Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen fuskarsa a Wan sake. Nayla ta sunkuyar da kai tana murmushi cikin farin ciki, ko babu komai yana kula da yanayin ta, hakan ya yi mata daWi sosai har bata san ta ri™e hannun Salma ba. Salma ganin fuskarsa a sake sai ta ce, "tana kewar Didi ne."

Bai amsa ba ya kalli Didi da ta ce, "Nayla tana kuka ne saboda taga Ina kuka, murmushin ma tana yi saboda Ina yi Omar. Bata da lafiya amma ta taho daga Kaduna tazo kawai saboda aurena, Ina ji da ita sosai kamar yadda nake ji da kai. Kai ™anina ne ita kuma ™anwata ce." Girgiza kai ya yi bai ce komai ba ya Wauke kai yana taSe baki, ya sake kallon gefen da take ya ga kanta a sunkuye amma murmushi take yi.

Didi ta ce, "Nayla mu shiga ciki." Tare suka shiga falon Nayla tana ji kamar kar ta shiga ta tsaya ta dinga kallon Omar tana samun sau™in abinda yake damunta.

Shigar su babu jimawa suka fito harabar gidan da niyar komawa gidan Hajja. Turus suka yi ganin Narma da Najwa sun shigo gidan har lokacin Omar yana tsaye a inda suka bar shi. Narma ta kalle shi ta ce, "Faruk!." Šago idanu ya yi ya kalle ta sai ta zube a wajan tana kuka sosai. Ido ya kulle ya buWe ba tare da ya kalle ta ba ta ce, "Omar me nayi maka ka ke hukunta ni da laifin da ba nawa ba? Faruk ni meye laifina da ko wayata baka Wauka?. Na yi maka message sau babu adadi amma ka ™i ka saurare ni Faruk, meye laifina a maganar nan?."

Bai motsa ba balle ya yi magana wani wajan daban yake kallo ta sake cewa, "Ina sonka, Ina ™aunar ka, Ina so na rayu da kai. Shikenan kuma sai laifin iyayena ya shafe ni Faruk? Daman laifin wani yana shafar wani ne Faruk?. Ban ™i ka ba, nace a haka Ina sonka, na ce zan bika mu dawo nan a Waura mana aure koda iyayena basa so amma ka ™i ji. Ya kake so nayi da raina ne Faruk? Na mutu kawai?."

˜aramin numfashi ya yi ya Wago idanunsa da suka fara komawa jajaye ya kalle ta. Zunbur ta mi™e ta ™arasa kusa dashi tana kallon idanunsa tana kuka ta ce, "kalli yadda na koma, kalli kaga yadda soyayyar ka ta kayar dani, ka tambayi Najwa ko bacci bana iya yi, ko abincin kirki bana iya ci kullum cikin tunanin ka da son ganin ka. Iyayena basu san na baro London ba, kai tsaye daga can Kano nazo saboda kai Faruk, saboda kai kawai na taho tun daga London dan na ganka. Wallahi in na rasa ka zan iya mutuwa" ta ™arasa faWa a sanyaye tana sake zubewa a wajan tana kuka.

Najwa ce tazo ta Waga ta a inda take zube, ta ri™eta a jikinta tana kuka ta kalle shi ta ce, "Yaya Narma tana sonka, a da bana goyan bayan auren ka da ita, amma yanzu Ina goyan baya sosai. Don Allah ka taimaki Yayata ko iya waya da ita ne ka dinga yi kafin komai ya daidaita a wajan iyayen mu. Na tabbatar maka da zasu soka zasu amince da auren ku nan kusa, don Allah ka yi ha™uri ka manta da komai kar Yayata ta rasa tunaninta a dalilin ka" ta faWa tana kallon sa tana hawaye.

Hasbunallahu wani'imal wakil shine abinda yake furtawa kawai a zuciyarsa, zuciyarsa bugawa take rauni ya mamaye masa jikinsa gabaWaya. Tausayin Narma na tasiri sosai a jikinsa amma ya kasa ce mata komai. To me zai ce mata bayan shi ya riga ya ajjiye shafin ta a rayuwarsa?. Hannunsa Narma ta ri™e ta ce, "baza ka ce komai ba?." Zame hannunsa ya yi daga ri™on da tayi masa, domin in ta ri™e shi kamar haWuwar wuta da ruwa haka yake ji a jikinsa. Kallon ta ya yi ido cikin ido kafin ya sauke numfashi ya ce, "Narma!." Luuu tayi ta faWa jikin Najwa ta ri™eta sosai tana kallonsa.

"Ki manta da abinda ya faru, ki manta da abinda ya wuce ki bi umarnin iyayenki. Babu abinda zan iya yi miki a yanzu, na yi iya abinda zan iya yanzu komai ya ™are!."

Narma ta bishi da kallo ta ce, "kenan kana nufin na manta da kai?." Ya Waga mata kai ta ce, "bazan iya ba, wallahi bazan iya ba. Ni kaina da ace na san inda zan ajjiye soyayyarka da na ajjiye na hutawa zuciyata. To ban sani ba Faruk, ban sani ba!"ta ™arasa faWa da ™arfi tana kallon sa.

A kausashe ya ce, "ya kamata ki sani Narma, ya kamata ki sani!. Komai ya ™are, komai ya wuce, bazan yaudare ki da kalaman da na san bazan cika su ba, bazan faWa miki abinda na san bazan yi ba. Shiyasa nake faWa miki gaskiya, kije ki bi umarnin iyayenki, sannan ki tafi!."

Narma murya na rawa ta ce, "na tafi kace fa?." Ya Waga kai ya ce, "eh ki tafi, babu abinda zan iya yi miki a yanzu, ki tafi kawai."
"Na tafi ka ce?" Ta sake maimaita tana kallon sa. A birkice ya ce, "eh ki tafi! Ki je ki yi abinda iyayenki suke so ki ™yale ni!."

Kuka take yi sosai mai sauti na kusan minti biyu bata ce komai ba, Waga kai tayi bayan ta goge idanunta tace, "Farul ka san mutane ™alilan ne suke samun kusanci da zuciyar mace? For examples iyayenta da ´an uwanta, tunda tana tare dasu tana samun soyayya da ™auna daga gare su tun tana yarinya. Kaima haka naji a kanka, na ji a raina kamar na tashi tare da kai tun ina ™aramar yarinya Faruk, ji take soyayyarka ta shiga jinina kamar na jima da sanin ka. Tun daga wannan lokacin naji kawai so nake nayi rayuwata a tare da kai, ko kaso ni ko kar ka soni har abada bazan daina sonka ba Faruk, ko ka so ko ka™i zuciyata saboda kai kaWai take bugawa. Har yanzu ina sonka Faruk!."

Ta sake goge idanu ta ce, "zan tafi Faruk, amma ka sani zan dawo ko ban dawo ba duk abinda ya same ni ka sani soyayyar ka ce sila. Bazan taSa daina sonka ba har a tashi duniya" ta faWa tana fita daga gidan a guje.


KRB2P014
Arewabooks@nanahaleema11.

Najwa bata bi bayan ta ba kallon Omar tayi ta ce, "na san kana tuna abinda iyayen mu suka yi maka ne, ta wani Sangare kana da gaskiya akan haka, amma ka tuna ita meye laifinta?. Tana sonka, tana so ta rayu dakai ta ko wanne hali, Meyasa baza ka amince ka aurata ba tare da iyayen mu sun sani ba?. In ka aureta ka riga ka karya lagon su babu abinda zasu yi a wannan lokacin. Ranta zaka ceto daga mutuwa, tana sonka ni shaida ce. Laifin mu da na iyayen mu bai kamata ya shafeta ba, koda zaka rabu da ita ka rabu da ita ta hanyar da zuciyarta zata iya Wauka ba ta wannan hanyar ba. Don Allah ka yi tunani Omar" Tana gama faWa ta juya ta fita da sauri itama.

Nayla jikinta mugun rawa yake yi tun shigowar Narma da duk kalaman da ta faWa, lokaci Waya zazzaSi ya rufe ta musamman yanayin Omar Win da take gani ta tabbatar da akwai soyayyarta a zuciyarsa. Hankalinta ya kai ™arshe wajan tashi, hawaye take yi wani yana bin wani kanta ya yi mugun nauyi. Salma hankalinta ya tashi sosai, bata so hakan ya faru a gaban Nayla ba dan Allah kaWai ya san halin da zata shiga.

Didi zuciyarta ta karye akan Narma, bata kula da halin da Nayla take ciki ba ta ™arasa wajan Omaar ta ce, "Omar meyasa haka? Meyasa zaka ce ta tafi?." A fusace ya ce, "to so ki ke na ce ta tsaya? so ki ke na ce ta dawo ta zauna a tare dani?." Didi ta ce, "tana cikin yanayin raWaWi Omaar, tana cikin zafi da ™aunar soyayyarka. Meyasa zaka ce mata kai tsaye babu kalaman rarrashi? Omar in wani abun ya same ta fa?."

"To ya zanyi Didi? Me zan yi mata?. So ki ke na aikata abinda take cewa?, baki ji abinda ta ce ba ne?. Tana faWin na aureta a yanzu iyayenta suna gida abinda ki ke so nayi kenan?."
"Ba haka nake nufi ba Omar, rarrashinta ya kamata ka yi shine zai saka hankalinta ya kwanta. Omar tun daga wata ™asar ta taho nan ba tare da iyayenta sun sani ba, ko iyayenta basu san tazo ba kawai tazo ta haWu da kai Omar. Omar tana sonka, son da take maka in kana tafiyar da ita ta wannan hanya zata iya samun matsala."

Kallon Didi yake yi bai ce komai ba ta kuma cewa, "Kamata ya yi ka rarrasheta ta in dawo nutsuwarta sai ka yi mata bayani yadda zata gane ba ta hanyar cewa ta tafi ba." Ya harWe hannu a ™irji yana kallonta ya ce, "Didi nifa ban iya rarrashi ba kin sani, me kike so nayi?. Aureta ki ke so nayi kamar yadda ta ce?."

Ganin ya tsare ta da idanu sai Didi ta ce, "ba haka nake nufi ba Omar, amma...." Ya katse ta ya ce, "Amma me Didi? Na ce amma me!? Duk abinda ya faru kin manta ne?. So ki ke na rarrasheta taji a zuciyarta zan sake komawa rayuwarta? Kina so na saka mata yardar cewa zan rayu da ita?. Kin san bazan aikata ba, bana Soye abinda yake zuciyata domin in na Soye mata kamar na cutar da ita ne. Sannan ni kin san ban iya rarrashi ba, ban san me zance mata ba, ban san ta wacce hanya ake rarrashi ba. Kuma ni gabaWaya ta fita daga kaina, ina ji kamar ban taSa sanin fuskarta ba wallahi, tausayi kaWai take bani."

Didi a sanyaye ta ce, "Amma Omar kuka take yi a kan soyayyarka."
"Dan an yi kuka a kaina ai ba wani abun bane, kowa ma zai iya yin kuka a kaina, kema zaki iya. Na zama silar kukan shine laifi, na zama silar zubar hawayen wani ko wata shine babban laifi da kuma babbar cutarwa. Ban zama silar kukan ta ba Didi, iyayenta sune suka zama silar hawayenta, na yi iya abinda zan yi domin farin cikinta. Mace ta farko da na samu kusanci da ita bayan ke itace, na je har gidan su a kanta ba tare da tsoro ko wani abu ba amma meye ya biyo baya?. Ko me iyayenta suka yi min bai dame ni ba, abu Waya akwai na sani bana sona ´arsu, bana ™aunar aurenta, kuma na barta har abada!."

Didi ta buWe baki zata yi magana ya dakatar da ita ya ce, "Didi in nayi gaba bana dawowa baya, in na wuce abu na wuce, in na tsallake bana sake tsallakawa. Na rufe shafin ta a rayuwata, ki Wauka kamar ban santa ba ko na santa na manta da ita. Ni wallahi mamaki ma nake yi, meye ya shiga kaina har na saurareta oho, asirin da iyayenta suke cewa nayi mata da alama itace tayi min, domin ina ganin abinda ya faru kamar mafarkin da zan farka a ce bai faru a gaske ba. Wai ni Omar ne da iya sauraren wata mace, macen ma irinta, wacce bana tunanin tana daga cikin irin tsarin matan da zan iya aura. Ai ni ya kamata na ce an yi min asiri ba itace zata ce an yi mata asiri ba ita ba wallahi. Ta je tayi abinda iyayenta suke so nima zan yi abinda nake so."

Didi a sanyaye ta ce, "Omar tana sonka, tana so ta rayu da kai." Omar ya ri™e haSa ya ce, "ba ke ki ke cewa bata dace dani ba? Ba ke ki ke faWa min tafi ™arfina ba?. Meyasa yanzu ki ke maimaita min tana sona?."
"Omar na fahimci son da take maka, kuma ai Wan adam baya kaucewa rabonsa, tana so ta rayu dakai."

"wata™ila ni kuma bana so na rayu da ita, ko da Ina so babu lallai tana cikin rabona Didi. Na rufe littafin da take ciki, na goge duk inda sunanta ya shiga rayuwata. Na faWa miki ina tantama akan dalilin da ya kaini na je har gidan su, har yanzu ina so na gano wannan dalilin amma na kasa, dan haka babu ita a cikin ™addarata, wata daban amma banda Narma!" Ya faWa yana kallon Didi dan sun manta da Nayla da Salma da suke baya.

Didi zata sake magana ya ce, "don Allah Didi ya isa, yau ranar farin ciki ce kar ki saka raina ya Saci kema na Sata miki rai, a bar maganar a nan kawai" ya faWa yana Waga mata hannu daga nan ya fita daga gidan.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ka jawo mafita a lamarin nan, Allah kar ka sa yarinyar nan wani abun ya same ta ta silar son da take yiwa Omar." A sanyaye ta juyo idanunta suka sauka cikin na Nayla da jikinta yake rawa Salma na ri™e da ita tana kiran sunanta.

Da sauri Didi ta ™araso ta ce, "Salma Lafiya? Me ya same ta?." Salma ta ce, "jikinta ne yayi zafi Didi, taimaka mu ™arasa da ita falo." Didi ta ri™e Nayla zuwa falon gidan suka kwantar da ita akan kujera. Hawaye take yi jiki na rawa, kalaman Narma da kalaman Omar suna ™o™arin tarwatsawa Nayla zuciya. Didi ta ce, "Salma ko mu kaita asibiti?." Salma ta ce, "Akwai allurar zazzaSi a gidan Hajja, bara na Wauko na yi mata" ta faWa tana fita da hanzari, Didi taja Nayla jikin ta da take hawaye.

Babu jimawa Salma ta dawo, a jijiya tayi mata allurar suka samu abu mai kyau suna goge mata jiki suna faman yi kata sannu. Hannun Didi na cikin nata a hankali zafin jikin nata yake raguwa sai kuma ta fara kuka da ciwon kai. Didi gabaWaya jikinta babu daWi ganin yanayin jikin Nayla ya bata tsoro sosai. A hankali bacci ya Wauke ta Didi ta kalli Salma bayan Nayla tayi bacci ta ri™e hannun Salma suka fito daga falon ta kalle ta tace "don Allah me yake damun Nayla? Ni jikina yana bani kamar akwai abinda yake damunta."

Salma ta yi ajiyar zuciya ta kalli Didi ta ce, "tabbas akwai Didi, amma babu wanda ya san meye yake damunta har yanzu. Amma bara Jidda tazo wata™ila ita ta san damuwar Nayla." Didi ta ce, "hankalina ya kasa kwanciya akanta, kana ganin ta ka san akwai abinda yake damunta tana Soyewa ne kawai bata so a sani." Salma ta ce, "gaskiya dai." Aikowa aka yi daga gidan Hajja akace Didi tazo sai ta fita ta bar su a gidan dan Nayla ta samu bacci.

Salma bayan Didi ta fita kuka ta dinga yi cikin tausayin Nayla, kuka take yi sosai tana kallon Nayla da take kwance tana bacci a wahale. Ta san Nayla tayi ™o™arin Soye abinda yake zuciyarta, ta san Nayla tayi juriyar azabar da take ji. Tabbas ya kamata ita da Jidda su yi wani abun kafin su rasa Nayla, ya kamata su san abinda zasu yi su ceto ta daga soyayyar mutuwa.

Nayla bata farka ba sai bayan sallar la'asar, da ta tashi ta ga Jidda da Salma da ™anwar Abbas mai suna Ummimi a zaune a kusa da ita. Mi™ewa zaune tayi tana cewa, "Naji daWin baccin nan Salma, har ciwon kan ma ya tafi." Salma ta ce, "shiyasa na yi miki allura ai." Nayla ta kalli Agogo ta ce, "Subahanallah, ban yi azahar ba ga la'sar ta wuce" ta faWa tana mi™ewa tsaye da™yar. Sai da ta nutsu sosai sannan ta iyawa tsayawa ta shiga Wakin Didi tayi alwala ta zauna a Wakin tana sallah.

Bayan ta idar ne sai hawaye ya fara sakko mata kawai ta koma tayi sujjada tana addu'a tana kuka. Jidda da Salma suna tsaye har ta gama ta Wago ta goge idanunta a sannan suka kalle ta Jidda ta ce, "Nayla yanzu haka zamu ja bakin mu muyi shiru kina cikin wannan yanayin? Ina kika kashe kan ki fa?." Nayla bata ce komai ba Salma ta ce, "Gaskiya Nayla ya kamata a samo mafita, son da kike yiwa Omar ba ™arami bane. Šazu akan Narma tazo da maganar da take faWa a akansa kika shiga yanayi na zazzaSi, Ina ga in aka ce yau yayi aure ya auri wata fa?."

Nayla ta kalle su ta ce, "Zan cigaba da ha™uri har Allah ya masa addu'a ta da nake yi kullum." Salma ta ce, "Amma kema sai kin yi wani abu." Nayla ta ce, "da bakin ki kin ce min ban dace dashi ba, sannan kun san bai san ma ina sonsa ba, ba kuma na so ya sani koda wasa. Sannan ga Narma, na san irin raWaWin da take ji a zuciyarta, wata™ila nata yafi nawa zafi ko nawa yafi nata zafi, abu Waya na sani raWaWin da take ji ba kaWan ba ne. Shi kansa yana sonta, wani dalili ne ya saka shi yake ™o™arin mantawa da ita kuma bazai iya ba. To me ku ke so nayi? Na hau bayan Narma a layin nima na ce Ina sonsa? In ya karSa aka ™i bashi aurena kamar ita fa?, in kuma bai karSa ba ya wulakanta ni fa?. Wanne ne mafita a nan?."

Judd ta yi ajiyar zuciya ta ce, "To Nayla haka zamu dinga ganin ki cikin mawuyacin hali muyi shiru?."

Nayla ta ce, "ha™urin da nake yi ina jurewa kuma shi zaku yi. Ni abinda yake bani tsoro bai wuce Abiy ba, ina komawa gida tambayar da zai yi ta son sanin abinda yake damuna ni ban san me zan ce masa ba. Ga maganar su Yaya Abbas, ya tabbatar min da kafin watan nan ya ™are na fitar da guda Waya a tsayar da lokacin aurena. Rashin lafiyar da nake yi akai-akai shiyasa baya yi min maganar. Ko wanne a cikin samarin nan guda huWun suna matu™ar sona, ko wanne ™o™arin bani kulawa yake yi, ko wanne so yake ya zama shine a sahun farko a zuciyata. Sai dai sun jima da makara, domin kuwa ni zuciyata ta jima da nisa a son Omar daga ranar da ya fara yin murmushi akan idanuna. Nayi dana sanin zuwa Kano a wannan lokacin, na kuma yi dana sanin shigowa gidan har naga murmushin sa" ta nuna Salma ta ce, "kuma kece sila, da ban dawo daga gida su Ya Shayida na tarar kun fita da Hajja ba da ban shigo gidan nan ba a ranar. Amma babu komai ™addarata ce a haka, kar ku damu komai zai wuce" ta faWa tana goge hawayen da ya sakko daga idanun ta.

Jidda a tausashe ta ce, "Allah ya yaye miki abinda ki ke ji Twiny, Allah ya kawo maki mafita da gaggawa."
"Amin Twiny, addu'ar da nake so ku yi min kenan." Salma ta goge idanunta da suke zubar hawaye. Nayla ta kalli Jidda ta ce, "Twiny baki faWa min wata nawa ba." Jidda tayi murmushi ta ce, "ban sani ba, keda baki ana ma an samu Babyn ba." Nayla ta ce, "tuba nake. Kana ji unborn, tuba second mum Winka take yi. FaWa min kwanan ka nawa?" Ta faWa tana kallon cikin Jidda.

GabaWaya ta sake karya musu zuciya, sun san tana yin haka ne saboda ta danne abinda yake zuciyarta amma rauninta ya riga da ya gama bayyana. Jidda ta ce, "Wata huWu ne fa Twiny." Nayla ta ce, "Allah ya fito nana dashi lafiya." Suka amsa da amin kafin Nayla ta ce, "mu je gidan bikin, mun zauna a nan ana can ana biki, ance har kiWan ™warya za ayi." Salma ta ce, "tun azahar ake kiWan ™warya, zuwa yanzu Ina jin ma sun tashi." Nayla ta ce, "Wayyo Allah, ban yiwa Didi li™i ba. Ku tashi mu je" ta faWa tana yatsine fuska saboda ciwon kai.

Mamakin dauriyarta suke yi ita kam sai dai tayi murmushi dan dauriya ta zamar mata dole. Suna fitowa daga Wakin Didi tana shigowa. Kallon su tayi one by one kamar bata yarda dasu bata ce, "sai naga kamar duk kun yi kuka." Nayla caraf ta ce, "kuka muka yi, kukan rabuwa dake Didi." Murmushi tayi ta ce, "ya jikinki? Tun Wazu nake zuwa sai ace bacci ki ke yi."
"Na ji sau™i sosai." Didi ta ce, "to abinci fa?."
"Zan ci yanzu in na shiga wajan Hajja."
"To ku yi sauri, kin san kune ™awayen amarya." Suka yi dariya gabaWaua har ita kafin su fita su barta a gidan.

Bayan sallar magriba kamar yadda aka tsara aka kawo motocin Waukar amarya. A lokacin matar Kawu ita ke ri™e da Didi wacce za a tafi kaita gidan mijinta. Hajja ce uwa wajan ta aka je tayi mata nasiha irin ta iyaye Didi duk jikinta yayi sanyi ta fara hawaye. Hajja ta gama bayaninta suka sake fitowa a nan take jin gidan Kawu zasu je daga can aje gidan Baba Adamu tunda duk su Mama Zainab suna tare da ita. Didi duk ta damu rashin ganin Omar, ta Wan Waga mayafin da aka rufe mata fuska dashi ta hango Nayla a zaune a harabar gidan Hajja ita kaWai tayi shiru.

Yafito ta tayi da hannu Nayla ta ™araso Didi ta ce, "Nayla kin ga Omar?." Nayla ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "ban ganshi ba gaskiya."
"Kira min shi a waya" ta faWa tana bata wayarta. Nayla ta kalli wayar gabanta na faWuwa ta buWe wayar ta shiga recents tana dubawa, sunansa ne na uku a jerin sunayen tayi waya dasu a ranar ta yi saving da Omar. A hankali ta danna number kamar mai jin tsoro ta saka a kunne tana jin ringing Win na bugawa da zuciyarta. Jin ta katse ba a Wauka ba sai hakan ya yi mata daWi ta ce, "Didi bai Wauka ba." Didi ta ce, "Ko ina ya je?."

Mama Zainab ta ce, "kar ki damu Omar ai ba yaro bane, wata™ila ya gujewa haWuwar ku ne saboda ya san rabuwar ku zata saka ki ji babu daWi shiyasa." Didi dai ba haka ta so gabaWaya bata ji daWi rashin ganinsa ba, daga haka suka fita aka shiga mota har su Nayla aka tafi kai amarya Didi.

" " " " " " "

Kowa ya zubawa likitan idanu jin abinda yake faWa akan Narma. Dad ya ce, "Yanzu Dr kana nufin damuwa ce tayi causing wannan yanayi da take ciki?." Dr ya ce, "yes sir. Damuwa ce tayi mata yawa shine ya haifar da wannan zazzaSin da yake jikinta, in ba ayi sauri an warware damuwar nan ba zata iya shiga wani hali nan gaba."

Mum tayi ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan Dr, mun gode." Dr ya yi musu sallama ya fita. Najwa ta kalli Dad ta ce, "Dad she's really in love with him, please grant her your consent to marry him." Mum ta harare ta tace, "you're not serious" ta kalli Dad ta ce, "kaga asirin nan bai karye ba ko? Yanzu haka zamu zuba ido ta mutu?." Dad ya kalli Najwa ya ce, "ya aka yi ku ka baro London bamu sani ba?."

"Dad ta matsa akan sai ta dawo, da naga ta damu sosai sai na biyo ta kawai saboda kar taho ita kaWai. Ashe ticket Win Kano ta siya a Kano muka sauka, ta kira wani driver a Kano ya zo ya kaimu gidan su Omar. Dad ya Omar ya nuna mata shi bazai iya sake dawowa gareta ba amma ta dage a kai. Har tausayi ta bani, naji a raina ina so tayi rayuwa da wanda take so."

Mum ta ce, "har gida su kuka je saboda tsabar baku da hankali ke da ita?." Najwa ta ce, "bani da zaSi ne Mum, dole na bita." Dad ya ce, "Najwa bata da laifi Dear, tayi abinda ya kamata. Maybe ba dan ita ba da yanzu bamu san halin da take
ciki ba. Meye mafita a lamarin nan nata ne?."


"Ku bata dama ta aure shi" Najwa ta faWa kai tsaye tana kallon su Dad ya kalle ta ya ce, "Shut up your mouth, Baki da hankali ki ke faWar wannan kalmar?." Najwa tayi shiru tana kallon su dan ta san babu mafita

Please Login or Register in order to submit comment