Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanunsa, ta Wan jure kallon idanunsa na wani lokaci kafin ta janye idon tana kallon ™asa. Kallon abincin ya yi ya ce, "A ina ki ka samu kayan girkin nan?." Nayla ta ce, "siyo min aka yi." Omar ya girgiza kai ya ce, "ba nace duk abinda ki ke so ki faWa min ba?." Nayla ta ce, "gani nayi wannan ba wani abun bane."

"Wani abu ne, daga yau kome zaki siya ki sanar dani." Nayla ta Waga kai alamun to ya saka hannu aljihu ya Wauko ragowar kuWin jikinsa da basu wuce dubu goma ba ya ajjiye mata ya ce, "Wauki kuWinki." Nayla zata yi magana ya zuba mata ido dole ta yi shiru ta Wauka ya ce, "bana son musu, ki ri™e wannan ma." Nayla ta ce, "To."

Abincin da ta ajjiye masa ya Wauka ya jingina da kujera bayan ya Wora ™afa a kan Waya. Ya kalle ta ya ce, "ke bakya ci?." Nayla ta ce, "na ka zan ci." Ga mamakin ta sai ya ajjiye ya ce, "bismillah." Murmushi ta yi ta ce, "Wasa nake yi, yanzu zan ci nawa."
"Ba ki isa ba, zo mu ci tare."

Babu yadda ta iya haka ta dawo kusa dashi ta saka spoon a abincin masa tana ci kamar yadda yake ci. Girgiza kai ya yi ya kalle ta murya a ™asa ya ce, "Abincin ya yi daWi." Farin ciki ya mamaye zuciyar Nayla ta ce, "Na gode." Bai ce komai har suka gama cinye na plate Win zata ™ara ya ce, "ke kaWai." Ta ce, "amma baka ci da yawa ba."
"Ya isa haka" ya faWa yana Waukar wayarsa jin ana kira. Šan tsaki ya yi ya ajjiye wayar ya sake mayar da yatsunsa kan goshinsa kamar ko yaushe.

"YaMar!." Sai da ya lumshe ido sannan ya kalle ta ta ce, "Shagunanka yanzu nawa ne?." Ya ce, "da bakya nan dan buWe guda huWu, shida kenan." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Allah ya taimaka ya sa ka fi haka."
"Amin."
"An fara haWa wanda Abiy ya ce zasu karSa?." Ya girgiza kai ya ce, "An fara, saura kaWan a kammala." Ta sake yin murmushi ta ce, "Allah ya sa albarka."
"amin ya rabbi " ya furta ba tare da ya kalle ta ba.

˜hamshin turarenta ya dame shi, ruWa masa tunani yake yi lokaci Waya shiyasa ko magana baya son yi dan kar ta fahimci yanayin da yake ciki amma ta kasa ganewa, shi kuma yanzu bazai iya yi mata banza ba, in dai zata ce sai ya tanka.

Šan ™aramin tsaki yayi tunawa da wani abu, a  bayyane ya ce, "Na manta." Nayla ta kalle shi ta ce, "'me ka manta?." Omar ya ce, "na so na tashi azumi yau, na manta."
"Azumin meye?."
"Kaffara." Nayla ta kalle shi da mamaki ta ce, "ta meye?."

Omar ya kalli idanunta yana juya nasa idon a cikin nata kafin ya Wauke kai ya ce, "Na yi rantsuwa bazan karSi abinda ya fito daga hannun wanda suka karSi min aurenki ba, na rantse bazan so abinda suka bani ba, na rantse bazan zauna dake ba, sai gashi komai ya canja sama ta dawo ™asa. Abinda na rantse a kan bazan so ba yanzu ita nake yiwa son da ban taSa yiwa wata halitta a duniya ba, ina kasa sarrafa kaina saboda yadda nake jin soyayyarta a zuciyata. Kin ga azumin kaffara ya kama ni. Abin mamaki ba a taSa karya min rantuswa ba sai a kan ki, in Omar ya ce eh baya dawowa ya ce a'a, haka in ya ce a'a ba ya cewa eh. Amma a kan ki na ce a'a yanzu na dawo na eh da babbar murya, canji yana ta zuwa ta dalilinki."

Nayla tayi murmushin jin daWi ta ce, "Naji daWi da na zama ta farko in sha Allah kuma ta ™arshe."
Murmushi ya yi bai ce komai ba Nayla ta ce, "Yaushe zaka fara azumin? Sai na ta ya ka." Kallon ta ya yi ya kulle ido ya buWe ya ce, "zan faWa miki." Nayla ta amsa tana murmushi, ta Wan juyar da fuskarta dimples Winta suka bayyana sosai.

Omar ya bita da kallo, cikin tsaddiyar murya Omar ya ce, "na faWa miki wani abu?." Nayla ta Waga kai tana kallonsa cikin shau™in ™aunarsa, in duk da ba wata doguwar hira suke yi ba, amma in yana yi mata magana cikin salon da yake yi daWi take ji sosai. Omar ya kalli idanunta ya ce, "Ki cigaba da murmushi, murmushi yana yi miki kyau sosai, ki cigaba da yinsa yana sake ™awata fuskarki." Bata san lokacin da ta sake faWaWa murmushinta ba, ta saka hannu ta rufe fuskarta cikin tsananin jin daWi da farin ciki.

Tashi ya yi ya bata wajan, dan in yana zaune kusa da ita bai san irin Sarin zancen da zai dinga yi ba, sai yanzu ya amince da maganar Didi da take cewa daga zuciyarsa maganar zata dinga zuwa kan harshensa, a lokacin da ta faWa ya Wauka faWarta ce, sai gashi kuwa ya ga zahiri.

Nayla da walwala ta tashi ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke ta ajjiye sannan ta shiga Waki ta shiga banWaki. Ba jimawa ta dawo ta Wora ruwan zafi, tana tsaye ya yi zafi ta juye ta kai banWaki ta yi wankan tsarki ta fito tayi sallar azahar da la'asar da suke kanta a lokacin. Babu jimawa aka yi sallar magriba, ta yi sallah ta fito falon dan tana so ta tambaye shi zata je gaishe da Hajja. Ta Waga hannu zata yi knocking ™ofar Wakinsa sai ta tuna ya hanata, sai ta fasa ta murWa handle Win ta shiga da sallama.

Yana tsaye ya fito daga wanka yana Waure da towel kalar blue, ya tattare towel wajan Waurawa dan gabaWaya bai wuce cinyarsa ba. Jikin sai Wigar ruwa yake yi, haka gashin jikinsa ya kwanta ya bi ruwan fatar jikinsa.

Kai tsaye ido suka haWa da Nayla ta yi wata irin zabura ta juya da sauri zata koma ya ce, "kar ki fita, shima wannan na hana ki, ki ri™e hakan." Nayla ta dakata daga fita daga Wakin jikinta na rawa sosai. Ashe jiya ba komai ta gani ba, yau ne ta ga cikakkiyar ™irar da Allah ya yi masa, yadda ruwa ya kwanta a jikinsa ya ™arawa fatarsa haske da wani irin kyau mai Waukar hankali.

Nayla bata yi zato ba ta ji ya juyo da ita ya ri™e kafaWunta yana kallon idanunta da ta kulle da sauri tana kiftawa kamar yadda ta saba. Sakinta ya yayi ya bar wajan, idanunta a rufe ya saka kaya ya zauna akan kujera ya ce, "kin shigo kin rufe ido, baki son ganina ne?." A hankali ta buWe ido, sai taga ya saka doguwar riga mai gajeren hannu ya Wora ™afa kan Waya yana gyara wani kamar zare da yake Waure a ™afarsa wanda ya haska ™afarsa sosai.

Ganin ya saka kaya sai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Daman ina so na je na gaishe da Hajja." Omar ya kalle ta ya ce, "To, in na yi sallah sai mu je tare?" Ya faWa da sigar tambaya. Bata ce komai ba ta juya zata fita ya ce, "Ina zaki je?."
"Šaki" ta bashi amsa a tsorace ya ce, "Nan ba Waki ba ne?." A sanyaye ta ™araso ta zauna a kujerar da take facing Winsa cikin sabon yanayi.

Bai mata magana ba ya gama gyara ba™in abun da yake ™afarsa ya sauke ™afar. Nayla ta bi ™afar da kallo tana mamakin namiji da abu a ™afarsa kamar sar™ar ™afa?. "Meye ya baki tsoro?." Tambayarsa ta ji a sama bata yi tunani ba. Ta daure ta ce, "Babu komai." Bai ce komai ba shima sai ya mi™e tsaye ya fita daga ™akin. Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "abinda baka saba gani ba, namiji da towel a tsaye a gabana, ko a mafarki ban taSa gani ba. dole na ruWe."

Sallah tayi kamar yadda ya fita sallah, bayan ta idar ta saka hijjab dogo har ™asa ya shigo ya kalle ta ya ce, "mu je." Tare suka fito suna tafiya a ™asa mutane suna ta kallon su wasu suna gulma. Ganin ana kallonsa sai ya ri™e hannunta, ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba tayi murmushi suna tafiya hannunsu a sar™e har gidan Hajja.

Itace ta fara shiga ba jimawa ya bi bayanta ya same ta a zaune kusa da Hajja ya shiga sallama. Sallamar da ya yi ya saka suka kalle shi suka amsa Hajja ta ce, "A'a Ummaru barka da zuwa, lallai yau farar rana ce, Omar ne da kansa ba aike ba?." Fuskarsa a Waure take kamar ko yaushe, sai da Hajja ta yi magana ya Wan saki rai amma ba murmushi ya ke yi ba ya ce, "Barka da dare."
"Barka dai Omar, ya gida ya iyali?."
"Lafiya" ya amsa cikin muryarsa ta ko yaushe, cikin aji da ™asaita.

Salma da take gefe ta ce, "ina yi Omar Win Nayla." Bai san ya yi murmushi ba sai da ya ji Hajja ta ce, "Lallai Ummaru, ni da yake ban saka Hauwa'u a ciki ba shiyasa baka yi murmushi ba." Bai ce mata komai ba ya kalli Salma ya ce, "Lafiya." Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru kamar ko yaushe. Kallon falon yake yi yana tuna ranar da aka sanar dashi an Waura masa aure da Nayla.

Hajja ta ce, "Ashe kun je Kaduna, hakan ya yi kyau Allah ya ™ara mu ku zaman lafiya." Dukkan su suka amsa da amin kafin ya mi™e ya ce, "sai anjima." Hajja ta ce. "To Ummaru na gode sosai." Bai ce komai ba ya fita.

Salma ta daki a bayanta Nayla ta ce, "Sai da ke tawan, na rantse da girman Allah gayen nan ya kamu. Ke ni ai ban san haka yake ba sai yanzu, wai daman haka kyaunsa yake fitowa in ya yi murmushi?."

Nayla ta harari Salma, sai kuwa ta sake yin dariya ta ce, "Nayla kishi ko?." Murmushi ta yi Hajja ta ce, "Ni wallahi daman na san auren ku da Omar ba mai rabuwa ba ne ba, da aka ce kun je Kaduna sai na ji daWi na kuma jinjina hankalin Omar Win, dan da ban Wauka yana da hankali da hangen nesa na yin abinda ya yi ba gaskiya."

Nayla ta ce, "Hajja ko ni ban san can zamu je ba sai ganina nayi a gidan, kuma Abiy ya san da zuwan mu." Hajja ta ce, "ya yi ™o™ari, yanzu ko babu komai kuna zaune da albarkar mahaifinki. Allah ya ™ara mu ku zaman lafiya." Suka amsa da amin ita da Salma kafin Hajja ta ce, "tashi ki je ku tafi, naga har yanzu shegen halin na sa dai yana nan." Nayla ta yi murmushi kawai suka yi sallama Salma ta rakota amma baya ™ofar gidan.

Salma ta ce, "na san yana gidansu, ki shiga ni kam na koma. Sai na zo na sha labari, ke wai har yanzu ba a wuce wajan ba? Duk wannan soyayyar ta ido ce babu wani bayani?." Nayla ta harareta ta ce, "akan Jawad." Salma ta ce, "ai ni da shi baza mu Wauki wannan lokacin muna kallon juna ba, da wuri kowa zai san ya Wan uwansa yake."
"Baki da kunya wallahi."

"Eh na ji, Gaskiya zan yiwa Jidda waya mu samo makaman ya™in da zamu ya™i Omar kawai a wuce wajan."
"Ban nema ba, dalla koma gida" ta faWa tana wuce ta tana dariya ita kuma ta koma ciki.KRB3P046
Arewabook@nanahaleema11.

Gidan ta shiga da sallama ya amsa yana fitowa daga falon ya ce, "har kin gama?." Nayla ta ce, "eh." Ta faWa tana kallon tsakar gidan abinda ya faru a kwanakin baya yana dawowa zuciyarta. Bangon da ya rits ta da wu™a ta kalla tayi murmushi ta ce, "A nan wajan ka Wora min wu™a a wuyana, na ga tashin hankali a ranar."

Abinda bata taSa gani yayi ba yayi, dariya taga yana yi sosai har ta waiwayo tana kallonsa duk da gidan babu haske. Suna haWa ido ya tsayar da dariyar bai ce komai ba sai da ya ™araso inda take ya ce, "mu je." Mamakin abinda ya bashi dariya haka take yia haka suka fito suka nufi komawa gida kamar Wazu.

Shi ya buWe gidan ta shiga ya biyo bayanta kamar jira ake ta shiga aka kira wayarta. Bata Wauka ba ta wuce Waki ta canja kaya zuwa na bacci ta fito falon aka sake kiran wayar a karo na uku kenan.

Šauka ta yi kawai sai ta saka a speaker ta yi sallama ta ji muryar namiji ya amsa. Bata kowa komai a ranta ba ta ce, "Waye yake magana?." Daga wayar aka ce, "Hawwa Najib ne, your colleague." Gaban Nayla ya faWi ganin Omar a tsaye a kanta, sai ta Wan ruWe kaWan, amma gudun kar ya kawo wani abun a zuciyarsa sai ta ce, "Najib ya aiki?" Ta faWa tana kallon Omar da yake tsaye har lokacin.

Daga wayar ya ce, "fine. I hope kwana biyu kina lafiya, baki zuwa aiki na tambaya an ce kin Wauki hutu, i hope everything is going well?." Nayla kasa bashi amsa tayi saboda kallon da Omar yake mata, gashi ya dawo kan kujera ya zauna zuba mata ido yana kallo. Sai ta yanke wayar da sauri ta kashe ta gabaWaya, ya zuba mata ido na wani lokaci yana jin zuciyarsa kamar zata fio waje saboda kishi.

Shiru ya ratsa falon na wani lokaci kanta yana ™asa ™irjinta yana bugawa sosai, kallon da yake mata kaWai ta san ta yi laifi ko bai faWa ba. Kanta yana sunkuye ta ji ya ce," daga ranar da abokin aiki ya sauke ki a mota na fara jin zafi a zuciyata, ban Wauki abin da mahimamci sosai ba amma na kasa Soyewa har sai da na yi miki magana. A lokacin da naji Didi tana yi miki maganar samarinki shima na kasa Soyewa sai da nayi magana, wani ya biyo ki ya ce yana sonki na kasa Soyewa shima na yi magana. Da na fahimci da jikinki ake yin talla na ji tashin hankali da Sacin ran da ban taSa jin irin shi ba a duniya, wani abu mai kama da yaji naji yana mamaye idanuna da zuciyata. Duk a lokcin ban san kishi nake ba, ban san haka ake jin kishi ba shiyasa ban fahimta ba sai da aka faWa min. Yanzu da na sani na tabbatar da zafinsa, na tabbatar da raWaWi da ™unar da kishi yake dashi. Ban ga laifin masu illata mutane akan kishi ba, ban ga laifin masu raunata kansu akan kishi ba, ban ga laifin ba su kashe kan su akan kishi ba, domin abinda na ji a zuciyata in aka ce zan iya zama sanadin taSuwar lafiyar wani bazan yi musu ba."

Shiru ta ji ya yi kafin ta ji ya ce, "Jidda!." Gabanta ya faWi sosai, ta Wago a hankali ta ce, "Na'am."
"Raina aurena da yake kan ki ka yi ne?. Abokin aikinki ya dawo da ke daga wajan aiki saboda baki da lafiya, na san lokacin zaki ce ai ba sonki nake yi ba amma matata ce ke. Abokin aikinki ya kira ki muna tafiya Kaduna, har kina cewa kin gode da kulawa, abokin aikinki ya kira ki yanzu yana tambayar lafiya bakya zuwa aiki, Jidda auren ne bashi da mahimmaci ko ni ne bani da mahimamcin?."

Nayla a sanyaye ta girgiza kai ta ce, "ba haka nake nufi....." a tsawace ya ce, "to ya ki ke nufi? In ba rashin mahimamcin ba meye wannan? Raini ko kuma ™iyayya ce!?." Yadda ya yi maganar da tsawa ya saka ta zabura sosai,dan ya dawo mata asalin wanda ta sani. Tsawar ta ratsata, domin kwana biyu ta saba da yadda yake yi mata magana babu tsawa balle tsoratarwa.

Sanin baya so ayi masa shiru sai ta ce, "Ba haka bane ba wallahi, ba abinda ka ke tunani ba ne."
"In ba haka bane meye? Amsa min... meye in ba raini da rashin bawa auren mahimmmaci ba?. Dan kin raina min hankali a gabana ma? Ko dan kin ga ina sonki ne ya saka ki ke tunanin zaki iya komai a gabana?." Shiru ta yi bata amsa ba, a firgice ya ce, "Ina tambayar kin yi min shiru, sa'anki ne ni!?."

Nayla ta fara hawaye tana girgiza kai, ya nuna ta da yatsa ya ce, "in ki ka bari hawayen nan ya sake sakkowa mai raba ni dake sai Allah."

Cak ta tsayar da kukan tana jan numfashi a hankali, ya runtse idanu yana jin wutar kishi tana ruruwa a zuciyarsa. Wai matarsa ce take amsa kiran wayar wani abokin aikinta a gabansa. Ji yake kamar ana gasa masa zuciya, ji yake raWaWin gashin yana zaga jininsa yana kaiwa har ™wa™walwarsa. Nayla ta ce, "Don Allah ka yi ha™uri, bazan sake ba."

"kenan raina ni Win ki ka yi, kin Wauki aurena bashi da mahimmaci a gare ki shiyasa ki ke aikata hakan a gabana ko nauyi na bakya ji. Waya fa har sau biyu a gaban idanuna, kin kyauta" ya faWa cikin tsantsar Sacin rai da yanayi na fushi ya tashi ya bar mata wajan.

Nayla ta ri™e haSa ta ce, "Na shiga uku, ni wallahi ban Wauka ina sane ba, kuma ban shine ya kira ni ba, naji tsoron kar na ™i Wauka a gabansa ya yi tunanin wani abun ne. Yanzu ya zan yi?" Ta faWa tana hawaye. Abinda yake Waga mata hankali znacensa rainin da ya ce da rashin sanin mahimmacin aurensa da yake faWa, shine bata so.

Tsoro zuwa tayi masa magana take yi dan ta san halinsa, yadda ya birkice yana buga mata tsawa ta san in ta je yanzu hargitsewa zai sake yi. Hankalinta ya tashi, gashi bata so ya cigaba da tunanin abinda ya faWa haka ne. Shawarar zuwa ta bashi ha™uri ta yi koda zai zane ta, da wannan tunanin ta mi™e ta nufi da™in a Warare ta shiga.

Yana tsaye ya buWe taga yana kallo harabar gidan, kai da ka ganshi ka san yana cikin Sacin rai sosai, dan har fuskarsa ta komaja. Nayla ta taka a hankali ta ce, "Ka yi ha™uri YaMar, abinda ka ke faWa ba haka ba ne. Wallahi ban raina ka ba, kuma wallahi ina daraja aurena, ina bashi mahimmaci sosai. Kuma ni ban taSa waya dasu ba sai a cikin kwanakin nan, amma don Allah ka yi ha™uri."

Kallon ta ya yi da jajayen idanunsa, yadda idanunsa suka yi ja ya bata tsoro dan fuskarsa ma gabaWaya ta canja kamar ba shi ba. Nayla ta sake ™asa da murya cewa, "Ka yi ha™uri, ka yi ha™uri don Allah. Ban san number waye ba shiyasa na Wauka a ranar da mu ka je Kaduna, yau ma ban san lambar ba shiyasa na Wauka. Don Allah ka yafe min ka daina fushi da ni."

Nan ma bai ce mata komai ba ko kallon inda take ma bai yi ba. Batu na gaskiya ciwo yake ji a zuciyarsa, zafi da radaWi da kuma kishi da tashin hankali yake ji yana mamaye masa ko ina na jikinsa shiyasa ya™i kulata, dan shirun shine alkhairi. A hankali ta tako zuwa inda yake a tsorace dan umarnin zuciyarta take bi tazo inda yake. Ta ja numfashi ta ce, "Ka yi ha™uri ka yafe min, zan faWa musu kar wanda ya sake yi min waya."

Kallon ta ya yi jin abinda ta ce, bata san abinda ta ce Win ma sake bashi haushi ya yi ba. Wai zata ce musu, kenan ma sai ta yi musu magana har su ji muryarta, tsaki ya ja ya share ta bai yi magana ba ta ce, "Don Allah YaMar!."
"Ki fita ki baki waje bana son hayaniya."
"Don Allah ka...." Cikin tsawa ya ce, "ki bar nan na ce!." Firgita tayi ta juya kamar zata tafi, sai ta fasa ta dawo da sauri ta faWa jikinsa ta rungume shi ta zagaya da hannunta ta ri™e bayansa gam tana kuka.

"Ka yi ha™uri, ka yi ha™uri YaMar ka yafe min!"abinda take faWa kenan tana kuka akan ™irjinsa. Kulle ido ya yi ya buWe bai ri™eta ba kuma bai janyeta daga jikinsa ba. Kalmar ha™uri take ta jera masa tana hawaye yana jinta bai ce komai ba. Ta jima a haka tana kuka tana bashi bashi ha™uri, yadda take magana tana kuka a jikinsa ya saka ya runtse ido yana ji kamar ana Wura masa kukan da take yi cikin zuciyarsa. A hankali ya Wan sauka kaWan, ya Wago ta daga jikinsa yana kallon fuskarta da ta ji™e da hawaye gashi ta Wan yi ja kaWan.

Murya a tausashe ya ce "Baki yarda ina sonki ba?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Meyasa ki ke amsa wayar abokin aikinki a gabana? Ko neman aurenki nake yi in ki ka yi hakan a gabana raina zai Saci balle ke matata ce." Nayla ta ce, "wallahi ban sani ba, ban san number ba." Omar ya girgiza kai ya ce, "ya aka yi suke samun number ki? Meyasa suka damu da rashin zuwa aikinki? Sonki suke yi?."

Ta girgiza kai da sauri ta ce, "A whatsApp group na tabbatar suke Waukar numberta, tunda akwai group na ma'aikatan." Omar ya ce, "sonki suke yi kenan?." Ta girgiza kai alamun a'a kafin ta ce, "A'a."

"Meyasa suka damu dake haka?." Nayla ta sunkuyar da kai ganin yana bin fuskarta da kallon da yake kashe mata jiki. Ya Wan kawar da kai ya ce, "baki faWa musu kina da aure ba ko? Saboda aurena ba aure bane ba ko Jidda?." Cikin kuka da shagwaSa ta ce, "Wallahi sun sani, kowa ya san ina da aure, Ka yi ha™uri don Allah."

Ajiyar zuciya ya yi ya kalli window bai kalle ta ba ya ce, "na yi ha™uri ko Nayla? Kin san abinda nake ji da zaki ce nayi ha™uri?." Jin ya fara magana a kausashe ya saka ta sake langwaSewa ta ce, "ban sani ba, amma ka yi ha™uri wallahi ba halina ba ne, in kana ganin ™arya nake ka tura har inda nake aiki a tambaya."
"Hmmm!" Shine abinda ya furta kawai bai ce komai ba.

Barin jikin window ya yi ya ™araso ya zauna akan sofa ya harWe hannayensa waje Waya yana kallon wani wajan daban. Nayla ta ™araso inda yake tana kallonsa bata ce komai ba.

Shiru ya ratsa tsakaninsu, ya zubawa waje Waya bai ce komai ba ita kuma bata yi magana ba. Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "Tun farko na san da maganar aikinki, iyayenki sun faWa min amma a lokacin na ce ina ruwana, in ma duniya zaki bari ba aiki ba bai dame ni ba. Ashe na yi babban kuskure, ashe na yi kuskuren da ban taSa yin irinsa ba a rayuwata. Barin ki kina aiki kamar a ha™a rami ne a binne ni da raina. Amma...." Ya ja numfashi mai tasho kana ya ce,

"Bazan hana ba, bani da wannan ikon na hanaki aiki tunda na san dashi, in na hanaki ma na cutar dake. Amma akwai gabSar da za a zo zaki ajjiye aikin matu™ar kina son zama dani, bazan juri wannan abubuwan a tare da matata ba. Amma a yanzu zan yi ha™uri, na san da batun aikinki tun ba yanzu ba, ban isa na hana ba" ya faWa tana Wan lumshe idanunsa a hankali yana buWewa a hankali. Nayla ta ce, "i'm sorry." Ya kafa mata ido ™irr yana kallon fuskarta, ita kam idanunsa da suka koma ja ya saka ta sunkuyar da kai bata ce komai ba.

"Jidda kin san zan iya tashin garin Kano a kan kishinki? Zan iya fuskantar ko wanne ™alubale akan hakan. Zan iya aikata komai akan kishinki, zan iya...." maganar ma™alewa tayi yana girgiza kai kafin ya ce, "Ki kula!" Ya faWa yana girgiza kai yana cize bakinsa cikin sautin da yake nuna takaicin da zuciyarsa take ciki.

"Ka yi ha™uri!."
"Laifi ki ka yi ki ke bani hakuri!?." Yadda ya yi maganar cikin kaushi ya saka ta Wan yi baya bata ce komai ba.KRB3P47

Omar ya ja dogon numfashi ya kulle ido ya sake jan numfashi ya Wora ™afa a kan Waya ya ce, "laifina ne, ban san abin zai zama haka ba da tun farko bazan amince da aikinki ba. Bazan amince ba!" Ya faWa yana shafa fuskarsa da duka

Please Login or Register in order to submit comment