Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunawa da abinda ya faru da ita sai ba™in ciki ya mamaye zuciyarta, tsanar Ashraf ta yi mata dirrar mikiya a zuciyarta. Da™yar ta iya tashi ta kai kanta banWaki ta jima a ciki sannan ta fito. Doguwar riga kawai ta saka ba tare da ta saka komai ba ta saka hijjabi ta tayar da sallah. Jiri taji yana Waukarta a tsaye sai da ta zauna ta iya ™arasa sallar.

Tana idarwa kiran Mum ya shigo wayarta Wauka murya a dashe ta ce, "Mum!." Daga can Sangaren Mum ta ce, "Subahanallah! Daughter me ya same ki? Kar ki ce min kuka kika yi?." Narma ta ce, "Mum bana son zama a nan ni gida zan dawo, bana son zama da Ashraf baya sona ko kaWan."
"Me ya faru?."
"Mum raping Wina yayi" ta faWa murya na rawa alamun kukan zata sake yi. Mum da mamaki ta ce, "raping! Ashraf Win ne yayi raping Winki?."

Narma ta ce, "Eh Mum." Mum ta ce, "Narma! he's your husband fa, dan hakan ya faru baza ki kira shi da raping ba."
"Amma Mum ai ya faru ne without my consent, ya san bani da lafiya bana cikin nutsuwata amma bai iya ™yale ni ba sai da yayi raping Wina. Ya bari na amince mana, ya bari na samu lafiya mana. Ni na gaji bazan iya zaman nan ba Nigeria zan dawo."

Mum ta tausasa murya ta ce, "i'm sorry, yanzu me kike ji?." Narma a shagwaSe ta ce, "my whole body is in pain, I can't event sit properly. Mum I don't think I can stay here anymore" ta faWa a sanyaye cikin sangarta da shagwaSa. Mum ta ce, "ki daina kuka, kin sha magani?."
"Uhum uhum."
"Ina Ashraf Win?."
"I don't know."
"Okay, let me call him to take you out to hospital" Tana faWar haka ta yanke kiran.

Ba jimawa Ashraf ya shigo ya ™araso ya Wuka a gabanta ya ce, "i'm sorry my love, I'm sorry. Tun Wazu nace mu je asibiti kika ™i, yanzu ga Mum ta kira ni tace na kai ki asibiti. Please saboda Mum ki tashi mu je kin ji?." A tausahe yake maganar amma jin maganarsa take yi kamar ta aljanu saboda haushinsa da take ji.

"Please my love!" Ya sake faWa yana kallonta tare da Wagota ta mi™e tsaye. Zare hijjabin jikinta ya yi ya ajjiye ya kalle ta ya ce, "na saka miki kayan?." Idanunta a kulle yake ya kalli kayan jikinta yaga ana hango komai na jikinta. Wajan kayanta yaje ya duba ya Wauko doguwar riga wacce tafi ta jikin ta kauri sai dai itama roba ce. Bai damu ba ya ™araso ya bata ya ce ta saka.

Zame ta jikinta tayi ta fara saka wacce ya bata yana tsaye yana kallonta, lumshe ido yayi yana sake ™arewa surarta kallo da take a bayyane babu abinda ya rufeta. Ashe duk abinda yake gani a cikin kaya yana Waukar hankalinsa ba komai bane, yanzu ne yake ganin asalilin sura da abinda ya aura, dan shi kam surarta ya aura dan ba ™aramar sha'awarta yake yi ba. Babu abu mai Waukar hankali a jikinta kamar ™ugunta, hips Winta a cike yake sosai ga wrist Win nata Wan ™arami kuma siriri hakan ya bawa shape Winta damar fita sosai, in ta juya baya boobs Winta ma abin kallo ne.

Da™yar ya iya kawar da kai ta saka kayan amma ta™i motsawa ™arshe sai dau™ota ya yi suka fito harabar gidan. Da yake akwai mota a apartment Win da suke yana fita ya ajjiyeta ya buWe garage ya Wauko mota sannan ya sake fitowa ya Wauketa ya sakata ciki suka tafi. Koda suka je can ma duba ta aka yi aka bata magani aka saka mata drip dan jikinta ya saki. Bacci ta sake yi shi kuma yana tsaye yana kallon ta cikin tsantsar shau™i da son sake kasancewa da ita a karo na biyu.

" " " " " " " "

        Da daddare hankalin Nayla sam baya jikinta kasancewar washe gari shine ranar da Abiy ya bata zata faWa masa waye zaSinta. Bata cikin kwanciyar hankali dan bata san abinda zata ce masa ba. Tana zaune a falo tana kallon tv amma ba fahimta take yi ba tunanin ta na ga abinda zata cewa Abiy ya amince da ita. Dan ita dai ta san bata son waWannan mutane, in tace ta Wauki Waya wanda zata iya zaman aure dashi ta cuci kanta ne, kuma kamar yadda Mama ta faWa zata dinga kwasarwa kanta zunubi ne kawai.

Mama ce ta shigo Wakin har ta zauna kusa da ita bata sani ba sai da ta taSata sannan ta kalleta ta ce, "Nayla tunanin me kike yi haka?." Nayla ta sauke numfashi tace, "Mama tunanin gobe nake yi, ban san me zan cewa Abiy akan maganar nan ba."

Mama ta ce, "har yanzu bakya jin zaki iya zama da mutum Waya a cikin su?." Nayla ta Waga kai ta ce, "bana ji Mama, wallahi bana ji gabaWaya." Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "Kawai zan faWa masa akwai wanda ki ke so." Nayla ta wara idanu waje tana kallon Mama da firgici ta ce, "don Allah Mama kar ki faWa masa, in kika faWa masa ya nemi sanin waye shi fa?."
"Sai mu faWa masa waye, in ya kuma kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa da kina sona kuma aurensa kike so ki yi."

Nayla ta fara girgiza kai cikin tsoro ta ce, "bazan iya ba Mama, bazan iya ba wallahi." Mama ta dafata ta ce, "ni zan iya yi miki faWan Nayla, abinda nake so in ya kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa dake shi kike so kuma shi ki ke son aura. Zaki iya ko baza ki iya ba?."

Nayla ta kalli Mama cikin rauni ta ce, "Mama bazan iya ba, bazan iya kallon Abiy na tabbatar masa Ina son Omar ba, bazan iya ba gaskiya." Mama ta ce, "zaki iya, zuciyarki zaki saurara da zarar ya kiraki, kar ki bar harshen ki ya sarrafa kalaman zuciyarki, kai tsaye ki bari su fito daga cikinta ki faWa masa gaskiya, in ba haka ba in ya gano da kansa ransa ne zai Saci sosai."

Nayla ta ce, "Mama gwara ya gano da kansa da ace nice na tabbatar masa." Mama ta dafata cikin rarrashi ta ce, "Nayla bazan taSa bari naga kina son abu ina da damar baki shi ban baki shi ba, sannan bazan taSa bari naga kina shan wahala akan abinda bai fi ™arfin ki ba kuma na zuba miki idanu. Zan iya yin ko meye wajan ganin na samar miki da farin ciki koda ni zai zama silar ba™in cikina. Dan haka ki bani haWin kai Nayla, na tabbatar miki zanyi abinda mahaifinki zai baki abinda kike so ba tare da tashin hankali ba ko wani abun."

Nayla ta kalli Mama cikin gamsuwa da kalamanta ta ce, "Na sani Mama, amma bakya ganin Abiy zai yi fushi dani?."
"Babu fushin da zai yi dake, ki bar komai a hannuna ina tabbatar miki da babu abinda zai faru sai alkhairi." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "To Mama" ta faWa a sanyaye tana wasa da hannunta. Mama tayi murmushi ta ce, matar Omar." Kunya ta bata sai ta rufe fuska da hannunta kafin ta buWe ta ce, "Mama shi fa bai san Ina sonsa ba, taya zan aure shi?." Mama ta yi murmushi cikin shigar kwantar da hankali ta ce, "ke dai ki jira mu gama da Abiy zamu koma kansa." Kai ta Waga kawai bata ce komai ba Mama ta fita ta barta a zaune tana tunani.

    Washe gari a Warare ta shirya ta tafi aiki, ko a can ma haka take yin komai babu kuzari har lokacin dawowar ta gida yayi ™arfe biyar na yamma. Tana ajjiye motarta taga motar Abiy sai da gabanta ya faWi tayi saurin wucewa ciki ta shige Wakin ta harda kulle ™ofar da makulli.

Bayan sallar i'sha kamar yadda Abiy ya saba yana zaune shida Mama bayan ya gama dinner ya kalli Mama ya ce, "ya kuka yi da Nayla? yau ne kwana biyun da na bata." Mama ta fuskance shi sosai ta ce, "maganar gaskiya Nayla bata son samarin nan guda huWu." Abiy ya kalleta cikin mamaki ya ce, "kamar ya bata sonsu? Duka mutane huWun babu wanda take ji zata iya aure?. Wannan ai shirmen ne da rainin hankali, na bata iya lokacin da zan bata kuma tazo min da wannan iskancin?." Mama ta ce, "hmm wani daban zuciyarta take so ba su ba."

Abiy da mamaki ya ce, "wani daban kuma take so? Waye shi?." Tayi ajiyar zuciya ta ce, "Wani ne daban a Kano, babban abin haushi da tashin hankalin ma data buWe baki ta faWa min waye yafi komai Waga min hankali. Kuma wai bai ma san tana sonsa ba, duk wannan rashin lafiyar da take fama da ita cikin kwanakin nan duk saboda shi ne, wannan ramar da tayi da rashin nutsuwa duk akansa ne. In da ace mutumin kirki ne na gari dan tayi haka a kansa ba laifi bane, amma ni har kunyar faWa maka waye nake yi wallahi" Mama ta faWa cikin zallar nuna takaicinta.

Abiy da yake so Mama ta kai ™arshen maganar a ™agauce ya ce, "wa take so? Waye shi ki faWa min bana son zagaye-zagaye." Mama ta Wan yi shiru kafin ta ce, "wannan Wan daban yaron nan da ka yiwa hanya aka fito dashi har suka zo gidan nan godiya. Shi Nayla take mutuwar so, ta tabbatar min da in baka amince ta aure shi ba zata iya barin gidan nan, ta ce min zata iya barin kowa na gidan nan taje ta tare dashi kaWai. Wannan kalma ta tayar min da hankali, nayi rarrashin na nuna mata hakan kuskure ne amma Nayla sam ta kasa amincewa."

Mutuwar zaune Abiy yayi jin kalaman Mama ya zuba mata ido ya kasa cewa komai, Da™yar ya iya tattaro kalaman bakinsa ya ce, "Omar Wan daban Kano take so? Wai maganar nan gaskiya ce ko wasa kike yi min?."
"Wallahi da gaske nake, ita da kanta ta faWa min. Da farko na Wauka wasa ne amma Jidda ta tabbatar min da gaske shi take mutuwar so. Abin haushin ma ko ta ita baya yi, in da na kirki ne ma da sau™i to na banza ne. Wallahi ji nake kamar na yi kuka."

Abiy ya rasa ma abinda zai ce kawai sai ya mi™e ya shiga zuwa cikin gidan ya hau sama har Wakin Nayla ya same ta a zaune tana ganinsa ta firgita ta mi™e tsaye. Kallonta yake yi kamar yadda take kallon sa dan in ba rashin lafiya ba babu abinda yake kawo Abiy Wakinta sai dai in bata da lafiya.

Abiy kallon ta yayi ya ce, "Nayla da gaske ne abinda Maman ki ta faWa min? Da gaske kina son Omar na Kano?." Gabanta ya yanke ya faWi ta Wago ido ta kalli Mama da take gefen ta tayi mata alama da ta amsa ta sake saukar da ido ™asa tare da zube guiwarta duka biyun a gaban Abiy.

Abiy ya ce, "tambayar ki nake da gaske kina sonsa? Da gaske akan sa kike wannan rashin lafiyar?." Nayla ta sake sunkuyar da kai hawaye na zuba a idonta. Mama ta ce, "Abiy ka yi mata a hankali" ta ™araso kusa da Naylar ta ce, "Nayla ki faWa masa abinda yake ranki. Da gaske kina son Omar?." Nayla zuciyarta bugawa take yi sossai, zuwan Mama kusa da sai ya ™ara mata ™arfim guiwar da ta amsawa Abiy tana so Win.

Dafata Mama tayi hakan ya saka tayi ajiyar zuciya ta sake saukar da ido ™asa ta ce, "Da.....gas....ke....ne......Abiy....."ta faWa a rarraebe cikin tashin hankali da tsoro. Abiy ya ce, "da gaske ne me? Da gaske shi kike so?." Ta Waga kai alamun eh. Abiy ya ce, "'magana zaki yi min!." Tsawar da ya yi mata sai da ta tsorata, a firgice ta ce, "Eh Abiy, da gaske shi nake so..." ta ™arasa faWa cikin muryar tsoro da tashin hankali.


KRB2P019

 Hauwa! Abiy ya faWa cikin tsawa yana kallonta cikin Sacin ran jin kalamanta masu kama da rashin hankali ko wacce bata cikin hankalinta. Dumm ™irjin Nayla ya buga, ta wara idanu waje cikin tsantsar tashin hankali da firgici. Tunda take da Abiy bata taSa ji ya kira asalin sunanta ba, koda wasa bai taSa kiranta da Hauwa ba sai dai ya ce Mamana ko kuma Nayla, amma yau gashi ya kira sunanta da murya mai amo mai nuni da tsantsar Sacin ran da yake ciki.

Kasa Wago kai tayi dan yanayin muryar mahaifin nata da taji bata taSa jinta a kausahe haka ba, hakan ya saka ta kasa Wago kai ta amsa kiran da ya yi mata. Abiy ya ce,  kina cikin hankalinki kuwa?. Nayla ta sake sunkuyar da kai kamar ruwa ya cinyeta ko motsin kirki bata so ta yi.

 Wannan yaron ki ke kallona kina cewa shi kike so Nayla? Me ya shiga kaaki ne?. Wannan dalilin ne ya saka kika tayar da hankalin ki a karSo shi daga hannun Senator?. Yadda yake magana cikin murya mai amo ya saka Nayla yin danasanin furta abinda ta ce dan gabaWayata rasa nutuswarta. Abiy baya taSa yi musu tsawa tunda suka tashi, yadda yake yi mata a yanzu ya sakata take ganin abun ba™o shiyasa ya tsoratata sosai.

Mama ce ta kalle shi ta ce,  ka yi mana a hankali Abiy. A fusace ya ce,  bazan yi mata a hankalin ba, yarinya ce ko kuma bata da hankali? Bata san abinda ya dace da wanda bai dace ba ko me?. Duk mazan duniyar nan, duk mazan da suke Kano da wajan Kano ta rasa wanda zata fara so sai ri™a™™en Wan daba wanda aka yi masa shaida mara kyau?. Meye abin so a tare dashi!. Mama ta kalli Nayla da ta kasa motsi ma balle tayi magana, ta kalli Abi zata yi magana ya dakatar da ita ya kalli Nayla ya ce,  Hauwa!.

Nayla murya na rawa ta ce,  Na am Abiy.
 Tunda ta nan ki ka Sullo zan yiwa tufkar hanci, zan sake baki dama ki fitar da mijin aure a karo na uku, in kika sake aikata irin abinda kika aikata yanzu bazan sake baki dama ba har abada. Sannan ki cire batun wannan yaron daga zuciyarki, ba mijin aure bane, in ma bakya cikin hankalinki to ina mai baki shawara da ki dawo cikin nutsuwarki ki san waye a gaban ki! Ya ™arasa faWar maganar da tsawa yana nuna ta da yatsa.

 In da ace ya dace ya kuma cancanci ya zama mijinki zan iya amince miki, amma yanzu ki adana kalamanki bana son sake jin magana irin wannan daga cikin gidan nan, ki Wauka baki san shi ba, ki kuma manta dashi a cikin zuciyarki. Kin ji abinda na ce ko?. Nayla ta Waga kai kafin ta ce,  Naji abiy, zan yi in sha Allah.
 Yafi miki yana gama faWar hakan ya fita daga Wakin ya barta a ita da Mama.

Mama ce ta ri™eta ta mi™ar da ita tsaye ta ce,  ki kwantar da hankalinki komai zai zama daidai nayi miki alqawarin hakan, kar ki damu da kalaman mahaifinki zan san yadda zan yi ya sakko ya fahimce ki. Nayla ta ce,  Mama kawai ki ™yale shi, ni daman sai da nace tsoro nake ji kar a faWa masa kika ce a faWa masa, kinga ransa ya Saci yanzu ni kuma bana son hakan. Don Allah ki ™yale shi kawai Mama ni na ha™ura, zan Wauki mutum Waya a cikin waWancan kawai na huta. Mam ta ce,  kar ki cuci kan ki, kar ki cutar da zuciyarki saboda faWan mahaifinki na yanzu. Zai sakko na yi miki wannan alqawarin, zai amince da auren ki da Omaar kar ki damu.

Nayla dai hawaye take gogewa tana ji zafi a zuciyarta da ta fara son wanda soyayyar sa bata da wani amfani a gareta da cikin rayuwarta baki daya.

Mama fita tayi zuwa wajan Abiy ta same shi a zaune da alama har lokacin ransa a Sace yake sosai ta zauna ta ce,  Lamarin Nayla ya fara bani tsoro wallahi, da gaske sonsa take yi fa. Ka ji irin kalaman fitar hankali da take faWa bayan fitar ka? Ita sai ta aure shi, shine farin cikinta, kalamai dai barkatai. Allah ya kawo mana mafita a wannan lamari kawai.

Sake tunzura zuciyar Abiy Mama tayi ya yi ™wafa ya ce,  Ashe da gaskiyar Senator Sagir da ya ce na bincika anya nima bai yiwa Nayla asiri ba, a lokacin sai nake ganin ba haka bane ashe da gaske dai asirin yake yi, tunda ga Nayla ma tana neman fita daga hankalinta saboda shi.

Mama ta ce,  ni wallahi gani nake ba wani asiri da yake yi, kawai zuciyarsu ce bata yi musu adalci da take fara son wanda bai kamata ma ace ta so ba. Šan shaye-shaye, Wan daba, karen ´an siyasa, wanda ya yi zaman prison, abubuwa da yawa marasa daWi akan mutum meye abin so a wajan?. Allah yasa kar ya shirya ya Wauko ™afa yazo yace yana son Nayla.

Abiy ya yi shiru kawai amma gabaWaya zuciyarsa bata yi masa daWi, sam bai ji daWin kalaman Nayla akan tana son Omaar ba. Meye abin so a Omar don Allah? Me yake dashi da har Nayla ´ar cikin sa zata ji tana so duk wannan tarin abubuwa marasa kyaun da suke dabaibaiye shi?. Tsaki Abiy yayi ya sauke numfashi ya kulle ido amma bai ce komai ba. Mama ta ce,  Ashe daman yawan zuwa Kanon da take yi duk saboda shi ne, wallahi ™unar abinda nan nake ji har zuciyata. Inda mutum ne na gari ma da sau™i, amma irin wannan Wan iskan garin meye amfanin son sa?.

Abiy nan ma bai ce komai ba amma kalaman Mama tuna masa wasu abubuwan suke yi musamman yawan san zuwa Kano da Nayla take dashi, bai taSa kawo haka a zuciyarsa ba amma yanzu ya kawo hakan ya kuma tabbatar da saboda shi take zuwa Kano a kai a kai tunda ma™ocin Hajja. Girgiza kai ya yi kawai ya tashi ya barwa Mama wajan gabaWaya jikinsa ya yi sanyi.

Mama ta yi murmushi ta ce,  Ai indai Ina nan sai Nayla ta auri yaron nan, a gaban idonka Ina tare da kai, amma a bayan idonka ni ce zan dinga zuga Nayla akan Omar. Haba ai dole ma ta aure shi hakan shine zai saka ni farin ciki da kwnaciyar hankali a zuciyata. Ko babu komai na san zata je inda bazata taSa farin ciki ba a rayuwarta, tunda baya sonta itace take sonsa kuma ga yanayin halayyarsa komai zai iya faruwa ta faWa tana murmushi cikin farin cikin cikar burita.

Nayla haka ta kwana ciwon kai saboda damuwa da kukan da tayi, da safe kasancewar Sunday ce babu aiki ta jima tana bacci sai sha biyu na rana sannan ta fito babban falo ta tarar da Jalil yana game a tv. A sanyaye ta ce,  Auta Abiy yana nan?. Kai ya Waga mata ya cigaba da game ta nufi Sangarensa.

Mama ta gani ta fito daga apartment Win Nayla ta kalleta ta ce,  Mama Ina kwana. Da kallo ta bita kana ta ce,  Lafiya lau Nayla. Lafiya naga fuskarki ta kumbura? Kar ki ce min kwana ki ka yi kina kuka?. Nayla ta sunkuyar da kai kafin ta ce,  Mama Abiy yana nan?. Mama ta ce,  ya kwanta sai dai zuwa anjima. Zo mu je ta faWa tana jan hannun Nayla zuwa Wakin ta.

Mama ta kalleta ta ce,  Nayla faWa min kuka ki ka kwana kina yi?. Nayla a sanyaye ta ce,  na dai yi kuka amma ba kwana nayi Ina kuka ba Mama. Mama ta ce,  mahaifin naki ai ya fara sakkowa, shiyasa nake faWa miki indai ina nan zan san abinda zan yi ya amince da auren ki da Omaar. Tunda yaron yanzu kince ya daina abinda yake yi ya kama sana a hannu biyu, to meye aibu? Ai ba a tuna da abinda ya wuce abinda yake faruwa yanzu ake kallo. Yanzu kafin ya kwanta maganar mu ke yi yana tambayata da gaske kina sonsa, na ce kina sonsa mana shine ya ce yana so ya sake tabbatarwa daga bakinki, in kina sonsa sosai zai iya amincewa ki aure shi tunda kina so. Amma in bakya sonsa zai bari ki samu wanda ki ke so.

Nayla ta kalli da sauri Mama ta ce,  Da gaske mama?.
 Da gaske mana Nayla. Ke kin san Abiy yana matu™ar son farin cikinki, zai iya sadaukar da nasa farin cikin saboda naki farin cikin kawai. Dan haka ki daina damun kanki a hankali zai amince kawai ki bashi lokaci. Sannan in ya sake tambayarki akan Omar ki tabbatar masa da Omar shine rayuwarki, rasa Omar daidai yake da rasa ranki. Na tabbatar yana jin haka zai amince miki Wari bisa Wari.

Nayla ta ce,  Amma Mama sai nake ganin kamar bazai amince ba. Ni na ha™ura wallahi, daman shi ma bai san Ina sonsa ba, bai san ina yi ba gwara na auri wanda suke sona da na auri wanda nake so shi ba sona yake yi ba. Ni kawai ki daina masa maganar,in ya tambaye ni zan faWa masa sunan Waya daga cikin waWanda ya ce na zaSi mutum daya a cikin su.
 Kar ki aikata haka, in kika aikata haka daidai yake da kin saka ™afa kin yi fatali da farin cikin ki ne. Na faWa miki Abiy yana son farin cikinki, zai iya yin komai saboda farin cikin ki meyesa ki ke haka? Ko baki yarda dani ba ne?.

Nayla kamar zata yi kuka ta ce,  Mama in ban yarda dake ba da wa zan yarda?. Mama ta ce,  to ki kwantar da hankalinki na faWa miki zanyi duk abinda uwa take yi dan samarwa da Wanta farin ciki a kan ki, haihuwar ki ce kawai banyi ba, amma ni na raine ki har kika kawo yanzu. Kedai ki bani haWin kai ko me nace miki ki yi shikenan komai zai wuce. Mahaifinki zai daina fushi dake, kema zaki samu abinda kike so ba shikenan ba?.

Nayla ta Waga kai ta ce,  To Mama, na yarda dake zan kuma yi duk abinda ki ka ce. Na gode Mamana, ina sonki. Mama ta shafa fuskarta ta ce,  ai ba ke kika Worawa kanki soyayyar ba, Allah ne ya Wora miki kuma shine zai yaye miki. Tunda har Allah ya saka miki soyayyarsa a zuciyarki wata™ila alkhairi ne ga rayuwarki, kar ki ji komai ki Wauka kamar an yi an gama ne.

Nayla ta rungume Mama itama ta rungume tana shafa bayanta ciki sigar rarrashi. Nayala gabaWaya jinta yake wani iri, wani Sangare na zuciyarta ya amince da maganar Mama wani kuma zuciyarta tana rawa a kai. Ta san Mama bazata cutar da ita ba amma ta rasa dalilin da ya saka zuciyarta take rawa akan kalaman Maman ta.

Nayla bata haWu da Abiy ba sai yamma, ta same shi a falo a zaune dashi da yaye ta da ™anenta. Abin mamakin bai nuna mata komai ba sun gaisa kamar ko yaushe, sai taji kalaman Mama sun samu gurbi sosai a zuciyarta, kamar yadda ta ce Abiy ya sakko kenan ya sakko Win tunda gashi sun gaisa hankali kwance bai yi mata faWa ba bai kuma Waure fuska ba. Duk da dai walwalarta ta ragu sosai amma hakan yayi mata daWi yana lura da yadda yake ta murmsmushi amma bai ce mata komai ba.

Abiy bai sake yi mata maganar ba sai ranar talata da daddare tana zaune a falo ita da Mama da Abiy tana cin abinci kasnacewar su Auta sun kwanta saboda akwai makaranta washe gari. Abiy ya kalle ta yana lura da ita cikin kwanakin gabaWaya komai

Please Login or Register in order to submit comment