Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanakin nan sai na samu labarin da ya fi min komai daWi& . Ya girgiza kai yana murmushi ya ce,  matar ka tana da ciki!.

Omar ya zuba masa ido cike da mamaki yana kallonsa. Šan ™aura ya sake girgiza kai yana murmushi ya ce,  ka tuna Damisa? Ka tuna ta silar ka tawa matar cikin ta ya salwanta?. In ka manta na tuna maka, saSanin da muka samu har ya kai ga kun shiga har gida kun tsorata ta ya zama silar zubewar cikin ta, cikin da na ™wallafa rai a kansa ka zama silar da ya zube, cikin da ya kasance daga shi bazan sake samun wani ba har kawo gobe. Daga wannan zubewar cikin bata sake kwana goma a duniya ba ta bar duniyar&  ya sauke numfashi kana ya ce,  na yi fushi da kai, zuciyata tana faWa min na je na huce haushina akan Yayarka. Amma sai ban yi hakan ba, saboda a lokacin baka san zafin matar aure ba, baka san daWin samun ciki a wajan mata ba, ko na Wauki fansa akan Yayarka ba wani damun ka zai yi sosai ba. Ni kuma so nake na saka maka ciwon da bazai warke ba a zuciyarka.

Omar sai a lokacin ya ce,  ka kai ™arshen maganar ka, bana son Sata lokaci kafi kowa sanin haka. Šan ™aura ya yi shewa ya ce,  har yanzu halinka yana nan, nima kuma nawa halin yana nan Damisa. Nazo ne dan na faWa maka lokacin Waukar fansa ta ya zo, lokacin da zan saka cikin jikin matarka ya bi rariya yazo, lokacin da zan saka maka ciwo a zuciyarka ya zo. Na jima ina dakon wannan rana, shekarun da na Sata ina jiran wannan rana basu tafi a banza ba. Ko ta wuya ko ta arzu™i sai na zama silar zubewar cikin jikinta, ina so ka WanWana kaWan daga cikin abinda na WanWana a shekarun baya.

Omar ya yi murmushi yana kallonsa, cikin dakiya da son Soye ruWaninsa ya ce,  da bakin ka ka ce Damisa yana nan da halinsa, ka tabbatar da halina yana nan babu inda yaje. Amma saboda ganganci ni ka kake faWawa wannan maganar?.

 Zan kuma sake maimaita maka, sai na zama silar zubewar cikin jikinta, yadda baka bar nawa ya rayu ba nata ma bazai rayu ba wallahi. Nayi kwantan Sauna ne ina jiran wannan lokaci, gashi kuma yazo. Ka jira ka gani&  ya faWa yana hawa machine Winsa zai tafi Omar ya ce,  In ka fasa baka ™aunar Allah. Šan ™aura ya yi dariya ya ce,  mu zuba ya faWa yana barin ™ofar gidan.

Omar ya kalli su Bashir da suke nesa dasu, ganin ya tafi suka ™araso wajan, Bashir ya ce,  Boss akwai matsala ne?.

Omar ya ce,  daman yana cikin garin nan?. Bashir ya ce,  Šan ˜aura yana nan, wani lokacin kamar yayi wani hankali, wani lokacin ya sake lalacewa. Omar ya Wauke kai baice komai ba amma maganar ta daki zuciyarsa sosai, ya san waye Šan ™aura farin sani, ya tabbatar tunda ya faWa sai ya aikata. Ya sauke numfashi ya aiki Tk ya siyo sa™on Nayla yana tsaye ya kawo masa ya shiga gidan.

Duk yadda yake jin zuciyarsa da rauni haka ya dake ya share maganar ya shiga kamar ba shi ba. Da kansa ya bata abinda ta ce ya siyo mata duk da apple Win kawai ta ci. Da kansa ya canja mata kaya zuwa na bacci ya kwantar da ita a jikinsa. Ya saka hannu a rigarta yana shafa ™asan cikin ta kamar yadda ya saba ko yaushe. A haka Nayla ta yi bacci. Shi kuwa Omar ya kasa baccin, tunani yake yi kar a cutar masa da Nayla da unborn. Ya san waye wanda ya furta, tunda yace wallahi sai ya yi shiyasa yake jin maganar har zuciyarsa. Da™yar bacci Sarawo ya sake shi, da ya motsa maganar ce take faWo masa.

Razananniyar azaba ce ta farkar dashi daga bacci, ya tashi a firgice jin zafi da raWaWi ta ko ina a jikinsa. Yana buWe ido ya ga mutane sama da goma a kansa ko wanne da makami a hannunsa. Hannunsa ya kalla a na yaga ™aton saran da aka yi masa jini yana zuba sosai.

Da gaggawa ya kalli Inda Nayla take ya ga bata nan, kallon Wakin yake yi a fircice ya hango ta a hannun maza guda biyu ko wanne ya ri™e hannunta sun tala hannunta kamar zasu tsinka. Zabura ya yi zai sakko daga kan gadon ya ce,  Jid& . Dukan da aka yi masa a kansa ya saka ya koma ya zauna yana ganin biyu-biyu idanunsa suna kullewa saboda nauyi da azabar da take ratsa cikin ™wa™walwarsa.

Šan ˜aura yana kallom Omar ya ce,  Ba na faWa maka ba? Daman ba nace maka sai na salwantar da cikin jikinta ba? Gani ka ke ™arya nake ko?. Bara ka gani, a kan idonka zan zubar da cikin sannan kuma na kashe ta, na karSo aikin Waukar fansa a kan ka da yawa, kowa ya ce na kashe ta, kowa yace kashe ta shine kaWai fansar da za a Wauka a kanka wacce zata yi maka ciwo da raWaWi a zuciyar ka, tunda sun biya da kuWi mai ni zan kashe ta Win. Sai naga in zaka iya hana ni, in ka isa ka nuna min kai Damisa ne ka tashi ka hana ni! Ya faWa yana kallon Omar da idanunsa suke lumshewa saboda nauyin kai.


Nayla kuka take yi sosai jikin ta yana rawa tana cewa,  YaMar ka taimaka min, YaMar zasu kashe ni, YaMar zasu kashe maka ni!. Wanda suke ri™e da ita Waya ya tsinka mata mari ya ce,  tunda ki ka aure shi ai kin san me kika aura, zaki ba™unci lahira a yau Win nan! Zaki biya bashin da mijinki ya ci yaci kafin ya aure ki. Ba tare da Sata lokaci ba aka fito da ™atuwar wu™a siriri mai kaifi, a lokacin Omar gab yake da suma saboda yadda kansa ya yi nauyi ga azabar da take ratsa ko ina a jikinsa.

 Ku Wago mana da kansa, dan ya shaida an kasheta. Ina so in ya farfaWo ya ji raWaWi da ciwo a zuciyarsa. Suka Wago da kan Omar a lokacin da ya nufi Nayla kai tsaye da niyar kashe ta. Šan ˜aura yana zuwa ya karSi wu™ar ba tare da tausayi ko imani ba ya Waga wu™ar zai soka mata a ciki. Wani irin numfashi Nayla ta ja ta sauke, a daidai laokcin da Omar ya ce,  Jiddaaaaa!. KRB3P087
Nana Haleema.


 Rouhi!. Firgigit ya farka yana sauke numfashi zufa ya gama lulluSe masa jiki kamar Wakin babu fanka. Jikinsa rawa yake yi sosai, tashin hankalin da bai taSa shiga ciki ba ya mamaye masa zuciyarsa da gangar jikinsa. Baya cikin nutsuwarsa ko kaWan, jikinsa rawa yake yi gab gab gab yana zare ido yana kallon Wakin kamar mai son gano wani abun. Nayla tana tsaye tana kallon sa cikin tsoro, daga banWakinta ta ji yadda ya kira sunanta da ™arfi ba shiri ta Wauro towel ta fito, tana shigowa ta same shi jikinsa yana rawa yana juya kai gumi ya gama wanke masa jikinsa.

Nayla ta zauna a kusa dashi ta ce,  YaMar lafiya ka ke? Ta faWa a gigice tana kallonsa ganin kamar a firgice yake. Idanu ta ga ya zuba mata yana kallon ta, har lokacin bai dawo nutsuwarsa ba, a gigice yake kamar zararre. Ganin yadda yake kallon ta sai ta Wora hannunta akan fuskarsa ta ce,  lafiya ka ke?. Kamar ta tuna masa, ya zubura ya jawota jikinsa. Wata irin runguma ya yi mata har yana mi™e guiwarsa akan gadon, yana sake jawota jikinsa yana sake matse ta yana wata irin ajiyar zuciya ya kasa furta komai.

Nayla ta ce,  YaMar ka matse ni ta faWa da™yar jin numfashinta yana neman Waukewa jin yadda ya matse ta. A hankali ya sake ta ya mi™e tsaye ya ri™e hannun ta yana kallon ko ina na jikinta. Nayla ta bishi da kallo ganin yana ™are mata kallo kamar bai santa ba. Towel Win jikinta yake son kwancewa ta ce,  YaMar lafiya ka ke? Me ya faru ne haka? Ta faWa tana ri™e hannunsa ta hana shi kwance towel Win.

Bai saurare ta ba ya cire towel Win, ya zubawa cikin ta ido yana kallo ganin yana nan yadda yake babu abinda ya same ta. Nayla ta Wauki towel Win ta Waura tana kallon yadda yake binta da kallo kamar zararre. ˜o™arin barin wajan tayi da niyar samo masa ruwa ya ri™o hannun ta ya ce,  A a Jidda, kar ki je ko ina, ki tsaya a tare dani ya faWa yana jawo hannunta da hanzari ya sake matse ta a jikinsa yana juya kai a jikinta ya rasa yadda zai sarrafa abinda yake nu™ur™usar zuciyarsa.

Ganin kamar baya cikin hankalinsa sai Nayla ta saka hannunta a bayansa tana shafawa a hankali ta ce,  Shikenan ina tare da kai, ka zauna na kawo maka ruwa ka sha. Bai iya sakinta ba tana ™irjinsa har lokacin yana sauke numfashi a wahale. A hankali ya Wago kansa ya kalli fuskarta, ya ri™e fuskarta da duka hannayensa yana girgiza mata kai. Nayla ta ce,  Rouhi mafarki ka yi?..

Ya kasa bata amsa sai kallon ta da yake yi kawai, ta ri™e hannunsa suka zauna a gefen gadon ta Wora hannunta a fuskarsa ta ce,  ka yi mummanan mafarki ne?.

Bai bata masa ba ya kifa kansa a kafaWarta ya ce,  Kar ki tafi Jidda, kar ki je ko ina. Murmushi ta yi tana shafa kansa da taji yayi zafi tana ™o™arin samar masa nutsuwa. Sai da ta ga ya Wan nutsu har ya Wago daga jikin ta sannan ta ce,  ka taso ka yi wanka ka ci abinci. Naji kanka ya yi zafi, sai ka sha magani. Bai musa ba ta ri™e hannunsa har banWakin, zata fito ya hanata dole ta tsaya har ya kammala suka fito, har ya shirya hannunsa yana cikin nata.

Tare suka fito falo ta bashi tea ta zauna a kusa dashi ko kaya bata saka ba har lokacin towel ne a jikinta. A hankali yake shsn tea Wiin kamar mara lafiya, bayan ya gama ya kwantar da kansa a kan cinyarta yana jin zuciyarsa kamar zata fito waje saboda bugawar da take yi.

Nayla tana shafa kansa a hankali ta ce,  mafarkin me kayi da ya firgita min kai haka?. Ajiyar zuciya yayi yana kwance a jikinta ya ce,  mafarki nayi& .. sai ya kasa faWa, ya tashi zaune ya kalle ta ya ce,  wai ana faWan daba an kashe su Bashir.

Nayla ta ce,  mafarki ba gaskiya bane Rouhi, duk yadda aka yi da zaka kwanta baka yi addu a ba kuma bayan sallar asuba baka yi azhkar ba ko?. Gudun kawar mata da zargi sai ya Waga kai alamun eh, ta ce,  kaga illar kwanciya babu addu a, sannan ka ga illar rashin yin azhkar. Ka kwantar da hankalin ka, babu abinda zai faru. Ya Waga mata kai yana kallon idanunta kamar ™aramin yaro. Ta yi murmushi ta ce,  ™arfin kiran sunana da naji kayi ina wanka na fito babu shiri, ni na Wauka ma ni kayi mafarki an kashe ta faWa tana dariya tana kallonsa.

Wani irin bugawa ™irjinsa yake yi, tsoro da fargaba ya gama mamaye masa zuciya da ganganar jikinsa. Bashi da nutsuwa ko kaWan, ™o™ari yake ya nutsu saboda itama ta nutsu, baya so ta ji maganar shiyasa ya Soye mata dan lamarin ba abinda za a faWa bane, baya so ta dalilin aurensa ta dinga shiga tashin hankalin akan abinda bata ji ba bata gani ba, lokacin da ya aikata bai santa ba. Nayla tayi pecking Winsa a goshi ta mi™e ta shiga Waki.

Da hanzari yabi bayanta, sai ganin sa tayi kamar an cillo shi ya shigo. Ta bishi da kallon tsoro ta ce ,  Anya Rouhi iya mafarki nan ne yake damunka? GabaWaya ka ruWe. Bai ce komai ba ya sake jan hannunta ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a kulle. Nayla ta raba kanta daga jikinsa ya ri™e hannunta har wajan kayanta, da kanta ta Wauko ta saka tana yi tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta.

Tana gamawa ya yi murmushin ™arfin hali ya ce,  zo mu je ki ci abinci. Bata musa ba suka fito falo ta ci abinci tana ci tana kallonsa kamar yadda ya kafa mata idanu yana kallo. Fita yake so ya yi amma bazai iya tafiya ya bar ta ita kaWai ba, yana so ya je ya yiwa tufkar hanci, dan ya tabbatar mafarkinsa zai iya zama gaskiya.

Dabara ta faWo masa ya ce,  kwana biyu baki je gidan Yayarki ba. Nayla da mamaki ta ce,  wace?.
 Mai sunanki.
 Wai Twiny?. Ya Waga mata kai alamun eh.

Nayla ta ce,  nayi niyar zuwa, na san baka son ina fita shiyasa na ha™ura. Da hanzari ya ce,  tashi ki shirya na kai ki. Nayla ta bishi da kallo ta ce,  haka kawai ka ji a ranka kana so ka kaini gidan Twiny?. Omar ya ce,  ba dai kina son zuwa ba?.
 A a bana so ta bashi amsa tana kallonsa. Omar ya ce,  Fita zan yi, kuma bana so na bar ki ke kaWai.

Nayla zata yi magana ya ce,  ki Wauko hijjab mu je na kai ki, in anjima zan dawo da kaina na Wauko ki. Nayla ta dinga kallonsa da mamaki a haka ta Wauko abinda zata Wauko ta fito, da kansa ya ri™e hannunta har mota sannan suka tafi.

Ko a motar hannunsa yana cikin nata, abu kaWan ya kai hannunta bakinsa ya sumbaci hannun ko ya Wora shi akan fuskarsa ko ™irjinsa. Ita dai kallonsa take yi har suka je ™ofar gate Win Twiny. Ya tsayar da motar ya kalle ta ya ce,  kar ki fito ko bakin gate sai lokacin da na ce miki nazo, sannan in kin shiga kina zama a falo ki kira ni ki ce kin shiga.

Nayla ta ce,  Rouhii anya lafiya? Kodai wasu ne suka sake ™o™arin& . Ya Wora hannunsa a bakin ta ya ce,  shiii! Ki yi abinda na ce kawai. Ta Waga kai alamun to. Ya taso daga kan kujerar ya yi kissing bakin ta sannan ya bari ta fita. Shima fita ya yi har bakin gate Win, mai gadin ya buWe mata ta shiga yana kallon ta yana tsaye a wajan. Sai da ta shiga ta kira shi kamar yadda yace sannan ya hau mota kai tsaye ya wuce gidan Didi.

Sai da yaje ™ofar gidan sannan ya kira ta, sai da yaga ta buWe gate Win sannan ya fito daga motar ya shiga ciki. Bayan sun zauna ta ce,  nayi tunanin tare da Nayla ku ke. Ya yi shiru bai ce komai ba ta ce,  Ya dai?. Ya Wan sauke ajiyar zuciya sannan ya ce,  ina Marmerh?.
 Bacci take yi, tana Waki. Me ya faru ne?.

 Didi suna son kashe Jidda ya furta ba tare da ya kalle ta ba. Didi ta dafe ™irji ta ce,  innalillahi wa inna ilaihir raji un! Kuma dai? Me ya kuma faruwa?. Bai Soye mata ba ya faWa mata komai har mafarkin da yayi. Ya Wan yi shiru kafin ya ce,  Hankalina ya tashi Didi, ban taSa jin tashin hankali kamar yadda nake ciki a yanzu. Tunda har abin ya kai ga mafarki mai munin wannan na tabbatar da akwai abinda yake shiryawa. Me cikin ya tsarewa Šan ™aura? Meyasa bazai huce haushinsa a kaina ba sai a kan ciki jikinta?.

Didi ta girgiza kai tana jinjina lamarin ta ce,  To kai meyasa ka zubarwa da matarsa ciki?. Ya kalle ta ya ce,  haka kawai sai na zubarwa da matarsa ciki? Ya akayi ma na san tana da ciki harda zan zubar?. Kawai an samu incident ne har cikin ya fita ta dalilina, amma ni a lokacin ko yatsan hannunta ban jiwa ciwo ba.

 Ya akayi ya san Nayla tana da ciki?.
 Abinda ya Waure min kai kenan, na rasa ta inda ya san tana da ciki har yazo Waukar fansa akan cikin ta.
 alamun ana bibiyar duk abinda ka ke yi kenan, ana bibiyarka itama ana bibiyarta. Babu lallai mutum Waya ne, wata™ila akwai masu da yawa Omar.

Omar ya ce,  na sani Didi, na san hakan zai iya faruwa. Ni na san masu bibiyata domin fansa suna da yawa wallahi. Didi ta sauke numfashi ta ce,  illar cutar da wani kenan a rayuwa, da baka aikata ba da hakan bai faru ba.

 Didi tunda Wal™iya ya saka a kashe Jidda nake nadamar rayuwar da nayi a baya, tunda na ga Jidda da ciwo a hannunta nake danasanin abinda na aikata. Meyasa baza su Wauki fansa a kaina ba? Ai ni na aikata ba ita ba, kuma yanzu ina ruwan cikin da yake jikinta da aka tsallako kansa?.

 Illar dabar kenan ai, wannan gabar da son Waukar fansar da take tsakaninku zata iya zuwa har kan jikokinka wallahi, bama cikin Nayla kaWai ba, har jikan da zaka bari a duniya sakayya zata iya faWa masa. Ka kiyayi sakayya Omar, ka kiyayi ha™™in wanda ka zalunta ba tare da laifin komai ba. Allah yana yafewa bawansa laifin da ya yi masa duk girmansa, amma laifi tsakanin bawa da bawa Allah baya yafewa, sai dai in Waya ne ya yafewa Waya. Itama matar Šan ™aura yake ko waye ai itama ba ita tayi laifin ba, bata san komai ba balle kuma cikin jikinta da bai zama mutum ba. Ka kwashi yara aka je har gida aka yi mata abinda ya firgita ta har ciki ya zube, daga ™arshe ta rasa ranta. Omar in nace ha™™in mutuwar ta a kan ka yake kar ka musa.

Ya girgiza kai ya ce,  A a Didi, babu ha™™in ran kowa a kaina, don Allah ki daina faWa. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  abar tausayin ma Nayla ce ba kai ba, ta auri mijin da sakayya da fansa take bibiyar rayuwarsa ta ko ina. Sau biyu ana ™o™arin kashe ta, yau ga na uku ana so a kashe ta har da Wan cikinta. Wannan aure bai amfana mata da komai ba sai tashin hankali, meye ribar wannan auren don girman Allah?. Ta gaba da baya Nayla bata dace da kai ba wallahi.

Omar ya yi shiru bai ce komai ba, Didi ta ce,  yanzu in aka sake cutar da ita da wanne ido zaka kalli mahaifinta? Wancan ya samu labari ya yi shiru bai ce komai ba, ya sake faruwa nan ma bai ce komai ba. Kana tunanin in ya sake faruwa zai yi shiru?. Omar bai ce komai ba ya sake yin shiru yana jinta. Didi ta ce,  Omar domin ceton rayuwarta da rayuwar abinda yake cikinta me zai hana baza ka sake ta ba?. KRB3P088
Nana haleema

Wani irin kallo yake yi mata mai kama da baki da hankali, ya buWe ido yana sake kallon ta dan ya tabbatar tana cikin hankalin ta kuwa. Didi ganin kallon da yake mata sai ta buWe baki zata yi magana ya dakatar da ita cikin fusata ya ce,  da ina da wani wajen da zan je a bani shawara wallahi bazan zo wajan ki ba, a ko yaushe sai kin Sata min rai akan duk maganar da na kawo miki. Ni ki ke kallo ki ke cewa na saki Jidda? Ni ne zan sake ta?. Anya baza a kai ki asibitin mahaukata a buWe miki file ba? Dan wannan kalaman na ki bai yi kama da aikin mai hankali ba!.

Didi ta Wan yi murmushi dan wallahi dariya ya bata, ta ce,  Ni ba haka nake nufi ba, saboda ceton rayuwarta shiy..! A fusace ya katse ta ya ce,  shiyasa ki ke kallona kina cewa na sake ta? Ko kunyar idona baki ji ba ni ki ke faWawa haka Didi?. Kin ce aurena bai amfane ta da komai ba sai tashin hankali nayi miki shiru ban tanka ba, kince bata dace dani ba shima na share ban ce komai ba. Yanzu kuma idona ki ke kallo ki ke cewa na sake ta? Anya Didi ke jinina ce?.

Bata san lokacin da ta fara dariya mai ™arfi ba, ta kwanta a akan kujera tana dariya dan wallahi dariya ya bata, ko kaWan bata ji haushin kalamansa ba dan inda sabo ta saba. Tsaki taji ya yi, ta san ™arshen abun kuma fita zai yi. Da sauri ta mi™e ta ri™e hannunsa yana niyar fita, ta ce,  Don Allah yi ha™uri, ni ba da wani abun na faWa ba wallahi, bana so a cutar mana da unborn shiyasa na ce haka. Amma ka yi ha™uri bazan sake irin wannan maganar ba, ka dawo ka zauna don Allah.

Hannunsa ya zame ya ce,  bazan zauna ba, dan nazo ki bani shawara ki ka saka ni a gaba kina dariya dan kin mayar dani mahaukaci.
 Naji, ka yi ha™uri mu cigaba da maganar.
 Wallahi bazan zauna ba ya faWa yana Wauke kai. Didi ta ce,  to mu cigaba da maganar a tsaye. Yanzu ya kake ganin za a yi? Wanne mataki za a Wauka akan hakan?.

Banza ya yi mata bai amsa ba, ta ce,  don Allah ka yi ha™uri mu yi magana. Shirun nan bazai amfane mu ba, kar a cutar mana da ita ko abinda yake cikin ta. Omar ya sauke numfashi ya ce,  Meyasa baza su Wauki mataki a kaina ba sai kan Jidda ko abinda yake cikin ta?.

 In aka taSa maka ita sai kafi jin zafi akan a taSa ka, ko me suka yi maka baza ka ji ciwo a ranka ba, zaka fi jin ciwo in aka taSa Nayla ko abinda yake cikin ta. Shiyasa Šan ™auran ya yi jinkirin Waukar fansa, dan yana son ya taSa rayuwarka gaba da baya.

Ya yi shiru bai ce komai, Didi ta ce,  yanzu meye mafita? Zaka je ka samu Šan ˜auran ka bashi ha™uri?. Wani kallo ya yi mata mai cike da harara, Didi ta ce,  eh Omar, abinda ya kamata ayi kenan. Ka je ku yi sulhu hakan zai fi, in aka bar maganar nan bamu san abinda zai faru ba.

Ya gyara tsayuwa ya ce,  Didi kai tsaye akwai wanda ya taSa ce miki baki da hankali?. Dariya ta kama Didi, amma gudun kar tayi ya fita sai ta ce,  a a, ba a taSa ba.
 To yau na faWa miki. Na daina tantama, tsaf aka buWe miki file a gidan mahaukata gado zasu baki. Didi ta karyar da kai tana Soye dariya ta ce,  to na gode.

 Dan mai hankali bazai cewa Omar ya je ya nemi sulhu da wani ™aramin alhaki kamar Šan ™aura, ni zan je na nemi sulhu dashi Didi? To Wal™iya da Kb ban je na nemi sulhu dasu ba sai wannan ™aramin abun da bai wuce na taka shi kamar yadda yake taka ™asa ba. Ni bazan je neman sulhu ba, nafi ™arfin neman sulhu.

Didi ta bishi da kallo, ta Wauka yayi sanyi akan Nayla zai iya watsar da girman kai ya je ya nemi sulhu a wuce wajan ashe da saura. Didi ta ce,  ni

Please Login or Register in order to submit comment