuciyarsa saboda jin kukan ta har cikin ruhinsa, in da a baya ne take faWa masa wannan maganar tsaf zai iya sakinta amma a yanzu bazai iya ba, sakinta daidai yake da barazana ga numfashinsa.

Omar murya a sanyaye ya ce, "Bazan iya sakin ki ba Jidda! Yanzu na fara rayuwa dake in sha Allah. Bana tunanin ko duniyar nan zata taru akan na sake zan sake ki, bazan iya ba!.." Cak ta tsaya daga shiga cikin gidan da take yi, ta juyo ta kalle shi ya Waga mata kai alamun abinda ya ce kenan. Ta girgiza kai ta ce, "maganar farko da ita ake amfani, ka ce baza ka taSa sona ba har abada?." Ya sauke numfashi kaWan ya tako yazo daf da ita tana jin saukar numfashinsa, idanunsa yana kallon na ta ya ce, "Maganar farko ba gaskiya ba ce, maganar yanzu itace gaskiya. Jidda ko za a raba ni da numfashina wallahi bazan sake ki ba!." Janye ido tayi daga kallonsa, ta kawar da kai tana jan numfashi. Da sauri ta juya ta shiga gidan dan tsaf zai iya karya mata zuciya, ita kuma tayi udirin bazata koma ba sai dai son da take yi masa ya kasheta.

Omar sai ya ji daamuwa ta mamaye masa zuciya a karo na babu adadi. Kalamanta basu tsaya masa a rai ba kamar yadda ganin hawayenta ya tsaya masa a rai, da alama abinda ya faWa mata ya yi mata ciwo sosai a wancan lokacin.

Dafe kai ya yi a bayyane ya ce, "meyasa ka ce haka Omar?." Dan aramin tsaki ya yi ya sauke ajiyar zuciya ya fita harabar gidan ya tarar da Daddy yana niyar shigowa. A nan suka yi sallama da Daddy cikin girmamawa ya fita ya bar gidan.KRB3P037
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla a guje ta shige falo da mutan gidan suke zaune, ta shiga Waki ta faWa kan gado tana kuka mai sauti. Kuka take yi da zuciyarta da gangar jikinta ba tare da ta san dalilin kukan ba. Jikinta har rawa yake yi saboda yadda take kuka mai matuar sauti kamar ranta zai fita.

Wai Omar Winta ne fa yazo yana so ta koma gidansa, shine yake cewa bazai iya sakinta ba, kenan sonta yake yi ko me?. Wannan tunanin shine yake sake karya mata zuciya take kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa.

Daddy da ya shigo falon da suke ya ga Mama da Mummy sun mie tsaye suna cewa, "Me ya samu Nayla take wannan kukan?." Daddy ya kalle su ya ce, "Ku yaleta, Mijinta ne yazo." Mummy ta dafe irji ta ce, "sakin na ta Win ya yi?." Daddy ya girgiza kai ya ce, "ya ce bazai sake ta ba, babu abinda zai saka shi sakinta. Ya tabbatar mana da yana matuar son Nayla."

Mama Sa'adatu ta ce, "to wai me ya haWa su har ta dawo gida haka?." Daddy ya ce, "ya sanar damu komai, ya tabbatar mana zaman da suka yi na wata shida ba zama ne na mata da miji ba, ya zauna da ita ne saboda dolen da Yayarsa tayi masa ba dan yana so ba. Amma a yanzu shi ya kawo kansa yake kuma so a sake bashi Nayla a karo na biyu." Mummy ta ce, "ikon Allah, da bai san da hakan ba sai yanzu?."

Daddy ya kalle su dan ya katse musun ya ce, "kuna ji, na amince da son da yake mata sosai, na kuma amince a yanzu zai rieta hannu biyu matsayin matarsa. Abinda ya rage zamu zauna mu ji ta bakinta gobe in Allah ya nuna mana. Sa'adatu ki barta ta kwana a nan, gobe Ali da Khabir zasu zo dan a tabbatar da abinda yake zuciyarta, in zata koma masa shikenan, in bazata koma ba babu wanda yi mata dole."

Mama Sa'adatu ta ce, "Gobe ya yi wuri Yaya, sati biyu tayi fa bai neme ta ba, shi kuma daga zuwa yau sai a zauna da Nayla gobe kamar daman jira mu ke yi ta koma? A sake bata lokaci ta Wan samu nutsuwa don Allah."

"Amma kin san tana son mijinta ko?."
"Na fi kowa sanin hakan, wannan kukan da take yi zai tabbatar da soyyayar da take masa." Daddy ya ce, "to ni dai na riga na ce masa gobe, bazan canja daga goben ba." Mama ta ce, "ai shikenan, amma gaskiya yayi wuri kamar daman shi muke jira" ta faWa tana Sata rai.

Nayla kuwa Salma ce ta shiga wajan ta ganin kukan da take yi sai ta riota ta ce, "Haba Nayla, wannan kukan fa? Me ya faru ki ke wannan kukan?." Nayla ta kwanta a jikin Salma tana kukan har lokacin kafin kukan ya fara raguwa a hankali tana jan numfashi. Salma ta ce, "Haba don Allah, wannan wanne irin kuka ki ke ke yi haka? Wani abu ya faru ne?." Nayla ta kalle ta ta ce, "Ya zo Salma."

"Daman ai na faWa miki zai zo ko? Kuma na faWa miki in yazo ba sakin ki zai yi ba."
"Salma na kasa gane a wannan yanayi nake ciki, ban san me nake ji ba a zuciyata."

Salma ta ce, "farin ciki ki ke ji, na tabbatar da yanzu yana sonki bazai iya kuma rabuwa dake ba Nayla." Nayla ta ce, "bai ce min yana sona ba Salma, amma ya ce bazai iya sakina ba." Salma ta yi murmushi ta ce, "To a gidan Daddy zai zae ya nuna miki soyayya ne Nayla? Ai soyayya da auna sai kin koma gidansa, na tabbatar daga ranar zaki fara jin daWin duniya. Don Allah ki bar wannan kukan, abinda mu ke so ne ya samu farin ciki ya kamata mu yi ai."

Nayla ta yi murmushin jin daWi ta ce, "Don Allah bakya jin hakan kamar a mafarki?." Salma ta ce, "ke addu'ar da muka yi akan hakan ta wasa ce? Ai na tabbatar da indai Omar alkhairi ne a gare ki zaman ku zai zama na soyayya da farin ciki kamar a asar larabawa. Amma fa ba daga su Daddy sun tambayarki zaki koma ba, yauwa...sai kin ja masa aji wallahi, saiya Wan jigatu kamar yadda ya wahalar mana da ke." Nayla tayi dariya ta kwanta a jikin Salma ta ce, "Salma na rasa me zan yi wanda zan nuna ina matuar farin ciki. Wai shine da kansa yazo, baya Soye abinda yake zuciyarsa kenan abinda ya ce min gaskiya ne?. Wallahi ban san wanne irin farin ciki nake ji ba."

Salma ta goge mata hawaye ta ce, "komai zai zama labari in sha Allah, zaki fara rayuwar jin daWi daga nan Abiy ya yafe miki ya tabbatar da yanzu Omar ki ka aura ba Tiger ba. Tiger ya jima da mutuwa yanzu Omar ne yake rayuwa." Nayla ta rungume Salma cikin farin ciki.

Bayan sallar magriba Mama ta shigo Wakin da Nayla take har lokacin hira suke yi da Salma ta ce, "Nayla Daddy ya ce ki zauna a nan saboda gobe suna so zasu tambayeki ra'ayinki akan komawa gidan mijinki. Amma nima goben zan dawo ai, in zaki bi ni mu je gabaWaya kawai."

Nayla ta ce, "To Mama zan bi ki Win."
"Yauwa mu je mu tattauna, dan bazan bari daga an zauna dake gobe ki koma ba, akwai abubuwa da yawa da ba mu yi a wancan lokacin ba zamu yi yanzu. Na san kina son mijinki, wannan lokacin ki ke jira kuma gashi yazo, Daddyn ki ya tabbatar min da gaske mijinki yana sonki kuma zai gyara abinda ya Sata. Baza ki koma da wuri ba sai min yi shirye-shiryen da ba mu samu mun yi wancan lokacin ba." Nayla ta yi murmushin jin daWi ta kwanta a jikin Salma tana murmushi. Sai dare suka bar gidan suka tafi gidan Mama

Omar kuwa tunda ya fita daga gidan yake jin zuciyarsa a matuar damuwa, a haka ya ajjiye motar ya shiga cikin gidan ya zauna yana furzar da iska. Bai samu zarafin tunani ba aka yi kiran sallah ya tashi ya shiga masallaci.

Bayan an idar ya dawo yana tuna yadda take hawaye sosai sai ya ji jikinsa gabaWaya ya mutu.Tsigar jikinsa har tashi take in ya tuna yadda hawaye suke mata zarya akan idanunta. aramin tsaki ya yi kawai ya mie ya Wauki key Win motar ya fita ya hau motar kai tsaye ya tafi gidan Didi.

Sai da ya je a hanya ya ga wani masallaci ana sallah ya tsaya ya yi sallah sannan ya arasa ofar gidan ya kira wayar Didi ya ce gashi a ofar gida. AbdulHamid ne ya fito yana cewa, "Omar kamar bao, har yanzu wai in kazo sai ka yi waya, baza ka shiga kai tsaye ba? Gidan Yayarka ne fa." Omar ya bi bayansa yana cewa, "Gwara dai hakan."

A falon ya samu Didi a zaune ya bita da kallon tausayi, gabaWaya tausayi take bashi ta koma wani iri kamar ba ita ba. Ya ce, "Sannu Didi, har yanzu wai lokacin haihuwar nan bai yi ba? Duk kin canja." Didi ta ce, "da saura Omar. Zauna mana." Omar ya zauna yana kallonta ya ce, "Sannu" ya faWa cikin sanyi da nuna tsnatsar damuwarsa akan yanayinta. Gaisuwa suka yi kafin Didi ta ce, "Ya na ganka da damuwa? Ko basu amince da dawowar na ta ba?."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "A'a Didi, sun karSe ni hannu biyu fiye da yadda nake tunani, mun yi magana dasu cikin fahimta da wasa da dariya. Amma sun ce min sai an tambayeta an ji in zata koma, kamar yadda aka bani dama a wancan lokacin itama za a bata dama." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "gaskiya ne ai Omar, ya kamata a bata dama itama kam gaskiya. Amma meye na ga ka damu?."

"Didi...." Sai bai arasa ba saboda damuwa, ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ita da kanta ta ce min ita bazata sake zama dani ba, ita dole sai na saketa ta gaji. Didi babban abin haushin ma kuka fa take yi, ban san ana jin zafin hawayen wani a cikin rai ba sai da naga tana kuka. A duk lokacin da na ga kina kuka ina ji a zuciyata, amma ban taSa jin irin haka, na kasa mantawa da yadda take kuka Didi, na kasa mantawa" ya faWa yana Wan lumshe idanunsa.

AbdulHamid ya yi dariya amma bai ce komai ba. Omar ya kalle shi ya ce, "ka ce in ina buatar shawara na neme ka, me zan yi?. Ni ban san me ake yi ba, ban iya rarrashi ba, ban iya magana da mace ba, ban iya komai ba. Duk arfina da tunanina ya are akan matarka, me zan ce mata?."

AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "To ayi hauri da muka arar maka da arfinka, amma yanzu ya kamata ka yi tunani, a duk lokacin ka ke tare da ita duk abinda ya zo zuciyarka shi zaka faWa mata." Ya nuna Didi ya ce, "Gurguwar shawarar da matarka ta bani kenan, ta ce na faWi duk abinda yazo raina amma da na faWa mata sai ta ke kuka. Me na ce mata da ya saka ta kuka? Didi me kika saka na faWa ne?" Ya arasa faWa yana kallon Didi. Didi ta yi murmushi ta ce, "babu lallai kalamanka sune suka kasa ta kuka Omar, wataila akwai abinda ta tuna ne. Wataila yadda ka kalle ta ka ce baka sonta shine abinda yazo zuciyarta har ya sakata kuka."

"Kuma fa ko Didi...ko lokacin Sata min ran da kika yi ne ya saka na ce haka, amma ko a lokacin jin abinda nake ji a kanta sosai." Didi ta yi murmushi ta ce, "ita bata ga haka a lokacin ba, dole ta ji babu daWi."
"Duk laifin ki ne, da baki Sata min rai ba da yanzu tana gida muna zaman mu lafiya."
"ata maka rai ya yi amfani, ba dan haka ba da har yanzu baka tabbatar da kana sonta ba, kana nan kana zuba mata wulaancin da ka saba."

Ya kalle ta ya ce, "ni bana wulaanta ta, kuma ko baki Sata min rai ba zuwa yanzu na fahimci mahimmacin da take dashi a rayuwata." Didi ta taSe baki ta ce, "kai dai ka sani. Ita abinda ta sani ka kalli fuskarta ka ce bana sonki, bata san wannan bayanan naka ba."

"To wai ita tana sona ne? Meyasa take jin haushi dan na ce ban sonta?." Didi ta kalle shi ganin ita yake kallo ta ce, "ba lallai ai sai tana sonka ba Omar, ta karSi aurenka kuma tana kallon ka a matsayin mijinta dole ta ji babu daWi in ka furta haka akanta." Ya yi aramin tsaki ya ce, "ni yanzu ku bani shawara kawai, in dai kuna so na cigaba da zama cikin nustuwa ku bani shawara." Didi ta ce, "Dole ka yi hauri na wani lokaci, kamar yadda iyayenta suka ce zasu bata dama to ka yi hauri ka ji me zata ce. In ta amince da kai daman abinda mu ke so kenan, in bata amince ba sai mu haura."

Omar ya yi mata banzan kallo yana harararta cike da faWuwar gaba ya ce, "a haura da me?." Didi ta ce, "mu haura da ita mana."
"Mtsw! wani lokacin kamar kina shaye-shaye. Yanzu kina tunanin akwai abinda zai saka na rabu da ita a kaf duniyar nan? Ko meye zan yi yai dashi wajan ganin na yi nasara a kansa. Ai wallahi ko iyayenta ne zasu ce na rabu da ita a yadda nake jin zuciyata bazan rabu da ita ba. In kaf duniya ne zasu taru a kaina a saka min wua a wuya ace na rabu da ita wallahi sai dai su kashe ni, in suka kashe ni su kawo miki gawata."

Zata yi magana ya katse ta ya ce, "Don Allah kar ki Sata min rai, ki bar ni da iya abinda yake raina ki adana kalamanki bana so, kar ki sake tarwatsa min tunani. Kar ma ki sake saka min baki, da mijinki nake magana ba ke ba." Abdulhamid shi dai dariya yake yi sosai, saboda dramar Didi da Omar abar dariya ce, umarni yake mata kamar shine yayan itace anwa.

AbdulHamid ya ce, "ka yi hauri Omar, ka bada lokacin kamar yadda akace, ni na tabbatar baza ta i dawowa gareka ba. Kaine fa Tiger, ga kyau, ga aji, ga nutsuwa, ga kuma soyayyar da ka ke yi mata, ta ya zata bari wannan damar ta kuSuce mata?."

Wani irin kallo Omar ya yi masa ya ce, "Matar ka bata faWa maka bana son zuga ba? Haushi take bani, na tsani a zuga ni, ka faWa min gaskiya ba abinda zan ji daWi ba." Abdulhamid ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "ba zuga ba ce Omar, amma tunda baka so shikenan. Maganar gaskiya sai ka jira tukunna, sannan ka yi oari kana ganinta ko kana waya da ita, hakan zai sake nuna mata da gaske kana sonta."

Omar ya Wan yi shiru yana jin nauyi a zuciyarsa sannan ya ce, "Bani da number ta, kuma ni babban tashin hankalin ban san me zance mata ba, ban iya magana da ko wacce mace ba a duniya sai Didi, ban san ta ya zan faWi maganar da zata amince ba." Didi ta ce, "Da ka fara maganar zaka ji tana fitowa daga zuciyarka Omar. Wai kamar baka so Narma ba? In kana waya da ita da wanne irin kalamai ka ke amfani wajan yi mata magana?."

Ya kalle ta yana buWe idanu ya ce, "Ai na ce ki daina saka min baki ko? Kuma ita Narma ban taSa rarrashinta ba, ban taSa tsayawa na yi wani abu dan faranta mata ko dan nuna ina sonta ba, ko yaushe itace take takura min da waya, na kan manta da ita in ba kirana tayi ba. Ki daina sakata a maganata. Magana ake ta wacce nake so ba waccan sharar ba, ki daina haWata da matata kamar cin fuska ne a gareta."

Didi ta ce, "yi hauri, amma ya kamata ka koyi yadda ake tafiyar da soyayyar mace, musamman kai da ka faWa mata kalamai marasa daWi. Ka nemi class na koyar da tattalin mace ka shiga" ta arasa faWa cikin shaiyanci tana dariya.

AbdulHamid ya ce, "Omar ita soyayya wani lokacin sai ana haWawa da arya tafi armashi, zaka iya faWa mata wani abun wanda kai kanka ka san arya ka ke yi itama tasan arya ne amma zata ji daWi a zuciyarta."

Omar ya hakimce yana wara idanu yana kallon Abdulhamid ya ce, "Oh to ke kin ji Didi, daman can wasu kalaman na sa ba na gaskiya bane arya ya dinga jera miki har ki ka aure shi." Didi tayi ar aramar dariya dan bata jin daWin jikinta dauriya kawai take yi.

Omar ya kalli AbdulHamid da yake ta dariya ya ce, "Ban tsara rayuwata akan arya ba, dan haka bazan tsara aurena a kan arya ba, duk kalaman da zan faWa zan tabbatar da na gaskiya ne zan sanar da ita. Dukkan ku taron tsintsiya ne babu shara, dana sani ma ban zo ba" ya faWa yana shafa kansa.

Didi ta ce, "Ka ga ka yi duk abinda ka ga ya kamata, amma sai ka yi hauri gaskiya, wannan gaggawar bazata saka ta dawo ba. Kuma ya kamata ace an haWa mata lefe, tunda yanzu kana son aurenta ya kamata ayi mata lefe kamar ko wacce mace." Ya kalli Didi ya ce, "kin san da hakan ki ka saka na kwashe kuWina na siyi waccan motar?."

"Yanzu abin ya zo raina ne Omar."
"Ana kashe nawa?."
"Iya arfin ka iya kuWin da zaka kashe. Ba zaka yi abinda ya fi arfin ka dan a burge ba, duk abinda zaka bata tafi arfinsa dan kawai kayan aure suna da daWi."

"To ai baki da lafiya, waye zai yi wannan aikin in ba ke ba?.." Didi ta ce, "Zamu ga ni dai, bara mu ga zuwa yaushe zata dawo." Omar ya bita da kallo sosai cikin kulawa ya ce, "kina lafiya kuwa? Ni ban yarda dake ba, kin canja gabaWaya."

Didi ta ce, "na gaji ne kawai, kwanciya zan yi."
Omar ya ce, "ki je ki kwanta, nima zan tafi yanzu." Wayar Didi ya Wauka ya Wauki number Nayla ya ce, "in wani yaji bani da number ta akwai raini a ciki, ko iya ganin number ta zai rage min kewa." Murmushi ta yi kawai suna hira da AbdulHamid kaWan-kaWan har ya raka shi ya tafi.

Kusan raba dare Omar ya yi yana kallon number Nayla, ya rasa wanne suna ya kamata ma ya saka mata. In ya saka Nayla ya goge, in ya saka Hauwa ya goge, in ya saka Jidda ya goge ya rasa wanne ya kamata ma ace ya saka mata. Shi su my love, my world Win nan duk basa burge shi balle ya saka. A haka ya yi bacci ba tare da ya yi saving number ba.

arfe takwas na safe ya farka saboda arar wayarsa, da ya duba sai ya ga AbdulHamid ne
ya Wauka da sauri tunawa da ya bar Didi babu lafiya a jiya. Yana Wauka AbdulHamid ya ce, "Omar Aisha ta haihu, ta haifi a mace."

Wata wawiyar ajiyar zuciya Omar ya yi, farin ciki ya mamaye masa zuciya lokaci Waya. Cikin zumuWi ya ce, "Da gaske? Tana nan Lafiya? A wanne asibitin ta ke?." Abdulhamid ya ce, "Muna nan asibiti da yake kan kwanar layin mu, yanzu haka lafiyar ta lau."
Omar ya ce, "gani nan" ya faWa yana kashe wayar ya tashi da sauri. A gaggauce ya shirya ya kira Goje a waya suka fita tare a motar.


Asibitin suka je Omar ya ga AbdulHamid a tsaye suka gaisa ya nuna masa Wakin ya ce, "tana ciki." Omar ya arasa Wakin ya buWe ya shiga da sallama. Mata uku ne suka amsa masa har Didi, kallo Waya ya yi musu ya kawar da kai gefe ya arasa wajan Didi yana kallon ta kamar yadda take kallonsa. Murmushi ya yi ya ce, "kin san zaki haihu baki faWa min ba tun jiya? Kina lafiya amma ko?."

Didi ta yi murmushi ta ce, "ai nima ban san da haihuwar ba Omar, yadda suka rubuta na rage sati Waya na haihu."
"Kina lafiya dai ko?."
"Lafiya lau Omar, na warware sosai, da yake ai tun jiya ne." Omar ya kalle ta ya ce, "Tun daren jiya kika haihu amma da yake an raina matsayina ba a kira ni ba sai yanzu?."

Didi ta ce, "Cikin dare ne fa Omar." Omar ya ce, "Ina tsoron dare ne ni? Meye amfanina in ban zo ba? Da wani abun ya same ki fa?." Didi ta ce, "to ka yi hauri, yanzu tunda lafiya lau nake ba shikenan ba?. Ga arka" ta faWa tana nuna masa gefen ta.

Zubawa yarinyar ido ya yi tare da kai hannu ya shafi fuskarta sai ta motsa, ya yi murmushi yana kallon yarinyar. Didi ta ce, "ka Wauke ta mana." Ya girgiza kai ya ce, "A'a Didi, bazan iya Waukarta ba, zan ga kamar zan karyata ne, yaleta kawai."

Didi ta Wauke ta cak ta saka masa a hannunsa ta ce, "ta ya zaka ce baza ka Wauki arka ba? In ma ka karyata Win ba arka ba ce? In baka Wauketa ba tana da wani Uncle Win ne bayan kai?." Zubawa yarinyar ido ya yi yana kallonta idanunta a rufe, bai taSa

Please Login or Register in order to submit comment