Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi domin sallar bana wankan su za a yi.

Daren ashirin da bakwai ga watan ramadan yana zaune yana addu a wannan dare mai matu™ar falala da lada da kuma amsa addu a, addu a yake yi sosai domin shigarsa islamiyya da yake karatu online ta ™ara masa sani akan abubuwan da bai sani ba a baya. Ya ™ara ilimi ya kuma san addu o i da yawa da matakan amsa addu a. Yana zaune yana jerawa Allah bu™atarsa sai yake jiyo kamar sautin kuka daga falon. Katse addu ar ya yi ya taso ya fito ya shiga ™aramin falon da take zama ko yaushe dan ganin lafiya take kuka. Itace Win kuwa take kuka amma cikin addu a, ta yi sujjada tana kuka mai ratsa zuciya babu wanda ya san abinda take faWawa wanda ya haliccita sai shi kawai.

Wani irin rauni Omar yaji wanda bai taSa jin sa ba a rayuwarsa, lokaci Waya zuciyarsa ta shiga bugawa da ™arfi ba tare da ya san dalilin da ya kawo hakan ba. Ya bita da kallo cikin wani yanayi da bai san meye ba, shi dai ya san ya tsaya yana kallon ta amma bazai ce ga dalilin kallon ba. Ba a bayyane take addu ar ba dan haka bazai ce ga abinda take cewa ba, shidai yana jiyo shashshe™ar kukanta. GabaWaya sai ya rasa kuzarinsa ya kasa daina kallonta, gashi dai ba fuskarta yake gani ba amma ya kasa Wauke ido daga kanta.

Šagowa ta yi daga sujjadar ta kifa kanta akan hannayenta tana cigaba da kuka. Da™yar ya iya jan ™afarsa ya koma ya zauna akan sallayar ya cigaba da ta sa addu ar cikin rauni. Ba tare da ya sani ba ya tsinci kansa yana ro™on Allah ya yaye mata duk abinda yake damunta ya bata abinda take so.

Lokacin sahur ne ya yi gashi ya manta bai shigo da fruits ba kamar yadda ya saba sha, hakan ya saka shi ya taso ya fito ya kalli inda take taga tana shan ruwa. Tambayar kansa yake yi ita bata sahur ne? Bai taSa ganin ta tana cin abu ba sai dai ya ga tana shan ruwa. Bai tambayeta ba ya sha kawai ya koma ba tare da ya ce mata komai ba.

Washe gari da safe da ™arfin guiwa ta tafi aiki, ji take kamar Allah ya amsa mata dukkan addu arta, ji take komai ya wanke daga zuciyarta kamar ta samu duk abinda ta tambayi mahaliccinta a daren jiya. ˜arfin guiwa take ji da karsashi tun a daren jiya, shiyasa ta saka a ranta komai ya zo ™arshe.

Tunda ta fita take bada sadaka cikin fariin ciki har ™arasa wajan aiki. Da wuri ta gudo daga wajan aiki ta wuce saloon a inda suke zuwa ita da Salma in tazo Kano. Gyara mata kai akayi da gyaran ™afa harda facial, ta bar wajan da niyar zata dawo washe gari ayi mata black henna.

Maimakon tayi gida kawai sai ta wuce gidan Abba, ta san duk shekara yana haWa shan ruwa ranar ashirin da bakwai ga wata. Bata taSa zuwa ba, yawanci ko yaushe tana Kaduna ko tana Saudia shiyasa wannan karon tayi ™udurin zuwa tunda tana Kano. Kowa da ya ganta ya yi farin ciki musamman yadda take walwala tana ta tsokanar mutane ana dariya. Da ita aka sha ruwa dan su Mama Sa adatu duk suna wajan har Abbas.

Da farko ta Wan ji babu daWi ganin Abbas, amma sakewar da ya yi yana janta da hira sai ta manta ta saki jiki aka sha ruwa tare. Bayan an gama aka zauna ana ta hira cikin zumunci ana tsokanar juna kafin lokacin i sha ya yi a haWu ayi sallah gabaWaya har tarawee tare aka yi.

Bayan an idar ne Abba ya kalle ta ya ce,  Hauwa Ina fatan baki da damuwa ko?. Nayla tayi murmushi ta ce,  babu komai Abba, babu abinda yake damuna.
 Ko a gidan auren na ki babu matsala?.
 Babu komai Abba.
 Haka ake so, Allah ya Worar da zaman lafiya a tsakani. Ta amsa da amin aka cigaba da hira.

Ta shi tayi ta ce,  dare yayi har tara tayi, bara na wuce. Abba ya kalle ta ya ce,  Zaki iya tafiya ke kaWai ko na haWa ki da driver in yaso ya hawo keke napep ya dawo?. Nayla tayi dariyata ce,  zan iya Abba, ai garin da jama a sosai tunda azumi ne. Abbas cikin tsokana ya ce,  in fa baza ki iya ba ki faWa, na san ki da shegen tsoro. Dariya ta yi sosai ta ce,  Nayla Kaduna kenan Ya Ab, Naylan Kano ai bata da tsoro.

Wata daga cikin cousins Winta ™anwar Abbas wacce suke kira Ummimi ta ce,  saboda Naylan Kano tana auren Tiger ko?. Kallon ta Nayla tayi kafin Nayla tayi magana ta kuma cewa,  Eh mana, matar Wan daba ai babu ita babu jin tsoro, ke da har gida aka shiga aka kusa kashe ki kuma kika cigaba da zama lafiya, kema ai kin zama jan wuya matar Tiger

Sai fara ar fuskar Nayla ta gushe gabaWaya saboda rashin jin daWin maganar, ta san gaskiya ta faWa amma bata ji daWin abinda ta ce ba ko kaWan. Abbas ganin ta canja alamun rashin jin daWi sai ya kalli Ummimu ya ce,  Zama matar Wan daban ma matsayi ai ne, wata ta zama mana in ta isa, ko ba haka bane Nayla?. Murmushi tayi ganin tayi murmushi sai ya ce,  mu je na raka ki mota ki wuce gida dare yana yi. Sallama ta yiwa su Abba tana ji suna yiwa Ummimi faWa.

Nayla kuwa tana shiga mota suka rabu da Abbas bayan sun yi sallama da al™awarin zai kawo mata ziyara ta wuce gida. Tana zuwa ™ofar gidan ta tarar da yaran sa su uku a tsaye suna ta waige-waige kamar masu neman wani abun. Ta tsayar da motar dan yanzu sune suke shigar mata da ita gidan, ko basa nan a waje take barin motar da sun zo zasu shigo su karSi key su shigo da motar gidan.

Nayla ta fito daga motar bayan ta Wauko jakarta da wayarta da snacks Win da ta taho dashi daga gidan Abba. Bash ne ya ™araso wajan ta ya ce,  Antyn mu ina kika shiga tun Wazu muna neman ki? GabaWaya hankalin mu ya tashi, na kira ki sau babu adadi ban same ki ba. Hankalin Damisa ya tashi sai faWa yake yi.

Nayla da mamaki ta ce,  na je gidan Yayan Mamana ne, a can na yi iftar.
 Amma antyn mu da sai da kin sanar dashi ko a waya ne, ya tayar da hankalin kowa, ya ce in ba a nemo ki ba akan mu zai wuce. Nayla mamaki ya cika zuciyarta jin wai ya tayar da hankali, kafin ta yi magana Tk ya ce,  kuma an kiran ki bakya Wauka.

Nayla ta ce,  Ina can cikin ´an uwa wayar ma tana cikin jakata har yanzu ban Wauko ba. Tk ya ce,  Gaskiya Antyn mu kin Waga mana hankali, kin san Boss ya tara ma™iya da yawa tsaf wani zai cutar take, don Allah ki daina nisa haka babu sanarwa. Nayla tayi murmushi ta ce,  to ku yi ha™uri, in sha Allah baza a sake ba.

Goje ya ce,  dole mu karSi ha™urin ki Antyn mu, kawo key Win. Ba musu ta bashi ta ce,  Na gode. Daga haka ta shiga cikin gidan tana mamakin meyasa ya tayar da hankalinsa dan bata dawo ba?.

Tana shiga falon dashi suka haWa ido, sai ya Wauke kai kamar bai ganta ba amma ya amsa sallamar da tayi. Nayla ta ™arasa nesa dashi ta kalle shi ta ce,  an sha ruwa lafiya?. Banza ya yi mata bai amsa ba. Da yake ta saba kwana biyu yana amsawa sai ta sake kallonsa taga ya wani basar kamar basarake, daman marocon jallabiyya ce a jikinsa mai zubin al™yabba, ya hakimce ya Wora ™afa kan Waya sai ya koma tamkar yarima. Nayla ta ce,  na biya gida Abba ne a can muka sha ruwa gabaWayan mu shiyasa ban dawo ba.

A ™ufule ya kalle ta ya ce,  Wani ya damu da zuwan ki da dawowarki ne? Kin ji na ce ina kika je?. Samun kanta ta yi da yin murmushi jin abinda ya ce ta ce,  A a, sanin baka damu ba shiyasa ma ban faWa maka zan je tana faWa ta bar wajan da sauri kar ya make ta, dan yanayin da yayi magana ya nuna mata kamar ba a daidai yake ba.

Tsaki ya yi cike da jin haushi, ya rasa meyasa ya damu da rashin dawowarta da wuri har haka, gabaWaya ya bi ya Waga hankalinsa sai ka ce Didi ce ta Sata. Tsaki ya sake yi ya kalli inda ta bi, ya sauke numfashi tunawa da ta dawo kuma lafiya lau take babu abinda ya same ta. Ido ya lumshe ya buWe ya tuna murmushin da tayi kafin ta bashi amsa. Gashin kansa ya shafa ya sake yin tsaki ya mi™e ya bar falon.

Nayla kuwa da fara a ta shiga ciki tana tuna abinda Bash ya ce mata akan Waga musu hankalin da Omar ya yi, dariya tayi tunawa da ya ce in basu nemo ta ba akan su zai huce. A bayyane ta ce,  kenan dai ya damu dani har haka? tayi juyi a kan gado ta girgiza kai ta ce,  tunda har ka damu haka wallahi sai na saka ka magantu da kan ka, Allah ya kaimu bayan sallah ta faWa da fara a tana cigaba da murmushi.

Sai a wannan ta Wauko wayarta daga jaka, a lokacin kiran Didi ya shigo ta Wauka ta saka a kunne Didi ta ce,  Ya Allah! Nayla ina kika shiga Ina ta kira bakya Wauka? Omar gabaWaya ya Waga min hankali, wai baki dawo ba shi bai san inda kika tafi ba.

Wani daWi ya sake mamaye zuciyar Nayla ta ce,  Didi ina gidan Abba fa, a can na sha ruwa gabaWaya har su Mama da ´an gidan Baba.
 Amma bai sani ba ko?.
 Eh bai san zan je ba, daga wajan aiki na wuce.
 Amma da kin sani koda a waya kin sanar dashi.
 Didi shine fa ya ce duk inda zan je bai dame shi ba, cewa yayi naje lahira ma ai ba a kansa nake ba, shiyasa na yi tafiyata ta ™arasa faWa da shagwaSa harda turo baki. Didi tayi dariya ta ce,  ai kam ya dame shi wallahi, sai cewa ya yi yanzu wani abun yana samun ki zan fara yi masa faWa ina cewa baya kula dake shiyasa ya ke so ya san inda kika tafi.


Nayla tayi dariya ta ce,  To yanzu ma da na dawo ina faWa masa inda naje ko kallon kirki ban ishe shi ba, da ya gama shan ™hamshi sai cemin ya yi ya damu da inda naje ne. Didi tayi dariya sosai ta ce, ban taSa ganin Wan rainin hankali kamar Omar ba, amma zamu kama shi hannu biyu. Nayla ta yi murmushi ta ce,  Didi bara na yi wanka na gaji. Daga nan suka yi sallama ta fito ta dafa ruwan zafi a kettel ta shiga dashi banWaki ta yi wanka cikin karsashi da farin ciki.

Bayan ta shirya ta fito sanye da hijjabi ta Wauki ruwa a falo yana zaune a falon yana duba wani littafi. Tv a kunne take, ta tabbatar ba shi ya kunna ba sai dai in tun safe take a kunne dan ta kunna da safe kafin ta fita, kuma da ta dawo bata lura da tv ba. ˜arasowa tayi zata kashe aka fara tallan company sa da ta bayar a tashar. Kallon sa tayi sai ta ga ya Wago ido yana kallon tv fuskarsa cike da mamaki mai yawan gaske. Tsayar da idanunsa yayi cak ganin komai ana haskawa harda number wayarsa a cikin numbers Win da aka bayar.

Waya ya Wauka ya kira Bash yana Wauka ya ce,  Zo abinda ya furta kenan ya yanke wayar yana sake kallon tv Win. Lokacin an gama tallan Nayla ta kashe tv a sanyaye ta san shikenan asirin ta ya tonu, fata take Allah ya raba su lafiya kar ya yi mata wani abun. A hankali ta bar wajan ta shiga kitchen ta ji an buWe ™ofa alamun Bashir ya shigo.

 Yaushe aka bada talla a wannan tashar? Ya faWa tana nuna tv, Bash ya kalli ya ga tv a kashe take ya sake kallon Boss Win nasu da yake kallon sa. Bash ya gane abinda yake nufi hakan ya saka ya ce,  Tiger ai tun farkon watan nan aka bayar. Ya zuba masa idanu yana binsa da kallon mamaki ya ce,  da izinin wa? Kuma waye ya ce ayi?. Bash ya Wan ruWe saboda idanun Boss Win nasu abin tsoro ne ya ce,  Da izinin Antyn mu, itace ta ce ayi.
 Wace haka?.
 Matar gidan nan ya bashi amsa a hankali.

Numfashi ya fesar ya yi masa alama da ya tafi Bash ya juya ya fita a lokacin Nayla ta dawo falon ya juyo yana kallonta.KRB3P013
Arewabooks@nanahaleema11.


Nayla ganin ya juyo ya zuba mata idanu sai ta firgita jikinta ya fara rawa saboda tsoron da ya tsirga mata lokaci guda. A hankali take ™o™arin Soye tsoron amma ta kasa sai da ya bayyana akan fuskarta, takawa ta fara yi da niyar barin wajan ta ji muryarsa ya ce,  Zo.

Cak ta tsaya jin abinda ya ce ta kulle ido ta buWe ta dawo a hankali hannunta ri™e da mug na tea ta zauna a kan kujera. Shiru taji bai ce komai ba hakan ya saka ta Wago ido ta kalle shi sai ta samu kallonta yake yi kamar mai son gano wani abu a tare da ita.

Suna haWa ido ya Wauke idonsa da sauri kamar irin wanda aka kama yana kallo ba tare da ya so an ganshi ba. Ajiyar zuciya ya yi ya ce  meye ma sunan ki?. Jin abinda ya ce ya saka ta wara idanu bata san tayi ba tana bin fuskarsa da kallo jin rainin hankalin da ya yi mata.

Wai meye ma sunan ki, ita yake kallo yake tambaya meye sunanta dan bata da matsayi da mahimmaci a wajansa? Tana matsayin matarsa amma ya tsareta yana yi mata irin wannan tambayar ta rainin wayo. Cikin ™aramin lokaci wannan nishaWin da ta yini dashi ya gushe, ta ji babu daWi a zuciyarta.

Omar ganin tayi masa banza bata amsa ba ya ce,  Bana tambaya na sake maimaitawa, ki ri™e wannan. Nayla ta daure a hankali ta ce,  Ai na ga ka san sunana shiyasa ban ce komai ba. Idanu ya fiddo waje yana girgiza kai yana ayyana lallai yarinyar nan ta fara raina shi, dan yana shiga lamarinta yanzu har ta samu damar faWa masa haka?. In less than two seconds ya koma Tiger na asali wanda ta sani, ya sake tamke fuska matu™a a kausashe ya ce,  Koma meye sunan naki bai dame ni ba, waye ya baki izinin bada talla a gidan tv?.

Nayla tayi shiru bata ce komai ba, shima bai sake magana ba amma tana jin irin kallon da yake jifanta da shi a jikinta, tana jin kaifin idanunsa a jikinta kamar shigar allura cikin tsokar naman jikinta. Wannan yanayi da take ji ya saka ta ce,  Babu kowa.
 Na ce miki ina da bu™ata ne?.
 Baka ce ba.
 Meyasa ki ka yi?.
 Haka kawai ta bashi amsa a hankali dan wallahi a tsorace take, bata jurewa zama a inda yake ko kaWan, yanzu sai ta fita daga nutsuwarta.

 Ba a yin abu haka kawai dole akwai dalili, meye dalilin?. Nayla kamar zata yi kuka ta ce,  na faWa maka babu komai.
 Karya ki ke! Ya faWa kai tsaye ba tare da ya kalle ta ba. Nayla ta ji babu daWi a zuciyarta musamman yadda ya ™aryata ta lokaci Waya, ta kawar da kai a raunane ta ce,  Nayi ne dan na taimakawa kasuwancinka ya sake zuwa inda ba a yi tunani ba, bayan wannan babu komai.

Gira ya Waga zuwa sama yana taSe baki ya ce,  a matsayinki na wa kenan?. Šago ido tayi a lokacin da suka fara tara hawaye ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba, kafin ta janye idanunta ya kalle ta suka haWa ido ta sake mayar da kanta gefe. Hawayen ya sakko kan kuncinta ta goge ta ce,  A matsayina na ´ar uwarka musulma. Kuma kana matsayin Yayana, tunda ™anin Didi ne kai ta faWa a sanyaye.

 A a ni bani da ™anwa a duniya, iyayenmu mu biyu kawai suka haifa daga ita sai ni, ba a lissafo ki a cikin wanda suka haifa ba balle ki zama ™anwata. Gwara ki barshi matsayin ´ar uwa ta musuluncin, amma ba wai Yayanki ba. Ya faWa da wata irin murya mai nuni da gaskiyar sa yake faWa mata.

Nayla ta yi murmushin takaici bata ce komai ba, amma jin zuciyarta take tana bugawa sosai. Omar ya share ta kamar bazai yi magana ba kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce,  ko ita Didin baki san sai da izinina take shiga abinda ya shafe ni ba, balle ke mai kalen ´ar uwarta ce?. Zuwa lokacin hawayen da take ri™ewa ya fara sakkowa kan kuncinta. Omar ganin tana hawaye ya zuba mata ido yana kallonta cikin mamaki, to me yayi mata da zata yi masa kuka? Duka ko zagi ko cin fuska? Raini ne ko kuma wula™anci?.

Murya ya na rawa ta ce,  Allah ya baka ha™uri.
 Ke in ina magana dake kina yi min kuka wallahi wata ran sai na saka kin haWWiye ha™orin ki, sa an ki ne ni?!. Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka ta kuma tsorata sosai ta tuna lokacin haWuwar su a gidan Didi.

 Ni dai ka yi ha™uri kawai ta sake faWa murya na rawa sosai. Ya kalle ta ya ce,  Ko nan gaba ba a shiga lamarina in ba ni na saka mutum ba, ki kuma faWa min kuWin da kika kashe na biya ki. Nayla ta Waga kai alamun gamsuwa ta ce,  ni ba sai ka biya& & 
 Ki faWa min kuWin! Ya faWa a tsawace yana zare idanu. Nayla ta ce,  To& .zan faWa. Sai nayi lissafi na manta.
 Bar nan!. Ai da sauri ta mike tazo wucewa ta inda yake zaune yana facing Winta, tsabar tsoro ™afar center table Win wajan ta jata tayi gaba ta faWa kansa da yake zaune akan kujera.

Babu zato yaji faWuwar ta jikinsa, ya rutse ido da sauri tare da jan numfashi jin lafiyayyen ™hamshin da ya kai masa ziyara hancinsa ya kuma zagaya ko wanne sashi na jikinsa. Nayla kuwa bata banbance a ina take ba sai bayan ta faWo kansa Win sannan ta gane halin da take ciki, da sauri ta mi™e bata iya magana ba ta wuce ciki a guje. Lumshe idanu ya yi bayan ta bar wajan, sai kuma ya ja tsaki tunawa da rainin hankalin da tayi masa kafin ta bar wajan, da kuma daren da ta kai a waje ba tare da ya san inda taje ba.

Nayla da tana shiga ciki ta dinga mita ita kaWai a zuciyarta, shayin da ta haWa ma ta barshi a falon kuma ba iya komawa zata yi ta sha ba. In ta tuna kalmarsa ta meye ma sunan ki yana sakawa taji babu daWi, amma bata bar damuwar tayi mata tasiri ba ta yi kwanciyar ta duk da tana ta tuna abinda ya faru.

Mamakin sa take yi sosai dan yanzu yana iya yi mata magana mai tsaho, duk da ba alkhairi ne yake haWa su ba amma yana yi mata magana har ya amsa gaisuwarta. Sannan bai cika yi mata magana a kausashe ba sai dai ya yi kamar yadda yake magana da Didi ba kamar farkon zamansu ba.

Washe gari ma da ta tashi daga aiki saloon Win jiya ta wuce aka yi mata black henna sannan ta shiga store tayi siyayya dan akwai abinda take so tayi. Tun daga wannan maganar bata sake ganin sa ba ma gabaWaya, sai dai taji motsin buWe ™ofa da rufewa amma bata sake jin koda muryarsa ba. Tana mamakin rashin amfani da kayan gidan da ba baya yi, hana rantsuwa ta san yana shan ruwa bayan wannan ko lemo bata taSa gani ya Wauka ba duk akwai a fridge sosai har da yourgut amma baya sha.

Ranar ashirin da tara ga watan ramadan ana e gobe sallah kenan kasancewar lahadi ce tana gida a kitchen ta shiga tana ta aiki tun safe. Tayi abubuwa da yawa wanda hakan ya kawo mata gajiya matu™a. Da yake da wuri ta fara zuwa biyar ta gama duk abinda take so. Bashir ta kira a waya ta ce ya zo gida zata bashi sa™o.

Bata san tare suka shigo da Omar ba ta fito da hijjabi tana cewa,  Bashir ance min an kai sa™o Kaduna jiya, ashe& . Maganar ta tsaya ganin sa tare da Omar da leda a hannun Omar Win. Wani irin dumm ta ji a zuciyarta, dan tun ranar ashirin da bakwai bata sake ganin sa ba kwana biyu kenan yau. Tana so tayi masa sannu da shigowa tana tsoron kar ya yarfa ta a gaban Bashir, ta daure ta basar ta ce,  Sannu da shigowa, Bashir Ina zuwa ta faWa a haWe tana komawa ciki ba tare da ta bashi damar amsawa ba.

Kallon sa Omar ya yi alamun ™arun bayani, da sauri Bashir ya ce,  Ta yi min waya ne ta ce na zo.
 Ta yi maka waya!? Ya maimaita zahiri ba tare da ya sani ba dan abin haka kawai ya daki zuciyarsa, wai tayi masa waya. Bashir ya amsa da,  Eh, ita ta kira ni ta ce na zo.

Bai sake magana ba ya share Bashir ya zauna ya buWe masa ledar da ya shigo da ita. Kaya yake sakawa yana haWawa waje Waya yana ware takalma. Omar ya ce,  Ku Wauki wanda ki ke so gida biyu ko wanne. Bashir ya murmusa ya ce,  Godiya mu ke yi Damisa, bayan kayan sallah da kuWin Winki harda takalmi? Allah ya ja da rai ya ji™an su Mama.

A iya baki ya amsa da amin a lokacin ta fito ta ce,  Bashir gashi. Tasowa ya yi ya karSi manya-manyan foil packs har gida biyar. Šaya doya da ™wai ce mai yawa a ciki da wata lafiyayyar liver sauce, Waya irsh potatoes ne aka soya, sai ™wai a kai da aka soya shima, Waya tosted bread ne mai yawa wanda ya sha butter sai ™hamshi yake yi. Daya kuma milk cincin ™anannu mai yawa, na biyar Win kuma lafiyayyar fried rice ce da gasashhiyar kaza guda a kai.

Ta ce,  Ku yi iftar kai da sauran. Murmushi ya yi y ce,  Godiya mu ke Antyn mu, Allah ya biya. Wannan kayan daWi haka? Godiya mu ke yi. Murmushi ta yi ta koma ta zuba lemo da yawa a leda ta kawo ta ce,  ga drink. Ya karSa yana ta godiya kafin ya kalli Omar da kamar bai san me ake yi ba. Bash ya ce,  Damisa Antyn mu ta yi mana kyauta, yau mu ka zan samu yi iftar dan da shan ruwa mu ke yi. Sautin murmushin ta ya ji hakan ya saka ya juyo kamar zai yi magana sai ya fasa ya sake Wauke kai.

Bashir ya sake kallon ta ya ce,  Antyn mu Boss ya yi mana kyauta, an yi

Please Login or Register in order to submit comment