Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, kalli Faruk Wina, look at him Mum" ta faWa tana nuna mata Omar.

Mi™ewa tsaye ya yi ya Wauki Marmerh da take jikin Nayla a zaune, ya ri™o hannun Nayla ta tashi tsaye ya kalli Didi ya ce, "Didi mu je ko?." Mum ta bi shi da kallo ta ce, "wannan ba shine mai company Exclusive footwear ba?."
"Yes Mum, and shine Faruk Wina, ki tambayi Dad shine." Omar ya kalli Didi cikin gajiya da surutansu  ya ce, "Didi mu je!" Ya faWa yana yin gaba, haka kawai ranar yaji ya tsani ganinsu gabaWaya, tausayin Narma da yaji a kwanaki yanzu gabaWaya ya gushe daga zuciyarsa.

Wuce su suka yi yana ri™e da hannun Nayla ita kuma tana tura jakarsa da tata da ta haWesu waje Waya, Didi ma na turata ta. Fuskar Nayla a cushe matu™a Didi ma ta kasa magana, bata so ta nuna ta ji tausayin Narma Nayla tayi kishi, in kuma ta ce bata ji tausayinta ba wallahi ™arya take yi. Ta kuma san halin Omar, indai ba tsananin kiran rabo ba babu dalilin da zai saka ya Waga kai ya kalli Narma, ta san in ya wuce ya wuce kenan baya komawa, shiyasa take jin tausayinta dan ta san soyayyarsa bazata yi mata amfani ba.

A first class flight suka zauna, kujerar Didi ce a jikin taga, sai ta Marmerh da take kusa da ita, sai Nayla sai kuma shi. Kallon Nayla yake yi yadda ta Waure fuska bai taSa ganin ta haka ba, duk sai ya damu saboda ya san ba ita kaWai ba ce akwai babynsa. Har jirgi ya tashi Didi bata san inda suka nufa ba, kuma babu wanda yake magana a cikinsu. Abinci aka kawo ya kalli Nayla ya ce, "baza ki ci ba?." Kai ta girgiza bata ce komai ba.

Ya kalli Didi da take mamakin cabin chew Win da ta gani larabawa, sannan abincin bai yi kama da wanda aka basu a zuwa Abuja ba. Omar ya ce, "Didi ki ce mata ta ci, bata ci komai ba fa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "kici Nayla, duk da ma mun kusa sauka." Nayla ta ce, "bana son ci ne Didi."

Ajiyar zuciya Didi tayi bata ce komai ba, ta san kishi Nayla take yi kuma ya kamata daman ta yi. A gaban idanunka ace ana son mijinka ai sai inda ™arfinka ya ™are. Ita babban farin cikin ta da Allah bai tashi haWa Omar da Sen ba sai da rayuwarsa ta kai wannan mataki na alfahari, wannan abun ya yi mata daWi ta kuma godewa ni'imar Allah. Tana tuna lokacin da suka zo Abuja neman alfarma, ya wula™antata yana cewa gwara dabba a kanta. Amma yanzu gashi shine yake son magana da Omar shi kuma yana ja masa aji, Narman da aka wula™anta shi ta dalilinta gata nan har yanzu haukan sonsa take yi, in ba Allah ba waye zai yi wannan?.

Hannunta ya ri™e ya ce, "wai akan abinda ya faru ki ke fushi?." Ta zame hannunta daga cikin nasa ta ce, "Don Allah ka ™yale ni."
"Bazan ™yaleki ba, meye ya faru da zaki yi fushi ki ™i cin abinci huh? Kin san abinda yake cikinki yana bu™atar cin abincinki."
"Hmm, daman tunda aka samu cikin nan ai ba damuwa ka ke da ni na ci ba, ko yaushe saboda abinda yake cikina ka ke cewa ko yaushe. To bazan ci ba, ai na ga a cikina Wan yake ko? Ka ™yale ni."

Didi ya kalla ta yi masa alama da ya yi shiru, ya Wan yi tsaki kaWan yana kallon Agogo. Didi ta ce, "kai tafiyar nan tayi tsayi, har yanzu ba mu zo ba ne?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "Lagos zamu biya." Didi tayi dariya ta ce, "ki ce kawai yawo muka taho, ko babu komai na shiga jirgi." Nayla ta Wan yi murmushi ta ri™e hannun Marmerh da take kusa da ita.

Duk yadda ya so Nayla tayi magana ta™i, ta kuma ™i kallonsa dole ya ™yaleta har tayi bacci. Didi tana kallonsa yadda yake zuba mata idanu, da yadda zai mata kiss a goshi, da yadda zai du™a yana matsa mata ™afa. Ita dai murmushi take yi kawai dan Nayla ta cancanci a yi mata haka.

Sai da jirgi ya tsaya sannan Didi ta Wan yi mi™a ta ce, "Tafiyar Lagos kusan awa takwas kamar mun bar Nigeria?." Nayla bata ce komai ba suka fito, Didi na ta kallon wajan suka Wauki jakarsu da pusher Win Marmerh. Nayla ta ware pusher ta Wora Marmerh a kai. Didi ta ce, "wai nan Lagos ne? Naga wajan da larabawa sosai."

Sign board Win da aka rubuta welcome to Madina Nayla ta nuna mata ta ce, "ba Nigeria ba ce Didi, kina ™asar saudia, a cikin garin Madina!."KRB3P092
Nana haleema.

Didi ta kalli Nayla ta sake kallon sign board Win ta sake kallon larabawan da suke ta aikin su a wajan. Omar ta kalla ta ga yana murmushi sai ta ce,  Omar yau Nayla na zama abokiyar wasan ta. Ya yi murmushi ya ce,  Didi ba wasa ba ne, wallahi da gaske a garin Madina ki ke. Jin ya ce wallahi ya saka ta tsaya cak ta zuba masa idanu, ta san halinsa indai ya ce wallahi to wallahi Win ce baya rantsuwa akan ™arya kuma baya yi sai ta kama.

Didi ta kalli Nayla ta ce,  Wai da gaske?. Nayla ta mi™a mata passport Win hannunta ta ce,  kin gani, daga Abuja mun taso mun sauka a ina& ? Nayla ta faWa da sigar tambaya tana nuna mata. Didi ta kalli wajan ta sake kallo ta kalli Nayla ta ce,  A Madina nake da gaske?. Nayla ta ce,  Mu je mu hau mota mu je hotel, zan kai ki masallaci annabi, na tabbatar in muka je can zaki gasgata

Ita dai Didi gani take kamar wasa suke mata hakan ya saka ta cigaba da tafiya suka fito wajan airport Win da taimakon Nayla. Zuciyar Didi ta tsinke ganin larabawa a mota, garin kana gani ka san ba Nigeria ba ce ba. Omar ya ga kamar tana jiri ya ri™eta ya ce,  Ki nutsu Didi. Ta kalli Omar ta ce,  kuma son haukata ne kai da matarka, ku daina yi min wasa don Allah.

Omar bai ce komai ba Nayla kuwa har ta gama magana da driver ta faWi inda zai kai su ta kalle shi ta ce,  mu je. Baby pusher in aka naWe aka saka a bayan mota Omar ya shiga gaba Nayla ta shiga baya ita da Didi. Didi ta zama kurma sai kalle-kalle ta ke yi zuciyarta na bugawa sosai, wai itace a Madina dan kawai an raina mata hankali, madinan masallacin gidan sarkin Kano ne da zata je lokaci Waya haka?.

Tafiya suka yi mai Wan nisa kafin su tsaya, Nayla ta Wauko kuWi ta biya ta ri™e hannun Didi ta ce,  Didi zo mu je Hannunta ta ri™e suna takawa Nayla na jan jaka Waya haka Didi ma na ja Omar da Marmerh suna tafiya. Hotel suka shiga Nayla ta zaunar da Didi suka ™arasa reception ita da Omar, Nayla ta nuna musu evidence na rooms Win suka yi reserving da komai suka bata card Win Wakin.

Wajan Didi suka dawo ta kalle shi ta ce,  ka taho da kayan zamu je da Didi, floor 18 ne.
 Mu je tare dai.
 To tsaya na samu empty elevator sai mu shiga gabaWaya, ko da yake lokacin sallar asuba ya kusa da™yar a samu empty. Barin wajan ta yi ta ™arasa wajan elevators ta danna Waya aka ayi sa a aka samu, suka saka kayan ya ri™o Didi suka shiga Nayla ta danna floor 15 suka wuce.

Suka fita daga elevator Win Nayla ta ™arasa wajan Wakin ta saka card Win ya buWe suka shiga da kayan parlor, ta buWe rooms Win ta ga bedrooms biyu ne da parlor kamar yadda ta yi booking. Didi ta kalla da ta zama kurma sai kallon Wakin take yi cikin ruWewa. Nayla ta ce,  Didi mu je ki huta kin gaji. Didi ta kalle ta ta ce,  Nayla kar ku haukata ni don Allah. Kiran sallar asuba aka fara yi, sai Nayla ta ce,  ga kira nan ana yi, Rouhii zamu je sallah ko sai ta huta?. Ya girgiza kai ya ce,  A gajiya ki ke kema, ya kamata ki huta.
 Amma ina so Didi ta fita daga ruWanin nan, gwara mu je kawai. Didi taso ki yi wanka zamu je masallaci na tabbatar miki.

Didi kamar Nayla umarni take bata ta tashi suka shiga Waki Waya daga cikin Wakunan, Nayla ta buWe mata banWaki ta fito da kayanta ajjiye harda sabulun wanka ta ce,  ki yi wanka Didi. Fita tayi ta barta a Wakin, tana fitowa tayi kamar zata faWi ya ri™ota ya ce,  Yi a hankali, kin gaji ko?. Gimtse fuska tayi ta kalle shi ta ce,  ta shiga wanka, nima wanka zan yi ta faWa tana jan jakarta shiga da ita Wakin Didi, ta buWe ta Wauko hijjab da doguwar rigar da zata saka ta fito da kayan a hannunta zuwa Waya Wakin ta shiga wanka.

Tana fitowa daga wankan ta same shi a zaune a Wakin, bata kula shi ba ta saka kaya ta Wora hijjabinta kalle shi ta ce,  Mu zamu wuce. Omar ya bita da kallo ya ce,  Ashiq ba haka muka yi dake kafin zuwa nan ba, kin ce min zaki kula da kanki da lafiyarki, yanzu meye ki ke yi haka? Daga zuwa yau kin canja maganarki. Ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Ni ban gaji ba, kuma sallar asuba kawai zamu yi zan dawo.

Zata fita daga Wakin ya ri™e hannunta ya ce,  Jidda!. Ta tsaya cak bata juyo ba ya ce,  Duk wannan abun na meye ne wai? Duk akan& . Bata bari ya ™arasa ba ta zame hannunta ta ce,  Muna jiran ka in ka shirya mu tafi gabaWaya. Fita tayi ta bar shi ta koma wajan Didi ta tarar har Marmerh ta yiwa wanka tana mamakin kayan da ta gani na Marmerh.

Nayla ce ta ta ™arasa shirya Marmerh ta ce,  Didi mu je. Tare suka fito har lokacin bai fito ba, ta nufi Wakin zata shiga Wakin ya fito ya saka doguwar riga jallabiyya mai kyau da laushi. Ta ce,  ka Wauki key Waya ko da zamu rabu.

Bai tanka mata ba suka fito tare tana ri™e da Didi, Marmerh kuma tana hannunsa suka sake shiga elevator suka sauka zuwa reception suka fita. Da yake babu nisa sosai daga hotel Winsu zuwa masallaci ba jimawa suka ™araso. Didi tunda ta hangi masallacin jikinta yake rawa dan ta tabbatar da gaske ne ba ™arya ba.

Tana saka ™afarta a harabar masallacin ta ji wata faWuwar gaba da wani ™hamshi da bata taSa ji ba, ta kalli Nayla ta ce,  Nayla mafarki nake yi ko gaske?. Nayla ta ce,  da gaske ne Didi, gaskiya ce. Didi bata sake cewa komai ba ta zube a wajan a sume.

Omar ya ™araso da sauri ya ri™e Didi yana kiranta amma Didi ta suma. Da gaggawa ´an agajin masallacin suka ™araso aka saka ta a motar da take yawo a cikin harabar masallacin aka wuce da ita zuwa asibitin da yake can ™arshe a masallaci. Duk tare suke, Nayla tana ri™e da hannunta, ana zuwa aka karSe ta aka kwantar dan taimaka mata.

Nayla ta zauna akan kujerun da aka tanada ta dafe kanta, ya zauna kusa da ita Marmerh tana jikinsa dan ta tashi daga bacci ya ce,  Ashiq don Allah ki nutsu, ki nutsu don Allah bana son wannan yanayin na ki. Kwanciya tayi a jikinsa dan ta gaji sosai kanta ya yi nauyi tana bu™atar bacci. Ri™eta ya yi ba tare da ya ce komai ba, ba su jima da zama ba aka tayar fa i™ama, tare suka fita dashi ya hau sahun maza ta hau na mata bayan ya bata Marmerh suka tayar da sallah.

Shi kansa mamaki yake yi wai yau shine ya yi sallar asuba a masallacin ma aiki, abinda bai taSa kawo shi zuciyarsa ba ko da wasa, sai gashi cikin lokaci kaWan Allah ya yi masa ni imar ziyarar masallacin annabi har ya yi sallah a cikinsa. Sai ya samu kansa da zubar da hawayen rauni da godiya ga Allah, ya goge idonsa ya kalli Nayla da take kallonsa daga can gefe, suna haWa ido ta Wauke kai ya yi murmushi yana mamakin wanann kishin na ta.

Tare suka koma aka yi musu bayanin dalilin suman nata, suka ce sun saba samun irin haka, shau™i ne da farin ciki yake saka mutane suma. Aka tabbatar musu da lafiya lau take ta kuma farfaWo. Tare suka shiga Wakin suka same ta a zaune, Nayla ta ™arasa ta zauna kusa da ita ta ce,  Didi sannu, ya ki ke ji?. Didi ta ri™e hannunta ta kalli Omar da yake tsaye ta ce,  Nayla ya aka yi haka ban sani ba? Ta faWa hawaye yana sakko mata.

Nayla ta ce,  Duk aikin ™aninki ne Didi, ya ce yana so ya baki mamaki ya kuma saka ki farin ciki shiyasa ba ya da bu™atar ki sani, shiyasa da aka faWawa Yaya AbdulHamid aka ce kar ya faWa miki. YaMar ya yi ne dan ki ji daWi ki kuma yi farin ciki, sannan ki san Allah ya azurta shi zai iya yi miki komai dan ki ji daWi.

Kuka sosai Didi take yi cikin farin ciki, ta kalle shi cikin kuka ta ce,  Omar!. Zuciyarsa sai ta karye yaji rauni ya mamaye masa zuciya, ™aunarta da tausayin wahalar da tasha dashi suka zo zuciyarsa, ya tako a hankali ya zauna kusa da ita ya ri™e hannunta guda Waya ta Wora kanta a kafaWarsa tana kuka sosai. A hankali ya ce,  Ki daina kuka Didi, kinga baki da lafiya. Bata iya magana ba ta fi mintina biyar tana kuka kafin ta koma sauke ajiyar zuciya.

Ta Wago ta kalle shi shima ita yake kallo ta ce,  Omar& ! Sai ta kasa magana ya ce,  ba sai kin ce komai ba, don Allah ko yi shiru, ki nutsu mu je ki yi sallah ki huta. Didi ta goge ido ta ce,  Omar na rasa me zan ce, na rasa me zance Omar.
 Ba sai kin ce ba Didi, kawai ki kwantar da hankalinki shine abinda nake so.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta kalli Nayla da take kallon ta itama tana hawaye, ta sake ri™e hannunsu duka biyun ta ce,  Nayla me zan cewa Omar? Da wacce kalma zan yi magana?.
Nayla ta ce,  Didi ba sai kin ce komai ba kamar yadda ya ce, ki zo mu je ki huta a gajiye ki ke sosai. Da™yar suka lallaSa Didi suka fito Nayla na ri™e da hannunta. Kasancewar asibitin indai kana da visa umra ne free ne ba a karSar komai, basu biya komai ba har magani aka bawa Didi.

Didi kallon masallacin take yi tana hawaye, ta sake Wurkusawa a wajan tana kuka sosai. Wai itace a harabar masallacin annabi, to me zata yi in ba kuka ba? Me ya kamace ta in ba kukan ba?. Nayla ta ri™eta ganin ta sake fita daga hayyacinta, ™aramar motar da suka hau Wazu ce ta zo wucewa Nayla ta yi musu magana suka shiga aka kai su ™arshen harabar masallacin daga nan suka ri™e Didi suka koma hotel.

KB3P094
Nana haleema.

Nayla alwala ta saka Didi tayi sannan ta yi sallar asuba. Bayan ta idar Nayla ta ce,  zaki ci abinci ko sai kin tashi daga bacci?. Didi ta ce,  bana jin yunwa Nayla, ba na son cin komai.
 A gajiye ki ke Didi, na san kina jin yunwa. Rouhii bara na sauka ™asa na siyo mata tea. Hannunta ya ri™e yana kallon ta ya ce,  babu inda zaki je, kema ai kina bu™atar ki huta, sai zirga-zirga ki ke yi kin san ba haka mu ka yi dake ba. Zauna ya faWa yana zaunar da ita cikin bada umarni.

Didi ya kalla da take kallonsa ya ce,  Didi don Allah ki bar wannan kukan kin ga ba lafiya ce da ke ba, in kina kuka sai naga kamar baki farin ciki ba. Didi ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, me zata cewa Omar? A ganinta kalaman bakinta sun yi kaWan wajan nuna masa jin daWin ta da farin cikin da take ciki. Tun bayan da tayi aure, Omar ya auri Nayla suka fara zaman soyayya da jin daWi bata da wani buri da ya wuce ta ziyarci Madina. Ko tafiyar da mijinta zai yi sai da taji kamar ta bishi, har ya yi mata al™awari indai yana da rai a shekarar zai biya mata taje. Ga ™aninta da suke ciki Waya ya cika mata wannan burin a matsayin bazata, to in bata yi kuka ba me zata yi?

Ta ri™e hannunsa gam ta ce,  Omar Allah ya cigaba da farantawa rayuwarka, Allah ya kare ka ya cigaba da Waukaka ka zuwa matakin da baka yi tunani ba. Allah ya ji™an iyayenmu, Allah ya raba matarka da abinda yake cikin ta lafiya, Allah ya baka mai faranta maka kamar yadda ka ke faranta min&  ta faWa sabon kuka yana ™wace mata.KRB3P093
Nana haleema.

Omar ya bita da kallo ™auna da tattali, a sanyaye ya ce, "Amin. Ya isa kukan don Allah. Didi in ban miki ba waye zan yiwa? Ke kaWai nake da ita, ke nake kallon a matsayin uwa, uba, ™anwa, ™awa, sannan Yayata. Kece matakin nasarata, kece silar auren wacce nake so, kece silar zuwana wannan mataki. To in ban saka ki farin ciki ba wa zan saka farin ciki Didi?. In dai ina da rai yanzu ki ka fara farin ciki in sha Allah, a yanzu ne zaki san kina da Wan uwa Omar!. Ki nutsu ki daina kuka" Ya faWa yana ri™e hannunta yana kallon ta.

Murmushi take yi tana kuka tana kallonsa ta ce, "tunda nake a duniya ban taSa farin ciki irin na yau ba, Omar ko ranar da nayi aure ban yi farin ciki irin wannan ba. Ni ce Madina har na shiga masallacin Annabi..?. Allah ya saka maka da alkhairi Omar, Allah ya baka abinda ka ke nema duniya da lahira."
"Amin Didi. Indai kina so na san kin yi farin ciki ki daina wannan kukan, sannan ki nutsu ki huta zuwa anjima sai ki koma masallacin."

Ta share hawaye ta ce, "To Omar na daina."
"Kina jin yunwa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "mu je ki huta, kin ga Marmerh har ta sake yin bacci." Da kansa ya ri™e ta har Wakin da ta shiga Wazu, sai da Didi ta kwanta ya dawo ya kwantar da Marmerh a kusa da ita ya kashe hasken Wakin.

Bayan ya fito ya kalli Nayla ya ce, "Ashiq don Allah taso mu je ki huta kema." Ta mi™e ta ce, "zan kwanta tare da Didi." Da yake so yake ta kwanta Win sai ya ce, "To ki je." Sai da ya bita ya tabbatar ta kwanta Win sannan ya iya kwanciya shima.

GabaWaya Didi ta sanyaye masa zuciya, rauni da ™aunarta yake ji a cikin zuciyarsa sosai, ya kuma ji a ransa sai yanzu ya fara rama alkhairi akan wanda ta yi masa. Ta sha gwagwarmaya dashi shi kansa ya sani, bata da nutsuwa kullum saboda Wauko mata magana da yake yi, ta saka shi a gaba tayi kuka amma hakan bazai saka gobe ya ™i yi ba. Mahaifiyarsu ta haife shi ne kawai, amma Didi itace uwa a gare shii. Yana son Didi sosai, yana ™aunar tayi farin ciki, ya san zuwa saudia yana Waya daga cikin burinta na duniya shiyasa ya fara mata dashi. Da wannan tunanin shima ya yi bacci.

Nayla ta riga su tashi lokacin ana gab da yin sallar azahar, ta sauka daga kan gadon ta sake yin wanka ta saka hijjabi ta fita daga Wakin. Ba jimawa ta dawo da abinci da kuma paper cup da ta siyo tea ta zauna tana sha. Motsi ta ji a bayanta, ta juya ta kalle shi ta ga ita yake kallo ya ™araso ya zauna kusa da ita ya ce, "Daga zuwa Madina kuma sai ki canja Jidda?." Šaure fuska ta kuma yi ta kawar da kai gefe ta ce, "Ai kaine ka jawo hakan."

"Da na yi meye Ashiq!?" Ya faWa murya a can ™asa yana kallon idanunta. Ta ce, "Budurwar ka mana." Murmushi ya kubce masa ya ce, "yanzu daman duk akanta ki ke ta wanna fushin?. Kamar mun gama maganar nan tun a baya ko?."

Nayla ta ce, "mun gama kaine ka dawo da ita baya." Ya matso kusa da ita sosai yana jin ™hamshin turarenta murya a ™asa ya ce, "to me nayi? Uhum me nayi kuma?."

"Meyasa baka faWa min kun haWu a airport ba?."
Ya Wan buWe ido ya ce,"Shikenan daman fushin?." Ta harare shi ya yiwa idanunta kiss, ya dawo bakinta ya yi kissing sannan ya ce, "Lokacin na so na faWa miki sai sawun guiwa ya take na ra™umi, da na zo zan faWa miki sai ki ka sanar min da kin karSi ajiyata. Jidda ta ya zan tuna da batun wata bayan ina murna zan zama uba?. Daga nan na manta da batun, amma na so na faWa miki."

Nayla ta shagwaSe fuska ta ce, "to me ta ce maka?." Ya shafi fuskarta ya ce, "Ba ki ji abinda ta maimaita ba? Ni ban nuna na gane ta ba Jidda, kuma na gane ta Win amma kawai bani da lokacinta."

"Amma ita tana da naka lokacin, gashi tana cewa tana sonka zata aureka, Har maahifinta yana zancen yana son ganinka." Ya sake ri™e ta a jikinsa ya ce, "Ashiq!." Ya yi shiru ya zuba mata ido yana jujjuya idanunsa a kanta sannan ya ce, "Baki yarda da mijinki ba ne?."

Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "ki bani amsa." Nayla ta ce, "A'a, na yarda da kai." Omar ba tare da ya daina kallon idonta ba ya ce, "To meyasa ki ke tunanin zan iya amsa kiran mahaifinta ko kuma zan iya aurenta?."

Ta yi shiru bata amsa ba ya kuma cewa, "Ki daina wannan tunanin, ni naki ne ke kaWai kawai. Saboda ke kaWai Allah ya halicce ni, ki amince da wannan maganar da nake faWa miki. Inda ina da ra'ayin aure zan sanar dake, kece ta farko da zan fara faWawa zan yi aure lokaci kaza, ko kiji daWin maganar, ko kar kiji ni dai bani da wanda zan faWawa sai ke Win. Kuma koda ina da ra'ayin auren bana tunanin zan iya aurenta. Jidda in nayi gaba bana dawowa baya, in na ce na bar abu na bari kenan har abada!."

Wasa take da azurfar hannunsa tana shafa gashin hannunsa ta ce, "Amma ai nima ka ce baka sona kuma daga ™arshe ka canja, ka ga itama zaka iya canjawa ai."

"Jidda ke daban ita daban, wallahi ban taSa sonta ba, sai da na fara sonki na tabbatar da ita ba sonta nayi ba Jidda. Ki amince dani, ki bani yardarki bazan ci amanarki ba har abada....." ya matse hannunta a cikin nasa cikin taushin murya ya ce, "Jidda koda zaki ganni da mace a Waki Waya kawai ki tuna da yardar da ki ka

Please Login or Register in order to submit comment