Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin tsane ni kika ce?.
 Eh natsane ka, bana son ganinka ko kaWan.
 Wannan mahaukacin yaron kike so?. Ba tare da shakka ba tace,  eh shi nake so, ganganar jikina kawai kake tare da ita a nan amma zuciyata tashi ce. In ka sake kuskuren zuwa kusa dani zanyi maka illa babba a jikinka.

 Wow! Daman ni ai ganganar jikin naki nake da bu™ata ba zuciyarki ba Narma. Jikinki nake so kuma na riga na mallaka, ko yanzu nace Ina son wani abu a tare dake baki isa ki hana ni ba. Dan yana ri™e da zuciyarki Ina ri™e da jikinki hakan yayi min daidai. Da ki soni, da kar ki soni ni dai ina son jikinki. Narma ta bishi da kallo kamar zata yi magana sai ta fasa ta koma gefe ta harWe hannaye a ™irji bata ce komai ba.

Ashraf ya ce,  this is the last time da zaki sake yi min maganar sa a nan, ni mijinki ne ko bakya so, in kika sake ambatar wancan shashashan mara hankalin a gabana ranki zai Saci matu™a. Harararsa tayi ta ce,  Sai na faWa baka isa ka hana ni ba, kuma kaine shashasha mara hankali amma ba shi ba. I love Faruk! I love him!i love him!! I love him!. In kaga dama ka kashe ni kar ka barni da rai ta faWa tana harararsa cike da jin haushi da tsana.

A firgice ya tako inda take ya na zare mata idanu ya ce,  ni kike kira da mara hankali Narma?.
 Eh na faWa, baka da hankali& .. bata ™arasa ba ya Wauketa da mari mai zafi yana huci. Sai da ta gigice jin zafin marin da yayi mata, in tace tunda take Dad ne kawai ya taSa dukanta lokacin da Omar yaje gidan su bata yi ™arya ba, amma kafin nan iyayenta basu taSa marin ta ba tunda tazo duniya, zata iya cewa babu wanda ya taSa marinta a duniya bayan Dad sai shi. Nan da nan idanunta suka yi ja ta kalle shi ta ce,  ni ka mara Ashraf?.

 Na mare ki, in ki ka sake furta maganar da kika furta wallahi sai na yi miki dukan tsiya a wajan nan.
 Ni Narma ni ka mara? Ta amsa faWa tana kallon sa. Ta Waga hannu zata rama ya ri™e hannun tare da murWa shi baya, tayi ™ara mai sauti tana runtse ido.

Ashraf ya ce,  lallai baki da hankali, ni zaki daka?. Narma ta ce,  to ka sake ni, bana son aurenka, ka sake ni na koma gida bana sonka.
 Nima bana sonki amma bazan sake ki ba, zama dake nake so yi ko dan na mallaki jikinki a duk lokacin da nake so ya faWa yana jawowa jikinsa da ™arfi ya fara kissing Winta da zafi-zafi cike da mugunta. Da faWa da dambe da Asharaf ya samu yaje inda yake so yaje a jikin Narma, tun tana fizge-fizge har ta daina ta koma zubar da hawaye cikin ™unar rai da kuma ™unar zuciya.

Shi kam Ashraf ko a jikinsa, abinda yake so a tare da ita ya samu yana barin wajan yaji gabaWaya haushinta yake ji, abinda yake ji a zuciyarsa gabaWaya ya kau, indai yana jin shau™i akanta to tabbatar akwai abinda yake bu™ata a tare da ita, da zarar wannan bu™ata ta gushe shikenan sai yaji ta fita daga ransa gabaWaya komai tayi baya burge shi. Kallonta ya yi tana kuka yaja tsaki ya fita ya barta a wajan bai ko sake kallon ta ba.

Narma da™yar ta iya mi™ewa ta shiga banWaki tayi wanka ta fito da zazaaSi da ciwon kai. Hannu na rawa tasha shan pracetamol sannan ta Wauki waya hannunta na karkarwa tana neman ticket na Nigeria dan baza ta sake kwana a America ba, gida zata koma duk abinda zai faru sai dai ya faru amma ta gaji.

" " " " " " " " "

Nayla ta shirya tana jiran Baba Salisu yazo su tafi tana zaune a falon Hajja, gabaWaya jikinta babu daWi ji take kamar tayi ihu bata san dalilin faruwar hakan ba. Hajja ta kalleta ta ce,  gashi ba a siyawa Abban naki gurasa ba, ko zaki jira?.
 Hajja ki ™yale shi kawai, ai duk zuwa kina siya masa wannan dan ba a siya ai ba komai.

Hajja tayi shiru bata ce komai ba amma zuciyar ta bata yi mata daWi in taga Nayla a wannan yanayi na damuwa. Babu abinda zata iya, ta tambayeta tace babu komai amma ba dan ta amince ba. Tana zaune ba jimawa Baba Salisu ya ™araso kamar ko yaushe ta kai masa ruwa ya sha yace ba sai ya huta ba tazo kawai su wuce. Sallama ta yiwa Hajja da Salma ta shiga motar suka tafi gabanta yan faWuwa bata san dalilin hakan ba.

Tafiyar awa uku ta kai su garin Kaduna har cikin gidan su Nayla. Yana faka motar ta fito tare da jakar kayanta zuwa cikin gidan. FaWuwa gabanta yake yi abinda bata taSa ji ba in ta dawo daga Kano, ta saba tana jin zumuWin ganin ´an gidan amma yau ta rasa meyasa take ji haka.

Da sallama ta shiga babban falon Mama ce kawai sai Jalila suka amsa mata ta ™araso ta ce,  Mama na dawo. Mama ta bita da kallo ta ce,  sannu da zuwa, na Wauka sai gobe.
 Yaya J ne ya kira ni yana ta faWa ya ce lallai na dawo yau.

Gaisawa suka yi da Mama Jalila ta kalle ta ta ce,  Ashe Abiy bai san kin tafi Kano ba? Bayan kin tafi ya dinga faWa. Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce,  na dawo na bashi ha™uri abinda tace kenan ta mi™e ta wuce zuwa ciki. Sai da tayi wanka tare da yin sallar azahar, tana idar da sallar Jawad ya shigo Wakin nata abinda bai saba ba. Da kallo ta bishi ta mi™e tsaye ta ce,  Yaya J Ina yini.

Harara ya sakar mata ya ce,  Nayla ashe baki da hankali ban sani ba? Ashe ilimin ki bashi da amfani?. Nayla ta sunkuyar da kai duk a tunanin ta akan son da ta ce tana yiwa Omar yake wannan maganar.
 Yanzu Nayla sai ki saka ™afa ki bar Kaduna ba tare da sanin Abiy ba? Guduwa kike son yi saboda an hana ki auren Wan daba ko?.

Ta girgiza kai ta ce,  ba guduwa nayi ba Yaya J, kuma Mama&  dakatar da ita yayi ya ce,  Mama me? Me maman tayi?. Kin bani mamaki wallahi, kin kuma cuci kanki, kin cuci rayuwarki, in kai kanki inda zaki sha wahala. Ba dai kin zaSi Wan daba akan mahaifinki ba? Kin zaSi Wan daba akan mu, kin zaSi Wan daba akan iyalan gidan nan gabaWaya ko?. Shikenan gaki gashi nan sai ki je ki kwaWa soyayya ki cinye, banza mara hankali! ya faWa yana harararta cike da Sacim rai.

Gaban Nayla ta faWi tana tunanin yaushe ta zaSi Omar akan su kuma?. Bata damu da faWan da yake mata ba duk da karo na farko kenan a rayuwarta, ta kalle shi ta ce,  Wallahi Yaya J ni ban zaSe shi na barku ba, taya zan zaSe shi na bar ku?. Ni na ha™ura ma fa, na ha™ura bazan sake maganar ba in sha Allah.
 Ko kiyi min shiru ko na buge miki baki, ha™urar taki me zata hana faruwarsa yanzu kuma? Ai aikin gama ya riga da ya gama. Tunda haka ki ka zaSa gaki ga shi nan ai ya faWa yana fita daga Wakin nata.

Jikin ta gabaWaya ya gama yin sanyi, dana sanin tafiya Kano ya mamaye mata zuciya. Amma Mama ce tace ta tafi ta Wauka zata yiwa Abiy bayani in ya tambaya. Da wannan sanyi jikin ta fito falo. Gabanta ya faWi da ta hango Abiy a zaune yana cin abinci, ga Yaya, ga Yaya J, ga Mama, da kuma Jalila. A hankali take takowa zuwa tsakiyar falon ta zauna akan carpet ta ce,  Abiy Ina yini.

Kallonta yayi yana tuna irin abinda ta sake turo masa cikin wayar, ya kasa yarda Nayla ´ar cikinsa zata iya aikata abinda ta aikata masa akan soyayya, har tana cewa ta zaSi ta zauna dashi akan shi da ya haifeta. Zafin kalaman yake ji a zuciyarsa sosai, hakan ya saka ya kafa mata ido ba tare da ya sani ba. Sai daga baya ya Wauke idanunsa ya ce,  Har kin gaji da zaman Kanon?. Nayla ta ce,  Daman ba zama zanyi a can ba.
 Zaman can ya kama ki kam yanzu ya faWa yana cigaba da cin abinci.

Shiru falon yayi bai ce mata komai ba itama bata ce ba, sai daga baya ya ce,  naga sa™onki, hala dai ke kika rubuta ko?. Nayla ta Waga kai ta ce,  ni ce Abiy. Ka yi ha™uri in na Sata maka rai. Girgiza kai yayi ya ce,  Sata min ran me zaka yi Nayla? ke ki ka zaSi abinda kike so, kuma abinda yake zuciyarki kika faWa min, Meye zai bata min rai a kalaman ki?. Ai haka ki ka zaSa ko? Ya faWa yana kallonta.

Nayla ta Waga kai a sanyaye ta ce,  haka na zaSa Abiy, kayi ha™uri ta faWa kai tsaye tana sunkuyar da kai. Abiy ya girgiza kai cikin tsananin jin zafin amsar da ta bashi, ya kalle ta zai sake magana sai ya fasa saboda abinda yake ji a cikin zuciyarsa game da ita.

Shiru yayi na wani lokaci yana sarrafa zuciyarsa sannan ya ce,  shikenan tunda haka ki ka zaSa ai aikin gama ya gama. Ga Maman ki nan, kuje kasuwa tare duk abinda ya kamata a siyawa amarya ki siya, ki zaSi abinda kike so dan iya yau kawai kike de ita, Gobe zaki tare a gidan mijin ki!. Wani irin yarrrr Nayla taji jin kalaman Abiy da kuma kalmar mijinta da ya faWa, ta Wago ta kalle shi idonta ya ciki da hawaye, Abiy ya Wauke kai daga kallon ta.

Mijinta? Wanne irin mijinta kuma ake zance?. Ko dai Abiy ya zaSa mata miji a cikin masu neman aurenta ne kamar yadda ya ce?. Abiy ya katseta ya ce,  ki tashi kije kasuwa. Mama ta ce,  Abiy siyayya bazata yu a iya yau ba, don Allah ka janye kalaman ka mu zauna a tattauna tukunna. Wannan wanne irin hukunci ne lokaci Waya?. Ya kalli Mama ya ce,  bazan lamunci matar aure ta cigaba da zama a gidana da auren wani a kanta ba.

 Amma Abiy abin yayi kusa, ko sanar da ita ba a yi ba, bata san abinda ya faru ba ka dinga zancen tariya gobe? Wacce irin tariya ce wannan? Wanne irin aure ne wannan?. Babu wanda ya san an yi a dangi, kuma kawai sai a Wauketa akai Kano?.


Abiy ya ce,  Haka nayi niya haka kuma nayi ra ayi, ita ta zaSi mijin ita zata zauna dashi ba mutane ba, dan haka ban ga amfanin sanar da mutane biki ko wani abun ba. Taje ta zauna da zaSinta shine kawai. Mama ta ce,  amma iya yau ya yi kaWan a siyayya, ko dan siyayyar ka ™ara mana lokaci don Allah. Bai ce komai ba yaja kujerar dining Win da yake kai yayi baya ya tashi ya hau shiga Waki bai sake kallon kowa a cikin su ba.

Nayla dai ta daskare a wajan, wai me hakan yake nufi kenan? Kayan Wakin wa Abiy yake nufi za a siyo?. Muryar Yaya taji a bayanta ya finciki hannunta ta mi™e tsaye ya ce,  kin cuci rayuwarki, kin lalata rayuwarki, kin Sata rayuwarki Nayla. Abinda ki ka yi ba kowa kika cuta ba sai kanki, na tabbatar Umma da take kwance a kabari baza tayi alfahari dake akan abinda kike aikata ba.

Nayla da take a firgice ta ce,  Yaya me ya faru? Me na aikata haka?. A fusace ya ce,  au baki san abinda ya faru ba? Na ce baki ana abinda kika aikata ba ko!?. Nayla tana hawaye ta ce,  ban sani ba, wallahi ban sani ba. Ku sanar dani abinda na aikata don girman Allah.

Yaya ya Wauketa da mari cike da ba™in cikin da yake ji a zuciyarsa, Nayla ta fashe da kuka mai sauti, ya ce,  in kika sake furta baki sani ba wallahi sai fasa miki baki, ba dai kin zaSi Wan daba akan mu ba? Kin yi daidai ai Nayla. Kin ji daWi kin fusata zuciyar mahaifinmu, to wallahi bara kiji, duk abinda ya faru a tsakaninki dashi kar ki nemi kowa ki yi kuka da kanki, tunda har kin iya tattara kaya ki bar gida saboda ke ga ´ar soyayya ko?.

Nayla ta kalli Mama tana kuka ta ce,  Mama me nayi? Mama me na aikata ne haka?. Me su Yaya suke faWa wanda bana fahimta ba?. Mama ta bita da harara ta ce,  Nayla kinfi kowa sanin abinda kika yi, kin aikata abinda ya saka ran mahaifinki Saci, kin kuma san Abiy bai iya Sacin rai ba. Sai kije ki shirya kizo mu je ki zaSi abinda zaki zaSa, kina ji ya ce gobe ne tarewarki.

 Tarewata, tarewata kuma Mama? Tare ta a ina kenan? Ta faWa cikin fitar hankali tana kallon Mama. Jawad ya ce,  a gidan wanda kika zaSa mana Nayla, a gidan wanda kika ce shine rayuwarki. Yanzu maganar da nake miki ke matar Omar Wan daba ce, Abiy yaje har Kano da kansa ya Waura miki aure dashi tunda abinda kike so kenan yana faWa yaja tsaki ya bar falon, Yaya ma ya fita dan in ya cigaba da zama da Nayla sai ya Salla ta.

Wani irin yuuuu Nayla take ji a tsakiyar kanta kamar zata kifa, jiri ne yake Waukarta daga tsaye hakan ya saka ta saurin zama ta dafe kai da hannayenta duka biyu, kalaman Jawad suna yi mata amsa kuwa a cikin kunne ta. Aure fa ya ce, an Waura auren mata da Omar, abinda taji daidai ne ko kuma dai ba daidai bane, da gaske ne ko wasa yake yi mata?. Sai kuma ta firgita ta kalli Mama ta ce,  Mama da gaske abinda Ya J ya faWa? Da gaske ne wai ko mafarki nake yi.

 Da gaske ne, yanzu ke matar Omaar ce Nayla. Jiya mahaifinki yaje Kano ya Waura miki aure dashi. Baya tayi zata kifa Allah ya taimaka ta dafa kujera.  Innalillahi wa inna ilahir raji un! Innalillahi wa inna ilaihir raji un! Mama meyasa Abiy yayi haka? Meyasa?. Mama dan na tafi Kano? Mama ba ke kika ce min na tafi Kano ba? Ta faWa a gigice tana kallonta.

Mama ta ce,  ba a kan zuwan ki Kano yake magana ba, bai yanke wannan hukuncin dan kinje Kano ba Nayla, yana da dalili mai ™arfi wanda ni ban san dashi ba. A guje Nayla ta nufi apartment Win Abiy dan yadda take jin zuciyarta kamar zata fito dole tayi magana dashi. Mama ta rufa mata baya zuwa Wakin ta same ta a lokacin da take shiga ta zube akan tiles a gabansa.

 Abiy! Abiy don Allah, don Allah Abiy! Abinda yake furtawa kenan ta haWe hannayenta waje Waya tana kuka sosai. Abiy da ya kalle ta sai ya mi™e ya Wauko sadakinta ya buWe hannayenta da ta haWe waje Waya ya saka mata ya ce,  Sadakin ki na auren masoyinki, kije ki fara shiri gobe zaki tare a gidan sa. Jin kalaman take yi tamkar saukar aradu, ta saki kuWin a ™asa ta ri™e hannun Abiy ta ce,  Abiy don Allah kace wasa kake yi min, Abiy dan na je Kano ka yanke min wannan hukuncin?. Mama& Mam& .tasan zan je Kano&  ta juya tana kallon Mama ta ce,  Mama& baki san zanje Kano ba? Ba ke kika ce min na je Kano ba?. Meyasa ki baki faWawa Abiy ba har ya yi fushi da ni?.

Mam ta ce,  ni nace ki je Kano Nayla? Yaushe mu ka yi haka dake?. Ke kin san ban taSa baki umarnin zuwa Kano ba, Abiy ne yake yanke hukuncin lokacin da zaki je da lokacin da zaki dawo, ni na taSa cewa tafi Kano ki dawo rana kaza Nayla?. Ban taSa ba, kawai kin shiga ruWani ne kike tunanin nace miki kije amma bamu yi haka dake ba. Nayla sakin baki tayi tana kallon Mama jin kalaman da take faWa ta ce,  Mama ta ya zan shiga ruWani akan wannan? Wallahi& . Cikin tsawa Abiy ya ce,  Nayla ki tashi ki bar min Waki! kije can ki zauna da wanda kika zaSa, mu da zaki iya barin mu saboda shi ki barmu kije kiyi zaman ki dashi tunda shine zaSinki. Ki tashi ki fita kafin na saSa miki!.

Nayla kuka take yi kamar ranta zai fita magana take so tayi amma ta kasa bakin ta rawa yake yi sosai, jikinta rawa yake yi cikin tashin hankali. Maganar ta ma™ale ta kasa furta komai, so take ta kare kanta a wajan Abiy amma ta kasa sai rawar jiki da rawar baki. Abiy kukan ta yake ji har zuciyarsa, baya so ya bata wata gaSa da zai ji tausayinta, hakan ya saka ya ce,  ki fita na ce! Jin yadda yayi maganar bata san ta mi™e ba sai ganin ta tayi a bakin ™ofar Wakin jiki na rawa.KRB2P023
ArewaBooks@nanahaleema11

Nayla tana fita daga Wakin Abiy Mama ta ™arasa wajansa ta ce, "kayi ha™uri ka sassauta wannan Sacin ran don Allah. Nayla bata kyauta ba na sani, abinda tayi sam bai kamata ba, taci amanar kauna da soyayyar da ka nuna mata, na tabbatar ko mahaifiyarta da take kabari baza taji daWin wannan abun da Nayla tayi ba. Da me aka rageta dashi a gidan nan? Da ci ko sha ko suttura?Amma ta rasa da abinda zata saka maka sai wannan abun?. Na san dole zaka ji babu daWi a zuciyarka, amma ka yi ha™uri ka kwantar da hankalin ka komai zai wuce in sha Allah."

Kalaman Mama sake hura wutar Sacin rai suke yi a zuciyar Abiy, gasgata maganarta yake yi dan tabbas Nayla bata yi masa halacci ba, tunda mahaifiyarta ta rasu bai taSa bari tayi kukan rashin uwa ba amma da haka zata yi masa sakayya. Tabbas bata kyauta masa ba, ta cutar dashi ta kuma cutar da rayuwarta.

Haka Mama ta dinga lallaSa Abiy da kalamai masu kwantar da hankali tare da kai suka ga abinda zai saka ya sake yin fushi da Nayla. A haka ta samu ya Wan sauka ya ce ta bashi waje bacci zai yi ta fito daga Wakin.

Nayla kuwa lokacin da ta fita daga Wakin da™yar ta iya ™arasawa dakinta tana kuka mai tsuma zuciya. Ta jima tana wannan kukan babu mai rarrashinta, babu mai bata shawara, babu mai faWa mata laifin da ta aikata.  Tun tana kukan cikin daWin rai har kanta yayi bala'in yin nauyi, zuciyarta kam kamar dutse haka take ji saboda nauyi. Lokaci Waya take ji kamar ana zare mata son Omaar Win daga zuciyarta, bata sani ba ko dan bata nutsuwar ta ne, amma gabaWaya ya fita daga ranta cikin ™aramin lokaci.

"Aure fa, aure fa da Omaar Abiy yayi min. To meye dalilin hakan? Me na aikata masa ya yanke wannan hukuncin a kaina?. Wa zan tambaya ya bani amsa?" Ta faWa hawaye na ganganarowa daga idanunta.

Sautin buWe ™ofa taji ta juya taga Mama ce ta shigo ta ™araso inda take ta mi™a mata kuWin ta ce, "yace na tabbatar na baki sadakin auren ki, sannan ki bani number Yayar Omaar Win Ina so zan tambaye ta a gidan da zasu ajjiye ki. Na saka za a kawo kaya gobe ban sani ba ko zasu burge ki, kawai na zaSa ne saboda babu lokaci."

Nayla ta bi kuWin da kallo ta mi™e tsaye tana kallon Mama ta ce, "Mama me na yiwa Abiy ya yanke min wannan hukuncin?."
"Nayla nima ban sani ba, abinda na sani ya dawo jiya ya ce min ya aurar dake ga Omar. To me zan ce masa? Shine ya haife ki Ina da magana akan haka ne?."

Nayla ta ce, "Mama amma ke kika ce naje Kano ko? Meyasa baki faWawa Abiy ke kika tura ni ba?."
"Na tura ki Kano dan a samu mafita ki auri wanda kike so ne ba dan ran mahaifinki ya Saci ba, abinda na lura ba zuwan ki Kano ne ya Sata masa rai ba, akwai wani abun a ™asa da ya saka ransa ya Saci." Nayla ta dafe kai ta koma da baya ta zauna ta ce, "me na yiwa Abiy haka? Bai taSa fushi dani kamar yau ba, me na aikata masa ni Hauwa?" Ta faWa cikin rawar jiki dan zazzaSi ne yake neman kamata.

Mama ta Wauki wayar Nayla ta buWe ta nemo number Didi ta Wauka a tata wayar sannan ta ajjiye mata wayar kana ya ce, "to wai meye na wannan koke-koken? Naga burinki ne na son auren Omar ya tabbata ko? To meye na kukan ke da ya kamata ace kina farin ciki?."

    "Mama Abiy fushi yake yi dani, kuma ni ba ta wannan hanyar nake son samun farin cikin ba. Meye abin farin ciki bayan mahaifina ransa yana "Sace? Meye abin farin ciki bayan kowa haushina yake ji?. Ban san me na aikata ba, ban san me nayi ba!."

"Aikin gama ai ya riga ya gama Nayla, yanzu ke matar Omar Wan daba ce, akwai igiyoyin aurensa guda uku chas akan ki. Dan haka kawai ki yi tawakalli ki karSi ™addara komai zai warware."

Wani haushin Mama taji a zuciyarta abinda bata taSa ji a zuciyarta ba, ta kawar da kai gefe Mama ta fita daga Wakin ita kuma ta cigaba da aikin tunani. Ko Twiny da Salma ta kasa faWawa, gani take wannan ba abinda za a faWa bane gwara kawai taja bakin ta tayi shiru.

Washe gari Ranar Sunday da safe Mama ta siyi kaya aka kawo aka dinga shigo da kwalaye na gado da kujeru. Nayla na sama ta kasa fitowa saboda zazzaSi da ya rufeta ga azabar ciwon da kanta yake yi. Jalila ce ta shiga Wakin ganin yadda take ya saka ta fito da sauri ta samu Abiy da Yaya Jawad a tsaye fitowar Abiy Win kenan ta ce, "Abiy Anty Nayla bata da lafiya." Abiy ya nufi Wakin shida Jawad, ganin yadda Nayla take rawar jiki Abiy ya matsa kusa da ita ya taSa goshin ta yaji yadda yayi zafi sosai.

Jawad ya kalla ya ce, "kira Dr yazo ya duba ta, ka faWa masa zazaabi ne da ciwon kai kuma kuka ne ya kawo shi. Sai ya san da abinda zai zo." Jawad ya amsa yana kallon Nayla nan take sai ta bashi tausayi, yaji tausayinta ya maamaye masa zuciya. A kasalance ya Wauki waya ya kira Dr aka yi sa'a yana kusa ya ce gashi nan zuwa. Suna zaune a Wakin har Yaya ya shigo da Jalila da Mama, Dr yayi waya ya ce gashi yazo Jawad yaje ya shigo dashi.

˜arasowa ya yi suka gaisa da mutanen Wakim kafin ya taSa jikin Nayla. Jin zafin sai da ya tsorata shima, ya haWa allura yayi mata ganin yadda take ta juya kai alamun ciwon kan yake mata sai ya saka mata har da ruwa. Kallon Abiy yayi ya ce, "in ta farka taci abinci ta sha wannan maganin, in sha Allah zata dawo daidai." Abiy ya karSi maganin yayi masa godiya ya fita.

Nayla ta kalli Abiy da yake kallonta cikin jajayen idanunta ta ce, "Abiy kayi ha™uri, kayi ha™uri Abiy. Na fasa aurensa, na amince ka aura min wanda kake so."

Tausayi ta bawa Abiy amma har lokacin bai yi dana sanin abinda yayi mata ba, dan shi kaWai ya san abinda ta turo masa

Please Login or Register in order to submit comment